Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akan ki ina gudun na fara ganin baƙinki, dan Allah ki fita sai zuwa anjima”


Ya faɗa ba tare da ya buɗe idonsa ba. Kwantawa tayi a gurin, sai ya buɗe ido ya kwantar da Sultan gefensa na dama ya juya mata baya. Hakan ya bata damar matseshi sosai ta kurɗo hannunta ta ƙasan haɓarsa ta ɗora shi dai-dai zuciyarsa.


“Namra tana nan Ya Omri kuma tana nan a bayan ka, tun bayan abunda Asim yayi min sai na daina ganin maza a mutane ina musu kallon wani abu daban, amman daga lokacin da na ganka sai na ganka a mutun cikakkensa, kai ne mutumen da ya tsayar da zubar hawaye a lokacin da nake tunanin hawaye ba zasu taɓa tsayawa ba, kai nw ka dawo min da farinciki na da kuma na iyayena, Wallahi na rantse maka da Allah babu son kowa a zuciyata sai kai, ka shiga ka mamaye ko ina na zuciyata, ban taɓa mafarkin samu miji irinka ba, saboda ina tunanin kamar ba ayi ni dan jindaɗin rayuwar aure ba. Sai dai bana ganin laifin zuciyar mai Imani idan har taji tausayin rai da zata koma ga Allah yana kirawa kansa hallaka, irin wannan tausayin na ke ma Asim ba irin wancan wanda kai kake tunani ba”


A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya kai hannunsa ya shafa hannunta da ke ƙirjinsa.


“Kinji bugun zuciyata...! Duk ranar da kika so wani ba ni ba mutuwa zan yi Abnam don't ever try it”


“Ina son ka mijina, ina son ka sosai”


Juyowa yayi ya rumgumeta yana sumbartar goshinta, lafewa tayi a ƙirjinsa, hannunta yana gurin kunnenta tana wasa da shi, ɗayan kuma yana cikin yatsunsa.


Basu tashi daga gurin ba sai da aka kira sallah magariba, shi ya fara tashi yayi alwala sannan ya dawo gurin gadon ya sumbance ta ya sumbaci Sultan.


“Tashi ki yi sallah magariba ta yi”


Sai da ya fice sannan ta miƙe tsaye ta shiga banɗaki. Be dawo gidan ba sai da aka yi sallah isha'i, ko da ya shigo ita ta gama nata sallah ta shirya cikin wani shegen riga da ɗan guntun wando, ta kama kalabar kanta ta yi masa tukkuwa wato tayi parking ɗinsa guri ɗaya. Ko da ya shigo tana tsaye gurin dinning tana haɗa ma Sultan madara.


“Wow”


Ya faɗa sannan ya ƙarasa kusa da ita ya zagaye kwankwansonta da hannayensa yasa halshensa yana wasa da kunenta.


“Ba zaki daina bawa yaron nan madara ba ko?”


“Ya cika ci da yawa idan ba a bashi madara ba zai riƙa tsutse ni ne”


Ya juyo ta ita ya ɗagata ya ɗora saman dinning ɗin.


“Ke baki cin abinci ko?”


Ta matso da fuskarta har hancinta na gugar nasa.


“Ni abincin mutane nake ci”


Ɗayan hannunsa tasa ya ɗauke ta cak ya nufi ɗaki da ita.


“Shi kuma yaro na abincin aljanu yake ci?”


Tasa masa dariya hannayenta lanƙame da wuyansa. Ko da wasa Namra bata yarda ta tayarda firar Asim a gaban Abdallah ko da kuwa muagunarwar da yayi mata ne zata faɗa gudun kar ya ce ta tuna da su, yadda yake nuna mata kishi akan Asim baya nuna mata haka akan Lamido, wata ƙila saboda Abbah ya rigaya haɗa auren Lamido da Aisha ne, ko kuma dan yana ganin shi Asim ya taɓa aurenta ne.


Tayi zaton idan zata je bikin auren Aisha sai ya saka mata dokoki kamar yadda yake mata a duk lokacin da yasan zata je bikin da zata haɗu da wasu mazan ko da kuwa ƴan uwanta ne ko nashi, ko mata ne wani lokacin ya kan cilasta mata rufe jikinta wai hakan ne mutuncinsa da na gidansu da kuma nata, sai ya ɗora mata da cewar baya son tana sakin jikinta ko da kuwa cikin mata ne ƴan uwanta domin a yanzu akwai ɓata gari, wanɗanda siffarki kawai zasu gani sheidan ya ƙawata musu sha'awarki.


Ciki farinciki da annashuwa aka yi bikin Aisha da Lamido, ranar Assabar aka ɗaura aurenta kuma ranar aka kai amarya, a unguwar sama road dake cikin sokoto, a lokacin Sultan na da shekara ɗaya da wata takwas, Namra kuma na ɗauke da wani cikin duk da bata haye Sultan ba saboda Abdool ya hana wai zai cutu.
Duk wanda ya ga Sultan baya buƙatar tambayar ɗan waye ne, domin kamaninsa ɗaya da Abdool kai baka ce ma Namra uwarsa ba ce kasancewarta black beauty Sultan kuma fari tas kamar ɗan larabawa.


Family Lamido da kuma na Namra yanzu an koma kamar ƴan'uwa, tun da har auratayya ya shiga ciki, sai dai duk da haka Abdool be taba barin Namra taje Kaduna da sunan gaishe da Neine ba, wai ai zata iya haɗuwa da Lamido tun da yana yawan zuwa akai akai. sai Neine da Uwani sun je Abuja lokacin da ta haifi ƴarta ta biyu wato Fatima, daman suna son zuwa yi mata godiya, ta jidaɗin ziyarar haka ta haɗa musu goma ta arziki lokacin da zasu tafi, har tana waƙen sai ta zo Kaduna idan tayi arba'in duk da tasan Abdool ba zai barta ba.


Wasa-wasa Namra ta zama uwar mata domin bayan ta haifi Fatima sai ta ƙara haifo Juwuriyya da Mai sunan Ummi wato Zuwaira, wacce ake kira da Nasrin, sai kuma mai sunan Anty Amarya da ake kira da Iman, sai a haihuwarta ta shida ta haifi Muhammad Kabir. Ko da wasa ta dake su Abdallah rufe ta yake da faɗa wai bata san zafin haihuwa ba tana cin amanar ƴaƴansa, duk wani horo da zata musu sai idan baya cikin gidan, domin ji yake yi da abunsa wai ita zata iya gudunsa amman ƴaransa ba zasu guje shi ba, ita kanta yana nuna mata kulawa yadda yake treating ɗinta ba zaka ɗauka ita ce ta zuba masa waɗannan yaran ba, sai idan ka gansu. Babu ruwansa da ta haifi yara da yawa kullum kamar amarya take a gunsa, ita kuma tana kula da jikinta sosai da duk wani abu da tasan mijinta na so.




ALHAMDULILLAH.
Godiya ta tabbata ga Ubangijin da ya bani ikon fara rubuta littafin nan, kuma na kammala. Ina roƙon Allah ya yafe min kuraranda na yi akan ganganci ko rashin sani.




Zan yi amfanin da wannan damar na roƙi yafiyar duk wanda na ɓatawa a cikin rashin sani ko da gangan, mai rai ajizine, masu cewa littafin nan yayi tsawo dole zai zo a haka kasancewar labarin ya kasu gida uku ne, kuma dukan abunda yayi farko zai yi ƙarshe.


Ku yi haƙuri da yadda labarin ya zo muku, fatana dai a ɗauki darasin da ke a ciki, kuma a guji mugun hali ko ɗabi'ar da ba ta ƙwarai ba. Allah ka ɗora mu a dai-dai ka bamu ikon bin gaskiya da tsareta, ka tsaremu daga mugun ji da mugun gani da tsaka mai wuyar sani da aikin inda na sani...


SON SO FISABILILLAHI, godiya ta musamman ga Zagon Ƙasa paid group 1 and 2, da male abroadcast. Sai mun hadu a littafina na gaba *HAFSATU MANGA* _Yarinyar ƙauye_ I LOVE YOU ALL ♥️🌹😍😘❤💜🌷✨


Zan yi missing ɗin ku 😭😭😭 Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment