Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

roƙon Allah ya tsayar a nan kar wannan abun ya shafi rayuwar auren da zanyi nan gaba”


Ɗayan hannunshi yasa ya zagaye cikinta.


“Wannan rigimar ma na ɗan lokaci ne, kar zuciyarki ta sake irin wacan tunanin, ko kaɗan Abdallah be yi kama da Asim ba, a halitta balle kuma a hali da ɗabiyu da halaiya, Wannan karon da Abdalla aka ɗaura miki aure ba Asim ba, kar ki sake irin wacan mafarkin”


Juyowa tayi ta riƙa fuskarsa tana hawaye.


“Zuciya bata iya tantance gaskiya da ƙarya a yanzu, shi ma haka yayin ya yaudare ni da daɗaɗan kalamai, da su ya siye ni har na rufta a duniyarsa mai cike da duhu da kuma hayaƙi”


Jin an buga ƙofa yasa tayi saurin janye hannunta daga fuskarsa ta zauna saman gadon tana share hawaye. Haleema ce da Fauza sai Shukura mai aikin Ummi.
Sai da suka fara gaisawa da Abdool sannan ta ƙaraso kusa da Namra tana mata ya jiki.


“Senu senu Ajiya, Allah kew wo sauƙi, Allah baka lafiya get well soon”


“Thank you, ya Mama?”


“Lafiya ƙalau yace a agaise ki”


Haleema ta matsa tana ƙare mata kallon tare da yi mata ya jiki.


“Sannu adda Namra Allah baki lafiya”


Sai Fauza ta ɗora da nata


“Ummi tace a gaishe ki, Allah ƙara sauƙi”


“Amin amin na gode”


Bayan sun dire mata kulolin abinci suka tafi. Da kanshi ya ɗauki plate ya zuba mata abincin da aka kawo ya soma bata da kanshi sai da ya tabbatar ta koshi sannan aje plate ɗin ya ɗauki ruwa ya bata, yana dire kofin sai ga Sisters nashi sun shigo tare da Maryam sun kawo abincin cikin manyan kuloli na alfarma masu mugun tsada.
Da sauri Maryam ta zauna kusa da ita tana mata ya jiki cike da tausayin ƴar'uwarta.


“Na ji sauƙi kin yi waya da Anty?”


“Eh tun ɗazu take son ta yi magana da ke wayarki na hannuna shi kuma wayarsa a kashe, tace mun ma sun kamo hanya ita da Abbah da asubar nan”


“Kin faɗa musu abunda ya faru”


“Eh Abbah ma yace Mai Martaba ya kira shi, Namra karki saka ranki a damuwa Asim yana son ya saka ki cikin matsala ne kawai kuma yana son ganin zubar hawayenki saboda yasan a yanzu ba zaki taɓa dawowa gareshi ba”


Abdool ne yayi saurin katse musu fira saboda baya son sisters ɗinshi su gane inda matsalar take, duk da bashi da tabbacin ko Mai Martaba ya faɗa a masarauta.


“Maryam ku zo ku tafi Doc yace ana buƙatar ta huta sosai”


“Okay Allah ya baki Lafiya”


Maryam ta faɗa idonta cike da ƙwalla ganin hawayen da ke zuba a idanuwan ƴar uwarta. Tare da Sisters ɗinsa suka fita sai ya sake buɗe kulolin ya zuba mata abincin da aka kawo amman bata ci ba shi ma kuma baya jin cin abincin sai kawai ya aje. Yana kallon Likitan da ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, murmushi suka yi ma juna shi da da Abdool kamin ya miƙa masa hannu su gaisa.


“Ango Ango daya tare a asibiti, ina fatar dai ba ƙarfin amaryar mu ka ci ba har ka kawo mana ita asibiti, kasan baƙauye be iya sintar agogo ba”


Abdool yayi murmushin ƙasaita Hafiz abokinsa ne tare suka yi karatu a waje.


“Ni dai duba min matata please bana son ƙananan magana”


“Ai yanzu kana da baki jiya da na tsaya iya bayani ai ko kallon inda nake baka yi ba”


“Ai ban ma san da kai ba”


“Ai ba zaka sani ba, hankalinka yana tashe”


Ya shiga duba hannun Namra da Abdool ya cire mata drip. Sannan ya tambayi Namra abunda take ji.
Magani ya rubuta mata sannan ya faɗi yadda za a bata shi ya kuma rubuta musu takardar sallama, daman ba wani ciwon ba ne sai gajiya da kuma iɗima a lokaci ɗaya.


Sai basu bar asibitin ba sai da an gidansu Abdool ta ɓangaren Mai Martaba suka cika motoci suka zo ganin Namra, hakan kuma ba ƙaramin faranta ran Namra yayi ba, at least tasan ta shigo familyn da ake marhabun da ita kuma ake sonta da ɗaukinta ta ko wane ɓangare.


Sai ƙarfe goma sha ɗaya har da rabi sannan suka bar asibitin, Abdool be nufi gida da ita ba kasancewar shi ne yake tuƙin motar sai Sis ɗinsa ɗaya da ke gaban mota yayinda Namra da wasu ƴan gidansu suke baya su uku.


Ya tararda gidan cike da mutane kasancewar har yanzu ƴan biki basu gama watsewa ba, balle ma yau Ummi take da niyar yin nata walimar sai dai wannan abun daya faru ya kashe mata jiki, ganin hakan yasa be shigo ba, sai su Meesha da Ƴan Gidansu wato Maryam da Raihanatu da Gwaggo Ramatu, ba laifi tana iya tafiya dan ta samu ƙwarin jiki sosai tsaɓanin jiya da bata da wani kuzari sosai.
Da kanta take takawa har suka isa bacony ɗin, sannu mutanen da ke cikin falon suka riƙa mata har aka nufi ɗaƙin Ummi da ita saboda Ummi tace a shigo da ita cikin.
Kanta a ƙasa ta shiga ɗakin, dan haka bata iya gane mutanen dake cikin bathroom ɗin sai dai taɓa jin ba Ummi bace kaɗai a ɗakin.


Da ɗai-ɗaya Ummi ta riƙa nuna mata su tan gaishesu a nan Namra take ɗan ɗaga ido ta kallesu saboda ta tantancesu.
Sai sannu suke mata suna tsinewa Asim Albarka duk da basu san shi ba, domin Ummi ta faɗa musu komai, ganin ƴan'uwanta babu abunda zata ɓoye musu.


“Tashi ki zauna saman gadi magana zamu yi”


Ummi ta faɗa fuskarta da murmushi kamar babu damuwa cikin ranta. Sai duk suka tashi suna dariya tare da cewa basu su bata guri, daman ana ta kiransu su zo su duba Donuts ɗin da ake haɗawa idan yayi. Namra na zaunawa saman gado Hajiya Sadiya ta buɗo ƙofar Bathroom ta fito ta fito.
Suka haɗa ido da Namra sai ta yi tsaye jikin ƙofar kamar marar gaskiya, Namra kan saurin kawar da idonta tayi saboda bata gama yarda ita ɗince ba ko a'a idan ɗince miya kawo ta nan? Anya ma itace wannan ta rame sosai kamar ba ita ba, duk jikinta nan ya zube ta koma siririya sosai.


“Hajiya Ƙaraso ku gaisa da ƴar ta ki”


Ummi ta faɗa ba tare da ta lura da halin da take ciki ba, cikin kasala da rashin kuzari ta ƙarasa tana kawarda fuska kamar mai jin kunya. Sai Ummi tace


“Kin ga ɗayar nan itama ƙanwata ce”


Cikin nuna ladabi Namra ta gaisheta.


“Ina lafiya wuni”


Ta amsa murya na rawa idanuwanta kuma na cika da ƙwalla.


“Lafiya Ƙalau ya jikin na ki?”


“Alhamdullah”


“Daman ita ce wacce Abdallah ɗin ya aura?”


Ta tambaya tana kallon Ummi.


“Eh itace”


“Yayi sa'ar mata Allah ya baku zama lafiya”


Ummi ta amsa da Amin, sai Namra ta ɗago kai ta kalleta, Hajiya Sadiya ta sakar mata murmushin da yafi kuka ciwo ta juya ta nufi ƙofa.






KU SANI A CIKIN ADDU'AN KU, ALLAH YA BIYA MIN BUƘATUNA KUMA YA YAYE MIN DAMUWA😭🙏Wallahi I'm not in the good mood today, na yi typing ne kawai saboda nasan kuna jira. Pray for me please included me in your addu'ah ba a rubuce nake so ba a cikin five daily prayers naku nake son ku saka ni Alfarmar Annabin Rahama rasululliah salallahu alaihi wassalam 🙏😭
[8/1, 10:44 PM] Khadeeja Candy♥: *94*


“Ƴata Abdallah ya labarta abunda ya faru, nasan ba komai ba ne wannan sai hassada da neman fitina, komai zai wuce karki saka ranki a damuwa, ni dai nasan ni na haifina nasan halinsa kuma nasan abunda zai iya yi da wanda ba zai iya ba, nasan ɗana ba xai aikata irin wannan abun ba, dan haka na yarda wannan tsohon mijin na ki na neman fitina ne kawai”


Namra ta share hawayen daya zubo mata yana kallon Ummi dake mata magana cike da natsuwa da kuma nuna kulawa.


“Allah na miƙawa almurrana, kuma ni dai nasan a kan gaskiya na ke, wallahi ya sake ni kawai yana neman tayar min da hankalin ne kawai”


“Karki damu Allah baya bachi zai shiga a cikin wannan lamarin, Allah ya miki albarka”


“Amin”


“Ɓari naje na duba aikin da ake kar a min ba daidai, ki kwanta ki hutu”


Kai kawai ta iya ɗagawa, sai Ummi ta miƙe tsaye ta fice. Harabar gidan ta fita gaba ɗaya ta duba yadda ake kwaɓa donuts ɗin, sai Hajiya Sadiya ta kamo hannun Ummi suka nufi can ɓangaren garden inda babu mutane.


“Zuwaira na ce ko Namra tace miki wani abu?”


“A'a magana ce kawai muke akan lamarin auren nan da tsohon mijinta ya ɓullo da wannan lamarin”


“Ok na ɗauka ko tace miki wani abun ne, naga kamar zata yi wata maganar”


“Akwai abunda ya kamata ta faɗa min ne? Ita fa lamarin nan gaba ɗaya ya hanata sukuni”


Shiru Hajiya Sadiya ta yi tana sauke ajiyar zuciya.


“To yanzu ya za'ayi wannan lamarin Zuwaira?”


“Shine abunda nake tunani tunda ya tsaya kai da fata shi be sake ta ba”


“Wallahi yaron nan macuci ne, azzalumi ne kuma mayaudari, maƙetaci ne so yake ya shiga tsakaninsu so yake ya raba su, Asim mugun mutum ne wallahi, a lokacin da ka yi masa hallacin a lokacin yake ƙoƙarin cutar da kai”


Sai kawai ta fashe da kuka ta durƙushe, Ummi mamaki ya hanata cewa komai ga sunanshi da ta ambata, duk da bata da tabbacin sunan ne saboda bata taɓa jin sunan ba.


“Hajiya Sadiya kin sanshi ne?”


Ummi ta faɗa tana dafata. Kamar wacce ta tuno wani abu sai tayi saurin tashi tsaye tana share hawaye.


“Eh na taɓa taimakonsa a lokacin baya da lafiya Wallahi yarinyar nan ita tayi ta wahala da shi, kuma ya taɓa min aiki a lokacin ne ma yake faɗa min ya sake ta”


“Alhamdullilah Allah mun gode maka, kema ai sheida ce”


Ummi ta faɗa cike da farinciki. Sai Hajiya Sadiya ta daki ƙirji ta zaro.


“Ni kuma? Dan girman Allah ki rufa min asiri kar ma ki kawo zance na a gaban kowa, wallahi babu ruwana”


Bata tsaya jiran abunda Ummi zatace ba ta nufi gurin mutane gudun kar Ummi ta sake mata wata maganar, ta tsorata sosai ba kuma dan tana tsoron Asim ba sai dan gudun tonuwar Asirinta, ba dan hakan ba babu abunda zai hana ta ballasawa Asim asiri saboda ya cutar da ita.




ASIM POV.


A tsorace abokaninsa suka kai shi Pharmacy aka bashi magani aka saka masa bandeji a wani gurin sannan aka masa allura, sai suka dawo da shi gidansa saboda baya iya tuƙa motar ma, lokacin da suka sauke shi be shiga part ɗin Amaryarsa ba gudun kar taga halin da ya ke ciki sai ya sauka part ɗin Mardiya. Hankalinta ya tashi sosai ganin mijin a cikin irin wannan yanayin mutumen da ya fita lafiya ƙalau ya dawo haka.


Lokacin da ke labartawa Mardiya abunda ya aikata ta cika da tsananin mamakin da al'ajan ita kanta idan bata manta ba ya taɓa faɗa mata ya saki Namra.


“Amman Asim ba ka sake ta ba?”


Ya warga mata wani mugun harara.


“Uban waye ya saketa? Na sake ta zan dawo na ce matatace? Ko da na na sake ta a dole ta bani ɗa na domin da cikina ta gudu, wallahi duk abunda za'ayi sai dai ayi amman sai na dawo da Namra gidana”


“Taya zaka dawo da ita gidanka bayan ta zama matar wani? Ya kake magana kamar wanda baya cikin hankalin kansa”


“Hankalinki na ara na ke amfani, sakaryar banxa a duk ta fiku dan ita ba kuɗi na take so ba ni take so, kuma tana zuwa nan ta samu ciki ku fa kin je ki ɓarar da mahaifarki kin zubar da yaranki tun kamin ki shigo gidan ni nayi nadamar aurenki Wallahi”


Magana yake kamar zai cire haushin dake ransa a kanta. Ita kan zuciyarta ya kawo sosai dan me zai aibantata.


“Karka so ma min maganar banza kana son matarka ka sake ta ka auro ni, ba nan kake faɗar laifinta ba, sai yanzu dan ka gama more jikina sannan zaka ce kayi nadamar aurena? Ai ni ƙara ma da Allah yasa ban haihu da kai ba, mutum kullum sai kusanceka sai dai yabi ta bayanka ba ta inda Allah ya hallata masa ba”


“Ai dan kuɗina kika auri ne ba dan kuɗi na ba zaki aure ni ba, ƴar iskar banxa mai bin mazan waje”


“Ai ni wallahi allura ce cikin ruwa ko da kuɗinka sai da rabonka, yanzu ai ka auro wacce ta fini ko? Gata nan na gani”


“Namra dai zan dawo da ita sai dai ki mutu, ai ga alhakin mutane nan saman kanki kullum cikin gobara kike, ɓarauniyar banza ko ɓera be kaiki sata ba, duk inda nayi ajiya a gidan nan sai kin ɗauka, jahilar banza ashe ma ko karatu baki yi ba, shiyasa kike nan kamar dabba”


Ƙyalƙyalewa tayi da dariya.


“Mahaukacin banza Namra kan ta maka nisa sai gani sai hange daman can ba ajinka ba ce nice daidai kai, Namra kan ta yi gaba shine kake mata hassada ko? To Wallahu kayi kaɗan kai da dawo da Namra a gidan nan sai dai mai sunanta, ko kuma a mafarki daman can baka san tana da martaba sai yanzu”


“Wallahi kika sake wata magana marar daɗi sai na sakeki a cikin daren nan, kuma ki zuba ido ki gani kina cikin gidannan zan daqo da Namra sai dai ki mutu, wallahi ko zaki ran rasa raina ne sai na dawo da ita, ita ai nasan tana so na”


Tsire baki tayi ta tashi ta bar masa gurin zuciyarta cike da ɓacin rai. A daren daga shu har ita da tsoro suka kwana saboda tunanin ko sojojin zasu sake biyoshi su zo gida su hallakashi.


Da safe jikinsa sai ya ƙara yin tsami har idon ɗaya ya kumbura, ɗayan kuma daman tun jiya ya kumbura. Ƙafar da yake tsingilta da ita sai ma ya kasa takata gaba ɗaya.
Yana son yace Mardiya ta ɗora masa ruwan zafi ya gasa jikinsa amman babu dama tun da sun yi faɗa tun jiya da dare. Haka ta riƙa mulmula saman tabarmar dake falon sai tunanin yadda zai ɓullowa lamarin yake. Yana haka sai ga dogaran Mai Martaba ya aiko a tafo da shi, babu ruwansu da uzuri balle su tausaya masa umarnin Mai Martaba suke bi kuma ya zame musu dole su cika shi. Da aka je da shi can ne Mai Martaba yasa ya kira ƙanen Mahaifinsa da na mhaifiyarsa ya sanar da su halin da ake ciki, sannan ya kira waɗanda suke bakori
ya sanar da su halin da ake ciki. Mai martaba da kansa ya aika da Mota aka ɗauko na bakori sannan ya aika ɗayar a sokoto dan a ɗauko wasu daga cikin familynsa.


LAMIDO POV.


Tun da ana sauran kwana uku a fara bikin Namra ya bar gidan saboda baya son wani abun da zai kusantarda shi ga bikin. Sai dai a gida su Neina basu yi mamakin hakan ba, daman sun sa ran haka zai faru, tausasa masa zuciya kawai neina ta riƙa tana faɗa masa ita da shi ɗin basu dace ba, sai dai ta nuna masa jindaɗinta akan kyautar da Abbah yayi masa na kuɗi yace a kawo musu, ga kuma aikin da yace an samo masa, sai duk suka riƙa murna suna faɗin zaman Namra yayi musu amfani a gidan.


Uwani ce ta riƙa cewa ta so ta ga Namra amarya, daman komai yana da lokaci gashi ya wuce har suke ɗauko zancen zaman da tayi a gidan suna yaba tarbiyarta da kuma irin haƙuri da tayi da zama da Asim duk da basu sanshi.


A duk dare Lamido yana kwantawa da tunanin Namra a ransa, har ga Allah yana son Namra kuma ya so ya aureta saboda kawai ya nuna mata ba duka talaka ne azzalumi ba, kuma yaso ya tarairayeta ya muna mata rayuwar jindaɗi sai dai Allah be nufa ba a dole ya barwa Allah komai. Ko da yaushe yana ƙirga kwanakin da aka ƙara na bikin har aka kai asabar ranar da aka aka ɗaura mata aure, ranar wuni yayi kamar marar lafiya gaba ɗaya yaƙi ya sake ko abinci kasa ci yayi,Neina ta lura da hakan ta saka shi a gaba tana nuna masa halin rayuwa tare da ƴi masa tambihi akan abunda duk Allah be rubuta naka bane ba zai zama naka ba, tayi masa nasiha sosai wacce ta shiga jikinasa kuma ya yarda da hakan ɗin Allah ya ƙaddara babu yadda ya iya.


Ranar Monday da safe Abbah ya kira shi bayan sun gaisa Lamido yake tambayar ya hidimar biki, sai Abbah ya roko masa da zancen yana son su haɗu a Katsina yau.


“Lafiya Abbah”


“Lafiya ƙalau, ina son mu haɗu da kai acan kuma bana son ka rigani isa dan haka ina son ka tashi tun yanzu”


“Ok inshallah, amman a ina zan sauka?”


“Idan ka shiga Katsina ka kira ni”


“Okay Abbah”


Daga haka ya katse kiran zuciyarsa cike da ruɗani, yasan Abbah ba zai nemi ganinsa haka kawai ba, amman kuma me yasa yake son su haɗu ɗin kuma a Katsina? Haka yaƴi ta saƙe-saƙe har yaje ya gaishe da Neina ya faɗa mata sai kawai tayi masa addu'ah ta kuma bashi ƙwarin guiwar zuwa.


Ɗumamen da Uwani ta yi yaci ya kora da ruwan tea sannan ya shiga yayi wanka ya shirya cikin ƙanƙanen lokaci ya kama hanyar Katsina zuciyarsa cike da zullumi, sai dai hausawa sunce karka ji tsoron kira kaji tsoron laifin da ka aikata.


NAMRA POV.


Ummi na fita sai ta ɗalle gadon ta lumshe ido tana da shakar ƙamshin turaren Abdool dake jikinta saboda rumgumar da yayi mata ɗazu da safe. Meesha ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo sai ta shiga bathroom ta haɗa mata ruwan wanka mai ƙamshi da ɗumi, bayan ta haɗa ta fito ta nufo gurin da Namra take ta ɗan taɓa ta kaɗan tana murmushi.


“Adda Namra zaki yi wanka za a maida ƙe gidan Mai Martaba, kuma ga wasu nan zuwa su ganki”


Namra ta buɗe idonta dake cike da hawaye ta miƙe tsaye, sai Meesha ta ɗauko mata tawul sai dai Namra bata ɗaura tawul ɗin ba ta sai da ta shiga bathroom ɗin. Ta samu ƙarfin jiki sosai lokacin da tayi wanka ruwan zafin ya gasa mata jiki sosai, ga ƙamshim turare kamar karta fito.


Ko da ta fito ta samu shadda ash color saman gado aje da mayafi ja kamar yadda aikin shaddar yake, sai kuma kayan ciki wato underwears. Bata shafa mai ba dan bata jin yin wani kwalliya gaba ɗaya hankalinta baya jikinta, sai kawai ta ɗauki shaddar ta saka ta ɗaura ɗankwalin ta ɗauƙi jan mayafin ta yafa ta zauna gefen gado tana murza yatsun hannunta. Sai ga Haleema ta shigo da turen abinci Meesha kuma ɗauke da drinks.


“Ummi tace ki ci abinci Mai Martaba ya aiko kiranku tare zaku je”


“Ba da ita zamu yi walima ba?”


Meesha ta tambaya


“Haka Ummi tace wai ko basa nan za ayi walima”


Tashi suka yi suka bata guri yadda zata samu ta ci abinci. Amman har suka dawo yadda suka bar abincin haka suka tararda shi, Meesha ta lallaɓata akan ta daure ta ci abinci amman ta ƙi ita yanzu ba abinci ne a gabanta ba.


Sai da aka fita da ita aka sakata cikin mota sannan Ummi ta dawo ɗakin ta sake wani shirin ta fito tana kiran Hajiya Sadiya da wata ƴar'uwarta guda ɗaya wacce zasu je tare. Amman sai Hajiya Sadiya ta ƙeƙasa ƙasa ta ce ba zata je ba, aka yi aka yi tace ba zata je, har sauran ƴan'uwanta suka ce a canja aje da wata mata sai kawai Ummi ta kashe ƙafafunta da cewar ai ƙara ita dai tun da Asim ya taɓa mata aiki kuma har tasan da sakin Namra. Ba su ba har Namra sai da tayi mamakin jin kalamin Ummi, domin Asim be taɓa faɗa mata cewar yayi aikin a gurin Hajiya Sadiya ba, sai a lokacin ta tuna da ya taɓa faɗa mata uwar ɗakinsa ai macece. A nan kowa ya saka baki akan ƙara ita taje ɗin saboda tasan shi, sai ta sake nuna ƙin son zuwa ɗin a nan wasu kecewa ko dai tasan da wani abu ne idan ba haka be mai xai haka taje bada shedan akan matar ɗanta tun da Abdool zama ɗa yake a gareta.


“Bama fa lallai Asim ɗin yaje ba saboda Mai Martaba ne ya kira ni yace na zo da ita da kuma wasu ƴan'uwana ba lalle bane ya zama Asim ɗin yana nan, wata ƙila ma wani zancen ne zai yi daban”


Cewar Ummi tana ƙoƙarin kawar da Hajiya Sadiya tunani, sai dai hakan be hana ƴan uwanta tursasa taje ɗin ba. Babu yadda ta iya a dole ta shiga motar aka je da ita, uta kanta ba dan tana gudun abunda zaije ya dawo ba da babu abunda xai hana ta faɗi gaskiya game da Asim.


Suna isa cikin gida sai Ummi tasa direban yayi parking a ɓangaren Mai Martaba dan bata buƙartar shiga cikin gida, daman ita tama manta when last ta ganta a gidan, ba kasafai taje zuwa ba sai idan za ayi wani babban abu. Direban na fakawa ta kira Mai Martaba ta sanar masa data iso, sai yace ta shigo tun da gidan ba baƙonta ba ne.


Suna gaba ita da Namra su Hajiya Sadiya da Hajiya Mairo da Anty Farida suna biye, gaban Hajiya Sadiya kamar ya faɗo ƙasa saboda fargaba da tsoron abunda zata tarar. Wani Babban falo ne na Mai Martaba wanda ba kasafai yake shiga da mutane ciki ba, a cike suka tararda falon da mutanen amintatun Mai Martaba sai kuma Abbah da Anty Amarya dake zaune a kujera ɗaya, yayinda Abdool yake zaune a kujerar dake kusa da ta Mai Martaba, sai kuma Asim da ke zaune ƙasa shi da Lamido, sai kuma ƴan'uwan Asim.da ke gefe ɗaya zauna, wato yayar mahaifiyarsa da kuma ƴan uwan ubansa su huɗu.


Mai Martaba kuma yana zaune a wata ƙasaitacciyar kujera Mai Kyau da Haske irin da manyan sarakuna. Namra na haɗa ido ta Anty Amarya sai ta fara hawaye, Anty kuma ta sakar mata murmushi kamar ba komai.


Ummi ta zauna a kujera zaman mutun uku sannan Hajiya Mairo da Anty Farida suka zauna a saman kujerar Hajiya Sadiya kuma ta zauna ɗayar kujerar ta noce kai ƙasa, Namra kuma ta zauna ƙasa.


Asim na ganinta gabanshi ya faɗi, ya rasa yadda akayi ta haɗu da Ummi duk da bsan wacece Ummi sai dai yasan bata rasa nasaba da Namra saboda yaga tare suka shigo, zance ɗaya zuciyarsa ke nanata masa, wata ƙila Namra ce ta faɗi inda take akaje aka ɗaukota, sai kuma wata tambayar ta sake faɗo masa a rai ya akayi Namra ta san yayi mata aiki?




Waziri ne ya miƙe tsaye yana yima kowa sallama sannan ya kalli Mai Martaba ya sake kallon mutane ya ce.


“Muna saba data tara mu a wannan guri saboda jayayyar aure ne, ɗan wannan masarauta wato Yarima Abdool ya auro wata yarinya daga sokoto, kamar yadda kowa ya sani wannan yarinya bazawara ce, kuma sai da ta shekara ɗaya a gudansu har da wata uku sannan aka ɗaura mata aure da Yarima, bayan an taho da ita a nan Katsina sai Tsohon mijinta ya taso da zancen cewar shi be saki Matarsa ba, kuma har yana iƙirarin akwai ɗa ɗaya a tsakaninsu, a bisa wannan ne Mai Martaba ya tara mu saboda aji bakin kowa”


Waziri ya koma ya zauna, sai Mai Martaba ya kalli Asim ya ce.


“Ko zaka iya faɗa min dalilinka na cewar kai baka saki matarka ba?”


Asim babu kunya babu tsoron Allah ya soma magana ko tsoro baya ji.


“Allah ya taimakeka ni ban saki matata ba, idan har na sake ta dole ne na mata takardar sakinta, kuma babu yadda za'ayi na saketa bayan tana ɗauke da cikina kuma ni mai tsananin son haihuwa ne, ni dai nasan rigima ta shiga tsakani da ita har na dake ta kuma na ta gudu amman ni ban sake ta”


Malamin faɗa ya ɗaga hannu. Sai Mar Martaba ya bashi izinin magana, daga inda yaƙe zaune ya aikawa da Asim da tambaya.


“Yaro karka ruɗi kanka kar kuma kayi wasa da hankalinka, idan har ta gudu miyasa baka bita ba har tsowon wannan lokacin ka ƙyaleta”


“Saboda na san iyayenta basa so na ko naje masan ba zasu bani ita ba”


Kowa sai ya girgiza kai. Malamin ya kalli

Please Login or Register in order to submit comment