Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya risina gabansu, ya yi ƙasa da muryarsa sosai.


“Idan kun shirya zamu je Kaduna yanzu sai na nuna muku inda Namra take”


“Abunda muke jira kenan”


Anty Amarya ta yi saurin amsawa.


“Mai Martaba yana shiri ne, idan ya fita muma zamu kama hanya”


Ya faɗa yana kallon fuskar Abbah dan yaji me zai ce. Murmushi kawai Abbah yayi ya ɗaga masa kai, yana masa kallon mutum mai hankali da natsuwa.


NAMRA POV.


Murmushi kawai take, sai ɗaga kai tana maidawa, duk firar da ake, bata saka baki saboda itama nata ya isheta, su kansu suna firar ne ɗan kawai su rage mata kewa. Amman ta ƙi ta sake, sai dai a kan yi murmushi ko ɗaga kai, gudun kar suce ta ƙyale su, tun da Abdool ya takalo mata maganar gida sai ta koma wata irin, tunanin rayuwar jindaɗin da take ciki ta baya ta riƙa dawo mata, da kuma tunanin halin da Asim ya jefata, ga halin ko in kula da ya nuna mata, da kuma ƙin son haɗa jini da ita, ace duk tsawon wannan lokacin be neme ta, da gaske baya da buƙatar ta kenan? A ɗayan ɓangare kuma tana tunanin yadda zata shirya da iyayenta har ta koma ta zauna a tare da su wanda take ganin abu ne mai matuƙar wahala yin haka.


Duk dariya suka sa lokacin da Lamido yake bada wani labari na ban dariya, ita kam Namra sai ta saka kuka tana mai ɗaga murya dan damuwarta tasa ta manta da agaban jama'ah take, babu wanda hankalinsa ya fi tashi kamar Lamido, dan ya tsani ganin Namra cikin damuwa balle kuma zubar hawayenta. Sai da taga hankalin kowa ya dawo kanta sannan ta sassauta kukan da take ta tashi da gudu ta shige ɗaki. Ajiyar zuciya Lamido ya sauke cike da rashin daɗin rai ya ce


“Yarinyar tana cikin damuwa, ni ko bana son ganin ta cikin wannan halin, dan zai ƙara mata damuwar ne kawai, babu abunda yake raina a yanzu kamar na maza sanadiyar farincikinta, zan yi iya yadda zan iya na ganin na cire ta cikin wannan halin inshallah”


Neina ta miƙe ƙafafunta tana kallon ɗanta cike da son sa da kuma tausayinsa ta ce


“Cire yarinyar nan a damuwa abu ne mai wahala Lamido, ga dukan alamu ƴar babban mutunce, shiga irin lamarin gidan su sai yi wahala gareka tun da kai ba ɗan kowa ba ne”


Ɗauke kansa ya yi ya maida gurin ƙofar da Namra take. Sai da Neina ta tashi sannan ya miƙe tsaye yana ɗan ɗingishi ya nufi ɗakin. Zaune ya same ta kusa da ƙofa tana raira kukanta mai ban tausayi da taɓa zuciya.


“Namra kukan nan da zai miki magani da tuni yayi miki, kina ƙara saka kan ki ne cikin damuwa ne kawai”


Ɗago kai ta yi ta kalleshi.


“Idan ban yi kuka ba mi zanyi? Kana tsammanin mace data shiga cikin halin da nake ciki zata yi abota da dariya ko farinciki? Ba zaka gane abunda nake ji ba”


“Nasan kin shiga rayuwa kala-kala amman kuka ba zai miki magani ba, ki taimaka min ki tausaya min ki daina wannan kukan Namra, saboda gani nake kamar nine silar zubar hawayenki, ina damuwa sosai”


Hannayenta biyu tasa ta share hawayenta, sannan ta miƙe tsaye ta nufi gurin katifa ta zauna, ta yo ƙoƙarin tsayardar kukanta ne kawai dan ta lura da damuwar da Lamido yake idan tana kukan, balle kuma har ya kai ga yi mata magana, ita kanta tasan ba kowa ne zai juri zama da ita ta dinga masa kuka kamar ƙaramar yarinya.
Ajiyar zuciya Lamido ya sauke ya shafa fuskarsa sannan ya juya ya fice. Ba tayi minti talatin da zaman ba, taji yaro ya doko sallama wai Abdallah daga Katsina yana sallama da Namra. Wani baƙin haushi ta ji ya turniƙe ta, yau kuma da wacce ya zo? Me yake nema a gareta ne? Ba zai barta da damuwarta ba! Tana jin motsin shigowar Neina ta yi saurin kwantawa saman katifar ta lafe sosai kamar ta yi bachi.


“Na san ba bachi kike ba Namra, kuma kon ji lokacin da aka ce ana sallama da ke a waje, ki rufa mana asiri ki tashi kije”


Neina ta faɗa zuciyarta Fal da tsoro, dan ita tun da taji ance ɗan sarki ne, duk fargaba da tsoro suka kama ta, kullum zulluminta ɗaya kar yasa ayi musu wani abu.
Sosai Namra ta so tayi pretending like tayi bachi amman jin yadda muryar Neina take mata magana kamar mai magiya, yasa ta motsa har ta buɗe ido ta kalle


“Neina ban san me mutumen yake nufi da ni ba, me zai zo yayi min a yanzu?”


“Kije dai Allah, ko ma minene zaki ji, kin rufa mana asiri Namra, kin ga mu talakawa ne bayin Allah, karki ja mana abun ba zamu iya ɗauka ba”


“Bana nufin janyo muku komai Neina, amman kamar ba ki fahimci abunda nake nufi ba”


“Na fahimta, kawai ki tashi ki tafi, idan kuma har baki jin tafiyar, ni zan iya bashi izinin ya shigo nan yayi magana da ke, wata ƙila ma carpet ɗinsa da daya manta shekaranjiya ya zo karɓa”


Kamin ta Namra ƙara yin magana. Lamido ya ɗaga labulen ɗakin ya kunno kai yana faɗin.


“Neina kina tsoron masu milki da yawa”


“Dole na tsoraci masu milki Lamido, kafi kowa sanin sune sanadin shigar mu wannan halin”


Tana kaiwa nan ta juya ta fice. Shi ma Lamido juyawa yayi ya fice cikin rashin daɗin rai, yakan samu kansa a cikin rashin jindaɗi a duk lokacin da Yarima ya tsaya ƙofar gidansu da sunan kiran Namra.
Namra bata motsa daga inda take ba, sai ga Neina ta dawo ɗakin riƙe da carpet ɗin ta miƙa mata.


“Tashi kije ki kai masa, ko ba komai wulaƙanta ɗan Adam babu kyau, balle babban mutun kamarsa”


Wannan karon Namra bata yi mata musu, ta tashi ta karɓi carpet ɗin ta miƙe tsaye, already tana da hijab ɗinta sanye, sai kawai ta bi bayan Neina suka fice tare, takalminta ta zura, ta nufi ƙofar fita.


As usual gurin daya saba tsayuwa ya tsaya, tana tunkara inda yake tsaye gabanta ya soma faɗuwa, ta rasa dalilin daya saka yake mata kwarjini, tana isa kusa da shi ta miƙa masa carpet ɗin ta ce


“Ga carpet ɗin ka dan nasan ita ka dawo ƙarɓa”


Be ɗago ya kalleta ba, balle ta gane maganarta ta ratsa kunnensa, sai sha'aninsa yake da wayarsa, kamar be san da tsayuwarta a gurin ba.
Tayi tsayuwar minti ɗaya a gurin zuwa biyu, kamin ya ɗago ya kalleta ta cika sosai da taji kamar ta jefa masa wata baƙar magana amman bakinta be bata haɗin kai ba, gashi sai jin take kamar ta jefa masa carpet ɗin, sai dai kwajininsa ya hana hannunta kuzari, ballema ta yi ƙoƙarin yin hakan.


Babu enough hasken da zai iya haske fusakarta sosai, amman hakan be hana shi karantar tana ciki fushi ba, ko ba komai yasan ya ɓata mata lokaci, kuma ya shiga huruminta na ƙinjin gargaɗin da tayi masa akan kar ƙafarsa ta sake tako ƙofar gidansu.


“Ƙomai naki kyau yake min Namra, fushinki da faɗanki da tsawarki duka burgeni suke, abu ɗaƴa ya rage min yanzu na gani naki, shine dariyarki”


Ya faɗa yayinda ya ke cigaba da dannar wayarsa, amman hankalinsa da idonsa suna kan Namra. Wannan karon tayi nasarar yaudarar kanta, har ta samu haɗin kan idanuwanta, ta jefe Abdool da wani shegen kallo.


“Carpet ɗin ka kawai na fito kawo maka, ban fito dan ka yaba fushi ko faɗa na ba, kuma bana tunanin an halicceka dan ka ga dariyata kawai, saboda haka karka ɓatawa kanka lokaci, ka karɓi Carpet ɗin ka”


“Miya hana ki bar carpet ɗin a inda na barta tun ranar? Wane salo ne yasa kika ɗauke ta? Yanzun da nazo na aika nace a bani carpet ne? Wato ba zaki iya ganin abun Abdool ki ƙyale ba ko?”


Wannan karon da murmushi a fuskarsa, ya soka mata wannan maganar, ya gyara tsayuwarsa yana kallon taurarin da suka yi sama ado.


“Ai mu ƴaƴan Sarakuna bama shimfiɗa kuma bama ɗaukewa, wacan karon ma ba na shimfiɗawa kai na bane a karon kai na, nasan wata rana zan rubuta a diary, bayan Mai Martaba da Ummina, na taɓa shimfiɗawa Namra carpet har ma na zauna da ni da ita”


“Amman kai ka baka da aikin yi Wallahi, Allah yayi min tsare da mugun ƙudirinka, baka cikin hayyacinka ne? Miyasa zaka zo kana min wasu kalamai kamar wanda be san halin da nake ciki ba?”


“Ina ma ina da mugun ƙudiri a kanki! Da kin ga yanzu sace ci kawai zan yi na gudu naje nayi rayuwarda da nake so da ke, ni kaina ina mamakin halin dana shiga saboda ke, ban san miyasa ƙwaƙwalwata take ƙoƙarin zautuwa da lamarin ki ba”


Kai ta girgiza ta jefar da carpet ɗin a ƙasa.


“Wallahi baka da tausayi baka da tunani kwata-kwata a zuciyarka, taya zaka kalleni ka yi irin wannan maganar, you're fake Prince ba asalin Yariman ƙwarai bane kai, wata ƙila sarautar ta ku ta ƙauye ce, dan yariman ƙwarai ba zai tsaya mace kamar ni tana faɗa masa magana ba”


Lumshe ido yayi yana murmushi, tare da tsutsar baki kamar mai shan Sweet Candy. Ko da ya buɗe idonsa har ta ɓace daga gurin kamar walkiya.
Murmushin da ke fuskarsa ya faɗaɗa, kamin ya shiga muhalin massages ya aika saƙo. Cikin mintunan da basu fi goma ba, sai ga wata mota ta faka a gurin ɗauke da Anty Amarya da Abbah.


“Ga gidan can”


Ya faɗa yana nuna musu da kai, sannan ya buɗe motarsa ya shiga. Su kuma suka doshi ƙofar gidan, Abbah ne ya tsaya daga waje, Anty Amarya ta kunna kai ciki, zuciyarta sai bugawa take fat fat fat...




HILAL POV.


Ba a'ayi wasu events ban da walima, daman can shi baya ra'ayi sai kuma aka ci sa'ah amaryar tasa uztaziyace ita bata da son duniya. Ranar jumma'ah akayi walimar bayana an saka amarya lalle kamar yadda al'ada ta gada. Sai aka ɗaura aure ranar asabar, an yi taro sosai musamman ta ɓangaren Teema tun da ita aurenta ne na fari, kuma ita ta farko mace da mahaifinta zai fara yi ma aure. Yadda Hilal yaƙe yaƙar baki yana amsa gaisuwar mutane da ala sa albarka sai ka ɗauka auren so da ƙauna ne suka yi shi da Teema, tun da sha biyu aka ɗaura aure aka yi liyafar cin abinci bayan a sauko daga sallar azahar. Shi kam be samu dawowa gidansa ba sai da yamma ta yi lis.
Yadda ya tararda Kalsoom be yi zaton zai same ta haka ba, ta bala'in ruɗashi, kyau tayi har na fitar hankali, bakar shaddace jikinta an mata riga da saket, ɗinkin ya matse ta ya fitarda surar jikinta sosai, ta kashe ɗaure ɗankwalinta ya kalli kudu masu gabas, ga wata uwar kwalliyar kanti da aka mata a fuska, yadda take motsa bakinta ma abun kallo ne.


“Ango ka sha mai”


Ta faɗa tana wani fari da ido. Shi dai mutuwar tsaye yayi a ƙofar falon yana kallonta, sallama ma sai ta gagari bakinsa, ji yayi kamar ya je ya rumgumeta sai dai ƙanenta da kuma Amiyarta Salma dake falon sun han shi rawar gaban hantsi.
Yana amsa gaisuwar da suke masa ya nufi ɗakinsa, zuciyarsa cike da ƙaunar matarsa, dan yaji daɗin halin daya same ta ta bashi ƙwarin guiwa sosai, shi da ya zo da zimmar ya lallaɓata kar ta saka ranta a damuwa, sai gashi yaga kamar ma ta fi shi farinciki.


Babbar rigarsa ya fara cirewa sannan ya zauna saman gado, sai gata ta shigo hannunta riƙe da copin madara ta yanka masa ayaba ciki ta saka sugar kaɗan. Saman ƙafafunsa ta zauna ta riƙa aika masa madarar a baki, shi ko sai wani lumshe ido yake yana buɗewa kamar wani tsohon ɗan iska, kamin yasa hannayensa ya zagaye kunkurunta.


“Wannan ado haka ai sai ki haukata, so kike amaryar nan ta rasa gane kai na ko?”


Murmushi ta yi ta aje kofin a ƙasa tasa hannayenta ta riƙa kunnensa ta ɗora goshinta saman nasa.


“Ai niban yarda zata gane kan ka ba, dan wata mace bata isa ta shigo gidana ta fini gane mijina ba, da dai Rashida ce da ita ba zan musa mata ba, saboda ta rigani saninka, ni kuma a yanzu na fi Amaryar ka sanin waye kai”


Murmushi yayi yana shafa bayanta da suka hannayensa biyu. Dauke kanta tayi daga nassa but stilll hannayenta na rike da kunnensa guda biyu.


“Wai ance ƙawar Rashida ce da gaske?”


Ya ɗaga mata kai yana wani lumshe idonsa da suka kaɗe.


“Uhnn amman ai ba ni nace ina son ta ba, Hajiya ce ta haɗa auren saboda ta yaba da tarbiyarta”


Ta yi murmushi kamar ba komai, alhalin na ciki na ciki.


“To Allah ya baku zama lafiya”


Sai ta saki kunnensa ta riƙa hannayensa dan tana jin yana ƙoƙarin wuce gona da iri, ta miƙe tsaye.


“Ina zaki?”


“Aiki zanje na ƙarasa”


Yayi saurin miƙa hannu ya riƙota.


“Haba karki zalince ni baiwar Allah”


“Ba wani zalinci, nima fa mai tsada ce kamar amarya, dan haka ni jiki zaka siya ba baki ba”


“Ai har kin fi amarya tsada, ke da ga wannan ciki, amman dai amin farashi mai sauƙi ta yadda zan iya biya”


“Ba yanzu zamu yi cininki ba, kai fa ango ne karka manta, nan da ƙarfe goma na dare sai yadda ka ga dama zaka yi da amaryarka”


“Bari wanka da kashi indan ganin hadari, ayi jiran abunda ba tabbas bayan ga ki ina gani”


Ta fisge hannunta ta nufi ƙofa.


“Ni kan nan gani na bari wannan wunin da daren ba nawa ba ne”


Ganin zata fice da gaske yasa shi wara ido, jikinsa a mace yace


“Wai da gaske kike yi? Ki taimaki bawon Allah, karki jefa rayuwarsa cikin haɗari”


“Au naka wasa ne kenan!”




Ta fice tana dariya kamar ba komai, sai dai can cikin zuciyarta ji take kamar an aza mata garwashin wuta a ciki, saboda kishi da baƙinciki. Tana ta ƙoƙarin yaƙar zuciyarta ne, dan bata son ta saka kanta cikin matsala saboda cikin dake jikinta, daman can lafiyar cikin be isheshi ba, idan kuma tace zata saka damuwa a ranta, to zata cutar da kanta ne kawai, tun dai aure an ɗaura, kuma tasan mijinta yana sonta, sai dai ɗan kishi da ba'a rasa ba.
Bayan fitarta, ta shiga bathroom ɗinsa yayi wanka, ya fito ya shirya cikin wata shaddar gizna mai kyau da sheƙi. Yana cikin saka agogon hannunsa Kalsoom ta shigo ɗakin ɗauke da plate ɗin abinci. Fried rice ce and pepper chicken sai ƙamshi take, kallo ɗaya yyi ma abincin ya ɗauke idonsa wai shi ala dole yana fushi da ita.


“Waya ce miki abincin zan ci? Ai ba yunwa na ke ji ba”


“Shikenan kuma ango sai yayi fushi ranar aurensa?”


“Waya ja nayi fushin? Sai ka taɓa abu a hanaka lasawa, ai wannan cin zalin ne”


Gwalo ta mishi taja ƙofar ta fice. Sai ta fashe da dariya.


“I love you”


Ya furta tana shirin zama ya ci abincin. Shi kansa be san yaji yunwa kamar haka ba sai yanzu, tass ya cinye abinci da da lemun kankana data haɗa masa mai lemun tsami ciki da sugar kaɗan, har ƙashin sai da ya taune ya tsotse ruwan, dan yaji daɗin abincin sosai, ga lemun da sanyi sai rmratsa ƙwaƙwalwarsa yake, bayan ya gama ya tashi yana hamdala. Tana shigowa ta saka masa ɗariya, har da riƙe ciki.


“Ni dai nasan mijin Amarya yana jin yunwa”


Shima dariyar kansa yake dan yasan yayi aiki.


“Ai ba ni na ci ba, aljanuna ne suka ci”


Matsawa yayi ya maita kiss a goshi.


“Amarya tace ta yafe miki daren nan na ta”


“Uhmmmm”


Ta wara ido.


“Wace sakaryar amaryace zata yarda ta yafe wannan daren mai tsada a rayuwar ko wacw ya mace, balle kuma da gwarzon namiji kamar ka”


Ya kalli kansa yana wani kaɗe shaddarsa.


“Allah? Ina jin daɗin yadda kike yaba ni”


“Ai ka haɗu ne Malam, dole a faɗa”


Ya riƙa fuskarta ransa fari ƙal da farinciki.


“I love you so so so very much”


Murmushi ta masa as respond, ya fice yana dariya. Sai ta ji tashin motarsa cire ɗankwalinta ta jefar, ta faɗa saman gadonsa ta fashe da kuka.




ASIM POV.


“Yes...!”


Ya bugi ganbun motarsa yana dariyar da har zuciyarsa ita ce.


“Kin biyani Mardiya, zan baki mamaki, kuma auren mu nan kusa nake sonsa ba sai nesa ba, dan haka daga yanzu ki shirya a ko yaushe zan iya zuwa gaishe da iyayenki, sannan na turo magabatana”


Hannayenta biyu tasa ta rufe fuskarta 5ana dariya, sai tayi cikin gidansu da gudu kamar wata mai kunyar gaske.
Ya daɗe tsaye a gurin yana kallon ƙofar gidansu, sannan ya zaro wayarsa dake ringing ya kara a kunne.


“Na'am Hajiya kin dawo ne?”


Ban ji ma tace masa ba, sai kawai naga ya gyaɗa kai yana faɗin.


“Okay kina ina yanzu?”


Can kuma sai naga fuskarsa ta canja.


“Eh nasan gurin. Okay gani nan zuwa”




Ya sauke wayar kamar mai tunani. Can kuma ya ɗaga kafaɗunsa. Ya buɗe motarsa ya shiga.


Yana cikin driving ya kira ƙanen mahaifinsa dan jin yadda aka yi maganar gida.


“Eh yana da kyau sosai? Bedroom nawa ne a gidan? To ko dai mu bari sai an samu wani? Okay ba matsala”


Ya kashe wayar, sannan ya ƙara gudun motarsa, cikin ƴan mintuna ya isa unguwarsu Nably, a kusa da gidansu ya faka ya sake kiran Hajiya.


“Gani na ƙaraso unguwar, amman ban ganr gidan ba”


Daga ɗayan ɓangaren ta amsa masa.


“Baka ga wani green gate ba?”


“Na gani, Mai farin fenti”


“Eh to ka shigo ciki amman ka tsaya daga gate zan fito na kawo maka”


“Okay”


Ya tashi motarsa ya nufi gate ɗin gidan. Be ƙara gasgatarwa ba har sai da ya shiga harabar gidan, kusa da gate ya faka, yana ƙara kallon harabar gidan.


“Akwai bura'uba...”


Ya faɗa yana kallon Hajiya Sadiya wacce ta fito riƙe da ƙatuwar leda, sai faman sauri take kamar wacce ta yi sata.

“Ka saka min a wannan account ɗin”


Ya miƙa masa farar takarda tare da ledar dake hannunta. Cikin ladabi ya karɓa ya na faɗin


“Hajiya wannan ma gidanki ne?”


“Eh jeka dan Allah da sauri, bana son a tararda kai”


“Okay”


Ya koma cikin motar yana ta kallon gidan. He just can't believe gidan Hajiya ne, mi hakan yake nufi ita mahaifiyar Nably ce ko yar'uwarta.? Har ya bar gidan be samu amsar tambayarsa ba.




YASMEE POV.


Tana jin tsayawar motarsa ta tashi da sauri ta nufi kitchen, cox she dunno what to do, kuma tana jin kamar bata son ganinsa, duk da tana ƙoƙarin yaƙar zuciyarta dan sanin gaskiyar lamari. Hannayenta biyu tasa ta dafe fuskarta tana busar da iskar bakinta.


‘Ni fa lauya ce, ni nake fawa wasu magana, ni na saba bincike, dan me yau kuma zan rikice, i need to do this ko dan na cire kaina daga zargi’


A zuciyarta take wannan maganar, a fili kuma murmushi ne shimfiɗe a fuskarta ta juyo tana amsa kiran da yake mata.


“Yau wace rana baki je office ba ne?”


Yayi mata kiss.


“No naje yau cases biyu ne kawai da ni, ina gamawa na dawo, ya aikin naka?”


“Alhamdullah, ina da labari mai dadi, Abbah (Baban Namra) ya buɗa mana wani sabon kamfani a Abuja, kuma nasan niɓe zan kula da shi”


“Wow amman Abbah ya kyauta mana, Allah yasa hannu a ciki, ko shi yasa aka aiko maka da wasiƙa? Ɗazun an kawo wasiƙa a aje maka”


“Waya kawo”


“Wallahi ban sanshi ba, tana nan ɗakinka na aje maka”


Freezer ya buɗe ya ɗauki gorar ruwa ya nufi ƙofar fita yana tambayar abunda aka dafa. Da kallo Yasmin ta bishi bayan ta bashi amsa idonta cike da ƙwalla.


“Allah ka sani ina son mijina, Allah karka tabbatar da zargina akan sa”


Ta share hawayen da suka zubo mata. Tana ƙoƙarin fita sai gashi ya shigo riƙe da wasiƙar hankalinsa tashe.


“Kin karanta wasiƙar nan Yasmin?”


“A'ah miya faru?”


Ba komai, ya juya ya fita da sauri. Sai da ta tabbatar ya shige ɗakinsa sannan ta rufa masa baya. A bathroom ɗin falo ta tsaya ta sakama ƙafafunta ruwa gudun kar yaji sawun takun ƙafarta. A bakin ƙofar ɗakinta ta kara kunnenta, sai dai bata ji alamar motsinsa a cikin ɗakin ba. A hankali ta tura ƙofar ɗakin daman be mata rufin ƙwarai ba, nan ma babu alamunsa har toilet ɗinsa taje ya leƙa bata ga kowa ba. Mamaki ne ya kamata ina yaje,da sauri ta juyo ta fito. Har zata shiga ɗakinta, sai kuma ta nufi gurin engine ɗin wankinta. Daga inda take tsaye ta hangosa yana waya, daga gani ba wayar aiziki bace yake, dan yadda yake jinjiga jikinsa yake safa da marya na ya nuna haka. Yana gama wayar ya juyo yana faɗin.


“Namra bata zame min matsala ba ke zaki zame min, babu wanda ya isa ya datsa min rayuwar jindaɗi wallahi”


Karaf idonsa cikin na Yasmin, dake tsaye gafen ƙofa.




THE GAME IS ABOUT TO START...😿
_____________________________________




I feel much better Alhamdulillah. Na gode sosai da addu'ah da kulawa, Allah ya bar zumunci. Jazakallahu khairan all 😘
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *74*


Ko parking ɗin kirkir bata yi ba a gidansu Teema ta fita Motarta, zuciyarta na bugun bugawa, taron mutanen da tara a gidan ya ƙara tabbatar mata da maganar Asmee da kuma Momi.


Teema na hangota ta tashi daga cikin mutanen da take ta nufi wani ɗakin wanda babu kowa a cikinsa.
Kai tsaye Rashida ta bita daman ta ga shigowarta, wasu daga cikin ƙawayen Teema har sun fara magana, dan wasun su sun san mijin Rashida ne zata aura, wasu kuma a yanzu suke samun labari, ganin yadda ta shigo cikin gidan a birkice.
Da wani irin ƙarfi Rashida ta banki ƙofar ɗakin da Teema take ta shiga hasale.

“Marar mutumci wacce bata gaji arziki ba, ni zaki yiwa ha'inci? Ki zagaya ta bayan idona ki ci dunduniyata”


Hannayenta biyu Teema ta kama ta riƙe tana hawaye.


“Dan Allah ki saurare ni, karki yanke min hukumci ba tare da kin saurare izuri na ba...”


Rashida ta fisge hannunsa tana mata wani kallo na uku saura kwata, kamin ta katsa mata tsawa kamar wata ƴarta.


“Babu wani daɗin baki da zaka min, macuciya wai tsabar rashin kunya ni zaki ciwa amana..”


“Ban ci amanarki ba Rashida ko kowa ya zarge ni ke be kamata ki mun haka ba, ni kaina ban san da wannan haɗin ba, dan be taɓa zuwa fira gurina ba sai da zai kawo min iv, su Hajiya ne suka haɗa komai”


Ta ƙarasa da kuka tana wani ƙara narkewa kamar gaske. Rashida ta watsa mata wani kallo.


“Ke kar nake kallon ki, kamar naira a hannun yaro, yadda kika yi boka haka na yi karki nemi raina min hankali, wallahi mafitarki ɗaya ki fasa auren nan ko kuma na ci uwarki”


Teema ta yi wani Shu'umin murmushi tana kawardar hawayen ƙarya dake fuskarta.


“Idan kuma ba ki ci uwata ba, ni sai na ci ubanki, da aka halitto Hilal an ce miki ke kaɗai zaki aure shi ne? Ke in ban da haukarki ma miye na kishi bayan ya sake ki da ya kama ki da wani ƙato ko kin ɗauka ba'asan abunda ya fitar da ke gidan Hilal ba? Kina ganin kamar ba san komai a rayuwarki ba ko? To malamin dana kai ki gunsa, shi ya faɗa min komai a kan ki”


Jikin Rashida yayi sanyi har tana sassauta murƴarta duk da tana cikin zafin rai ne.


“Yayi dai-dai kuma ina fatar ya duba miki ya faɗa miki igiyar aure ba zata taɓa shiga tsakanin ki da Mijina ba, dan Wallahi sai na rusa wannan auren ko ta yaya, dan babu yadda za'ayi yar iska irin ki ta tarbiyantar min da yara, sai na faɗawa Hilal irin matar da zai aura”


“Yar iska kamar uwarsu ko? Ai abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne, kuma idan baki rusa auren nan ba, baki haihu ga uwarki da ubanki ba, ai Hilal ba mijin ki bane mijin Kalsoom ne da Angon Teema, ƴar baƙin asiri kinje kin yi ma kiahiya ya dawo kan ki kin kashe ɗan ki da hannunki, Ni ko nafi ƙarfin ki gaba ɗaya ke da danginki, kuma wallahi duk kika kuskura sake saka baki a maganar auren nan sai na faɗawa duniya dalilin mutuwar auren ki, da kuma dalilin mutiwar ɗan ki, ga kuma cutar da take tare da ke, dole har ƴaran ki su gujeki, ko kin ɗauka ba a san dalilin korarki da ubanki yayi ba?”


Gaba ɗaya jikin Rashida ya gama sanyi, zafafan

Please Login or Register in order to submit comment