Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba nayi ta kallo ko me? Yanzu ma a hanya nake saƙon da kika min ne yasa na biyo”


Kawarda kai tayi ta haɗe hawayen da take da tabbacin idan har suka fara zubar mata bata san lokacin tsayawarsu ba.


“Daga Asibiti na ke likita ya ce ina da ciki, kuma akwai roba a jikina”


“To ya aka yi haka?”


“Nima ban sani ba, amman yace min daman akan samu hakan wani lokaci, yace naje nayi hoto aga lafiyar cikin, Asim ina tsoron ko mahaifata bata gama warkewa ba”


“To a zubar da cikin mana”


Miƙewa tayi tsaye tana kallonsa.


“A zubar fa kasa kasan abunda kake faɗa?”


“Na sani mana, Namra wannan ba lokacin samun yara bane, muna planning na neman kuɗi kuma yara zasu shigo, ki duba irin wahalar da muka sha a baya yanxu kuma hanya ta fara buɗe mana sai kuma haihuwa ta zo, gaskiya ni ban shirya ba”


“Ni kuma na shriya Asim, ni nake da matsalar da nake da a mahaifata kuma im ready to give birth saboda nima haihuwata aka yi, Allah ba xai bani kyauta na jefar ba”


Cikin wata murya tayi furucin muryar da bata san tana da ita ba sai a yau. Shi kuma ya gyara tsayusarsa yana mamakin ta


“Wallahi Namra sai yanxu na gane lallai ke ba masoyiyata bace. Kin manta lokacin da nake cewa kije ki cire robar nan amman ki ƙi, ko wannan zubar da ciki da kika sha ban san lokacin da kika sha ba, wata ƙila kin yi zubar da cikin ne shiyasa har mahaifarki ta samu matsala, sai yanxu da kika ga zan yi kuɗi ko shine zaki nuna min baƙin hali ki ɓullo min ta haihuwa, to ni ban shirya haihuwa yanzu ba dan haka dole a zubar da cikin nan”


“Wallahi tallahi ba zan zubar da wannan cikin ba, ko da kuwa wannan cikin yana nufi ya rayu, ni na mutu”


“Haka kika ce?”


“Haka na ce kuma haka xaka gani”


“To sai dai ki zaɓa ko ni ko cikin nan...!”


Wani kallo tayi masa na ƙara tantance zancen daya fito daga bakinsa. Shi kuma sai ya ɗaga mata kai dan ya tabbatar mata da maganarsa.


“Yes Idan har baki xubar ba sai dai kije can gidan ku ki haife ɗan, ke kan ki ba samun lafiyarki bane ace kin haihu cikin kuɗi kuma a lokacin mahaifarki tana lafiya ƙalau, na baki lokaci ki yi tunani akai”


Juyawa yayi ya fice, zuciyarsa cikr da tabbacin abinda yayi be yi kuskure ba.



*ANTY AMARYA POV*


Sai da dare Abbah da Hajiya Barau da Anty suka samo ganin lefen da ka kawo, Abbah ya yaba sosai, Hajiya Barau ma ta yaba amman yabon baka yabon daya zame mata cilas dan sam bata jidaɗin ganin yadda aka zubawa ƴaƴan Anty wannan uban lefen ba. Hindatu kala 54 Maryam kuma 79 cikin su kuma babu shege balle ɗan iska.


“Allah yasa alheri ya nuna mana lokacin, amman na ɗauka Namra zata xo tarbon lefen nan”


Anty Amarya taji babu daɗi, sai dai bata nuna ba, sai kawai ta ce.


“Ta so tazo mijin nr ya hana ta yace wai ta bari dai nan gaba sai su zo tare”


“Allah ya taimaka, lefe yayi mashallah”


Haka ta taso ta fito daga falon da ƙahon baƙinciki daya tsaya mata a zuciya. Part ɗinta ta shigo tana shiga ta shige ɗakinta ta zauna, babu abunda take tunanu sai duniyar da Abbah xai kashe masu gurin auren, kamar ita ba a ma ƴaƴanta.


Ummi ce ta shigo ƴar gurin Hajiya Barau mai sunan mahaifiyarta hakan yasa take kiranta da Ummi.
Duk cikin ƴaƴanta mata ita kaɗaice tazo tarbon lefen. Kusa da mahaifiyarta ta xauna tana kallon yanayinta kallonta Hajiya Barau tayi


“Kin gani ke kina son kashe na ki aure su kuma suna yi, idan so kike ki dawo gida mu zauna sai ki dawo”


“Haba Hajiya wallahi ni na gaji da irin wannan rayuwar da yake nuna min, kwata kwata bana gabansa, baya da aiki sai neman mata, tun abu na ɓoye har magana ta fara fita, ko fita nayi sai ya kawo wata a gida”


“Ina ruwanki da neman matansa? Ai kedai yana baki ci da sha ko yana baki na kashewa ina ruwan ki da lamarin, yanzu neman maza ma ake balle mata, abun ai yyi ne wanda be yi ba to bashi da kuɗin yin ne, ko ni ya nema kya ce ki kashe auren ki ki dawo gida balle kuma wata can daban”


Miƙewa tayi tsaye cikin ɓacin rai ta fice, dan tasan duk yadda take son mahaifiyarta ta fahimci matsalarta ba fahimta zata yi ba.
Ƙwafa Hajiya Barau tayi taja wayarta tana soma labartawa abokin gulmarta rashin zuwan Namra tarbar lefen ƙannenta.


Duk hirar da suke be nuna mata jindaɗin hakan ko rashin jindaɗin saboda yana gaban Yasmin ne, yawancin maganar bata wuce uhn a'a ato, Har suka gama wayar.


Ƙaton cikin Yasmin ya kalla yana murmushi.


“Allah yasa karki haifa minɓɗa mai kahuwa”


Ta tsuke baki


“Mai hali dai baya fasa halinsa, ni wallahi haushi kake bani sosai”


“Daman duk kina da ciki ai baki ƙaunata kamar na kashe miki wani”


Ya faɗa yana jawo wayarsa da tayi ringing, number abokinsa Tahir ya gani.


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ”


Shine abunda ya furta bayan ƴan daƙiƙu da karɓa wayar.


“Okay gani nan zuwa”


Ya tashi tsaye da sauri, har Yasmin ta kalleshi


“Lafiya?”


“Wai Najeeb yayi hatsari, nan cikin gari”


“Subhanallahi, ina fatar be ji ciwo ba”


“Ban sani ba, sai naje tukunan”


Da sauri ya ɗauke Adnan da ke saman jikinsa ya ɗauki wayoyinsa ya zuba aljihu tare da keys ya fice hankali tashe.


*HILAL POV*


Lallaɓata yayi har sai da tayi shiru sannan yaja ta zuwa saman gadonsa ya zaunar da ita ya kama hannayenta ya riƙa.


“Na yarda ba ki aikata ba shikenan?”


“Har zuciyarka ka yarda da ni?”


“Na yarda da ke?”


“Zaka daina fushi da ni?”


“Zan daina”


“Zaka dawo da su Ezzah”


“Idan Hajiya ta yarda”


Haka yake ta amsa mata kamar tambayar babba da yaro, sai ya hau saman gadon yaja ta ƙirjinsa ya rumgume.


“I Love You”


Ƙamkamshi tayi


“I love you too”


Sun daɗe a haka kamin ya sake ta ya shiga yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin sai ta ɗauko masa abinci. Ba dan yana so ba ya zauna yayi ƴan lomomi kaɗan ya tashi ya nufi gidan Hajiyarsa.


Da shigarsa Ezzah da Ulfah da sauran yaran gidan suka rugo da gudu suka tarbeshi. Ulfah ce kawai ta tambayi Kalsoom Ezzah kan ko a jikinta. Bayan ya gama ganinsu ya miƙa musu chocolates ɗin ya shigo da shi sannan ya wuce gurin Hajiyarsa.


Tun daga yanayin yadda ta amsa masa sallamarsa yasan akwai abunda ya faru. Guri ya samu ya zauna yana kallon tv dake ɗakinta, kamin daga bisani ya gaishe ta. A maimakon ta amsa sai kawai ta hau shi da faɗa


“Yanzu fisabilliahi abunda kake ƙoƙarin yi kyautawa ne? Kace xaka kare ta idan kun je kutu bayan ga abunda tayi ma ɗan ka, irin waɗannan matan fa zama da du matsala ne dan kai ma xata iya maka haka”


Daga yanayin maganar ta ya gane Amina ce ta kawo mata zancen, dan ita kaɗai yasan yayi zancen a gabanta sai kuma Alh Bashir.


“Amman Amina munafukace wallahi, zuwa tayi ta faɗa miki ko?”


“Ai dole ta faɗa min mana tun da abun yayi mata zafi, ni kama rabu da wannan matar ka nemi wata ka aura”


“Gaskiya ba zan iya rabuwa da ita ba”


“To ko zaka auro wacce zata riƙa maka ƴaƴanka, dole ne ka ƙara aure ko kuma ka rabu da ita idan baka shirya zama da mata biyu ba”


“Haba Hajiya, kuskure ne nima a yanzu na gane ba ita ce ta aikata ba”


“To waya aikata? Ga abu ƙiri da muzu ka nemi takewa dan kana son ta, ah lallai ba banza ta barka ba, Ezzah ma tana ta faɗar irin abunda take musu a gidan, cin amana zalla”


Dariya abun ya bashi yau kuma Hajiya da kanta take irin wannan furucin.


“Babu maganin komai Hajiya, amman wannan matsalar nima ban san kan ta ba”


“To ni dai na faɗa maka ko ka ƙara aure ko ka rabu da ita, tashi ka bani guri”


Kansa ya dafe yana sauke ajiyar zuciya


“Hajiya ki fahimta...”


“Ba zan fahimta ba, ka tafiyarka kawai”


Yasan duk yadda zai yi ba zata fahimta sai kawai ya tashi ya fice da jimmar idan ta huce zai dawo ya fahimtar da ita.




-----------------------------------------------------------------


*Jiya naje biki ban samu na yi typing ba, so wannan zai zama na jiya, na yau kuma sai dare zan kawo. Thank you 🖤*




[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *60 - NOT EDITED ⚠️*


*RASHIDA POV.*


“Teema ya faɗa min abinda ya fi ƙarfin zuciyata da tunani, ya bani labarin yau da kuma gobe na, ƙoƙari raba ni yake da Ubangijina”


Ta faɗa cikin kuka, tana mai jin tsantsar ƙyama da kuma tsanar bokan a ranta, ta kuɗiri aniyar zata iya aikata komai akan duniyarta amman ba zata iya aikata abunda ya faɗa mata ta aikata ba.
Teema ta tsire baki, tana mamakin ƙawar ta'ta.


“Ai kin daɗe da rabuwa da raba hanya da Ubangijinki, tun da kika soma neman taimakon wani daga cikin bayinsa, Abunda zaki yi kawai ki aikata wannan in yaso daga baya sai ki nemi yafiyar”


“Ya ce min baƙin hudu yana bibiyata, kuma wannan baƙin duhun baƙar rana ce, what if ranar mutuwa na ne? Ba shine na farko daya faɗa min haka ba, Teema ina tsoro”


Kyalƙyalwa Teema tayi da dariya har da taɓawa tana kallon Rashida.


“Amman Wallahi kina da abun dariya, miye abun tsoro kuma? Ashe ke sabowar shiga ce wannan harka, ba lallai baƙar rana ta zama ranar mutuwa ba, yana nufin akwai abunda zai same ki marar daɗi wanda ke da kan ki zaki kira abun da baƙar rana”


Ta ɗan ji sassauci a zuciyarta, har ta samu damar haɗe yawun da ya tsaya mata a maƙoshi.


“Ni dai ina ganin haƙura zan yi, kar naje na sake mata kuma ya dawo kaina dan yace zan yi nasara amman akwai yiyuwar ya dawo kai na”


“Amman wallahi Rash kin ban mamaki, ke da na ke ganin, kamar zaki iya aikata komai akan Hilal, ashe son da kike masa na ƙarya ne, tun da har zaki iya bar wa wata shi, yanzu duk soyayyar da kuka yi ta tashi a banza kenan? Ƴaƴanki sun zama nata mijinki ya zama nata? Ko akwai wani wanda kike so bayan Hilal?”


“Babu shi, Hilal ne kawai, wallahi ina sonsa sosai”


“Kuma kin yarda ki barwa wata shi ko?”


“Na samu matsala akan jifar da nayi mata Teema, na jefeta ya faɗa kan ɗa na, kin ji ai yanzu yana faɗa min, yanzu haka Rafiq yana can kwance asibiti babu lafiya, ya damu matsalar ƙwaƙwalwa”


“Lallai wannan mata ita bata tsaya akan ta, irin wannan matar maganinta ki samu fitsari ki zuba mata a ruwa ya jiƙa ta sha, wallahi duk wani magani na tsari jikin data sha sai ya karye, amman kin ce tana shiga malamai ita ma?”


“Haka nake gani, saboda gaba ɗaya Hilal ya haukace ba shi da magana ta kowa sai na ta, baya kula ni a yanzu, kuma kin ga da dane ba zai iya sakina ba amman yanzu duba ki ga ya sake ni”


“To ina ganin ba tsari bane itama ta iya shige-shigen ne, sai aka bata aljana ta tsare ta, kin san wasu suna haka fa dan akwai su cimma burin su”


“Da gaske? Ballatana ta daɗe ba tayi aure ba zata iya haka”


“Dan haka ki kwantar da hankalin ki, ki share hawayen ki matuƙar ina raye sai kin koma cikin ƴaƴanki, yanzu kin ga mun fito cikin tashin hankali baki masa sallama ba, amman yanzu idan hankalinki ya kwanta natsuwarki ta dawo jikin ki, sai mu koma yayi mana aikin kawai”


“Amman ya ce sai nayi fashin salla fa?”


“To miye a ciki? Wasu ma baki ga rai suke kashewa ba? Ai daga baya sai ki ranka ki nemi yafiyar ubangijinki Allah fa gafurun rahimun ne, kin ga sai ma ki daina kwata kwata”


Shiru tayi tana nazari, tasan idan har ta aikata wannan abun ta yi, babban saɓo, ta yi fashin salla saboda biyan buƙatar da bata da tabbacin zata biya? Ajiyar zuciya ta sauke ta cigaba da tuƙin.


“Zan yi tunani akai Teema, amman ina jin tsoro sosai”


“Ai da tsoro zaki cuci kan ki, kawai ki cire wannan tsoron ki yaƙi zuciyarki”


“Zan yi ƙoƙarin yin hakan”


Daga nan Teema ta ɗauko mata firar ƙawarsu, ita mai bin bokaye marar tsoro, wance ta mallake miji da uwarsa.
Duk tana yi ne dan kawai ta ƙara tunzira Rashida ta aikata, so that ita ma ta samu abokin shiga wuta, dan mugu be son ace shi kaɗai yake aikata abu.
Sai da ta fara biyawa ta sauke Teema a gidansu, sannan ta wuce na su gidan dan ta yi shirin zuwa gurin aiki, ganin karfe ɗaya ma bata yi ba.


Tun da tayi parking a harabar gidansu ta fara saƙe-saƙen abunda zata faɗa gurin aikin, dan gaba ɗaya kashe wayarta tayi. Tana shiga falo sai ga Momy ta fito daga ɗakinta jiki na rawa, Rashida na ganinta ta gane hankalinta a tashe yake.


“Momy lafiya?”


“Lafiya ba lau ba, tun ɗazu nake cikin zullumi Rashida”


“Me ya faru?”


Momy ta tsaya tunanin ta inda zata soma, dan tana jin faɗin kalamar kai tsaye.


“Safiya tace min ta ga ƙawarki Asma'u a... Hiv unit....”


Yadda kasan cida haka gaban Rashida ya riƙa faɗuwa, zuciyarta na zillo kamar ta fito, a take yawun bakinta ya tsarƙe ta har sai da ta soma tari. Tasan Momy ba Asmee take nufi ba, idan kuma har da gaske Asmee take nufi to Safiya ce ta faɗa, kuma taya Safiya zata ga Asmee ita ce ta gani.


“Safiya ce ta faɗa?”


Momy ta ɗaga mata kai tana hawaye.


“Ni ta ce ta gani ko?”


Nan ma kai Momy ta ɗaga mata.


“I tell not once not twice several times, naje nemanta ne a asibitin amman ta ƙi ta yarda gani take kamar ni ce naje a karan kai na...”


Maganar take tana nuna da gaske take, amman bata son kallon Momy. Kai Momy ta girgiza na tausayin ƴarta da kuma ganin wautarta akan abunda take ta ƙoƙarin ɓoyewa.


“What about the results?”


Da sauri ta kalli Momy, tana mamakin kalamanta. Kenan bincike suka mata lokacin da bata nan! Ita da tayi ma results ɗin mugun ɓoyo taya aka yi suka gani?
Durƙushewa tayi a gurin ta fashe da kuka mai ƙarfin gaske. Momy bata san lokacin data ƙarasa gaban ƴarta ta rumgume suka soma kukan tare.


“Taya haka ya faru Rashida ta ya? Miyasa kika yi ƙoƙarin ɓoyewa?”


Cikin kuka Momy take tambayarta, tana jinjigata. Da sauri Rashida ta zame jikinta daga na Momy ta tashi da sauri ta shige ɗakinta ta kulle da maƙulli. Jinginawa tayi jikin ƙofar tana kuka, irin kuka mai sa kaji kamar ka cire ranka ka huta.


Momy ma kuka take sosai, dan yanzu ne ta ƙara tabbatar da zancen Safiya. Daman tun Safe Safiya ta shiga ɗakin Rashida tana mata bincike har Momy ta same ta a ciki, anan takr faɗawa Momy haɗuwarsu da Rashida a asibiti. Da kuma maganin da abokan aikinta suke bawa ƙawarta Asmee, a wacan Asibitin ta su.


Babu irin bugun ƙofar da Momy bata yi ba, amman Rashida ta ƙi ta buɗe, kuma ta ƙi tayi magana, sai kuka take. Waya Momy ta ɗauka ta kira Dady ta faɗa masa, cikin ƴan'mintuna sai gashi ya dawo gida hankali a tashe, ɗan har gumi ke keto masa ta ko'ina.


Kai tsaye ɗakin Momy ya nufo, sai ya same ta itama tana kuka.


“Ya aka yi haka ta faru? Amman an tabbatar?”


Kallonsa Momy tayi idonta na zubar da ƙwalla.


“Safiya ce ta faɗa, nima ban yarda ba har dai yanzu dana nuna mata na ga takardun, bayan kuma ban gansu ba nace ne kawai dan na gano gaskiyarta, kuma the way she act ya nuna tana da shi”


Jiki a sanyaye Dady ya zauna idonsa sun rine sun yi wani ja sosai, irin na ɓacin rai da damuwa sun sauka ga mutum. Can kuma ya sauke ajiyar zuciya yana ta nazarin inda Rashida zata samo hiv da tsakar rana.


“Amman ƙara dai a bincika, ba lallai ba ne tana ɗauke da ciwon to ina ma zata kwaso wannan ciwon?”


“Hilal mana, ai shi kaɗai ne mutunen da take taraiya da shi”


Cewar Momy tana kuka, zuciyarta na ayyana mata shi ɗin ne tun da shine kaɗai mijin Rashida. Da sauri Dady ya kalleta


“Wallahi idan kuwa shi ne ya saka mata shi, sai na ɗaure shi gidan yari har ƙarshen rayuwarsa, marar mutumci marar taddako wanda be san halin girma ba, Allah ya usar mana, wallahi ya cuce mu, shiyasa ya sako ta. Ina Rashida take ne?”


“Tsna ɗakinta, ta ƙi ts buɗe tun ɗazu sai kuka take, ta ƙi tayi magana ma”


Tashi yayi yana cire ƴar saman suit ɗinsa, yana sassauta necktie ɗinsa, ya nufi ɗakinta jikinsa har rawa yake kamar mazari.


Sai da ya soma kiran sunanta, jin bata amsa ba yasa ya soma ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin.


“Rashida ni ne buɗe mana... Ba wani abun za mu miki ba kawai magana za mu yi, kuma ba zamu faɗawa kowa ba”


Tana jinsa amman ta kasa amsa masa dan bata da abinda zata faɗa masa, tasani matuƙar suka gano gaskiyar dalilin cutar nata ba zasu zauna da ita ba, who else kuma zai zauna da ita bayan iyayenta, lallai ko a haka rayuwa ta tsaya mata ta san ta kai karshenta.


Babu irin maganar da Dady be mata na rarrashi da tausasa zuciya ba, amman ta ƙi ta amsa masa balle ma har ta buɗe ƙofar.
Dawowa yayi ɗakin Momy ya tsaya daga jikin ƙofa fuskarsa da damuwa ya ce


“Ko dai za mu kira shi ne mu tambaye shi?”


“Idan shine taya zai amsa cewar shi ne? Zai yi ƙoƙarin kare kansa ne, kuma kasan babu wanda Rashida take mu'amala da shi sai Hilal dan shin mijinta kuma ni ƴata ba ƴar iska ba ce, ta bakinta ya kamata aji komai”


“Ta ƙi tayi magana, ɗakin ma ta ƙi ta buɗe”


“Zata yi magana, dole zata buɗe kabarta hankalinta ya kwanta kawai, ka koma gurin aikin ka”


“Ba zan iya wani aiki ba ko naje, jikina ya riga da ya mutu, Wallahi Hilal ya cuce mu, amman miyasa Rashida ta yi ƙoƙarin ɓoye irin wannan babban al'amari?”


“Allah kaɗai ya sani, amman rufawa irin wannan mutumen asiri ai ba abun yi ba ne, wallahi sai na sashi yayi nadama sai ya ƙwammace kiɗa da karatu”


A bakin ƙofar Dady ya zauna irin zaman nan na baka san ka yi ba, hankalinsa baya jikinsa, natsuwarta ta gudu ta barsa.


*NAMRA POV.*


Maganganun Asim sun tsaya mata a zuciya, duk bayan dogon numfashinta sai kalmar rabuwa da yayi mata ya maimata kanta a kunnenta. Da zancen ta kwana a ranta, tana mamakin Asim, yadda yayi tsaye yana faɗa mata magangu kamar wani ɗan shaye-shaye. Bw ɗauke a matarsa ta sunna ba be riƙe ta da muhimmaci ba, shiyasa har ya zaɓi aikin da yake sama da ita, yanzu kuma yake neman rayuwa da ita saboda tana da ciki. Sai yanzu take nadamar rashin bin Anty, dan tasan babu makawa Asim rabuwa zai yi da ita, matuƙar bata zubar da cikin ba, dan ta ga gaskiyar maganarsa a idonsa, sai dai ita kuma bata jin zata iya zubar da cikin ko da kuwa shege ne balle na Sunna.


Sai dai idan Asim ya sake ta ina zata je? Ta koma gida da ciki ta faɗawa Abbah Asim ya sake ta? Ta bi sawon Anty bayan ta nemi taje gidan ta ƙi yarda sai yanzu da Asim ya sake ta kuma take ɗauke da cikinsa.?
Tashi ta yi zaune, sai ta nemi kuka da take ta rasa, washe ƙaramin abun ake yi ma kuka, tashin hankalin dake tare da ita baya barin hawayenta zuba.


“Kaico na ni Namra, Ina zan sa kai na sanyi? Ina zan sa rayuwar na samu sassauci? Haƙiƙa wanda duk ya so abinda iyaye suka ƙi yayi hasara, da nasan haka aurena da Asim zai kasance da ban aure shi ba, Allah ka yi min gata Allah”


Hannayenta ta ɗaga sama, tana roƙon Ubanjiginta, zuciyarta cike da yaƙinin lallai Allah zai ƙarɓa mata.


“Ya Allah ka tsare min mutunci na, ka tsare min lafiyata,
Allah ka yi min gata ka tsare min imani na da hankalina,
Allah ka yi min sutura ka kwantar min da hankali
Allah ka kyautata min rayuwa ta, Allah idan aure da Asim Alheri ne Allah ka tabbatar da shi, idan rabuwa da shi ne samuwar jindaɗina Allah ka zaɓa min abunda yafi zama Alheri a gare ni,
Allah ka shirya tsakani na da iyaye na, Allag ka gafarta min kurakurai na
Allah ka tabbarda duga duga-dugaina akan addinin ka”


Bayan ta shafa ta koma ta kwanta, ta kai hannu ta shafa cikinta, tana mai jin tsantsan ƙaunar abinda yake kwance a mararta.


*ABDOOL POV.*


Misalin ƙarfe biyu da rabi na rana jirginsa max air ya sauka a tashar sauka da kuma tashin jirage da ke katsina.
Be sanar da Ummi zuwansa ba, dan haka be tsamaci ta tarbe shi ba, ko ta aiko da motar da zata ɗauke shi. Sai dai hakan be a aiko masa da motar da zata ɗauki daga headquarter ba dan sun san da zuwansa.


A yadda suka tarbi shi ya burge kowa a gurin, mota uku suka faka. Already sun buɗe motar suna hangosa tafe sai suka duk suka fito wajen motar suka tsaya, a jikin kayan gida yake amman hakan be hana dukansu su tsara masa ba, babu wanda yayi motsi a cikin su har sai da ya shiga motar sannan suka rufe masa suka shiga.


“Gurin Mai Martaba zamu je”


Yanda yayi maganar ba ka ce shi ne ba, dan hankalinsa gaba ɗaya yana kan wayarsa sai faman duba shafukan yana gizo yake dan sanin abinda ƙasa take ciki.
Har aka isa Ahmad Mai-doki road, Abdool be ɗago ya kalli mai driving ɗinsa ba, balle ti-ti. Yana jin motar ta tsaya ya buɗe ya fito ƙamshin gidan ne yasa shi murmushi, dan ƙanshim gidansu daban yake, ko'ina ya ke zai iya gane ƙanshin gidan Mai-martaba.


Sai da ya shiga cikin gidan ya gaishe da mahaifansa, matan sarki sannan ya wuce faɗar mai-martaba. Be same shi a faɗar ba, hakan ya tabbatar masa da yana can turakarsa yana hutawa, tun da yaga motocinsa a waje balle yayi tunanin ko ya fita. Ta faɗar ya bi ya shiga turakar Mai-Martaba, a falon farko ya same shi zaune yana duba air conditioner da ake kan saka masa. Faɗawan na ganin Abdool duk suka faɗi suna ɗiban gaisuwa, shi dai hannu kawai ya ɗaga musu dan baya son irin gaisuwar nan da suke masa, ya fi gane a tsara masa ko a maƙe idan an ganshi. Da murmushi ya zube gaban mahaifinsa yana ɗiban gaisuwa.
Kallonsa Mai-Martaba yake da mamakin zuwan ba zata ta, sai kuma ya kai mafeshin Peacock dake hannunsa ya shafi ka ɗansa da shi. He didn't say a word dan baya son magana da Abdool a gaban faɗawansa ko baboro, yafi son sai ya keɓance yadda zai dake da shi kamar ba ɗansa ba.
Ko ba komai nuna tsantsar ƙaunar da kake wani daga cikin ƴaƴansa babban laifi ne kuma ya kan haddasa ƙiyayah, sai dai hakan be hana familynsa depending ya fi son Abdool da kowa ba, dan abu ne da ko ya ɓoye sai dai ya ɓoye mai yawan ka buɗe kaɗan.


Yana unƙurawa zai miƙe tsaye sai faɗawansa suka zo da sauri suka tara rigunansu, suna masa kirari har ya miƙe tsaye sannan suka rufa masa baya suna masa fita.
Hannu kawai ya ɗaga musu suka fahimci baya buƙatar su raka shi har can, sai kawai suka juyo gurin Abdool suna masa nasa kirarin. Be tsaya jinsun ba ma balle ya nuna masu jindaɗin abunda suke masa sai kawai ya bi bayan Mai-Martaba hannayensa laƙƙame a baya yana tafi guda-guda kamar mai takewa President baya.


Sai da suka wuce falon biyu da na uku, suka wuce garden ɗin Mai-martaba sannan Mai Martaba ya ƙarasa a wata ƴar ƙaramar rumfa mai kyau da ɗaukar hankali ya zauna, shi kuma Abdool ya zauna ƙasa complain ɗin kiraren da suke masa.
Ɗan murmushi Mai-Martaba yayi irin na na manyan sarakuna, yana kallon ɗan nasa cikin farinciki da jindaɗi.


“Wata rana kai Sarki Abdool, irin wannan kalaman be kamata yana fita daga bakin ka ba”


“Haba Mai -Martaba

Please Login or Register in order to submit comment