Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallama magariba sannan ya bada aka siyo mata tea, yadda yake damuwa ta ci abinci shi kansa be damu da ya ci abincin ba, sam mantawa yake da nasa ciwon wata ƙila ko dan be jimu sosai ba, yake dauriya irin ta maza, ko kuma dan hankalinsa ya ɗauko gurin Namra ne. Shi kansa yana mamakin yadda yake damuwa da Namra, sai dai yana fi karkata hakan da tausayinta da yake, su kansu su Neina suna kula da halin kuwalar da Lamido yake bawa Namra, duk da sun san halinsa na karancin amman wannan kamar yana ƙoƙarin wuce guri, dan ko magana ake Namra ta saka baki zasu ga ya tattara hankalinta ya miƙa mata ya natsu sosai yana saurarenta.


Yau Neina taja Namra da fira sosai musamman bayan Sallah isha'in nan, abinci na fula take labarta masa da kuma al'adansu na fulani, a nan take taɓo labarin Baban su Lamido da kuma ƙuruciyar Lamido, dariya sosai Namra take idan ana faɗin labarin halin ƙiriniyar da Lamido ya yi. Shi kam iya karsa murmushi idan Neina ta faɗi wani abun.


“Salamu alaikum, wai Abdullahi daga Katsina ya ce yana kiran Namra”


Dam dam dam, gabanta ya tsinke ya faɗi, duk wani farinciki da yake zuciyarta sai ya ta neme shi ta rasa, a take murmushin fuskarta ya disashe. Da sauri ta kalli almajirin dake tsaye can jikin ƙofar gidan yana jiran amsa.
Bata san ko waye ba, amman jikinta ya bata wani yanayi na daban, ga shi kuma anxe daga Katsina, kuma an faɗi sunanta, lallai ko wanene ya santa. Sai dai ya akayi ya san inda take zaune? Miyasa be zo da rana ba sai da dare? Shin waye Abdallah ma? Ko dai Asim ne ya canja suna? Amman taya Asim zai san inda take?


“Ko mijin ki ne?”


Tambayar da Lamido yayi mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. Kai ta girgiza.


“A'a ba haka ne sunansa ba”


“Ɗan'uwan ki ne?”


Shiru ta yi tana tunanin irin amsar da zata bashi, idan har ta ce ɗan'uwanta ne zata sanu damar fita ta ga ko waye ne, to idan kuma ya kasance Asim ne ya canja suna fa?
Idan ma shi ɗin ne ai babu yadda zai yi da ni, dan yanzu babu aurensa a kai na, idan kuma har aurensa ya zo maidawa to yayi satti, dan na cika idda tun da na yi ɓari!


“Eh ɗan uwana ne”


Sai a sannan hankalinsu ya ɗan kwanta, Neiɓa ta ce da almajirin.


“Je ka ce tana zuwa”


Sai da almajirin ya juya sannan ta kalli Namra ta ce.


“Ɗauki fitila ki je”


Miƙewa tayi tsaye sai Lamido ya ce.


“Ya aka yi ya san gidan nan?”


“Ni na kwatanta masa, a waya”


Kai tsaye ta bashi amsar ta nufi fitilar ta ɗauka ta nufi ƙofar fita gabanta sai faɗuwa yake. Sam Lamido be so ta fita ba, haka kawai ya samu kansa da rashin jindaɗin kiran da aka mata duk da be san me kiran ba. Neina kuma ta kawo wani zargi a ranta, dan tana ganin kamar Namra ta ɓoye musu wani abu ne.


Zuciyarta cike da tsoro ta fita daga gidan, da tunani biyu, Asim ne ko kuma wani nasa yake mata sallamar. Bata ga kowa a ƙofar gidan ba, hakan yasa ta ɗan ɗaga fitilar tana yade, hangota da ya yi yasa ya tako ya ƙaraso kusa da ita.


“Assalamu alaikum”


Ya furta nata cikin murya mai taushi, da sanyaya zuciyar mai sauraro.


“Amin wa'alaikassalam”


Ta amsa masa ba tare data wayence shi ba. Ya ɗan yi gyaran murya.


“Na san baki gane ni ba”


Ya fido wayarsa ya kunna fitar wayar ya haska fuskarsa. Wannan karon ba faɗuwar gaba kawai Namra ta ji ba, har da tsoro, ja tayi da baya yana nuna shi da yatsa, sai maganar ta naƙale ta ki fitowa.


“Nasan zaki yi mamakin gani na, amman ina son ki ba ni aron lokacin ki kuma ki saurari abunda zan faɗa miki”


“Ba kai ba ne ɗan sarki daya kaɗe Lamido?”


“Ni ne, kuma na san ba a nan kika san ni ba, a Katsina ko?”


Kai ta ɗaga masa duk da bata da tabbacin zai ga hakan kasancewar akwai duhu a gurin.


“Miyasa kake bibiyata?”


“Ba saboda ke na zo garin Kaduna ba, ke ma kuma ina da tabbacin ba dan ni kika zo ba, amman zuciyata ta kasa natsuwa da hakan, direba ne ya kaɗe yaron gidan sai kuma na gan ki a gidan shine abun yake bani mamaki, bayan nasan a Katsina na san ki”


“Ba wasu kalamai na ce ka min ba, amman bari na gargaɗe ka, karka sake zuwa ƙofar gidan nan da sunan gurina ka zo”


Ɗan murmushin takaici da mamaki yayi.


“Babu mace da ta taɓa ɗaga hannu ta mare ni sai ke, babu mace da nake gani na bibiya sai ke, babu mace da ta taɓa faɗa min irin wannan maganar sai ke. Zan bar ƙofar gidan nan amman ina son ki faɗa min tsakanin ki da Allah kina da aure? Kuma ina son ki faɗa min tsakanin ki da Allah waye Mahaifinki, kuma miye alaƙarki da mutanen gidan nan?”


Wani haushi ne ya cika mata zuciya, har take jin kamar ba zata iya amsa masa tambayoyinsa ba, amman Allah daya haɗa ta da shi ne take jin ba zata ɗaga daga gurin ba har sai ta ba amsa.


“Ba na da aure, kuma babu wata alaƙa tsakani na da mutanen gidan nan, sunan Mahaifina Manjo Usman Zamau”


Bata tsaya jiran Abunda zai ce ba ta juya ta shige ciki gidan. Shi har tsoro ta bashi cox the way da take bashi amsar kamar tana masa faɗa.


“Wow”


Ya faɗa yana shafa fuskarsa, kamin ya zuba hannayensa aljihu ya nufi motarsa.










Sorry for the short chapter 🙏🙏🙏
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *70*


‘Manjo Usman Zamau, Manjo Usman Zamau’


Sunan yake ta maimaitawa, tana tunanin kamar ya san mai sunan amman ya kwanta masa, sai dai jin Manjo ma ya tattabatar masa da soja ne.
Murmushi ya samu kansa da yi lokacin daya tuna wasu kalamai da Namra ta yi masa.


“She's so Unique”


Rage gudun da yake, ya fido wayarsa ya nemo number Sadiq ya aika masa kira. Ringing ta yi sai da ta kusa katsewa sannan aka ɗaga.


“Shegen gari baka kira sai ta samu”


Ƙyalƙyalewa ya yi da dariya.


“Chief Sadiq Northwest”


“Au yau Chief na samu kuma? Kai dai faɗa min abunda yasa ka kira ni”


“Kiran ka kawai na yi na gaishe ka, ko kuskure ne kiran manya kuma?”


“Na ji, ya gida ya hutu, ku ai kun samu hutu”


“Gaskiya ba laifi, amman ba wani mai yawa ba ne, ina Madam”


“Madam na nan ƙalau go straight to the point miyasa ka kira ni?”


Dariya sosai Abdool ya yi kamar ba shi ba, sam ba zaka za ci akwai mutumen da Abdool yake sakewa da shi ba, bayan mutanen gidansu.


“Kasan waye Manjo Usman Zamau?”


“Aha ni nasan akwai wata a ƙasa, ai baka kiran mutum hakan nan kawai”


“Ni dai amsa min kawai, ban ce ka min surutu ba”


“Na san shi, kai ma ai kasan shi, amman yanzu ya yi ritaya ai”


“Nima ina jin kamar na san shi amman sunan ya kwanta min”


“Ai mun yi zama barrack da shi ai, a Yola, shine mahaifin su Salwee and Abdulraman na manta sauran ɗiyansa dai, yanzu ina jin yana sokoto zaune, ance ya zama babban ɗan siyasa ma”


Abdool ya bugu sitiyari motarsa da ƙarfi.


“Yes I knew it!”


“Easy Man what happened to him?”


“Ba komai, kawai wani ɗan bincike na ke ne”


“Okay abokin su ekwieu ne tare suka yi aiki, suna shiri sosai”


“Amman kana da addireshinsa?”


“Kai Malam, tun da ba shi na ke wa aiki ba, haka kawai zan aje addireshinsa”


“Okay okay bye”


Sai kawai ya katse kiran zuciyarsa cike da farinciki. Wata number ya sake lalubowa ya aika mata kira.


“Salim a bincika min addireshin Manjo Usman Zamau mai ritiya, kuma a bincika min a cikin ƴaƴansa akwai Namra, aɗan min bincike akan ta”


Be jira abunda Salim ɗin zai bashi amsa ba ya katse wayar, dai-dai loƙacin daya faka a harabar gidan. A yanayin yadda ya shigo cikin gidan ba zaka ce shine ɗazu ya fita a haka ba, yadda ka san wanda aka yi bushara da aljanna haka ya dawo fuskarsa a sake, zuciyarsa fari ƙal.


Yana shigowa falo ya zauna saman cushion yana kallo falon kamar wani baƙo. Kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yana ciki nishaɗi, dan hankalinsa ma baya gurin da yake kallo. Wayar hannunsa ya kallo kamar mai son magana da wayar, sai kuma ya watsa yatsunsa saman screen ɗin ya danna number Sadauki, bugu ɗa ya ya ɗauƙa.


“Sadauki ga ni a falo ina jiran ka”


Be jira abunda Sadauki zai ce ba, ya katse kiran fuskarsa shinfide da murmushi. Ba ayi minti biyu ba sai ga Sadauki cikin falon da rawar jikinsa.


“Allah ya taimaki Yarima, Allah yaja kwanan ka, Allah ya baka abunda kake so”


Abdool ya kallesa fuskarsa da Murmushi.


“Amin Sadauki, addu'ah tana tasiri sosai, kaga Allah ya fara ba ni nasara. Yariman ka ya kusa samun gimbiya”


Sadauki ya riƙe baki tare ta washe da dariya


“Mashallah, babban goro sai magogin ƙarfi, Allah ya taimaki Yarima, Mai Martaba zai fi kowa jin farincikin wannan labari”


Abdool ya ɗan risino daga zaunen da yake


“Ya kake auna farincikin Mai Martaba idan ya samu labarin na samu matar aure?”


“Allah ya taimake ka kamar mutum ne, da yake cikin tsamman nin ƴanci, yake cikin baƙin ciki da damuwa, ga yunwa da ƙishin ruwa ya dame sa, masaukinsa kuma babu daɗin zama, me kake tsammani idan aka aka basa sabon masauki mai cike da ƙuramon wanka, ga kuma abinci da abun sha, bayan kuma an ƴanta shi?”


Komawa Abdool ya yi dai-dai saman cushion ɗin ya ɗora hannayensa saman kushin ɗin yana kallon silin.


“Zai kasance mai tsananin farinciki, har zai ji kamar ya haɗe zuciya ya mutu saboda jindaɗi”


“Toh haka zuciyar Mai Martaba zata kasance matuƙar ya samu labarin Yarimansa ya samu Gimbiya”


Murmushi mai ƙayatarwa Abdool ya yi, ba tare da ya kalli Sadauki ba ya ce


“Bana Sadauki da kai za'aje Umara”


Faɗuwa Sadauki ya yi yima Abdool godiya, yana zuba masa kirari, da yabo. Hannu Abdool ya ɗaga masa alamar ya tashi ya bashi guri, haka ya tashi ya fice baki har kunne tsabar murna da farinciki.


Sai da Sadauki ya fice sannan Abdool ya maida dubansa gurin wayar yana lalubo number Mai Martaba. A handsfree ya saka wayar ya ɗorata saman center center tebur ya nufi freezer ya bude ya ɗauko power horse, ya kai bakinsa.
Daga inda yake tsaye yana jiyo muryar Mai Martaba da yayi picking wayar tare da sallama.


“Allah ya taimaki Mai Martaba, i have a good news for you”




“I have good news for you too Son”


“Amman nawa ya fi na ka daɗi, dan nawa idan ka ji ma sai ka bani goro”


“Nima ai sai ka bani goro ba kuma ɗan ƙarami ba ma”


“Me zaka ba ni idan nayi maka albishir da abunda ka daɗe kana jira”


“Zan baka yankin Bakori da kewaye, kuma za a naɗa ka motar Mai Martaba kai fa wace kyauta zaka min?”


Zauna Abdool yayi saman kujera yana dariya har da buga ƙafa, ko ba komai Sarautar da Mai Martaba ya ce zai bashi ta sashi dariya balle kuma yau yana cikin nishaɗi.


“Ni kuma bana da gumi na zaka je Ummara gaida Ubangiji”




“Lallai yau Ɗan Sarki yana ciki farinciki, ɗan tsakura min kaɗan daga cikin labarin ka mana”


“ Ina ai ba tsakure, sai ga ni ga ka, gobe zan sauka sokoto cikin rahamar ubangiji, kuma ba zan kwana ba, har sai na labarta maka abunda zan labartawa Ummi”


“Allah ya kai mu, ya dawo da kai lafiya”


“Amin ya Rabbi. Na gode Mai Martaba, mu kwana lafiya”


Daga haka suka yi sallama, sai Abdool ya ɗauki wayarsa ya nufi bedroom yana kalle kallen gidan kamar yau ya fara shigo shi.
Bayan ya rage tufafin jikinsa ya aika ma wani yaronsa saƙo. Akan ya nema masa jirgin da zaije Katsina gobe.


Bayan kamar minti goma sha biyar yaron yayi masa reply da akwai wanda zai tashi da safe zuwa Katsina.
Daga nan Abdool ya aikama Sadauki da text na maganar tafiyarsu gobe gida, akan yayi duk abunda ya kamata cikin lokaci, duk da be so hakan ba, sai dan Ummi da ranta ya ɓaci.




NAMRA POV.


Da tunanin abunda zata faɗa ma su Neina ta shiga gida, a ɗayan ɓangaren kuma tana tunanin bibiyar da Abdool yake mata. Babu abunda ya fi tsaya mata a rai kamar tambayoyin da ya yi mata.


“Har ya tafi?”


Tambayar da Neina ta yi mata ya firgita ta, har ta zabura, sam bata san ma ta kawo kusa da su ba.

“Eh ya wuce”


Karaf idonta cikin na Lamido da ke dannar waya, kasa kawar da idon ta yi, shi ma kuma ya kasa janye nasa, suka yi ta kallo kallo ita da shi, har sai da Uwani ta maimaita tambayar da take mata.


“Na ce shi ne wanda kika sani ɗin?”


Sannan ta lumshe ido, tana sauraren bugun zuciyarta. Kamin daga bisani ta buɗe idon dake cike da hawaye ta kaɗawa Uwani kai alamar ‘Eh’ ta wuce ɗaki.
Samun kanta ta yi da kuka marar dalili, wani abu take ji yana ratsa mata zuciya mai wuyar fassara, numfashi take da ƙarfi kamin ta samu saita kanta, ta numfasa a hankali tana gode Ubangijinta.


Abdool ya tsaya mata a rai, tambayar ina ya fito ina zaije ya hana ta sukuni, wace manufa yake da ita akanta, shi ya hana ta rumtsawa har dare ya raba.




RASHIDA POV.


Hawaye ne suke mata masu zafi sosai suke mata zuba, keys ɗin dake hannunta take ta juyawa, tana mamakin irin abunda iyayenta suka mata.


‘Ashe akwai ranar da iyaye suke tsanar ƴar cikin su? Ashe rana zata zo da Momi da Dady zasu buƙaci na bar gidan nan? Ban ga laifin Hilal ba dan ya zaɓi rabuwa da ni, ga shi yanzu iyayena ma sun zaɓi haka’


Matsa ƙwallar tayi ta kai hannu ta ɗauki wayarta ta nemi number Teema ta aika mata kira.


“Ƴar gari”


“Teema kin ce zaki shigo kuma har yau baki zo ba, wallahi ina cikin matsala”


“Me ya faru wace irin matsala kuma?”


“Daddy na roƙa ya ba ni keys ɗin gidansa da yake by pass”


“Me hakan yake nufi?”


“Zan fi jindaɗi idan ina ni kaɗai, shiyasa na roƙa ya bani gidansa can na zauna, kuma ya anince min, yanzu matsalar da nake ciki ta rashin makama ne, Teema ina son na koma gidan miji na ko ta halin yayana”


Daga can cikin wayar Teema ta sauke ajiyar zuciya.


“Rashida miyasa ba zaki haƙura da mijin nan ki ba? Ya nuna miki ƙiyayya tsantsarta, ki ƙyale shi mana, Allah zai kawo miki wani”


“Teema har yanzu baki san miye so ba, saboda ba ki taɓa yi ba, bakin irin zafin da mace take ji idan ta rabu da uban ɗiyanta ba, dan Allah ki taimaka min”


“Gaskiya Rashida taimako ɗaya zan iya miki, kawai ki haƙura da shi, Allah zai saka miki, amman idan kuma baki ji ba, zan zo gobe na kai ki gurin wani malamin wanda zai taimaka miki ko Allah zai sa a dace”


“Eh ki zo dan Allah, da ƙarfe nawa zaki zo?”


“Tara da rabi?”


“Sai kin zo, daga nan ma sai ki taya ni maida kayana wacan gidan”


“Okay Allah ya kai mu”


“Amin Sai na ji ki”


Ta katse kiran tana share hawaye.


“ I deserve happiness, Allah ka duba lamari na, Allah ka sassauata min wannan rayuwa, ka rufa min asiri, Allah ka juyo da hankalin mijina a gare ni, Allah na tuba ka yafe min”


Ta shafa addu'ar fuskarta shakaf da hawaye, tana jin tsantsar nadamar zinar data aikata da aure, tun da itace silar shigarta duk wannan halin da take ciki, ta rasa kowa nata saboda ciwon dake jikinta, idan ta tuna yadda Mahaifinta ya matsu ta bar gidan sai ta ji kamar ta haɗiye zuciya ta mutu.





KALSOOM POV.


“Anty Kalsoom, Daddy yana kiran ki, yana falon baƙi tare da Hilal da Abban Hilal”


Da sauri Kalsoom ta ɗago ta kalli Saleena dake tsaye riƙe da gambun ƙofarta tanaata magana. Gabanta ya faɗi sosai, a take ta aje jaridar dake hannunta ta ɗauki Hijabinta ta saka, ta ƙaraso kusa da ƙanwarta Saleena.


“Me kika ji suna tattaunawa?”


“Ban ji komai ba, amman dai har Momi tana can, kuma duka fuskokinsu ɗauke da farinciki”


Ajiƴar zuciya ta sauke sannan ta ratsa ta gefen Saleena ta nufi hanyar da zata sadata da falon Dady, zuciyarta cike da fargaba.
Cikin natsuwa ta shiga falon, bakinta ƙumshe da sallama, sai da ta fara gaishe da Abban su Hilal sannan ta zauna kusa da Momi kanta ƙasa.


“To ga mijin ki nan shi ba zaki gaishe shi ba?”


Cewar Dadyn Hilal yana murmushi, sai duk suka sa dariya har Hilal ɗin da zuciyarsa ke cike da farinciki. Dady ya kiran sunan Kalsoom a natse, ta yadda zata maida hankali ga abunda zai faɗa mata.


“Kalsoom. Hilal ya mayarda sauran igiyoyin aurensa da ke tsakaninku, kuma yace yana da buƙatar ki koma ɗakin ki”


Samun kanta ta yi da kasa furta ko da kalma ɗaya, wani abu ta ji yana ratsa zuciyarta shi ba farinciki ba, ba kuma ɗan 'uwansa ba, wato baƙinciki. Su kuma duk natsu suna son su ji abunda zata ce, ganin hakan yasa Abban Hilal magana.


“Ai ba zata iya cewa komai ba, kasan ita mace ce, kuma ko ba komai suna son junansu. Kawai shiga tsakani ne irin na mata, kai kuma ka biye musu ka zama macen”


Dadyn Kalsoom ya ƙyalƙyale da dariya.


“Matan ne ai sai a hankali, ni na so ta zauna har sai yayi auren ne, tukuna ta koma, zamanta a can a yanzu zai ƙara saka tsanarta a zuciyar Hajiya ne kawai”


“A a ƙara ta koma ɗakinta, aure kuma ban hana yayi ba, kin dai shirya zama da kishiya ko?”


Ya ƙarasa yana kallon Kalsoom wacce ta noƙe kai tana mai jin kunya.


“Tashi ki ɗauko kayan ki muje”


Sai a lokacin Momi ta saka baki


“Tun yanzu ai da an bari har gobe sai ƙanwarta da Ƙawarta ta raka ta”


“A'a nima ai na isa na rakata, tashi ki ɗauko kayan ki”


Kasa tashi Kalsoom ta yi har sai da Momi ta zo ta riƙa ta suka bar falon tare. Daddy Hilal ya kalli Daddyn Kalsoom yana faɗin


“Wato abun ne da ɗaure kai, kasan kuma zuciya wani lokacin bata da ƙashi, ni kai na abun ya ɗan ɗaure min kai da farko, amman ganin soyayyar dake tsakanin dole a ɗaga musu ƙafa, kuma koma minene shi uban ɗa be yarda ba, kai miye na ka a ciki har ka raba musu aure ƙaramar ƙwaƙwalce kawai ta mata”




Murmushi Dadyn Kalsoom ya yi ya girgiza kai


“Allah dai ya kyauta ya bayyana gaskiya”


Dukasu suka amsa da Amin har Hilal dake ƙoƙarin miƙewa tsaye.


YASMEEN POV.


A gajiye ta aje hakar hannunta ta karɓi Babynta daga hannun mai mata reno tana murmushi.


“Sorry Dear i'm back”


Uzair ya aika mata wani kallo mai cike da jin haushi.


“Ni fa wannan aikin na ki ya ishe ni, ace har kana jego ma sai kaje, yau kwana biyu da suna har kin fara fita”


Kallonsa ta yi fuskarta da annuri.


“Am sorry dear, daga yau ba zan sake fita ba sai next week”


Wani tsakin haushi yayi


“Ai kaji fa fitan ya fara kenan, ai ba aure lawyer ba, zamanta a gida ma aiki ne”


Dariya tayi tana gyara sunan da take ba ƴarta, tare da kallon Adnan dake wata tafiya a wahalce.


“Kai me ya same ka?”


Bude baki yayi zai yi magana sai Uzair ya karɓe.


“Da...”


“Ina jin Basir ne yake damunsa, ko kuma ya zauna wani abu ne, ɗazu ma na duba gurin ya masa ja sosai, i will take him to hospital”


Yana gama faɗar hakan ya miƙe tsaye ya riƙa hannu Adnan da sauri suka fice, ita kuma bata wani ɗauke abun serious ba, ta maida hankalinta gurin Mai mata reno.


“Me aka girka?”


“Wake aka yi, shi yace na girka ta daya ga Namra na ta kuka”


“Ayyah Namra na, i'm sorry ba zan sake fita ba dake ba, i love you”


Ta aikawa babyn kiss tana murmushi. Sannan ta tashi ta nufi ɗakinta tana cire ɗankwalin kanta, ɗayan hannunta kuma na ɗauke da new babynta Namra.




ASIM POV.


Be farka ba, sai bakwai da rabi, yana yin sallah asuba ya sake komawa baci,ba shi ya tashi ba sai sha ɗaya na safe, wayarsa dake kusa da shi ya ɗauka ya lalubo number Mardiya dan yau a bachinsa na safe ita yayi mafarki, be wani daɗe sosai yana waya da ita ba, ya miƙe ya shiga wanka.
Sha biyu saura ya shirya ya fita, kai tsaye gidan Hajiya Sadiya ya zuwa, tun kamin ya taso ya tanadi ƙarya da zai mata akan Namra, sai ya tarar bata gidan, mai gadi ya labarta masa tun jiya da dare ta bar gidan wai taje birnin kebi.


Ko kaɗan Asim be jidaɗin hakan da Hajiya tayi masa ba, sai ya zuciyarsa ta soma nuna masa ko dai Hajiya ta yi fushi da shi ne, shiyasa har taje Kebi bata faɗa masa ba, duk da ta faɗa masa zata bashi hutu saboda baƙi zata yi ai bata ce masa zata bar garin ba. Har ya ciro wayarsa ya kirata sai kuma wata zuciyarta ta hanasa, a ganinsa yanzu ba zata sauraresa ba tun da tana cikin fushi ƙara ya bari har sai an kwana biyu sannan ya kira ta, idan bata dawo ba.


Ƴar ƙara wayarsa ta yi, yana duba ya ga alert daga diamond bank saƙon miliyan biyar ya shiga asusun ajiyarsa.


“Wow”


Ya faɗa yana karanta sunan wanda ya aiko masa da kuɗin.


“Yayi Kyau Alhajina”


Ya faɗa cike da tsananin farinciki, kaminɓya ɗora da saƙon daya biyo baya.


“Na aiƙo maka da kuɗi, kazo gobe sokoto ina son ganinka, kuma ka zama mai riƙe sirri”


“Zan zo gobe tun da safe inshallah”


Haka ya mayar masa da amsa, sannan ya rumgume wayar a ƙirjinsa yana dariya har ta fitar hankali. Komawa yayi motarsa ya shiga, yana cigaba da dariya har da jijjiga jiki.


Yana yi ma motar ki kiran Nably ya shigo wayarsa, cikin sauri ya ɗauka yana dariya.


“Hello my second wife”


“Au ba ma nice ta farko ba kenan?”


“Yes karki sa ma ranki zaki zauna ke kaɗai a gidan Asim”


“Ashe kai ba Saurayi ba ne?”


“Saurayi ne kuwa sabo hul, amman bayan ke wata zan ƙara, ko kuma ma akai ku ku biyu a tare”


“Kai da bakinka kake faɗin haka, lallai na yi fushi, na bar mata”


Da sauri ya haɗe hannayensa kamar tana gabansa.


“Sorry my nurul khalbi, wasa nake miki just to get your angry, yanzu dai ya hanya?”


“Au kasan da tafiya na, amman baka kira ka tambaye ni ba”


“i'm sorry dear i'm just kind of busy, In fatar kin sauka Lafiya”


“Na sauka ƙalau idona sai ƙaiƙayin ganinka suke yi ”


“Gani na kan hanya nan da mintuna talati”


“I can't wai to see you”


“The same here”


Yana aje wayar ya ƙara ma motarsa jiya ya nufi wani boutique, dan siyen kaya mai kyau da tsana wanda zai sa yaje gurin gimbiya Nabila.




ABDOOL POV.

Ƙarfe goma sha ɗaya da rabi jirginsa ya sauka Katsina, yana sauka ya kira Ummi ya faɗa mata ya sauka, amman ta ƙi ɗaukar wayarsa, har sai da ya aika mata da saƙo, Sannan ta aiko masa da direba.
Daga filin jirgi zuwa gida tafiyar minti goma sha biyar ce, amman sai yaga ta yi masa tsayi kamar na awa ɗaya saboda zumuɗin da yake na bawa Ummi labarin dake cikin ransa.
Suna shiga harabar gidan farincikin fuskarsa ya ɗaɗa ƙaruwa, ko fakin ɗin kirki direban be yi Abdool ya buɗe ya fito, sai duk sojojin da suke gidan suka maƙe guri ɗaya suna sara masa, hannu kawai ya ɗaga musu ya nufi Babbar ƙofar gidan.




Amira da Haleema na tsaye dinning suna jera abinci Abdool ya shigo da sallama.
Da gudu Amal taje ta rumgume shi.


“Dude i miss you”


“I miss you more”


Kaɗan kaɗan Amira take satar kallonsa tana murmushi, Haleema ma kallonta take tana murmushi dan tasan abunda yake zuciyarta. Fitowar Ummi ne ya ɗago da duka hankalinsu har Amira ta samu damar kallon Abdool da kyau tana auna irin missing ɗinsa da ta yi.


“Ka kuru da baka dawo yau ba ko”


Dariya yayi yana wasa da hannun Amal.


“Ummi ina da labari mai daɗi da zan ba ki, duk da kin

Please Login or Register in order to submit comment