Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruwa a kwano daga ta dire gaban Neina daga bisani ta miƙa mata ganyayyakin. A cikin ruwan Neina ta mirza su, ta miƙawa Namra, daker ta ɗan kurɓa kaɗan, sannan Neina ta shafa mata lafiya dubu a goshi, sai ta maida kwanon ta aje gefe da taimakon Uwani suka riƙa ta ta miƙe tsaye.


“Tashi muje banɗaki”


Tana fara takawa jiri ya ɗibeta sai ta rafke a gurin ta faɗi ƙasa. Hakan yasa Neina ta tura ƙofar ɗakin, ta rufe gudun kar wani ya shigo.


Gaba ɗaya idonsa da hankalinsa ya tattara ya koma kan ƙofar ɗakin, baya buƙatar a faɗa masa komai tun shi ba ƙaramin yaro ba ne, tun daga yanayin ihun Namra da ya ji da kuma gayyen da ga Uwani ta samo, yasan abunda yake faruwa. Wani irin tausayinta Namra ne ya lulluɓe masa zuciya, gaba ɗaya ya manta da nasa ciwon, he feel her pain, masu shigo suna masa sannu ma ba jinsu yake ba, sai dai ya amsa masu sama-sama, dan gaba ɗaya hankalinsa yana can, ga masu shigowa sai tambayar Neina suke daga shi har su Maryam babu wanda ya iya furta ga inda take, sai duk suka yi kamar bata cikin gidan. Hankalinsa ya fara tashi ganin an ɗauki lokaci, daga Neina har uwsni babu wanda ya sake leƙowa, ya san duk wani abu da Neina zata mata ba zai kai na asibiti ba.


“Maryam zaki iya zuwa bank ki ciro kuɗi?”


Ya faɗa yana kallon Maryam ɗin dake zaune kusa da shi. Kai ta girgiza masa alamar a'a.


“Okay je gidan su Mustafa ki ga idan yana nan ki ce masa ya je ya samo mota kuma ya ciro min wannan kuɗin sai a kaita asibiti”


Ya miƙa masa takardar kuɗin da Yarima ya bashi na one million. Zuwa tayi ta karɓa sannan ta sakata cikin hijabin dake jikinta ta nufi ƙofar fita. Bata ɗauki lokaci ba sai gata ta dawo sai faman sauri take.


“Baya gida”


“Aro min wayar uwani na aro wayarta na kira shi”


Miƙa masa takardar ta yi sannan ta nufi ɗakin tana buga ƙofar.
Daga can cikin ɗakin Neina ta tambayi waye, sai Maryam ta amsa da.


“Ya Lamido yace Uwani ta aro masa wayarta zai kira mustafa a kai Namra asibiti”


“Ai ba sai anje asibiti ba, Allah ya kawo mata sauƙi”


Buɗe ƙofar Neina ta yi, sai ga Namra tana takawa a hankali Uwani na riƙe da ita an ɗaura mata zane saman wani zane suka fito. Kallo ɗaya Lamido ya yi mata ya ɗauke kai be sake kallon inda take ba, har suka shige banɗaki.
Har cikin ransa yake aiyana irin zafin da Namra ta ji, a take wani irin tausayinta ya lulluɓe masa zuciya, idan kuma ya tuna irin rayuwar da ta fito ciki sai yaji kamar ya zubar mata da ƙwalla.


Uwani ce ta taimaka mata wajen gyara jikinta, sannan ta fito ta ɗauki kuɗi cikin jakar Namra ya aika Maryam ta siyo mata Pad, sai ta bi ta gidan maƙotansu ta karɓo mata bashin pant guda huɗu hannu Sadiya mai haja.
Neina ta gyara ɗakin sam kamar ba ayi komai ba, sannan taje ta ɗora mata ruwan wanka masu ɗan ɗumi ta kai mata banɗakin ki. A nan ne uwani ta bar mata banɗakin dan ta yi wanka.


Ta ɗan samu ƙarfin jikinta lokacin da ta yi wanka ta saka pad sannan ta ɗauki zanen da Uwani ta ɗora mata saman ƙofar banɗakin ta ɗaura ta saka hujabi, ta ɗan ɗauki lokaci zaune a banɗakin sannan ta unƙura ta fito. Da sauri uwani ta zo ta riƙa ta suka nufi ɗayan ɗakin da su Maryam suke kwana.
Saman katifar ta kwanta idonta tab da hawaye, tausayin kanta take ji irin ƙaddarar dake faɗa mata ɗaya bayan ɗaya, idan ta fita wannan sai kuma wannan. Bata da tabbacin cikin ya zube gaba ɗaya amman a yadda taga tsare tsaren jini bata zaton akwai abunda ya yi saura a cikinta. Bata bari Uwani taga hawayen da suka zubo mata ba, har sai da ta fita sannan tasa hannu ta shafa cikinta, tana tuna dalilin barin gidan Asim saboda cikin da yanzu babu shi, kuma bata da madafa, dan ba zai yiyu ta zo ta zauna musu a gida haka nan kawai ba, sai dai har yanzu tana tsoron komawa gurin Abbah, to tace masa me? Mutumen daya ce kar tayo fushi ma balle kuma saki ya shiga tsakaninta da Asim.


“Ba adili ba ne”


Ta furta a fili zuciyarta cike da ƙololon baƙinciki, tana tuna irin hallacin da tayi masa yayi mata wannan sakamakon.
Kai kawai take iya girgizawa tana tuna yadda ta rabu komai nata saboda shi, shi kuma a yau ya butulce mata. Dafata da Maryam tayi ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da take.


“Ki yi haƙuri Allah zai sake baki wani”


Kai ta ɗaga mata, tana mata kallon wacan Maryam ɗin ƙanwarta.


“Haka ne, babu abunda bata faɗa min ba, amman na ƙi na yarda na riƙa ƙaryata ta, yau gashi na ga komai daman duk wanda ya ƙi ji ba ya ƙi gani ba”


Da kuka ta ƙarasa maganar kamar wanda bata cikin hayyacinta. Maryam ta girgiza ta.


“Namra lafiya kike kuwa?”


Da sauri ta ɗaga mata kai tana ƙoƙarin share hawayanta.


“Lafiya ta ƙalau”


“Tau ga Maltina nan Ya yace ki sha da madara, mustafa zai karɓo kuɗi a kai ki asibiti”


Ta faɗa tana dire mata gwangwanin maltina guda biyu da madara.


“Ba sai an kai ni asibiti ba, na gode sosai Allah ya saka muku da alheri”


“Amin”


Maryam ɗin ta miƙe tsaye ta bar mata ɗakin. Dawowa tayi gurin da Neina take zaune da Uwani da Lamido, suke zaune ta zauna tana faɗin.


“Tace wai ba sai an kaita asibiti ba, ta gode Allah ya saka mana”


“A'a ba za'a barta haka ba kam, bari dai mustafa ya dawo”


“Ai taji sauƙi Lamido ko ba a kai ta ba, ko minene a cikinta be nina ba”


Neina ta faɗa, Lamido ya kaɗa kai.


“Ƙara dai aje asibiti nan ba zasu rasa abunda zasu mata ba”


“Kuɗin zaka ɗauka ka kashe kuma? Lamido kana ganin Napep ɗin nan taka ta lalace an baka ka siya wani ka samu na jari sai kuma ka ce zaka kashe”


“Haba ai kuɗin yayi yawan da ba zan iya kashesu duka a maganin baiwar Allah nan ba, kuma ko duka za a kashe mata wallahi zan iya badawa, kai ko Napep ɗin ce zan iya siyarwa dan nemaw yarinyar nan lafiya, wallahi mugun tausayi take ba ni”


Daga Uwani har Neina kallon juna suke da mamaki. Maryam ce ma tayi ƙoƙarin magana.


“Lallai Yaya kana tausayin yarinyar nan, Allah dai yasa labarin gaskiya ta ba mu dan kasan duniya yanzu yadda take”


“Amman ta miki kama da wacce zata baki labarin ƙarya? Haba Mairo ki duba yanayinta mana”


Har Neina zata yi magana sai ga Mustafa ya shigo, sai kawai ta sauya maganar da amsa masa sallamarsa. Kusa da abokinsa ya zauna yana bashi labarin yadda suka yi a bank.


“Wallahi akwai layi sosai, kuma naga rashin lafiya ne shiyasa sai nace bari na dawo sai ayi amfani da abunda yake aljihuna in yado idan aka ciro kuɗin sai na ɗauka, kuma kasan manyan kuɗi ne ba zan iya zuwa ni kaɗai ba, kar abiyo ni”


Duk da Lamido baya jin dariya hakan be hana shi darawa ba.


“Wallahi kai dai Mustafa kamar baka yi boko ba, ko da yake karatun naka iya diploma ya tsaya, amman miliyan ɗaya indai ƴan dubu dubu ne ai ba wasu kuɗi ba ne”


Neina ta girgiza kai.


“A a nan Alhaji Isa ba dubu ɗari ya zo dasu gida akan haka aka kashe shi balle mai miliyan ɗaya, ni tun ranar da Allah ya yi ni ban taɓa ganin dubu ɗari biyar a idona ba, balle kuma miliyan ɗaya”


Mustafa ya amsa.


“Wallahi fa ai zamani ne ya riga da ya lalace shiyasa komai sai an yi kafa kafa da shi”


“Allah dai ya shirya mana, ko bana ma son ana faɗar an fashi kuɗi har haka da yawa”


Cewar Neina tana miƙewa tsaye. Uwani ta ce


“Ai babu wanda ya sani idan ba mustafa ba, tun da ba mu faɗawa kowa ba”


“Allah dai ya tsare mu”


Duk suka amsa da Amin har Maryam dake ƙoƙarin tashi ita da Uwani su basu guri.
Bayan sun wuce Mustafa ya kalli Lamido.


“Wallahi babu wanda ya faɗa min haɗarin nan da ka yi in ba dan daka kira ni ba”


“Toh ai ba wani abun daɗi ba ne balle a riƙa yayatawa, kuma ba a daɗe da yin abun ba, Allah ma dai ya tsare”


“Allah ya ƙara tsarewa, amman dai wannan ɗan sarki ko sarki zan ce Allah be yi shi da rowa ba har miliyan ɗaya! Kamar wanda be san zafin kuɗi ba”


“Ya za'ayi ya san zafin kuɗi? Iyayensu suna kawashe kuɗin ƙasa, yanzu dai idan ka fita ka biya ka biya bilya kuɗin maltina da madara na aika am karɓo mata”


“Okay maganar asibitin fa?”


“Tace ba sai an jibe kuma naga kamar Neina bata son aje, ƙara mu ɗan saurara tukuna”


“Okay yayi Allah bata lafiya, amman ƴar'uwar ku ce ko? Naga kamar baƙuwar fuska ce”


Shiru ya ɗan yi yana tunanin faɗawa abokinsa nasa, sai dai baya jin zai iya ɓoyewa mustafa komai, kamar yadda mustafan baya ɓoye masa, kuma yasan idan ma be faɗa masa yanzu ba zai faɗa masa gaba, ko kuma ƴan gulma su tsegunta masa.


Hakan yasa be ɓoye masa komai daga haɗuwarsa da Namra da kuma labarin da Namra ta ba su nata.
Shi kansa Mustafa ya girgiza kuma ya tausayawa Namra matuƙa. Babu ma abunda yafi taɓa shi kamar rabuwa da tayi da iyayinta.


“Ai kaji matsalar mata suna da ƙaramar ƙwaƙwalwa, dan me zaka rabu da uwayen ka kan saurayi?”


Lamido ya numfasa.


“Ai mutum baya iya tsallake ƙaddararsa, sannan mu kan mu maza muna da matsala, da yawa sai ki ga dan kuɗin gidansu yarinya ake son ta, ni ina mamakin irin mazan nan wallahi, haka kawai abun wani ya tsune maka ido, ni dai Allah be sa min irin wannan rayuwar ba wallahi”


“Ai irin ka irin ka kaɗan ne Lamido, ni ma nan idan na ga arziki ba zan ƙi bi ba, masu arzikin nan suke kawai suke watayawa, ka duba kaga tun yaushe ka gama digiri ka yo bautar ƙasa, amman aiki ya gagareka, yanzu da kai ɗan wani mai kuɗi ne, da yanzu kana can Abuja kana hanawa kana aiki a wani babban kamfani”


Ajiyar zuciyar Lamido ya sauke.


“Muma Allah be manta da mu ba, kuma kaga wannan sana'ar Napep ɗin da nake? Ni ta wadarta da ni kamin Allah ya buɗo min wata hanyar kuma”


“Allah ya tabbatar mana da alheri, amman babu wanda ya ƙi kuɗi”


“Ita yanzu kallo ɗaya zata yi ma duka mazan takalawa alhalin ba haka muke ba, dan bamu taru muka zama ɗaya ba”


“Uhm, rayuwar ce sai a hankali, Allah ya bata wani na gari, ya shirya tsakaninta da iyayenta”


“Amin Amin”




*ABDOOL POV*


```Yana tsaye jikin wani upstairs, ya hango ta tana wani irin gudu kamar zata faɗi, kare na biye da ita a baya yana mata haushi, da alama karen take ma gudun, bata ankara da ƙaton ramen dake gabanta sai kawai ta faɗa cikin kamar an jefata. Daga can cikin ramen ta ɗagowa Abdool hannu tana son ya taimake ta sai kuma take, shi kuma ya yi tsaye yana kallonta kamar zai je, kamar ba zai je ba.```


Firgigit ya farka daga ɗan kajeren bachin daya kwashe shi yanzu-yanzu.
Haƙi yake sosai yana maida numfashi, jin yake kamar a zahiri ne abun ya faru. kyakkyawan askin kansa ya shafa, ya lumshe ido ya buɗe yana kallon agogon ɗakin.


“Mtsssss mi zai sa ba zan yi mafarkinta ba? Bayan na kwanta da ita a raina? Why this? Miyasa na zurfafa akan yarinyar nan ne? I'm totally mad”


Ya unƙura ya tashi ya nufi bathroom, zuciyarsa na raya masa ba zai yi mafarkinta haka nan kawai ba, shi kumasai yaƙar zuciyar tasa yake yana ƙaryata ta, dan ganin yake idan har ya yarda da ita to zata kai shi ga hallaka ne kawai.
Sai faman faɗa yake ma kansa kamar wani taɓaɓɓe. Har yayi wanka ya fito mafarkin be daina tsaya masa a rai ba. Haka ya shirya cikin tufafi na alfarma, wata musulmar shadda ya saka har wani maiƙo take tana shining daya ya motsa sai shadda ta amsa amo, shaddar ta karɓesa sosai, ta zauna a jikinsa kasancewarta sky blue, shi kansa da ya kalli kansa a madubi sai da yayi murmushi.


Wayarsa ya ɗauka ya ɗauki kansa hoto, sannan ya baro gaban madubin baya ya feshe jikinsa da turare mai mugun tsada da ƙamshi.
Already ya saka agogo hannunsa da zabban azurfa.

Yana doso sitting room mafarkinsa ya faɗo masa a rai. Wani irin faɗuwa gabansa ya yi har sai da ya rumtse ido ya murƙushe bakinsa.


“Wai miyasa yarinyar ta tsaya min arai ne? Ko dai akwai wani abun ne? Yeah na ga kare yana binta, ta faɗa rame? Me wannan yake nufi ne?”


“Allah ya taimaki Yarima, ba mu da masaniya akan abunda kake magana a kai, Allah yaja kwanan ka”


Kallon mamaki yayi musu yana juyar da kai, dan shi be san ya iso sitting room ba ma sai yanzu, ashe a fili yake maganar.
Iskar bakinsa ya furzar ya kalli tsadadden agogon hannunsa. Ƙarfe biyu saura minti goma ya gani, ya san ɗaurin auren ƙarfe biyu ne.


“Allah ya taimaki Yarima, tuni Mai martaba, ya kira kana bachi har ya bada umarnin tashin ka”


Hannayensa ya zuba cikin aljihu.


“Yanzu dole sai an naɗa min rawani?”


“Allah ya taimaki Yarima, haka Mai Martaba ya ce, har alkibar da zaka saka mun zo da ita”
Haka ya zauna suka naɗa masa rawani akai, ya fito fes Sarki, ba ma ɗan Sarki ba.
Miƙewa yayi tsaye suka saka masa baƙar alkyabar mai ratsin zaiba, sannan suka fiddo takalmin alkyabar suka aje masa ƙasa. A ƙoƙarinsa na saka takalmin ya kalli Sadauki ya ce.


“Idan ka yi mafarki kare yana bin ka me hakan yake nufi?”


“Allah ya taimaki Yarima, Maƙiyi ne.”


Ya ɗan yi shiru na wasu mintuna, kamin ya sake furta.


“Idan kuma ka faɗa a rame fa? Sai kuma ka miƙo min hannu kana son kamo ni?”


“Wannan Makaru ne, Allah yaja kwanan ka, idan kuma ina miƙa masa hannu to ina neman taimakon ka ne”


Sai da Sadauki ya gama amsa masa duka tambayoyinsa sannan ya saka takarmin, zai soma tafiya Sadauki ya ciro wani turare zai fasa masa.


“Allah yaja kwanan ka Mai Martaba ya ce afesa maka wannan”


“Na saka turare bana da buƙata”


“Allah ya taimaki Yarima, wannan na gidan sarautar ne, na Masarautar Katsina ne, ƙamshinsa ne zai sanar da isowar ka, kuma wannan turaren na gidane da ake haɗawa tun gadon gadon”


Ba dan yana so ba, ya tsaya suka fesa masa turaren sannan suka shiga gaba, wasu kuma a baya, shi kuma sai wata tafiya yake kaɗan-kaɗan, mai cike da tsantsar kasaita, da nuna isa, bayan kuma shi hankalinsa yana can wani gurin dabam.


[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *66 NOT EDITED ⚠️*




AMIRA POV.


Ta san yau zai dawo, amma hakan be hana ta kiwarsa ba, duk sai taji gidan ya mata girma kamar ita kaɗai ce a ciki. Tana son aika masa da saƙon tana tuna gargaɗin da yayi mata akan ta daina.
Bata san hawaye sun zubo mata ba, har sai da ta ji ɗuminsu a kumatunta, ɗan murmushi ta yi ta kai hannu ta share hawayen tana magana da kanta.


“Idan na ce zan yaƙi zuciya akan ka, zan cuce kai na, ban cancanci komai ba sai kyakkyawan sakamako, zan iya barin komai a kan ka, zan jure haƙurin rasa komai akan ka amman ba zan iya raka ka ba, ni nafi dacewa da kai Abdool, ba zan jure ganin wata ta raɓe ka ba, ba a hallinta maka wata matar aure ba, face Amira.
Wallahi ina son ka Abdool fiye da irin son da uwa take yi ma ɗan ta, kai mafarki, kuma kai kaɗai ne cikar burina, idan har na rasa ka Abdool to sai dai ko wace mace ta rasa ka”


Cige bakinta ta yi tana karɓar kukan da ya zo mata gadan-gadan. Mulmulawa ta yi ta mulmulo saman gado tana jin abu marar daɗi yana ratsa zuciyarta. Hoton da Abdool ya yi da Amal tafi tsurawa ido, tana masa wani kallo kamar wacce bata san shi ba.


“Kin yi sa'ar ɗan'uwa ni kuma zan yi sa'ar miji, ina son ka da iyalan ka Abdool”


Bata ankaro da ɗauki lokaci tana kukan ba, har sai da ta ji abu na ƙoƙarin rufe mata ido, alamar idon ya kumbura kenan.
Muryar Ummi da ta ji ne yasa ta sauri sauka saman gadon ta shiga bathroom ta wanke fuskarta, ta fito ta nufo falo.
A tsaye ta samu Ummi tana rataye da jakarta, mayafinta a hannu, Amal ma na tsaye a bayanta sai kumburi take, ita ala dole ga auta.


Tun da Amira ta soma saukowa downstairs Ummi take kalle da yanayinta, ga kuma kumburin da idonta da ƴa yi, fuskarta har ya soma ja abun ka da farar mace.


“Ba ki da lafiya ne?”


“A'a... Eh... Kai na ne yake ɗan ciwo”


Ummi ma uwace, ta fahimci Amira tana cikin damuwa ne, ko da bata fito a fili ta faɗa mata ba. Hannu ta kai ta shafa kan Amira zuwa wuyanta.


“Ki yi haƙuri kin ji, komai mai wuce wa ne, kin ji? Rayuwa bata tabbata haka amman dai ki yi tunani kin ji? Mu zamu fita, Haleema da Meesha ma sun fita Fauza ce kawai take bachi”


“Okay to sai kun dawo, me za'a girka?”


“No no kije kawai ki kwanta Shukura za ta yi komai, kije kawai ki yi ma kan ki karatun ta natsu”


Daga haka Ummi ta fice Amal na binta a baya, tana waigo Amira da harara dan ita har yanzu haushinta take ji, wai ta maida mata ɗaki kamar nata, daman can Amal ba son mutane take ba.
Maganar Ummi ta tsaya a mata a rai, me take nufi da ta yi ma kanta karatun ta natsu? Me hakan yake nufi? Juyawa ta yi ta nufi upstairs zuciyarta da tunani kala-kala.


RASHIDA POV.

Tana kewar ɗan ta sosai, wata ƙila dan kasancewarsa shi kaɗai ne ɗa namiji a gareta, ko kuma dan ita silar mutuwarsa.


“Na rasa abubuwa da dama, na rasa mijina, ɗa na, na rasa lafiya ta, yanzu kuma ina ƙoƙarin rasa iyayena, ni ka ɗai ce mai Aure da nake aikata zina? Ba suna nan da yawa ba? Miyasa ni bana da sa'a?”


Miƙewa ta yi tsaye daga saman prayer mat da take ta cire hijabinta ta nufi window.


“Idan har na bar gidan nan kowa zai tambayi dalili, kuma dole wasu za su gane abunda yake faruwa, idan kuma na zauna zan fuskancin tsagwama da takurawa, miye mafita?”


Hannu ta kai ta riƙa window, wannan karon sai ta koma zancen zuci.


‘Hakan yana nufin na rasa aure kenan har a bada? Idan kuwa gaka ne, to ba ni kaɗai zan shiga matsala ba, har Asmee tana ciki, kamar yadda nima ta jefa ni, kuma mijinta ma yana ciki, dan asirina ba zai tonu su na su ya rufu ba, bayan su ne silar komai, idan har na rasa Hilal ba zan rasa Alh Bashir ba’


Juyowa tayi ta jingina da window, yana motsa bakinta.


‘Idan kuma har na tona musu asiri na tonawa kai na, na matso da mutuwa ta kusa bayan kuma tana nesa da ni.
Amman kuma ba zai yarda ya tonawa kansa asiri ba, dan ba zai yarda ya rasa martabarsa da aikinsa ba, ni kuma ba zan rasa mijin aure ba, kuma hakan ba ƙaramin ƙona zuciyar Hilal da Asmee zai yi ba, su ma ya kamata su ɗanɗana yadda zafin baƙin ciki yake. I will never gave up, i will fight for my happiness, i deserve happiness again’


‘Idan kuma har Hilal ya rasa ni, be cancanci sake farin ciki ba, ya kamata ya ɗanɗana zafin rabuwa da ni, yasan akwai banbanci tsakanina da ita, Idan har ban more Hilal ba the love of my life be kamata wata ta more shi ba’


Komawa ta yi saman gado ta zauna ta ɗauki wayarta ta soma kiran Teema.




HILAL POV.


A gidan Hajiyarsa ya zauna har dare, sai da kowa ya watse sannan ya shiga sallama da Hajiya zai mata sai da safe.
Wani kallo uku saura kwata ta yi masa iron kallon Namijin da be san ciwon kansa ba, ƙasan carpet ya zauna kansa a ƙasa yana mai nuna mata tsantsar ladabinsa.


“Ban yarda ku kwana daki ɗaya da matar nan ba, kai dai ba jahili ba ne tun da kasan babu aure a tsakanin ku a yanzu”


Ba tare da ya ɗago kai ba ya ce


“Amman musulumci ya yarda da zaman idda, Hajiya zan bi duk wani umarni na ki, amman dan Allah karki gina katanga tsakanina da matana wallahi ina son ta”


“Kai wawaye Hilal, baka iya son mata ba, kana zurfafawa har ya zama baka iya ganin laifinta, ba zan gina katanga tsakanin ka da matar ka ba, dan ni ba irin surukar nan ba ne, amman zan nisanta ka da ita har sai ta gane kuskurenta ta yadda gaba ko ance ta aikata ba zata aikata ba, kuma ya zama dole ka ƙara aure!”


Ajiyar zuciya ya sauke still be ɗago ya kalleta ba, sai dai ransa be masa daɗi ba akan kalamanta.


“Zan yi duk yadda kika ce Hajiya, ke na fara sani kamin na san kowa a duniyar nan, ba zan zaɓi wata akan ki ba”


“Allah ya yi maka albarka, zan nema maka matar da zaka aura da kaina inshallah mai mutunci”


“Consider it done Hajiya, mu kwana lafiya”


Miƙewa ya yi tsaye idonsa sun rine sun yi ja sosai, irin ran maza ya ba ce sosai.






KALSOOM POV.


Tun da kowa ya watsa aka barta ita kaɗai sai duk ta ji babu daɗi ga kuma danuwar data saka ta gaba, tana ji a jikinta Hajiya ba zata barta ta zauna da Hilal ba. Haka ta zauna ta ci kukanta tun tafiyarsu har dare bata aikin komai sai kuka.


Tana jin tsayawar motar Hilal gabanta yayi dakan uku-uku. Ji take kamar ya zo mata da wani sabon abu, jin take kamar wata maganar zai faɗa mata wacce kunnuwanta ba zasu iya ɗauka ba.
Bata ƙarasa tsorata ba, har sai da ta ga ya ɗauki tsawon lokaci be shigo cikin gidan ba, hakan yasa ta unƙura cikin rashin kuzari ta miƙe tsaye, ta fito falo. Zaune ta same shi saman kujera ya haɗa kan sa da gwuiwa.


Ta ji babu daɗi sosai, sam bata jin damuwarta, ta sa damuwar take ji, bata san me Hajiya tace masa ba, amman a yanayin yadda taga mijinta ta karanci damuwarsa, duk abunda Hajiya zata ce mata ba zai wuce akan zamanta gidan ba, ko kuma wani abun daya shafe ta.
Juyawa ta yi zata koma ciki, sai kawai ta ji muryarsa ta daki dodon kunnenta.


“Ɗauko mayafin ki zamu je gida mu yi na su Momi bayani”


Bata juyo ba, ba kuma amsa masa ba, sai kawai ta cigaba da tafiyarta, hawayen na bin fuskarta.
Hijabinta yana kusa da gadonta, amman tsabar hankalinta baya jikinta haka ta bi tufafinta ɗaya bayan ɗaya bata ga Hijabin ba, sai kawai ta bude wardrobe ta ɗauko wani, Sannan ta ɗauki wayarta, ta handbang ɗin ta ta fito hawaye na cigaba da bin fuskarta.


Kamar mai koyan tafiya haka ta fito daga ɗakinta zuwa falo, shi kuma har lokacin yana nan zaune a yadda ta bar shi. Zuwa tayi ta tsaya bayansa tana hawaye.
Be yarda ya haɗa ido da ita ba, sai kawai ya miƙe tsaye ya nufi ƙofa ba tare da ya ce da ita komai ba.
Sai da ya yi ma motar key sannan ta fito daga falon ta shiga gidan baya, ja fisgi motar da ƙarfi, mai gadi na buɗe masa gate ya fara gudu kamar zai tashi sama. Shesshekar kukanta ne yasa ya rage gudun da yake ya faka gefen titi. Ya juyo ya kalleta.


“Try and cry so that i can tell you not to cry, Na fi ki shiga damuwa Kalsoom, ga damuwa na ga na ki ga na Hajiya ga na ƴaƴana ga na rashin yaro na duk ni kaɗai. Ba ki

Please Login or Register in order to submit comment