Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙwaƙwalwarta na juyawa.


“Amman gaskiya Anty Namra karki bar karatun ki, idan har ba zai iya bari ki ƙare makarantar ba kawai ya haƙura da auren ki, ai ba akanki aka fara cin amanar ba, kuma wallahi duk mai maka son gaskiya dole ne yaso cigaban ka, amman gani nake kamar cin amanarki kawai zai yi”


Maganar Hindatu ce ta ɗago da hankalin Namra har tasa ta kalleta, sai dai bata iya tace musu komai ba ban da ruwan hawaye daya fito daga idonta.
Maryam ta tsire baki


“Ke dai kika sani, tun da baki da ra'ayin kan ki sai na Miji, kuma wallahi kina daf da yin nadama dan duk mace da bata da ra'ayin kanta wahala tana tare da ita, ina tunanin wani abu ne ya ƙire kuma sauran kaɗan ya faɗa miki, ko kuma a ɗaga auren har sai kin ƙarasa karatun ki”


Hannu Namra tasa ta share hawayenta ta tashi jiki ba ƙwari ta nufi ɗakinta tana wata tafiya kamar marar lakka.
Sai a lokacin Anty Amarya ta kalli Maryam tace


“Kar na sake jin kun mata wata magana akan auren nan, kuyi mata fatar alheri kawai, wannan maganganun ba zai haifar mata da komai ba sai baƙinciki, idan kuna mata wannan maganar damuwa zata mata yawa.


Gani nake yi abun kamar zai taɓa ƙwaƙwalwarta, dan Allah karku sake mata magana nan, ita kan ta a yanzu bata iya banbance fari da baƙi, bata daɗe da fita lamarin Uzair yanzu kuma ta faɗo wannan, ko wane ɗan'adam baya wuce ƙaddararsa, no matter how you try baka iya tsallake ƙaddararka,
Kuma ba musan alherin da yake cikin wannan auren ba”


Maryam ta tsire baki.


“Wallahi babu wani alheri a ciki, daga gani ma amanarta zai ci shiyasa yake son yaje can nesa da ita, kuma ya hanata karatun ta tun da shi be san muhimmancin karatun ba”


“Babu alheri a ciki kin san gaibu ne? Idan ma amanarta zai ci ai ita ba yarinya ba ce, idan bata iya karatun duniya ba ai sai duniyar ta karantar da ita, ai kowa ya ƙona rumbunsa, ya san inda toka ke kuɗi”


Daga haka Anty Amarya ta tashi ta nufi ɗakin Namra, zaune ta tararda ita tana aikin kuka. Kusa da ita Anty Amarya ta zauna ta jata jikinta tana rarrashinta.


“Ki riƙa sauraren zuciyarki Namra, Allah yasa wannan auren ya zame miki alheri, kada Allah ya bar ki da kanki Allah ya dafa miki lamarin ki”


Rumgume Anty Amarya Namra tayi sosai tana wani irin kuka mai taɓa zuciya. Anty Amarya bata san lokacin da nata hawayen suka zubo ba.


*** *** ***


Ranar Assabar suka kawo lefen, tarba ta musamman akayi musu, tun daga kan drinks har zuwa abubuwan ciye-ciye, Hajiya Barau ta soya musu kaji da wasu abubuwan. Sai dai wannan karon ba'a tara mutane kamar wacan ba, iya su ƴan gida ne kawai suka tarbi lefen.


Su basu ga wani abun a'zo a gani ba, a lefen tun da abun masu hannu da shuni idan ba an saka tufafin dubu ɗari, ɗari biyu ba su ba ƙimarsa suke gani ba. Sai dai Anty Amarya bata bari sun yi magana a gaban idonta ba, sai dai idan bata nan, a fuska kuma sai tasa suka nuna mata ai yayi ƙoƙari. Ita kanta tasan yaba mata ne kawai suke dan su ƙarfafa mata gwuiwa, amman ba dan sun ga darajar kayan ba.


Tun daga ranar da aka kawo mata lefen Namra tayi sallama da abinci, duk yadda aka tursasata sai tacw bata iya ci, sam bata ma jin sha'awar abincin balle ta ci. Iyakarta abu mai ruwa, ko kuma tea, gashi ta yi baƙi sosai kamar ba farar mace ba, ta rame kamar marar lafiya.
Ita kaɗai tasan abunda yake cin ta a zuciya, tana jin son Asim, wani ɓangaren kuma tana jin kamar ta fasa auren amman babu dama, ta kasa samawa kanta mafita. Haka take wuni a ɗaki kamar wata marainiya, duk wata hidima da ake na zuwa siyen kayan aurenta ba da ita ake yinsa ba.


Da dare Maryam ta samu Namra ɗakinta tana nuna mata pictures ɗin gadaje wato furniture ɗin da za a zuba mata.


“Kin ga wannan miliyan ɗaya da rabi, wannan kuma miliyan ɗaya da ɗari bakwai Abbah yace ki zaɓi wanda kike so”


Kasa zaɓa tayi, ita sam zuciyarta bata mata daɗi.


“Kawai ki zaɓa min wanda duk kika ga yayi miki”


“Amman Anty zaki yi event ko?”


“ Babu abunda zan yi Maryam wanda ya wuce walima”


Kallonta Maryam tayi kamar tace wani abu sai kuma wani tunanin ya zo mata, sai kawai tayi shiru ta shiga nuna mata kujeru.
Sai da suka kai ƙarshe sannan Namra ta riƙa hannunta cikin rashin kuzari tace


“Maryam dan Allah kar ku yi fushi da ni dan na aure Asim, ku yi miki kyakkyawar fahimta dan Allah”


“Babu wanda yake fushi dake, kuma kin yi ma Asim halacci iya halacci Allah yasa kar ya zamo butulu, ya riƙe ki Amana”


“Amin na gode”


Daga haka Maryam ta tashi ta bar mata ɗakin. Ita kuma ta gincira tana sauke ajiyar zuciya.






KALSOOM POV.


Yanzu kam ƙofar farinciki ta buɗe mata dai-dai gwargwado bata da wata matsala a gidan mijinta.
Tun da safe zata tashi ta haɗa yara breakfast, tayi musu shirin makaranta, sannan ta tashi Doc. Sai dai yanzu kusan wata ɗaya kenan, Rashida babu ruwanta da Kalsoom duk kuwa da kasancewar yaranta ne take yima hidima, da ranar girkinta da ba girkin ta ba duk Kalsoom ce take girki, sai dai da dare ne zaka banbance ba ita ke da girki ba, kasancewar kwana biyu-biyu yake musu.
Doc. Hilal kam ji yake kamar ya ɗauki Kalsoom ya haɗeye, saboda yadda take masa komai daki-daki a gidansa, yana jindaɗin yadda take tashi tun da asuba tayi aiki, daman maza basa son raguwar mace. Gashi tana nunawa yaransa so hakan ba ƙaramin daɗi yake masa ba. Sai dai a ɗayan ɓangaren yadda Rashida taƙi ta sake Kalsoom abun na sosa masa rai, dan duk wahalar da zatayi da yaran Rashida ba zata iya ce nata sannu ba, balle na gode, ko kuma ta nuna mata jindaɗinta a kansu.


Yau ma kamar kullum bayan ta gama sallamar yara, sun karya sai ta raka shi bathroom suka yi wanka tare.
Ita ta shafa mishi mai ta murza masa turare, jaka yazo ya zauna ta saka mishi tufafi ko kunya. Har ta ɗora masa hula akai bakinta yake kallon.


“Perfect everything clear”


Ta faɗa tana ƙara gyara masa girarsa. Bakinsa ya miƙa mata.


“Na siye wannan lips ɗin”


“Yau ba za'a sai da maka ba”


Lumshe mata ido yayi, ya langaɓar da kai


“Haba Ma'am... Pity me”


Sai taja kumatunsa.


“No Toy”


Miƙewa tayi tsaye. Ganin da gaske ba zata masa kiss ɗin ba yasa yayi hanzarin fisgota ya jefar saman gado.


“Idan ban samu kiss ba toh zan nemi abunda ya fi kiss ɗin”


Hannu ta ɗaga masa


“Tsaya Wallahi zan baka, amman kiss kawai”


“Naji kiss kawai aya tashi”


Ya faɗa yana nuna mata bakinshi. Kamin ta miƙe tsaye ya buɗe durowa ya ɗauki sweet candy yasa bakinsa. Riƙe ta yayi gam kamar wanda zata tsire masa sai da ta tsosar masa bakin da kyau da kyau sannan ya sake ta bayan ya mayar mata da sweet ɗin cikin bakinta.
Sai ya zaunar da ita.


“It my turn”


Mai ya ɗauka ya fara shafa mata, sannan ya shafa mata hoda, sai janbaki. Sannan ya ɗauki underwears ya saka mata, ya ɗora mata da gown, haka ya mundula mata ɗankwali saman kai sai dariya yake.
Bayan sun gama, ta rako shi har gurin mota, sai da yayi mata side hug sannan ya shiga motar tana masa addu'ah.


“Allah ya haɗa ka da halak komai ƙanƙantar ta, ya nisanta ka da haram komai yawanta”


“Amin I Love You Dude”


“I love you more”


Bayan ya wuce ta dawo falon ta ƙarasa gyarasa. Guraren goma da rabi Rafiq ya tashi, sai tayi masa wanka ta bashi abincin sannan ta ɗauko shi suka dawo falon suka zauna.
Ƙonƙosa ƙofar data ji anyi ne ya ɗago da ita ɗaga kallon MBC2 da take.


“Waye?”


Daga inda take zaune ta tambaya.


“Nice Amarya”


Jin muryar Asmee yasa ta tashi ta buɗe mata ƙofar fuskarta a sake.


“Amarya gida sai ƙamshi yake”


Ta faɗa bayan ta zauna. Kalsoom tayi dariya


“Daman gidan mace a gidan ƙamshi ne, ya aikin ya kwana biyu?”


“Lafiya ƙalau, kina nan kina fama da rainon yara ko?”


Murmushi Kalsoom tayi.


“Asmee ke nan, ai yara na kowa ne, kuma ƴaƴan Hilal ai ƴaƴana”


Asmee ta wani gyara zama tana tsire baki.


“Ke ni dan Allah raba ni da abun haushi, ke kika zama ni nake miki kishi”


“Asmee kenan nikan na so naga kishiyarki”


Kalsoom ta faɗa tana dariya. Da sauri Asmee ta matsa


“A'a Wallahi mugun abin ki ya biki, ke daman Allah be raba bakin ki da tsaɓo ba, bari ma na bar miki gidan daman wani haki ne na siya nace bari na sam miki”


Ta faɗa tana fiddo wani baƙin abu a ƴar ƙaramar roba.


“Kin ganshi ɗan matse ne mai kyau Wallahi, sai kin ban labari, nasan ai kayan amarcin ki sun ƙare yanzu ai”


“Wallahi sun ƙare, duk na kyautar da su ni ba son irin abubuwan nan nake ba, nafi son masu zaƙi ko kuma ƴan fruits haka, kin san suma suna gyara jiki”


“Amman gaskiya kiyi amfani da wannan dan Wallahi yana da kyau sosai”


“To na gode zan gwada”


Bata daɗe ba ta tashi ta fita, har gurin gate Kalsoom ta rakata, sannan ta dawo gida.


Tun kamin Asmee ta isa gida ta buga Rashida tana labarta mata cewar saƙonta ya samu isa yadda ake so. Daga ɗayan ɓangare Rashida tayi murmushi tayi mata godiya sannan suka yi sallama.


Tana aje wayar ta tsire baki. Mutumen dake zaune saman wata huge chair ya kalle a ƙasaice yace


“Wacece?”


“Matar ka ce”


Yayi saurin ɗagowa


“Miya kai ta gidan ki? Bayan baki nan?”


“Ai abokiyar zama na nan, gurinta taje”


Ɗan murmushi yayi


“Mata Allah be raba ku da kicihiba”


Dariya tayi ta ɗauki documents ɗin da suke saman teburinsa, ta nufi ƙofa.


“Ki kai min waɗancan documents ɗin a guesthouse”


Ya faɗa yana kallon mazaunanta dake cikin suit.


“Gaskiya yau ba zan samu shiga ba da wuri zan koma gida”


Daf da zata fice ta amsa masa, sannan ta fice.






___________________________________________


Assalamu alaikum Habibaties💖. To all those that are asking about Amira and Uzair labarinsu zai zo nan gaba, so please wait patiently. And masu cewa kaza ya kamata ayi ba kaza ba, blah blah blah, yen yen yen, this and that, na gode duka amman please ku bar tafiyar nan ta tafi a yadda na tsara ta. Ba ku san dalilin da yasa Yasmeen ta fito a Barrister ba, ba ku san miyasa asiri ya koma kam Amira ba instead of Uzair, so please judge less.


Na gode Sosai Jazakallahu Khairan 🌺


I Love You All Fisabilliah 😘
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa20.html


*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng


NOT EDITED ⚠️


*PAGE - 20*




Ba'ayi wasu events ba, bayan salalle da wanki a Amarya, sai Walima da akayi ranar Jumma'ah. Bikin yayi mutane sosai musamman ta ɓangaren Anty, kasancewar Anty Amarya yanzu ne ta fara aurarwa. Har Ƴaƴan Hajiya Barau da suke nesa sai da suka zo.
Kaɗan daga cikin ƙawayen Namra ne suka samu halartar walimar, kasancewar bata yi gayyatar mutane ba, wasu ma ta hanyar Maryam suka ji.
A babban masallacin Jumma'ah akayi ɗauren aurenta, manyan mutane da dama sun tafi ta dalilin Abbah.


Yadda Asim.yake far'ah da nuna jindaɗinsa kamar ya zuba ruwa ƙasa ya sha. Takeaway na Manyan mutane Abbah yasa aka shirya masa ya rabawa abokansa. Asim kan shimkafa da miya yasa aka shirya masa a gidan wani abokinsa, sai ya tare da Abokansa a can bayana ɗaurin auren sukayi liyafar cin abinci.


Namra na zaune ɗakinta tare da wasu cousins ɗinta, Maryam ta shigo da guɗa.


“Ayyyyyyy Yau an ɗaura auren Namra da Asim”


Wani irin faɗuwa gaban Namra yayi, a maimakon tayi murna sai kawai idonta ya cika da ƙwallah. A take ta soma ganin kamar mafarki take. Farinciki da baƙinciki sai suka taru suka mata tsaye a guri ɗaya.


Yadda ƴan'uwan nata suka riƙa zolayarta yasa ta fito da kukan nata a fili, su kuma suka cigaba da zolayarta. Daker wata Gwaggonta ta lallaɓata ta tashi, tayi wanka lalle ta shirya cikin jar atamfa, mai makeup ta zo ta gyara mata fuskarta.
Sai suka fito da ita harabar gidan inda ake ta kiɗin ƙwarya.
Tsaye tayi a tsakiyar filin riƙe da hannun wata jikar Hajiya, ƴan'uwan Abbah da Hajiya Barau suka riƙa mata ruwan kuɗi suna cashewa, ƴan'uwan Anty Amarya ma sun watsa mata kuɗi sosai. Bata daɗe sosai ba a filin aka dawo da ita dan ta canja wasu kayan, saboda tafiyar da zasu yi, dan tuni motocin da za su ɗauki Amarya zuwa katsina suka iso.


Lokacin da Gwaggwaninta suka fara mata huɗuba akan zamatakewar aure da haƙuri, sai ta riƙa kuka kamar ranta zai fita. Tana faɗuwa tana tashi a aka riƙota aka shiga part ɗin Abbah da ita.


Duk fita suka yi suka barta daga ita sai Abbah, sai Maryam dake riƙe da gefenta itama tana hawayen rabuwa da ƴar'uwarta.


“Maryam tashi ki bamu guri”


Ya faɗa lokacin daya sauke idonsa kar kam Namra dake aikin kuka. Tashi Maryam tayi ta fita. Sai Abbah ya tattara duk kan natsuwarsa ya maida kan Namra.


“Haƙiƙa Khadija ke ƴata ce, kuma ina farinciki da Allah ya gwada min yau na aurar da ke, farinciki ko wane uba ne ya aurarda ƴarsa da ransa kuma ga wanda take so.
Khadija yau igiyar aure ta shiga tsakanin ki da wanda kike so, ina jan kunnenki akan haƙuri zaman aure, duk abunda yayi miki na daɗi ko akasin hakan kiyi haƙuri ki zauna da shi a haka, kar wani tsaɓani ya shiga tsakanin ki da mijinki ki kin tunawa cewa kina da uba! Na ɗaira miki aure da wanda kike so a yau, kuma na sallama masa ke har abada!


Karki kuskura wanke ƙafarki ki zo gidan nan da sunan yaji ko saki. Nayi miki iya abunda ya kamata uba yayi ma ƴarsa na abunda al'ada ta tanada, sai dai kiyi haƙuri ba zan miki gara ba, ba kuma zan ɗora masa kuɗi ba, ke dai yake so kuma ga ki nan na bashi, Allah yayi miki albarka ya baku zama lafiya”


Tun da Abbah yake maganar kan Namra na ƙasa tana wani irin kuka kamar ranta zai fita, duk yadda taso ta tausa muryarta tayi ma Abbah magana sai ta kasa saboda kuka.
Har Abbah ya gaji da sauraren kukanta, ya kira Maryam ta fita da ita. Ko da aka koma da ita part ɗin Anty Amarya numfashinta har rawa yake. Nan ma barinta akayi daga ita sai Anty Amarya. Amman Anty Amarya ta kasa mata magana saboda kukan da take na rabuwa da ƴarta.


Har lokacin da aka bata ya ci ya cinye, Anty Amarya bata iya cewa Namra komai ba, daga ita har Namra suke. Sai da su Mama Zainab da Hajiya Barau suka shigo zasu fita da Namra sannan Anty Amarya ta iya furta


“Na yafe miki Namra Allah yayi miki albarka”


Juyowa Namra tayi ta rumgume Anty Amarya iya ƙarfinta. Har Hajiya Barau da Mama Zainab sai da idonsu ya cika da ƙwallah. Daker suka ɓanɓareta daga jikin Anty Amarya saboda yadda ta rumgumeta.
Yadda Namra take kuka yasa duk wanda yake falon sai da yayi hawaye. Ƙanen Asim da wasu ƴan'uwansa suna tsaye gefe suna kallo.
Muta ɗaya suka shiga da Maryam da Mama Zainab da Hajiya Barau. Ɗayar motar kuma ƴan'uwan Asim suka shiga daman ciki suka zo. Biyun wasu ƴan'uwan Abbah suka shiga, sai ta su Maryam da Aisha da Hindatu da wasu Cousins ɗin su. Ƙarfe uku da ƴan mintuna suka kama hanyar Katsina.




KALSOOM POV.


Yanayin yadda Doc. Hilal ya shiga yau, ya bata tsoro, sai dai bata damu sosai ba, dan tasan haka rayuwa take yau daɗi gobe ba daɗi. Ballantana ma yau ba ɗakinta bane wata ƙila ma uwargidan tasa ce ta ɓata masa rai.


Sai dai hakan be sa tayi ƙasa a gwuiwa ba, wajen zuwa tayi masa kyakkyawar tarba. Sai ta aje Rafiq a falo ta tashi ta nufi ɗakinsa, tana faɗaɗa murmushinta.
Kwance ta kararda shi saman gado ya lumshe ido yana, hannunsa ɗaya dafe da kansa.


Kusa da shi ta zauna, ta kai hannunta ta shafi gefen fuskarsa.


“Ya Omri lafiya kake kuwa?”


Shiru be amsa ta kamar ba zai yi murmushi ba, can kuma ya buɗe ido ya kalleta, sam baya jindaɗin ransa, amman a haka yayi ƙarfin hali ya ƙirƙiro murmushi ya kai hannu ya shafa bayanta.


“Matar Doc. Yau jina nake sai a hankali Wallahi?”


Duk sai taji babu daɗi, daman tasan ba banza tun da taga ya shigo babu ko sallama, kuma be kulata ba ya shigo ɗakinsa.


“Wani abun ne yake maka ciwo?”


“No”


Ya sake lumshe ido.


“Kawai bana jindaɗin rai nane, shiyasa na baro office ɗin”


“Ko wani ne ya ɓata maka rai?”


Idonshi a lumshe ya girgiza mata kai.


“No haka kawai Wallahi”


“Toh Allah ya sauwaƙe ammn idan irin hakan ya same ka, ka riƙa karanta Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, zaka ji sassauci”


Tashi yayi zaune, ya sakar mata ido kamar yau ya fara ganinta, sai kuma yaja ta jikinsa ya rumgume gam-gam, yana maida numfashi.








________________________________________


Yan Katsina ga Amanar Namra nan mun kawo muku 😢


Anya Hilal lafiya yake kuwa?🤔


#Comment
#Share
#Blogger
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa21.html


*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng


NOT EDITED ⚠️


*PAGE - 21*


Ana kiran Sallah magariba suka isa Katsina. Kai tsaye suka wuce unguwar Nasarawa. Sun yi mamakin ganin gidan da aka sauke su da sunan gidan da Namra zata zauna.
Ba dan komai ba sai dan sanin Asim ɗin ba shida halin da zai iya kama hayar irin wannan gidan balle kuma har ya siye. Daman tun lokacin da aka zo jere an labartawa Hajiya Barau irin tsarin gidan. Gida ne plate mai kyau da shike-shike, ga farin fentin daya ƙawata gidan. A can ciki an ware dinning area da kitchen a gefe sai two bedrooms da babban falo, ga manyan kujerun da Abbah yasa aka zuba mata kamar ƴar wani shugaban ƙasa, duk bedrooms ɗin an saka mata furniture masu kyau da tsada.
A ƙaramin ɗaki ta tare ita da ƙannenta, su Hajiya kuma suka fito falo sukayi sallah, bayan sun gama direba ya kawo musu takeaway data aika a siyo musu, sai da suka ci abinci suka ƙoshi sannan Hajiya Barau ta shiga ɗakin da Namra take tana mata sallama, wai zata je gidan wata ƴar'uwarta ita da sauran waɗanda suka zo tare, su Maryam kuma sai idan Ango ya shigo sannan za su je.


Ko da Hajiya Barau ta bar gidan ana kiran sallah I'sha'i. Sai a lokacin Namra ta tashi ta shirya cikin wasu tufafin duk da kasancewar fuskarta a kumbure, ta koma babban ɗakin. Tara da rabi ango ya shigo tare da abokansa, ba a wani yi siyen baki ba, bayan addu'ah da fatan alheri da suka musu. Maryam dai sai ta watsawa abokan nasa wani mugun kallo take, tana Allah-Allah wani yace yana son ta cikin su tayi masa wankin babban bargo.


Tare suka fita da abokan angon, ɗayan yana ƙoƙarin magana da Hindatu dan itace mai ɗan dama a cikin su, sai wata cousin ɗin su Sameera. Lokacin da Namra taji ɗakin yayi tsit sai sabon kuka ya dawo mata, sai dai wannan karon hawaye ne kawai ba kamar na ɗazu ba.


Bayan ya rufe ƙofar gidan ya shigo ya rufe ƙofar falo, sannan ya nufi ɗakin da take da Sallama, bata iya amsa masa ba saboda kukan daya cika zuciyarta, sai shaƙar majina take tana haɗeye yawu da jimmar dannen kuka daya kasa ɓoyuwa.


Kusa da ita ya zauna, ya yaye mayafinta fuskarsa ɗauke da murmushi.


“Namra kukan me kike kuma? Bayan Allah ya cika mana burin mu”


Ɗagowa tayi ta kalle shi, kamar tace wani abu sai hawaye suka silala daga idonta zuwa kumatun ta.
Shi kansa baya buƙatar da faɗa masa dalilinta na kuka tun da yasan iyayenta basa son sa, gashi ya rabo ta da garin su. Shi kan ta ɓangarensa yau take sallah, tun da ya cika burinsa na aurenta ya fita kunya, ga uban dukiyar da aka zuba masa, ga kuma wanda yake jira a matsayin gara a kawo masa.


Jin kawai ta yi ya rumgume ta yana rarrashinta.


“Na san ban kyauta miki ba, dana nesanta ki da iyayenki, amman ni a nawa tunanin hakan shine zai fi mana, Namra a can abubuwa da dama zasu iya faruwa idan muna tare da iyayenki, amman a nan ba komai zasu ji ba, kuma a nan zamu tabbata ba zaman na ɗan wani lokaci ne kawai idan muka ga abunda Allah yayi sai mu koma can, kiyi haƙuri kinji?”


A yanayin da take bata iya magana, sai kawai ta ɗaga masa kai tana sauke ajiyar zuciya, tasa hannayenta ta rumgumeshi.
Har kusan shaɗaya dare suna zaune a gurin, daker ya lallaɓata ta tashi suka yi sallah nafila, kazar ma shi kaɗai ya ci ita kan lemu kawai ta sha ta hau gado ta kwanta. Washe gari guraren takwas na safe ya fita ya siyo musu kayan haɗa tea, ya shiga kitchen ya dafa ruwan zafi a electric, sannan ya dawo ɗakin ya haɗa ya zuba mata nata ya zuba nasa. Nan ma tea kawai ta sha bata ci birede ba, tsakanin jiya zuwa yau ta rame sosai kamar ba ita ba.


Shi kuma be yi matsa mata akan sai ta ci ba, tun da dai ita ba yarinya bace taya zai yi forced ɗinta akan cin abinci, shi duk ma ta cika sa dan yayi hating kuka for no reason, ita kanta ta san babu abunda ya tsana kamar kuka. Daman zuciyarsa ta faɗa masa, dan a rufa mata asiri ne aka yarda aka aura nasa ita, dan yasan babu dalilin da zai sa Abbah ya yarda ya aureta har ya baro garin da ita ya kuma hanata karatunta haka kawai ba tare da wani abu ba.


Sai dai hakan be dame shi, tun da ko ba komai ya taka first step of success, tun da ya auri ƴar masu hannu da shuni, kuma zama da kutuwar uwa dole, a dole dai Abbah ya kyautata masa tun da ya zama surikinsa.


Tashi yayi ya kwashe kofunan ya kai kitchen, sannan ya dawo kusa da ita ya zauna. Sai ya kai hannu ya shafa bayanta, dan tana daga kwance ne.


“Namra ko kina buƙatar wani abun ne? Naga baki ci komai ba”


Tashi tayi zaune hawaye cike a idonta, ta riƙa hannunsa tasa cikin nata, ta kalli ƙwayar idonsa tace


“Asim ka min alƙawarin ba zaka ci amana ta ba, ka min alƙawarin ba zaka taɓa rabuwa da ni ba, ka min alƙawarin ba zaka wulaƙanta ni ba, ka min alƙawarin zaka zauna da ni a duk halin da muka samu kan mu”


Gabansa ya faɗi sosai, a take ya ɗauke idonsa ɗ
Daga kallon da take nasa, yaja jikinsa ya rumgume.


“Taya kika wannan maganar kamar baki san waye Asim ba? Namra bakin ki ya daina furta irin waɗannan kalaman Asim ne naki har abada”


Sallamar su Hajiya Barau da Maryam ne, yasa shu saurin sakinta ya tashi ya fita yana amsa musu, a falo suka yi karo, sai ya kai har ƙasa yana gaida Hajiya Barau, ba laifi Maryam ma ta ɗan sakar masa fuska sun gaisa kamar daman can shiri suke.


Ko da suka shiga ɗakin Namra na gyara fuskarta da hoda, sai ta juyo ta kalli Maryam da murmushi a fuskarta.


“Hajiya Maryam an samu isowa”


“Toh ba dole ba, Hajiya ta sha kai muzo mu kawo miki abinci muyi sallama dake da wuri zamu koma”


Ta faɗa tana dire kular abinci a gaban Namra. Saman gado Namra ta dawo ta zauna tana ɗan ɓata fuska.


“Yanzu tafiya za kuyi ku bar ni?”


“Ahaf to ba aure kika zo yi ba”


Cewar

Please Login or Register in order to submit comment