Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jingina da kujera yana cigaba da kallon ɗansa. Abdool ya cigaba ba tare da ya ɗago ya kalli Mai Martaba ba.


“Idan har ka amince min, ina son ka roƙa mahaifin Namra akan ya rage lokacin da ya saka na aurenmu saboda yayi tsawo...”


Sai da aka ɗauki tsawon ɗakika talatin da huɗu wata kalma bata fito daga bakin Mai Martaba, sannan ya nunfasa kana ya ce


“Ni kaina na yi tunanin hakan, saboda maganganun da suke ta zuwa suna dawowa, ba a son magana ta yi yawa akan aure, kuma idan har aka ja abu nesa wannan kan iya haifarda da wata matsala wace ba a tsammanin zata zo, sai dai ganin lokacin auren yayi dai-dai da lokacin auren ƴan'uwaka yasa ban ce komai a kai ba”


Abdool ya jidaɗin wannan maganar, daman yana neman da inda zai fake yayi hujja da shi akan maganar auren. Sai gashi Mai Martaba ya taɓo masa inda yake masa ƙai-ƙaiyi.


“Nima hakan na gani, kada sheɗan ya shiga ciki, ko kuma baki yayi mana yawa”


“Gaskiya ne, amman kai zuwa yaushe kake ganin ya dace a saka auren?”


“Allah ya taimake ka ina son ace nan da wata ɗaya”


Mai Martaba yayi masa wani kallo.


“Nan da Wata ɗaya sai kace wanda zai auri ƴar tsana? Wata ɗaya yayi mana kaɗan da shirya lamarin auren ka”


“Allah ya taimake ka duk yadda ka yanke dai'dai ne, amman be yi kaɗan ba, indai matsalar lefe ne ciki sati ɗaya za a iya haɗawa, kuma na san bama buƙatar komai daga gareta”


Ɗan Murmushin gefen baki Mai Martaba yayi, lallai ya tabbatar da ɗansa ya matsu, hakan ma yasa shi gane Abdool yama neman girma a yanzu, bayan kuma a da neman masa ake yana gudu.


“Za mu yi tunani akai, kar ya zama mun matsa musu, zan yi shawara da Umminka, nan kuma cikin gida zamu shawara”


Mai Martaba na gama faɗar hakan ya miƙe tsaye...






__________________________________


I think we should create a team for LAMIDO ko 🤔 i pity him bawan Allah 😢
[7/24, 9:38 PM] Khadeeja Candy♥: *89*


Yau day ta leƙa whatsapp domin ta kwana biyu bata hau ba, daman bata hawa sai idan tana da time saboda karatun da ta sawa gaba.


“Abbah na kiran ki”


Aysha ta faɗa tana tsare jikin ƙofar ɗakin Namra.


“Okay ga ni zuwa”


Ta kashe data ta sauka saman gado. Ko da t fito Zinatu na zaune falo ita da Anty Amarya suna cin ɗatun zogale (kwaɗo). Wara ido tayi ta sha mur


“Lallai Anty shi ne cika zauna da ƴarki kika ci ɗatu ni aka ƙyale ni”


“To idan ban ci da ƴata ba da wa zan ci? Kaji min yarinya”


Anty Amarya ta faɗa fuskarta da annuri tana murmushi. Zinatu tasa dariya.


“Na gan ki online fa kuma na miki magana kika share ni”


“Allah ban duba ba, hankalina yana can ina duba chat ɗin grp”


“Gashi ai sai ki zo ki ci”


“Abbah ya kira ni, aje min na dawo”


Ya aje wayarta saman kujera ta nufi part ɗin Abbah. Zaune ta same shi sanye da jallabiya, idonsa sanye da farin gilashi hannunsa da jaridar daily trust. Ƙasa ta zauna bayan ya amsa mata sallamar da tayi idonta kan Arewa24 da suke maimaita shirin Daɗin kowa.


Remote Abbah ya ɗauka ya kashe tv, ya aje jaridar da ke hannunshi sannan ya fuskanci Namra ya ce.


“Magana na ke son mu yi a tsakanin ni da ke, kuma bana son ki takura kan ki, na fi son ki faɗi ra'ayinki”


Ta ɗan kalleshi kaɗan.


“Abbah maganar me ce?”


“Akan date ɗin da aka saka ne na aurenki, Mai Martaba ya kira ni yace a rage musu ranar da aka saka ta yi musu tsawo, amman yace baya son a cilasta miki yafi son sai anji ta bakinki”


“Abbah ban da wani zaɓi sai naka, abunda duk zai fito daga bakinka shi xai fito baki na, kai da Mai Martaba duka iyayene a gurina, duk yadda kuka yanke yayi, idan ma a yanzu kuke son a ɗaura auren babu matsala ni dai a guna, sai idan gurin Abdool”


Abbah ya jidaɗin maganarta sosai, daman haka yake son ta kasance gareshi mai biyar dukan umarninsa da yarda da abunda ya zaɓa mata, babu ruwanshi da duba zamani ya canja a ƙyale yara su yi ra'ayin kansu, yafi son duk yadda ya zaɓa maka kawai ka bi.


“Na jidaɗi da wannan kalami na ki Namra, kuma tun da har kin amince zan faɗawa Mai Martaba kuma na san shi ma zai jidaɗin wannan maganar, daman shi yana son a saka me nan da wata ɗaya”


Dam! Gaban Namra ya yanke ya faɗi sai ɗai bata nuna komai a fuskartaba.


“Babu matsala a gurina Abbah, amman ya maganar Lamido?”


Abbah ya sauke ajiyar zuciya.


“Yadda kike so Namra ba zai yiyu ba, ba zan ɗauki mutun haka kawai na bashi MD, mutanen duniya a yanzu ba abun yarda ba ne, abunda Uxair yayi min kawai ya isa ya lurar da ni duniya, zan iya bashi aiki dai a ƙarƙashina, kuma daman ina da niyar gyara musu gidansu kuma na ƙullawa mahaifiyarsu jari, ko da be yi komai ba zan iya masa haka balle kuma ya taimake ki sun riƙa ki tsakani da Allah, na san yana son ki Namra kuma kema kin san da haka, sai dai hakan ba zai sa na ɗauke shi haka kawai na bashi mb ba”


“Amman Abbah idan ya fara aikin nan ka aminta da shi zaka iya bashi md, wallahi mutumen kirki ne”


Abbah yayi murmushi.


“Har yanzu akwai ƙurciya cikinki, ai ba a gane mutum mai amana a fuska sai a aiki, sai dai na yarda da abu ɗaya, duk yadda duniya ta lalace za a samu na ƙwarai, zan jarrabashi na gani”


“Na gode Abbah”


“Allah ya miki albarka”


“Amin Thank you”


Haka ta tashi jiki babu gwari ta fice. Tun daga lokacin aka fara shirye-shirye, a dukan ɓangarorin guda biyu. Kullum sai Abdool ya kirata safe, rana da dare domin jin muryarta da kuma son sanin ko akwai abunda take shiryawa, sai dai duk lokacin da ya tambaye cewa take bata shirin komai.


Hakan yasa ya baro Abuja a daren ranar ya sauka sokoto, dan kwata-kwata ya rasa gane kan matarshi (His wife to be). Haƙuri yayi har sai da yayi sallah isha'i sannan ya doshi gidansu Namra. Wannan zuwan na musamman ne baya son kowa yasan da zuwanshi sai ita, a harabar gidan ya faka motarshi ya kira a waya yace mata yana gefen gate. Bata yarda ba har sai da ta saka Hijab ɗinta ta leƙo ta hango mota a gurin sannan ta yarda da gaske yake.
Ƙarasa ta yi kusa da motar ta buga ƙofar motar sai ya fito ya buɗe mata motar ta shiga sannan ya koma mazaunin direba ya zauna. Wasa take da ƴatsun hannunta ta kasa buɗe baki ta gaisheshi ma balle ta yi masa wata maganar, ta dai yi shiru tana shaƙar turarensa da ke kaiwa hancinta ziyara. Wani dogon numfashi yaja ya sauke kana ya kalleta ya ce.


“Na miki zuwan bazata, saboda na lura kamar baki cikin yanayin da ya kama ki kasance, idan har bakya ra'ayin aurena Namra, wallahi ba zan cilasta miki ba, duk yadda nake son ki zan iya bawa zuciyata haƙuri matuƙar ke hakan shine farincikinki, ba jindaɗina ba ne muyi aure kuma mu koma muna zaman da be kamata ba ni da ke, ba zan aureki dan wani abu ya shiga tsakanin mu har na sake ki ba, burina idan mun yi aure ni da ke mutuwace kawai zata raba, ba zan aureki dan wani abu na ki ba sai dan so da tausayi waɗanda abubuwa ne guda biyu da ba zasu taɓa saka ka ganin laifin mutum ba, shiyasa bana ganin laifin abunda kike min, sai dai ina kallon hakan da rashin so, ina ganin kamar na cilasta miki ne akan abunda baki da niya...”


Ɗagowa ta yi ta kalleshi idonta tab da hawaye, cikin rawar muryar ta fara magana.


“Tun bayan abunda Asim yayi min, ban taɓa tunanin zan so wani ɗa namiji ba, haka na saka a zuciyata kuma haka na ayyana. Amman daga lokacin da na saka ka a idona gidansu Lamido, sai wani irin kwarjini da ƙimarka suka kama ni, sai kuma gashi ka zama sanadiyar haɗa ni da iyayena, wannan ne yasa son ka ya ɗasu a zuciyata, ko da ban aureka ba, zan son ka Abdallah, irin son nan da ƴan matan hausawa suke yi ma mazan hausa novels da larabawa, kasan irin wannan son yafi ko wanne haɗari da saka rayuwa cikin ƙunci da nadama, da kuma ganin munin kowa, sai gashi Allah ya ƙaddara zan zama matarka, amman son da na ke maka doesn't give you the chance to hurt innocent people”




Sanyayiyar ajiyar zuciya ya sauke ya kalleta irin kallon nan mai cike da shauƙin so da ƙauna.


“Wana cutar?”


“Lamido, ya ƙi ya faɗa min abunda ka yi masa amman nasan abunda ka yi masa ba ƙarami ba ne”


“Dukan abunda na yi masa saboda ke ne Namra, saboda ina son ki ne, nasa an kawo min shi daga kaduna zuwa katsina ne saboda na masa magana a akan ki, nace zan biyashi ko nawa ne, ya ƙyale ki saboda bana son mu tarayya ni da shi a lokaci ɗaya mu raba miki hankali, saboda na lura yana son ki, kuma zuciyata tana nuna min zai bibiyeki, amman shi be ƙarbi tayin da na masa ba, har ma yayi min iƙirarin shi ne zai mallake zuciyarki, kuma yayi nasarar aurenki, amman duka be faɗa miki wannan ba sai a yanzu da yaga komai ya kankama kuma ya ɓoye miki saboda yana son shiga tsakanin mu, wannan yasa na roƙi Mai Martaba akan ya nemi a rage tsawon lokacin auren da aka saka, saboda magangu sun yi yawa akan zan auri bazawara, kuma gashi Lamido yana ƙoƙarin yi min zagon ƙasa, ina gudun kar shedan ya shiga ciki ya lalata lamarin aurenmu, saboda duk lokacin da aka shirya abun alheri za'ayi sai ka ga shedan na neman ɓata abun”


“Amman abunda ka masa baka kyauta ba”


Ta faɗa da muryarta mai kamar zata yi kuka. Shi kuma ya kwantar da kansa jikin kujera yana kallonta, dan har cikin jininshi maganarta ta shiga ta zauna, a take kasala ta sauƙo masa.


“Naji Gimbiyata ayi haƙuri a gafarta min”


Yanayin yadda yayi mata maganar yasa ta jin kunya har murmushi ya suɓuce mata bata shirya ba.


“I love you, i can't wait to see us on one bed...”


Ya faɗa muryarsa ƙasa sosai kamar mai raɗa. Buɗe motar ta yi zata fita sai yayi saurin riƙo hannunta, ta zaro ido tana faɗin.


“A'uzubillahi...”


Sai ya saki hannunta da sauri.


“I cross the limit... But sorry wai ba mu gama maganar ba”


“Mun gama mana”


“Dan Allah ki yi magana da kyau Abnam ki daina kashe min jiki”


Ƙyalƙyale ta yi da dariya, saboda har ga Allah ya bata dariya ita bata yi dan ta kashe masa jiki amman shi yana ƙoƙarin juyarda abun. Shima dariya ya samu kansa da yi saboda be taɓa ganin ta yi irin wannan dariyar a gabanshi, ta tafi da imaninshi sosai.


“You're so cute Abnam na fi kowa sa'ar mata”


Ƙoƙarin kawarda maganar ta yi.


“Na san maganar akan events ne, so bazawara zaka aura bana buƙara events bayan walima”


“Amman ni saurayi ne ai, ina buƙatar ayi mana wani ɗan event haka ko da biyu ne ko ɗaya”


“Ni dai idan ta ɓangarena ne bana so”


Ya ɗaga kafaɗunshi.


“As you wish your royal highness”


Dariya ta yi ta rufe masa motarta ta tafi. Shima murmushi yayi yana mai jindaɗi.


Namra ta kusan minti talatin tsaye a jikin windo tana kallon motar Abdool, sai ya kunna motarsa ya bar gidan sannan ta fito ta nufi sashen BQ.


Tun daga nesa ta hango Lamido zaune yana danna wayarsa. Ta ƙarasa kusa da shi tana masa sallama.


“Wa'alaikissalam, Hajiya”


“Na'am hutawa kake yi”


“Ina ɗan duba duniyar facebook ne”


“Hakan na da kyau, amman miyasa bakinka yayi nauyi har ka kasa faɗa min Abdool ya nemi ka siyar masa da soyayyata ne?”


Murmushi yayi ya cire hular taɓani ka ji hadisi da ke kansa ya ce


“Saboda soyayyarki tana da girma a gareni, amman ina fatar ya faɗa miki mahaifinshi ne dalilin talaucewar mu”


“Abunda ke tsakanin Mahaifinka da mahaifinshi be kamata ya shiga tsakanin ku ba, balle kuma ni har na shigo ciki, be nuna min ya san kamin lokacin ba kuma kai ma baka nuna min ka san shi, dan haka babu ruwana da abunda ke tsakaninku”


“Na gode Namra na gode sosai”


Yana kaiwa nan ya miƙe tsaye ya shige ɗakinshi. Ita kuma ta juyo ta dawo part ɗin Anty Amarya, a bakin ƙofa ta samu anty amarya a tsaye tana mata wani mugun kallon.


“Me kika je yi can?”


“Magana na yi da shi”


“Wace magana bata da suna ne? Ban miki maganar tun ranar akan ki daina keɓewa da shi ba?”


“Wallahi ba abunda kike tunani ba ne, yana ta ƙoƙarin shiga tsakani da Abdool ne ni kuma ban ga ne ba sai yanzu, shi ne na masa magana”


“ko ma minene karna sake ganin ki part ɗin nan, ai ba zarginki nake ba, kawai ina gudun shaedan ne, kuma tun da yana son ki zai iya aikata miki komai, ki yi taka tsantsan”


Ta gyaɗa kai.


“Ba zan sake ba daga yau”


“Good”


Anty ta bata hanya sannan itama ta shiga.
Ko da Namra ta shiga ɗakinta ta tararda missed calls na Abdool. Dan haka tana cire Hujabinta ta kirashi.


“Hi Babe-Abnam”


“Abdallah”


“Faɗa min wani abu mai daɗi...”


“Ni ko tambayar ka zan yi, miye tsakanin mahaifinka da Mahaifin Lamido”


“Me kuma ya sake ce miki?”


“Yace wai mahaifinka ne silar talaucinsu”


“Ya ɓoye miki ne kawai ko kuma be san gaskiyar zancen ba, a da mahaifinshi abokin Mai Martaba ne kamin a bashi sarauta, sai dai mahaifinshi yana safarar ƙwayoyi ne daga wata ƙasar ana sakawa cikin kayanshi da yake oder, sai yace musu zai kai kaya kaduna alhalin ƙoyoyine yake safara, babu irin jan kunne da mahaifina be masa ba amman yaƙi ji, ranar da ya shirya dainawa sai ya aika duka kuɗinsa waje ya siyo kayan fasa ƙwairi,wanda sanadin hakan customs suka kama kayan, kuma aka bincika aka gano yana safarar ƙwayoyi sanadin hakan aka maka shi, amman sai yake ganin kamar mahaifina ne ya saka shi a matsalar”


“Amman daman ka san Lamido baka taɓa faɗa min ba?”


“Ban san shi ba Wallahi shi ma kuma be san ni ba, sai a lokacin da nasa aka kawo min shi daga Katsina, a lokacin ina gida ne gurin Ummi, Ummi ce ta ganshi ta gane shi, shi ma kuma ya ganeta bayan ya tafi take bani labari, dan ni ban san anyi abun ba ma, lokacin da aka yi abun ina waje gurin karatu, so duk wasu abokai na Mai Martaba ni ban sansu ba domin ban dawo naija ba sai da na yi digiri na biyu”


Namra ta jinjina lamarin sosai, daga nan zance ya cigaba, har ya ɗauko mata labarin labarin zamansa a England.




*** *** ****


A GURGUJE...


Gyara na musmman Anty tasa ake mata irin wanda ake ma amare, tun daga kan dilka da kuma kayan mata.


Daga Dubai Abbah yayi mata odar furniture aka kawo su ta jirgin sama, saboda jirgin ruwa za a iya ɗaukar watanin basu iso ba, gashi kuma aure ya maso kusa, duk da Mai Martaba yace kar su kashe kuɗinsu hakan be hana Abbah siya mata kaya mai shegen tsada ba dan nemawa ƴarshi mutumci da ƙima a idon manyan mutane.


Ranar da aka kayo lefen Namra ana sauran sati ɗaya, bikin ranar kowa ya sha mamaki, sai dai duk wanɗa ya ji labarin ɗan sarkin Katsina zata aura sai su daina mamakin dan sun sa waye mahaifinsa balle kuma shi ɗan da kansa, an kashe neira a ɓangaren Abbah saboda tarbar lefe yayi duk abunda ya kamata wajen ganin ya kashe kunya.


Bayan kowa ya watse Hajiya Barau da Anty suka zo suna ƙara duba kayan, daga ɗan kunne har ribbon babu wanda aka siya a naija duk daga waje Ummi taje ta ɗawa ɗan lelenta lefe. Akwati ashirin da bakwai ɗan ƙaramin akwatin zinari ma daban ne, motar da aka kawo lefen da ita ba a koma da ita ba wai ita tana cikin lefen, ga kuɗin tsintuwa da ake sakawa a gefen akwati su daloli suka saka. Ko kaɗan wannan be yi ma Anty Amarya daɗi ba, domin ta tsani bidi'a a rayuwarta, dukan wani abun da za'ayi almubazzaranci da kuɗi Anty bata son shi.


“Ai ƙara ma da ba za ayi wani Event ba, da Allah kaɗai yasan iya bidi'ar da za'ayi, shi kesa aure yaƙi yin ƙarƙo, ni wannan abun ba burgeni yake ba”


Hajiya Barau ta yi murmushi tana danne abunda ke zuciyarta.


“Ai ke baki ga komai ba ma, mu da muka je jere mu muka ga abu, kin ga gidan da ya ƙera mata kuwa? Kamar ba Katsina ba, wallahi an kashe kuɗi sosai”


“Uhm Allah ya kyauta”


“Amin ai kinsan su masu abun idan ba sun fitar da kuɗin ba ne sun kashe basa jin sun yi, kuma tun da har Allah ya hore ai ƙara ayi, abunda kawai ba a so a zubar da kuɗin kamar kari haka”


“Ke dai Allah ya kyauta kawai, amman bidi'ah bidi'ah ce”


Haka suka yi ta firarsu suna duba kayan da tsayawa ƙirga ko kala nawa ne ɓata lokaci ne. A daren ranar Abbah ya kira Lamido ya bashi offer kuma ya sanar masa aikinsa ya ƙare a gidan da sunan driving. Ba laifi yayi farinciki duk da ɗayan ɓangaren yana baƙinciki an kasashi. Sai dai matsalar rashin aikin yi ita ta fi damunshi fiye da kowace irin matsala.




RANAR JUMMA'AH...


Da misalin ƙarfe biyu na rana aka ɗaura auren Abdallah Ahmad Mai-doki da Khadija Usman Zamau, a masallacin Muhammadu Maccido da ke Amir Yahaya. Duk wanda ya wuce a gurin sai ya tambaya ɗaurin auren wa ake saboda yadda aka taru sosai, ga manya mutane minister da sarakuna da ɓangaren Mai Martaba, da kuma gwannan Katsina, da na kano wasu kuma basu samu damar zuwa ba suka tura akillansu. Mr Presiden ma Wakiltarsa aka yi, saboda baya ƙasar.


Bayan an ɗaura aure aka yi ƙiyafar cin abinci a Shukura Hotel. a ranar Mai Martaba da muƙarrabansa suka koma Katsina, da dare Mai Martaba yayi nasa liyafar shi da manyan baƙinsa, a faɗarsa da aka sauyawa hallita kamar ba a naija kake ba.


Ta Ɓangaren Namra bayan an ɗaura aure da rana. Da dare suka yi walima, saboda an sauya salo yanzu walimar dare ake, an raba kayanyaki masu ɗubin yawa da burgewa. Sai dai ƴan ɓangaren ango basu halarta ba saboda Ummi ta ce zata yi nata walimar idan an kawo Amarya, saboda wasu haka suke sai idan an kai amarya sannan suke nasu walimar...








KALSOOM POV.




FIVE YEARS LATER...


“Happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday dear Izzah Happy birthday to you”


Tana yanka birthday Cake ɗin suka saka ihu.


“EyyyyyPpppppppp”


Sai kawai tasa dariya ta yanki wani abu daga cake ɗin ta sakawa Kalsoom a baki, Kalsoom ma ta yanka ta saka mata a baki, sannan ta bi sauran mutanen da suke gurin tana feeding the ɗinsu suma suna bata, bayan an yi musu hotuna Kalsoom ta basu guri ita da ƙawayenta su cashe...


Kalsoom ta shigo falo ɗauke da ƴarta Amatullah da ke ta kuccekuccen a barta can ta yi wasa.


“Ba zan barki can ba Amatullah su ture min ke na koma zaune”


Faɗuwa ta yi ƙasa ta fara shureshure da ƙafafunta tana kiran sunan Ezzah.


“Ijca ijca....”


“Easy girl, Ijca yau bata da time ɗin ki casu suke”


Haka ta cigaba da kuka, Kalsoom ta share ta a gurin, ta hau whatsapp tana saka hotonsu a status. Sai ga Rafiq ya shigo da gudu ya shiga kitchen ya ɗauko plate ya fito.


“Kai Plate ɗin nan na Dadyn ku ne, karka fasa min kaya”


“Cake za a sa mana ni da Amatullah”


“Kai mata wayo ka cinye ko..?”


Yasa dariya har da ƙyalƙyatawa, ya saba duk abunda za a saka masa sai yace shi da Amatullah za a saka musu saboda ya cinye ya barta. Sai ga Ezzah ta shigo idonta tab da hawaye kamar ta fasa kuka.


“Anty kin ga Husna wai sai an bata wannan cake ɗin ɗayan, gaba daya, kuma bamu gama hotuna ba”


Kalsoom ta aje wayar hannunta ta riƙe baki.


“Yanzu Husna ce zata riƙa saki kuka gaban abokanki? Ke baki jin kunya su ga idonki ya cika da hawaye? Shekara goma sha hudu ace ƴar shekara uku tana saki ƙwalla gaban friends ɗin ki? Wallahi Izza ki rage wannan shagwaɓar”


Ta turo baki tana matsar ƙwalla.


“Je ki kirata ki ce tazo ga wayata ta yi game”


Ta amsa da to ta fice ita da Rafiq. Tana fita Ulfah ta shigo.


“Anty Momie ta kira?”


“Eh tace ba zata samu damar zuwa ba, yanzu suka taso daga Abuja”


“To Anty ki ce Ezzah ta ba mu cake ɗin mu ai Dady yace saboda mu yasa aka yi cake da yawa”


“Ku ara mata ta yi hoto, ku bari a gama nama, ai ba gudu zai yi ya barku ba”


Ta buga ƙafa tana son kuka.


“A'a ni dai ta bamu abun mu, ko na kira Dady na faɗa masa”


“Duk kika faɗa masa sai na ɓata miki miyasa baki da nasiha ne ke? Kullum ke ce cikin rashin jituwa da ƴar'uwarki haba Ulfah”


“Ai itama bata raga min”


“To bari na ga kin ɓata mata party wallahi na ɓata miki rai”


Ta faɗa saman jikin Kalsoom tana kukan shagwaɓa.


“Yi ta kuka yarinya ki ɓata kwaliyarki”


Sai kawai ta zabura ta kaɓe rigarta ta koma gurin party. Amatullahi ta miƙe da saurinta ta bisu tana tafiyarta ta ta-ta-ta...
[7/27, 9:54 PM] Khadeeja Candy♥: *90*


On Sunday Amarya da muƙarrabanta suka kama hanyar Katsina, ta rigasu isa saboda ta jirgi suka je ita da Maryam da ƴan'uwan Anty Amarya su biyu.


A wani gidan Abdool da ke can bypass suka sauka daman tun kamin su zo Ummi ta yi masa wannna shawarar na su sauka a gidan saboda su samu damar sakewa su huta.


Tun lokacin da Abbah da Anty Amarya da Hajiya Barau suka saka ta gaba suna mata nasiha kan aure, ta fara kuka, sai duk ta ji wani yanayi na daban, kamar lokacin da za ayi aurenta na farin, banbanci wannan ba irin wacan auren ba ne.


Yasa an kawo musu komai daga hotel kama daga abinci har abun sha. Misalin ƙarfe uku Yarima ya kira wata ƙanwar Abbah wacce gwaggo ce gurin Namra ya faɗa mata zai aiko da motocin da zasu shiga ita da Namra da wasu mutun uku aje faɗar Mai Martaba.

Namra na zaune a ɗayan bedroom ɗin tare da Maryam da wasu Cousins ɗinta da Aysha da suka zo tare, gwaggo Ramatu ta shigo tana faɗin.


“Ki shirya angon zai aiko da mota a ɗauke mu muje faɗar mai martaba”


Maryam ta daka tsalle.


“Yeeee kaga daɗin abun malam, mu shiga cikin masarauta muna tinƙaho kowa yayi mana iskanci musa a tsire shi a gari”


Sai duk suka sa dariya, har Namra dake leƙa duniyar gizo. Gwaggo Ramatu ta juya ta fice tana jinjina kai.
Maryam ta nufi babban akwatin Namra da aka zo da shi ta buɗe tana duba irin tufafin da Namra zata saka. Wani tsadadden lace ta ɗauko red color da mayafi ta aje saman gado.


“Raihanatu duba min wannan lace ɗin yayi”


Wacce aka kira da Raihanatu ta miƙe tsaye tana duba lace ɗin.


“Kai wannan ai sai ace matar president ce gaba ɗaya”


“Gaskiya kam wannan lace ɗin yayi kyau sosai”


A gajiye Namra ta miƙe ta shiga wanka ta shirya cikin lace ɗin sai suka gyara mata fuskarta, ana cikin ɗara mata ɗankwali wayar Namra ta yi ringing.
Tana ganin Number Abdool ta yi dariya.


“Ango ango”


“Maryam ya gajiyar biki? Ina Amaryata? Na kira wayarta ta ƙi ta ɗaga ki ce ina gaidata kuma ki ɗaukar min pictures ɗinta”


“An gama ranka ya daɗe”


Ya sauke wayar tana dariya tare da amsa sallamar Gwaggo Ramatu.


“Ku fito ga motoci can an zo da su, Maryam ke kaɗai kin isa ni da Talatu zamu je sai a samu wasu cikin ƙannen Anty Amarya su biyu kuma suje tun da ance mutum biyar sun isa”


Raihanatu ta mike tsaye tana kare ɗankwali.


“Haba Baba Ramatu wane irin Maryam kuma ita da take da aure, ai ƙara dai ki ce ni ko zan samu ɗan saurayi da zai ɗauke cikin ƙannen Yarima”


Sai duk suka bushe da dariya Gwaggo Ramatu ta

Please Login or Register in order to submit comment