Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haifar minnda matsala nan gaba ba?”


“Gaskiya bana jin zai haifar miki da matsala, indai ba abunda Allah ya kawo ba, sai dai kinsan komai yana da side effects sai dai wani ya fi wani”


“Okay, ba matsala when za'a saka?”


“Ko yaushe kika tashi, a hannun hagu ake sakawa kuma idan an saka miki ba zaki yi aikin da hannun ba tsawon 24h, amman za mu buƙaci sa hannun mijinki kamin mu saka miki”


“Mijina baya tare da ni yana Katsina, kuma idan da hali ina son a saka min gobe”


“Consider it done, zan yi replacement ɗin mijinki a gurin sa hannu ko da wannan zan yi alfahari”


Tayi kamar bata ji shi, sai ta tashi ta nufi ɗakin Anty tana faɗin


“Zan shiga ciki”


“Around nine za ku shigo”


Ya faɗa sannan shi ma.yasa kai ya fice.


“Mun yi magana da shi zai saka min roba ta hannu”


Ta faɗa tana ƙoƙarin zama kusa da Anty.


“Ta shekara nawa? Ita bata da matsala kamar sauran ko?”


“Eh haka ya ce, gobe da safe za mu shiga”


“Allah ya kai mu, ya baki lafiya”


“Amin”


Kwantawa tayi saman gado, Anty ta tashi ta fita.
Washen garin ranar da yace musu suka tafi aka saka mata, duk wani shirin a ranar Anty tayi mata shi, saboda komawar da zata yi gobe.
Hajiya Barau tayi mamakin komawarta da wuri haka, a take ta raya a zuciyarta ƙila Abbah ne yace be yarda ta daɗe masa a gida ba, ita tama yi mamakin da ya barta har ta zauna, goma na arziki ta haɗa mata, tun daga kan kayan sawa zuwa kuɗi da kayan mata.

Ranar da zata koma taje yi ma Abbah sallama, ranar ta sha kuka kamar ranar da za'a kaita ɗakinta, Anty ma tayi kuka sosai har hakan ya saka sauran ƴaƴan na ta kuka.
Direban gidan aka sa ya kaita har katsina dan Anty bata son ta shiga motar haya. Sai da ta biya gidan Gwaggo tayi mata sallama sannan suka kama hanyar katsina.




RASHIDA POV.


Washe garin ranar data dawo Malamin ya kira yana labarta mata bayanin da ƙasa ta bada akanta.


“Ba zaki taɓa komawa gidan Mijin ki ba, matuƙar wannan matar tana cikin gidan, sannan idan baki tashi tsaye ba, to har ƴaƴanki mijinki zai wulaƙanta su akan ta, kuma kin yi kuskuren ba mu suna, Ummu Kalsoom take ba Ummulkhairi ba”


“Na ɗauka ai duka ɗaya ne”


“Ba ɗaya bane, sannan mun ga wani baƙin hudu a tare da ke, kuma bayani ya nuna a halin yanzu tana sama da ke sai kin tashi tsaye”


“Malam wane irin baƙin abu ne wannan?”


Duk ta tsorta.


“Bayani be fito mana fili ba, amman lailai akwai baƙin abu yana biye da ke, kuma akwai abu a jikinki wanda kike ɓoyewa dangin ki”


“To Malam a taimaka ayi mana aiki, ta fita gidan kamin na cika idda kuma ayi min abunda zai jawo hankalin mijina gare ni”


“Dika za'ayi aikin ma nasa a aiwatar da shi yau”


“Amman ƙasa ta bada bayanin zan koma gidan Hilal?”


“Ƙasa ta bada bayani kan mijinki, matakin da muka ɗauka yanzu idan be yi ba, sai mu yi na biyu idan be yi ba, sai na uku wanda shi kam dole ne a samu nasara”


“Wane mataki ne?”


“Dika zaki jisu, amman na biyu da na uku abubuwa masu matuƙar wahala”


“To Malam na gode, amman dan Allah a taimaka a bincika min baƙin duhun nan”


“Zamu bincika”


Ya kashe wayar, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya tana dafa kai. Baƙin abun nan ya tsaya mata a rai, sai faman tunani take wane baƙin abu ne? Ko dai Ƙalsoom ce ko kuma ciwon da take ɓoyewa ne? Bata samu amsar tambayarta ba har ta gaji da tunanin ta tashi ta shirya ta nufi makarantar su Ezzah. A hanyarta ta tafiya ne Alh Bashi ya kirata wai yana nemanta kwana biyu yayi kewarta, tsaki taja ta faka gefe tana magana da shi.


“Hala baka san aurena ya mutu ba?”


»“Na sani mana, sai dai ban san dalilin mutuwar auren na ki ba”


“Kishiyata ce ta fi ƙarfina ta mallake min miji da ƴaƴa”


Daga can cikin wayar yayi dariya ya ce


“Ke yanzu kamar ki har wata mace ta isa ta fi ƙarfin ki, anya mijin ki ya san mace kowa?”


“Hmmm ƙaddarace ta gitta irin wace zata gitta ka saki Asmee nan gaba”


“A'a aure na da Asmee ai na zobe ne, idan kin ga na rabu da ita to na mutu, indai ina raye ba zan rabu da ita ba, idan kin ga na rabu da ita to na rabu da uwata ne”


‘Hmmm saboda ta maka mugun magani ba, ai wallahi tayi ma kan ta ƙiyamul laili’


Rashida ta faɗa a ranta, a fili kuma sai ta ce


“Kasan da ita kake zama da ni”


“Wannan ai daban, ni dai ki zo ina son ganin ki”


“Ko na zo babu abunda zan maka, dan ni period na ke”


“Na sani haba, ke dai ki zo ina neman ki, amman fa anjima idan mun tashi aiki”


“Na ji”


Ta kashe wayar, ta kunna motar ta hau titi.




ABDOOL POV.


Ko da sha ɗayan safe tayi Ummi da Jidda sun sauka garin Abuja. Kai tsaye ta wuce masaukin Abdool, a lokacin baya ma gidan yana gurin meeting, haka ta zauna a gidan har ya dawo sannan hankalinta ya kwanta ganin da gaske babu abunda ya same shi.


“Ummi na faɗa miki am fine amman kika ƙi yarda da ɗan ki”


“Yanzu ai na yarda, ina ita yarinyar ta ji sauƙi?”


“Eh ance min jiya ta farka, amman ban samu na je dubata ba, amman na ce suje su ɗauƙi statement”


“Allah sarki baiwar Allah ai ta taimaka da yanzu kai ne aka harba”


“Ko bata tare ba, ba zasu harbe ni ba, dan Allah ya rubuta ba zasu same ni ba”


“Haka ne kuma”


“Ummi me kuke so a siyo muku?”


“A'a ni ba zaka ƙara siyen abincin nan ba, ai da gaskiyar Mai martaba da yake cewa ka daina yawo kai ƙaɗai, ni gaskiya ya kamata ace ma ka yi aure dan ka huta da wannan wahalar siyen abincin kullum”


Dariya yayi ya tashi ya fita. Be daɗe ba ya dawo, ya tsaya daga bakin ƙofa


“Ummi zan je asibitin idan kun huta kun ci abinci direba zai kai ku ku ganta”


“To a kula dan Allah”


“Inshallah”


Ya ciro wayarsa dake ringing ya amsa kiran ya juya yana magana ya fice. Sai da ya biya wani office nasu yayi wani meeting sannan ya wuce.


Sun masa bayanin abunda suke zargi akansa, suka nuna masa bayananta da suka ɗauka sannan ya shiga ɗakin da take.
Kife take saman gadon asibitin sanye da tufafin majiyanta, wani irin kallo take masa irin kallon nan na mutum be san yana yi ba. Har ya zauna a kujerar dake facing ɗinta bata ɗauke idonta akansa ba.


Hannunsa ya riƙa yawo da shi dan ya tabbatar tana cikin hankalinta ko akasin hakan. Sai kawai ta lumshe ido hawaye ya silalo daga idon nata. She just can't believe Abdallah take ganin da idonta, mutumen da ko a mafarki take ganin yayi mata nisa, sai dai tasan tayi betrayed wanda yayi mata mafaka a lokacin da bata da gurin zuwa, ga shi waɗanda suka mata tambaya a ɗazu sun tabbatar mata da ya mutu.


“How are you feeling”


Ta buɗe ido ta kalleashi, sai kuma ta kawarda kanta gefe kamar bata ji abunda yace ba.


“Ko ba ki jin turanci ne?”


Ya tambaya yana leƙen fuskarta.


“Ina ji”


Ta amsa ba tare data kalleshi ba.


“Me kike yi ma kuka?”


“Kukan baƙinciki nake, miyasa baka bar ni can na mutu ba? Sai ka ɗauko ni ka kawo ni asibiti?”


“Taya zan bar mace data sadaukarda ranta gare ni ta mutu?”


“Na sadaukarda raina a gare ka saboda ni na rasa nawa ran, kai kana da amfani ga alumma ni ko bana shi, kuma na san duk na sadaukarda rai na a gareka dole ne kai ka rayu ni na mutu”


“Sai gashi kuma sai dik muka rayu”


“Shiyasa ni nake baƙinciki, na yi tunanin ni tawa wahalar ta yanke daga nan ne, ashe akwai sauranta”


“Wacece ke? Miyasa kike irin wannan furucin?”


“Nice wacce ta rasa uwa da uba, wacca aka koreta daga gidan su saboda saurayi ya yaudare ta”


“Ban gane ba?”


“Ƙawata ta haɗa kai da ɗan'uwanta ta yaudare ni. Fyaɗe tasa ɗan'uwanta yayi min, sanadin hakan na samu ciki, ni kuma sai iyayena suka kore ni, na zaje garin Kaduna, ranar dana sauka a garin na haɗu da Guy son yaje tasha karɓar saƙo, sai ya ɗauko ni ya kawo ni gidansa da sunan zai kwana da ni ya biya ni, daya fahimci bana da gurin zama, sai yayi masauki a gidansa, ashe ɗan fashine kuma yana kidnapped ni ban sani ba sai bayan mun shaƙu da shi, shi ya zubar min da cikin da ke jikina ya mayarda ni karuwarsa”


“Ayyah sorry, amman me kika sani game da Guy Son?”


“Ban san komai akansa ba, baya bari na shiga lamurransa”


“Ya aka yi kika san yana attacking ɗi na?”


“Saboda ya san ina son zuwa Abuja, sai yace zai zo da ni, amman wani aiki zai zo yi, na kashe wani soja wanda wata mata tasa aka she shi, amman a nan ba su kashe ka sai ka koma Katsina”


“Ya faɗa miki wacece matar?”


“Be faɗa min ba, ban ma san kai wanene ba kawai ya faɗa min zai zo bibiyar sawon ka ne, ni kuma naga ba zan iya bari ta kashe ka ba, shiyasa na zaɓi mutuwa kai ka rayu, dan nasan dole zai nemi kashe ni, ni kuma buƙatana ya biya tun da ka rayu”


“Wane gari kike?”


“Sokoto”


“Amman miyasa kika zauna da shi bayan kin san yana aikata kisan kai?”


“Me kake tunani ga mace da iyayenta suka koreta? Idan ban zauna da shi ba da wa zan zauna? Wa zai min masauki? Ina za a karɓe ni?”


Kuka ta fara rerawa tasa hannu a baki gwanin tausayi.
Kallonta yake indai har da gaske na abunda ta faɗa, to ita abar tausayawa ce, sai dai shi yana jin be yardar da ita ba.
Jin kukan nata na son yawa yasa shi tashi ya bar ɗakin. Baga ɗaya fita yayi daga harabar asibitin ya nufi wani part na gurin. Wani ɗaki ya shiga ya kwashe waya ɗaya a ɗakin suna tattaunawa sai da aka ce masa ga Ummi nan sannan ya fito ya tare su.


“Jikin nata da sauƙi dai ko?”


“Da sauƙi sosai ma, mun yi magana da ita sosai sai dai a bayanan ta ban yarda da ita ba, dan haka nasa a bincika min komai a kanta”


“Hakan yayi mi tace maka ne?”


A nan ya fara bata labarin da Amira ta bashi, suna takawa zuwa part ɗin da Asibitin take da ƙafa.
Sosai da sosai Ummi ta ji tausayinta ya kamata, har idonta ya cika da ƙwallah, sai Allah wadai take ma iyayenta da ƙawar data cuce ta.


Amira na jin lokacin da suka shigo amman tayi pretending like she's seriously sleep. Fukarta kawai Ummi ta leƙa cike da tausayawa ta juyo ta fito tana mata addu'ar samun sauƙi.




KALSOOM POV.


Tayi mamakin ganin haila a yanzu, bayan tasan tana ɗauke da ciki, kuma rabonta da haila tun kamin ta samu ciki. Hakan yasa ta fara zargin ko dai bata da cikin ne? Sai dai kuma ita tasan tana jin alamun masu ciki kuma Doc ma ya tabbatar mata da haka. Wani tunanin ne ya zo mata, wata ƙila tana cikin matan da suke haila a lokacin da suke ɗauke da juna biyu.
Ita dai abun ya ɗaure mata kai. Tun a dare da abun ya same ta Doc ya sani sai ya ɗaga mata kafa ya saurara na tsawon kwana biyu ya gani ko jinin zai ɗauke mata, amman be ɗauke mata ba. Hakan ya bashi mamaki.
Yayi mata tambaboyi akan lafiyarta, kamin ya ɗauke ta suje suje su yi hoto dan tabbatar da lafiyarta.


Ya yi mamakin results ɗin da hoton ya bada wai bata da ciki, alamu ya nuna mahaifarta ma ciki be taɓa zama ciki ba.
A tare suka dawo gida sai dai be yarda da faɗa mata abunda result ɗin ya bada ba, dan har yanzu mamaki yake, daya sauke ta be shigo ciki ba, ya ce mata ya zai koma gurin aiki.


Ita sam bata lura ba, dan bata kawo komai a ranta ba. Tana shiga falon ranta yayi mugun ɓaci ganin yadda duk suka lalata falon kamar bata gyara shi ba kamin ta fita.
Saman kujera ta zauna tana kallon falon cike da takaici tace


“Ezzah zo ki share falon nan, Ulfah ke kuma ki kwashe plates ɗin nan shine bayan fita na kuka sake ɗiban abinci kamar ba ku ci ba? Kuma duk kuka lalata falon haba dan Allah miyasa ba ku tausayina ne?”


“Ezzah ce ta ce mu ɗibo mu ci tun da abincin Baban mu ne, wai ita bata ƙoshi ba kin sa mata kaɗan”


Ulfah ta faɗa tana shirin tattara plates ɗin. Kallon Ezzah Kalsoom tayi cike da mamaki.


“Abincin da nake sa muku ne baya isarku shine ba zaki yi magana a daɗa miki ba? Sometimes ba ke da kanki kike ɗiba ba? Ezzah me ke damun ki ne? Me yake cikin kan ki ne? Kwanakin nan kwata-kwata kin canja kina son lalata kan ki”


Wata irin harara ta bankaɗo ma Kalsoom kamar ta taso tazo ta maƙareta. Kalsoom ta nufi inda take tana nuna kan ta


“Ke ni kike harara? Warin ki ce ne?”


Ta zungureta. Sai kawai ta fashe da kuka daman jira take.


“Wayyo Ammyn mu....”


“Ooo munafuka, daman abunda kike nema kenan ko? Na dake ki so that ace na cuce ki ko? Ke ƙaramar yarinya da ke kin san munafurci? Tau Wallahi ba zan ɗauka ba, ba zai yiyu na yi kishi da uwarki ba yanzu kuma na yi da ke ba, tashi ki share falon nan ko na miki matsiyacin duka”


Cikin kuka ta tashi ta shiga kitchen ta ɗauko tsintsiya ta soma sharar. Ulfah na daga gefe tana kallon Kalsoom cikinta dik ya ɗuri ruwa ji take kamar itama zuwa zatayi ta dake ta.


Doc be dawo ba sai dare, tun a bakin ƙofa Ulfah ta same shi ta labarta masa abunda Kalsoom tayi ma Ezzah, sai dai be ɗauki abun serious ba dan yasan Kalsoom ba zata dake ta a banza ba.
Sai dai samun Ezzah a falo da yayi tana kuka ya ɗan sosa masa rai.


“Me kike yi ma kuka kuma?”


“Yunwa na ke ji, Anty tace karna sake ɗiba abinci har sai ta ga dama ta ba ni”


“Ba ki ci abinci dare ba ne?”


“Har na rana ban ci ba, wai dan nace sai na faɗa ma maka ta fita”


“Je ki ɗibi abincin zan yi magana da ita”


Ta tashi ta nufi dinning, shi kuma ya nufi ɗakin Kalsoom cike da gajiya.




[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: 4»»»»6»»»»»»»»»»»»»


Gaban mirror ya same ta chaɓa ado tana kallon kan ta. Dik wata gajiya da fushi dake tare da shu sai ya kushe, saboda yana son ado, mutum ne mai son ganin mace ta yi kwallaiya a ko yaushe. Murmushi ya ƙarasa kusa da ita yana ƙyaƙƙyawar fuskarta ta madubi.


Ita ma murmushin take tana lumshe ido tana buɗewa, irin na ɗaukar hankalin nan. Sun samu minti biyar a haka suna kallon junansu kamin ya risina ya rumgume ta.


“Who brought this Cute Babe here?”


Lumshe ido ta yi tana sauraren yadda yake shinshinar wuyanta.
Saukowa yayi ya duƙa gabanta ya kama duka hannayenta yayi mata kiss.


“Sweetheart, I'm sorry we lost our baby...!”


Farincikin da ke fuskarta ya gushe, idonta ya cika da ƙwalla, har sun fara zuba a fuskarta.


“How...?”


“I have no idea kawai result ɗin ya nuna ciki be taɓa zama a mahaifarki ba”


“Amman ina jin alamu na ma su ciki, kuma kai ma ka tabbatar min da ciki ne”


“Yes sai kuma yanzu ya zo akasin tunanin mu, ko kin sha wani abun ne?”


Kai ta girgiza masa tana kuka. Sai ya jata zuwa ƙirjinsa ya rumgume ta.


“Shiiiiii Allah zai ba mu wani”


Ƙamƙame shi tayi sosai tana kuka. Har ƙasan ranta take jin zafin zubewar cikin, ta yi buri akan cikin nan har mafarki take, kuma ita bata san ta sha komai na zubar da cikin ba taya za a ce ya zube?


Daker ya lallaɓa tayi shiru, amman duk kwaliyar da tayi ta dale ta ɓata mata fuska kamar yarinya ta yi kuka.


“Ya Salam, yanzu dik kin ɓata kwaliyar nan”


Bata ce masa komai ba, ta tashi ta hau saman bed ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya. Damuwar da take ciki yasa be yi mata maganar komai ba, sai kawai ya tashi ya koma ɗakinsa yayi wanka ya shirya cikin kayan bachi, sannan ya dawo falon ya kashe kayan kallo, ya tura yaransa ɗakinsu. Sannan ya ɗibi abincin mutu biyu a plate ya shiga da shi ɗakinta.


Dik yadda ya lallaɓata ta ci abincin ƙin ci ta yi, daya matsa mata ma, sai akwai ta fara masa kuka, a dole ya ƙyale ta ya aje abincin jefe dan shi ma baya jin zai iya cin abinci bayan matarsa tana cikin damuwa.
Haka ta kwana cikin damuwa tana ganin kamar dai wasa Doc yake mata, cikinta na nan tun da ita dai bata ji wani alamu na zubewar ciki ba, sai dai kuma jinin dake mata zuba ya tabbatar mata haka. Sai da ta yaƙi zuciyarta sosai, sannan ta iya godiya ga mahalaccinta, ta fawwala masa komai dan tasan shine mai yi, shi ne kuma ya bata yanzu ya karɓe dan haka sai ta gode masa.


Cikin kwana biyu ta manta abun a ranta, ta cigaba da walwalarta tana sakewa kamar yadda take a da. Ta cigaba da bawa mijinta kula sai dai har gobe matsala ɗaya take fuskanta ta ɓangaren Ezzah dan yanzu abun nata sai ƙara ta'azzara yake tana ƙara tirjewa.
Yau ma abunda ta saba mata a kullum shi tayi, ta ci abinci dik ta ɓata falon kuma haka zata tashi ta barshi haka sai dai Kalsoom ta gyara.


Da kallo Kalsoom ta bita har ta zauna saman wata kujera ta zauna ta buɗe school bag ɗinta tana fiddo littafai.


“Ezzah miyasa baki jin magana ne? Kullum idan kin ci abinci sai kin watsar kuma ki bar ni da gyara, da nace ki gyara sai ki buɗe baki ki fara yi min kuka? Wannan wane irin rayuwa ne?”


Gunguni ta fasa mata irin maganar nan ta can cikin maƙoshi ta wanda yara ke yi idan suna takarar rashin kunya. Hakan ya harzuƙa Kalsoom ta har ta ƙarasa inda take ta dangwale ta.


“Me kike faɗa? Ke marar kunya ko? Ina miki magana kina min gunguni”


Ɗan wannan abun da Kalsoom tace mata sai kawai ta ɓare baki ta fara kuka tana, ta tashi da gudu ta bar falon.
A harabar gidan ta je ta zauna tana kuka kamar wacce aka cirewa rai.


Haka ta zauna a gurin har mahaifinta ya dawo ta sanar da shi dukan da Kalsoom ta yi mata. Sam be jidaɗi ba dan babu abunda ya tsana kamar duka, komai zai iya ɗauka amman ban da a dakar masa yara, dan shi be sa musu hannu ba ba zai yarda wata ta sa musu ba, Rashida ma data haifesu baya bari ta dakesu.


“Ba ki mata komai ba zata dake ki? Kalsoom ba zata dake ki haka kawai ba”


“Wallahi ban mata komai ba, kawai tace na share falon nace ta bari na gama homework shine kawai ta mare ni”


“To ya isa yi haƙuri zan mata magana”


“Daddy yaushe Ammyn zata dawo?”


“Ba zata dawo ba”


“Miyasa?”


“Tace ta zaɓi haka”


Ya riƙa hannunta suka shiga ciki. Suna shiga falon ta fisge hannunta ta nufi ɗakinsu da gudu.
Kallo ɗaya Kalsoom tayi mata ta ɗauke ido tana masa sannu da zuwa.


“Yauwa me Ezzah tayi miki kika mareta”


Ya faɗa yana mai zama a kusa da ita.


“Mari? Ita tace maka na mareta haka tace maka?”

“Baki mare ta ba?”


“Haba Doc mi zai sa na ɗaga hannu na mareta sai kace wari na? Ni dai nasan na zungureta”


“Amman Kalsoom be kamata ace kin dake ta ba, Ezzah yarinya ce dik abunda take yi ƙurciyace, sannan rashin mahaifiyarta yana damunta dole sai kin yi haƙuri da ita, bata da uwa a yanzu sai ke”


“Amman idan ta ɗauke ni uwa mi zaisa ta min rashin kunya? Did i treated her badly ne? Miye bana mata tun mahaifiyarta na nan, sai yanzu dan daga bata nan zata fara min rashin kunya? I'm tired Hilal I'm tired ba rainon ƴaƴanka na zo yi ba, nima aure na zo, idan rainon ƴaƴanka kake so ayi maka kaje ka nemo mai raino, amman ni ba zan iya, ba kuma zan yi ba, ko da zai zamo silar mutuwar aurena ne!”


Kallonta kawai yake irin yadda take zuba masa ruwan masifa har hantanta tashi suke, gaba ɗaya ta fita hayyacinta saboda abunda be kai ya kawo ba.
But all what he thought tana cikin damuwar zubewar cikinta ne, he feel her pain, hakan yasa ya ɗaga mata ƙafa be biye mata ba, sai kaiwai ya tashi ya barta falon.


Fashewa ta yi da kuka ta cire ɗankwalinta ta jefar tana kuka.


“What is wrong with me? Miye same ni? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Ta tashi da gudu ta shige ɗakinta tana cigaba da kuka, zuciyarta cike da tsanar Hilal bayan be mata komai ba.






NAMRA POV.


Asim be yarda ta dawo ba, har sai da ya ganta asibitin, aiko ya dinga murna kamar ya ɗauke ta ya haɗiye, Mama ba laifi ta tarbe ta far'ah tana na'am-na'am kamar ba ita ba.
Namra ta jidaɗin haka, sai taga kamar saboda tayi fushi ne Asim ya tsorata yayi canja, duk sai ta ji farinciki ya baibayeta ance so hana ganin laifi, ita dai har gobe zuciyarta na son Asim, duk da da shakkun da take da shi akansa, dan ta ƙudiri aniyar naira biyar nata ba zai sake shiga hannun Asim ba, tun har ta gano nufinsa.


Ya samu sauƙi sosai, dan har likitoci suna maganar sallamarsa ganin yanzu yana taka ƙafar sai dai yayi ɗingishi, Mama ta fi kowa jindaɗin samun sauƙin nasa saboda ta matsu ta koma gida zaman asibitin dik ya isheta.
Ranar da Namra ta kwana biyu da dawo taja ƴar fulani suka je kasuwa ta siye wasu abubuwan na kitchen da na ɗaki, da kuma tufafi da hijabi, da ta dawo da yamma ne ta share ɗakin ta wanke ta zuba center carpet ɗin data siyo da taimakon yarinyar ta kira yayanta namiji ya laƙa mata labulaye sannan ta shiga da katifa, da sauran tarkace. Ta haɗa BQ ɗin ba laifi kasancewar ɗakun biyu ne sai ta mai da ɗayan kamar kitchen ɗinta, ta saka abubuwan zuba ruwa da sauran kayan aikinta ciki.






AMIRA POV.


Washe gari Ummi ta dawo ta ga Amira dan tasha alwashi ba zata bar Abuja ba sai ta yi ma Amira godiyar abunda tayi ma ɗanta.


Amira ta jidaɗin haka, ta san ko ba komai ta samu shiga zuciyar Ummi ganin yadda take tausayinta, har da zubar mata da ƙwalla, gashi jikinta ya nuna ita ɗin wata ce, tun daga kan tufafinta zuwa yadda naman jikinta ya kwanta.
Amira ta kama hannunta ta riƙe sai hawaye take tana son shige mata jiki.


“Na ji daɗi da kika zo, na ji kamar a'ce ke mahaifiyata ce”


“Ni mahaifiyarki ce mana miyasa kike magana haka, Allah ya baki lafiya”


“Amin na gode”


Ta faɗa tana kife saman gado asibitin. Abdool na tsaye hannayensa a aljihu yana kallonsu, shi dik ya gundira Ummi ta bar ɗakin, coz he don't trust Amira, kuma hankalinsa be kwanta da ita ba for no reason.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: 4»»»7»»»»»»»»»»»»»»»




“Wai Daddy yace kin ce ba zaki dawo ba”


“Yaushe yace miki haka?”


“Jiya da ina tambayarsa yaushe zaki dawo, wai yace ke kika ce ba zaki dawo ba”


“Baya son ya faɗa miki ne, saboda yanzu baya so na Kalsoom yake so, idan har kina son na dawo dole ne ki riƙa yin abunda na faɗa miki, idan kina irin haka shine sai za ya tausaya muku yace na dawo”


“Amman ita bata jin daɗin abunda nake mata”


“Ke kina jindaɗin data koreni?”


Ta girgiza kai alamar a'a.


“Idan baki yin abubuwan da nake faɗa miki ke ma wata rana sai tasa Daddy ki ya kore ki, sai ta

Please Login or Register in order to submit comment