Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nunawa juna kamar Romeo and Juliet.


LAMIDO POV.


Ya girgiza da Asim yadda ya mayarda ƙaryarsa gaskiya, har ya nemi ƙetare iyakar Allah, be yi mamakin abunda ya same shi a tun a falon ba, a tunaninsa ma ya cancanci fiye da haka. Bayan Mai Martaba ya tashi sai yayi ma su Abbah sallama Abbah yayi masa godiya, sannan ya kama hanyar Katsina.


A gida ne yake labartawa su Neine abunda ya faru, su kansu da basu ga yadda abun ya wakana ba amman sun jinjina lamarin suna yaba ƙoƙarin Asim na ketare iyakar Allah duk da basu san shi ba.


Abinci ya siya musu da kuɗin da Abbah ya bashi da kuma ƴan kayan masarufi, sannan ya koma Neine na masa addu'ah da kuma saƙon gaisuwa ga su Abbah.
Kwana biyu da komawarsa ya fara aikin a kamfanin Abbah wato Zamau Metals Work kamfanine da ke sarrafa ko wane irin ƙarfe da kuma dukan abunda ya shafi ƙarfi hakaɓ yasa ana yawan bashi kwangila saboda yana hulɗa da ƴan siyasa sosai kuma yana cikin mutane da ake damawa da su ciki da wajen jihar sokoto.


A gidan yake zama lokacin aiki ya tafi idan ya dawo kuma baya komai sai ya zauna a gida, hakan yasa wani mugun shaƙuwa da kula juna ya shiga tsakaninsa da Aisha, har ta kai idan bata ganshi ba sai ta kira shi ita ma haka, babu abunda yake ci mata tuwo a ƙwarya kamar tafiyan da yake akan abun hawa idan zaije aiki ko kuma fita wani gurin daban, wani lokacin ta kan ɗauki makullin motar Anty tasa ya kaota wani gurin, ta saka Abbah gaba da zancen ya siya masa mota sai Abbah ya mallaka masa motar da yake jan namra ada wato wacce yake kaita makaranta. A ranar Aysha ji tayi kamar ta haɗe Abbah dan murna tana ta jindaɗi sosai, daga lokacin duk inda zata je shi yake kaita matuƙar ba aiki yake ba ko kuma zaije ba, shi kansa yana jindaɗin fura da kuma sakewa da Aisha, lokuta da dama tana masa yanayi da Namra, yana samun nishaɗi sosai idan yana fira da ita. Kwana biyu ɗa bashi motar Neine da wani ɗan'uwanta suka zo yi ma Abbah godiya, kwanansu ɗaya suka koma, Yadda Aysha ta riƙa kula da Neine ya karantar da Abbah ba iya mutuncin ne a tsakaninta da Lamido ba har da soyayyar da ma ya lura da irin shaƙuwar da ke tsakaninsu, hakan kuma ba ƙaramin faranta ran Abbah yayi ba, a kullun tunaninsa da ina zai farantawa Lamido ya saka masa da abunda yayi masa, tun daga lokacin da yaje ya bada shedar a faɗar Mai Martaba Abbah ya ji daɗin abunda yayi masa.


YASMIN POV.


Tana ji tana gani kuma tana ciki gari aka yi bikin Namra ta ƙi ta leƙa saboda tana ganin kamar idan taje za a riƙa nunata ne, ko kuma mutane su tuna abunda ya faru.


Duk wani tunani na rayuwa da zullumi sai ta tattarashi gefe ta aje ta maida hankalinta kan aikinta, tun bayan abunda ya faru da Uzair sai ta tattara lamarin namiji ta aje gefe ɗaya saboda tana tsoron faɗawa a wacan halin na baya. Sai dai ba tayi nasarar yin hakan ba tun bayan da ta cika idda sai manema suka riƙa fito mata ciki har da abokan aikinta. Hakan yasa mahaifiyarta matsa mata akan ta yi aurenta zai fi mata mutuncin fiye da zaman gida domin mace bata da wata daraja idan ba gidan mijinta take ba, kuma hakan zai taimaka mata gurin da tarbiyar ɗanta, Allah ta riƙa roƙo akan ya zaɓa mata alherin a cikin manemanta.


AMIRA POV.


Mace ko mai mutuncin ta a yanzu tana wahalar samun miji balle kuma wacce mutane ke ganin ta riga ta zubar da ƙimarta, abunda ta aikata yafi damunta a yanzu saboda zantunkan mutane da kuma tsangwa da take samu a duk lokacin da wani ya nuna yana son ta, daga ya kwana biyu yana zuwa munafukan unguwa zasu labarta masa tsawon lokacin da tayi ba a gida ba sai mutun ya gudu wasu kuma daga gidansu ake labarta musu yarinyar ƴar mutunci ba ce dole mutun ya kama gabansa, tun abun baya damunta har yazo yana ci mata rai, bama kamar idan ta duba duka ƙawayenta sun yi aure ita kaɗai ce a haka, karatun ma ta kasa komawa saboda damuwa da ta sawa ranta, lokacin da maganar auren Namra da Abdallah ya same ta tayi kuka sosai har sai da ta raina kanta, domin har gobe tana son Abdallah. Wani lokacin ta kanji kamar ba zata iya auren ƙaramin mutun ba, sai dai ganin babu sarki sai Allah yasa ta fara kula Sani Engineer, wato mai yi ma Mahaifinta gyaran mota a duk lokacin da ta samu matsala, shi ma kansa ba dan arzikin da yake ganin ubanta na da shi ba da babu abunda zai sa ya aureta saboda familynsa suna yawan magana akan su basu yarda da ita ba, duk kuwa da kasancewar ita ce ta uku a cikin matansa.


Duk wani abu da take ji akansa ta kan yi haƙuri ta danne zuciyarta saboda samawa kanta da kuma iyayenta farinciki, duk da tana jin kamar ba zata samu farincikin da take so tun da ba sonshi take ba, kuma gashi yana da mata da ƴaƴa taya zata jidaɗin zama a gidansa, da ta nemi ya kama.mata haya sai ya ce mata bashi da wannan halin kuma wai shi baya son raba kan iyalansa, a dole tasa Mahaifinta ya kama mata haya, domin ƙannenta ma an aurar da su sai ita, kusan rabin hidimar auren ma duk Mahaifinta ne yayi saboda shi ba mai kuɗi ba ne sai rufin asiri duka abunda aka ɗora masa Mahaifinta ne yake yi saboda ya samu dai ta yi auren.


Assabar aka ɗaura aure bayan anyi ahagulgulan biki kamar yadda ake ma ko wacce Amarya, duk da ita Amira bata so haka ba Ammy ce ta matsa ayi wai saboda asan ita ma tana da gata kamar ko wace yarinya, ba kowa ba ne yasan wanene mijinta saboda ɓoyewa ake wasu kuma indan suka ji ance Engineer sai su ɗauka ko wani babban Engineer ne.
Ranar da aka ɗaura aure aka kaita gidan mijinta unguwar minannata.






ASIM POV.


Kusan hoto kala biyar ana masa amman result ɗaya yake badawa, jijiyoyinsa na ƙafa sun murɗe, akan maganin likitoci suka ɗorashi wai ko za a dace amman shiru babu wani labari, tun da aka kawo shi asibin sau biyu kawai abokansa suka riƙa zuwa suna dubasa, ko su ba dukansu ba, masu ɗan sauran imani domin basa kula mutun idan baya da lafiya ganin suke bashi wani amfani, Ubangidansa be taɓa zuwa duba shi ba sai dai ya turo masa da kuɗi kusan miliyan ɗaya ya siye magani, ganin babu wani canjin a ciwon nasa yasa suka nemi ya fita waje ko Allah zai sa a dace. India ya fara zuwa watansa ɗaya a can shi da Amaryarsa amman babu wani canji, bayan sun dawo naija ne ya sake biyan wasu kuɗin aka fitar da shi ingila nan ma labarin babu wani banbancin, can kan satinsa biyu kawai yayi ya dawo saboda kuɗinsa sun fara ƙasa komai na tsada ne a can. Wata asibitin ya canja da suka dawo nigeria, haka yayi ta kashe kuɗi amman babu wani sauƙi balle ma canji wani lokacin idan abun ya taso masa sai yaji kamar a cire masa ƙafafunsa gaba ɗaya ya huta. Lokacin da Amaryarsa ta fara lura da abubuwa sun yi ƙasa sai ta koma gidansu aka bar Mardiya da jinya.


A familynsu babu wani mai arziki sosai da zai iya ɗaukar ɗawainiyar Asim, wani lokacin ma zuwa su ganshi yana musu wahala musamman yanzu da suka ji shine dalilin mutuwar mahaifiyarsa sai kowa ya daina tausayinsa, suna cewa shi ya jawa kansa, mai gidansa ma tun yana ƙoƙarin aiko masa kuɗi yace ya siye magani har ya daina ganin ɓba sauƙi zai ji ba, kuma bashi da wani a amfani a gareshi yanzu, daman idan suna sonka to kana amfanarsu ne. Wasa wasa ciwon nan ya jawa Asim hasara da yawa duk abunda da ya tara sai da ya ƙare be ji sauƙi ba, hakan yasa suka tattara suka koma gida.


Daga nan ya fara saida filayensa guda biyu da kuma gidansa guda ɗaya da suka rage masa a rayuwa, ranar da aka kawo masa kuɗin jikinsa ya tsananta sosai har ya bawa Mardiya tsoro sosai.


“Asim ko asibiti zamu koma ne?”


Kai ya girgiza mata hawaye na masa zirya, ga wani wahalallen numfashi da yake.


“Ni kaɗai nasan irin azabar da nake ji Mardiya, ina zanje da waɗannan kayan?”


Kuka kawai take tana riƙe da hannunsa da yayi mugun zafi, sai shi ma ya kalleta cikin hawaye.


“Na yi hasara na tsaɓi Allah, yanzu gashi zan koma gareshi ina ƙazami, bana da ɗa Mardiya balle na samu mai min addu'ah kaico na!”


Ya damƙe hannunta ƙawai zuciyarsa na wani irin fisgarsa har jikinsa sai ya girgiza.


“Makomata tana jirana Mardiya, kwanciyar ƙabari Mardiya, idan Allah ya tambaye miyasa na aikata luwadi me zan ce masa? Nice silar mutuwar Mama, nine na keta haddin Allah, Mardiya na cutar da Namra, na yi isgili, na tara kuɗin da Allah zai tambaye ta ya na samu naira taya na kasheta, na tara kuɗin da basu tare min hisabi ko azabar ƙabari ba, Allah ya ce kar a kusanci mace ta dubura ni na yi, ina zan je da waɗannan kayan Mardiya zafi nake ji zafi zafi...”


Ya fara tari muryarsa na sarƙewa, a take baƙin idonsa ya ɓata sai farin akwai akw gani, halshensa ya karye, tana son ƙara wata magana amman ya ƙasa sai hawaye ke masa zuba, yana wani irin banƙara yana numfashi daker, zafin fitar rai ya tattara a jikinsa sai karkawar yake yana kallon sama.
Tashi tayi a gudu ta fita daga ɗakin ta shiga maƙota domin kiran jama'ah a kama mata ta kaishi Asibiti, tana ganin alamun ya fara fita hayyacinsa.


Kusan mutun shida suka shigo mata huɗu maza biyu domin taimaka mata, sai dai yanayin yadda suka tararda shi yasa jikinsu mutuwa, idonsa a kafe kansa ya malguɗe halshensa ya fito.
Dattijiwar cikinsu ce ta duba da kyau tana girgiza kai ta ce.


“Sai haƙuri Mardiya mijinki na amsa kiran mahallincinsa”


Da gudu Mardiya taje tana girgiza gawarsa tana kuka.


“Asim Asim”


Dattijuwar tasa hannu ta shafe masa idonsa tana hawaye kamar yadda kowa ke yi. Kamar wacce ta haukace haka Mardiya ta koma tana tsalle tana direwa tana kirama kanta hallaka, da shiga uku.


“Wayyo Allah na shiga uku Asim ya tafi ya bar ni, na bani na lalace wayyo ni Allah na kaicona ni Mardiya”


Sai da jama'a suka riƙata aka fitar da ita waje. Ba'a masa jana'iza ba sai da ƙanen mahaifinsa dake sokoto suka iso, misalin huɗu da rabi na yammancin ranar talata aka sanya Asim a cikin ƙabarinsa bayan an masa sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanada, a saman ƙabarinsa suka tsaya suna masa addu'ar samun sauƙin karɓa tambayar mala'iku kamar yadda Annbi ya koyar. Rayuwa kenan Allah kasa muyi ƙyaƙƙyawan ƙarshen, dukan mai rai dole ya bar duniya😭






NAMRA POV.


Tun da suka je abuja kullun sai ta yi waya da Anty Amarya da Abbah saboda kewarsu, da gangan Abdool ya hanata zuwa ɗauren auren Yasmin duk da taso zuwa, wai baya son yawan nan zata wahalar masa da baby, haka ta saka shi a gaba ta yi masa kuka amman ya ƙi ya barta taje.
Bata zuwa sokoto sai idan zasu yi jarabawa, shi ma dan babu yadda zai yi ne kawai, aiko tana ƙarewa be sake barin ta leƙo sokoto ba.


Katsinar ma tun aurensu Meesha da Haleema da Fauziya, shi ma dan Ummi ta matsa ne da yaso ba zata zo ba sai ranar da za'ayi ɗaurin aure su zo tare, Ummi ta tirsashi ya kawo ta wai zai koya mata ƙin shiga mutane bayan kuma yasan familynsu suna da yawan hidima.


A falo suke zaune, Namra na saman kujera yayinda shi yake zaune a ƙasa ta ɗora masa ƙafafunta saman kai suna kallon wani series drama ya ɗauki hankalin Abdool sosai, saboda criminal case ne ake. Sai dai duk yadda yake son maida hankali gimbiyar ta hana shi, sai wasa take da kunnensa tana sa kunnensa a babban yatsan ƙafarta ta matse sai ya ture mata ƙafa ta maida ya sake turewa ta maida, can kuma ta saka ƙafarta ta dinga zungurar masa kai, duk abunda tayi masa ƙyaleta yake saboda kawai yana son drama da ake.


“Omri yunwa na ke ji, ka ji? Yunwa na ke ji sosai”


Ya kama ƙafafunta gaba ɗaya ya riƙe yana cigaba da kallon tv.
Be bi ta kanta ba sai da ya gama kallon da yake sannan ya tashi ya zuba mata abincin da ke kan dinning a plate ya kawo mata ya koma ya ɗauko mata lemu da cup ya aje a saman tebur ɗin da take gabanta, shi ya riƙa feeding ɗinta har ta ƙoshi sannan ya miƙe tsaye ya kwashe kayan ya kai kitchen sannan ya dawo ya miƙa mata hannu ta riƙa hannunsa ta miƙe tsaye.


“Ɗazu Anty ta faɗa min wai Maryam bata da lafiya”


“Allah ya bata lafiya, babu inda zaki je”


Ta taɓe fuska kamar ta fasa kuka.


“Wallahi ni na gaji da zaman nan, kullum guri ɗaya”


“Ke kin fi son kullum kiyi ta yawo baki Katsina baki sokoto, haba Abnam ki riƙa tausayin abun da yake cikinki mana, kuma nima ki riƙa tausayina kin san ba son nake kina nisa da ni ba”


“Malam ba wani tausayinku, shikenan sai na kashe kai na ku na raya ku? Haka fa ka hanani zuwa gaisuwar Hajiya Sadiya ƙiri-ƙiri, kuma yanzu Maryam bata da lafiya ace ba zan je ba”


“Bari na kira Maryam ɗin naji yadda jikinta yake, kin san ai rashin lafiyarta ba zai wucw a ce ciki ne ba”


“Ni bance ka kirata ba”


Ta faɗa kamar tayi fushi ɗin nan. Zagayowa yayi ta bayanta ya ɗora hannunsa saman ƙaton cikinta.


“Idan kin haihu sai kije ki gansu ai, Abnam miyasa baki tausayin kan ki ne wai? Yanzu baki ganin ko guntun tafiya kika yi yadda ƙafarki yake kumbura balle kuma babba ace daga nan har sokoto haba Hajiya, a riƙa tausayawa kai mana”


Ta ture masa hannu ta nufi ɗakinta. Binta yayi yana rarraahinta shi kanshi yasan tayi missing ɗin gidan, sai dai shi baya son ta je ko'ina saboda cikin nan nata gani yake kamar da ta ɗaga wani abun zai same shi, hakan yasa indai ba aiki yake ba kullum yana gida saboda yi kula da ita da kuma kama mata wani aikin duk da likita yace ta riƙa ɗan wala jininta.
Duk ta bi ta motsaye ta tsomaye saboda cikin ya janye ta, Abdool kawai ke ta ƙiba abunsa hankalinsa kwance bashi da matsala ta ko'ina. Ita kaɗai ke ta fama ɗan chat ɗin da take tana rage kewa yanzu duk ta tattara ta watsar komai baya mata daɗin a duniyar nan, cikin ma ji take kamar ta cire shi ta aje. Wani lokacin idan suna fira da Abdool ta kance ashe haka iyaye suke ji shiyasa ake cewa ƴaƴa suna da haƙƙin iyaye, haka zata zauna tana masa kuka kamar ƙaramar yarinya, wai cikin ya haye mata zuciya ko ya taushe mata mara.
Kusan kullum shi yake daba abinci saboda bata cin abincin kowa sai nasa, ko takeaway yayi musu sai dai ya cinƴe abunsa wai warinsa take ji, ko ita ta girka abincin bata cinsa sai dai Abdallah yayi mata, da wasa-wasa ya ƙware gurin girki saboda yau idan yayi mata wannan gobe wacan zai mata.
[8/7, 2:48 PM] Khadeeja Candy♥: Ranar Monday EDD ta ya cika amman bata haihu ba sai wata assabar a babban asibitin Abuja, murna gurin Abdallah kamar ya soye Namra da yaron da ta haifa ya cinye dan tsabar jindaɗi da farinciki, Allah ya nuna masa ya ga jikansa ta ɓangaren Abdallah.
Mai Martaba ma sai ya rasa inda zai sa ransa saboda farinciki, tun a waya yasa aka turo masa hoton jaririn ta whatsapp. Ƴan uwan Abdallah babu wanda be saka hoton a instagram ba, a can sokoto ma murna suke, family Abbah da kuma Mai Martaba da suke Abuja suka ne suka riƙa kula Namra, awarta guɗu a asibiti bayan ta haihu sai da suka sa ta yi bachi sannan suka sallameta.
Ko da ta dawo gida yamma yayi a dole ta haƙura ta bi jirgin gobe. Tare da family Abdallah suka sauka sokoto, su sukaje da kansu suka kai Namra har gida, iya gata an nunawa Namra ta ko wane ɓangare.


An zuba mata kayaɓ barka kamar ba gobe, kayan jariri sai ka ɗauka wani ƙaramin shago za a buɗe na siyar da kayan jarirai, ga shi ƴan uwa sai kawo mata ake ta ko'ina.


Ranar suna yaro ya ci sunan Mai Martaba, wato Ahmad, akayi masa laƙani da Sultan. An kashe naira ranar suna kamar ba a san zafin nemanta ba, duk faɗin gidan sai da ya cika da jama'a, musamman ma da yamma da ƴan'uwansu Abdallah suka zo da kuma na Ummi. An ci ana sha kuma an watse cikin farinciki da kwanciyar hankali, kowa sai yabon bikin yake ana Allah sam barka.


Duk bayan kwana biyu sai Abdool ya zo sokoto ganin ɗansa, kira kan waya kan waya ta safe daban ta rana daban ta dare ma haka. Kamin ta yi arba'in duk ya takura, kunyar Anty yasa ya kasa magana har sai da ta ƙara sati biyu sama sannan aka maida ta Abuja, tare da bayinta guda biyu sabida su taimaka mata hidimar gida.


Komai ya koma musu kamar su suka tsarawa kansu yadda rayuwar zata zo musu, suna bawa junansu kulawa yadda ya kamata, sai dai wani lokacin tana fuskantar matsala ta ɓangare Abdallah saboda zafin kishi da yake da shi. Lokuta da dama yakan hanata zuwa wani gurin ita kaɗai duk kuwa da kasancewar a garin Abuja ne amman ganin yake kamar wani zai mata magana idan ta fita ba tare da shi ba.


Yau ma duk da tana son fitar dole ta haƙura har sai da yawo, ya ci abincin yayi wanka sannan ya ɗauki Sultan ita kuma ta riƙa jakarta suka fita, shi yake driving Sultan na jikinsa rumgume ita kuma tana front seat har suka isa, wani babban Shopping.
Tana gaba yana biye haka suka shiga shopping ɗin. Yana riƙe da Sultan har ta siye abunda duk zata siya aka zo gurin biyan kuɗi ya bada atm ɗinsa aka cire adaɗin kuɗin da ta kashe, sannan suka koma cikin motar ya ɗauki hanyar gidansu Hajiya Umaima, wato Ƙanwar Mai Martaba wacce take nan Abuja.


Ta tarbesu da far'ah daman ta jima tana masa magana akan ya kawo mata Namra. Hannu ta kai ta karɓi Sultan da ke hannun Abdool tana faɗin


“Ai har na yi fushi na ce ba zan sake maka magana ba”


“Ko yanzu ai nice na matsa”


“No.wonder ni nasan sai ƴata”


“Haba Hajiya taya zaki biyeta ni nace ta shirya mu zo fa”


Hajiya Umaimai tayi dariya.


“Duk abunda zaka faɗa ba zan yarda ba. Mardiya kawo lemu kamin abinci ya ƙarasa”


Ta ƙarasa tana ƙwalawa mai aikinta kira, ba a ɗauki tsawon lokaci ba sai ga Mardiya ta fito daga kitchen ɗauke da drinks da cups. Gabanta ya faɗi lokacin da tayi arba da Namra, ita kanta Namra tayi mamakin ganinta sai dai daga ita ha4 Mardiyar babu wanda ya iya yima wani magana, har sai da ta wuce sannan Namra ta kalli Hajiya Umaima ta ce




“Hajiya ina kika san Mardiya?”


“Wallahi daga Katsina aka kawo ta, na ce a nemo min wace zata riƙa taya ni aiki ne sai aka kawo min ita, kin santa ne?”


“Eh a Katsina take shiyasa na yi mamaki ganinta nan”


“Aiki ta zo yau satinta biyu ma”


“Allah sarki”


Umaima ta miƙawa Namra Sultan.


“Bari na duba abincin nan, kar na shiga muku da yaro Kitchen”


Abdool yayi dariya


“Wai ina su Jamila ne?”


“Wlh duk sunje biki kasan halin ƙanen naka sai a hankali idan kunnensu ya ji biki, ba manyan ba ba yara ba”


Hajiya Umaima na shiga Kitchen sai Namra ta miƙe tsaye ta miƙawa Abdool Sultan ta nufi ɗakin da ta hango Mardiya ta shiga. Da sallama ta shiga, amman Mardiya bata iya amsa mata ba saboda bata son ta gano kuka, gyaran ɗakin ta tarar tana yi. Har Namra ta juya zata fita sai Mardiya ta juyo ta ce.


“Namra Asim ya mutu, Asim ya koma ga Ubangijinsa”


Namra ta juyo tana zaro ido.


“Yaushe? Miya same shi?”


“Rashin lafiyar da ta kama shi a faɗar Sarkin Katsina bata barsa ba sai da ta tafi da ransa”


“Innalillahi wa'inna ilaihi”


Ta faɗa tana dafe kanta hawaye na zubar mata. Mardiya ta risina ƙasa tana kuka.


“Namra ki taimaki Asim ki taimake ni ki yafe mana, amanarki da na ci ta hanani sukuni, duk wanɗanda na yi ma zalumcin na nemi yafiyarsu ke kaɗai kika rage min, na tsorata da irin mutuwar da Asim yayi, bana son na yi irin mutuwarsa”


Namra ta duƙo dai-dai Mardiya tana dafata.


“Miya samu Asim?”


Babu abunda ta ɓoye mata daga rayuwar Asim daga rashin lafiyarsa da kuma mutuwarsa zuwa irin rayuwar luwaɗin da tasan yana yi, ga kuma saduwar da yake yi da ita ta baya.


“Bayan mun gama wanka aka raba mana gadon kuɗin da ya bari na gida da filayen da ya siyar, a take nawa kuɗin suka ƙare gidan da na siya kuma ya ƙone, ga rashin lafiyar da take jikina saboda saduwar da yake yi da Ni ta baya, a duk lokacin da wannan ƙaiƙayin ya taso min sai na ji kamar zan mutu, na kasa daina mafarkin wuta Namra, ada ina tunanin ko wutar da na kunna miki ce gidanki ya ƙone, amman sai nake ganin kamar har da wutar lahira ce take jirana, ki taimake ni ki yafe min Namra, na ci amanarki, na han'ince ki, na cutarda ke”


Wani kuka take marar murya saboda bata son Hajiya Umaima ta ji.


“Na yafe miki Mardiya shi ma Asim na yafe masa, Allah ya masa rahama”


Ta miƙe tsaye tana hawaye.


“Ki rufa min asiri karki faɗawa kowa sirrin, yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa na bar Katsina na dawo nan ga aiki saboda na canjawa kai na rayuwa, kuma na rufawa kai na asiri da abunda zan ci, na taimaki uwata da ƙannena”


“Babu wanda zai ji, na miki alƙawari ba zan taɓa faɗawa kowa ba”


Sai da ta share hawayen sannan ta fice. Sai dai hakan be hana Abdool gane ta yi kuka ba. Tana zaunawa kusa da shi ya kalleta ya ce


“Kin yi kuka saboda kinji Asim ya rasu ko?”


Da sauri ta kalleshi.


“Ka sani kenan?”


“Abnam har gobe kina son Asim”


“No ba haka ba ne, kawai ina tausayinsa ne”


“Tausayi ne silar so”


“Ba irin wacan tausayin ba”


Ya miƙe tsaye tare da ɗansa, ya ɗauki car keys ɗinsa ya fice. Tana zaune a gurin ta ji tashin motarsa. Lumshe ido ta yi ta buɗe sannan ta ɗago tana amsa maganar da Hajiya Umaima ke mata.


“Lafiya Babangida ya tafi?”


“Wai zai ga wani abokinsa ne, yace idan an ɗan jima kisa direba ya kai ni”


“Okay toh taso muje ɗaki ga abincin nan Mardiya zata kawo yau mun ranar girki”


“Wallahi Hajiya na ci abinci”


“Ai nasan kin ci abincin, karki so ma min musu ba tarbiya ba ce”


Da murmushi Namra ta tashi ta bita suka shiga ɗaki. Kamin ta gama cin abinci ayi sallah la'asar har ta tsawwala saboda tunanin Abdool yana can gida cikin ɓacin rai. Tana gama sallah la'asar ta yi ma Hajiya Umaima magana tasa ka direba ya kai ta gida. Bata same shi a falo ba, hakan tasa ta nufi ɗakinsa, kwance ta hango shi saman gado, Sultan na saman ƙirjinsa idonsa a lumshe kamar mai bachi.


Tasan ba bachi yake ba, domin be saba bachin yamma ba, sai dai wannan baya rasa nasaba da ɓacin ran da take tunanin ya sawa kansa akan abunda har ga Allah ba haka yake ba. Be buɗe ido ba har ta ƙarasa kusa da shi ta zauna saman gado.


“Ya Omri...”


“Abnam please, bana son na fara ganin laifinki, bana son zuciyata na ƙonuwa

Please Login or Register in order to submit comment