Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kalli Namra fuskarsa da murmushi ya ce.


“Namra ba gaisuwa, kin san ni fa yayanki ne”


“Ina wuni”


Ta gaisheshi ba tare da tayi murmushi ba, ita hankalinta gaba ɗaya ya tattara ya koma kan Uzair yanayin yadda ta ganshi ya bata mamaki, daman hausawa suka ce abunda duk ya baka tsoro wata rana sai ya baka tausayi, gaba ɗaya ya tafi da imaninta, ya rame sosai, ga ledar fitsari an saka masa ta ƙasanshi, saboda rashin tashin da yake. A ɗayan ɓangaren kuma tana mamakin ganin Amira a ɗaki tare da iyayenta da kuma abokinsa Tahir.


“Ka tara mutane a nan kuma baka ce komai ba”


Umma ta faɗa cikin rashin daɗin rai, dan bata so ya kira Amira ba, duk da bata san dalilinsa na kiranta ba.
Ya ɗauki dogon lokaci kamin hawayen da suke masa zuba su tsagaita masa har yaja dogon numfashi ya sauke, sannan ya soma magana.


“Abbah zaka iya tuna wani lokaci a baya da aka ce Namra ta gudu taje gurin Asim? Ni na ɗana mata tarko tare da aminiyarta Amira, na bata sabon number da sunan zata zo ta ga Asim a bayan gidansu su gaisa, alhalin ni ne ba Asim ba, bayan na ɗauke ta sai abokaina suka canja min shawara da sunan kar na mata komai, na maidata a can, abokina ne ya faɗawa mai gadin gidana abunda zai faɗa akan ya tsince ta a bayan gidan ana ƙoƙarin yaga mata mutunci, kuma ana kiran sunan Asim... Kasan dalilin da yasa na yi mata wannan sheri? Saboda ta tona min asiri akan abunda na ke aikatawa, wato na neman maza ƴan'uwana, ba ƙarya ta faɗa ba, ta gan ni da gaske ina aikata wannan abun, amman na ƙaryata ta ne saboda ina ganin kamar asirina zai tonu ne, a lokacin, shine dalilin da yasa na ɓullo da maganar neman aurenta, sai ita kuma ta ƙi yarda, sanadin hakan da kuma gudun karta tona min asiri abokina Najib ya kai ni gurin wani boka muka mata asiri, yace sai an kawo rigarta da ita za ayi wannan asirin, sai na samu Amira na biyata na faɗa mata haka kuma ta yarda ita taje ta aro min rigarta da sunan ita zata saka muka kai akayi mata asiri da wannan rigar, daman can bokan ya faɗa mana duk lokacin da ta saka rigar idan har asirin be kamata ba to zai dawo kan mu ne, saboda Namra tana da ƙarfin addu'ah. Da asirin be kama Namra ba sai ya kama Amira, sanadin hakan ta gudu ta bar gida, ban sake jin ɗuriyarta ba, sai a lokacin da ta aiko min da wasiƙar cewar idan har ban je na kare wannan aikin ba zata iya aikata min komai. A lokacin ne Yasmin ta gani, kuma ta gano abunda ya shiga tsakanina da Adnan, wata rana ne da rana na shigo sai na tarar bata cikin gidan, sai kawai na afkawa ɗa na, daman can nafi son yi namiji, tun daga lokacin na keɓe Adnan ina jiyarsa bata gane ba, sai daga baya, sanadin hakan tace zata kai ni kotu, ni kuma na ƙaryata gaskiyarta, Washe garin ranar ne Hajiya barau ta kira ni ta faɗa min Namra ta dawo, daman ita take labarta min halin da Namra take ciki, da kuma duk wani abu dake gudana a gidan...”


Tun da ya fara maganar be tsaya ba sai da ya kai aya. Idon Abbah sun rine sun yi ja sosai, Abbah Amira ma kansa ya ɗaga sama ya maida hannayensa baya yana jinjina lamarin. Anty Amarya da Ammy kuma suna hawaye, Amira kan kasa kuka ta yi duk ta rikice jikinta sai rawa yake gumi na keto mata ta ko'ina.


“Miye dalilinka na faɗar gaskiya Uzair miyasa ba ka yi shiru da bakin ka ba? Miyasa baka ɓoye sirrinka ba kamar yadda nima na ɓoye nawa? Ban yi niyar faɗawa kowa abunda ka aikata ba Uzair, duk da rayuwar da na shiga ta fi wacce kake ciki a yanzu, dan ni nafi ƙaunar irin ciwon nan naka na san zai sadani da lahira a nan kusa, sama da jiran gawon shanu, jiran abunda babu ranar zuwansa. Ban taɓa tunanin haka ba, na yi tunanin ka haɗa kai da Namra ne ka cutar da ni ashe ni na cutar da kai na! Yanzu na fahimci dalilin da ya sa na gudu na bar gidan mu, kuma bayan na gudu ban faɗa hannun ƙwarai ba, sai na faɗa hannun ɗan fashi, ya mayarda da ni kamar matarsa, ta sanadinsa na ceci wani mutun wanda nake wa jiran gawon shanu, a familynsu na zauna, ina ganin kamar wata sabuwar rayuwa zan shimfiɗa ashe a saman wuta na yi shinfiɗar....”


Amira ta ƙarasa tana durƙushewa a gurin cikin wani irin kuka da yake jin kamar ta haɗiye zuciya ta mutu ta huta. Lokuta da dama ta kan ji hakan idan ta tuna yadda Abdool ya juya mata baya, mutumen da ta fi ƙauna fiye da komai a rayuwarta, a yanzu haka bata da buri sai na shi, shiyasa ta kasa maida jikinta duk da tana tare da iyayenta.
Gaba ɗaya Namra ta ruɗe ta kasa gane komai, daga Uzair ɗin har Amira kallonsu take tana hawaye.


“Yasmin ta kasa samun fili a zuciyarta ta yafe min, saboda na yi mata sara ne a baƙin wuya, amman ke na san zaki iya yafe min, duk da kema na miki illah, amman ki dubi girman Allah ki yafe min ko Allah zai tashi ƙafaɗuna. Idan kuma har wani aikin ne Amira ta yi min dan Allah ki je ki warware shi, saboda na tsorata da kalamin da kika rubuta min cewar zaki ɗauki mataki. Ba zan iya jure zama cikin wannan rayuwar ba, ki taimaka min ki yafe min Namra...”


“Ba zata yafe maka ba, ashe kai ne silar komai, Namra ba zata yafe maka ba...!”


Abbah ya faɗa a tsawace, har sai da Namra ta kalleshi. Ya nufi ƙofa a hasale ya buɗe.


“Mamana wuce mu je”


Abban Amira yayi saurin riƙe Abbah.


“Haba ai babba baya haka, babba baya taɓa zama ƙarami, kuma tun da har yayi nadama ya kamata ka yafe masa”


Abbah ya girgiza masa kai yana ɓanɓare hannunsa daga riƙon da yayi masa.


“Sake ni Alhaji, yaron nan be kyauta min ba, babu abunda ban masa ba a rayuwa, acw ya rasa wanda zai yi ma zagon ƙasa sai ni da iyalina, wannan wane irin abu ne? Yanzu da be shiga wannan halin ba babu wanda zai san gaskiya, sai dai ayi ta zargin Namra, babu abunda ban ma yarinyar nan ba saboda shi, ashe tana kan gaskiyarta...”


Tuni Anty Amarya ta kama hannun Namra suka bar ɗakin, sannan Abbah ya rufa musu baya. Bayan fitarsu Big Bro ya kalli Amira dake taugune a gurin tana kuka ya ce


“Kinji kunya wallahi kin ci amanar ƙawarki”


Ya ƙarasa tare da jan tsaki ya juya a fusace ya bar ɗakin. Baka jin kukan kowa a ɗakin sai na Umma da Amira, dan Ammy hawaye kawai take, kamar yadda Tahir ke yi..






***


Kuka sosai Namra ta dinga yi a a motar har suka iso gida daga Anty Amarya har Abbah babu wanda ya iya buɗe baki ya furta wata kalmar balle kuma ya bata haƙuri.
Inda suka bar Lamido a gurin suka same shi zaune, Abbah be bi ta kansa ba ya wuce Anty Amarya ma haka, Namra ce ta tsaya dai-daice tana share hawayenta da Hijab ɗinta ta nuna masa wasu ɗakuna da suke can gefen gardem.


“Kaje ka zaɓi ɗaya daga cikin ɗakunan can, zan kawo maka keys ɗin ɗakin anjima...”


Gaba ɗaya hankalinsa na kanta, ya tsorata da yanayin da ya ganta saboda ya tsani zubar hawayenta.


“Allah yasa ba nine dalilin zubar wannan hawayen ba!”


“Ba kai ba ne, gaskiya ce ta yi halinta...”


Ta faɗa tana kallon sabuwar motar da aka buɗewa gate ta kunna kai a harabar gidan. A gurin da aka tanada dan faka motoci, aka nufa da motar kasancewarta mai baƙin gilashi baka iya hango wanda yake cikin motar. Ya ɗauki daƙiƙa goma sha biyar zuwa ashirin kamin ya fito daga cikin motar. Gaban Namra yayi mugun faɗuwa hango Abdool daya fito daga cikin motar sanye da farin yadi fuskarsa sai sheƙi take..
[7/18, 8:14 PM] Khadeeja Candy♥: *85*


Bayan Abdool ya fita Namra ta koma cikin falon Abbah, har lokacin tana jiyo shessehakar kukan Anty. Hannu ta kai ta tura ƙofar ɗakin Abbah ta tsaya daga bakin ƙofa tana hawaye. Bata san abunda Abbah yayi ba ko yace, sai dai tasan yadda ransa ya ɓace hakan nan dole sai wani abu ya faru.


Kallo ɗaya Abbah yayi mata ya ɗauke kai, ya zauna saman kujera yana kallon Anty Amarya.


“Dan Allah ki tashi ki ba ni guri ni bana son hayani”


Unƙurawa Anty ta yi ta tashi tana cigaba da kuka ta fito sai Namra ta riƙa ta suka nufi part ɗinta.


Saman kujera ta zauna tana kuka, Namra ta zauna kusa da ita ta kama hannunta ta riƙe.


“Anty mi Abbah yayi? Miyasa kuke kuka?”


“Yace Hajiya ta tafi ta bar masa gidansa, nayi nayi da shi amman ya ƙi, taya zai tura mace mai ƴaƴa da ƴawa kuma uwargidansa ya ce ta bar masa gida? Wannan sam be dace ba, komai ta aikata aiko ƙyaleta yayi ya barta da kunyarta, gaskiya dai ta riga ta bayyana babu abunda zata koma yi, amman yanzu ai ƴaƴanta ba za su ji daɗi ba”


“Ya sake ta ne?”


“Be sake ta amman ya ce da tafi duk inda zata je sai ya nemeta”


“Idan ya huce zai maida ta Anty, kowa dole ne yaji baƙinciki ace da matarsa za a haɗa kai a cuci iyalansa”


“Nasan abunda ta yi bata kyauta ba, amman ki duba ki ga halin da yaron nan yake wannan kawai ya isaahe ta ishara, ita sai ya zuba mata ido ko dan ƴaƴanta, wani lokacin mahaifinki yana rufe ido ya aikata abu kamar bai san kowa ba sai kansa”


“Zai dawo da ita, kawai ki bashi lokaci”


“Allah yasa”


“Amin. Abdallah ya zo”


Anty ta share hawayenta tana faɗin.


“Yaushe?”


“Yanzu ya tafi amman yace zai dawo”


“Na manta kin kaiwa Lamido abinci?”


Namra ta miƙe tsaye da sauri dan ita ta manta da shi gaba ɗaya.


Kitchen ta shiga ta haɗa masa fruits da drinks, ta dauƙa nufi waje. Zaune ta same shi cikin ɗakin hannunshi a bakinsa kamar mai nazari.


“Sorry mun cinye abincin rana amman yanzu xan girka maku wani”


Janye hannunsa yayi yana murmushi ya karɓi turen ya aje yana faɗin.


“Kin manta da direban ki saboda sahibin ki ya zo”


Wani kallo tayi masa mai cike da mamaki.


“Kai da Abdallah duk matsayin ku ɗaya a gare ni”


“Ba ɗaya ba ne, Shi ɗan masu kuɗi ne”


“Kai kuma ɗan talakawa”


“Shi ɗan sarauta ne”


“Kai kuma ɗan bayi”


“Yana da matsayi a zuciyarki”


“Kai kuma baka da shi. Na gode”


Tana miƙewa tsaye shi ma ta miƙe yana ƙokarin shan gabanta.


“Am sorry ban yi dan na ɓata ran ki ba, kawai ina ganin ba zan taɓa taka matsayin da Abdallah ya taka a zuciyarki ba ne, daga yau zan sauka a matsayin masoyinki, daga yau ni yayanki ne”


Ya faɗa cikin muryarsa marar daɗi, kallonsa kawai ta yi ta ɗauke kai, ta fice. Tana fitowa ta hango Abdool tsaye tare da Abbah suna magana, yadda Abbah yake watsar haƙora zaka rantse da Allah ba shi ya gama yi ma Hajiya Barau faɗa ba. Har zata wuce Abbah ya kira ta


“Mamana”


Sai ta ƙarasa gurin cikin ladabi.


“Ba ki ga ɗa na bane? Ko baki iya gaisuwa ba”


Ɗan risina tayi ta gaishe da Abdool suna haɗa ido ya kanne mata ido ɗaya ƴana murmushin gefen baki.


“Mun samu ku lafiya”


“Lafiya ƙalau”


“Je ki shirya zaki zaka shi wani guri”


Abbah ya faɗa, har ta buɗe baki ta yi magana sai kuma ta yi shiru ta amsa da to kawai ta nufi part ɗin Anty.


Ya kusan awa ɗaya yana jiranta sannan ta fito cikin ƙaton hijab, a lokacin Lamido na jikin window yana kallonsu, a front seat ta shiga sannan yayi ma motar key suka fita.




AMIRA POV.


Tun tana kuka hawaye na mata zuba har hawaye suka daina kukan kawai take ba hawaye. Gashi tun da suka dawo gida Mahaifinta be ce da ita uffan ba, Ammy xw kawai take bata magana.


Tashi ta yi ta nufi ɗakinta, tana shiga ta maida ƙofa ta rufe. Haƙiƙa ta yi rashin abubuwa da yawa, ta rasa mutuncinta ta rasa martabarta ta rasa wanda take so yanzu me ya rage mata?
Ta ci amanar ƙawarta dole ita taga ba daidai ba, tabbas hassada bata haifar mata da komai ba sai nadama da dana sani. Da ace tun farko bata hassadar Namra da bata yarda ta aikata abunda ya kai ta ga halaka ba, da ace ta zauna da ita da zuciya ɗaya da duk wannan be faru da ita ba.
Yanzu gashi daga ita har Uzair babu wanda yake cikin rayuwar jindaɗi, Allah ya jarrabeta da son Abdool idan ta tuna shi har ji take kamar zuciyarta zata rabe biyu.

Bugar ƙofar ɗakinta Ammy tayi dan tana tsoron kar ƴarta ta saje shiga cikin halin da ta shiga a baya, musamman yanzu da take ganin duniya ta juya mata baya.


“Amira an kira wayarki”


Miƙewa tayi tsaye taje ta buɗe ƙofar da idonta da suka kumbura sosai suka ƴi ja kamar an zuba mata barkono a ciki. Hannu Ammy ta kai ta shafa fuskarta.


“Amira karki sa ranki a damuwa, dan adam be isa ya wuce ƙaddararsa ba, Allah ya rubuto haka zai faru da ke babu yadda zaki yi, dan Allah kar zuciyarki ta sake tunanin guduwa ki bar mu”


“Idan ma na gudu ina zanje? Ko wace mace bata da daraja sai a gurare biyu, gidan iyayenta ko gidan mijinta, guduwa da na yi a wacan karon yasa na gane iyaye suna da muhimmanci sosai a rayuwa, rashin zaman mace a gaban iyayenta yana karyarda darajarta, wannan ne ya hana Abdool da family sa su kalle ni da daraja da ace ina a gidan iyayena xauna wata ƙila da zai iya aurena”


“Wanene Abdool kuma?”


“Shine mutumen da ya hana zuciya sukuni, Allah yayi min jarawata ta nan ne, ina son shi, shi kuma yana son wata”


Komawa ta yi ta zauna, Ammy ta zauna kusa da ita tana kallon ƴarta cike da damuwa. A nan Amira ta faɗawa Ammy komai a zaman da tayi da Abdool da kuma wanda ta yi kamin da haɗu da shi da yadda ta sadaukarda kanta gareshi.


“Kin sadaukarka da kanki gurin da bashi da amfani, kin salwantar da rayuwarki gurin da ba a san darajar rai ba, kin yi sadaukarwar da ba zaki taɓa cin ribarta ba, kin yi kuskuren da ba zaki iya gyarawa ba, kuma ina tsoron kar ɗaya daga cikin ƴaran mutumen nan ya farauci rayuwarki, kin yi kuakuren ba rin zuciyarki ta kamu da son mutum kamar wannan”


“Na sani, amman zuciya bata da laifi babu yadda ta iya, ina son sa Ammy amman shi baya so na, be san hallaci ba”




NAMRA POV..


Ta share hawayen da suka zubo mata cike da tausayin labarin da Abdool ya bata.


“Amman wannan yarinyar ta cancanci komai daga gareka, ya kamata kai ma ka yi mata hallaci, duk wanda ya sadaukarka da ranshi a gareka ya cancanci ko wane irin sakamako daga gareka, da yanzu ta mutu kai ka rayu”


Murmushi yayi yana cigaba da tuƙinsa hankalinsa kwance.


“Ashe ko na cancanci ko wane irin sakamako a daga gareki, dan na daɗe da salwantar da rai na akan ki”


“Kar zuciyarka ta raya maka abunda ba shi bane a Abdallah karka cuci kan ka ka cutar da yarinyar nan”


“Namra baki taɓa tambayar kan ki miyasa Abdool yake son ki ba? Baki taɓa wannan tunanin ba? Ko dan ban taɓa furta miki ina son ki ba?”


“Babu so agaban Namra a yanzu balle har ta yi tunanin dalilin na ka son, kar zuciyarka ta yaudareka a yanzu Abdool ban shiryawa irin wacan rayuwar ba”


“Ashe ke ba mumuna bace Namra, har yanzu kina da sauran cikon imani a zuciyarki tun da baki yarda da ƙaddara ba. Miyasa zuciyarki take ta nuna miki Asim kamar Abdool yake, dan me kike tunanin irin rayuwar da kikayi a gidan Asim irinta zaki yi a gidan Abdool? Mahaifiyata bata da buri a yanzu wanda ya wuce na maganar aurena da ke, ina da ayukan yi da yawa Namra amman na danne su na tako garin nan saboda ke kawai”


Hannu ya kai ya canja fm zuwa wata sannan ya ce


“Wata kila zuciyarki wani take so ba ni ba, na lura Lamido na da matsayi a zuciyarki sama da ni”


Kalamansa da fakin ɗinsa sun rikita ta a lokaci ɗaya, ya faɗa mata abunda yau ma Lamido ya faɗa mata, dan me suke ƙoƙarin saka ta cikin matsalar da bata daɗe da fita ba?


“Miya kawo mu nan?”


A fili ta tambaya tana kallonsa, ba tare daya kalleta ba ya sauke wayar kunnensa yace




“Zaku gaisa da yarinyar ne”


“Nan gidan su Amira ne”


“Ita ma yarinyar sunanta Amira”


Kamin ta ƙara wata magana sai ga Amira ta fito da gudu daga cikin gidan ta nufo motarsu. Buɗe motar Abdool yayi ya fita sai tazo gabansa ta durƙusa ta riƙe ƙafafunsa ta tada kanta sama ta kalleshi. Shi ma kallonta yake kamin ya janye ƙafafunsa ya nuna mata front seat. Bata fahimci mi yake nufi ba, ta shiga ko kuma ta buɗe ta gani, sai dai bata tambayeshi ba ta tashi tsaye ta nufi motar ta buɗe. Ganin Namra yasa ta murmushi da hawaye a lokaci ɗaya.


“Itace?”


“Itace”


Ya amsa mata kai tsaye. Sai ta ƙara faɗaɗa murmiahinta.


“Kayi dacen mata, itama kuma ta yi dacen miji, congratulations Namra Allah ya baki abubuwa da dama, ciki har da wanda na fi so sama da komai, Allah ya haɗa kan ku ya baku zama lafiya”


Uffan Namra bata ce mata ba, har tayi surutunta ta gama ta koma gurin Abdool.


“Haƙiƙa kun dace da junanku, namiji irinka be dace da ko wace irin mace ba sai Namra kamar yadda ita ma bata dace da ko wane miJi ba sai kai, na yarda da ƙaddara haka Allah ya so ta kasance a gareni...”


“Amir...”


Ta ɗaga mishi hannu.


“Na fahimta, na gane ƙaddaratace a haka”


Bata jira abunda zai faɗa ba ta juya ta koma cikin gidansu, hawaye na mata zuba kamar ruwa. Buɗe motar Abdool yayi ya koma ciki ya zauna yana kallon fuskar Namra.


“Itace yarinyar da ta cutar da ke ko?”


“Abunda ta yi min tsakanina da ita ne, kai kuma sadaukarwar da ta maka tsakanin ka da ita ne, ka maida ni gidanmu ban yi tunanin ka ɗauko ni dan ka ɓata min rai ba, na tsani yarinyar nan na tsane ta, idan ma kana son ta ni ina ruwana karka sake kawo ni gurin, idan ma zaka so ka kaje can ka so ta ni karka sake sako ni a matsalar ku”


Shiru yayi yana saurarenta har ta yi masa faɗan ta gama sannan ya tashi motar yana murmushi ya suka nufi hanyar gida. Sarai kalamata suka wanke masa zuciya ɗan ya fahimci inda ta dosa. Yana yin fakin ya buɗe motar ta fita a hasale ta shiga cikin gida.
Wayarsa ya ɗauka ya kira Abbah suka yi magana sannan ya faka motarsa ya fita ya shiga part ɗinsa.


Yayi awa ɗaya a part ɗin Abbah sannan ya fito tare da Abbah ya shiga motarsa ya kama hanya.




KALSOOM POV.


FIVE MONTHS LATER...
Daga ita har su Izza basa da wata matsala a yanzu, tana zaune da yaran lafiya ƙalau ga Hajiya sai nuna musu kulawa take. duk wani rashin kunya na Izza ta watsar, ulfah kan ba a magana daman tun da warke daga jinyar ruwana zafi sai ta ƙara ladabi, dan sosai yanzu suka gane muhimmanci Kalsoom, gashi lokaci-zuwa lokaci takan kira musu mahaifiyarsu su gaisa, ranar weekend kuma Hilal ya kaisu gidan Hajiya. Idan zai dawo Hajiya ta bashi rubutu ya kawo mata na neman ta sauka lafiya. Babu yadda Teema ba tayi ba akan ta dawo gidan amman Hilal da Hajiya suka ƙi, su Izzah kan ko zancenta basa so.


***
Bayan ta ƙare waya da Salma ne ta kalli Hilal dake kwance gefenta yana wasa da wayarsa tace.


“Salma na gaishe ka”


“Ina amsawa, bari naje na ɗauko su izza scul”


Ya faɗa yana unƙurin tashi, kai kawai ta ɗaga masa dan maganar ma wahala take mata ko wayar da take da Salma na ƙarfin hali ne, tun jiya take jin abu amman ta kasa faɗa, duk da ta kan ji irin haka lokaci lokaci amman wannan ya tsananta mata da yawa. Aiko kamar karya tashi daga gurim ta soma jin ana tsikararta, har zaman ya gagareta sai da ta kwanta.


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Shi take ta maimaitawa tana rumtse rumtsen ido. waƴarta na kusa da ita amman ta kasa miƙa hannu ta ɗauka, wani irin juyi take jin duniya na mata, tun tana faɗar Innalillahi a hankali har ta fara yi da ƙarfi tana ta rumtsar ido da buɗewa kamar wacce ta ci bashi. Ko da Hilal ya ɗauko su Ulfah daga makaranta Kalsoom ta jigata, jini har ya fara mata zuba, daman tun safe ya kula da yadda cikin yayi mata ƙasa sosai. Ɗakinsa ya shiga ya ɗauko kayan karɓar haihuwa ya dawo ɗakinta ya shiga ya rufe ƙofar ya shiga bata taimako, because ya san it too late yace zai ɗauke ta suke asibiti a yanzu bayan ga har kan yaro ya fara fitowa😷






ASIM POV.


Tun bayan rasuwar Mama ya daina ganin kam kowa da gashi, gani yake tun da yayi losing mahaifiyarsa a yanzu baya gudun komai, haka zai shigo cikin sokoto ya kwana gurin ogansa, ba zai leƙa ƙanensa ba sai zai tafi sannan ya basu kuɗi mai yawa, babban gida ya siya musu, dan yana ganin kamar su ne family da suka rage masa yanzu. Sai duk lokacin da ya shiga sokoto sai ya binka labarin Namra ace masa tana nan lafiya, har wani ya ɗauka mai aikin bincika masa labarinta, dan a tunaninsa tana nan ɗauke da cikinsa, burinsa kawai ta haifa masa ɗan ko ya ya ɗauke ta dan kawai ya ɗasa mata baƙin ciki. Sati ɗaya da rasuwar Mama aka saka ranar aurensa da Mardiya, yadda yake kashe mata kuɗi sai ka rantse da Allah shi ne yake buga kuɗi, dan yana samun kuɗi sosai a yanzu manyan mutane yake tare da su. Ya faɗa musu baya buƙatar komai dan tun kamin a kai lefe ya saka komai a gidan da zata zauna, kama daga kayan kitchen har zuwa na kwalliya da sutura kai kace ma be mata lefen gaba ɗaya ba sai taje can, har kayan abinci babu abunda be zuba ba, freezer goma ya saka a gidan jo wace cike take da kayan daɗi.
Ranar talata aka fara event an zubar da naira a kamu sosai kasancewar Asim ya bawa kawaye amarya kuɗi sosai, gashi shi ma yaje shi da abokaninsa dan yanzu yayi sabin abokai yayan manya sai kuma masu irin aikinsa, duk wani gaye mai kuɗi da kasani a cikin garin katsina mai ji da kansa sai Asim yayi abota da shi, dan gani yake sune sa'o'insa.

Friday aka yi walima, a instagram Namra take ganin bikin kamun su, tayi mamakin da ya auri Mardiya dan bata manta lokacin da yake yawan maimaita mata cewar shi sai ƴar da ubanta ya fi nata kuɗi zai aure, wata ƙila farin jikinta ne ya jashi hankalinsa ko kuma bayan ya aureta zai ƙara wata.


Tun ranar da aka gyara ɗakin aka saka komai Asim yake kwana a gidan. Wasu abokansa da suka zo daga sokoto da Abuja sai ya kama musu hotel wasu kuma ya sauke su a ɗayan gidansa dake GRA, shi kuma ya koma Light up road inda gidan amaryarsa yake dan kwana. Light up unguwace ta masu kuɗi ko wanne gida ka gani sai ya burge ka, amman duk da haka a layin da Asim yake gidansa ya fi ko wanne gida kyau da tsari, kana ganinsa kasan ba ƙananan kuɗi aka kashe ba gurin gina shi.
Ƙarfe ɗaya da rabi na dare ya shigo gidan, cikin wani irin yanayi marar misaltuwa, yana jinsa a wani matsayi na daban kwatankwacin matsayin da ya riƙa jin kamsa a lokacin da zai auri Namra, freezer da

Please Login or Register in order to submit comment