Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuɗin. Wayarsa ya ɗauka ya aika mata text sannan ya kunna data shi.


HILAL POV


Yana cikin aiki wayarsa tayi ringing. Sai dai be duba mai kiransa ba har sai da ya kai ƙarshen duba marasa lafiyar da yake.
Sai da ya gama da duka katinan da suke gabansa, sannan ya tashi ya nufi office ɗinsa yana duba wayar. Number Dady ya gani Abbah Rashida, yayi mamakin ganin kiran, sai dai be kawo komai a ransa ba dan a tunaninsa, akan maganar shiga kotu ne zai sa ya kira shi tun da monday nan mai zuwa za a shiga.


Sai dai ganin text ɗinsa ya sa gabansa faɗuwa, miyasa yake son ya zo gidansa ya gansa? Duk akan maganar ne ko kuma wani abun daban. Ba tare da shakar komai ba ya shiga office ɗinsa ya cire ƴar samansa ya ɗauki keys ɗinsa ya fice.
Cikin ƴan mintuna ya isa gidan su Rashiida yayi gudu ne a hanya sosai, dan baya son Rafiq ya farka baya kusa. Yana ganin Motar Rashida da ta Dadynta yasan tana cikin gidan.


Be fita cikin motarsa ba har sai da ya kira Dady yace masa gashi ya iso.


“Ka shigo ciki”


Shine reply ɗin da ya masa a wayar cikin tsawa, ko kaɗan Hilal be ɗauki haka a wani abuba dan har gobe yana girmama iyayen Rashida tun da akwai ƴaƴa a tsakaninsu, kuma duk mutumen daya aura maka ƴarsa ya fi gaban ka raina shi ko da kuwa kun rabu da ƴar ne.
Buɗe motar yayi ya fito, yana tuna when last ya shigo gidan nan. Babban falon Dady ya nufa daman ko lokacin da yana surukinsu a can Rashida take sauke shi idan sun zo gidan.


Yana shiga ya samu Dady zaune yana jiran ƙarasowarsa. Momy ma tana zaune daga gefe tana watsa masa harara. Cikin ladabi ya ƙarasa ya zauna saman kujera yana gaishe shi. Dady be amsa ba dan ba gaisuwar ce a gabansa sai kawai ya hau shi da kalamai masu zafi.


“Ma cuce mayaudari, yanzu da kaga ka laƙa mata ciwo shine ka sake ta ko? Ai ni daman nasan sakin da ka yi mata bana Allah ba ne, kaje can kayi yawon ka ka samu cuta kaxo ka laƙa mata”


Ɗaga kai yayi yana kallon Dady maganar ta xo masa a baibai kuma da halshe biyu. Radhida ce ta faɗa musu ko kuma su suka gano haka? Har da shi tace yana ɗauke da cutar ko kuma ita kaɗai?


“Dady zan so Rashida tana nan kamin na yi magana”


“Ta zo ka kunsa mata baƙinciki ko? Ka zo ka ƙaryata ta ka ƙara mata baƙinciki ko? Ɗan iska marar mutumci, wallahi Allah sai ya isar mata”


Wannan karon Momy ce take magana tana wani ɗagowa kamar ta kama Hilal ta dake shi.


“Kuna magana ne a jahilce baku san gaskiyar lamari ba, ya kamata a kira Rashida ayi komai gani ga ta sai a fitar da wanda be da gaskiya”


Dady ya kalli Momy.


“Jeki ki kirata. Wallahi na rantse maka Hilal sai duk abunda na tara ya ƙare amman tun da kayi ma ƴata haka sai na wulaƙanta ka”


Ya ƙarasa yana kallon Hilal, jijiyar kansa har wani tashi take irin na ɓacin rai ɗin nan ya kai maƙura.
Momy ta tashi a hasale ta nufi sashenta. Kai tsaye ɗakin Rashida ta nufa sai da ta soma da buga mata ƙofa amman ta ƙi ta Buɗe har yanzu, sai kawai Momy ta zauna a gurin ta soma mata kuka.


RASHIDA POV


Babu yadda Momy batayi amman Rashida ta ƙi ta buɗe ƙofar har duka ƙanenta suka dawo daga makaranta.
Sai da aka yu salla la'asar sannan ta buɗe shima dan Momy ta zo ta zauna a gurin tana kuka ne. Da sauri Momy ta shiga cikin ɗakin cike da tausayin ƴarta.
Bata yarda ta zauna kusa da ita ba, sai dai space ɗin dake tsakaninsu ba wani mai tsawo bane sosai.


“Hilal ne ko? Shine ya saka min wannan cutar shiyasa ya zaɓi rabuwa da ke”


“Miye amfanin sanin wanda ya sa min wannan cutar, bayan cutar ta riga da ta kamani, babu amfanin ayi ta jayayar abu har a tona asirinsa, duk abunda ya faru da ni, Dady ne ya ja min”


Momy ta kalleta


“Ga Hilal can mum kira a falon Dady ki amman ya ce ba zai yi magana ba sai kina nan”


Gabanta yayi dakan huɗu-huɗu har bata san lokacin data kalli Momy baki sake ba.


“Miyasa kuka kira shi? Me zai muku?”


“Shine silar wannan ciwon na ki Rashida dole na zauna da ke, dan me zai sake ki”


Fashewa tayi da sabon kuka.


“Ni bana son ganinsa dan Allah yayi tafiyarsa”


“Ba zai je ko'ina ba har sai an tabbatar da wannan maganar yau”


Momy ta riƙa hannunta suka fito tare. Ba dan Rashida ɗin ta so ba, sai jan Momy dake janye da hannunta har suka isa falon. A jikin ƙofar Rashida ta tsaya ta risina kanta na ƙasa dan bata son kallon Hilal.
Shi kuma ya tsare ta da ido tausayinta duk ya kama shi.


“Dawo nan ki zauna, babu abunda ya isa yayi miki”


Cewar Dady yana nuna mata kusa da shi. Tasowa tayi ta dawo nan tana shirin zama kukan da take ɓoyewa ya fito fili.


“Yi shiru yanzu ba lokacin kuka ba ne, faɗi maganar ki”


Kasa magana Rashida tayi har sai da Hilal ɗin da kansa ya soma bada labarin abunda ya faru from a to z. Sun gamsu sun kuma samu tabbaci ganin yadda Rashida take ta kuka ta kasa ta kare kanta.


Dady ne ya miƙe tsaye ya soma safa da marwa. Ajiyar xuciya kawai yake saukewa yana maimaita


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Momy kan saka kanta yai cikin hijabi tana kuka. Rashida ma kukan take kamar ta mutu. Dady ya kalli Hilal cikin idonsa na marasa kunyar iyaye ya ce


“Zaka iya tafiya”


“Na gode”


Hilal ya furta sannan ya miƙe tsaye ya fice, jiki a sanyaye.


“Kin cuci kan ki Rashida kin kuma watsar da tarbiyar dana baki yanzu ai kin ci ribar zina sai kije ki auri wanda kuke aikata saɓon tare, uban waye ne ma wannan mutumen?”


Dady ya tambaya a tsawace. A nan Momy ta ɗago kai ta kalleshi cikin ɓacin rai ta ce.


“Duk waya ja mata wannan abun ba kai ba? Tana zamanta lafiya ƙalau da mijinta kace dole sai ta yi aiki, babu irin lallaɓar da yarinyar da mijinta ba su maka ba, amman ka dage akan dole sai tayi aiki, ai ga ribar aikin nan ta kwaso ta kawo maka, shine yanzu zaka taso ka rufe ta masifa ka barta ta ji da abunda yake cikinta ko so kake ta kashe kan ta”


Tashi Rashida tayi ta bar musu falon tana wani irin kuka kamar ta mutu. Momy ma miƙewa tayi tsaye ta fice a hasale tana kuka da bata san ranar tsayawar haweyen ba.


Komawa Dady yayi ya zauna har yanzu xuciyarsa bata gama gamsuwa Rashida ƴarsa tana ɗauke da cutar ba, shi dai ya fi son ayi wani gwajin.
Ajiyar zuciya ya sauke, wani yana tuna wani kalami da wata tayi masa a 1952.




KALSOOM POV


Har yanzu hankalinta ba a kwance yake ba, amman ba kamar da ba, dan yanzu tana da tabbacin Hilal ya yarda da ita, ta kan samu sassaucin hakan idan ta tuna.
Sai dai har yanzu bata cin abincin kirki, sai dai abu mai ruwa ko kuma ruwan kawai.


Tana cikin kitchen ta ji ƙarar tsayawar motarsa, nan da nan ta je aikin da take ta nufi ƙofar falo ta tarboshi.
Yanayinsa ya kararta da ita damuwar mijinta, dan haka bataa buƙatar tambayarsa akwai damuwa ko babu mafi ala kawai ta kwantar masa da hankali sannan ta nemi sanin dalilin damuwar tasa.

Da kanta ta zaunar da mijinta ta ɗauko ruwan sanyi ta siyaya masa a kofi ta kai masa a baki, kaɗan ya sha, ya ɗauke baki, sai ta cire ɗankwalinta ta soma shafe masa gefen fuska.


Hannunta ya riƙe ya jata zuwa ƙirjinsa ya rumgume ta, zuciyarsa cike da tsantsar ƙaunarta.


“Hajiya ta har yanzu bata yarda da ke ba”


Ya faɗa dan ya canja tunaninta izuwa wacan damuwar ta gurin Hajiya.


“Ba lallai ne tayi saurin yarda da ni ba, kuma tana da damar ta zarge ni yadda ranta yake so, zan ɗauki ko wani irin hukumci Hajiya ta yanke matuƙar hakan xai sa ta aminta da ni”


Tana kwance a ƙirjinsa take maganar hawaye na bin fuskarta.


“Hukuncinta ɗaya ne, wai sai na ƙara aure”


Ɗagowa tayi ta kalleshi ta girgiza kai ta fashe da kuka. Ɗan murmushi yayi dan kukanta ya sashi nishaɗi, yana shafa gefen fuskarta ya ce


“Ba zaki yarda mijin ki ya ƙara wata ba ko?”


Kai ta ɗaga masa. Sai ya ce


“To ya zaki yi da Hajiya?”


“Wallahi ban aikata ba Hilal Allah shine shaida na”


“Ai ba nine ban yarda ba, Hajiya ce bata yarda dake ba”


“To a tambaye Rafiq ɗin ai yana magana idan na bashi wani abun zai faɗa”


“Rafiq baya magana yanzu, ya koma wani iri kamar ba shi ba”


Cikin rashin jindaɗi yayi magana, yana ciro wayarsa dake aljihu tana ringing. Saurin picking yayi ganin number Nurse ɗin dake kula da Rafiq.


“Subhanallah okay gani nan zuwa”


Yayi saurin ɗaga Rashida daga jikinsa, ya tashi ya nufi ƙofa hankali tashe. Rashida sai tambayar lafiya take be kula ta ba.


ABDOOL POV.


Sai da dare ya dawo Part ɗin Ummi ɗan ya tabbatar ta dawo a lokacin. Duka falo ya same su zaune suna ta fira. Ummi na ganinsa ta aje lemun fata dake hannunta tana masa kallon mamaki.


“Ni nace fa naga Motar ka Haleema tace min wai ba kai ba ne”


Ya ɗan wara ido yana kallon Haleema, kamin ya zauna a kujarar da Amira take zaune dan three seater ce.


“Ai ba zata faɗa ba, a ɗakin ki na same su suna ta miki taɓe taɓe ita da wannan yarinya”


Ya nuna Amira data tsare shi da ido.


“Wallahi gyara ne Amira take miki, ba wai komai muke miki ba, hba sai ka ce yara”


Ummi bata bi ta kan Haleema ba ta kalli Abdool.


“Ya hanya? Ka ci abinci?”


“Na ci gidan Babana, ku da ban ma tarar da ku ba”


“To ai baka faɗa ka ce za ka zo ba, gashi ma miyar kifi aka yi kuma baka son kifi”


“Ni wallahi wannan zuwan ma be min daɗi ba, ɗan hutu ne na samu ina da zumuɗi zan zo gida shine wai kuma Mai Martaba sai naje zaria ɗaurin aure”


“Ai shine dai-dai kai kenan baka son shiga mutane kamar wani aljani. Me za'a girka maka?”


“Wa zai girka min?”


“Ni”


“Okay to a min wani abu new. Ba wanda aka saba ba”


Tashi Ummi tayi ta nufi ɗakinta tana dariya.


“Kai kam matarka ta shiga uku kullum.ba maimata abinci sai anyi wani abu new”


Shima.dariyar yayi ya tashi ya rufa mata baya yana faɗin


“Lallai kam, idan kam mace bata iya abincin ba zamu samu matsala da ita”


“Ko da kana son ta?”


“Aifa...”


Amira ta bishi da ido, daɗi har cikin rai. Dan tasan indai ɓangaren abincine ba daga baya ba, tun daga kan waɗanda ake yayi har na gargajiya gwargwado ta iya. Ga kuma xama da yayi a kujerar da take zaune abun yayi mata daɗi.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *62*


*1952*


```Cikin rawar jiki ta shigo gidan sai rabon ido take idonta tab da ƙwalla, kana ganinta kasan tana cikin halin damuwa. Bata san inda zata dosa ba tun ba data samu masu gadin suka barta ta shigo cikin gidan, gaba ɗaya a rikice take har bata iya kwantar da hankalinta ta banbanta parts ɗin


“Ke me kike a nan?”


Da sauri ta juyo ta kalle tana ganinsa sak tasan ɗan mai gidan ne, hakan yasa ta risina har ƙasa ta gaisheshi muryarta na rawa. A maimakon ya amsa mata sai kawai ya ƙara haɗe fuska dan ya fahimci irin mutanen ne masu zuwa gurin mahaifinsa a taimaka musu


“Gurin Mai gidan nan na zo, taimako za a min, mahaufiyarmu ce bata da lafiya shine aka rubuto mata magani a asibiti kuma sun ce za a mata aiki, shine aka ce na zo nan za a taimaka mana”


Da kuka ta ƙarasa maganar tana nuna masa takardun asibiti dake hannunta. Karɓar takadardun yayi yana kallon fuskarta da kuma yanayinta, taga komai a rubuce amman saboda mugun nufinsa ya kasa gasgata ta.


“Wata ƙila ma ƙarya kike, haka kuke dan kawai kun ga mahaifina yana taimakawa mutane, kowa sai ya kwaso ƙaryarsa ya kawo ”


“Wallahi ba ƙarya na ke ba, idan baka yarda da ni ba zamu iya zuwa ka duba ta tana nan babbar asibibiti, layin masu ciwon ulcer”


Kallonta yake da kyau, irin kallon da idonsa zata siffanta masa sigar jikinta, yarinya sai dai ba sosai ba, fara ce kyakkyawa mai ruwan fulani, ko kuma na ce buzayen jajaye. Hawunta ya haɗe a bakinsa kana ya ce


“Nawa ne ake buƙata?”


“Dubu ɗari biyu da sittin”


“Tam yanzu kin ga mahaifina baya nan, ya za'ayi”


“Ina zan same shi?”


“Baya nan ta tafi Lagos ganin shugaban ƙasa” (A lokacin Lagos ce fct ba Abuja ba)


“Yaushe zai dawo?”


“Wallahi ban sani ba, amman idan kina so ni zan iya taimaka miki”


“Ina so dan Allah”


“Amman fa sai idan nima za ki taimaka min”


Kallon rashin fahimta tayi masa dan a iya ganinta da tunaninta baya buƙatar wani taimako daga gareta.


“Me zan taimaka maka?”


“Idan har kina son na baki kuɗi to ki iskoni a ɗayan gidan baban mu da yake nan kwalkwaɗa, zan ninka miki fiye da abunda kike so ba”


Sak tasan abunda yake nufi, kuma ta fahimci inda kalamansa suka dosa, ita kuma bata koyi wannan tarbiyar ba, kuma bata ji zata iya sadaukarda mutuncinta ba. Sai kawai ta kaɗe jikinta ta tashi tsaye.


“Ni ba ƴar iska ba ce, dan kawai na zo neman abu gurin mahaifiya ba shi yake nuna ni ƴar iska bace, rashi mahaifi ne, kuma duka dangi babu mai shi, idan har zaka taimaka min dan Allah ka taimaka min”


“Daman ƙarya kike ciwon mahaufiyarki be da me ki, da kin aikata komai akan ta. Wuce ki ba mu guri”


Da kuka yarinyar ta bar gidan. Shi kuma ya juya ya shiga ƴar marsandin mahaifinsa ya fita daga gidan. Kai tsaye ɗayan gidan mahaifinsa ya nufa, dake can bayan babban gidansu, daman ya saba a duk lokacin da mahaifinsa baya nan a can yake tarewa yana sharholiyarsa da abokansa wani lokacin har da mata, abu ɗaya ne baya yi shine shaye-shaye.


Bayan kamar sa'a ɗaya da isarsa gidan sai ga yarinyar ɗa zu ta dawo, a nan ma sai da ta nemi iso suka zo suka faɗa masa sannan suka bata dama sannan ta shiga.
Har cikin faɗar da yake zaune ta isa ta zube masa a ƙasa tana kuka.


“Na roƙe ka, na haɗa ka da girman Allah ka taimaka min mahaifiyata zata iya rasa rayuwarta daga yanzu har zuwa wani lokaci inji likita, saboda ulcer ta taɓa hanjinta har ya lalace”


“Idan kina son ran mahaifiyarki ai sai ki bada na ki rai, ni bana da wani taimako da zan miki wanda ya wuce wannan, idan kin san riƙona ne kawai ya kawo ki to ƙara ma ki tashi ki koma kar dare yayi miki”


Ɗaga kai tayi tana kallon idonsa, rashin imanin dake zuciyarsa take hangowa. Ta karanci tantiranci da ke cikin idonsa lallai idan har bata shirya siyar da mutuncinta to ko mahaifiyarta zata iya rasa ranta bayan kuma ita kaɗai ce ta rage mata a duniya. Hkan yasa ta yarda ta amince tana ji tana gani ya keta mata haddi, abunda bata taɓa kawo ma zuciyarta ba, cewar zata bada budurcinta ga wani wanda ba halalinta ba.
Wani tsabar zalumcin kuma sai da ya gama amfani da ita sannan ya ƙirga rabin kuɗin ya bata wai shi kawai suka rage masa, da tayi maganar har da zaginta yana faɗin daman ai buzaye kowa yasan ƴan iska ne. Da kuka ta bar gida tana mai jin zafin keta mata haɗi da yayi. Shi kuma ya kwanta a ɗakin zuciyarsa cike da nishaɗi, yana jindaɗin abunda ya aikata wanda a gareshu ba sabon abu ba ne.


bachinsa ya kwasa a gurin har sai da ya hantse, sannan ya tashi, yayi salla, sai ya aika mai musu aiki ya siyo musu abincin. yana cikin cin abincin sai ga yarinyar ta dawo idanuwanta a kumbure, wannan karon bata sha wahala a gurin shiga gidan ba ganin ɗazu yace a bar ta ta shiga. A falon ta same shi yana cin abincin hankali kwance. Kuɗinsa ta aje masa tana kuka.


“Ba ayi mata aikin ba saboda rai yayi halinsa, ga kuɗinka bana buƙatar ganin su ko amfani da su, dan amfaninsu a gare ni ya ƙare. Ka kita min haddi akan abinda be wuce ka bani sadaka ba, saboda kawai na zo nema gun ka, to ka rubuta ka aje ko ba daɗe ko ba jima, sai an yima ƴarka abunda ka yi min, sai ka ɗanɗana idan da daɗi, sai Allah ya ninka maka baƙincikin raina sau biyu, wata rana sai ka wayi gari kana nadamar abinda ka aikata min, na roƙi Allah ya isar min ya nuna maka a kan ƴar cikin ka...”


Bata gama kalamin ba ya ɗauki abinci ya jefeta da shi, ya hau ta ta shuri yana zaginta. Shi kansa ya ji babu daɗi a kalaman da tayi masa, duk da ya ba, amman duk waɗanda yake da su, sune suke kawo kansu ko ya neme su kusan dai za'ace karuwai ne, wannan ce kawai ya keta ma haddi da gangan...```


Ajiyar zuciya Dady ya sauke, hawaye suka silalo daga idonsa, sai jan majiya yake. Yanzu kan ya tabbatar da alƙawarin Allah gaskiya ne, kuma kowa yayi da ƴar wani sai an yi da tashi, sai dai nashi sakamakon mai zafi ne, tun da na ƴarsa har da cutar kanjamau, kuma ta keta mutuncin aurenta, wannan babban abun baƙinciki ma ita ta ba da kanta ba wai keta mata haddi aka yi ba, dan baya tunanin hakan da keta haddin ne da tuni ta faɗa.


Miƙewa yayi tsaye zuciyarsa na masa wani irin mugun zafi ya shiga ɗakinsa hawaye na cigaba da masa zuba. Nadama ce tsantsarta a zuciyarsa sai yanzu yake baƙincikin abunda ya aikatawa ƴar mutane, lallai zina bashi ce! Dole wata rana ka biya ko a biya maka....


RASHIDA POV.


Ɗakinta ta koma ta zauna tana rare kukan baƙinciki daya cika mata zuciya. Ji take kamar ta rataye kanta ta huta, ta san duk wanda yaji tana ɗauke da wannan cutar ba zai zauna da ita ba, ga kuma Hilal da yanzu take da tabbacin ta rasa shi kenan har a bada. Iyayenta ma a yanzu ta san ta rasa su dan ta san zamanta da nasu dole zai banbanta, dole a yanzu duniya ta san abunda ta aikata, rayuwar da take gudun shiga ta san a yanzu dole ita zata yi.


Duk kukan da take Momy na tsaye jikin ƙofar ɗakin tana kallonta tare da rera nata kukan. Haƙiƙa tana tausayin ƴarta sai dai babu yadda ta iya tun da ita ta jawa kanta.


“Za muje mu ƙara gwaji, so that mu tabbatar idan har da gaske kina ɗauke da cutar”


Ɗagowa kawai ta yi ta kalli Momy da idanuwanta da suke ta zubar da ƙwalla har ɓata gani sosai da su. Sai kuma ta maida dubanta gurin hannayenta tana duba jikinta kanta take kaɗawa tana jinjina lamarin ubangijinta dan shi kaɗai ya isa yayi mata haka, sauyin rayuwa a take....




HILAL POV.


A firgice ya isa asibitin dan tun bayan abunda Nurse ɗin ta faɗa masa sai hankalinsa ya tashi sosai.
Ko parking ɗin kirki be yi ba ya buɗe motar ya fito hankali tashe har yana gudu. Likitan yara uku ya tararar akan Rafiq suna ƙoƙarin ceto numfashinsa, amman ina rai yayi halinsa. Ƙasarawa yayi a rikice yana girgiza Rafiq, tare da kiran sunansa. Da sauri ɗayan likitan ya riƙe shi yayi baya da shi yana masa magana.


“Haba Doc ya kake abu kamaɗ ba likita ba, mutuwa wace iri ce ba mu gani ba? Ka yi imani da kaddara mana, komai ka yi ba zai sai Allah ya fasa abunda yayi niya ba, dan kasan ba'ayi Rafiq dan kai ba, kamar yadda ba'ayi Rafiq dan ka ba”


Lumshe ido Doc yayi ya dantse bakinsa, yana ta ganin Rafiq yana masa yawo a ƙwaƙwalwa, ƴana buɗe idon sai hawaye. A hankali ya furta Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Sannan ya juya ya fita daga ɗakin. Rufa masa baya likitoci suka yi suna tausasa masa zuciyarsa.
Ba laifi ya samu gwarin gwuiwa daga ƴan'uwnsa likito wanda hakan ya hana shi bayyana damuwar mutuwar ɗansa a fili, duk da yasan abunda da zai daɗe a zuciyarsa yana masa yawo kasancewar ƙananan yara suna da shiga rai.
Da kansa ya kira Hajiyarsa ya faɗa mata, kamin ya kira wasu daga cikin ƴan'uwansa da kuma ɓangaren Rashida.
Sannan abokansa suka saka shi a motarsu , shi kuma ya shiga a ɗayar motar abokinsa suka nufo gida dashi. Tun da Kalsoom taji ƙarar buɗe gate ɗin gabanta yayi mummunan faɗuwa, tana jin tsayawar mota ba ɗaya bugun zuciyarta ya ƙaru. Balle kuma da taga Hilal ya shigo idonsa a rine.


“Ya rasu ko?”


Kai kawai ya ɗaga mata ya zauna saman kujera. Ita kuma ta ɗora hannu saman kai ta fashe da kuka ta durƙushe a gurin. Yana unƙurawa zai tashi Hajiya ta turo ƙofar falon ta shigo tana kuka, tare da wasu sisters na shi.
Da sauri Hilal ya tare ta yana faɗin ta daina kuka.


“Hajiya be kamata ki masa kuka ba, haka Allah ya kaddara babu yadda muka iya”


Hajiya bata daina kukan ba ta nuna Kalsoom ta ce


“Idan baka saki wannan yarinyar ba ban yafe maka ba Hilal, kuma sai dai ka nemi wata uwar ba ni ba...!”


A gigice ya kalli Kalsoom sai kuma ya kallon bakin Hajiya da yayi wannan furucin. Kalsoom ma kallon Hajiya take hawaye na bin fuskarta. Rashida ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana kuka.


“Ina ɗa na? Ka hana ni ganinsa lokacin da yake da rai yanzu na zo na ga gawarsa ina ɗa na yake?”


Rumtse ido Hilal yayi ya zauna saman kujera ya dafe kansa ya dantse bakinsa gam.




NAMRA POV.


Ana kiran salla magariba suka sauka babbar tashar kaduna, da sauri passengers suke fita wasu saboda suna nesa ganin dare ya soma yi wasu kuma dan su samu bin jam'in salla magariba. Ita ce kawai ta fito daga motar kamar marar kuzari tana tafiya tana kallon tashar da bata taɓa mafarkin zuwa ba. Tana fita daga gurin da motoci suke sai masu Nepep irin wadanɗa suke tsayawa a gefen tashar suna neman masu shiga gari.


“Malama ina za kije?”


Ɗaya daga cikin matasan dake tsaye a gurin masu Napep ya tambaya yana shafe ruwan dake alwala dake fuskarsa. Matashin saurayi ne mai jini a jika fari kyakkyawa da shi, a zahiri akwai natsuwa da sanin ya kamata a shimfiɗe a fuskarsa. Ga sajensa gwanin sha'awa.


“Cikin gari...”


Ta faɗa da muryarta mai kamar zata yi kuka.


“Okay, shiga muje amman zan tsaya a hanya na samu jam'i”


“Ba matsala”


Ya jefar ledar pure water dake hannunsa ya shiga napep ɗin tasa mai kamar sabuwa ya kunna, ita kuma sai ta shiga gidan baya ta zauna tana ta tunanin inda zata ce ya kai ta. Har ya kunna Napep ɗin ya fara tuƙi be tambaye a ina za'a kai ta cikin garin ba, dan shi dai danuwarasa a yanzu ya samu jam'i.
Ba suyi tafiya mai nisa ba ya faka a gafen titi, ya fita yana faɗin


“Bari na yi salla a masalacin”


Kai ta ɗaga masa tana kallon mutane dake ta haɗa haɗa a kan babban titin. Tunanin unguwar da zata ce masa ya kai ta take, amman har yayi salla ya dawo bata samu unguwa ɗaya da zata ce ya kai ta, dan bata san garin kaduna balle yace ga inda zai kaita.


Sai da yayi mata sallama sannan ya shiga Napep ɗin ya tasheta ya hau titi. Can ya ciro wani ƙyale ya kare ƙasar salla dake goshinsa ya juyo kaɗan ya kalli Namra.


“Wace Unguwa za muje?”


“Uh...m ca..an can..gur.in gra”


Ta faɗin hakan ne dan bata san inda zata ce masa ba, amman ta san ko wane gari akwai gra.


“Okay GRA ta gurin ina?”


“Ta gurin manyan gidajen nan”


Daga nan wata kalma bata sake shiga tsakaninsu

Please Login or Register in order to submit comment