Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nesa da gurin tasa ya sauke ta ta sallame shi, sannan ta taka da ƙafa ta ƙarasa cikin gidan.
Sai da ta buɗe motarta ta saka jakarta sannan ta, ta shiga cikin gidan, bakinta ƙumshe da sallama. Da far'ah Momy ta amsa mata.


“Ma'aikatan kuɗi yau a gidan na mu?”


“Wallahi kuwa, yau kin san babu aiki”


“Yau kuma har da hijabi! Aiko kin ga yadda ya fitar da ke, mashallah”


Zaunawa tayi tana murmushi.


“Momy kenan, shi saka Hijabi har wani abun ne?”


“Wani abun ne mana, shiyasa abokiyar zaman ki take burgeni saboda ta san kanta sosai, duk inda zaka ganta da hijabi zaka ganta, kin ga irin wannan matar? Da wahala wani namiji yayi mata maganar banza, Hijabi ne abu ne mai muhimmanci Rashida tun da har ki ga musulunci ya koyar da mu saka shi ai kinsan yana da kyau”


Ta ɗanyi murmushi, wanda be kai ciki ba murmushin rashin jindaɗin maganar da Momy tayi na Kalsoom.


“Nikan bana burge ki ko Momy?”


“Ba haka nake nufi ba, yadda ɗabi'unta da halayenta yake haka na so naki ya kasance, amman sai ki ari wata rayuwar ta daban kika ratayawa kanki, kika ɗauki wani hali wanda ban san inda kika samo shi ba kika laƙabawa kan ki”


“Uhmm Momy ban yi breakfast, yunwa nake ji sosai”


Ta faɗa da nufin kawar da wacan maganar ta Momy, shiyasa bata cikin son zuwa gidan ba, duk lokacin da tazo sai ance tayi wani abu ba dai-dai ba, yanzu ma abun ya wuce guri har abokiyar zamanta Momy take yabo, ita kam bata taɓa ganin uwar dake yabon kishiyar ɗiyarta ba sai nata uwar.
6ana ɗaya daga cikin dalilin dayasa Kalsoom ta zame mata ƙashin wuya, amman wannan matsalar da take ciki yasa ta ma manta da ita sai yanzu da Momy take tsokaro mata tsatsar ƙiyayyar da tayi mata katutu a zuciya.


A gidan da wuni, duk irin tambayar da Momy tayi mata na barin motar ta da tayi taje wani gurin, ƙin faɗar inda taje tayi, balle ma har ta faɗawa Momy dalilin zuwan nata.
Tasan bayan sallah magariba Hilal baya gida, dan a masallaci yake sallah magariba kuma baya shigowa gida sai anyi isha'i, hakan yasa ta dawo gida a lokacin, dan bata son ta dawo lokacin da yake nan.


Ta jidaɗin rashin ganin ɗaya daga cikin motocinsa hakan ya tabbatar mata da baya ma unguwar kenan, sai da ta cire hijabin ta bar a mota sannan ta fito, ta nufi hanyar falo.
Ɗora ƙafarta da zatayi sai gabanta ya faɗi, maido ƙafar tayi tayi baya-baya tana sauraren bugun zuciyarta.
Ta kusan minti biyar a haka, sannan ta kai hannu ta tura ƙofar ta shiga, bata ga alamun motsin kowa a gidan ba, hakan ya tabbatar mata da dukansu basa nan. Sai da ta leƙa ɗakin yaranta, taga babu kowa sannan ta nufi ɗakinta.
Jakarta ta fara ajewa tana sauke gajiya, sannan ta cire tufafin jikinta, ta shiga banɗaki tayi wanka, ta fito.
Dressing mirror ta nufa, ta shafa mai da turare sannan ta zauna tana nazarin duniyarta, idan har ta aikata abunda take da niya, to asirinta ya rufu, sai ɗayan kuma tana tunanin makomarta, akan abunda take ƙoƙarin aikatawa. Wani dogon numfashi taja ta sauke. Sam bata lura da takardun dake saman gadonta ba har sai da ta unƙura zata tashi.


Gabanta ya faɗi, a iya tunaninta bata san ta bar komai a saman gadonta da zata fita ba, sannan yanayin takardar be yi kama da documment ko file ba. Matsawa tayi kusa da gando ta kai hannu cikinn rawar jiki ta ɗauki takardaun.


Tana fara karantawa ta ji kamar an mata shocking, wani abu yazo mata tsam tun daga saman kanta har zuwa cikin ƙafafunta, bata ankaro da duniyar da take ciki ba, har sai da jini ya fara bin ƙafafunta.




NAMRA POV.


Sai da yamma sosai ƴan gidan suka dawo, abun walima ɗaya Inna ta bawa Mardiya tace su raba ita da Namra. A tare suka ci, lemun da yake ciki Namra tacw ba zata sha, ta bar ma Mardiya.


Bayan sallah magariba, ɗaya daga cikin matan gidan ta kawo ma, Namra tuwon masara da miyar ganye, haka Namra tayi ta tura abincin ba dan tana so ba, abun ka da wanda be saba ba.
Kaɗan kawai ta ci ta bar ma ƙannen Mardiya saura, ta wanke hannunta, sai ta koma kusa da Maman Mardiya ta zauna tana labarta mata zasu koma BQ, Inna tayi mata murna sosai, har tana cewa zata ƙara mata da wani abun.
A daren sun sha hira, ita da Inna sai labarin rayuwa take bata, irin gwargwarmayar da ta sha kamin ta kawo yanzu, da kuma labarin ƙurciyarsu ta ƙauye, wani abun na dariya wani na ban haushi, wani kuma na ɗaukar darasi.


Sai kusan goman dare Namra ta kwanta, har kuma lokacin Mardiya bata gidan, kuma sam hankalin Inna be tashi ba, bata ma nuna damuwarta akan rashin sanin inda Ƴarta take ba. Sai kusan shabiyun dare ta dawo gidan, tana ta wani ƙunshen-ƙunshe, suna sun-sun ita da Inna a tunaninsu Namra tayi bachi.


Sai kawai ta warware Mardiya da ta zo da shi. Har suka ci suka cinye Namra bata motsa ba balle ta nuna musu idonta ba, sun tana bachin ƙarya har na gasken yayi gaba da ita.

*WASHE GARI*


Inna ta bada aka siyo musu koko da ƙosai, sai ta siyo ma Namra waina, dan ta lura sam bata son koko, tun farkon kwananta gidan. Sai da ta ci ta ƙoshi, sannan ta nufi akwatin Mardiya dan ɗauko kuɗinta, da zimmar ta siya ma Asim abinci ta kai musu.
Bata ga jakar a inda ta aje ta ba, sai ta sa hannunta tana ta lalabawa, wayan bata ji komai ba, wale akwatin tayi tana duba sama-sama ko zata ganta, amman bata ganta ba.


Zata canye hannunta kenan sai taji abu ya zargi hannunta kamar an soke ta da allura, da sauri ta janye hannun tana raki.


“Waisss Ina jakar nan ta shiga ne”


Sai ta soma ɗaga tufafin ɗaya bayan ɗaya, tana dubata, ganin tayi kamar be dace ta ya mutsa mata kaya ba, saboda neman jaka wata ƙila ma ta ɓoye mata a wani gurin, ƙara kawai ta tambaye ta.
Har zata mai da kayan sai abu ya faɗo daga cikin ɗankwalin atamfar Mardiya, dubawar da Namra zata yi sai ta ga wayarta, da sauri ta kai hannu ta ɗauka.
No it can't be her phone, ta duba wayar gaba da baya.


“Wayata ce wannan this is my phone, how... ”


Sai kuma tayi shiru, tana nazari. Da sauri ta barkata kayan ta kai har ƙasan akwati, sai ga sarƙarta, da wasu manyan ƴan kunne nata, da agogon ta. Da sauri ta ɗauki ta miƙe tsaye tana mamaki.
Cikin wani irin bachin rai ta fito waje ta isa har inda Mardiya take zaune suka fira da Matan gida, ta ɗauke ta mari. Namra bata damu da matan da suke cikin gidan ba haka ta shararawa mardiya mari har huɗu tana hawaye.


*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

_Write by_
*Khadeeja Candy*


*PAGE - 37*


NOT EDITED ⚠


Sare saren jini ne ya fara zubar mata, amman hankalinta gaba ɗaya ya tattara ya koma gurin takardar.


‘Ga result ɗin da kike nema nan, da kuma wanda Doc Sabo ya bani jiya, ranar Monday, na biyun zai fito, idan har baki tsallake ba, za'a sake miki na uku, bana son kowa ya san sirrin mu, na yi alƙawarin rufa miki asiri saboda ƴaƴanmu, amman ba zan zauna dake ba Rashida idan har hakan ya tabbata, kar ki kuskura canja komai kar kiyi unƙurin yin komai, har sai gaskiya ta bayyana kuma na baki damar zuwa gida idan kina da buƙata, bana son wata alaƙa ta sake shiga tsakanin ki da su Ezzah a yanzu’


Taya zai mata katanga da yaranta? Taya asirinta zai tono tun yanzu, ba zata iya jure rashin Hilal ba ta shirya sadaukar da rayuwarta a gareshi, tana son mijinta, miyasa zata farka daga bachi tun yanzu? Baya mafarkinta be ƙare ba?


Wani irin ihu ta saka ta silale a gurin.




NAMRA POV.


Faɗuwa Mardiya tayi ƙasa daga kan turmin da take zaune, tana kallon Namra da mugun razana a fuskarta.
Gaba ɗaya matan gida sai hankalinsu ya tattara ya ya koma kan Mardiya da Namra. Babu wanda yace uffan har Inna da take Mahaifiyar Mardiya, dan tasan Namra ba zata mari Mari Mardiya haka kawai kawai ba.


“Ashe baki da zuciyar Imani? Duk zaman amanar da nake dake Zagon ƙasa kike min? Kina ganin yadda na yi ta neman wayar nan, ashe tana gareki kika ƙi faɗa min? Taya kika ɗauki sarƙa ta da ƴan kunne na? Faɗa!”


Namra ta faɗa a tsawace tana mai jin kamar ta kama Mardiya ta ɓanlata gida-gida, ta watsar. A nan matan gidan kowa ya fara sun-sun da kai suna kallon-kallon ma junansu, daman sun daɗe suna jiran zuwan wannan ranar, tun da sun san Mardiya ta na ɗan ɗauke-ɗauke kuma sun san ba zata rasa yi ma Namra ba, tun da halinta ne.


Murje ido Mardiya tayi, ta mayarda hawayen da suke son zuba mata, wani dakewar zuciya ta samu kanta da ita, na mayarda ƙaryarta ta zama gaskiya.


“Namra ya kamata ace kina bincike kamin ki aikata abu, kuɗin ki na canja musu muhalline, sannan ni ban ɗaukar ka miki waya ba balle kuma sarƙa, sai idan wani sherin zaki min”


Tassss Namra ta sake marinta ta turata can baya har ta faɗi.


“Munafuna mai siffar ƴan wuta, nayi farinciki da Allah ya nuna min ko wacece ke tun a yanzu, na yi nadamar sanin ki a rayuwarta, baki da imani ba ki da tausayi Mardiya, duk irin halin da nake ciki sai da kika ƙafe zuciya kika min sata? Ɗaukar haƙƙin wani? kuma ki jira sakamakon ki”


Wannan karon Mardiya hawaye take. Mahaifiyarta ta matso tana hantarar Namra, magangannunta sun ɓata mata rai sosai, tana ganin dan me Namra zata musu haka.


“Amma ke kam ba ƴa bace sam baki da mutunci, ai komai Mardiya tayi miki ya kamata ace kin taushe zuciyarki kin ɗaga mata ƙafa, balle ma bayi ba dan ban haifi ɓarauniya ba”


Namra ta kalleta da jajayen idanuwanta, ta yarfe ta da hannu.


“Kin ji kunya Wallahi, tirr da uwa irin ki mai ɗaurewa ƴarta gindi tana abunda take so, uwar da ƴarta zata sa ƙafa ta fita ba zata dawo sai taga dama kuma hankalin ki kwance, sai murna kike tana kawo miki abunda daɗi, kina da tabbacin inda take zuwa? Idan har kin san hallaci ba zaki bar ƴarki ta ta ɗauki abu na ba, ko da kuwa yana zuba a ƙasa”


Maman Mardiyar ta jinjina kai


“Lallai ɗan adam butulu, lallai mun yi kuskure yi miki masauki min yi kuskuren yarda dake, a nan da kika yi gobara babu uban da yayi miki masauki sai mu, mu baki ci mu baki sha amman shine zaki watsa mana ƙasa a ido ko tafiyar yawon asibitin nan duk da Mardiya akayi shi, amman ki rasa abunda zaki saka mata da shi sai sata”


“Kune kukeyi kuskure, ni nadamar sanin da na yi mu nake, in mamakin bushewar zuciya irin na ƴarki, na yarda da ita ace ita macuciya ce”


Hawaye take kamar an buɗa fonfo, sai ta shiga ɗakin ta kwaso kayanta ta fito da su waje, sannan ta sake komawa ta ɗauke komai nata a ɗakin ta fito dashi waje, sai a sannan matan gidan suka fara saka baki a maganar, suna bata haƙuri tare da Mahaifiyar Mardiya.


“Wallahi ba zata sake kwana a gidan nan ba, indai ƴar halak ce ko ƙofar gidan nan karki sake bi, shi kenan dan anga yarinya bata magana sai a riƙa cin amanarna kowa ya kwaso shararsa sai ya zube akanta, to ta Allah ba taku ba Wallahi, Mardiya nan gani nan bari kashe di uku lahaula bakwai”


Namra ta nuna ta yatsa.


“Karki soma wulaƙanta ni akan wannan gidan, nima rayuwa ce ta canja min da ko a hanya kika haɗu da ni ba ki isa ki faɗa min magana mai ɗaci ba, kuma ni ƴar halak ce zan tabbatar miki da hakan ”


“To mu zuba mu gani, ai mu kujera ne, muna nan zaune zaki dawo”


Namra bata sake ce mata komai ba, uffan ba saboda baƙinciki, da taimakon yaran gidan ta kwashe ƴan tsomakaranta ta kai BQ ɗin gidan ta , sai ta zauna a balcony ɗin gidan ta tsurawar main house ɗin gidan ido, tana hawaye.


Miyasa Mardiya zata mata haka bayan ta yarda da ita? Miyasa duk wanda ta yarda da shi sai ya dawo yana mata Zagon Ƙasa? Ji take kamar ace akwai wani a kusa da ita ta faɗa masa matsalarta ta labarta masa damuwarta, ta faɗa masa abunda Mardiya tayi mata ko zata samu sassauci a zuciyarta.
Tashi tayi ta ɗauko wayarta, ta riƙe a hannun tana juyata, itace last kyautar da Anty Amarya tayi mata, jin son wayar take ya shige ya, lallai tana buƙartar mahaifiyarta a kusa da ita.


Ƙoƙarin kunna wayar take amman abun ya gagara, ta danna power bottom ɗin amman wayar taƙi ta tashi, sai ta juyar da gefenta da bayan ta tta duba ko ina, bata ga wani matsalar ba, amman wayar taƙi ta tashi.
Riƙe wayar tayi tana ta kallonta, kamin ta saka ta ajaka, ta tashi ta canja Hijabinta ta fito harabar gidan. Yau kam sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta samu Napep, kai tsaye tace ya kai ta asibiti.


Lokacin data shiga asibitin ta yi ta ƙoƙarin ta ɓoye damuwarta, amman abun ya ci tura, saboda baƙin cikin abun da Mardiya tayi mata ya tsaya mata a rai.
Ko da ta shiga ɗakin ta tararda likita na duba Asim, yana wasu ƴan rubuce-rubuce, bayan ya gama ya miƙa mata takardar.


“A siyo wannan maganin anjima za a bashi”


Hannu kawai tasa ta karɓa tana kallon likitan har ya fice, sannan ta zauna kusa da Asim ta ɗora kanta saman kafaɗarsa, ta fara hawaye.


“Miya faru?”


Kuka ta fara rarewa a hankali.


“I just need someone to tell everything will be okay”


Zungurarta yayi da kafaɗarsa ta ɗaga daga saman ƙafaɗar tana kallonsa, shi kuma ya wani ɓata fuska.


“Namra miyasa kike abu kamar wata ƙaramar yarinya, ya kamata ace kin san kin girma fa amman sai ki riƙa abu kamar wata ƙaramar yarinya, haba Namra baki ga halin da nake ciki ba, yanzu fa wani maganin ne likita ya rubuta min, ni wannan zaman asibitin ban san ranar da zai ƙare ba, da nasan wannan ƙaddarar zata same ni da ban je ɗauko motar nan ba”


Furucin da Asim yayi a yanzu, sai ya ninka ɓacin rai tazo da shi, tayi tunani zai barta ta faɗa masa damuwarta ne har ya rarrashe ta, amman sai ya ƙara mata wani.

“Miyasa kowa baya fahimtar damuwata, miyasa kowa baya jin abunda nake ji? Miyasa ba a ganin ƙoƙarina? Be kamata ka biye Mama ba, be kamata ace kana irin wannan furucin ba”


“Be kamata ba? To idan ban biye mata ba wa zan biyewa? Ai gaskiya take faɗa, komai ƙaddara ne amman kuma yana da sanadi, nan gaba idan ba bara ba me kike tunanin zamu koma yi? Tun ana baka rance wata rana ai hana ka za'ayi”


Kallonsa kawai take, tana mamakin kalamansa, taya Asim.ya juya ya koma ba shi ba? A yau ita Asim yake kallon tsabar idonta ya faɗa mata irin wannan maganar?
Turo ƙofar da Mama tayi ta shigo ne yasa tayi saurin share hawayenta, ta sanda kai ƙasa, zuciyarta na mugun ƙona.


“Ga waya mamanki ta kira”


Hannu ta kai ta karɓa, sai ta tashi ta bar ɗakin da saurin saboda kukan dake son cin ƙarfinta.
Mama ta bita da wani kallo.


“Me kuma aka mata?”


“Oho kukan data saba ne ta zo ta min”


“Hmmm wannan matar ita da iyayenta ba son ka suke ba, duk ta bugo wayar nan ƴarta take kira,ƴar wayar kiran ma ta kasa ta siya mata, ni wallahi ban san me suke nufi da kai, ni Wallahi da zaka bi ta nawa da ka saki yarinyar ka huta ma kan ka”


“Mama idan na sake ta a yanzu wace mace ce zata zauna da ni a haka? Bana da kuɗin auren wata, sannan kina ganin halin da nake ciki, ai ƙara ma na zauna da ita duk wahalar da zamu sha mu shata tare, komai zai ci ni sai ya ci ƴarsu”


“Hmmm Allah ya kyauta, amman wannan sun nuna maka ƙiyayyah zallarta, Allah dai ya azurta ka ya baka lafiya”


“Amin”


Ya amsa fuska a haɗe kamar ance iyayen Namra suna gurin. Lokacin da Namra ta fita, sai tayi can gefe nesa da inda masu jinya suke shinfiɗa dan shan iska, sannan ta riƙe wayar tana kuka. Sai ga kiran Anty Amarya ya shigo, cikin sauri ta ɗauka ta kara a kunne, tana cigaba da kuka.


“Lafiya Namra? Miyasa ki?”


“Ma....Ma...”


Yau kam da Mama ta kira Anty Amarya, sunan da be taɓa zuwa a bakinta ba tun tashinta, saboda sabo da yadda kowa ke kiranta da Anty Amarya.


Anty Amarya jin kukan ƴarta take har cikin ranta, bata san abunda yasa Namra kuka ba, sai kawai ita ta fashe da kuka tana dafe zuciyarta.


“Namra faɗa min minene? Miye damuwarki ƴata faɗa min? Indai kuɗi ne na turo miki 300,000k a account tun jiya, ko ba za su isa ba na ƙaro miki?”


“Mama ina son ganin ki, i miss you”


“Okay ki faɗa ma mijin ki idan ya bar ki zan turo direba ya ɗauko ki kin ji? Akwai wani abun ne? Jikinsa dai ƙalau ko?”


“Ya..ji sauƙi”


Ta amsa da in'innar kuka.


“Namra ki kwantar da hankalin ki kinji? Komai zai wuce? Rayuwa bata tabbatuwa haka nan dole ne za a jarraba bawa”


“To Anty na gode”


“Ki sayi waya ki saka layin ki, ki kira ni kin ji”


“Tau”


Ta kashe wayar, sai ta duƙa a gurin ta riƙa rusa kuka kamar wacca akayi ma mutuwa. Ko da ta tashi har hijabinta ya ɓace da hawaye, sai ta cire ɗankwalinta ta ɗora saman hijabinta, ta koma ward ɗin.


HILAL POV.


Tun bayan fitar Rashida daya gama shirya ma yaransa abun kari, sai ya ɗauko tsohon result ɗin ya ɗora a saman gadon Rashida tare da takardar rubutun da yayi mata. Sannan ya koma yayi wanka ya kwashi yaran suka wuni gidan Hajiyarsa, tayi farinciki da murna sosai, sai da suka yi sallah isha'i sannan yace ma Kalsoom ta tashi tayi shirin zuwa gida. Ita kuma sai ta riƙa kiran yaran da zimmar su zo suje gida sai ya riƙe mata hannu ganin babu kowa falon.


“Ba da su zamu je ba”


“Amman....”


“Don't talk gobe da yamma direban hajiya zai mai da su gida, suna jindaɗin zaman nan let them enjoy themselves”


“Amman suna zuwa islamiya da safe fa”


“Just for one day, please a daga musu kafa mana, yau bana son jin muryar yaran nan a gida”


“Saboda me? Wai Doc miyake damun ka?”


Ya kwanto da kansa saman jikinta, kamar wani ƙaramin yaro.


“Ke kike damu na? Son ki ne yake wahalar da ni”


“Ba so na bane wannan, wata damuwar ce ta daban, dan Allah ka faɗa min abunda yake damun ka”


“Tashi muje kar muyi dare”


Ya tashi da zimmar kawar da maganar dan baya son faɗa mata komai.
Shi ya fara zuwa yayi ma Hajiya sallama sannan ita ma tayi masa, suka kama hanya, tun da suka hau titi bata ce masa komai ba in ban da ido ta da sakar masa tana kallon yanayinsa, a fuskarsa take karantar damuwarsa, zuciyarta na nasalta mata lallai akwai abunda yake damun Mijinta.


Parking taga yayi a gefen ti-ti, sai ya juyo ya kalleta yana murmushi, kamin ya kai hannu ya jaka izuwa ƙirjinsa, ya rumgumeta. Ya ɗauki dogon lokaci a haka sannan ya tashi motar suka ƙarasa.
Jikinsa ne ya bashi ba lafiya ba, tun daga lokacin da yayi parking ɗin, sai kuma ya soma jin rashin dacewar abunda yayi ma Rashida, ko ba komai uwar ƴaƴansa ce, sai dai babu yadda ya iya tun da hiv indan be zama aids ba, akan iya kamuwa dashi ta hanyoyi da dama, tun da a yanzu shi dai ya samu tabbacin shi da Kalsoom da ƴaƴansa basa ɗauke da cutar.


Sai dai ya san Rashida ba zata iya rayuwa babu shi ba, yasan yadda take ƙaunarsa, amman zai gogeta a ransa matuƙar result ɗin ƙarshe ya fito, kuma ya tabbatar da a sex ta samu cutar.
Sai da ya raka Rashida har ɗakinta, sannan ta fito ya shiga ɗakin Rashida. Yanayin yadda ya ganta ya tsorata sosai, tana kwance cikin jini babu numfashi. Be san lokacin daya ɗauke ta ya fito da ita da gudu ya nufi mota.


AMIRA POV.


Daga rarrashin da yake mata, sai wasan ya sauya salo, ya fara bin jikinta yana wasa da dukan ɓangarorin jikinta, har yayi nasarar jan hankalinta, ya biya buƙatarsa.


Sannan ya nufi ɗakinsa ya kwanta, ita kuma ta nufi wani ɗakin, tayi wanka ta shirya cikin wasu tufafin ta fito kamar ba ita ba.
A falon ta dawo, ta buɗe freezer ta ɗauki lemu tasha tana ƙoƙarin kawar da damuwar dake cikin ranta dan samawa kanta nishad.
Ta zauna, saman kujera tana ƙoƙarin canja MBC bollywood, zuwa AIT, program ne suke akan yadda za'a magance matsalar tsaron data addabi Nageria, har zata canja sai channel sai kuma ta tsaya tana kallon yadda Abdool yake watsa turanci yana koro bayani kamar wani ba'amerike, hakan ya ɗauki hankalinta har ta kula da kyausa, da kuma muƙaminsa, kamin su sake naɗo sunansa.


“Major General Abdullah Ahmad Mai-Doki, wow nice guy, nice work, nice name, everything perfect”


Ta furta a hankali tana mai maida hankali ga kallonsa sosai. Dif nefa suka ɗauke wuta, wani irin buga ƙafa tayi, ta sosa hancinta.


“Oh they Fuck up”


Zata tashi sai ga mutumen ɗazu ya dawo, yana bata rahoton Doc Sabo. Dafe kai tayi tana tashi tsaye.


“Eyyyyyy karka cika ni da wani magana, ga wayana nan ka duba number ta ansa banker ka tura mata text ɗin abunda zata biya, sannan kace Samuol ya tada mana injin”


Tana kaiwa nan ta nufi ɗakin da Guy son ya shiga ɗazu.








[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

_Write by_
*Khadeeja Candy*


*PAGE - 38*


NOT EDITED ⚠


Ko da ta shigo ɗakin ta same shi tare da Mama suna magana, bata iya zago zancen da suke amman jikinta yana bata kamar maganar ta ne suke. Cikin Ladabi ta miƙawa Mama wayar.


“Kun gama maganar ko?”


“Eh mun gama”


“Tau madallah”


Yanayin yadda ta tayi maganar ya tabbatar ma da Namra da biyu tace haka ɗin, sai ta tashi ta fice daga ɗakin ta basu guri.
Da kallo Namra ta bita har ta fita sannan ta zauna kusa da Asim


“Anty ta aiko min da 300,000k, zan bawa Dillaiya su in yaso sai ta bini hansin ɗin”


Asim yayi shiru be ce komai ba, sai ma yayi kamar ba dashi take magana ba, baya son nuna mata be jidaɗi ba, sai dai a can kasa zuciyarsa rashin jindaɗin ne, ganin ba shi Anty ta aikowa kuɗin ba, tun farkon fara rashin lafiyarsa har zuwa yanzu babu wani abu daya fito daga hannunsu izuwa gare shi da sunan yayi lalura da su.


Hannunshi ya kai ya riƙa nata hannun.


“Namra ya zaki ji idan aka ce yau Mama bata son ki kuma kina auren ɗan ta?”


Tayi shiru tana nazarin inda maganarsa ta dosa, tambayace yayi mata mai ma'ana ɗaya, dan kai tsaye ta san da ita yake.
Sai kawai tayi murmushi tace


“Be zai dame ni ba, saboda Kai na aura ba Mama ba, sannan ban aure ka ba dan wani abu naka

Please Login or Register in order to submit comment