Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samun damar kawarda wancan tambayar da tayi mata.
Ajiyar zuciya Amira ta sauke, har yanzu kan ta kulle yake ta rasa dalilin da yasa Uzair ya yi mata ƙaryar yana son ta, kuma ya ƙulla alƙawarin zai aureta, lalai akwai wani abu a ƙasa.


“Zan raka ki mana, kwana biyu ya daina zuwa makaranta, nima ina tunani ko lafiya?”


Ta faɗa lokacin da Namra ta girgiza tana maimaita mata zancen.


“Tashi muje kamin four ta yi”


Namra taja hannunta suka tashi. Har suka isa gidan, Amira tunanin maganar Namra take, wani ɓangare na zuciyar na nuna mata lallai Uzair so yake ya yaudareta.
Namra nayin parking ta dafa Amira, ganin tun ɗazu hankalinta baya jikinta.


“Wai lafiya kike kuwa?”


Saurin buɗe motar ta yi, gudun kar Namra ta samu damar zargin wani abu.


“Lafiya ƙalau, fito muje”


Fitowa Namra ta yi gabanta na faɗuwa, a bakin ƙofar gidan ta tsaya tana tunanin abunda zata ce musu idan ta shiga.
Amira ce ta yi sallama taja hannun Namra suka kunna kai cikin gidan.


Ƙannen Asim ne suka amsa mata, mahaifiyarsa na haɗa ido da Namra, ta sauke kai ta cigaba da ƙullin zoɓonta kamar bata gansu ba.
Har ƙasa Namra ta risina ta gaisheta, yayinda Amira ta gaisheta a tsaye. Can ƙasan maƙoshinta ta amsa musu, fuska a haɗe kamar ta ga mutuwarta. Kasa magana Namra tayi, har sai da Amira ta ce


“Umma ko Asim na nan?”


Ɗago kai ta yi tana musu wani ƙazamin kallo.


“Ai ku zan tambaya, dan yau kusan sati uku kenan, ban saka Ibrahim a ido ba, tun ranar da ya zo nan yana hawaye yace kin cuceshi, ban sake ganinsa ba, ni kaina nemansa nake”


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Namra ta faɗa idonta na ƙoƙarin cika da ƙwalla.


“Wani Innalillahi zaki yi? Ashe kin san Allah? Babu irin roƙon da ban miki ba akan ki rabu da Ibrahim amman kika ƙi, duk irin maganar da na masa a banza saboda idon sa, ya rufe akan ki”


Amira ta yi saurin saka bakinta.


“Wallahi Umma ba haka ba ne, ita kanta Namra tana son Asim, laifin mahaifinta ne”


“Ni ban tambaye ku laifin kowa ba, dan Allah ku fitar min daga gida, kuma wallahi sai Allah ya saka masa”


Har suka fito kuka Namra take, kasa tuƙa motar ta yi, sai Amira ce tayi driving ɗinsu.


“Yanzu ina Asim ya tafi? Duk abunda ya same shi ni ce sila, ba zan yafewa kai na ba”


“Namra ki daina kukan nan indai ba so kike muje gida a riƙa tambayar ki me ya faru ba. Ke ni fa ban ma yarda da zancen ta ba, ta ya za'a ce namiji kamar Asim ya bar gidan iyayensa dan kawai ya rabu da ke? Ai wannan fashion ɗin ya wuce”


“Zai iya saboda gudun waɗanda za su masa dariya, kuma ɓacin rai babu abunda ba ya sawa Amira”


“Amman ke dan Allah rabuwa da shi be fi miki alheri ba? Saboda shi kika ɓata da duk samarin ki, kuma mahaifinki ya ɓata da ke, shiyasa ma yanzu yake ƙoƙarin miki auren dole, abunda aka bar yayi tun kakanni”


Shiru Namra bata ƙara cewa komai ba har Amira ta yi parking a bakin gate ɗin gidansu Namra, dan bata jin shiga cikin gidan, ita ma kanta tana da nata damuwar.


“Ni dai zan wuce, idan kin gama kukan sai ki shiga da motar ciki”


Bata jira abunda zata ce ba, ta buɗe motar ta fice. Sai da Namra tayi kusan minti talatin a gurin sannan ta buɗe motar ta fito ta dawo mazaunin direba ta yi ma motar key tare da horn.
Mai gadin na buɗe mata gate, ta shiga da gudu har sai da tayi kaura da wata motar dake gabanta fake.
Buɗewa tayi ta fito, tana cigaba da kukan ta nufi part ɗinsu.


Anty Amarya na tsaye jikin window tana kallon abunda Namra ta yi, tasan Namra da zafin zuciya nan gaba har kanta zata iya jima ciwo da motar, ranta ya ɓace sosai, ita kanta ta damu da halin da ƴarta take ciki, sai dai babu abunda zata iya yi tun da ita ta jawo kanta haka tun farko.
Namra na shigowa Anty Amarya ta miƙa mata hannu.


“Bani makulin motar?”


Ba musu ta miƙa mata, tana share hawayenta, bayan Anty Amarya tace ta karɓi key ɗin tace


“ATM ɗin Abbanki yana nan na aje miki, shi ya aiko yace a baki yace ki ciri ko nawa kike so ki yi lalurarki, kuma yace ki samu ƙawayen ki ku rubuta events ɗin da zaku yi, on Wednesday za'a kawo lefen ki da IV”


Wani irin abu ta ji ya ratsa zuciyarta, idonta cike da ƙwalla ta kalli Anty Amarya.


“A tunani na uwa ce zata fi kowa fahimtar halin da ɗan ta yake ciki. Ke kika haife ni, ke kika raine ni har na kawo yanzu, ashe be isa yasa ki karance wacece ni ba? Ashe za'a iya zuwa a'ce miki nayi kisan kai kuma ki yarda? ”


Anty Amarya ta sauke ajiyar zuciya.


“Namra kin yi furucin ne a idan ba zan iya goge zanen rubutun ba, ba zan iya musu da Baban ki ba, idan har na goya miki baya wajen butulce masa duniya zata zage mu, shi kuma ayi masa dariya ace ƴar waje na tafi ƙarfin sa. Ban san dalilinki ba, amman nasan na za ki yi ma Uzair irin wannan sheirin ba haka kawai ba, amman ni da ke duk babu abunda za mi iya yi”


“Na gode da kika fahimta, na gode da zuciyarki ta raya miki ba ƙazafi na yi ma Uzair ba, Allah ya fahimtar da Abbah”


Anty Amarya tace


“Namra ina nan ina miki addu'ah, idan auren ki da Uzair ba alheri ba ne kada Allah ya bari ayi shi”


Da kuka ta rumgune Anty Amarya


“Na gode”


Anty Amarya ta riƙa hannunta suka zauna, ta soma tambayarta taya ta ga Uzair yana aikata wannan mummunan aiki na luwaɗi, kuma miye hujjarta.


Babu abunda Namra ta ɓoye Anty Amarya, tun daga lokacin daya fara nemanta, har zuwa lokacin data kamashi da friends ɗinsa da irin gargaɗin da ya yi mata.
Anty Amarya taja wani dogon numfashi ta sauke tana jinjina lamarin.


“Lallai Uzair ya cika tantiri, shine kuma ya zagayo ya zo neman aurenki?”


“Ina tunanin yayi hakan ne dan Anty Namra ta rufa masa asiri, tun da mijinta ne ai ba zata tona masa asiri ba, kuma kin ga yanzu data faɗa sai ta zama ita ce mai laifi”


Cewar Maryam tana riƙe ƙoƙarin zama kusa da Namra.


“Amman miyasa baki faɗa min ba tun farko? Miyasa kika kirashi a waya kika masa cin mutunci? da wannan ne ya zagayo yazo ya ɗaure ki a gurin Abbanki, miyasa ba ku shawara idan zaku yi abu?”


Namra ta share hawayenta.


“Ban zaci abun zai zame min haka ba, nayi tunanin zai ji tsoro ya janye maganar auren ne”


“A ƙasashen yahudawa Uzair yayi karatu, ya fiki iya makirci, kuma mai son abun ka ya fi ka dabara”


Maryam ta kalli Anty Amarya


“Yanzu meye abun yi?”


“Abun yi kawai mu duƙufa da addu'ah, daga ke har ita, kuma In'shallahu wannan aure Allah ba zai bari a yi shi ba, tun da akwai zalumci a ciki”


Sun daɗe zaune a falo suna firar, sannan Namra ta tashi ta nufi ɗakinta zuciyarta cike da sassauci. Daf da zata shige Maryam ta kira ta


“Anty Namra”


Juyowa ta yi, ta amsa murya a daƙishe


“Na'am”


“Ki sawa zuciyarki sanyi, Mama na tare da ke, nima ina tare da ke, Allah ma yana tare dake, kuma zai kawo miki mafita”


Daga inda take tsaye ta ɗan murmusa


“Na gode Maryam”


Ko ba komai ƴar hirar da suka yi, da goyan bayan da suka nuna mata, yasa ta samu kanta da ɗan sakewa, tsaɓanin baya da take ganin kamar ita kaɗai ce a cikin matsalar.
Daman komai na duniya yana son tattaunawa, ta haka ne zaka fahimci wasu, wasu kuma su fahimce ka, matuƙar kace zaka kulle sirrinka a zuciyarka, shine mataki na farko wajen gurɓata tunaninka, da jawa kanka ciwo.


Sai dai duk da haka maganar da Mahaifiyar Asim ta yi mata ɗazu ta tsaya mata a rai, cewar Allah sai ya saka masa, yasa jikinta sanyi, da kuma zancen bata san inda ɗanta yake ba.


“Ina ka shiga Asim? Miyasa zaka yi haka? Zaka lalata karatun ka, ka guji iyayenka saboda ni Asim?”


Rumgume filo ta yi, tana tuna ranar da yake labarta mata irin rayuwar da suka taso ta maraici shi da ƙannensa, da kuma irin wahalar daya sha kamin ya samu kuɗin registration, wanda shi ya hana shi shiga makaranta da wuri.


Lumshe ido tayi, tana buga kanta da hannunta. Wayarta ta sake ɗauka ta kira layinsa still switch off, sai kawai ta aika masa da sako.
Sannan ta kira Amira ta labarta mata yadda suka yi da Anty Amarya, da kuma goyon bayanta da suka yi a yanzu.


************
ONE WEEK LATER...


Wednesday tun da sanyi safiya Anty Amarya da Maryam suka fara shirya abunda za su tarbi masu kawo lefe dashi, snacks da meatballs da sauran abubuwa Hajiya Barau ce tace zata yi, dan ɓangarenta za'a kai lefen.


Tun safe Namra ta bar gidan, kasancewar ba su da lacca sai kawai ta yanke shawarar zuwa gidan su Amira. A can ta wuni tana aikin kuka, tun Amira na iya rarrashinta har ta gaji ta zuba mata ido.
Sai bayan sallah Azahar Amira take labarta Namra wai jiya taga Asim. Da sauri Namra ta kalleta.


“A ina kika gan shi?”


“Shi ya zo nan gidan, ya kara ni a waya na fito, kuma yace karka faɗa miki”


“Haba Amira? Baki faɗa masa halin da nake ciki bane? Wai da gaske kike ko wasa?”


“Na saba miki irin wannan wasan ne? Babu abunda ban faɗa masa ba akan halin da kike ciki, kuma nayi-nayi ya faɗa min inda yake zaune ya ƙi, Namra karki so ganin Asim duk ya koma wani iri”


Namra ta dafe kanta


“Wayyo Allah na. Da wace number ya kira ki?”


“Wata baƙuwar Number ce”


Ta ɗauko wayarta tana nuna mata number. Cikin rawar jiki Namra ta kofe number tasa a wayarta ta soma kiransa. Ƙasa-ƙasa Amira take kallonta har kiran ya katse ba'a ɗaga ba. Daga bisani sai aka kashe wayar gaba ɗaya.


Har aka yi Magariba Namra nata trying ɗin Number amman kashe.


“Ki haƙura da kiran nan Namra, idan ya ga dama zai kira ki tun da kin tura masa saƙo”


“Baki fahimci yadda nake ji bane Amira, ni kaɗai na san halin da nake ciki”


“Yanzu dai kin ga anyi magariba, ya kamata a'ce kin koma gida, nima kuma ina son na biki dan naga lefen, zaki ci abinci ko na haɗa miki tea?”


“Tea zai fi dan bana jin cin wani abu”


Tashi tayi ta fice daga ɗakin, sai gata ta dawo riƙe da kofin tea, yaji Lipton da ginger da lemun tsami sosai har ya canja kala.
Ta daɗe riƙe da kofin kamin ta miƙa ma Namra.


“Ki daure ki shanye, tun da baki ci komai ba, nasan kina jin yunwa zai taimaka miki”


Ba musu Namra ta karɓa, tayi bismillah ta riƙa kuɓa tea har ta shanye. Sannan ta tashi sukayi Sallah, sai Amira ta ɗauko Hijabinta ta saka suka fito.


Napep suka tsaida, dan Namra yanzu bata da Mota tun lokacin da Anty Amarya ta amshi key ɗin bata mayar mata ba, ita kuma Amira daman ba Mota ne da ita ba.
Magana suka masa yace zai kai su ɗari biyu, sannan suka shiga.
Be aje su ko'ina ba sai ƙofar gidan su Namra, Amira ce ta biya kuɗin, sannan suka fito suka shiga cikin gidan.


A falon Anty Amarya suka tararda ƙannenta biyu, Hajiya Lariya, da Mama Zainab.
Cikin ladabi Namra ta gaishe su, suka amsa suna mata fatan alheri, sai yaba lefen suke suna shi masa albarka.
Ita dai bata ce komai ba, idonta dai cike da ƙwalla, sai Amira ce take amsawa da


“Amin”


Fitowar Anty Amarya ne yasa Namra tashi tsaye, ta kalleta.


“Kin dawo?”


Nan ma Amira ce ta amsa


“Eh, Anty ina wuni?”


Anty Amarya ta lura da hawayen da suka idon Namra, kuma bata son ta yi kuka har ƙannenta su fahimcin halin da take ciki, sai ta yi saurin cewa Amira.


“Lafiya Ƙalau, Amira ku shiga ɗaki”


Hannun Namra, Amira ta riƙa suka nufi ɗakinta.
Saman gado suka zauna, sai Namra ta kwanta jikin Amira tana kuka, jikinta duk ya mace kamar marar lakka.
Amira ta ciro wayarta dake cikin pose, tayi ƴan danne-danne sannan ta mayarda wayar, ta cigaba da rarrashin Namra tana bata Haƙuri.


Ba'ayi minti ashirin ba, sai ga kira ya shigo wayar Namra, da number da Amira ta bata tace mata number Asim ce.
Cikin rawar jiki Namra tayi picking ta kara akunne tana.


“Asim! Asim!! Asim!!! Dan Allah kayi magana”


Shiru ba a amsa mata ba, daga bisani sai aka kashe wayar. Kira ta riƙa aika ma number amman ba'ayi picking ba, bayan kamar minti biyar sai ga sako ya shigo wayarta.


‘Namra ki fito yanzu, ina son na yi wata muhimmiyar magana da ke, ina nan bayan layin ku ta gurin gidan Alhaji Sani’


Tana gama karantawa ta nunawa Amira, sai Amira ta riƙe ta


“Namra karki je...”


Sai kuma ta yi shiru kamar wacce ta tuno wani abu, sai ta kalli Namra da ke kallonta tace


“Amman idan ba wannan ba, ba ki da wata dama ta ganinshi, kuma idan ba kije ba zai iya fushi da ke”


Namra ta sauke ajiyar zuciya


“Zaki raka ni?”


“A'a ni ba zan je ba, kar a shigo ɗakin ba kowa, kuma idan mun fita tare za'a zarge mu, wata ƙila ma Asim ya kasa yin magana da ke idan yaga muna tare, amman me zaki ce wa Anty idan ta gan ki?”


“Nima ban sani ba, kuma idan har na faɗa mata ba zata bar ni naje ba”


“Toh karki faɗa mata, kibi ta ƙofar kitchen ki fita, zan jira ki a nan har ki dawo”


Ba tare da fargabar komai ba, Namra ta tashi ta nufi ƙofar fita.
Sai da ta fice sannan Amira ta ɗauki wayarta ta kira number, ana ɗauka ta ce


“Gata nan zata fito yanzu”


Namra na fitowa taga Anty Amarya na zaune falo tare da ƙannenta suna hira. Da faɗuwar gaba Namra ta nufi kitchen ɗin, tayi sa'ah babu kowa a ciki.
Hakan ya bata damar buɗe ƙofar a hankali ta fice. Da wage-wage ta isa gate, nan ma a hankali ta soma buɗe ƙofar, sai ga mai gadi ya taso ya nufo ta yana tambayar lafiya.
Dan ya san indai ba dolen-dole ba babu abunda ke fitar da su da zarar anyi sallah magariba, dan Abbah baya son fitar dare.


“Lafiya ƙalau, saƙo zan karɓo nan baya, yanzu zan dawo”


“Toh Allah ya tsare”


Sai ya maida ƙofar ya kulle. Sauri-sauri take tafiya tana wage, sai kiran wayar take amman anƙi picking.
Sai data kai ƙarshen layin, sannan ta karya kwana ta nufi gurin daya kwatanta mata, jiki babu ƙarfi sai jin take kamar ta faɗi, dan ƙafafunta basa iya ɗaukarta.
Kamin ta ƙarasa taji kamar ana binta a baya da mota, ta ɗan ji tsoro daman da fargaba ta fito gida, kasancewar unguwarsu ba kasafai zaka ga mutane ba ko da rana balle da dare, ga kuma fargabar kar wani ya ganta yaje ya faɗa a gida. Tsayawa tayi tana kallon ƙatuwar Bus ɗin mai baƙin gilashi.


Wasu maza ne guda huɗu suka fito ɗaga ciki Bus ɗin suka nufo ta ciki har da Uzair, ganin Uzair ne ya hana ta gudu daman can bata jin ƙarfin gudun, sai ta tsaya tana masa kallon mamaki da tunanin me ya kawo shi nan.


‘Daman yana biye da ni kenan? So yake ya tona min asiri yace ya gan ni na gana da Asim da dare ko me?’


Kiran daya shigo wayarta ne ya ankarar da ita daga tunanin da take. Number ce wanda aka turo mata saƙo da ita da sunan Asim ne. Da sauri ta kalli Uzair daya ƙaraso kusa da ita


“Uzair daman kai ne? Ko kuma wayarsa ka karɓa?”


Ta tambaya a kasale, jiri na ƙoƙarin ɗaukarta.
Murmushi kawai ya yi mata, ya kai hannu ya riƙo ta iya ƙarfinsa.
A nan Allah ya bata ikon yin ihu da dukan muryarta. Cikin sauri mutumen dake tare da Uzair ya fitar da wani ƙyalle ya danne mata hanci dashi, daga nan bata sake sanin inda take ba, sai numfashinta ya ɗauke dif.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa07.html




🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated


NOT EDITED⚠




*PAGE - 7*


A hannunsa ta suma, sai ya ɗauke ta ya miƙawa mazan da yake tare da su yana faɗin


“Ku shiga da ita, kuma ku tabbatar bata farka ba, har sai na dawo”


“Yes Boss”


Cikin girmamawa suka amsa, suka saka ta cikin Bus ɗin. Sai da Uzair ya ga sun bar gurin sannan ya nufi ƙofar gidan Alhaji Sani inda yayi parking ɗin Motarsa.
Bude Motar yayi ya shiga, ya ɗauko wani turare ya fesa, sannan yayi ma Motar key. Ribas yayi ya dawo ta bayan layin sai gashi a bakin gate ɗin gidan su Namra.
Horn yayi mai gadin ya buɗe masa yana gaisheshi. Guri ya samu a harabar gidan ya yi parking.
Sai ya fita ya taka da ƙafa ya isa part ɗin Abbah, dan yaga motarsa a waje, alamar yana nan kenan.
Hankalinsa kwance ya shiga falo, Abbah na kishimgiɗe yana duba jarida, Uzair ya shigo sai yayi saurin zubewa ƙasa yana kwasar gaisuwa.


Da far'ah Abbah ya amsa, yana nuna masa gurin zaman, bayan sun gama gaisawa, sai Uzair yayi shiru be ce komai ba har sai da Abbah ya kalle shi ya ce


“Uzair kana da wata magana ne?”


Abbah ya tambaya, yana mai jin son Uzair ɗin a cikin ransa, kusan ma ya fi kowa jindaɗin wannan haɗin, dan Allah ya sa masa son Uzair shiyasa komai na harkar kasuwancinsa sai ya saka shi, duk kuwa da cewar shima yana da ƴaƴa maza.


Sun-sun ya yi da kai


“A'a Abbah, akan maganar IV ne na mata, har yanzu Namra bata rubuta ba, kuma lokaci na tafiya, shine Hajiya tace na zo, na mata magana, shine nace bari na gaishe ka”


Abbah ya yi murmushi irin nasu na manya, sannan ya yi gyaran murya yace.


“Uzair sai ka yi haƙuri da lamarin Khadija, har yanzu akwai ƙurciya a tare da ita, kuma ita ba zata gane alfanun wannan auren ba har sai anyi, haƙiƙa ina son Khadija matuƙa sai dai tayi tsalle ne da ɓata rawarta tun daga lokacin data tsaya kai da fata akan lalle ita sai wannan yaron,
na bata dama na fitar da wani ta ƙyale wannan yaron amman sai ta buga min ƙafa a ƙasa ita sai Asim, shiyasa kaga na fita lamarin ta, saboda so da yawa zaka abunda mu iyaye muke hangowa ba shi ƴaƴa ke hangowa ba, a tunanin ta na yi mata hakan ne dan na cutar da ita, tun da ta nuna bata so.
Nasan anbar auren dole a yanzu, amman duk abunda na yi ma Namra ita ta jawa kanta”


Abbah ya ɗaga kai ya sake kallon Uzair da kyau yana mai nuna masa abunda yake faɗi a bakinsa shine a zuciyarsa.


“Uzairu ina fatar zaka riƙa Khadija da amana, kuma zaka nuna mata so da kulawa, irin son da zata san lallai ta yi dacen mahaifinta be mata mugun zaɓi ba, ina son ka sani duk abunda ya samu Namra ni ya sama, kuma zai taɓa mahaifiyarta, ina addu'a wannan aure Allah ya sa masa albarka, ya baku haƙuri zama da junanku”


Jikin Uzair yayi san yi sosai da kalaman da Abbah yayi masa, sai yake jin kamar Abbah ya san abunda yake son aikatawa.
Cikin rashin kuzari ya yi ma Abbah sallama, ya tashi ya fice.


Har ya iso gurin motarsa tunanin kalaman Abbah yake.


‘Abunda duk ya sami Khadija ni ya sama’


Same shi ya fi tsaya masa a rai, tunani yake what if Abbah ya gane gaskiyar dalilinsa na neman aurenta? Shi kuma baya jin yana da wata mafita ta rufa ma kansa asiri bayan wannan, tun shi dai ba zai ce zai kashe Namra ba, gashi ta ce sai ta tona masa asiri.


Ya kwashe minti arba'in a gurin yana tunani, ba tare da ya sani ba. Can sai ya nufi gurin Mai gadin yayi masa magana kan ya shiga yayi masa sallama da Namra.
Cikin girmamawa mai gadin ya nufi part ɗin Anty Amarya, shi kuma ya dawo gurin Motarsa ya tsaya ransa a jagule.


In few minute Mai gadin ya dawo ya shaida masa ance gata nan zuwa. Chanji ya fiddo a aljihunsa ya miƙawa Mai gadin, sannan ya gyara tsayuwarsa yana jiran fitowarta.


Lokacin da Mai gadin ya shigo falon, Anty Amarya, na zaune tare da ƙannensa suna cin abinci, sai tace da Mai gadin yace tana zuwa, sannan ta tashi Maryam ta ce taje ta kirata ɗakinta.


Maryam ta aje littafin dake hannunta ta tashi ta nufi ɗakinta. Tana yin sallama Amira ta zabura kamar marar gaskiya.


“Anty Amira, ina Anty Namra?”


Shiru tayi tana dube-dube kamar mai neman abu, can kuma ta kalli Maryam tace


“Maryam idan na faɗa miki wani abu zaki fahimta ai ko?”


“Uhmm minene?”


“Namra ta fita ɗazu, Asim ne yayi mata texs wai yana son ta zo suyi sallama, shine ta fita tun ɗazu”


Gaban Maryam ya faɗi


“Amman kika barta taje ita kaɗai? Idan wani abun ya same ta fa?”


Shiru tayi tana tunanin ƙaryar da zata ƙaƙaro


“Ba yadda ban yi ba, amman tace ba zan bita ba, wai na tsaya kar a zo nemanta ba'a ga kowa ba, amman bari na kirata”


Cikin sauri ta shiga kiran wayar. Maryam bata tsaya ba, ta juya ta fita.
Daga bakin ƙofa ta tsaya tana kiran Anty Amarya. Daker ta taso saboda abincin da suke ci da kuma firar da suke da ƴan'uwanta.
A tunaninta Maryam zata ce mata Namra taƙi zuwa ne, sai kawai taji wani labari banbaragwai. A take Anty Amarya ta ɗauko wayarta ta shiga kira amman ba a picking.


Sai duk hankalinsu ta tashi, Anty Amarya ta koma ɗakin Namra ta samu Amira zaune tana faman kiran waya.


Anty Amarya ta katsa mata tsawa.


“Ina tace miki zata?”


Jiki na rawa ta amsa ma Anty Amarya dan ta ga ranta ya ɓace sosai.


“Tace min nan bayan layi”


“Amman dai Anty Amira kin yi wawanci Wallahi, shine kika bar ta taje? Maimaiko ki hanata ko ki faɗawa Anty, kuma kika ƙi binta kuje tare”


Maryam ta faɗa tana hararar Amira. Anty Amarya tace


“Ita ma Namra ai da wayon ta”


“Ko da wayonta ai wani abun sai an nuna mata, tun da kinsan yadda Anty Namra take ko ni sai na fita wayo, waya sani ma ko da ke ya haɗa kai kika lallaɓa masa ita ta tafi”


Amira ta kalleta


“Haba Maryam wane irin magana kike haka ne? Kina tunanin ni zan iya cutar da Namra?”


“Waya sani abu a duhu, ƙawayen yanzu ai ba abun yarda bane, kuma Wallahi duk abunda ya samu Namra ki ƙaddara ke ya sama dan ba zan taɓa yafe miki ba”


Amaimakon Amira tayi magana sai kawai ta fashe da kuka, ta tashi ta ɗauki pose ɗinta ta fice tana kuka.
Anty Amarya sai ta hau Maryam da faɗa


“Wai Maryam ba zaki bar fitsarar nan ba ko? Kullum ina miki magana kan shegen bakin nan naki amman baki ji, yanzu miye na wannan furucin fisabillahi? Ita Namra ƙaramar yarinya ce da Amira zata ɗorata a layi ta hau?”


Maryam ta tunzure baki.


“Wallahi zata iya ɗora ta a layi wannan Amirar da kike gani shegen wayo ne da ita, kuma Wallahi tun ba yau na lura kamar tana hassadar Anty Namra, wani fa sam baya son yaga cigaba a gareka sai ci baya, kuma wani maƙiyi na ɓoye ba gane shi ake ba”


Anty Amarya ta katsa mata tsawa


“Zaki je kiyi magana da Uzair, ko tsayawa zaki yi, kina ƙara min ɓacin rai”


Juyawa tayi ta fita tana faɗin


“Wallahi duk wani abu ya samu Anty Namra Amira zan zarga”


Ɗakinta ta shiga ta ɗauki Hijabinta ta saka, sannan ta fito ta nufi harabar gidan gurin da Uzair yake, tana harararsa.


“Bata jindaɗi ba zata iya fitowa ba”


Ta faɗa ba tare data masa sallama

Please Login or Register in order to submit comment