Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau likita a gidana na”


Da sauri Hilal ya miƙa masa hannu suka gaisa, har da ɗan risina masa yana murmushi.


“Wai daman nan ne gidan ka?”


“Nan ne kasan abu ga talaka”


Ya faɗa yana dariya, yasan Doctor Hilal sosai dan shine likitan da yake dubashi a duk lokacin daya je asibiti, sai dai Doctor Hilal be waye shi sosai ba, sai yanzu.


“Shigo ciki mana”


A falonsa ya shiga da Hilal ya ɗauko masa lemu da kansa, zai zuba masa Hilal yayi saurin karɓa ya zuba da kansa.


“Ya fama da jama'ah”


Daddy ya faɗa yayin da ya zauna saman kujera.


“Al-hamdulillah da fatar dai na same ku lafiya”


“Lafiya ƙalau, yau dai sai ga likita gidana, ina ji dai hanya ce ta biyo da kai, ni dai nasan Likita be san gidan ba”


Doctor yayi dariya.


“Yanzu ma dalili ne ya kawo ni, akwai wacce na gani naga ta shigo nan gidan”


“To, kuma bata faɗa maka sunanta ba? Ta yiyu ma ƴar maƙota ce”


“A dai yadda nake tunani ƴar nan gidan ce, sunan ta Kalsoom wata doguwa haka”


Daddy yayi murmushi.


“Kalsoom ai ƙanwar ka ce Likita”


Hilal yayi ƙasa da kanshi


“Ina fatar ba'ayi mata miji ba?”


“Ba'a mata ba, amman akwai manema”


“Ina fatar shiga cikin su, amman idan kayi min izini, dan ni da gaske nake yi idan Allah ya yarda”


“Ba ni da matsala Likita, inda har kun dai-dai ta kanku, ni da Kalsoom ai duk mallakin ka ne, tun da ni Patient ɗin ka ne”


Ƙasa Hilal yayi da kansa cike da jindaɗin maganar Daddy, be ɗago ba har sai da Daddy ya tashi yana faɗin


“Bari na kira maka ita”


Daddy na ficewa ya miƙe tsaye ya ƙara karkaɗe shaddarsa, sannan ya zauna a natse yana kallon ƙofa. Sai gata ta fito cikin hijabi tana tafiya a hankali, sallama ta fara masa sannan ta nemi guri ta zauna, tana gaishe shi.


“Lafiya ƙalau, ina fatar Gimbiyar tana nan lafiya”


“Al-Hamdulillah”


“Mashallah, na zo mun gaisa da Daddy ki sai yace ze kira min ke mu gaisa, ina fatar ban takura ki ba, kuma in babu matsala zan so ki gabatar min da kan ki”


“Sunana Kalsoom ni budurwace ina aiki a MTN Service, nan ne gidan mu kuma ina ƙarƙashin kulawar iyaye na ”


Gabansa ya faɗi, jin tana aiki, shi da yake son ƙara aure saboda aikin da matarsa take sai kuma ya sake karo da wata ma'aikaciyar. Sai dai be nuna mata ba, sai kawai yayi murmushi yace


“Mashallah, ni kuma sunan Doctor Hilal Abubakar Mai-lafiya, ina aiki a American Hospital dake nan Kaduna, ina da mata ɗaya da yara uku, ina fatar zan samu karɓuwa, duk da kasancewar na san muna da yawa”


Murmushi kawai tayi masa, ta shiga murza hannunta.


“Ba zan cikaki da surutu ba, dan na fahimci kamar Gimbiyar tawa bata son yawan magana, ni kuma gani kamar wazirin aku, zan nemi alfarma ɗaya zuwa biyu”


“Allah yasa zan iya”


Ta faɗa da murmushi.


“Ina farko ina son ki bani damar zuwa muna gaisawa, bace kullum ba gudun kar na takura miki, amman zan riƙa kwatantawa, sannan ina son ki samin number wayarki”


A take ta karanto masa number, sai da yasa yayi saving sannan ya kalle ta


“Amman fa ni bana son na kira naji User busy, dan ni ina da kishi sosai, ba kamar sauran samarin ki bane”


Nan ma murmushi tayi, sai ya tashi tsaye yana faɗin


“Bari na zo na tafi, kar Daddy yace zan sace masa ƴa”


Sai a lokacin tace


“Ai Daddy ya san be kawo ɓarawo gidansa ba”


“Kar kiyi saurin yanke hukunci, Wallahi sata na zo nayi masa”


A kaikaice ta kalleshi zuciyarta na raya mata abunda ze fito bakinsa.


“Zuwa nayi na sace zuciyar ƴarsa, daga nan sai na sake sace gangar jikinta, na kaita gidana na aje”


Fuskarta da murmushi ta lumshe ido yana girgiza kai. Yau kam Allah ya haɗa ta da Mutum me son raha.


“Ba dan kar na takurawa Sarauniyar ba, dana nemi izinin a rakani ”


Lumshe ido tayi ta buɗe


“Ai duk umarnin da sarki ya bada, da shi baiwa zata yi amfani”


Hannunsa ɗaya yasa aljihu sai ya nuna mata ƙofa da ɗayan.


“Zan so Sarauniya ta wuce gaba, gudun kar bafade yayi mata ba dai-dai ba”


“Amman ai ko a fagen yaƙi, Yarima ne yake sharewa Gimbiya hanya”


Wani irin murmushi Hilal yayi murmushin daya ƙara fito da kyaunsa. Sai kawai ya shiga gaba ta rufa masa baya.
A tare suka isa gurin motar sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro sabbin kuɗi ya miƙa mata.


“Nasan wannan ba ze siye kalamai da kuma tsadadden murmushin ki ba, amman zai iya zama tukuici ga rakiyar da kika min”


Naɗe hannayenta tayi


“Ai wanda ya cika da yaƙi, ya mallake ka duka kai da iyalan ka”


Yasan me take nufi sai kawai yayi murmushi yace


“Zan yi farin ciki idan kika karɓa”


“Ni kuma zan fika farin ciki idan baka cilastani na karɓa ɗin ba, kuma nasan farincikin na naka ne”


Mayarda kuɗin yayi aljihu.


“Na gode da wannan karramawar Kalsoom, ni zan tafi ki kula min da kanki”


“Ni kuma ka kula min da Anty na da duk yarana, kuma ka miƙa min kyakkyawar gaisuwa na a gare su”


Ya buɗe baki


“Baki ce min na kula da kai na ba”


Murmushi tayi masa as respond ta juya ta shige cikin falon, tana mai jin sonsa a zuciyarta.
Shima murmushi yayi ya buɗe motarsa ya shiga.


Ko da ya isa gida, Rashida na zaune falo tana jiransa, duk ta haɗe rai sai kallon agogo take, jikinta na bata ba gurin kai ango yaje ba, gurin wata yaje.
Yana yin sallama ta amsa masa


“Wa'alaikassalam, amman pyar ba gurin kai Amarya kaje ba ko? Gaskiya wannan fitar daga gani gurin wata kaje”


Kusa da ita ya zauna yana murmushi.


“Na gode Allah daya sa matana ta iya karantar mijinta har haka, inda zuciyarki ta raya miki can naje kinsan ba zan iya ɓoye miki ba, ɗa zun ma dan bani da tabbacin zan karɓu ne shiyasa ban faɗa miki inda zanje ba”


Ta masa wani kallo


“Ka karɓu kenan?”


“Sosai ma har da tukuici”


Nan da nan idonta ya cika da hawaye.


“Doctor wasa dai kake”


“Banker da gaske nake, ba tuni nake miki waƙen zan yi aure ba kika ganin kamar wasa nake ba”


“Wallahi baka isa ba, ba a gidan nan ba”


“Toh ai sai ki hana idan gidan ki ne, ni dai tashi ki zubo mana abinci yunwa nake ji”


“Ba zan zubo ba, sai ka koma can kaje ta baka abinci”


“Toh ai ba'a ɗaura mana aure ba, amman dai idan na aure ta zaki ga soyayyah ba ni ba har ke sai tayi feeding ɗin ki”


“May God forbid ,kuma Allah ya tsine mata albarka”


Ta tashi ta nufi ɗakinta da kuka, shi kuma ya bita da murmushi yana jin son matar tasa har cikin ranshi.




UZAIR POV.


A mota ɗaya suke zaune shi da Najeeb, suna jiran fitowar Amira.
Sai ta ɓata musu lokaci, sannan ta fito sanye da abaya, tazo tayi musu tsaye tana hararar Uzair.


“Me ya kawo ka gidan mu?”


“Shiga mota zamu yi magana”


Ba musu ta buɗe motar ta shiga gidan baya ta zauna. Sai da ya gabatar mata da Najeeb sannan ya faɗa mata abunda ya kawo su.


“Lallai Uzair ban zaci zaka iya zuwa da wata buƙatar a gare ba, kira nawa nayi maka amman baka ji ba, yanzu ka haɗa ni da ƙawata har ta fara zargina”


Najeeb yayi murmushi mai sauti.


“Wannan ita kaɗaice mafita a gareki a gare mu kuma gaba ɗaya, kin ga idan mun aikata haka har ke asirinki zai rufu, amman idan asirinki ya tonu zaki fi kowa shiga cikin matsala”


Shiru tayi tana tunani.


“Amman nawa zaka biya ni?”


Uzair yayi murmushi.


“Zan baki 100k yanzu idan aiki ya yi zan baki 300k har abunda ya yi sama, amman ki tabbatar ta saka rigar”


“Taya zan iya tabbatar wa tun da ba tsare ta zan yi ba?”


“Ko ya ya zakiyi a kin sani tun da ke mace ce kuma Aminiyarta, idan ta kama sai ki kwana a gidan, yanzu dai kije ki karɓo mana rigar da dare zamu zo mu karɓa”


Cewar Najeeb.


“Naji amman ni ba zanje gurin wani Malami ba, kuje ku yanke min kai”


Duk dariya sukayi, sai Uzair yace


“Mun ji amman dai ki tabbatar rigar data taɓa sakawa ce, zan miki transfer 100k an jima”


Uzair be yarda ya faɗa mata abun ze iya dawawa idan be kamata ba, sai kawai ya ƙaleta har ta buɗe motar tayi ta fita.
Su kuma suka yi kwana suka wuce, daman baki gate suka tsaya basu shiga ciki ba.
Cikin gidan ta koma, a tsakar gida ta samu Ammy da Yayanta a tsaye suna magana, sai ta wuce ciki ta ɗauko handbag ɗinta sannan ta cewa Ammy zata je ta duba Namra.


“Kice ina gaishe ta dan Allah”


Cewar Ammy, sai ta fice tana faɗin


“Toh zan faɗa mata”


Waje ta fito ta tari mai napep ta shiga. Lokacin data shiga falon Anty Amarya ce kawai a zaune, su Maryam da Hindatu duk sun tafi makaranta, Mama Zainab kuma tun jiya da yamma suka kama hanya.
Har ƙasa ta risina ta gaishe da Anty Amarya sannan ta tambayi Namra, Anty Amarya tace mata tana ɗakinki sai ta tashi sun-sun ta nufi ɗakin.


Namra na kwance saman gadonta tana hawaye.
Kusa da ita ta zauna ta kai hannu ta riƙa hannunta.


“Haba Namra yanzu kina ganin kukan naki maganin ne?”


Tasowa Namra tayi ta rumgume Amira.


“Amira kowa fushi yake da ni, ina jin tsoro Amira”


“Tsoron me?”


“Ina tsoron kar ace sun taɓa min mutunci”


Amira ta fara hawaye.


“Nima ina wannan tunani Namra, kuma idan har haka ta tabbata kika yi ciki kin gama wulaƙanta a rayuwarki ta duniya”


Ƙara fashewa Namra tayi da kuka.


“Wallahi duk na gano wanda yayi min wannan abu sai na kashe ki, sai na masa wulakacin mafi ƙasƙanci a duniya”


Gaban Amira ya faɗi, ji take kamar da ita Namra take.


“Mafita ɗaya ce Namra, ki gwada shan magani da haila zata zo miki, kin ga ko da kina da cikin sai ya zube, tun ba daɗe ba”


Namra ta ɗago ta kalleta


“Amman ba ni da tabbaci”


“Shiyasa nace ki sha ɗin, kin ga idan ma anyi ko ba'ayi ba ke dai kin san babu ciki a tare da ke”


“Ina zan samu maganin?”


“Zan nemo miki, zan bincika na siyo miki”


“Na gode sosai Amira Allah ya bar zumunci, amman har yanzu baki da labarin Asim”


“Wallahi har yanzu, amman ki kwantar da hankalinki na san zai dawo komai daren daɗewa”


“Allah yasa”


“Amin, ni bari na tashi na tafi, daman gurin ɗinki zanje sai nace bari na biyo na duba ki, daga nan na ari rigarki ta atamfa”


“Gashi can je ki duba wanda kike so”


“Na jikin ki zaki ara min, dan bana son ɗinki mai hayaniya”


Ba tare da tunanin komai ba, Namra ta tashi ta cire rigar ta miƙa mata tare da zane sai ta saka wata gown.


“Ai dama kin bar Zanen tun da ba shida wani style, rigar kawai nake so”


Mayarda zanen Namra tayi ta aje, ta ɗauko mata jaka ta saka rigar, sannan ta tashi tana faɗin.


“Bari na je kar Ammy ta ga na daɗe tace na gaishe ki”


“Ina amsawa yaushe zako dawo?”


“Da na siyo maganin zan zo na kawo miki, amman ki kwantar da hankalin ki kinji?”


Kai kawai Namra ta ɗaga mata.Sai Amira tayi mata sallama ta fice.


Bayan fitar Amira Anty Amarya ta shigo ɗakin. Ɗaga bakin ƙofa ta tsaya tace


“Uzair ya janye zancen Auren shi dake yace shi ya haƙura, Abbah ki yace shi ba zai sake miki zaɓi ba ki kawo Asim ɗin zai ɗaura miki aure da shi”


Anty Amarya na kaiwa nan ta juya ta fice. A maimakon ta ji farinciki, sai kawai ta ji wani kalar abu ya baibaye ta, shi ba farinciki ba kuma ba baƙinciki ba. Sai kawai ta rushe da kuka.


Amira na fita gidan ta kira Uzair ta faɗa nasa yadda sukayi da Namra, ya jidaɗin abunda Amira tayi tun da yana ganin ta nan zasu samu mafita. Da dare yazo ya karɓi rigar, yace mata jibi ze kawo mata tare da maganin.




RASHIDA POV.


Tun da safe tayi shirin office, wace ke fita takwas ko takwas da rabi yau tun shida ta bar masa gidan, tun jiya da dare kuma ta ƙi sake masa sai fushi take dashi.
Kai tsaye gidan su ta nufa, Mahaifiyarta tayi mamakin ganin ta tun da sanyin safiya, ga fuska duk hawaye.


“Ke lafiya?”


Sai kawai ta faɗa jikinta tana kuka. Sai duk ta rikita mahaifiyarta a zatonta ma ko sun yi faɗa da Hilal ne ko kuma wani ne ya mutu. Sai da tayi kukanta mai isarta sannan ta faɗa mata abunda ya faru.


“Mom wai Hilal aure ze ƙara”


“Amman shine kika zo kika ta da mun hankali na ɗauka ko wani abun ne ma? Toh dan ze yi aure hana shi zakiyi ko me? Ke kaɗai aka ce masa ya aura?”


“Mom kishiya fa ze min ko baki gane ba”


“Na gane mana, ba'a aure ke aka aureki? Tun yaushe yake miki zancen ƙarin aure?”


“Mom wannan karon da gaske yake”


“Toh idan da gaske yake sai me? Hana shi auren zaki yi? Ke idan mai hankali ce ai da kanki ma kyace masa yaje yayi aure, duk irin haƙurin da yake da ke, idan ma yayi auren ai sai ki samu me riƙa miki yaranki”


Ɗaukar gyalenta tayi ta yafa ta ɗauki jakarta


“Ai daman nasan ba zaki goya min baya ba”


“Oh so kike na goya miki baya ki yima mijinki rashin mutunci ko? Shine kika wani ɗauko gyale kika zo gida ko kunya baki ji, kuma Wallahi bari jiki na faɗa miki kar ki biye son zuciyarki kije ki kawa kanki, kar naji wata matsala ta shiga tsakanin ki da mijinki akan auren nan”


Ficewa tayi tana hawaye tana faɗin


“Ba zan sake zuwa gidan nan ba”


Mom taja tsaki ta tashi ta nufi bathroom.




NAMRA POV.


Haka Anty Amarya ta kwashe kusan kwana huɗu babu ruwanta da Namra, ita kuma tana cikin ɗaki ta kasa fitowa kullum sai kuka take da ƙaratun Ƙur'ane, abun duniya duk ya isheta ji take kamar ta kashe kanta ta huta.
Bayan sauko Sallah Jumma'ah Namra ta tashi ta shiga banɗaki tayi alkwala ta fito ta gabatar da Sallah Azahar, bayan ta ƙare ta ɗauko Ƙur'ane tana karantawa.
Ta tsagaita karatun ne lokacin data ji sallamar Amira, sai da bata tsaya ba sai da ta kai ƙarshen aya, sannan tayi addu'ah ta rufe Ƙur'ane, ta juyo ta kalli Amira.


“Amira”


“Na'am”


A kasale Amira ta amsa mata, dan jikinta ya gama mutuwa tun ɗazu, gashi ko ɗazu sai da Uzair ya jaddada mata baya son a samu matsala.


Sai da Namra ta kai Ƙur'ane mazauninsa ta aje sannan tazo ta zauna kusa da Amira.


“Amira tun ranar ban ganki ba, gashi bana da waya balle na kira ki”


“Wallahi ban samu zama bane kinsan ga makaranta, wai miyasa kika daina zuwa ne mutane sai tambayarki suke”


“Amira kunyar shiga makaranta nake yanzu, a gida ma na kasa sakewa balle makaranta”


“Amman da kin daure ai tun da gani, zai riƙa cire miki kewa, kin ga yanzu fa kina ajin ƙarshe idan kika ce ba zakije ba duk wacan karatun naki zai tafi a banza fa”


Namra ta sauke ajiyar zuciya.


“Ni dai ba wannan ba, kin kawo min magani?”


“Na kawo miki gashi a jaka na, amman ban zan baki ba har sai kin min alƙawarin zaki saka atamfar nan mu fita tare da ke, dan zaman nan ke kaɗai shi ke ƙara miki tunani”


Ta ƙarasa ta ciro rigara daga jaka.


“Ba zan iya ba Amira bana iya fita ko ina yanzu”


“Ni dai ko cikin gida ne”


“Naji yanzu ina maganin?”


“Gashi nan”


Ta ciro ta miƙa mata.


“Gashi amman yace idan kina son yayi sauri zo miki toh ki sha huɗu, kuma yace idan kin sha ki ɗan yawata”


A take Namra ta karɓa ta ɓare huɗu ta shiga bathroom ta sha. Tana fitowa Amira ta miƙa mata rigar.


“Tun jiya na wanke miki ita, ɗinkin nan yaɓa fitar dake ke, je ki saka sai mu fita ko garden ne mu zagaya”


Bata zaton da wata manufar Amira take son ta saka rigar, dan ko a mafarki bata zaton Amira zata iya cutar ta ko kuma a haɗa kai da ita a cuce ta. Sai kawai ta kai hannu ta karɓa, a gaban Amira ta ɗaura zanen rigar kuma da zata saka sai da tayi Bismillah, hakan kuma ba ƙaramin tsoro ya bawa Amira ba, sai dai bata yarda ta nuna ba, har suka fito tare suka nufi garden ɗin.
Wayarta ta ciro ta aika ma Uzair da text.


‘Ta saka yanzu, amman Haila be zo mata ba, na san dai ze zo mata tana sanye da ita’


Ƙarkashin bishiyar mangoro Namra ta zauna, kasancewar ta riga Amira isa gurin, kamin ta zauna taji wayarta tayi ƙara alamar saƙo, sai kawai ta fasa zaman sai ta koma gefen tana ƙoƙarin buɗe saƙon.


‘Amira you fuck up’


Ba shiri ta zaro ido ganin irin reply ɗin da yayi mata.
http://www.khadeejacandy.com.ng/2019/02/zagon-asa12_28.html




🌺🌺🌺 *ZAGON ƘASA* 🌺🌺🌺

_Wattpad @_
*KHADEEJA CANDY*

Click www.khadeejacandy.com.ng for your updated


*PAGE - 13*


Hankalinta ya tashi sosai, har ta kasa jin kiran da Namra take mata, sai da ta yi mata kiran kusan sau huɗu sannan ta amsa kamar a firgice ta juyo ta kalleta.


“Lafiya?”


Namra ta tambaya ganin yanayinta duk ya canja.
Ƙasarowa tayi kusa da ita ta dafa ta tana faɗin.


“Ba komai, Yaya ne yayi min text ina jin Ammy ba lafiya bari naje gida”


“Ko na raka ki?”


“A'a No yi zamanki da sauƙi ai”


Bata tsaya jiran abunda Namra zata ƙara cewa ba, ta nufu hanyar fita da sauri. Hankalin Namra sai duk ya tashi tana jin kamar mahaifiyarta ta ce, har ta unƙura zata tashi sai kuma ta koma ta zauna hango Maryam da tayi tafe ta doso inda take. Kusa da ita ta zauna ta aje hangout ɗinta gabanta tana ƙoƙarin cire hijabinta.


“Anty Namra yanzu shikenan kin yi watsi da karatun ki ko?”


Namra ta sauke ajiyar zuciya.


“Haba Maryam kina min wannan maganar kamar ba kisan halin da nake ciki ba?”


“Allah ya kyauta! Amman ai ke kika jawa kan ki, ya dai kamata ace kin fara yima kan ki karatun ta natsu, ba wai azo a zuga ki kawai ki hau kan layi ba”


“Maryam babu wanda ya zuga ni, kawai kisan bawa baya wuce kaɗɗararsa, dan Allah ki daina ganin laifin Amira”


“Ba laifi ta nake gani ba, amman dai ina tunatar da ke kiyi hankali da yarinyar nan, jikina yana bari babu alheri a abotar nan taku, dan ni tun ba yau na lura da irin shigo-shigo ba zurfi da Amira take miki, dan tana kishin ki”


“Amira bata da wannan Maryam baki fahimce bana”


“Bata da wannan, take kishin ki? Yai Amira tana baƙinciki ta ga kin ɗinka sabon kaya ita ata ɗinka ba, Amira tana baƙincikin ace kin fita zarra a jarabawa, Amira bata ƙaunar a tare ki a hanya ita ba'a tare ta ba, in yau kika saye sabon takalmi sai Amira ta siye, idan aBun farin ciki ya same ki a take Amira take canja fuska, idan wani abu kika samu sai tasan yadda ta shiga ta fita kika hallakarda da shi sannan hankalinta ya kwanta, ke duk baki lura da hakan ba?
Anty Namra ƙarshen duniya muke fa, kuma Annabi da kansa ya faɗa a cikin alamomin ƙarshen duniya akwai rashin amana da cin amana da rashin yarda, Wallahi kiyi hankalin da mutane.
In ma wani sirrin ki ne karki ƙara faɗawa Amira, dan daga lokacin da ke da kanki kika kasa ɓoye sirrinki a cikin cikinki, har kika faɗawa Amira Wallahi kamar kin faɗawa duniya ne”


Namra tayi shiru tana kallon yadda Maryam take tsire baki tana faɗin maganganun, zuciyarta na nazarin kalamanta. Ita kanta a yanzu tana zargin Amira tun daga abunda ya faru da ita, sai dai yadda Amira take nuna mata akwai Aminci a tsakanin su ya kan rikita zarginta.


“Forget about Amira, yanzu dai Abbah yace ki kawo Asim ze aura miki shi how do you feel?”


“I don't know, amman ina jin kamar ban kyautawa Abbah ba, kuma ba zai fahimce ni ba, idan kuma na kawo wani wanda ba Asim na aura Asim zai cigaba da kallo a matsayin mayaudariya, ban san yadda zan yi ba”


“Yanzu dai Uzair ya fasa auren ki, dan haka duk wanda zaki aura babu ruwan Abbah ba kuma ze karɓi wani excuse daga gare ki ba, kinga ƙara ma ki auri Asim ɗin, in yaso sai kiji da Abbah”


“Maryam ban san inda Asim yake ba, Mahaifiyarsa ma tace min bata san inda yake ba, saboda ni ya bar garin nan”


“Ƙarya take tace bata san inda yake ba, shi Asim ɗin yaro ne da zai gudu be faɗawa mahaifiyarsa ba? Baya gari ya akayi Amira ta ganshi?”


“Nima ban sani ba, tace min kiranta yayi a waya”


“Kin gani ko? Wannan Amirar munafukace. Ni zan taya ki nemansa, har gurin uwarsa zanje idan kuma tayi min maganar banza na ci mata mutunci”


“A'a ni dai dan Allah karki mata rashin mutunci, ki bita da lalama”


“Ke fa Anty Namra kina da matsala, mutanen duniya in ka sake sai su ci maka tuwo a ka, kawai idan mutum ya maka zuma sai ka masa wuta, idan kuma ya maka yayyafi sai ka masa ruwa”


“Nidai na ji amman ban da rashin mutunci kinji?”


Ta tsire baki gefe.


“Naji tashi mu shiga ciki, ni yunwa ma nake ji ganin Amirar yasa na shigo nan”


Miƙewar da Namra zatayi sai taji abu ya gangaro mata a ƙafa, tana ɗaga zagen taga jini. Lumshe ido tayi ta buɗe ta kalli Maryam dake kallonta sannan ta riƙa hannunta suka shiga ciki.
Suna shiga Maryam ta nufi kitchen, Namra kuma ta nufi ɗakinta, ta cire kayan jikinta ta gyara jikinta ta saka pad sannan ta saka wasu tufafin.


UZAIR POV.


Sai safa da marwa yake, hankalinsa ya kasa kwanciya, tun lokacin da Amira ta masa text ɗin shirmen data aikata. What if aikin ya dawo gareshi? Tun da malamin yace indai akayi aikin dole ne ya ci.
Najeeb ya dafa shi


“Uzair ka kwantar da hankalin ka mana”


“Haba Najeeb wane irin kwantar da hankali kamar baka san yadda abun nan yake ba, kuma kana ganin taje ta aika mana shirme, ban san abunda yake damun ƴar iskar yarinyar nan ba”


“Ka natsu mana sai mu kira malamin mu faɗa masa abunda yake faruwa”


Sai a lokacin ya zauna, tashin hankali ƙarara a fuskarsa. Kira biyu Malamin ya ɗauka, sai Najeeb yayi masa bayanin komai. Malamin ya daɗe yana jimamin abun sai tambayar yadda akayi suka yi wannan kwaɓar yake.


“Yanzu dai mu saurara nan da kwana biyu mu gani”


“Yanzu Malam babu wani abu da za'a iya yi, babu wata mafita?”


“Mafita ɗaya ce, a nemo kurciyar nan acire layar da aka laƙa mata, kasan kuma mun riga mun saki kurciyar kamunta yanzu ba abu ne mai yiyu ba, sai dai kasan ai da sunan ita yarinyar mukayi dan haka ku ɗan dakata tukuna mai yiyuwa ya iya kamata”


“Ko asa ta cire rigar?”


“A'a duk ta cire rigar ba tare da aikin ya shiga jikinta ba, zai iya dawowa, kasan lamarin iska”


“Okay toh mun gode”

Najeeb na kashe wayar Uzair ya miƙe tsaye yana faɗin


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah ka cece ni Allah”


Jafar ya aje wayar hannunsa ya kalli Uzair yace


“Haba be a Man mana, ai ko aiki zai dawo ba akanka zai koma ba akan Amirar zai koma”


Uzair ya kalleshi


“Amman ai ba ita tayi aikin ba”


“Easy Man ai ita tayi kuskuren, kirata muji yadda tayi wannan banzan shirmen”


Jafar na gama maganar, Uzair ya ciro wayarsa ya danna mata kira.




AMIRA POV.


Kuka take sosai, tun da ta baro gidan su Namra take kuka har ta iso gida. Bata bari Ammy taga shigowarta ba, sai kawai ta shige ɗakinta ta hau kuka baji ba gani. Ita kanta idan za'a tambayeta bata san dalilin kukan ba, ita dai tana jin kuka yana zo mata kawai.


Ganin Number Uzair ce yasa ta ɗauka ta kara a kunne.


“Amira taya kika yi wannan shirmen? Ban faɗa miki ba a son a samu matsala ba?”


“Ai tasa rigar”


“Toh Uban wa yace ki bari tasa ba tare da haila yazo mata ba? Wace irin mahaukaciya ce ke?”


“Yanzu idan ba a yi dai-dai ba me zai faru?”


“Ban sani ba”


Sai ya kashe wayar. A take zuciyarta ta soma raya mata Namra haukacewa zatayi. Kuma

Please Login or Register in order to submit comment