Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wannan kayan idan kun cire”


Dariya kawai suka yi, suka je suka ma Daddyn u sai da safe suka fice. Shi kuma ya mai da ƙofar ɗakin ya rufe ya nufo ta yana murmushi.


“Yanzu shi kenan, daga fitar su sai kuma ki ɗaure min fuska, ni da su waya fi cancanta da far'ar nan naki?”


“Su kasan ana canja miji ba a canja ƴaƴa ba”


Dariya yayi ya rumgumota.


“Haba ni da nazo miki da albishir kuma”


Ta tsire baki tana ƙoƙarin zamewa daga jikinsa.


“Wallahi da gaske na ke, nayi shawara zan fara baki 50k duk month, tun da ita Rashida aiki take, ina ganin kamar ban yi adalci ba idan na bar ki haka”


“Dan Allah da gaske”


Ta tambaya cikin murna da jindaɗi, sai kawai ta saki jiki ta rumgume shi.


“Yauwa yanzu da kika ji maganar kuɗi sai na samu rumguma ko? Ko kunya baki ji ba”


Ta rufe kanta cikin ƙirjinsa tana dariya.
Duk wannan maganar da Hilal yake Rashida ya tsaye jikin ƙofa tana jinsa, wani ƙashin baƙinciki ne ya taso ya zo yayi mata tsaye a wuya, har ta kasa jurar tsayi a gurin ta wuce ɗakinta.
Har ta cire tufafin da suke jikinta, tsanar Kalsoom sai ƙaruwa yake a ranta, gani take duk ta zo cikin gida ta hana ta tsukuni ta ƙauce mata miji. Tawul ta ɗauka ta shiga bathdroom tayi wankan tsarki sannan tayi na sabulu ta ɗora da alwalah ta fito. Ta rama sallah magariba sannan ta yi na Isha'i.


Sai kusan goma saura Hilal ya leƙa ɗakinta. Ƙiri-ƙiri tayi kamar bata ganshi ba, ta cigaba da chatin ɗin da take a waya. Shi kuma ya tsaya a kanta.


“Bayan kin dawo aiki sai kika sake fita baki faɗa min”


“Amman ai kasan idan ba aiki ba, babu abunda zai sake fitar da ni ko? Kuma na ga kai ka bani damar nayi aikin, ita wacan da yake ƴar gatan ka ce ai sai ka hanka mata albashi tana zaune a gida ko?”


Murmushi yayi mai sauti.


“Kalsoom bata nufin komai dake sai alheri, ki duba kiga yadda take kula da yaran nan, ke kanki baki kula da su haka, a ganin ki kema kan ki be ci ace kin yanka mata albashi ba, naga ke kina aikin ai”


“Ƙwarai aikin kam yanzu na fara saboda abunda mahaifina ya koya min kenan, be nuna min na zauna a nema a bani ba nima na san Freedom ɗina”


“Good of you, amman idan har aikin yana da rana a gare ki be kamata ki saka hannu ki ɗaukar min dubu ɗari uku ba ba tare da sani ba, bayan kuma babu nauyin da ban ɗauke ba na cikin gidan nan, kin san iya abunda na aikata a rashin ganin kuɗin nan?”


Cikinsa tayi da masifa tana kuka.


“Ka yi min duk abunda zaka yi Hilal, ka kira ni da ko wane irin suna ka siffanta ni da duk sunan da yayi maka a duniyar nan, saboda kayi amarya, daman haka halin ku yake a duk lokacin da kuka aure mune abun wulaƙantawa, mune banza mune wofi”


Kallonta yake har ta gama faɗan ta koma gefen gado ta zauna tana cigaba da kuka. Sai ya sassauta zuciyarsa, duk wani abu da yake ji sai ya aje shi gefe, ya zauna kusa da ita ya jata ya rumgume.


“Bana da niyar wulaƙanta ki dan na yi aure Rashida, i love you so much”


Ƙara narkewa tayi.


“Hilal ina kishin ka, ina kishin ka kwana da wata Mace ba ni ba, Hilal i can't deny it and i can't take it, please divorce her Hilal”


“I can't and won't, ita amana iyayenta suka bani, son da nake miki ba zai sa na rabu da ita ba a kan ki, ke ma kuma ba zan miki haka ba, so karki yaudari kan ki”


Ganin ba zata daina kukan ba, yasa ya ɗaga ta ɗaga jikinsa, ya tashi cikin rashin daɗin rai ya nufi ɗakin Kalsoom.




NAMRA POV.


Sun yi sa'ar samun likitan har ya duba ta, ya sanar mata ciki ne amman ta samu miscarriage, ya rubuta mata gani da allurai sannan ya bata gado. Sai bata yarda ya kwanta ba sai tace mishi sai taje ya faɗawa mijinta. A cikin asibitin ta siye wasu maganin nikan.
A bakin gate ɗin suka samu Napep, Namra kamar jira take, suna shiga ta fara kuka. Ita sam bata jidaɗin ɓarewar cikin ba, gashi har yanzu zugi mararta take mata.


Ba karamin ƙarfin hali Mardiya tayi ba, wajen bata haƙuri dan ita gaba ɗaya hankalinta ya tattara ya koma gida, zuciyarta sai yaye yaye take mata. Ita kanta tana jin bata kyauta ba idan har gidan Namra ya ƙone, sai dai bata da mafita sai wannan.


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ”


Ta furta a razane lokacin da mai Napep ya sauke su cikin jama'ar da suke gurin. Da sauri Namra ta buɗe idonta dake rufe ta fito daga Napep ɗin ta nufi gida a ruɗe.
Mardiya ce ta sallami mai Napep ɗin ta rufa mata baya, tana ta innalillahi. Haka Namra ta ƙira kusa mutane da suke tsastsaye suna kallon wutar, har ta shiga cikin gidan. Da sauri wani daga cikin yan fire service ya tare ta sai matan unguwar suka zo da gudu suka riƙe ta.
Wani irin fisge-fisge take take tana son ta kuɓuce ta shiga cikin wuta, sai ɗakinta take nuna musu tana wani irin kuka mai ban tausayi.


Wani irin tuma take tana direwa ƙasa, kamar sabuwar mahaukaciya. Sai kuma ta koma can gefe ta rumgume kanta, jikinta sai rawa yake kamar mai sabon fever.


“Allah na gode maka Allah, mijina ya kare, cikina ya ɓare yanzu kuma gidana ya ƙone, Allah ka sassauta min haka nan Allah, Allah ka yafe min na san ni mai yawan zunubi ce mai yawan saɓa maka Allah”


Wani irin ajiyar zuciya ta sauke sai jiri ya kwasheta, ta soma ganin mutane biyu-biyu sai ta jinginar da kanta, tana numfashi a hankali. Mardiya na can gefe tana kuka sosai, kamar gidan nata ne ya ƙone, idonta har ya kumbura ya daina hawaye.
Haka wutar ta ci ta cinye, ba a samu nasarar kasheta ba, sai da ta ƙone ilahirin gidan gaba ɗaya, ya rage saura BQ kawai. Har kuma lokacin Namra sama-sama take ganin mutane, komai ya zame mata kamar mafarki, yanzu kam bata da gabas bata da yamma, bata da madafa, bata da mafita sai ta Allah. Gashi babu abunda ya fita nata sai tufafin da suke jikinta.
A tunaninta kuɗin da Dillaliya ta kawo mata ya ƙone, ga sarƙarta ga tufafinta kayan ɗakinta da kayan kallo freezer da sauran kayan kitchen, yanzu bata da komai sai rai, gashi lafiyar jikinta ma bata isheta ba.


Mutane sun yi ta bata haƙuri suna nuna mata yarda da ƙaddara, da mata fatan Allah mai da alheri, a gidansu Mardiya ta kwana, ba kuma dan kwanan bachi ba, dan a zaune ta kwana, tana jinjina lamarin Ubangiji.
Da safe Mahaifiyar Mardiya ta siyo mata koko da ƙosai, Namra ta kasa sha, ta aika a siyo mata tea shima ta kasa sha. Sai tayi zaune jigum, tunani ya taru yayi mata tsaye a rai.


Tunanin yadda zatayi da Dillaliya, da kuma yadda zata faɗawa Asim gidansu ya ƙone, bata tunanin faɗawa Anty Amarya, saboda a ganinta sun juya mata baya, ita kuma ta ɗauki alƙawrin ba zata sake nuna musu tana buƙatar wani abu ba.


Sallamar Dillaliya sata ta razana sosai, kamar ance mata ga baƙon mutuwa. Sumi-sumi Dillaliya ta shigo ɗakin fuskarta ɗauke da damuwa da kuma tausayi.


“Allah sarki Baiwar Allah, haka Allah ka kawo miki wannan ƙaddarar ke kuma?”


Ta faɗa yayinda take ƙoƙarin zaunawa. Idon Namra ya cika da ƙwallah.


“Kin dai gani, duk abunda Allah ya kawo ba a iya guje mishi, Wallahi komai ya ƙone”


“Haka na ji ƴar nan, ai ni jikina duk yayi sanyi na haɗa ɗan jarin na miƙa miki har da kuɗin mutane gashi komai ya ƙone”


Ta fara hawaye. Dubu biyar ma Dillaliya jin su take kamar ranta balle har dubu ɗari uku da hansin.


“Ni ko yau ina zan samu wannan kuɗi, ba kaya ba kuɗi mutane ba haƙuri ne da su ba, yanzu wanda na karɓar wa kuɗin nan ba yafewa zata yi ba, nima ɗan jari masu son ganin baya na yau burinsu ya cika, na shiga uku na lalace”


Namra tayi mata wani kallo wanda ita ka ɗai ta san fassararsa.


“Allah satki Dillaliya, ke dubu ɗari uku kawai kika rasa, ni ko mijina ya karye cikina ya zube yanzu kuma gidan ya ƙone gaba ɗaya komai be fita ba, kuma yanzu ki zo kina min wannan maganar, ba sai kin yi lunƙe-lunƙe ba, ki kwantar da hankalin ki zan biya ki, sisinki ba zata yi ciwon kai ba Inshallah”


Namra ta ƙarasa maganar da kuka. Wani daɗi da Kunya ya lulluɓe Dillaliya a lokaci ɗaya, daman ita tana ganin alamu tasan Namra ƴar masu kuɗi ce, kuma haka da Namra tace ya ƙara tabbatar mata da zancenta. Sumi-sumi ta tashi tana share hawaye.


“Ba haka bane ƴar nan, Allah dai ya sassauta miki amman ba shine nufi na ba”


Tana ficewa Namra ta rafka uban tagumi tana tunanin rayuwarta. Babu wanda ta faɗo mata a rai sai Hajiya Saratu matar data taimaketa lokacin da Asim be da lafiya, sai dai zuciyarta bata yarda da zata taimaketa dan Allah ba. A ɗayan ɓangare na zuciyarta kuma Anty Amarya take tunani, su biyu nan sune kawai mafitar ta a rayuwa.


KALSOOM POV.


Kwana biyu nan ta miƙa lamarinta ga Ubangiji, nafila dare da Karatun suratul yaseen da Salma ta faɗa mata shi kawai ta sawa gaba.

Yau ma da wuri ta tashi ta shirya musu komai na karya. Amman Rashida bata tsaya karyawa ta fice, yara kuma tasa musu nasu a kula suka tafi makaranta.


Sai da ta sawa Hilal ruwan wanka yayi wanka sannan suka fito dinning sai tsokanarta yake.


“Ni duk gajiyar da ni, sai fama nake, Allah dai yasa ina da juriya ba zan iya zama da ke ba”


Ya kashe mata ido ɗaya, yana ƙoƙarin zaunawa saman kujera. Ita kam ido ta sakar masa tana kallon ikon Allah, daman yasan abunda zata faɗa ne shine ya rigata faɗa.


“Kai dai Allah be raba ka da abun magana ba”


“Ba wani magana sai gaskiya kema ai kin san ina ƙoƙari in ba haka ba ai sai abun yayi min yawa”


Dariya kawai tayi ta cigaba da haɗa masa tea. Shi kuma ya kwantar da kai yana kallon rigar bachinta dake buɗe.
Tana gama haɗa masa tea aka buga ƙofar falo, saurin miƙewa yayi yana faɗin bari na duba, dan nasan ki da shegen salo zaki iya cewa bari ki duba, har wani yaga halalina.


Kai kawai ta girgiza tana dariya, shima dariyar yake har ya isa gaban ƙofar ya buɗe.
Mai Gadi ne jikin ƙofar riƙe da wani farin abu kamar wasiƙa, ya miƙawa Hilal.


“Alhaji, gashi aka ce a bawa Auntie su Ulfah”


“Waya kawo?”


Doc. Ya karɓa yana tambaya.


“Wani ne a mota har ya tafi ma”


“Okay”


Ya mai da ƙofar ya rufe. Sannan ya juyo ya nufo dinning inda take Kalsoom take zaune yana faɗin.


“Ga saƙo aka ce a baki”


“Saƙon me?”


“Oho sai kin buɗe”


Sai da ya zauna sannan ya miƙa mata. Ita kuma ta karɓa da hannu biyu, ba tare da fargabar komai ba ta yage takardar.


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Da sauri ta miƙe tsaye tana zaro ido, sai hotuna suka faɗo tare da kofin tea dake gabanta.


“Subhanallah”


Hilal ya faɗa lokacin da idonsa ya sauka kan hotunan.






____________________________________________


#Share
#Comment
#Candy
#Blog
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng


*PAGE - 29*


NOT EDITED ⚠️


Shiru-shiru Mama bata aga an kawo musu karin safe ba, gashi har rana tayi kuma babu wani labari, ga yunwa tana ji ita da Asim.
Dan yauzu sauki ya fara zo masa yana son abinci sosai har fira ya kan yi sama-sama.


“Hajara tashi na baki kuɗin achaɓa ke je ki karɓa mana abinci wata ƙila na yanzu zata zo ba,marar lafiya kuma sai da abinci, wannan zunzunzun ba amo ba labari,
Ko tana nufin ba zata ake zuwa asibitin bane dan nayi magana?”


Ta ciro naira hansi ta miƙawa ƴarta Hajara.


“Ungo idan kin je ta baki na dawowa”


Da kallo Asim.ya bi ƙanwar tasa, sai da ta fice sannan ya kalli Mama yace


“Wallahi ko maƙiyinka ya faɗa a hali dana shiga sai an tausaya masa, ki duba ki gani ace ina sirikin su amman har yanzu ba su sake zuwa duba ni ba, ai ko wani na kashe musu sa duba ni tun da ƴar su nake aure”


“Hmmm ai Wallahi mutane nan basa son ka da alheri, su fa basu ƙi ka mutu ba, nifa ina zargin kamar ma da sa hannunsu a haɗarin nan da kayi”


“Nima haka nake tunani saboda lokacin dana je karɓar motar sai da suka sa Direban su, ya duba motar gaba da baya sannan aka ba ni key ɗin, sannan idan har ba plan ba taya daga haɗari mota zata kama da wuta haka kawai”


“Ato nifa na faɗa maka ba su ƙi ka mutu ba, sai ƴarsu ta auri wanda take so, daman can ba a banza aka baka ita ba”


“Amman Namra sai naga kamar tsakani da Allah take so na”


“Hmm ai wannan hidumar da tayi maka, saboda itace silar komai shiyasa tayi maka, kuma yanzu kaga ta kama kayan ɗakinta ta sai da dan ace kai ƙa canye komai sai a fara cewa ta sai da komai dalilinka, ai ba zata rasa kuɗin da za'a maka komai a bankinta ba amman ta zaɓi ta siyar da kayan ɗakinta ai kasan da walakin goro a miya”


“Kayan ɗakinta ta siyar?”


Ya tambaya a wahale dan ciwon kan ya fara dawo masa.


“Eh ba shine ka ji jiya ina magana ba, har kake ganin laifina”


Shiru yayi be sake magana ba, sai ciwon kan yake saurare.




NAMRA POV.


Ta ci kuka sosai har sai da ta goɗe Allah, ba tare da ta bari kowa ya gani ba, dan wuni tayi a ɗakin su Mardiya, duk wanda ya zo mata tanzanko sai yayi mata a cikin ɗakin ko kuma daga bakin ƙofar.


Guraren Uku da rabi Hajara ta shigo ɗakin da sallama, Namra ta amsa mata murya can ƙasa-ƙasa.


“Wa'alaikissalam Hajara”


“Na'am Anty naje gidan naga duk ya ƙone aka ce min kina nan”


“Wallahi jiya ne muna dawowa daga asibiti muka tarar ana kashe wutar”


“O'o wannan abun be yi daɗi ba, nima Mamace tace na zo na karɓo abinci tun safe bata gan ki ba shiru, ashe abunda ya faru kenan, Wallahi ba mu sani ba”


Ta faɗa cike da tausayawa.


“Ina Asim ɗin yaji sauƙi?”


“Ya samu sauƙi sosai ɗazu ma har fira muke yi da shi, har shi ma yace na zo na karɓa abincin”


“Bari na baki ƙuɗi ki siya masa na hanya”


Ta tashi cikin rashin kuzari, suka fita a tare daga cikin ɗakin. Kular Maman Mardiya ta ara tana cikin wanke wa, wata maƙociyar su ta shigo tace kiran Namra.


“Kin yi baki masu gida sun zo su duba gidan su”


A take ta aje wankin kular da take ta gyara tsayin Hijabinta ta fita. Manyan motoci ne fake a ƙofar gidan.
Cikin faɗuwar gaba ta nitsa ta shiga cikin gidan tana musu sallama.




“Wa'alaikissalam ke ce matar gidan?”


Hajiyar ta tambaya tana cire gilashin dake zaune a idonta.


“Eh Nice ance masu gida sun zo”


“Eh ina mai gidan na ki?”


“Yana asibiti ba shi da lafiya ne”


“Ayyah so sorry, amman kin san musabbabin tashin wutar ne?”


“A'a wallahi nima asibiti naje ko da na dawo na tarar wuta na ci”


“Allah sarki Allah ya maida alheri, daman mun zo ne mu duba ance muna anyi wuta”


Ta faɗa tana picking ɗin wayar dake hannunta.


“I'm my way Abdool, har na ga gidan ma”


Sai kuma tayi dariya, ta kashe wayar. Tasa hannu a jaka ta ɗauko kuɗi masu ɗan dama ta miƙawa Namra.


“Ga wannan Allah ya tsare gaba”


Har ƙasa Namra ta ɗuka mata.


“Na gode Allah saka miki da alheri”


Murmushi farar Hajiyar tayi


“Ba komai”


Har gaban mota Namra ta raƙa ta ta shiga motar ta wuce, sannan Namra ta koma gidan ta ɗauki kular da plates da cibi, suka fito ita da Hajara.


A bakin titi ta siya musu shinkafa da miya da nama na 1k. Sannan suka tari Napep suka hau.
Daga ita har Hajara sululu suka shiga ɗakin, kama kamar ita dake ta sun-sun da kai bata son a ga kumburin dake fuskarta.


Sai da ta gaisa da Mama sannan ta nufi gurin da Asim yake ta zauna, yana kallonta.


“Ya jikin ka?”


“Alhamdulillah”


“Likitan ya duba...”


Jin abunda Hajara take faɗa yasa ta kasa ƙarasawa. Mama ta ɗora hannu a ka, tana faɗin


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Asim kuma ya kalli Namra cike da tashin hankali. Ita kuma babu abunda take sai kuka.


“We lost everything Asim, i lost my baby, shine naje asibiti ko da na dawo na tarar gidan ya ƙone”


Rumtse ido Asim yayi, zuciyaraa ɗauke da abubuwa biyu, jindaɗin ɓarin da tayi, da kuma baƙincikin ƙonewar da gidan yayi.
Ringing ɗin wayar Asim dake hannun Mama ne yasa ta share munafukan hawayenta ta danna picking tana kara wayar a kunne.


“Wa'alaikissalam.
Lafiya ƙalau
Alhamdulillah”


Shiru ta ɗan yi kamin tace


“Allah sarki. Namra karɓi ga Maman ki”


Hannu Namra ta kai ta karɓa sai ta fice daga ɗakin. Mama ta kalli Asim cikin ruɗu tace


“Ibrahim idan kaji sauƙi ka rabu da yarinyar nan, ina ganin babu alheri a zaman auren ku, wannan irin bala'i haka”


Shi dai be ce mata komai ba, shi ta kansa yake abunda duk yake tunanin zai zame masa alheri yana ƙoƙarin koma masa sheri.
Yanzu da wannen zai ji ciwon jikinsa ko wannan rashin da suka yi?


“Kuma ina ganin abunda yafi kawai ku koma gida, a can ma dole ta samu wani abu saboda a gaban iyayenta take”


Har lokacin be ce komai ba, Hajara tace


“Ni Wallahi duk ta bani tausayi”


“Ai ba itace abun tausayi ba, Yayanki ne shi da ba shi da kowa sai Allah ita kau har iyayenta suna da abun hannun su”


“Ita ai da tausayi Wallahi”


“Hmmm Allah dai ya kyauta kawai”




Namra na fita ta ƙara wayar a kunne tana dda ƙoƙarin gyara muryarta kar Anty Amarya ta gane tana cikin damuwa.


“Anty”


“Na'am Namra y jikin mijin na ki”


“Ya ji sauƙi”


“Allah ƙara lafiya Wallahi Abbah kin ya hana na dawo duba shi, ko jiya sai da nayi masa magana sai ma masifa ya riga min, Abban ki ya kira ki?”


“Ba komai ai yaji sauƙi, be kira ni ba wayana ya faɗi ban sani ba ko ya kira”


“Har yanzu baki daina halin ki na sakarci ba ko? Ya faɗi ko dai kin siyar?”


“Wallahi faɗuwa yayi”


“Namra ki yi hankali da mutane, ba kowa ne yake son ya gan ka a cikin alheri ba, wani yana baƙincikin yaga kana jindaɗi, wasu fa hassadarsu ba ƙarama bace, kowa abunda yake ƙoƙarin yi ya ture ka daga jindaɗin shi ya shiga, ko kuma ya ture ka duk ku rasa, ba kowa bane zai so ki tsakani da Allah ba, idan kina da shi kowa naki ne, sai ranar da kika rasa komai zaki gane masu son ki da gaskiya


Wani ƙiyayyar tasa a ɓoye take ba zaki taɓa ganewa ba, haka zai ta miki zagon ƙasa har sai ya ga kin rasa komai sannan hankalinsa ya kwanta, dan haka kiyi tunani sosai da duniya, idan baki da hankali mutanen duniya za su miki shi, ki rage damuwa a ran ki ki sawa ran ki sassauci”


“Na gode Anty”


Ta faɗa har cikin ranta, kalaman Anty sun mata daɗi, sai dai tasan ba kowa Anty ke nuna mata ba, sai Asim dan tana tunanin kamar da biyu ya aureta, gani take har yanzu Anty bata yarda da Asim ba.


“Allah ya ƙara masa lafiya, na kira wayarki ban samu ba, shine Maryam ta karɓo min number Asim”


“Eh ai naga line Maryam ne, na gode sosai”


“Tau Sai anjima”


“Okay




Daga haka suka yi sallama. Wayar na yankewa wa Namra ta tsara text ta tura mata Anty Amarya a wayar Maryam.


“Maryam... Zo ki karɓi wayar ki”


“Na'am”


Ta aje system dake jikinta, ta taso ta nufo ɗayan ɓangaren inda Anty Amarya take. Tana karɓar wayar text na shigo, Anty Amarya bata kula ba, ta miƙa mata wayar ta nufi gurin sha'aninta.


_Anty ina cikin matsala, bana iya faɗa miki a waya nasan faɗa zaki min, dan Allah ki taimaka min da kuɗi ko kaɗan ne_


Maryam ya gama karanta saƙon taja wani dogon tsaki ta danna deleted ta goge saƙon.


“Ai fa kullum haka zai riƙa saki kina yi, tun da yaga be samu abunda yake so ba, kai mutanen duniya nan da abun haushi da mamaki suke, ala dole dan auri yar masu kuɗi kai sai kayi arziki, to sai kaje ka ci ubanka, ya mayar da ita saniyar tatsa”


Ta koma mazauninta tana mai jin haushi Namra da Asim ɗin.




KALSOOM POV.


Hilal na kallonta ta girgiza masa idonta da hawaye.


“Wallahi ban aikata ba, ban san wannan mutumen ba Wallahi”


Hannu Hilal ya kai ya ɗauki hotunan yana kallo. A-uzubillah hotunan babu kyau kallo, Kalsoom ce tsirara ita da wani, wani gurin yana kissing ɗinta wani gurin kuma tana kissing ɗinsa.
Ɗaya bayan ɗaya ya riƙa duba hotunan har ya gama sannan ya kalleta yace


“Kin san wannan mutumen”


“Wallahi ban san shi ba, ban taɓa ganinsa ba”


Ta faɗa da kuka.


“Daga ganin wannan ma ai haɗi ne, i trust my wife's ba zaki aikata irin wannan abun ba, duk yadda akayi wannan abun shirya sa akayi”


Ta ƙara fashewa da kuka


“Wallahi sheri ne kawai, na rantse da Allah ban taɓa ganin wannan mutumen ba”


Shiru Hilal yayi kamar mai nazari.


“Ina suka samu hoton ki?”


“Wallahi ban sani ba, dan Allah ka yarda da ni Wallahi sheri ne”


“Na yarda sheri ne, daga gani ma ai kasan haɗi ne, daɓ ga fatar fuskar ta banbanta dana jikin hoton, kuma miyasa ba a kawo lokacin da bana nan ba, sai da ina nan? za a iya haɗa irin wannan hoton a computer? But i can't believe is taya suka samu hoton ki?”




“Wallahi ban sani ba”


“Baki sani ba kamar ya? What kind of nonsense is this? Aljani za a turo ya ɗauki hoton ki ko me?”


Durƙushewa tayi ƙasa tana kuka.


“Wallahi ban sani ba Hilal na rantse da Allah ban aikata ba”


“Naji baki aikata ba, faɗa min ta ina suka aka samu hoton ki?”


Ya faɗa a tsawace irin zuciyarsa ta fara kawowa ɗin nan.


“Wallahi ban sani ba, ni ban turawa kowa hotona ba”


Ɗuƙawa yayi a hasale ya kwashe hotunan ya nufi ɗakinsa da su. Wani irin zugi zuciyarsa ke masa, baƙin kishi ya taso masa.
Haka ya tiƙa duba hotunan kamar wanda zai haddace su, shi dai what he believe Kalsoom ba zata aikata haka ba, sai dai kuma kansa ya ɗaure har yana jin tunaninsa na ƙoƙarin canjawa.


Bedside drawer sa ya buɗe ya zuba hotunan ya rufe, sannan Shirya cikin ƙananan kaya ya feshe jikinsa da turare ya ɗauki atms ɗinsa ya saka a aljihu da wasu ƴan canja, sannan ya ɗauki wayarsa da keys, ya fice daga ɗakin fuska babu annuri.


Sheshekar kukanta ya ɗago da hankalinsa i zuwa gareta, ashe duk tsawon lokacin tana a gurin tana aikin kuka, jikinsa ya mutu yaji ba daɗi ganin kamar shine silar hawayenta. Ƙarasawa yayi kusa da ita ya ɗafa ta


“Kalsoom Calm down, nima fa wayayyen mutum ne nasan za a iya haɗa wannan, amman kin ƙi ki bawa zuciyata damar yarda da hakan”


Ɗagowa tayi ta kalleshi tana kuka fuskarta da majina nashe-nashe.


“Wallahi ban sani ba, ni ban turawa kowa hoto na ba”


“Kina da grp ɗin da kika chat da maza ko?”


Ta ɗanyi shiru tana tunani.


“Grp ɗaya ne, shima kuma na koyon sana'ah ne, kuma ban taɓa magana a grp ɗin ba Wallahi, Instagram ɗina da Facebook tun da nayi aure ban sake hawan ko ɗaya ba Wallahi”


“Good indeed, kina instagram ba? Kina facebook?”


“Amman tun da nayi aure ban sake shiga ba”


Zaunawa yayi kusa da ita yana cire password ɗin wayarsa.


“Ba ni handle ɗin ki”


“Kalsoom_Miss-Arewa”


Instagram ya shiga yayi searching sunanta, sai ga account ɗinta. Yadda ya riƙa ganin hotunan ta sai wani baƙin kishi ya motsa masa.


“Duba nan, yanzu miye amfanin waɗannan hotunan? Kina tallar kan ki kamar ba mace ba, miye abun burgewa a sakin jiki

Please Login or Register in order to submit comment