Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sameera tana mata kallon zolaya. Zata ƙara cewa wani abu Hajiya Barau ta shigo bakinta ƙumshe da sallama. Duk haɗa baki sukayi gurin amsa mata, Namra ta saukar da kai tana gaishe ta.


“Lafiya ƙalau, Amarya ya tashin ku?”


“Alhamdulillah, ya gajiya”


“Gajiya ta bi lafiya, muna ta sauri a kawo muku breakfast, sai angon yake ce min ai kun karya”


“Eh da safe ne ya haɗa mana tea”


“Toh ai yayi kyau”


Juyawa tayi ta koma falo, Sameera ta bita tana nuna mata abu a wayarta. Sai ya rage daga ita sai Maryam da Aisha. Maryam ta ciro waya a jakarta sabuwa ta miƙawa Namra.


“Gashi inji Anty tace na baki, akwai layi a ciki”


Da murna Namra ta karɓa


“Wayyo Mamana ta kai na”


Cikin zumuɗi ta buɗe kwalin kwayar iPhone 6+ ce golden color yayi kyau sosai. Rumgume Maryam Namra tayi tana rawa.


Sai kusan azahar sannan su Hindatu da sauran mutanen suka ƙaraso. A lokacin ne Hajiya ta shigo ɗakin tayi ma Namra jan kunne akan zamantaewar aure da haƙuri, nan ma kuka Namra tasa mata, bama kamar lokacin da suka fito za su kama hanya. Tayi kuka sosai kamar ranta zai cire, a take taji kewarsu ta kama ta, sai duk taji kamar ta bisu. Tana tsaye bakin gate tana kallon motarsu har sai da ta daina hangota sannan ta dawo cikin gidan da sabon kuka.


Asim kan be dawo ba sai yamma, ya shigo tare da wasu dangin Babansa da suke Bakori, kallo kan kallo suke sun daga kan gidan zuwa kayan da suke cikin gidan.
Da far'ah Namra ta tarbe su, ta zuba musu abincin da Hajiya ta kawo mata ɗazu, waina ce da miya sai doya da ƙwai, sannan ta kawo musu ruwa. Sai daf da magariba suka tafi, ƴar fitar da Asim yayi ya rakasu ya dawo duk tsoro ya kamata tun da bata saba zama ita kaɗai ba a gida.


Ko da ya dawo tana tsaye bakin ƙofar falon tana jiransa, da murmushi ya riƙa hannunta, ya lago ɗayan hannunsa a ƙogunta suka koma cikin falon. A tare suka zauna saman kujera maƙalle da juna

“Aiko.kina da aiki duk kika sakawa ran ki tsoro dan ke kaɗai zaki riƙa rayuwa a cikin gidan nan ƙara ma tun wuri ki cire tsoro a ranki”


Maganar yake yana kallon ƙirginta, rigar lace ce a jikinta, kuma kalar ɗinkin da aka mata ya bayyana breast ɗinta. Ita kanta ta lura da yadda yanayinsa ya canja, hakan yasa ta tashi ta nufi da jimmar shiga ɗaki. Sai yayi sauri riƙe hannunta.


“Ina zaki je?”


“Ɗa... Ɗaki”


“Okay”


Sai ya tashi tsaye yayi mata side hug suka nufi ɗakin tare, har suka isa ɗakin mazaunanta yake shafawa, tana zaunawa sai ya kwanto mata saman jikin ta yadda breast ɗinta zasu shafi ƙirjinsa, ya kai ɗayan hannunsa yana shafa ta.


Lumshe ido tayi ta buɗe tana murmushi, sai ta haɗe bakinta da nashi, duk yadda tayi ƙoƙarin abandoned na ƙin yarda sauri yarda da shi sai ta kasa, saboda yadda ya kashe mata jiki, ga kuma irin kayan mata data sha tun jiya suke damunta, a take ta shiga mayar masa da martanin irin saƙon da yake aiko mata.
Basu samu kansu ba sai kusan asuba. Basu yi bachi daya kai minti ashiriba aka kira sallah asuba, shi ne ya riga ta tashi ya shiga bathroom yayi wanka tsarki sannan ya zuba wasu ruwan yayi alwala. Sai da ya canja ya saka jallabiya sannan ya tashe ta dan tayi sallah.


Daker ta unƙura ta tashi zaune, har ta samu ta ɗauki zanenta ta ɗaura sannan ta tashi tana wata tafiya kamar wanda aka ɓarewa kafafu ta nufi banɗaki.


Shi dai da kallo ya bita zuciyarsa cike da zarge zarge, sam shi be ga alamun budurci a tare da itaba, jinin da aka ce ana ganin idan anyi sex da virgin shi be gan shi ba, an faɗa musu wasu har kasa tafiya suke amman ita gashi har ta kai kanta banɗaki.
Kuma the way da take mayar masa da kiss da yadda take romance ɗinsa ya nuna ta taɓa sanin wani namiji kamin shi, daman yasan za'a rina, zargin mahaifiyarsa ya zama gaskiya.


A take wani ƙololon baƙinciki ya taso masa, yana ayyana irin cin amanar da Namra tayi masa, zuciyarsa na nuna masa tayi masa zagon ƙasa, shi take son ta yaudara.
Har sukayi sallah suka gama be kalli inda take ba, har sai da ta gama addu'o'inta sannan ta gaishe shi cikin kunya. Duk wani abu da yake ji a zuciyarsa sai ya dannesa ya ƙirƙiro far'ah da murmushi ya yaɓa a fuskarsa.


“Lafiya ƙalau Amarya, ya gajiyar jiya?”


Tayi saurin sauke kanta, tana mai jin kunya, shi kuma ya watsa mata wani kallo ƙasa-ƙasa, zuciyarsa na ayyana masa abubuwa ƙala-ƙala.
Tashi yayi ya je ya siyo musu kayan tea, ita kuma ta hau gadon ta kwanta saboda ta gaji da yawa. Shi ya haɗa musu tea kamar jiya, har yayi ya gama tana bachi abunta.


Bayan ya kawo kayan tea falo wayarsa tayi ringing, ganin number mahaifiyarsa yasa ta fita daga harabar falo gaba ɗaya, ya nufi can bayan kitchen sannan ya ɗaga wayar.


“Mama ina kwana”


“Lafiya ƙalau Ibrahim ya gida?”


“Lafiya ƙalau”


“Kina lafiya dai ko?”


“Lafiya ƙalau muke, ina su Amma?”


“Kowa lafiya ƙalau, nace ba a aiko da komai ba ko?”


“Eh kin san ai yau kwana biyu da auren a ɗan jira tukuna kuma ko zasu aiko a nan gida zasu kawo sai ku aiko mana ko?”


“Eh toh haka ne, kasan dashen da aka shiga ne jiya ta aiko mana”


“A ɗan jira dai Mama na san suna kan hanya”


“Toh Allah ya taimaka, amman dai karka yi wasa da kuɗin nan ana kawo su ka samu wata sana'ah babba ka riƙa”


“Haka zan yi ai, ko abokaina haka suke cewa”


“Toh Allah ya taimaka, ina Namra ɗin take ne?”


“Bachi take”


“Toh idan ta tashi a gaishe ta”


Daga haka suka yi sallama, sai ya dawo falon ya cigaba da haɗa tea, sannan ya shiga ya tashe ta.
Sai da tayi brush shima yayi sannan suka dawo falo suka karya. Bayan sun gama ya kwashe kayan ya kai kitchen, ita kuma ta shiga kiran wayar Anty Amarya suka gaisa.
Kowa dai da ta kira a gida har Hajiya Barau, sannan ta kira Abbah, kira biyu tayi masa be ɗauka ba saboda sabon layi ne, sai a na uku yayi picking, be wani sake sosai ba sama sama suka gaisa, sannan ta kashe wayar.


Duk tsawon lokacin data ɗauka tana gaisawa da ƴan'gidan su Asim na kusa da ita yana lalabenta, tana aje wayar ya shiga saka mata hannu ƙasanta. Sanin abunda yake nufi da ita yasa ta unƙura ta tana tureshi, cikin yanayin damuwa take masa magana tana son ya fahimceta


“Asim, not now please, Wallahi na gaji kuma har yanzu zafi nake ji”


Kallonta kawai yayi ba dan yana da niyar fasa abunda yake yi ba, idonsa sun rikiɗe sun canja sosai, sai wani numfashi yake.
Ita kanta tasan a yanzu ko da wane yare tayi masa magana ba ganewa zai yi ba, a dole ta ƙyaleshi ya riƙa wasa da ɓangare jikinta, kamin ya jata su koma ɗaki.


Har yayi abunda zai yi gama, be ji ya gamsu ba, ita kuma duk ta ƙosa ya fita ma ya bata ɗakin, da ita kaɗai tasan irin azabar da take ji. Daker ta samu ya rabu da ita, ta tashi a wahale tayi wanka dan ta karanta ta gani kuma ta sha ji a wa'azi ana faɗar cewa ba kyau ka kwanta bachi da janaba a jikinka, ko yaya ne ƙara dai kayi wankan. Ta gasa jikinta sosai da sosai sannan ta fito kamar da rarrafe ta dawo bedroom ɗin. Ko tufafi bata tsaya sawa ba ta hau saman gado, sai bachi.




KALSOOM POV.


A cikin ƴan kwanakin nan kwata-kwata ta rasa gane kan mijinta, duk yabi ya birkice mata kamar ba shi ba, abu kaɗan sai ya hauta da faɗa, ko kuma yayi ta haɗe mata fuska yana nuna baya son tana zama kusa da shi. Sai dai a ɗayan ɓangaren ta samu sassauci gurin Rashida yanzu kan zamansu babu laifi tana ɗan sakewa da ita, har ma tayi mata godiya a wani lokacin.


Yau ta kama weekend Rashida bata da aiki, kuma Doc yau a ɗakinta yake. Sai ta tashi tun da asuba ta haɗa musu breakfast, sai ta gama shirya komai sannan yaje ta tasheshi, ta shiga ɗakin Kalsoom ita ta taso ta.


Da gangan Rashida ta ɗauki dinner set mai plantain da kuma mai kifi ta aza gaban kujerar Kalsoom.
Sannan ta shiga haɗa masa tea dan tuni ya iso gurin yana duba chat ɗinsa na whatsapp. Har Kalsoom ta iso gurin ta zauna be kalli inda take ba, gaisuwar da tayi masa ma can ciki ya amsa mata still be kalle shi ba.


Rashida na lure da yanayin Kalsoom da Hilal zuciyarta cike da shauƙi, sai dai a zahiri sai tayi kamar bata gani ba, ta hidimar haɗa masa tea kawai take.


“Maman Rafiq miƙo masa plantain gata nan a gabanki”


Ta faɗa tana dire masa tea ɗin a gabansa. Ba tare da tunanin komai ba Kalsoom ta ɗauki kwanon ta dire masa a gabansa. Ta miƙa masa birede, sai a lokacin ya samu damar aje wayar har ya kalleta, sannan ya miƙa hannu ya karɓa. Yana buɗe kwanon yaga kifi sai yaja wani dogon tsaki ya kalleta.


“Ace ki miƙo min plantai sai ki bani kifi kifi kika san ina ci ne?”


Bata iya cewa komai ba, sai Rashida ce tayi magana.


“Haba Doc toh ai kwanukan biyu ne bata san wannenen a ciki ba”


Kallonta kawai yayi ya tashi a hasale ya nufi ɗakinsa. Daman haka ya koma mata abu kaɗan yasa shi zuciya indai ita ce tayi masa abu. Rashida taja wani dogon numfashi tana kallon Kalsoom da idonta ke ƙasa


“Tashi ki bi mijinki mana, haka halinsa yake sai kin yi haƙuri, nima fama nake da shi”


Murmushi Kalsoom tayi ta nuna mata kamar ba komai.


“Fushi fa yake da ni, dan nace masa ina buƙatar hutu, shine tun ranar yaƙi ya sauƙo”


Ta faɗa tare da tashi ta nufi ɗakin nasa. Hakan da tace ya ɓata ran Rashida kuma ya dagula mata lissafi.
Kwance ta tarrada da shi ya lumshe ido yana dafe da kai.


“Doc...”


Buɗe ido yayi ya kalleta, sai ya tashi zaune ya zaunar da ita.


“Sorry for what i did earlier, i just that... ”


Sai kuma yayi shiru. Hannunsa ta riƙa tasa yatsunta cikin nasa.


“Doc idan akwai abunda nayi maka kayi haƙuri kasan ɗan'adam ajizi ne, amman be kamata ace kullum kana fushi da ni ba, a zamantakewa kullum tattauna ake so da fahimtar juna, idan har wani abun nake maga kamata yayi ka faɗa min zan gyara inshaAllah”


Rumgumota yayi jikinsa.


“Baki min komai ba, kawai ina abu ne a ciki na mai ƙarfi, irin ii can't control myself when I'm angry at you, I'm sorry too”


Lafewa tayi jikinsa kamar wata mussa, sai toshe hanci take, dan warin turarensa yana son sata a mai. Duk yadda tayi ƙoƙarin daurewa sai ta kasa saboda aman daya ci ƙarfinta, da gudu ta tashi ta nufi bathroom ɗinsa. Sai ya rufa mata baya da sauri yana tambayar lafiya.


Amai ta riƙa kwararawa ba ji ga gani kamar zata amaye hanjinta, gashi komai bata ci ba da safen nan. Har tayi aman ta gama yana riƙe da da ita yana shafa bayanta.


Sai da ta gama ya wanke mata bakinta, sannan ya riƙota suka fito yana mata sannu.






__________________________________________


Share it please I'm busy 🙌


Best regards 💖
Khadeeja Candy 🌺
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng




*PAGE - 22*


NOT EDITED ⚠️


Yau kusan two weeks kenan, babu gara babu labarinta. Sosai da sosai hakan ya dami Asim, sai dai ya ɓoye maitarsa, be yarda ya nuna mata komai ba. Ya kan yi ƙoƙarin siyo duk wani abu na buƙata wanda za'aci ko ayi amfani da shi a gidan. Sai dai duk tsawon wannan satin biyu Namra a wahale tayi su dan kullum yana manne da ita, bata da wani dogon hutu indai yana gida.


Bayan sun gama cin abinci ya aje Spoon ɗin hannunsa yana sauke ajiyar zuciya. Kallonsa tayi dan ta lura da yadda yanayinsa ya canja.


“Lafiya dai?”


Ya ɗan kalleta kaɗan ya ɗauke kai yana ɗan murmushi, fuskarsa na nuna alamun damuwa.


“Ba komai”


“Haba Hubby ai ni da kai yanzu mun zama ɗaya, ya kamata ace damuwarka ta zama nawa, babu wani ɓoye-ɓoye”


“Wato bana son nayi maganar ne kiyi mata wani ɗauka, wata ƙila ba zaki fahimce ni ba”


“Idan ban fahimce ka, wa kake tunanin zai fahimce ka? A tunanin ka idan ka ɓoye min damuwarka zan jidaɗi ne?”


Tashi yayi daga ginciren da yake ya gyara zamansa yana tsara kalamanta, ta yadda zasu zaunu a ƙwaƙwalwarta.


“Namra ina gudun ki shiga cikin irin rayuwar ta ne, kin min abubuwa da yawa, zuciyana bata da muradi illah na kyautata miki. A kullum tunani ina zan zam sama mana mafita muyi rayuwar jindaɗi, sai dai gaskiya I'm scared”


Sai yayi shiru be ƙarasa ba yana auna yadda kalamansa zasu kamata.
Ita kuma sai ta tambaya zuciyarta cike da shauƙin kalaman nasa.


“Scared of what?”


“Namra ba ni da wani aiki ko sana'ah mai ƙwari da zan iya riƙe ki da ita, ƴan kuɗi dana ke tunanin zasu ishe ni na kama sana'ah da su na kama hanayar gidan nan 50,0000 per year dan kawai na burge ƴan'uwanki da ke kan ki, nasan ke kika bada kuɗin amman naso nayi saving ɗin su dan mu samu wata madafa, sauran da suka rage min kuma gasu muna cin abinci da su kamin Abbah ya yi mana aike”


Ta ɗan ji babu daɗi da kalmar ta fito daga bakinsa, kusan kullum da tunanin take kwana take tashi, na rashin garar da Abbah yayi mata, a tunaninta hakan da Abbah yayi mata ya mata ne dan ta auri Asim, tun da ba haka yake ma sauran ƴaƴansa ba, ita kam ya kasa sai mata girma.


Can ƙasa-ƙasa ta fara magana, zuciyarta cike da rauni.


“Abbah ba zai aiko mana komai ba, da zai aiko da yanzu ya kawo mana ai, sai dai mu yi tunanin wata mafitar”


Sosai da sosai gabansa ya faɗi, kalamanta sun haddasa masa ciwon kai, har zufa na ƙoƙarin karyo masa. Janta yayi jikinsa ya rumgume.


“Toh Allah yayi mana mafita, ai Abbah ya gama mana komai tun da ya yarda na aure ki, Allah dai ya ƙara masa nisan kwana da ƙyaƙƙyawar rayuwa”


“Ameen”


Ta faɗa tana shafa rigarsa.


“Amman yanzu wace sana'ah kake gani yafi? Nifa da zaka bi shawarana da ka koma makaranta, ka cigaba da karatun ka”


“Bana son karatun nan a yanzu kwata-kwata ya fita rai na, na fi son sana'ar da zata riƙa kawo min ƙuɗi sosai ta yadda zan riƙa kyautatawa matana”


“Wace sana'ah zaka yi?”


“Wai da naso na kama wani shago dake nan Uguru Plaza na zuba atamfa haka da lace da shaddodi na gwada na gani, na ma yi maganar shagon dan akwai wani abokina daya ce babansa yana ba da rancen kuɗi ko nawa kake so kayi sana'ah kuna raba riba, toh shine nake son na masa magana”


Ɗagowa tayi ta kalleshi, damuwa ƙarara a fuskarta.


“Kamar nawa zaka kashe?”


“Zai kai 1.5 million, har kuɗin hayar shagon, indai ana son a saka kaya masu kyau”


“Tau me zai hana na siyar da motana sai na...”


Bata ƙarasa ba yaja wani dogon tsaki, ya tureta daga jikinsa ya tashi ya nufi ɗakin. Da sauri ta rufa masa baya tana karantar yadda ransa ya ɓace nan take.


“Kuɗin ba zasu iya ba ne?”


Ta tambaya lokacin data kunna kai cikin ɗakin. Sai ya juyo kamar a fusace yace


“Ban taɓa sanin baki da wayo da hankali ba Namra sai yau, da badan na sanki ba da sai nace shaye-shaye kike yi, taya zaki ce a siyar da motarki saboda na kama sana'ah? So kike zargin da mutane suke min ya tabbata gaskiya ko? Daman ance na auri ki ne dan dukiyarki, dan Allah dan Annabi ki taimaka wajen shanye raɗa da riƙe amanarki”


Sai yanzu hankalinta ya kwanta, data ji dalilin fushi nasa. Murmushi tayi tasa hannyenta ta laƙamo wuyansa tana kallon hawayen da suka cika masa ido.


“Bana nufi komai sai alheri, kai kan ka yanzu ai abun kunya ne kaje wani guri neman rance bayan ni ina da hanyar samo maka wannan kuɗin. Zai zame kama abun magana ace kana angonka kaje wani guri rancen kuɗin da zaka yi sana'ah, kuma ni Wallahi ba zan faɗawa kowa ba.


Nasan motar zata yi 2.5 ko ma 2 million, kaga idan ka kama sana'ah sauran sai mu siye abinci da sauran kayan gida, ni kai na ina buƙatar ƙuɗi a yanzu”


Kai ya girgiza mata ya cire hannayenta daga wuyansa.


“A'a kima daina wannan maganar dan Allah, kin san ko kuɗin da kika bani na haɗa lefe sai da nayi baƙinciki karɓar su? Nayi nadama sosai da zuciyata ta yaudareni na karɓi kuɗin”


“Amman ai baka da wata mafita Asim, idan ban baka kuɗin ba a ina zaka samo? Wannan ma ai dole ka karɓa”


“Da baki bani ba, da dole zan nemo mafita a duk inda take, ko wane hali zan iya shiga dan na samo kuɗin aurenki”


“Wannan ma ni zan taimaka maka da yardar Allah, kawai ka amince da buƙatata dan Allah, ba ma acan za'a siyar ba, kawai zan yi ma Anty waya nace zaka zo ka karɓa min motana, idan an zo nan sai a siyar Asiri rufe”


Kai ya girgiza mata, irin shi fa sam ba zai karɓa ba, ya nufi ƙofa yana wani huci kamar gaske.
Da kallo ta bishi tana murmushi har ya fice, zuciyarta cike da shauƙin son Asim, tana jin lallai tayi dacen miji.
https://www.khadeejacandy.com.ng/2019/03/zagon-asa22_13.html


*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng


*PAGE - 23*


NOT EDITED ⚠️


Haka ta cika gidan da ihu sai kuka take duk ta bi ta rikice, zuciyarta na nasaltama Asim ya tafi ya bar. Yarinyar da suke tare ne taje da gudu ta faɗawa Mahaifiyarta, sai gata ta zo da gudu cikin gidan tare da Babbar ƴarta.


Dafa Namra tayi tana girgiza ta.


“Haba ke kuwa sai kace ba musulma ba? Cewa akayi ya mutu ne?”


Cikin kukan Namra ta amsa mata.


“Ban sani ba, sun ce yana asibitin Funtua”


“Yanzu ba kuka ya kamace ki ba, tashi ki wanke fuskarki Mardiya ta raka ki, kuje Asibitin”


Da sauri ta tashi ta shiga ta wanke fuskarta ta ɗauko Hijabinta ta saka, keys ɗin gidan ma sai da Mardiya ta karɓa ta rufe mata gidan, sannan ta koma gida ta shirya sannan ta suka kama hanya Mahaifiyarsu na mata Allah ya tsare.
Keke Napep suka hau ta kai du tasha, sannan suka shiga motar Funtua.
Tun cikin Motar Namra take kuka, har suka isa Funtua, kowa sai tambayar yake lafiya, Mardiya ce kawai take iya amsawa, Namra kan ji take kamar ta yi tsalle ɗaya ta ganta gaban Asim, sam zuciyarta ta kasa aminta da be mutu ba.


Suna isa cikin asibitin suka tambaya, sai a nuna musu emergency ward. Hankali a tashe ta shiga gurin, sai rabon ido take, akwai mutane da yawa a gurin ga kuma ɗakunan bata san wanda zata shiga ba.
Daga gefe ta tsaya ta kira wayar Asim, ringing biyu aka ɗauka.


“Ga mu cikin Asibitin yana ina?”


“Yana ciki suna duba shi, bari na fito yanzu”


Ba a ɗauki dogon lokaci ba, sai gashi ya iso gurin sanye da uniform ɗin road safety. Sai ya miƙa mata wayar hannunsa yana faɗin


“Hajiya ki kwantar da hankalin ki be mutu ba, sai dai ɗan abunda ba za'a rasa ba, ba shi kaɗai yayi haɗarin ba tare da wata babbar mota da kuma ƙananan motaci uku, duk babu wanda be ji ciwo ba, motar ma da yake ciki duk ta ƙone”


Wani sabon kuka ne ya dawo ma Namra.


“Dan Allah da gaske yana da rai?”


“Ko da muka kawo shi nan yana da rai, mutun biyu ne kawai suka rasa rai ciki, amman shi yana da rai”


“Na gode...”


“Ba komai, amman ki kwantar da hankalin ki babu abunda zai faru”


Hawayen idonta ta share, ta fidda wayarta ta saka number Anty Amarya ta kira ta, sai da kiran ya katse bata ɗauka ba, sai ta sake kiranta, sai a uku ta ɗaga.


“Assalamu Alaikum, Namra kin kira ina sallah”


“Anty Asim yayi haɗarin mota yanzu haka muna asibiti”


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Da sauki dai ko?”


“Eh sun ce be mutu ba, amman har yanzu likitoci suna kansa”


“Wace Asibitin?”


“Specialist dake Funtua”


“Toh ki kwantar da hankalin ki kin ji? Kin san abunda Allah ya ƙaddara ma bawa baya wuce shi ko? Ki daina kuka ke ma malama ce Namra, ki fawwalawa Allah komai”


“Toh Anty”


“Kin kira mahaifiyarsa?”


“A'a”


“Toh ki kira ta yanzu ki faɗa mata, Allah ya bashi lafiya, gobe zamu zo inshallahu”


“Tau Anty”


Daga haka ta kashe wayar. Ta ɗauki tasa wayar ta kira number Mahaifiyarsa. Ringing ɗaya ta ɗauka tana faɗin.


“Yanzu nake cewa a sawo min kati na kira ka, na ji ko ka isa lafiya”


“Mama ba shi bane Namra ce, yayi haɗari ne a hanyarsa ta dawowa, yanzu haka muna asibitin Funtua”


“Wayyo ni Allah na shiga uku, ya mutu ne? In ya mutu ki faɗa min Namratu”


“Be mutu ba yana da rai”


“Ba shi waya muyi magana”


“Likitoci suna duba shi yanzu, ba zai yiyu ki yi magana da shi ba”


“Kice min kawai ya mutu, wayyo Allah ni Halimatu, na shiga uku na lalace”


Kuka take sosai cikin wayar, Namra na amsa mata da nata kukan. Daga bisani ta kashe wayar, ta risina a gurin tana kuka.


“Haba Namra, ki gode Allah mana da ba mutuwa yayi ba, ki tashi muje muyi Sallah”


Cewar Mardiya tana goge ma Namra hawayenta. Tashi tayi suka nufi wani ɓangare na asibitin suka siye pure water suka yi alwala Mardiya ta shinfiɗa ɗankwalinta tayi Sallah, sannan Namra ta yi.


Ta daɗe tana yi ma Asim addu'ah kamin ta tashi su koma cikin emergency ɗin. Sai kusan goman dare likitoci suka fito da shi tare da wasu mutane maza da mata kusan mutum shida.
Wani ɗakin aka kai shi, irin ɗakin da ake aje majinyata, aka ware masa gado ɗaya, suka saka masa jini. Kusa da shi ta zauna tana kallon fuskarsa. Idonsa a rufe, gefen kansa an saka masa bandeji, an ɗaure ƙafarsa ɗaya, da cinyar hannunsa.


Wani irin tausayinsa take ji, ji take kamar ta cire ciwon ta maida a kanta. Sam bata ji maganar da likitan yake mata ba har sai da Nurse ɗin dake tare da shi ta taɓa ta.


“Kece Matarsa?”


Kai ta ɗaga mata, dan bata jin zata iya magana a yanzu, saboda bakinta kumshe yake da kuka.


“Ki zo likita yana son ganinki”


Tashi tayi tabi bayan Nurse ɗin dan likitan tuni ya tafi duba wasu masara lafiyar.
A kusa da wani marar lafiya likitan yake tsaye yana masa tambayoyi, sai da ya ƙare dashi sannan ya kalle ta ya miƙa mata wata takarda take cikin file ɗin dake hannunsa.


“Ki siyo masa wanɗannan magungunan yanzu, kuma ki siyo masa ɗan ƙaramin wando da riga a saka masa, kin ga yanzu zane kawai aka rufa masa”


Hannu biyu tasa ta karɓa, sai ta koma gurin da Asim yake, Mardiya na zaune a kujerar dake kusa da shi. Namra ta dafa ta.


“Zan je na siyo magani yanzu na dawo”


“Amman kin san guri?”


“Zan tambaya”


“Toh Allah ya tsare”


“Amin”


Haka ta sa kai ta fice ba dan tasan inda zata ba, bata ma jin kuɗin da yake jakarta zai isa ta siye duka maganin. Da tambaya ta isa pharmacy dake cikin asibitin, suka duba magungunan suka ce mata babu irinsu a cikin asibitin sai ta fita waje.


Bata bar gurin ba sai da ya kwatanta mata inda zata samu, can unguwar dake kusa da asibitin. A harabar Asibitin ta hau Napep ta faɗa nasa inda zai kaita. Be direta ko ina ba sai bakin pharmacy ɗin. Sai ta ciro naira ɗari ta miƙa masa. Ta taka da ƙafa ta shiga pharmacy ɗin, sai da aka gama da

Please Login or Register in order to submit comment