Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ya zan zama sarki bayan Ina da yaya? Kuma ni wannan sarautar sam ba burgeni take ba”


Mai-martaba ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗora akan ɗayar yana murmushin ƙasaita.


“Har gobe Babana baka san Sarauta ba, saboda ka guje mu a lokacin daya kamata acr ka zauna ka karanci komai na gidan nan, baka san jidaɗin sarauta ba, shiyasa kake wannan furuci, na kan lura da yanayin ka sam baka sakin jiki a harkokin sarautar gidan nan, balle na wani gurin, abu kake kamar ba ɗan sarki ba, ai yanzu kuɗi da milki su ake ɗubi abawa mutum sarauta balle kuma kai da ka cancanta dan kana da natsuwa da hankali ga tarbiya”


“Mai martaba wannan sarautar fa dai ku. Ina fatar na samu sarki cikin ƙoshin lafiya”


“Yareema ya samu Mai Martaba cikin ƙoshin lafiya da walwala, ya aka yi ka yi mana zuwan ba zata? Gashi ba ko wane abinci kake so ba balle na ce a ɗibo maka”


“Na samu hutu ne jiya, shiyasa na dawo gida as surprise kasan turawa sun ce surprise is better than disappointed”


“Aiko kayi tsara kan gaɓa, daman akwai ɗaurin auren Abubakar Saturday, daman kai na ke son ka walkice ni, kuma daman can Abubakar ɗin nan abokin ka ne”


Abdool ya shafa kai


“Wai har auren ya tashi ne ? Kwanaki wani friend na mu yake ce min an kai masa kaya”


“Kai ma ai naka yana kusa, mun soma duba maka na dangi kamin mu fita waje, tun ka bamu zaɓi”


Ko be tambaya ba yasan Ummi ce tayi wannan maganar, on behalf of him. Ɗan murmushi yayi ya ce


“Ina za'ayi ɗaurin auren?”


“Zariya, ƴar sakin Zazzauce zai aura, Saturday nan”


“Okay zan je inshallah”


“Ba wai zaka je ɗin ba, ka tabbatar an ganka, zan haɗa tawagar da za kuje daga nan, kuma zaka je ne cikin shigar sarauta, sadauki zai naɗa maka rawani idan kunje can”


Ƙure yayi ma Mai martaba da ido yana kallonsa. Mai martaba yasan waye ɗansa kuma ya san kallon da yake masa.


“Kar ma ka soma, kai shikenan baka son shiga mutane? Ƴaƴan saraku irinka amman baka son shiga cikin su? Rabon ka da rawani tun a hawan salla, ni wannan rayuwar ta ka bata min Yareema, wasu ma basu kao darajarka ba basu kai muƙamin ka ba, sannan sarautar ta su ƙarama ce amman su yi ta tinƙaho suna nuna isa balle ka!”


Yayi tsuntsun da kai, yana murmushi, dan yasan Mai Martaba ya kamo tasharsa.


“Ai ban ce komai ba Mai martaba”


“Na san zaka ce ɗin ne. Tashi ga ruwa can ɗauko ka sha, kar kaje ka ce wa uwarka baka ci komai gidan Mai Martaba ba”


Ya tashi yana murmushi ya nufi wani ɓangare na gurin da aka jera freezer biyar a gurin dan shan ruwa kawai da lemu.


Be bar gidan ba sai da Mai- Martaba yasa aka daba masa wani abu ya ci. Bayan yayi la'asar, yayi ma Mai Martaba sallama sannan ya nufo gida gurin Umminsa.
Gaisuwar ban girma da tadabi sojojin gida suka masa suna masa maraba da zuwa.
Har zai wuce part ɗinsa sai kuma yaji ba zai iya ba har sai ya saka mahaifiyarsa a ido. Da far'ah da zumuɗi ya nufi part ɗinta.


Tun daga yanayin yadda yaga falon zuciyarsa ta raya masa Ummi bata cikin gidan. Sai ya ɗauki remote ya kashe plasma ɗake falon sannan ya nufi ɗakin Ummi dan tabbatarwa. Haleema ya gani kwance saman gado Amira kuma na gurin tufafinta tana gyarawa.


“What nonsense is this?”


Ya faɗa a tsawaci. Daga Haleema har Amira zuyowa suka yi suka kalleshi dan babu wanda yasan da shigowarsa. Da sauri Amira ta zube ƙasa tana miƙa masa gaisuwa zuciya na bugawa da ƙarfi, haka kawai ta samu kanta tana mai tsantsar kunyarsa.


Be amsa gaisuwar ba sai kawai ya watsawa Haleema harara, ita kaɗai tasan abunda Hararar tasa take nufi sai ta sauka saman gadon da sauri ta kama hannu Amira suka fice.


Sai ya ƙofar ɗakin ya rufe da key, ya cire keys ɗin ya nufi part ɗinsa da shi. Yana shiga ya cire tufafin jikinsa ya ɗaura tawul ya shiga Bathroom.


Ya ɗauki kusan mintuna arba'in a banɗakin yana cuɗa jikinsa kamar wanda zai canja fatarsa. Bayan ya gama wanka ya ƙarasa gaban madubi yana ƙara gyara gemensa da babu komai a gurin.


Sallamar da yaji ana ta dokawa ne yasa ya wanke fuskarsa ya fito. Ya nufo falonsa. Amira ya samu tsaye a gurin hannunta riƙe da cup ɗayan hannun kuma riƙe da wasu dinner set an rufe su da ɗayansu.
Tana kallonsa gabanta yayi mummunan faɗuwa, bodybuilding ɗinsa ne ya tashi hankalinta, yadda aka tsara jikinsa da faffanɗan ƙirjinsa, ga fararen idon nan kamar an watsa masa madara tabbas shine irin mijin da take so.


“How may i help you?”


Ya tambaya ganin yadda take kallonsa kamar bata san da shi a gurin ba. Sai da ta gyara tsayuwarta gudun faɗuwa sannan ta miƙa masa duka abunda yake hannunsa.


“Coffee and fruits, tuwo ne aka yi kuma Haleema tace ba ka son tuwo, shine na haɗa maka wannan”


“Thanks i'm not a coffee drinker”


Fruits ɗin kawai ya karɓa ya aje saman kujera ya bar mata coffee. Har ya juya sai kuma ya juyo ya kalleta


“By the way bana son texts ɗin nan da kike tura min, ki daina please”


Kai ta ɗaga masa idonta na son cika da hawaye.


“Note”


“You may go”


“Thank you”


Jikin sanyi jiki ta juya ta fice, hawaye na bin fuskarta. A yadda ta fahimta kamar bata burge Abdool kwata-kwata irin ɗan sakewar nan ma baya mata shi.


Haleema na gani hawayenta tasan ba lafiya ba, daman kuma tasan za'a rina indai Abdool ne.


“Wani abun ya ce miki ne?”


“A'a kawai ina ganin kamar bana gabansa, kwata-kwata bana burgeshi”


“Daman ai shi namiji ba zai so ki lokaci ɗaya ba, komai a sannu yake zuwa, ni yanzu abinda nake so ki yi ta yin abinda zai ja hankalinsa gareki, har shi da kansa ya furta yana son ki, dan naji Ummi na maganar wai Mahaifinsa yayi masa mata”


Amira ta kalleta da sauri.


“Da gaske?”


“Wallahi amman kin ga idan shi da kansa ya ce ke yake so kin ga dole ki a ƙyale”


“Amman me kike ganin zai sa ya so ni?”


“Irin wannan ladabin da kike cigaba, kuma ki riƙa shige masa ki riƙa haɗa masa abu ko da be buƙata ba, sannan idan da hali ki koma gidanku, saboda zama a gaban iyaye yana da muhimmanci, sosai Ummi ma da kanta zata fi ganin darajarki idan kina zaune a gidan ku”


Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya, har ga Allah ita kanta tana son komawa a gurin iyayenta amman ba hali bata iyawa, bata san yadda zata yi ba.


“Zan yi ƙoƙarin yin hakan inshallah”


“Allah ya taimaka nima ina son ki auri Yaya Wallahi”


Amira tayi shiru yana cigaba da tunanin rayuwarta.




*ASIM POV.*


Tun ranar daya bar gidan Namra be sake leƙawa ba, duk jin yake ya tsane ta ma, daman can baya akan cilas ne yake zaune da ita yanzu kuma yaji zai iya auren wata. Sannan yana ganin haihuwa a yanzu zata iya kawo masa matsala, dan haka shi be shirya haihuwa a yanzu ba.


Yau ma kamar kullum da tea da kwai yayi breakfast, sai da ys ci yayi nas sannan ya tashi yayi wanka, bayan ya fito ya shirya cikin wasu tufafin masu kyau da tsada ya shiga sashen uwar ɗakinsa dan gaisheta.
Be same ta a falo ba, sai kawai ya wuce har ƙurƴar ɗakinta dan ta daɗe da bashi damar hakan matuƙar ba mutanr ya tarar a gidan ba. Bedsheet ya tarar tana gyara jikinta sanye da kayan bachi.


Yana ganinsa ta zauna saman gadon tana murnushi.


“Asim an tashi?”


“Eh Hajiya ina kwana?”


“Lafiya ƙalau Alhamdullah, ka yi kyau mashallah”


Ya ɗan sunkuyar da kai.


“Hajiya na ce ko akwai abunda za'ayi miki?”


“A'a gaskiya yanzu kam babu sai dai zuwa anjima. Amman karka manta fa na faɗa maka za mu yi baƙo gobe zai zo daga garin ku, kuma dan kai kawai zai zo garin nan, ina fatar zaka ba shi haɗin kai, yana gida a nan idan ya zo a gidansa zaka je, zan baka maganin da zaka sha, kums ka tabbatar kana kallon videos dana tura maka ɗin dan kasan yadda zaka sarrafashi”


“Karki da mu inshallah ba za'a samu matsala ba”


“To yayi kyau haka na ke so, sai kuma a samu wata ƴar sana'a a riƙe gudun zargin mutane, ina ganin ma nan gaba kadan garin ku zai maida kai dan can yake”


“Nima ai zan fi jindaɗi dan akwai waɗanda na ke son su san nayi kuɗi dan sai na rama wulaƙancin da duk aka min”


“Allah dai ya taimaka, idan ka saki jiki ina faɗ Maka nan gaba kaɗan sai an saka ka a cikin matasan da suka fi kowa kuɗi a nigeria”


Wani kalar daɗi ne yaji marar misaltuwa. Kaɗan ya labarta mata irin gwargwarmayar da yayi da iyayen Namra sannan ya taso ya fito yana auna kansa a mizanin arziki.


Falonta ya dawo ya zauna, yana duba shafin facebook da sabuwar wayarsa. Yau ma ya tararda friend requests kamar wacan lokacin. Da kuma da kuma saƙon wata kyakkyawar yarinya ta tura masa dan katun ɗin nan na facebook mai cewa mutane Hi.


Reply yayi mata.


_“Hey How you darling”_


Sannan ya shiga profile ɗinta yana duba hotunanta.


“Wow wannan kan ba dai fari ba da kyau, irin wannan idan ka samu irinta ai ka huta”


Nan da nan yayi saving hotunanta, sai ya dawo inda taƴi masa reply yana ƙara amsa mata.


_i'm fine. By the way am Nabila Lawal Alƙali aka Pretty Nably. from Katsina living in Abuja_


_Nice to meet you dear, i'm Asim Ibrahim Sanusi aka Asim From Sokoto living in Katsina_


Bayan kamar minti ɗaya sai ta sake aiko masa wani.


_Wow which area in Katsina? I know Katsina in and out_


_Nasarawa road. Send me your number let's chat on whatsapp_




Cikin ƴan mintuna ta turo masa number. Sai da yayi saving sannan ya sauka daga kan facebook ɗin ya tashi ta fito ransa fari fes.
Motar daya saba shiga ya shiga, wacce ta zame masa kamar tasa.
Tun da ya doshi hanyar Nasarawa rayuwarsa ta soma baci, sai faman jan tsaki yake yana nasalta yadda zai tararda Namra.


“That's why i hate baƙar mace, da sun kwana biyu zaka ga sun lalace babu ko kyau kallo, ji jikinta dan Allah duk ta bi ta zube sai ƙassa me zaka kallo a jikinta ma ka yi sha'awa, mtsssss”


Be ji zai shiga da motar cikin gida ɗan haka ya faka ta a ƙofar gidan ya shiga yana wani yatsinar fuska, kamar bada aka yi rayuwa a gidan ba.


Zaune ya hango ta tana ta faman wanki tufafinta. Tana jin sawon tafiyarsa amman ta ƙi ta ɗaga kai ta kalleshi dan be yi sallama ba, kuma tasan abunda ya kawo shi a gidan be wuce abunda take zargi ba.
Zaunawa kawai yayi kusa da ita yana mata wani kallo kamar ba matarsa ba.


‘Ai dole na yi aure a ina zaka nuna wannan ka ce matar ka ce? Abu busasai haka’


Furucin da yayi a zuciyarsa kenan, a fili kuma sai ya ce.


“Sannu da aiki”


“Yauwa”


Ta amsa ba tare data kalleshi.


“Kin koma asibitin ne?”


“Bana da kuɗin hoto”


“To ma ba wannan ba, wace shawara kika yanke ne?”




Kallonsa tayi sai hawayen dake maƙale a idonta suka zubo


“Yanzu abunda kake min ka min adalci kenan? Shikenan kai babu ruwanka da danuwata kullum ni kaɗai nake kwana a cikin gidan nan idan ma wani zai shigo yayi min fyaɗe ko ya kashe ni sai dai ya zo? Asim miyasa kake min haka ne? Ka mayarda ni kamar karya marar amfani”


Hannu ya kai yana shafa ta, dan har ga Allah yayi missing ɗin jikinta.


“Ba haka bane Namra, sai da muka xauna da ke muka yi magana kan aikin nan kika ce kin yarda sai kuma yanzu ki fara complain ko dai ki shi kike ne?”


“Kishin me?”


“Kin ga zan yi kuɗi mana”


Ya faɗa da ƴar dariya, ita kuma sai tayi masa wani kallo.


“Ka min ka yi kuɗi Asim, dubun ka sun yi, wasu sun mutu sun bar kuɗin, wasu kuma kuɗin sun guɗu sun bar su. Kamin ka sanya rigar dubu goma, sai da nasa ɗan kunnen biliyan biyu da rabi na zinari, dan haka kuɗin da zaka yi basa burge ni balle na yi ƙyashinka”


Wata dariyar rainin wayo yayi.


“Amman ai kyau abu akan gashi a ƙasa, da muka yi aure mi Babanki ya kawo mana?”


“Me zai kawo maka, bayan yasan ka auri ƴarsa saboda abun hannunsa ne? Ai shi ba lurasari ba ne, irin Mama mai nuna sun abun duniyarta a fili”


Ya nunata da yatsa.


“Karki sake uwata a maganar ki wallahi”


“Nima karka sake saka ubana, dan cin mutunci ba gado bane kowa ya iya”


“Dube ki dan Allah ni in ban da kaɗɗara ma mi zan yi da irin ki?”


“Lallai kam kaɗɗara ce Asim da nima babu abunda zan yi da irin ka, dacan baka san da haka ba, sai yanzu? Dan kana jin nera ta fara keta wuyanka? Ko da yake hausawa sun ce ɗan talaka be iya samun guri ba”


Tasssss ya wanke mata fuska da mari. Ita kuma ta ɗauki bokitin da take wanki da shi ta juye masa ruwan wanki ta jeɗa masa bokinta. Zuciyarta ta kawo sosai ita kanta a yanzu ta san ba kuka take da buƙata ba, dan ta fahimcin idai har ta ƙyale Asim zai iya hallakata.


“Karka sake kuskuren taɓa min jiki dan ni ba baiwa ba ce kuma ba jaka ta siyo ba”


“Ni kika jiƙe da wannan ruwan? Wallahi sai kin raina kan ki dan sai jikinki ya gaya miki, ba ke fa wallahi yanzu ko ubanki nafi ƙarfinsa balle ke, banza a banza, kuma wallahi kije a zubar da cikin nan ko yanzu ki yi gidan ubanki wallahi, dole ki zaɓa”


“Wallahi ba zan zubar ba. Sai dai ka sake ni amman ba zan zubar da wannan cikin ba”


“Haka kika ce?”


“Haka nace kuma haka na zaɓa”


“To kije gidan ku na sakeki sa..ki ...ɗaya.... Idan kin zubar ki dawo zan maiyar da ke”


Kamar an sako duwatsu haka Namra taji saukar furucin Asim da bata tsammaci zai mata shi da gaske ba. Zubewa ta yi ƙasan guiwowinta tana masa kallon mafarki.


“Da gaske Asim ka sake ni?”


“Na sake ki mana, ba kin zaɓi abunda be isa aka masa numfashi ba balle ma har ya zo duniya ba, sama da ni”


Kai ta ɗaga masa wasu hawaye masu zafi suna bin kumatunta tace


“Na zaɓe shi sama kai, kamar yadda na zaɓe ka sama da iyaye na acan baya, na zaɓi ka sama da karatu na, na zaɓe ka sama da jindaɗi da arzikin da yake gidan mu, na zaɓe ka sama da samarin da suka yi so na, na biyo ka garin da ban san kowa ba sabida kai. Amman yau ni ka yi watsawa ƙasa a ido, lallai kai butulu ne Asim, ka tabbata ɗan bushiya. Duniya ce Asim wanda be zo ba ma ta shiriya masa balle wanda yake cikinta, ka taka a sannu dan duniya ƴar ɗauka da ajewa ce...”


Tsaki kawai yaja ya ɗauki keys motarsa da suke gurin ya juya ya fice cikin fushi. Da kallo Namra ta bishi wani irin abu ya soma zillo yana neman numfashinta.






*Best regards 🌺*
*Khadeeja Candy ♥*
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: Akwai inda na yi mistake jiya nasa ɗan kunnen biliyan biyu da rabi, miliyan biyu da rabi na ke nufi typing errors ne kuma ban yi editing ba.


*61*


NAMRA POV


Kwance tayi a gurin tana ɗaukar numfashi, sai lumshe ido take tana buɗewa, abu ya zo ya tsaya mata a zuciya kamar ƙashi kamar dutse.


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Allahumma ajirna fi musibati wa'kalif ni khairan min ha”


Shine abunda take ta maimatawa tana yaƙi da zuciyarta, tana ji tana gani idonnuwanta suka fara nuna mata ba haka, sai dinshi-dishi take gani, kalmar sakin da Asim ya furta mata ne yake ta mata yawo a ƙwaƙwalwa. She just can't believe Asim ya sake ta, ina zata je? Minene a fita a gareta yanzu bata sani ba.


Hango kanta take a cikin gidansu Abbah yana korarsu ita da Anty. A ɗayan ɓangaren tana tunanin abubuwan da mutane zasu faɗa idan har aka ji aurenta ya mutu, duk wanda be son aurenta da Asim zai mata dariya idan ya ji aurensu ya mutu. Duka yaushe aka yi auren da har za'ace auren ya mutu, gashi duk ta lalace ta koma wata iri? Ciwon da yake jikinta za a ce sai da ta kwashi ciki da ciwon mahaifa sannan ta dawo gida.


“Azzalumi ma cuci Allah ya isa tsakani na da kai, Allah ya bi min haƙƙina”


Daga kwance da take tayi furucin tana kuka mai taɓa zuciya. Bata san inda zata je, tun da taƙi ta bi Anty Amarya tun da farko, yanzu kuma tace mata me?
Haka ta kwanta a gurin jikinta ya ɗige gaba ɗaya, kamar an zuba kayan wanki.

Sai ta taji an kira sallah azahar sannan ta samu kuzarin unƙurawa ta miƙe tsaye. Har taje tayi wanka tayi alwala abu ɗaya ne yake mata yawo.
Idan har Asim ya dawo ya tararda ita a gidan zai zaci ko dan tana son ya mayar da ita ne. Ita kuma yanzu ta yanke ƙauna da shi, idan akwai wanda ta tsana a duniya Asim ne, kuma har gobe bata nadamar zaɓar abunda yake cikinta saman da Asim.
Bayan ta yi sallah azahar ta ɗora da nafili sannan ta rokowa Allah buƙatarta, ta kai masa kukanta ta miƙa masa lamurranta.
Jingina ta yi da ginin gurin tana kuka, da hawaye masu zafi. Irin mutanen da suka yi nemanta aure take tuna amman kowa ya zo tace sai Asim, ayau Asim ɗin ne ya zaɓi rabuwa da ita saboda cikin shi, jininshi.


Tashi tayi ta koma saman katifa ta kwanta, tana kukan zuci wanda ya fili illa da baƙinciki. Wayarta tayi ƙarar saƙo duk da taji daɗin kwanciyar hakan be hanata unƙurawa ta ɗauƙi wayar ta duba ba.


_Karki kuskura cewa za ki siyar da gidan nan, amman na miki lamani ki zauna har ki canja shawara, idan kin yi tunani mai kyau na shirya maida ki a matsayin mata ta!_


“Kaico...”


Shine kawai abunda ta furta bayan ta gama karanta text ɗin ta share hawayenta. Kanta ta ɗaga sama tana kallon ɗakin, kwata-kwata jin tayi gidan ya fita a ranta. Sai dai kuma bata da gurin zuwa, duk inda zata je be yi kamar gidan mahaifinta ba, da ace Abbah ba xai wuƙantata ba, da ba zata damu da maganar mutane ba matuƙar tana gidansu, a ƙarƙashin iyayenta.


Hijabinta ta ɗauka ta saka, ta ɗauki jakarta da wasu ƙaƙanan abubuwa nata ta saka a jakar sannan ta fito, tun da ta baya bq ɗin baya ta sake kallon ta ba har ta fice daga gidan.
Fuskarta ta kumbura sosai haka ma idanunta, duk wanda ya ganta zai san tayi kuka, hakan yasa ta sanda kai ƙasa har ta isa titi. Napep ta tara sai da ta shiga sannan ta soma tunanin inda zai kai ta. Bata da wadataccen kuɗin da zata kama wani gidan ta zauna, kuma ta san ba mutuncin ta ba ne ta kama gida a wani gurin. Kuma bata jin zama a gidan dan zata iya aikata komai saboda baƙinciki.


“Hajiya ina za a kai ki?”


Tsayawa tayi tunani, har tashi Napep ɗin.


“Kai ni tashar mota, inda ake hawa motar sokoto”


“To amman yanzu tashar gov sun tashi sai dai babbar tasha”


Ya hau kan titi yana ƙara ƙure volume ɗin napep ɗin dake tashin wakar Umar m shariff. Ita dai saurare kawai take tana hawaye har suka isa, ɗari biyu ta ciro ta bashi ya miƙa mata canjin naira hansi sannan ta fita shi kuma ya juya.


“Sokoto, Kano, Kaduna, Abuja, jigawa, Kebbi, Zamfara”


Haka ƴan union ɗin suke ta faɗi suna neman passengers. Wasu suka yo kan Namra da gudu suna tambayar ta inda zata ta, tsaye kawai tayi tana tunanin inda zata ce duk da ta zo da niyar zuwa sokoto ne sai kuma ta ji ba zata iya, har tana jin ma kamar ta koma gida...


“Hajiya Kaduna zaki je?”


Wani daga cikin su ya tambaya, sai ta ɗaga masa kai.


“Eh Kaduna zan je”


“Ga mota can daman mutum biyu ake jira, ina kayan ki suke?”


“Bana da kaya”


“Okay muje ga mota can”


Shine yayi mata ja gaba har gurin motar, sannan ya faɗa mata kuɗin motar. Cikin rashin kuzari ta cire ta biya, sannan ta shiga motar tana ta doubting akan taje can ɗin ko kuma a'a. Idan taje kaduna gurin wa zata je? Tun da bata taɓa zuwa ba duk da akwai taubashiyar Anty Amarya a can amman bata tunanin zata gane inda take tun da zuwan da duka yi tun da daɗewa ne kuma da motar gida, sunan unguwar ma bata riƙe sosai ba.




ASIM POV


A sale ya fito daga gidan, bama abunda ya fi baƙanta masa rai kamar jiƙa masa tufafi da Namra tayi, Yana ƙoƙari buɗe motarsa ya hango Mardiya tafe, ɗan tsayawa yayi yana kallon takunta, cikin yanga izza take tafiyar dan kuma kawai ta ɗauki hankalinsa ne. Shi kam yasakar mata ido sosai yana kallonta duk da jiƙaƙin tufafin ne a jikinsa, amman hakan be hana shi tsayawa gurun motar ba har ta iso, dan kawai ta ga shine yake tuƙa motar, yasan ko ba komai zai burge ta tun da yasan mata sun fi son mai mota.

Sai da ta kusa ƙarasowa sannan ya buɗe motar ya ciro ƙyale yana goge jikinsa.


“Asim ina kwana?”


Ta gaishe shi cikin kashe murya da ƙarawa muryar zaƙi. Da sauri ya kalleta yana murmushi kamar ba shine ya fito rai a ɓace ba.


“Ah lafiya ƙalau Mardiya ya gidan?”


“Gida ƙalau wallahi miya jiƙa mata kaya haka?”


“To sha'anin ne kin san halin na ku sai a hankali. Gari za a ne?”




“Eh wallahi zan ɗan shiga gra ne”


“Okay shige na aje ki”


“Mashallah ka siye sabon mota ne?”


Ta faɗa tana kallon motar cike da burgewa.


“Eh ai tama kwana biyu, sabuwa dai muke jira”


Buɗewa tayi ta shiga, sai shima ya shiga yana ƙoƙarin tashin motar ta kalli gate ɗin gidansa ta ce


“Kar fa Namra ta hango mu ko a kai mata rahoto”


“Mtsssss amman Mardiya ma kin mai yarda ni wani wawa, ni kam ai nafi ƙarfin matata ba irin mazan nan bane na banza, ashe ke matsoraciyace ba zaki iya kishi da ita ba”


“Ai kishi dabam, da ace yanzu aurna na ne zaka yi to bana shakar taji komai, amman kaga yanzu babu wata magana ta aure dole na ji tsoron irin maganar da zata je mata a kunne”


“To kisa a ranki auren ki zan yi”


Ya faɗa yana ƴar dariya. Itama dariyar tayi mai cike da jindaɗi. Har ya kai ta inda zata je fira suke kamar masu masoya ita kuma sai wani lanƙwashewa take tana karairaya. Daman shi tuni da kasheshi da kalamanta ma.
Daga gra ya wuce gidan Hajiya Sadiya, be same ta a gidan ba hakan ya tabbatar masa da akwai inda taje kenan. Ɗakinsa ya shiga ya canja tufafin jikinsa ya saka waƴan can a washing machine sannan ya dawo ya zauna. Yarinyar ɗazu ce ta faɗo masa a rai a ƙoƙarinsa na kawarda tunanin Namra a ransa dan ganin yake ita babbar maƙiyiyarsa ce, ko kaɗan baya nadamar sakinta da yayi kuma he's ever ready ya mai data idan ta yarda ta zubar da cikin.
Number yarinya ya nemo ya danna mata kira, ringing biyu ta ɗauka ciki muryarta mai sanyi. Cikin turanci ta soma watsa masa tambayar wake kiran shima ya maida mata da yaren da tafi ganewa. Nan da nan ta sake da shi suka gaisa duk kalmar da tayi masa sai ya maida mata, ya ɗan tambaye kaɗan daga rayuwarta, sai da amsa masa a inda abunda take tunanin ya sani. Ya jidaɗin da tace masa ita ƴar Katsina ce, daman ta faɗa masa tun a chat amman a yanzu ne take faɗa masa sunan unguwarsu a Katsina.


Sun daɗe suna waya sannan yayi mata sallama ya kashe wayar. Ko da ya kalli ogagon ɗakinsa ƙarfe biyu saura ya gani, sai ya tashi yaje yayi alwalah yayi salla a cikin gida. Bayan ya sallame zancen gidan ya faɗo masa rai, wai kar dai Namra tace zata sai da gidan ta gudu da

Please Login or Register in order to submit comment