Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sheiɗan yake son masa, sannan ya buɗe ido ya haɗe fuska kamar be taba dariya ba.


“Su waye ku?”


“Mu ne waɗanda suka kama hanyar wannan gidan”


Ta amsa masa a gautse.


“Bq kuka kama ko Main house”


“Main house muna ciki aka yi gobara sai muka dawo nan da zama”


“Ina mijin ki?”


“Baya nan ya tafi kasuwa”


“To idan ya zo ki ce an baku one week ku tashi za ayi gyaran gidan”


Gabanta yayi mummunan faɗuwa.


“Innalillahi wa'inna ilaihi dan Allah ku gyara babban gidan sai ku bar mana BQ ɗin wallahi ba mu da gurin zuwa idan muka bar nan, dan Allah ku taimaka mana”


Ta haɗe hannayenta idonta na son cika da ƙwalla.


“Da yaushe ake tarar da mijin ki?”


“Da safe ko kuma da dare guraren goma”


“Okay zan zo na yi magana da shi gobe”


“Allah ya kai mu na gode”


Be sake cewa wani abu ba, ya juyo hannayensa zube a aljihu ya fito gidan. Har lokacin Amira na cikin mota zaune tana jiransa, yana shiga motar yayi mata key suka juya. Wannan karon ita ce ta ke ɗan jansa da fira shi kuma jikinsa duk ya mutu baya ma iya amsa mata. yawancin tambayarta akan gidan ne da kuma unguwar, sai kuma yaba garin Katsina da take. Shi dai har suka isa gida sai dai ya ɗaga mata kai kawai.


Ta rigashi fita daga motar, dan yau ranta fes yake ta ta fita tare da sahibinta. Bata tsaya a falo ba sai kawai ya wuce ɗakinta tana ƙoƙarin ɓoye nishaɗinta. Shi kuma ya zauna a falo, kusa da Ummi da take zaune a inda ya barta ɗazu, sai dai wannan karon ita da Shukura ne kuma carrots take gyarawa.


“Har kun dawo?”


“Yeah ai ba wani nisa”


“Kaga gidan ko?”


“Eh duk ya lalace idan aka ce za a gyara shi sai anci kuɗi kam ”


“ Ai dole a gyara shi tun da gidan marainiya ce, a ciro kuɗinta ayi mata gyaran, daman kasan Amal bata da daɗi ta matsa min tuni kamar ni ce na ƙone gidan.Yanzu sai ci nawa idan za a gyara shi?”


“A lot, nawa kika siya mata shi?”


“Ba da kai aka yi cinikin ba, da Alhaji Ƙasimu da Mansur”


“Kai ai bana iya tunawa kin san abu da yawa”


“Nine million aka siye shi”


“Na siya 15 million”


Ummi tayi saurin dubansa.


“Joking abii?”


“I'm serious wallahi na siya”


“Ba zamu siyar ba”


“Saboda me?”


“Muka sani ko zinari aka gani a gidan zaka mana wayo”


Ta faɗa tana tashi ta nufi kitchen, dan ga dukan alamu yai da kanta zata yi girki. Dariya Abdool yayi ya cire hular kansa ya jingina da kujera yana faɗin


“Indai Amal ce ai abu mai sauƙi ne”


Lumshe ido yayi yana sauke ajiyar zuciya. Babu wacce yake gani sai Namra, da sauri ya buɗe ido ya tashi ta nufi Gardem.








FIVE READ MORE.....🙌🏻


[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *57*


Bata taɓa sanin haka jikin da zuciya suke ba idan wani abu marar daɗi ya faru da mutum sai yau. Duk tashin hankalin da ta shiga lokacin da Rafiq ya kamu da ciwo be kai wanda take ciki ba yanzu.
Wannan karon kuka ma yayi ƙaura daga idonta duniyarta sai juya mata take. Gani take kamar mafarki take ba da gaske ba ne Hilal ya miƙa mata wannan takardar.
Miƙewa tayi tsaye sai gata ta dawo xaune saboda rashin ƙarfin jiki, ga wani sanyi da take jin ƙafafunta sun mata.
Wani abu taji yayi mata tsaye a zuciya, hango kanta take a bazarawa, irin rayuwar da tayi ta budurci kuma yanzu ace aurenta ya mutu bayan bata daɗe gidan mijin ba. Takardar ta ƙurawa ido tana auna yadda Mominta zata ji.


Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shi tai ta maimatawa sannan ta samu ƙarfin jiki, har ta unƙura ta tashi. Durowarta ta buɗe ta ɗauki canjin da yake ciki da Atm ta saka a jikarta tare da takardar ta saka hijabin ta fito falo. Saman kujera ta zauna tana maida numfashi kamar wanda tayi gudun fanfalaƙi. Hannu ta kai ta rufe bakinta saboda kukan daya zo mata gadan-gadan.
Sai dai hakan be hana hawayenta zuba ba, ashe da gaske hawaye suna da zafi, sai a yau ta tabbatar dan yau ta ji hawayenta kamar ruwan zafi.


“Me yasa zan yi kuka akan abunda ba zai sauyu ba? Miyasa zan kuka akan mutumen daya zaɓi rabuwa da ni? Anya Hilal ya cancanci hawaye na?”


Sune tambayoyin da tayi ma kanta a fili, sai dai har ta tashi ta kai bakin ƙofar falon bata samu amsarsu ba. Kamin ta ƙarasa gate ta gyara fuskarta, ta goge idonta da Hijabin gudun kar wani ya gani ya zargi wani abu.


Sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu Napep, sai da ta shiga sannan ta faɗa masa inda zai kai ta. Har suka isa estate ɗin su idanuwanta basu daina cika da ƙwallah ba.
Tana biyan Mai Napep ɗin ta shiga gida hawaye na bin fuskarta. Bata samu kowa a falon ba, daman by this time ba zata samu kowa a gidan b Sai Momynta. A saman kujera ta zauna ta haɗe kai da gwuiwa tana kuka. Sautin kukanta ne tashi daga bachi da take ta fito da sauri falo. Ganin Kalsoom ya tashi hankalinta, tasan da maganar kotu da Rashida ta sata amman bata zaton shine zai sa Kalsoom wannan kukan bayan ko kotun ba'a shiga ba. Kusa da ita ta zauna tana ƙoƙarin ɗago kanta.


“Ke miya same ki?”


Ɗagowa tayi cikin kukan ta rumgume Mominta. Girgiza Momi tayi


“Ke ki min magana mana, waya mutu? Ko Rafiq ɗin ne ya mutu?”


“Ni ce Momi Hilal ya sake ni...!”


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, me kika masa?”


Kasa magana tayi sai kuka take kamar zata shuɗe, Momi ma hawaye take, ita kanta bata jidaɗin maganar da Kalsoom ta faɗa mata ba, babu mace da zata so auren ƴarta ya mutu sai dole, balle Kalsoom da aka samu aka yi auren daker.


“Ya isa bari kuka, aure rai ne da shi idan lokacin yin sa yayi sai an yi, idan kuma mutuwarsa yayi dole ya mutu, ki kwantar da hankalinki”


Ta faɗa tana share mata hawaye, sai dai kuma ita na ta hawayen ba su daina zuba ba. Daker Momi ta lalaɓa Kalsoom tayi shiru, har ta shiga ɗakin Momi ta kwanta, kanta sai sarawa yake, ga wani ɗan banzan nauyi da yayi mata kamar an ɗora mata dutse, idonta kuma har ji take kamar ƙasa ce a ciki.


Momi kan cikin rashin kuzari tayi girkin yau, sai dai har tayi ta gama bata lasa miyar ba balle ma ta ci abincin. Sai da ta zuba a plate sannan ta kaiwa Kalsoom, banɗaki ta tararda ita tana alwala, dan lokacin ɗaya da rabi tayi, ta daɗe a banɗakin tana aikin kuka sannan ta fito.


“Haba Kalsoom ina ce kin saba da irin wannan jarrabawar, komai fa idan an yi haƙuri za'a ga riba”


Momi ta faɗa tana kallon fuskarta data kumbura. Kusa da ita Kalsoom ta zauna, idonta cike da ƙwalla ta ce


“Momi yanzu duniya zata ɗauka da gaske na aikata, yanzu kowa zai zarge ni akan ni ce ma bawa Rafiq guba, tun da ga shi har Mahaifinsa ya zaɓi rabuwa da ni”


“Amman baki masa bayani ba ne? Ko da yake ba lallai ne ya gamsu ba, saboda gidan daga ke sai yaron ne, kuma abun mamaki ne ace ya sha guba, dole duk wanda ya ji ya zarge ki, ni ba ma abunda ya ɓata min rai kamar zuwa kotun nan da za'ayi”




“Ya ce min babu maganar kotu, ɗazu da zai ba ni takarda”


“Allah ya sauwaƙe, idan auren ku akwai alheri a ciki Allah ya maida shi, idan babu kuma Allah ya kawo miki na ƙwarai, shi kuma ya haɗa shi da matar ƙwarai”


“Ina jin saki uku ne, aure ba zai sake shiga tsakamin mu ba”


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, miya kai shi aikata wannan babban kuskure? Har saki uku? Ai idan rai ya ɓace hankali baya gushewa, amman Hilal be yi ɗa ba, ai komai bincike yake so”


Ƙasa tayi da kanta tana kuka.


“Daddyn ki ba zai ji daɗin wannan lamarin ba, ana murna an yi abu sai gashi kuma ya zama na riƙici, ko da yake malamai sun ce idan saki uku aka yi shi a lokaci ɗaya za a iya ɗaukarsa a matsayin ɗaya”


“Ba furtawa yayi ba, a rubuce ya bani”


“Rubuta ya yi saki ɗaya, biyu, uku? Kalsoom bana son ki dawo xaman gidan nan ne, sannan duk wanda ya ji dalilin mutuwar auren ki ba zai aure ki ba, saboda wannan ɓacin suna ne. Nasan ba halin ki bane ko kin ji kin haɗu da mugayen ƙawaye ne masu kai mutum kai hallaka”


“Wallahi ban aikata ba, ke ma zargina kike ko?”


“Ba zargi bane Kalsoom kawai ina tsoron sherin zuciya ne, da kuma kishi, babu abunda basa sawa”


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah kaɗai zai shede ni shi kaɗai zai shede ni da ban aikata ba”


“Ba zargin ki na ke ba Kalsoom, amman wannan lamarin abu ne mai sarƙaƙiya, ga abincinki ki ci”


Kai ta girgiza hawaye na mata zuba.


“Ki daure dai ki ci, Allah zai kawo mafita inshallah, wallahi wahala bata taɓa tabbata, kuma tun da har ya ci amanar ki sai Allah ya saka miki, Hilal butulu ne”


“Karki ga laifinsa Momi ni na nemi ya sake ni, a tunani na hakan shine mafita, ashe bala'i ne, ni ce na ce yayi min saki uku”


“Subhanallah Kalsoom ke kika jawa kan ki matsala, dam me zaki yi haka? Kin fi son ki dawo gida ki zauna tare da ni? Mutane da suka zage ki lokacin da aure yayi miki tsawaiko su sake buɗe miki sabon shafi? Kin tonawa kan ki asiri kowa zai ji dalilin fitar ki gidan miji, gashi ba saki ɗaya bane balle a gyara saki har uku wallahi baki da hankali Kalsoom kin yi wa kan ki, da wane ido zaki kalli baban ki? So kike ciwon zuciyarsa ya tashi ko?”


Ta ƙasara da kuka. Tana mai jin kamar ta kama Kalsoom ɗin tayi ta dukanta. Wani irin kuka Kalsoom take sai yanzu take nadamar abunda ta aikata.


“Ina takardar take?”


Momi ta katsa mata tsawo. Jikarta ta nunawa Momi tana cigaba da kuka. Tashi Momi tayi taje ta ɗauki jakar ta zazzage kayan ciki sai ga takardar ta faɗo, ita kanta ta ji wani ɗarrr kamar ka ta ɗauki takardar sai dai tana da buƙatar sanin ko saki nawa ne idan da gyara a gyara tun kowa be ji ba.


Warware takardar tayi tana karantawa. Wani dogon tsaki taja lokacin data gama karantawar ta jefa ma Kalsoom takardar ta fice tana faɗin.


“Yayi tunani da hankali wallahi...”


Sai da Kalsoom ta ci kukanta ta ƙoshi sannan ta ɗauki takardar tana dubawa cikin kuka.




_Idan na sake ki ina za ki? Wa kike tunanin zai aure ki a halin da kike ciki yanzu? Kowa yana zargin ki da kin kore Rashida kina son kashe ƴaƴata, saboda basu san dalilin sakinta da na yi ba._


_Zan miki uzuri Kalsoom akan abinda kika aikatawa ɗa na, saboda kin nuna musu so a can baya, xuciya bata da ƙashi, dukan abunda kika aikata dan kina so na ne, kina kishi na shiyasa kika aikata, kina ganin kamar ina son ƴaƴan da ba naki ba da yawa ko?_


_Ba zan sake ki ba, saboda naga so na a idonki, kina neman sakin ne saboda kina ganin kamar shine mafita a gareki ko? To ba zan sake ki ba, har abada haka zamu zauna da ke, amman ba zan sake barin ƴaƴana a tare da ke ba, ba zasu sake raɓar ki ba, saboda zuciyarki ta sauya a yanzu, kin tashi daga Kalsoom ɗin da nasan ki kin koma wata dabam, amman hakan ba zai hana na so ki ba, ba xai hana na xauna da ke ba, ina son ki sosai Kalsoom amman ban cancanci abinda kika min ba, nasan mace ce ke kina da rauni shiyasa kawai na ɗaga miki ƙafa_


_Idan kuma har sakin kike so da gaske sai ki kai ni kotu._


*Ur Faithful Husband*




Shine abinda ya rubuta daga ƙarshe cikin manyan harufa. Rumgume takardar tayi a ƙirjinta tana sauke ajiyar zuciyar da bata san lokacin data zo mata ba.
Wani sanyi ta ji ya saukar mata tun daga saman kai har ƙasan ƙafafunta, nan take ta nemi ciwon kanta da kuka da take ta rasa, wani irin ƙaunar Hilal ne ta ji ya ratsa zuciyarta.


Hijabinta da ta bari falo Momi ta jefa mata.


“Tashi ki koma ɗakin ki tun Mahaifin ki be dawo ba”


Buɗe ido tayi tana kallon Momi da murmushi a fuskarta babu ko kunya.


“Bari na yi sallah”


“Idan kin je can kya yi, amman wlh karki sake kuskure cewa ya sake ki, in ba dan Allah yasa yana da tunani ba ai da shikenan”


Bata musa ma Momi ba ta ɗauki hijabin Momi ta saka ta ɗauki takardar da jakarta ta fito falo ranta tasss kamar ba ita ce ta gama kuka ba. Har bakin gate Momi ta rakata tana mata gargadi, sai da ta hau Napep sannan Momi ta koma ciki tana yi Allah Hamdala tare da sawa Hilal albarka...




*NAMRA POV*


Sai da dare Asim ya dawo, kamar yadda ya saba, idan ka ganshi ba zaka ce shine ya fita da tsoro ba ɗazu, yau yayi ciniki shine sirrin farincikin na yau.
Ba laifi ya ɗan sake fuska ya shigo har da sallama, kamar ba shi ba. Ita kanta Namra da mamaki ta amsa masa sallamar tana ƙara kallon fuskarsa dan ta tantancesa. Ya zauna kusa da ita, yana shewa.(fito)


“Sannu da zuwa”


“Yauwa ya gidan?”


“Gida yana nan yadda ka bar shi, masu gidan ma sun zo guba abun su kuma sun ce mu tashi”


“What? To ina za mu koma? Ai kuɗin dana biya be ƙareba, ba zamu tashi ba wallahi”


“Su zaka faɗawa ba ni ba, ni dai na faɗa masa ya zo da safe ko da dare zai same ka”


“Bari ya zo ɗin amman wallahi ba zamu tashi ba, duk inda za a je sai dai aje, amman wannan iskancin ba zan ɗauke shi ba, haka kawai dan ina talaka sai a nemi wulakanta ni”


“Miye abun wulaƙanci dan masu guri sƴn nemi aba su abun su? Sai mu tashi mu basu gidan su, ni dai na roƙe su akan su bar mu mu zauna bq idan har basu yarda ba shikenan sai mu nemi wani gurin kuma”


“Ai kaji matsalar masu kuɗin nan, wallahi duk inda yake baya ƙaunar talaka”


“Ka cika mai da zazzaɓi ciwo Asim, yanzu sun san kai mai kuɗi ne ko talaka? Amman kasan babu talakan da zai iya kama gida kamar wannan ya zauna ko?”


“Sun san talaka nake mana tun da na zauna bq, nima lokaci na yana zuwa zan yi kuɗi har na mamaki”


“A haka za kayi kuɗi matarka tana cikin ƙunci? Ban taɓa ganin ragon namiji irin ka ba Asim, sai dai na girka na baka da ƙarfin ka da komai?”


“Dan Allah ki yi haƙuri Namra, kin ga ɗan aikin da nake be wuce na samu na shan ruwa ba, amman yanzu na samu wani aiki, sai dai aikin mai gidan ya faɗa min cikin gidan zan koma da zama saboda aike-aike idan sun taso, kuma a matsayin driver zai ɗauke ni kuma yaron gida, tun last week muka yi maganar amman nace ba zan kama aikin ba sai na ji ta bakin ki”


Ta jidaɗi dan tasan aikin ya fi wanda yake yi yanzu, sai dai maganar komawa can ne bata gane ba.


“Amman ka koma can har da ni? Ko ya”


“A'a ni kaɗai zan koma can saboda ya fi son ana kwana ta can”


“Amman kai ba aikin gadi ba ce kuma sai ka kwana ina ma laifin kaje da safe wuni”


“Ba kullum zan riƙa kwana can ba, ina jin wani lokaci ne kawai, kin ga ƙara mu samu mu riƙa wannan aikin kamin mu ga abinda Allah zai yi gaba kuma”


“Allah yasa haka shine mafi alheri”




“Amin ya rabb”


Ya rumgume ta yana murmushin jindaɗi, daman ya faɗa mata ne kawai dan ta karta daina ganinsa da dare, amman ko da tace bata aminta ba zai sa ya fasa aikin ba.




*ABDOOL POV*


Suna dinner yake nanatawa Ummi maganar siyen gidan da zai yi, but still bata yarda ba, duk da ta ga alamun da gaske yake.

“Wai mi za ka yi da gida daya ƙone har xaka siye shi 15m?”


“Just”


Ya faɗa yana ɗaga kafaɗu.


“Dude na bar maka, ko kyauta ma zan iya baka ma”


Amal ta faɗa jikin har rawa yake. Kallon Ummi Abdool yayi yadda take watsawa Amal harara yasa shi dariya, sai ya aje spoon ɗin hannunsa ya tashi ya ɗauki kofin tea ya wuce ɗakinsa. Haka kawai ya samu kansa da murmushi ba dalili.


Wata ƙaruwar durowa ya buɗe ya ɗauko wata ƴar ƙarmar jaka baƙa. Ya nufo part ɗin Ummi hannunsa ɗaya riƙe da tea ɗin.
Saman kujera ya jefar da jakar yana kallon Meesha dan ya yarda da natsuwarta.


“Aisha zo ki cire min 15m a nan, ko wanne 1m ne”


Dinning ɗin ta baro ta zo ta zauna saman kujera ta buɗe kuɗin ta fara ƙirgiwa har ta cire 15m, ta aje gefe.


“Ga su”


Sai ya kalli Ummi


“Ummi ga kuɗin”


“Abdallah ana ciniki dole ne? Na ce ba xa a siyar ba”


“Amman mai abu tace ta siƴar”


“Wai me za ka yi da gidan ne”


“Kawai ki sai da min”


“An siyar maka, shikenan?”


“Thank you”


Ya ɗauki ragowar kuɗin ya maida ɗakinsa. Saman madubi ya ɗora copin tea ɗin ya faɗa saman gaɗon zuciyarsa cike da nishaɗi.


Haka ya kwana da nishaɗin da be san ta ina yake xo masa ba balle dalilinsa ba. Shi dai baya iya faɗin abunda ɗaya ta san ya shi ne silar farincikinsa tun jiya har zuwa yau.
Yau zai koma abuja ko ba komai dole yayi sammakon tashi, balle kuma Namra tace masa da safe ake samun mijinta.


Be tsaya wani karin kirki ba, dan a tunaninsa kamar idan ya daɗe ba zai samu mijin nata ba
Ko da bakwai tayi yana ƙofar gidan, sai dai be shiga ba sai da ya buga gate ɗin, ganin babu wanda ya fito yasa ya tura gate ɗin ya shiga cikin, black suit ne jikinsa yayi mugun masa kyau kamar balarabe.


Nesa da bq ɗin ya tsaya yayi sallama cikin muryarsa mai sanyin da daɗin saurora, da ace ma'aikatan sa zasu ganshi a yanzu da sun rantse wannan muryar arota yayi.
Asim ne ya fara fitowa yana samawa, daman tun da yaji sallamar ya raya a ransa cewar masu gidan ne. Sai dai yayi mamakin ganin mutuen duk da be san sunansa amman yasan shi ne ya biyo Namra asibiti. Ƙarasowa Asim ya yi yana masa wani kallo da shi kaɗai ya san fassararsa.


Hannu Abdool ya miƙa masa.


“Sunana Abdallah Ahmad Mai-doki, na zo ne a kan maganar wannan gidan, matarka na ciki?”


Be masa hannun nasa ba sai kawai ya ce


“Eh miye haɗin ka da matata?”


Abdool ya ɗan wara ido tare da taɓe baki haɗi da ɗaga kafaɗu.


“Nothing, jiya na zo akan maganar gidan nan ne sai take roƙo na akan dan Allah na taimaka na bar su a bq su zauna dan basu da gurin zama, so shiyasa na yi ƙoƙarin mai da gidan mallakin ku gaba ɗaya”


Asim ya washe baki, tare da miƙa masa hannu


“Mashallah Allah ya saka maka da alheri”


Daga nan da yake ya ƙwalama Namra kira. Sai gata ta fito cikin hijabi, kamin ta ƙaraso gurin asim fuskar Abdool kawai yake kallo ya gani idan ya kalli Namra. Babu abinda yake rayawa a zuciyarsa sai munafurcin da Namra take masa, wai shi za a maida wawa ya kawo mata gida ya ce ya basu dan tasan idan ya bata ita kaɗai dole za a gane abunda yake tsakanin su. A fili kuma murmushi yake kamar gaske yana kallon Namra da take gaishe da Abdool. Kallo ɗaya Abdool yayi mata ya ɗauke kai ya ciro takardar dake aljihunsa ya miƙawa Asim


“Daga yau wannan gidan ya zama na ku, ba zaku sake biyan kuɗin haya ba balle ace ku tashi”


Hannu biyu Asim yasa ya riƙe hannunsa yana masa godiya kamar zai shige cikinsa. Namra kan mamaki ya hana ta tace komai balle har ta yi godiya.
Sai Asim ne yake ta zuba masa godiya yana murna baka da zuci dan yasan shi zai mori gidan ba Namra ba.


“Mun gode sosai Allah ƙara arziki ya ƙara wadata jazakallahu khairan”


“Amin”


Ya faɗa sannan ya juya ya nufi gate, yana ƙara kallon gidan. Har cikin ransa yaji addu'ar da Namra tayi masa. Sai da ya wuce sannan Asim ya juyo ya shigo gida zuciyarsa cike da zarge zarge. Sam be nunawa Namra ya gane shi ba, sai kawai ya nuna mata ya fi kowa farinciki abinda yayi musu duk da zucin ma farinciki ne dan yasam shine zai ci amfanin abun.


“Kin gani ko yanzu kan alheri ya fara shigo mu, yanzu duk wannan gidan na mu ne kai Alhamdulillah Allah”


Namra tayi murmushi dan ita tun ɗazu mamaki take da tunanin dalili kyautar gidan da Abdool yayi mata, bayan acan baya ya taɓa binta yace yana sonta, ko dai akwai biyu a kyautar ne? Bata bar Asim ya gane abunda yake ranta ba, gudun karya zargenta, ko kuma yayi wani tunanin na daban daman can ya taɓa zarginta.


Dumamen shimkafar da tayi ne ya zuba masa, ya ci sannan ta kai masa ruwan wanka yayi wanka ya shirya cikin wasu tufafin data wanke masa. Sannan ya fito waje ya ciro ɗari biyar ya miƙa mata.


“Gashi ayi cefane”


Hannu biyu tasa ta karɓa tana muryar yau mijinta yyi abun kai


“To Allah amfana”


“Amin sai na dawo”


“Allah ya tsare”


Ya nufi gate zuciyarsa cike da ƙunar cin amanar da Namra take masa, abun har ya fara wuce gurin har ana kai ga kyauta gida.


“Hmm Lallai ma wannan matar wai har ni za a rainawa hankali, bari na zama Asim ɗi na na ƙwarai ki ga yadda zan yi da ke, ku yi ta abun ku yanzu na ba ku dama”


Ya filin yake maganar ya miƙe hanyar data zata kai shii babban titi, sai dai hanyar gidan su Mardiya ce, da gangan ya bi dan ya ganta.
Ya ko yi nasarar angota da ɗaura gaba tana tsaye ƙofar gida tana ciniki a warwaro da mai tutu-rutu, ƙirjinta kawai yake kallo yana siffantawa kansa ita, har ta kawo kusa da inda take.


“Barka da safiya Asim”


“Yauwa barka Mardiya ya gida?”


“Lafiya ƙalau, ina Namra?”


Ya ɗan ƙara washe baki dan be yi tunanin zata kawo maganar Namra a yanzu ba.


“Tana nan ba kin guje mu ba”


“A ni na isa ku ne dai kuka guje ni”


Dariya yayi ya ƙarasa gaban mai ɗan kunnen yana kallon kayan


“Me aka siya?”


“A warwaro ne da ɗan kunne”


Babu ko kunya take masa magana kamar bata sam ɗaura gaba ne a jikinta ba. 1k ya ciro ya miƙa mata


“To a siya da yawa”


Hannu tasa ta karɓa.


“Na gode sosai Allah kawo wa su, ayi irin mu huɗu”


Dariya yyi kamar ba shi ba ya amsa da amin yana tsayardar mai okada. Sai da ya hau sannan ya faɗa masa inda zai kai sa.
Hajiya Sadiya tayi mamakin ganinsa sosai dan a ƴan kwanakin daya ɗauka ta zata ko ba zai dawo ba ne, ruwa ta kawo masa da abinci, sai wani ƴauƙi take kamar ta ga mijinta. Shi kuma ya sake jikin sosai kamar gidansa, baya kallonta idan tana kallonsa ko taɓa gabansa sai ta bada baya yake kallonta.


“Baka buƙatar kwaso kayan ka ko wani abu, akwai komai da zaka buƙata a ɗakin da za a sauke ka, ni na ɗauka ma ba zaka dawo ba”


“Me zai hana? Mutum ya bar samu?”


Dariya...


“Aiko dai, ina kallon lokacin da kake ta ciwon nan kamar ba zaka tashi ba”


Gabansa ya faɗi dan be yi tunanin ko ta san shi ba, se dai be gama saƙe saƙensa ba ta cigaba.


“Lokacin da muƙa ɗauko ka daga asibitin Funtua zuwa nan katsina, lokacin kana cikin ciwo ba zaka gane ba, amman na san kana da mata ka ɓoye min ne kawai”


Ido cikin ido yake kallonta dan tantance abinda take faɗa.


“Ban gane ba”


“Hmmm Asim ko? Ni ce na ɗauko ka da mota na na kawo ka Asibitin katsina na biya kuɗin gado da magani, amman nasan ba zaka iya tunawa kancewar lokacin kana cikin ciwo”


“Eh...eh..ha...k...a..ne.... Ashe kin san ni”


“Na san ka nima farko ban gane ka ba sai daga bayan

Please Login or Register in order to submit comment