Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗakinta tana rangaji irin na ji da kai ɗin nan. Da Ido Amira ta bita har ta shige sannan ta ƙara mai da hankalinta gurin Ummi dake faɗawa Shukura abinda za a girka musu. Sai da Ummi ta tashi sannan Amira ta bi bayan shukura kitchen ta karɓi girkin ta girka musu white rice and pepper soup. Ummi bata san Amira tayi girkin ba har sai da taga tana jerawa a dinning. Ita kuma tana saukowa daga stairs.


“Shukura...”


Ummi ta ƙwala mata kira. Sai gaba da gudu tazo gaban Ummi ta tsaya.


“Ya kika barta tana jera kaya? Aiki aka ce miki ta zo yi ne?”


“A'a Wullahi Haseya sene yase zse girka ni in tafee”


Ummi tayi murmushin jindaɗi da kuma yabawa da halin Amira.


“To je ki taya ta jera kayan”


Da sauri shukura taje tana taya Amira har suka gama.


YASMIN POV.


Tun da ta dawo tunanin Namra take damunta, tana ganin idan har bata faɗawa Anty halin da Namra take ciki ba bata kyauta ba. Sai dai kuma tana tsoron faɗa musu kar ya zama tayi ma Namra kashin aure ko kuma ita Namra ɗin taga laifinta.
Dan Uzair ya gargaɗe ta akan karta faɗa tun lokacin data faɗa masa a irin halin data samu Namra.
Yau ma nanata mata yake kamar kullum.


“Babu ruwanki da matsalarta idan abin ya dame ta ai ita zata faɗa da kan ta, ba ita ta zaɓe shi ba, kin manta irin cin mutuncin da yarinyar nan tayi min?”


“Komai tayi maka Uzair be kamata mu ƙyaleta a halin da take ciki ba, wallahi baka gan ta abin tausayi, har dukanta yake duk ta canja kala”


“Ina ruwanki da canja kalar ta? Ba auren soyayyah tayi ba? To taje can su ci soyayarsu, wallahi Yasmin idan baki fitar da maganar nan daga ran ki ba, sai mun samu matsala da ke, kiji da cikin da yake jikinki dan Allah”


“Amman Uzair ni lauyace kuma..”


Ya taso ta haɗe bakinsa da nata......








DEDICATED THIS CHAPTER TO ZAGON K'ASA PAID GROUP MEMBERS. I LOVE YOU ALL 💖💖💖
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *53*


KALSOOM POV.


Haka ta fito asibitin hawaye na bin fuskarta amman bata damu ba, kamar ma bata san suna zuba ba. Bata iya gani sosai saboda hawayen daya cika idonta, sai dai hakan be hana ta tsayar da Mai a daidaita ba.
Tana shiga be sauke ta ko ina ba sai unguwar su Salma mai Napep ɗin ya sauketa, ɗari biyar ta miƙa masa bata tsaya karɓar canji ba ta smtura gate ɗin gidan ta shiga hawaye na bin fuskarta.
Ganin motar mijin salma yasa ta tsayawa a bakin ƙofar falon ta share hawayenta ta gyara tsayuwar hijabinta sannan ta tura ƙofar ta shiga tana sallama da muryar kuka.


Babu kowa a falon kasancewar yau monday ce yara basu dawo scul ba kuma ita da mijinta suna ɗaki. Saman kujera Kalsoom ta xauna ta dafe kanta tana sauraren hawayen da suke son zubo mata. Ta ɗauki mintuna talatin zuwa talatin da biyar a haka sannan Salma ta fito daga ɗakin mijinta tana dariya. Ganin Kalsoom ya razanata, dan da farko ta zata ko ba ita bace sai daga baya ta yarda Kalsoom ɗin ce jin sheshshekar kukanta. Ƙarasawa tayi ta dafata


“Ke miya same ki”


A maimakon ta yi magana sai kawai ta ƙara fashewa da kuka. Hakan yasa hankalin salma ya tashi sosai, har zauna kusa da ita tana girgiza ta


“Dan Allah ki yi magana ko wane ni ya mutu”


Daker ta samu natsuwar sai ta kanta sannan ta kalli salma ta soma mata bayani ba tare da hawayen sun daina mata zuba ba.
Salma ta girgiza da jin labarin har ta rasa yadda zata fassarashi tun da Kalsoom tace be ci guba ba.


“Kalsoom ko dai ya ci baki sani ba?”


“Wallahi be ci ba, bachi ma yake yi”


“Dole ne ya zarge ki Kalsoom ni kaina zan iya aikata kwatankwacin abinda Hilalya aikata, ba ze iya banbance ƙarya da gaskiya ba a yanzu, wata ƙila ya ci gubar ne ba tare da kin sani ba”


“Ba mu da abinda Rafiq zai yi saurin ɗauka ya ci a yanzu, he's just three years old, ni kuma ba zan dauka abu mai cuta na bashi ba, wallahi ban masa komai ba”


“Ba za ki masa ba Kalsoom ba halin ki ba ne, amman taya haka ta faru”


“Ban sani ba Salma wallahi ban sani ba”


Ta faɗa cikin wani irin kuka mai ban tausayi. Salma ta dafa ƙawarta tana hawaye ita tace


“Rashida bata zo gidan ba?”


“Bata zo ba, tun ranar daya sallameta bata sake zuwa gidan ba, kayanta ma sai daga baya ta turo ƙannenta suka ɗibi wasu”


“Allah kaɗai ya san ko mienen wannan abin. Amman abin akwai ban mamaki”


“Amman dai ɗazu na ji ana kirana a muryar Hilal lokacin dana leƙa ban ga kowa ba, har sau uku, a lokacin ne na ji ƙyalowar Rafiq”


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah yasa ba lamarin iska ba ne, kar ace ke aka jefa ya faɗa kan yaron ko kuma tayi ma yaron jifa dan ya mutu ace ke ce”


Kalsoom ta kalleta da sauri


“Ɗan ta ne fa”


“Ko ɗan ta ne fa? Ai zata iya aikatawa, idan zuciyar mutum bata da imani komai zai iya aikatawa”


“Na ji ni zata iya yin amman ba zata iya yi ma ɗanta ba, mu riƙa kyuatata zato Salma”


“Hmmm Allah dai ya kyauta, yanzu ina zaki je?”


“Ni ban sani ba, idan naje gida ban san me zan faɗa musu ba, ba lalle bane suma su yarda da ni”


“Kar ma kije gida a yanzu ki koma ɗakin mijinki”


“Amman yace min basa buƙata a yanzu”


“Komai yace miki tun da be ce kije gida ba karki je, idan kin koma gidan ki sa masa ido shi da yaransa babu ruwanki da sha'aninsu, har sai idan ya saki, amman yanzu idan kika koma gida zai ƙara jin haushin ki ne, ki bashi lokaci ya huce ya fahimci komai shi da kansa zai dawo yayi miki magana”


“Idan kuma na koma gidan ya wulaƙanta ni fa?”


“Ki jira har ya wulaƙanta ki ɗin amman yanzu gaskiya ban baki shawarar zuwa gida ba, Kalsoom ki koma ɗakin mijinki”


“Da nasan haka aure yake da ban yi ba, tun da na shiga gidan kullum da matsalar da take buɗe min sabon shafi, idan kuma ka zauna ba kayi auren ba jama'ah su zage ka, idan kuma auren ya mutu ace ka kaso auro ka dawo ma zaman gida, ba su san matsalar ka ba”


“Haƙuri zaki yi, haka LAMARIN DUNIYA (my previou novel) yake, kowa da yadda Allah ya tsara masa tasa rayuwarwa, no matter what you do how you try you can't escape your destiny and you can't change your past, all what you can do is wait for your future with hope and smiled behind your tears, rayuwar aure kala kala ce kowa wace ta kalar nata jarrabawar idan kika ji wani ma sai kin riƙe ba ki marriage is like going to a restaurant and order your choice from the menu, and then look at neighbouring table n wish you”d ordered that dole ki yi haƙuri babu komai a cikin rayuwar aure sai ƙalubale shiyasa kika ji akan ce kayi haƙuri haƙuri dai, kuma idan kika yi haƙuri tun a duniya sai Allah ya saka miki”


Kuka kawai take, bata iya cewa komai ba har Salma ta gama nusar da ita akan hanyar da take ganin kamar ita ce mafita a gareta.
Sai da tayi sallah la'asar sannan salma ta raka ta ta shiga Napep ta koma gidan mijinta, ba dan ranta yazo ba.
Cikin fargaba da tunani ta koma gidan a zatonta ko Hilal ya dawo, kar ya tambaye ta ina ta fito bata san me zata ce masa ba, tun da ba gida yaje ba. Sai ta tarar be ma dawo ba sai su Izzah da suka lalata falon da shinkafa suka watsar da uniform ɗin su a tsakar falon da scul shoes da bags duk a falon. Saman kujera ta zauna tana sauke ajiyar zuciya. Sai ga yaran sun fito cikin shirin islamiya sun, Ulfah ce taje ta rumgume ta, Izzah kam ko gefenta bata kalla ba ta fice.


“Anty mun dawo baki gida”


“Eh naje wani gurin ne”


Ta faɗa tana murmushin ƙarfin hali idonta duk ya cika da ƙwalla.


“To mun tafi makaranta kina da biyar ki ba ni?”


Ta tambaya tana cizon hijabinta. Naira ashirin Kalsoom ta ciro daga jakarta ta miƙa mata.


“Ki raba ke da Izzah”


“To mun gode”


Ta daka tsalle ta nufi ƙofa. Tana daf da ficewa Kalsoom ta kira, sai ta juyo tana kallon Kalsoom dake hawaye.


“Ki min addu'ah kin ji?”


“To mi zan ce?”


“Kice Allah yayi min mafita”


Sheƙowa tayi da gudu ta dawo ta rumgume Kalsoom tana share mata hawayenta.


“Ki daina kukan zan miki addu'ah i love you”


“I love you too”


Ta sake ta, ta juya da gudu ta fice tana kiran sunan ƴar'uwarta.


“Ezzah jira ni......”


Sai da suka fice sannan Kalsoom taja dogon numfashi ta cire hijabinta ta shiga gyaran falon.






YASMIN POV.


Duk irin jan kunne da kuma gargaɗin da Uxair yayi mata akan karta faɗawa kowa halin da Namra take ciki bata ji ba. Dan ta kada samun sukuni tun lokacin data ga halin da namra take ciki. Abin ya tsaya mata a rai, da ace ba Namra bace da kotu kawai zata saka Asim ta nemawa Namra haƙƙinta, an suna da ƙungiyar data hana cin zafin mata musmman mata hausawa da basa iya magana akan komai.


Daga kotu bata zame ko'ina ba sai gidan Anty. Daga Aisha sai Anty Amarya kawai ta tarar a gidan. Daga Hajiyia Barau har su Maryam sun je walima.
Anty Amarya tayi mamakin ganinta, duk dai ta kan biyo wani lokacin idan Uzair ya kawo ta gaishe da Hajiya Barau, sai dai ba kamar yau ba, dan ta sake sosai kamar ba ita, ta koma Normal kamar yadda take da.


“Yau Yasmin gidan mu? Hajiya ko bata nan”


“Eh Na sani ai, dan nasan zata je walimar Fateema, gurim ki na zo ma”


“Mashallah yau tafiyar tawa ce kenan”


Anty Amarya ta faɗa tana murmushi. Aisha ta dire mata drinks sai ta bar musu falon, daman can tun lokacin data na shiri da Namra jininta be haɗu da Aisha ba balle yanzu da suka koma zaman doya da manja.
Sai da ta sha lemun sai ta fara tunanin ta inda zata fillowa Anty dan bata jin zata iya faɗa mata maganar kai tsaye.


“Na ce when last kika je gurin Namra”


“An daɗe gaskiya tun mijinta na jinya, na so na koma sai tace na yi zamana ai za ta zo, lafiya dai ko?”


“Ayyah nima samina mukaje katsina sai na biya gidan ta”


“Ai ko kin kyauta Yasmin ko ke fa? Amman ace ɗan abu kaɗan dan ya shiga sai taren ku ya ɓace? Yadda kuke da Namra kamar wacce kuka fito ciki ɗaya da ita”


“Ni kai na da nasan haka rayuwar auren Namra zata kasance da ban hana Uzair aurenta ba...”


Jindaɗi da Murmushin dake fuskar Anty Amarya ya ɓata, ba tare da ta ƙarasa fahimtar gun da kalaman Yasmin suka dosa ba.


“Wani abin ne ya faru?”


“Anty da dai kin shirya kin je da kan ki kin ga Namra, kar na zama sheɗan”


“Babu wani Sheɗan Yasmin faɗa min, dan Allah ki faɗa min”


“Anty Namra tana cikin wani hali tana rayuwa irin rayuwar da babu wanda ya taɓa mafarkin zata shige ta, gidan da take ciki na ƙone a bq sune zaune, kuma mijinta ba shi da sana'ar yi, manja da magi take saidawa, kuma ko da naje fuskanta duk ya kumbura da alama dukanta yayi, tayi baƙi ta lalace kamar ba ita....”


Jikin Anty Amarya yayi sanyi sosai, har ta kasa furta kalma daga bakinta, mamakin labarin da Yasmin ta bata take ta sakarwa Yasmin ido tana kallonta har Yasmin ta koma.tunanin wata ƙila Anty bata yarda da maganar ta bane.


“Kishirya kije ki gano ma idon ki dan Allah karki ce ni na faɗa miki”


Kai kawai Anty ta ɗaga mata ta kwanta a kujera ta lumshe ido tana yaƙi da hawan jinin dake son taso mata. Yasmin na ganin hakan gabanta ya faɗi sai duk tsoro ya rufe ta kar wani abu ya samu anty ace ita ce, da sauri ta ɗauki makullin motarta da wayarta ta fice.




RASHIDA POV.


Tana aiki wayarta tayi ringing, amman bata ɗaga ba sai da ta kammala dukan abinda take. Sannan ta duba Number mai kiran.
Cousin ɗinta ce Shafa wacce suke aiki a asibiti ɗaya da Hilal.


Sai da ta kiran numbers ɗin da suka kira bayan ita suka gaisa suka yi maganar da za su yi sannan ta kira Shafa.


“Matar likita, ina ta kira baki ɗaga waya ba”


“Wallahi ina office ne aiki yayi min yawa, ya kike?”


“Au har kin samu damar aikin ɗan ki na kwamce asibiti”


“Ɗa na? Ɗa na na cikina ko na ƴan'uwa”


“Wai tsaya karki ce min baki sani ba”


“Wallahi ban sani ba me ya faru?”


“Wallahi ɗa zu da safe aka kawo shi guraren goma wai ya ci guba daker aka ceto shi”


“Guba...?! Garin ya?”


“Wallahi ban sani ba, mu dai muka taimaka masa gurin coto rayuwar yaron. Ni kam nayi mamakin rashin ganin ki a gurin”


“Guba ta bama ɗana kuma?”


Rashida ta faɗa cikin kuka.


“Au wai baki sani ba? Zance duk ya karaɗe asibiti ɗan doc ya ci guba an kawo shi asibiti, amman dan Allah ki rufa min Asiri karki ce gare ni kika ji”


Kashe wayar Rashida tayi ta tashi yana kuka ta fice daga office ɗin. Tana fitowa kowa ya soma tambayar ba'asi ganin tana kuka.


“Kishiya ta ce ta sama ɗana guba, yana can asibiti”


Kowa Amsar data ke basa kenan. Su kuma sai tsinewa Kalsoom Albarka suke suna aybantata. Kamin ta ƙarasa gurin motarta har ta kira su Momy ta faɗa musu.
Wani irin kuka take tana tuƙin motar har cikin ranta take jin abinda Shafa ta faɗa mata. Kamin ta ƙasara asibitin ana ta kiranta numbers ɗin ƴan'uwa da alama suma sun ji ne.






AMIRA POV.


Wani kalar daɗi ne ya baibaye ta tun lokacin data ji Ummi na labarta ma ƴaƴanta Abdool na nan zuwa dan sun gama meeting ɗin da zasu yi, ya samu free days zai dawo gida yayi su, daman tun faruwar abin nan be zo gida ba.
A ranta take shirya irin nata tabarda zata masa, wanda take tunanin zai ɗauki hankalinsa izuwa gareta. Girki ne abinda ta fara kawowa a ranta dan tasan ta ƙware a wannan fannin. Sai dai matsalarta ɗaya Amal dan itace mai cewa ba zata ci abinda Amira ta girka ba, a kullum idan Amira tasa hannunta a abincin gidan sai ta ce ba zata ci ba.


Ta baro part ɗin falon inda take zaune ta nufo gurin da Ummi take zaune ta zauna ƙasa kusa da Ummi kamar ta shige jikinta.


“Eh haka nek son ayi idan ya dawo sai kuje a duba gidan nan a gyara a zuba sabbin ƴan haya, dan gidan marayu ba a barinsa haka”


Sai da Ummi ta ƙare zancen da take sannan ta kalli Amira dake ƙasa zauna tana murmushi.


“Amira akwai da son jiki kamar Abdool”


Amira tayi murmushi idonta na cika da hawaye.


“Haka nake jin ki kamar mamana kina tuna min da mamana sosai, yanayin rayuwarki”


Hawaye ya silalo daga idon Amira, wannan maganar har cikin zuciyar Amira take, tabbas tayi missing Ammy gashi kuma bata san ranar da zata sake haɗuwa da ita ba, bata san halin da take ciki ba.
Zubar hawayen Amira yasa Ummi ta ji babu daɗi, wannan karon da kanta tasa hannunta ta share mata hawaye.


“Ki daina kuka kin ji? Zan zame miki uwa inshallah, kuma nan gaba zaki koma gurin uwarki na miki alƙawari”


“Na gode”


Ta rumgume Ummi tana wani irin kuka mai taɓa zuciya........


[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *54*


Hankali a tashe ta isa asibitin, hawaye na bin fuskarta. Duk wanda ya ganta a lokacin sai ya tausaya mata dan sun san abinda ya kawo ta asibitin. Daman tuni labarin ya karaɗe asibitin cewa Amarya Doc ta saka ma ƙaramin ɗansa guba. Sai ma a yanzu ne wasu ne suke jin cewar Doc ya rabu da Rashida.
Kowa tsinewa Kalsoom yake wasu na faɗin daman kishiyoyin yanzu haka suke su shigo su kore uwargida kuma su mallake ƴaƴan miji da miji.

Wani irin banka tayi ma ƙofar office ɗin Hilal ta shiga kamar zata tashi ɗakin.


“Ina ɗa na yake?”


Shine abinda ta tambaya hawayen na bin fuskarta. Ɗagowa yayi daga dafe da kan da yake ya kalleta. Be yi msmakin ganinta ba daman yasan zata zo tun da akwai ƴan'uwanta a asibitin da zasu kai mata labari.


“Ina ɗa na yake Hilal?”


Ya sake tambaya ganin yayi mata ƙuri da ido kamar ba dashi take magana ba.


“Ɗan ki ko ɗa na?”


“Ɗa na, si kai baka san zafin sa ba da baka bari wata ta kai ga ba shi guba ba”


Miƙewa yayi tsaye ya daki teburin dake gabansa.


“How dare you, idan kin san zafinsa ai bs zaki taɓa zuwa wani gurin ki aikata zina ba, ba zaki taɓa bada kan ki ga kowa ba sai ubansu, amman haka kika taka igiyar aure Rashida kika tsallae ƴaƴanki kika aikata zina da namijin da ba muharramin ki ba, na ƴi nadamar haɗa zuri'ah dake da ace wats na aura ba da rayuwar ƴaƴana bata kasance a halin data kasance a yanzu ba”


Tun da yake maganar take baya baya har ta jingiya da ginin ƙofar idonta na hawaye.


“I need to my son”


“You won't see him”


Ta muna kanta yana mamakin yadda duniyar Hilal ta birkice mata.


“Hilal ni ce!”


“And so what? Get the hell out of my office”


“Kotu zata raba mu da kai ba zan ƙyale kai da matarka ku kashe min ɗa ba”


Ta buɗe ƙofar da ƙarfi ta fice. Be damu ba dan yasan ya riga ya kulle ɗakin da Rafiq yake ciki tun bayan tafiyar Kalsoom.
Ba shida wani aiki amman haka ya zauna a office ɗin dan baya son zuwa gida kwata-kwata gidan ya fita aransa.
Haka ya riƙa karɓar masu shigowa suna masa jajen abinda ya faru tare da masa Allah ya tsare gaba, wasu kan tambaye shi ta ya lamarin ya faru wasu kuma su kuma basa tambaya ganin kamar cin fuska ne.


Bayan yayi salla magariba ya koma ɗakin da Rafiq yake ya zauna yana kallonsa. Ga dukan alamu ya samu sauƙi dan bachinsa yake hankali kwance, humfashinsa na tafiya dai-dai kamar yadda ake so. Ana daf da kiran salla isha'i Hajiya ta iso tare da wasu ƙanensa.
Hilal na ganinta ya tashi a kujerar da yake zauna ya miƙa mata ta zauna, sannan ya soma miƙa mata gaisuwa. Bata karɓa ba ta kalli Rafiq cikin tausayi tace


“Hilal ya aka yi haka ta faru? Wai Kalsoom tasa masa guba?”


Shiru yayi yana tunanin ta ta inda zai soma maganar da bata daɗin faɗi. Idan har ya amsa da ita ɗin ce bashi da tabbaci ita ɗin ce idan kuma ba ita ba ce to wanene bayan daga ita sai Rafiq ne abin ya faru?


“Wallahi ina meeting ta kirana ni ban ɗaga ba sai daga baya na kirata sai ta ce min na zo fida Rafiq babu lafiya, ina zuwa na tarar bakinsa na kumfa ko da na ɗauko na kawo sa asibiti kamar ba zai yi rai ba, bincike dai ya nuna guba ya ci. Tun ɗazu aka masa hoto amman ban karɓo ba”


Hajiya ta taɓa hannu tana salati.


“O o ita kuma haka take? Hilal baka dace da matan ƙwarai, yanzu ɗan wannan ƙaramin yaro ko kashe tayi me zata ji? Kai duniya”


Shi dai yayi shiru be ce komai ba, hannyensa zube a aljihu. Kamin su ƙara cewa wani abu sai ga Ummu Faisak ta turo ƙofa ta shigo fuska babu annuri irin yau tana cikin masifa ɗin nan.
Hajiya tayi mata kallon marar kunya da tarbiya ganin yadda take huci kamar baƙin maciji.


“Haba Maman Faisak ai ko ɗakin kafirai ne kya dokko ƙofa kamin ki shigo balle musulmai”


Uffan bata cewa Hajiya dan tana cikin zafin rai tasan kuma idan har tace zata tsaya maidawa Hajiya magana to dukansu rayuwarsu sai ta ɓace dan Hilal ba ƙyalewa zai yi ba.


“Ɗa zu Adda Rashida ta zo nan ka hana ta shiga ta ga ɗan ta, akan wanenen dalili ko ita ba uwarsa bace? Ba zamu ɗauki tsarin wulaƙancin da kake son mana ba akan shegiyar matar ka, ta fitar da Rashida cikin gidan yanzu kuma tana son ta bi ƴaƴanta ya kashe, idan ba zaka iya wani abu ba mu za mu iya dan ba zamu zuba ido ta kashe mana ƴaƴa ba”


Wani wulaƙantancen kallo Hilal ya watsa mata kana yaja tsaki, sannan ya kai hannu ya kwaɓe wayar wata ƙanwar Rashida dake ɗaukar Rafiq a waya.


“Ku fita ku bani guri ko nasa ayi muku wulaƙanci, idan ita Rashida bata iya ba ke taya zaki iya, banza a banza, ko dan kina ƴar jarida? Ku fitar min daga office yanzu nan”


“Za mu fita ai bamu zo dan zama ba, amman ka jira sakamakon ka, ba za mu ɗauki a wulaƙanta mana ƴar'uwa ba”


Cewar Khady sannan ta duƙa ta ɗauki wayarta, Suka fice. Hajiya ta dafe kai.


“O Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wannan masifa da me ta yi kama? Hilal ka rabu da matar nan ka huta daman masu tsantsar ladabi sun fi komai cuta”


Balki ta taɓe baki.


“Ni wallahi ban zata Kalsoom zata iya aikata haka ba, shiyasa ake cewa baka shedun mutum, mutum mugun ice”


“Hilal ka rabu da matar nan tun wuri kamar abin yayi maka yawa, ko ma shari'ah za su yi da ita suje can su yi amman ba tana gidan ka ba, sannan duk mace data fara da ƴaƴanka wata rana akan ka zata faɗa”


“Idan na rabu da ita kuma.. Da wa zan zauna”


“Sai ka nemi ƴar gidan malamai ka aura, kai ni ma zan nema maka ga mu da su a family masu hankali da natsuwa”


“Amman Hajiya zai zama ina ta aure aure”


“Ai kowa ya ji dalilin ka dole ya ɗaga maka ƙafa, amman ni gasjiya ban baka shawarar zama da matar nan ba”


Agogon hannunsa ya kalla.


“An kira Salla bari naje kar na rasa jan'in”


“Muma ai tashi za mu yi, amman wa xai kwana da shi?”


“Ni zan kwana da shi gida zan koma na canja tufafi sai na dawo”


“A'a ga Balki da Amina ai zasu iya kwana a nan”


“Akwai abubuwan da zan masa idan ya farka, so zai fi kyau na kwana da shi ɗin”


“Allah ya sauwaƙe ya bashi lafiya”


“Amin ya rabb”


Tare suka fito, sai da ya raka su gurin mota sannan ya nufi masallacin asibiti yayi salla isha'i.
Bayan ya fito daga masallaci ya koma office ɗinsa ya kulle office ɗinsa sannan ya nufi ɗakin Rafiq ya duba ya fito ya nufi gurin da aka tanadar likitocin asibitin su yi fakin ɗin motocin su.
Motarsa ya shiga, yayi mata key. Har ya fita harar asibitin be daina jin baya son zuwa gida ba. Be ƙara jin gidan ya fita ransa ba sai da yayi farkin harabar gidan. Ya ɗan daɗe cikin motar sannan ya fito.ya shiga cikin gidan.


Da gudu Ezzah da Ulfah suka zo suka rumgume ahi suna masa sannu da zuwa. Durƙusawa yayi a gurin yana shafa kansu.


“Dady Anty tana ta kuka tun ɗazu tace min Rafiq be da lafiya wai yana asibiti”


Ulfah ta faɗa tana wasa da rigarsa.
Be ce musu komai ba sai kawai ya nuna musu kujera alamar suje su zauna. Ezzah ce ta riga zuwa dan yau tana cikin nishaɗi, ganin Kalsoom na kuka duk yasata jindaɗi kamar wata kishiryarta.


Tashi yayi ya shiga ɗakinsa. Kwantawa yayi saman gadon ya lumshe ido yana sauraren kansa da ke tsarawa. Buɗe idonsa da zai yi ya ga Kalsoom tsaye a kansa hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarta, ta canja kama sosai fuskarta ta ɗan zurma idonta kuma ya kumbura har bata gani sosai da shi.


“Ya aka yi?”


Ya tambaya yana tashi zaune.


“Ya jikinsa?”


Maimakon ya amsa mata sai kawai ya miƙe tsaye ya soma cire kayansa har ya ɗaura tawul be ce mata komai ba sai kawai ya shige bathroom. Ta so ta nuna masa takardar sammaci da ɓoye a bayanta wanda Rashida ta aiko mata, amman rashin samun damar haka yasa ta juya ta koma ɗakinta, cikin wani irin baƙiciki da take jin kamar ta mutu a yau ta huta.


Bayan ya fito

Please Login or Register in order to submit comment