Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rashida na zaune falo riƙe da plate tana cin abinci, ba laifi yanzu kan ta ɗan samu sauƙi dan ita ma tayi girkin sa kanta. A bakin ƙofar falon ya tsaya yana kallonta wani tausayinta yaji ya lulluɓe shi har idonsa suka cika da ƙwallah.


Ita kuma ta ɗan kalle shi kaɗan ta kauce kai, ba dan bata son kallon nasa ba, sai dan baƙin kishi daya rufe mata ido, gani take yanzu ai ba ita kaɗai ce da shi ba.


Yana sako ƙafarsa a first step ɗin falon, sai ta tashi ta nufi ɗakinta. Shi kuma ya tsaya a gurin ya bita da kallo zuciyarsa cike da tausayinta.








______________________________________________
Assalamu alaikum Habibaties 🌺
Ina fatar kuna cikin koshin lafiya? Allah yasa haka Amin
My dear readers idan Allah yasa muna cikin masu rai da lafiya, idan na yi page 35 tau ZAGON ƘASA na Khadeeja Candy ya koma na siyarwa, daga bakin Page 35 har zuwa karshe na kudi ne, daga page 1 zuwa 35 free ne. Nasan zaku ga chanji yazo muku ba ta yadda kuka zata ba, ku yi hakuri ku min uzuri, haka sauyin ya zo. Kuma ina fatar zaku goya min baya, fiye da yadda kuke min a da, soyayyar ku da haɗin kan ku, shi na ke fata a kullum, Allah yasa ku min kyakkyawar fahimta. 😊👌


Ga waɗanda suke sha'awa. Naira ɗari biyu ₦200 zaku turo ta wannan account ɗin 0314795884 Abubakar Hadiza GT Bank.
Ga wanɗanda basa da account kuma za su iya turo katin waya na line mtn na dari biyu da hansin ₦250 ta wannan number 08036126660


Idan kun tura. Sai ku turo da shaidar biyan kudin wato screenshot ta wannan number 08036126660.


NA GODE 😊


BEST REGARDS 💖🌺
KHADEEJA CANDY😘
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng


*PAGE - 32*


NOT EDITED ⚠️


Ɗakinsa ya wuce ya aje kayan da suke hannunsa, sannan ya fito ya shiga ɗakinta. Zaune ya same tana taunar naman abincin data gama ci, kusa da ita ya zauna yayi mata ƙuri da ido, kamar mai tunanin abunda zai faɗa mata.


“What?”


Ta tambaya shi sam be san ta lura da kallon da yake mata ba har sai da tayi magana.


“Bana da ikon kallon ki ne?”


Ya faɗa yana murmushin ƙarfin hali.


“Kallo na nawa kuma, ai na gaji da kallon nawa ne shiyasa kaje ka ɗauko wata, kuma ni ka faɗa mata ta daina zuwa min yawo da yara karta lalata su”


“Uhmm, Pyar ki daina sawo zance Kalsoom a gurin da muhallinta ba, ke da ita duka ɗaya kuke a guna, wani abun da kike faɗa akanta ba daɗe yake min ba, and you know what ita bata taɓa wani mugun furuci akan ki ba, balle kuma akan ki ba, sannan tana kula da ƴaƴanki”


Ta taɓe baki ta aje plate ɗin ƙasa.


“Wallahi duk son ƙarya ne, babu kishiyar data zata so ƴaƴan kishiryarta, wannan duk Zagon ƙasa ne”


Ya kai hannu ya riƙo hannunta.


“Naji pyar faɗa min when last nayi miki gwajin jini?”


“I can't remember, ba kai kake min ba?”


Ya ɗanyi shiru.


“Ina ganin anyi shekara biyu yanzu, saboda ba samun zama nake ba, miya faru?”


“Ba komai, zan sake ɗibar wani ne, wacan a mota ya ɓata fitsarin kawai na auna”


“Okay amman yau zaka ɗiba, dan gobe zan je aiki”


“Daga jin sauƙi sai kuma zuwa aiki?”


“Kasan matsalar banki tun yau ma aka so na koma”


Hannu ya kai ya shafa gefen fuskarta.


“Pyar i love you so much ki sa wannan a zuciyarki, mijinki yana son ki sosai”


“Yana son mu dai point of correction”


Ta faɗa tana wani yatsina fuska, shi kuma yayi murmushin da be kai zuci ba, ya tashi tsaye.


“Bari na yi wanka”


“As you wish”


Bayansa ta bi da kallo zuciyarta na mugun tafarfasa, duk yadda take so mijinta idan ta tuna da ba ita kaɗai yake so ba, sai ranta ya ɓace.

Sai da yamma lis sannan Kalsoom ta dawo, dan yau gidan su ta wuni ita da yara, daman duk ranar da ba'a zuwa makarantan ilamiya, ta kan yi amfani da lokacin ta koyar da su wani abu na rayuwa ko kuma addini, sai ya kasance yau kan tana buƙatar zuwa gida gaida du Momy, shiyasa ta kwashi yaran duka suka je gidan.
Tayi mamakin ganin Rashida tayi abinci a yau bayan kuma jiya ta gama koken bata da lafiya, kusan kwana biyu nan ma har cewa take ita ba zata iya cin komai ba.


Ta san yau Doc ba a ɗakinta yake ba, hakan yasa bata damu da dole sai ta ganshi, dan ko da suka dawo, baya gidan Rashida ce kawai, kuma har dare be dawo ba.
Da wuri yaran suka yi bachi saboda gajiya, sai ya rage ita kaɗaice a falon sai tv tada tisa a gaba tana kallo. Saman kanta Rashida ta zo ta tsaya sai wani yauƙi take kamar ance mata Doc ne a gurin zaune.


“Ammyn Rafiq ya idan zaki fita da yara ki riƙa faɗawa Dadyn su, yazo nan yana ta min faɗa wai shi baya son yawo kar a lalata masa yara”


Kalsoom ta ɗago kai ta kalleta tana murmushi


“Ai ni kaina ban fita ba, sai da na nemi izininsa, balle kuma na ƴaƴansa, I'm friendly Rashida feel free to tell me baki son ina fita da yaran ki, is okay sai na tura su duk inda nake so”


Bata tsaya jiran abunda zata sake cewa ba, ta aje remote ɗin dake hannunta, ta tashi ta bar mata falon.
Da wani mugun kallo Rashida ta bita ji take kamar ta tashi taje ta maƙareta, bata san tana kishinta ba ma sai a yanzu data kwana biyu nan a gida, ita dai gani take Kalsoom ta tare mata guri.


‘Ni ban ga abunda matar nan ta fini da shi ba, yaje ya kwaso ta, mace sai baƙin munafurci, Wallahi kin yi kuskuren auren mijina dan mijina mijin Rashida ne ƙadai ba dawata macen ba’


Ƙwafa tayi tana wani huci kamar maciji, ta juya ta koma ɗakinta. Saman gado ta zauna tana sauraren yadda zuciyarta take mata zafi, kishin Mijinta take ji sosai, sai a yanzu take gane abunda wasu ƴan grps nata na whatsapp suke faɗa mata akan kishiya, ya karɓe mata ƴaƴa, yanzu kuma tana ƙoƙarin karɓe mata miji, gashi Hajiya ma tafi son Kalsoom da ita.


Wayarta ta ɗauko ta aika ma da Asmee kira, sai da ta mata two missed calls sannan tayi picking.


“Ina ta kira hala baki kusa?”


“Eh Wallahi ya gida?”


“Gida ƙalau, ni dai ce hankali ba kwance kuma ban ji kin kira ni, Asmee idan mukayi sake fa matar nan ƙwace min miji zata yi”


“Wallahi ban samu naje bane, bana jindaɗi sosai, amman inshallah gobe zan je”


“Ayyah me ke damun ki?”


“Ina jin ƙiba ne sai kuma Infection ya shiga ciki”


“Indai Infection ne ki nemi ɗayyar citta da tafarnuwa ki feraye cittar ki ki jiƙa su, su jiƙu sai ki riƙa sha ko kuma ki nemi maganin nan Cantin yana yi sosai. Na rage tumbi ko kiba kuma ki samu ganyen guava guda bakwai ki tafasa with one liter of water kisha for seven day's mrng before breakfast da kuma last thing kafin kwanciya, shi Momy take kuma wallahi na sauka ta rage ƙiba sosai cikin satina ɗaya yayi mata aiki wallahi, masu ulcer ma zasuyi yana maganinsa, irin wannan yafi na asibitin dan shi ba shida side effect. Allah ya baki lafiya”


“Amin na gode sai kin ji ni”


Daga haka sukayi sallama, Rashida ta aje wayarta tana faɗin


“Garin kwashe kwashen ki dai sai kin kwasowa kan ki, ba ko wane malami bane zai haɗe yawunsa akan ki, ni ko zan yarda ai ba zan malaman ƙauye ba ƙazamai”


Ta ƙarasa maganar da tsire baki, duniyar tunaninta na son dawo mata.
A gogon ɗakin ta sakarwa ido daga seconds zuwa minutes take ƙirgawa har ya kai ga hours, Doc be dawo gida ba, haka ta gaji ta kwanta saman gado idonta a ƙafe, babu abunda take tunani sai Rashida.
Yadda ta shiga cikin gidan da kuma irin rawar data taka tun daga shigowarta zuwa yanzu, bata ankara hawaye suka silalo mata.
Sai yanzu take jin yadda ɗacin zuciya yake, sai yanzu take jin son Hilal na haƙiƙa a zuciyarta, sai yanzu take gane ta tabka kuskure da tabar shi ya ƙara aure, yanzu haka zata kasance ita da wata a cikin gida? Haka itama zata gina nata rayuwar ta karɓe mata kowa?


Tafiyar daƙiƙa biyar zuwa shida numfashinta yayi kamin ya dawo izuwa gareta har ta ankaro da duniya take, ta samu damar amsa sallamar mai gidan nata.


“Wa'alaikassam”


Sautin muryarta ya isar masa da saƙon damuwarta, ga kuma hawaye dake kwance a fuska. Ledar dake hannunsa ya aje ya zauna kusa da ita gabansa na faɗuwa, har zuciyarsa ta fara raya masa wani abun na dabam.


“Miya faru kike kuka?”


“Kawai ina tunanin rayuwa ne, da kuma irin sakamakon da kayi min, bayan nayi maka dukan hallacin”


Masauki yayi mata a ƙirjinsa, ya kai hannu ya dafa cikinta, zuciyarsa na hasaso masa wani tunanin na daban.


‘i just can't believe that, taya wannan cutar zata kusance mu? Allah kar ka jarabe mu da abunda zai sa rayuwar mu data ƴaƴansu cikin damuwa’


A can cikin duniyar tunaninsa, kunnuwansa suka cinto masa wasu kalamai da Rashida take ta maimata masa.


“Ni kar ta sake fitar min da yara, kar taje ta lalata min su, kaji”


“Ba zata lalata su sai dai ta gyara tarbiyarsu, bakin ki ya daina furta mummun kalamai a kan Kalsoom, zamana take ba zaman ki, dan haka babu ruwanki da ita”


Da gautsi ya ƙarasa mata kalam, wanda har zuciyarsa haka take, dan kawai yana son ta ba zai yarda ta da aybanta masa amarya ba, dan shi ya san darajarta, kuma yasan gidan data fito.


“Ƙara ma ku haɗa kan ku dan ni ba zan ɗauki irin wannan abun ba, mu taru mu gode Allah akam kyautar da yayi mana, kuma ku yi fatar Allah ya sauke ku lafiya”


Kalamansa basa buƙatar fassara, kai tsaye ta san inda suka dosa, daman ita ta san ciki ne da ita, to Kalsoom fa ita ma cikin ne.


A take yawun bakinta suka tsinke, cikinta ya ɗauki kuka, ba ƙaranin ƙoƙari rayi ba wajen ƙawata fuskarta da murmushi, dan ta nunawa Hilal ta jidaɗin.


“Mashallah Kalsoom ita ma tana da ciki? What a blessed”


“Tana ma har ya riga na ki, bata da matsala sosai ne shiyasa ba za a gane tana da cikin ba”


Amsarsa ta tabbatar mata da zarginta, daman dalilin tambayar kenan. Wata duniyar take ƙoƙarin kai shi dan ta nuna masa farincikinta, ta kuma ɓoye masa baƙincikin da ke son bayyana a fuskarta.


Zuwana Kalsoom yasa ya daina takura akansa a kanta, duk magiyar da yake mata yake nuna mata maitarsa yanzu ya daina tun da ya samu wani halalin nasa, sai dai daren yau da raya masa shi fiye da yadda yake zato, a yau tayi masa abunda ta shekara goma bata masa ba, ta sakar masa jikinta sosai, har sai da shi kansa ya gaji dan kansa ya bar.


Tare suka yi wanka, suka ci abinci da kuma dan abun taɓawa daya siyo musu ɗazu, a lokacin ƙarfe biyun dare yayi. Suna gamawa ta kwanta dan ba gado haƙƙinsa, shi kam be kwanta ba sai yayi nafisa raka'ah biyu, raka'ar farko ya karanta fatiha da ayatul kursiyu sai ya dora kulhuwallahu sama, a raka a ta biyu kuma ya karanta fatiha da amanar rasulu ya ɗora kulhuwallahu sama, sannan ya zauna yayi zaman tahiya kamin ya sallame a cikin tahiyar ya faɗawa Allah buƙatarsa, sannan ya sallame.
Sai da yayi salatin annabi da godiya ga Allah da istigifari ƙafa ɗari ɗari sannan ya sake ɗaga hannu yayi kirari ga ubangijinsa ya nemi yafiyarsa, sannan ya sake koro da buƙatarsa.


A cikin ɗauko abun ɗibar jini ya ɗibi jininta dan yasan da safe ba zai samu damar ɗiba zata ce masa aiki.
Washe garin da zai kai yaransa makaranta suma ya ɗibi nasu, Kalsoom kam sai daf da zai fita sannan ya ɗibi nata sai raki take masa tana masa shagwaɓa, wai da zafi ita zai ƙarar mata da jini, haka ta riƙa narke masa a jiki har yayi lattin zuwa aiki.






NAMRA POV.


Kwata-kwata bachi ƙaura yayi mata daga ido, bata ma jin alamunsa balle har tasa rai zai so mata, abu ɗaya zuwa biyu yayi mata tsaye a rai, maganganun da Asim yayi shi da mahaifiyarsa, wata zuciyar na shawarta akan ta bayayyana masa ta kuma tambaye shi abunda yake ƙoƙarin ɓoye mata, yayinda ɗayar kuma take ce mata ta haƙura taga iya gudun zuwansa dan tabbatar da zarginta.


Babu amfani da raya dare da tunani bayan Ubangijinta yana kallonta, kuma yana shirye ya amsa buƙatunta, tayi haramar ƙorar sheiɗan sannan ta samu kuzarin fita tayi alwalah, sannan ta dawo ɗakin tayi nafila ta ɗora sa salatin Annabi.


Firgigit Mardiya ta farka daga dogon bachin da take a farkigice har tana ihu. Namra ma dake kusa da ita sai da ta ji tsoro kowa dake cikin ɗakin ya matsa, Mahaifiyarta ta tashi tana kallonta.
Gabanta ta fara kallo kamin ta kalli bayanta, sai kuma ta bi ko'ina na ɗakin da kallo, ajiyar zuciya ta sauke yafi ashirin, sannan ta haɗe yawun bachin da suka cika mata baki, ba dan tasan tayi ba.


“Ke lafiyarki?”


Ashe dai duniya take, jin muryar mahaifiyarta ya ƙara tabbatar mata da a farke take.


“Wallahi wani mumunan mafarki na yi, wai wuta tana bina”


“Subhanallahi, ke kuwa ai addu'ah zaki yi”


Namra ta faɗa, tana rufe ƙur'anen dake hannunta, sannan ta nufi gurin bachinta tayi addu'ah bachi ta kwanta ba dan tana jin bachin ba, sai dan tana buƙatar jinginar da jikinta da tabar suka saba mata shimfiɗa da ita.




Washe gari...
Da sassafe ta siye tea da buroɗi ta nufi asibiti, dan bata son su Mama su kama hanya bata isa ba, tun da babu wanda zai kula da Asim sai ita. Duk yadda take ganin ta doka sammako sai taga har sun fi ta, dan tana shiga ɗakin taga alamar sun kama hanya.
Bata yarda ta nunawa Asim komai ba, ta gaisheshi sannan ta masa ya jiki ta soma zuba masa tea ɗin.


“Jiya kika tafi baki faɗa ba”


“Eh pad ɗina ne ya lalace shine naje gida na canja, su Mama sun kama hanya ko?”


Ajiyar zuciya ya sauke, yanzu kam hankalinsa ya kwanta, daman can yana tunanin ko ta ji maganar sune yasa taje ba tare data faɗa musu ba, ashe shi da Mama ba su canka dai-dai.


“Eh tace da wuri zata je yadda zata tararda matar da za a ranto kuɗin gareta”


“Allah yasa a dace”


Ta faɗa tana miƙa masa tea, kallon da tayi masa da kuma maganarsa sun zari zuciyarta, miyasa Asim yake ɓoye mata? Wani tunanin ne ya zo mata sai ta kawar da fuskarta gefe.




_______________________________


BEST REGARDS 💖🌺
KHADEEJA CANDY😘
*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

Website
www.khadeejacandy.com.ng


*PAGE - 33*


NOT EDITED ⚠️




Washe garin ranar da Mama ta tafi ta dawo, guraren uku da rabi na rana. Ita kaɗai ta dawo ba tare da Hajara ba, Namra bata nuna mata komai ba ta tarbeta da far'ah tana mata sannu da zuwa.
Tana son tayi labari Namra ta tsare su taƙi ta tashi, shi kansa Asim yana son magana da ita amman ba dama, tun da Namra tana gurin.


Kamar ta san Namra bata tanadar mata komai, tun a hanya ta tayi gurin biredin ta da lemu, sai ta ta ci ta ƙoshi, sannan ta tashi ta fita.
Da kanta taje ta biya kuɗin maganin dan kar taba Namra.


Ta dawo daga biyan maganin ne, Namra ta tashi tayi musu sallama ta baro asibitin.


Har ta iso gida kuka take, tana tunanin yadda Asim yake ɓoye mata lamarin, dan ta lura da yadda suke kallon kallo da Mama, hakan ya soma tabbatar mata da abunda Anty Amarya ke faɗa mata.


“Idan har ta tabbata Asim na son yaudarata....”


Sai kuma tayi shiru ta share hawayenta, ta miƙawa mai Napep kuɗinsa ta shige gida.




*** ***
“Thank you”


Ta faɗa tana murmushi tare da kallon mutumen daya tashi daga saman kujerar ta ya nufi ƙofar fita. Sai da ya fice sannan ta kalli wayarta dake ringing, sannan ta kai hannu ta ɗauka zuciyarta na raya mata irin labarin da Asmee zata bata.


“Ƴar gari kamar kin san yanzu nake tunanin ki nace ko kin samu zuwan kuwa?”


Kuka ta fara ji kamin Asmee ta ɗora mata da zancen dalilin kiran nata.


“Rashida ina ciki matsala”


“Lafiya miya faru?”


“Wani malami ne da muke zuwa gurinsa, yana ba mu taimako, shine yanzu ake ce mana malamin yana da ciwon nan na zamani, shine tun ranar na kasa sukuni ban ma sama naje gurin matsalar ki ba”


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Asmee garin yaya? Ya taɓa sex dake ne? Ko me?”


Kuka tayi sosai har ka kasa magana.


“Ki faɗa min mana ki daina kuka”


“Ya taɓa lokacin da je neman wani taimako sai yace min sai na kawo sperm ɗin wani wanda ba mijina ba, da jinin al'ada da shi za a haɗa, ni kuma na ce masa ban san inda zan samo ba, shine....”


Ta ƙarasa da kuka


“Ke yanzu kin je an gwada jinin ki ance kina ɗauke da ciwon ne? Stop crying and tell me Asmee”


“Ban je ba, tsoro nake ji ban san wanda zan faɗawa ba sai, dan bani da ƙawa irin ki, na rasa yadda zan yi tsoron gwajin na ke, aiki ma na daina zuwa yanzu”


“Innalillahi Ya salam Ya salam”


Ta soma zagaye office ɗin tana dafe kai, da wayar a kunnenta.


“Ki kwantar da hankalin ki kinji karki faɗawa kowa, kuma karki yi abunda zai sa mijin ki ko wani ya zargi wani abu, i will call you back”


Tayi saurin kashe wayar tana tuna jininta da Hilal ya ɗiba, idai har Asmee ta kamu da cutar to itama zata iya kamuwa da ita tun da har suna using mutum ɗaya.
Faɗuwa tayi zaune zumi na keto mata ta ko'ina, hannu ta kai tana shafa kanta, tana girgiza shi kamar wani ne a gabanta.


“Ko shiyasa ya sake ɗibar jinina? Amman kuma ai da ba zai kusance ni ba, amman yanzu idan ya auna dole ya gano idan akwai shi”


A fili take furucin zuciyarta a karaye, jikinta har tsimi yake, yanzu kam hannaye biyu tasa ta dafe kanta tana tunanoma kanta mafita.


“Dole ne na dakatar dashi daga yin gwajin, kuma dole ne nima naje na bincika kai na, indai har da gaske ne Asmee kin cuce ni”


Da sauri ta tashi ta kaɗe jikinta ta fiddo hoda a jakarta ta gyara fuskarta sannan ta ɗauki jakar ta fita. Sai da ta biya ta faɗa musu fitar gaggauwa ta kamata, sannan ta fito harabar bankin ta shiga motar, ta ɗauki hanyar Asibiti.


Akwai ƴar tazara tsakaninta da asibitin, amman yadda ta sakarwa motar wuta yasa ta isa cikin ƙanƙanen lokaci. A harabar asibitin tayi parking, ta fito ta duba gurin da aka tanadarwa manyan likitoci dan faka motocinsu.


Motar Doc Hilal ce ta uku a gurin, that's means yana cikin asibitin, safa da marwa ta fara yi tana tunanin ta inda zata fara. Lab ne ya faɗo mata a rai. Da fargaba ta kutsa kai cikin asibitin ta ɗauki hanyar da zata hada ta da lab ɗin, ƙasa-ƙasa take kallon mutane, tana fargabar haɗuwa da Hilal, dan ko ganinta yayi bata san me zata ce masa ba.


Ta tararda mutane da ɗan yawa a gurin da aka tana da dan karɓar results ɗin jini da fitsari, hakan yasa ta zagaya ta shiga ciki tun da ita ba baƙuwar asibitin ba ce.
Biyu daga cikin mutanen da suke gurin sun gane, tun da sun san matar Doc ce, cikin mutunci da far'ar ta gaisa da su tana yi tana kallo ƙofa.


“Habib na ce kun gama gwajin jinin da Doc ya kawo? Za a tafi dashi wani garin ne”


Wanda ta kira da Habib ɗin ya amsa da.


“Eh tun ranar muka shi ba ai”


“Ba yau ya kawo ba?”


“A'a ina jin tun monday ne, Monday or Tuesday? Abbas kai ka bashi ko?”


Wanda aka kira da Abbas ɗin be ma kula.da zancen su ba sai rubuce-rubucen sa yake, Habib ɗin ya kalleta.


“Ina jin Monday ne, an dai kwana biyu yanzu”


Gabanta ya faɗi sosai.


“O'o nasan ya jefar da results ɗin wani wajen shiyasa ya ƙi ya faɗa min, amman yau be kawo maka wani ba?”


“Gaskiya be kawo ba, dan mu muka yi duty safe yanzu zamu tashi”


Nauyi zuciyarta sosai tayi mata har sai da ta tsayi ya gagareta, ta zauna a kujerar dake gurin.


“Amman dan Allah ya za'ayi na samu results ɗin wacan gwajin? Tun da ya ɓatar nasan ba zaku rasa a littafin ku”


“Wallahi da an fito da results ɗin an rubuta a littafi ansa a paper na results ɗin ake kai su ɗakin ajiya, sai dai shi Doc zai iya zuwa yayi ma Doc Omar magana, sai ya bincika masa, amman nan results kawai muke badawa”


“Okay Thank you bari na koma gurin Doc ɗin nayi masa magana”


“Okay a gaida yara”


Ya faɗa yana kallon bayanta, irin ƴan iskan samarin nan ne da basa gani su kauda idonsu.
Ƙafafunta sun mata nauyi, ga idonta dake son ciki da ƙwalla tana mayarwa, akwai ƴar tazara tsakanin office ɗin da lab, hakan ya bata damar tunanin abunda zata cewa Hilal idan ya ganta, idan kuma ta koma bata shiga ba ta san zai iya samu labarin ta shigo cikin asibitin tun da akwai waɗanda suka santa, kuma zasu iya faɗa masa.


_Thank you so much my tomatir my albasa my daddawa my miyar kuka_


Yana dannawa Ƙalsoom reply ɗin ta whatsapp. Rashida ta turo ƙofar office ɗin ta shigo da murmushi a fuskarta.
Tashi yayi daga jinceren da yake saman kujera ya kalli da dariya.


“Surprise surprise surprise”


“Yes Darling, na biyo ta nan baya ne shina nace bari na biyo na ga farinciki na”


Ya ɓata rai sosai lokacin daya lura da yanayin tufafin dake jikinta. Suit ne mai wando ta riga sai ɗan ƙaramin hijabi dake kanta.


“Daman Haka kike fita daga office? Ba mun yi maganar nan dake ba dan me zaki fito baki ɗora abaya a sama ba, a cikin office ɗin ki kawai na yarda ki riƙa zama haka, kika ce kin ji ashe ni kike ma ko? Yana ɗaya daga cikin dalilin daya sa bana son aikin nan na ki, bana son wani na ganin matana abun nan yana min zafi”


Sai a lokacin ta kula da tufafin da suke jikinki, tsabar hankalinta baya jikinta bata ma san ta fito a haka ba. Hannayenta tasa ta laƙamo wuyansa.


“Im sorry Wallahi fitar gaggauwace shiyasa amman ba zan sake ba i promise”


“Yanzu haka kika shigo a asibitin nan kowa na kallon ki? Haba Rashida idan an girma a san an girma mana, kefa uwace kamata yayi idan kin ga Ezzah tayi wannan shigar kiyi mata faɗa ba wai ki yi ba”


Ta saki wutan nasa ta nufi freezer dan ita ba faɗan da yake mata bane a gabanta, abunda ya kawo ta take ƙoƙarin yi, tsayawa tayi ta duba da kyau drinks ɗin da tasan babu a freezer ɗin tace masa tana so.


“Nidai nace kayi haƙuri, kuma ina son nasha coc”


Ta faɗa tana marairaice masa, daman tasan baya shan coca-cola saboda irin abubuwan da ake faɗa akanta, kuma ta san yadda ya tsani kayan yahudawa.
Kamar zai ce mata babu, sai kuma ya ƙyaleta tun da yasan tana da ciki wani abun dole ya ɗaga mata ƙafa, sai dai be sakar mata fuska ba dan har yanzu ransa a ɓace yake, sai kawai ya juya ya fita.


Da sauri ta nufi teburinsa ta fara duba takardun da suke gurin, bata ga abunda take nema ba, hakan yasa ta nufi wata ƴar ƙaramar wardrobe dake gefen kujerar, har ta kai hannu ta buɗe sai kuma wani tunanin ya zo mata.


‘Idan na yamutsa masa takardu dole zai zargi wani abu’


Sai kawai ta fasa buɗewa ta koma ta zauna a kujerarsa

Please Login or Register in order to submit comment