Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai dan son da nake maka, to dan me wani abun zai rufe min ido har na zarge ka?”


“Uhmm”


Ya janye hannunsa, yana kallon ƙofar ɗakin kamar mai jiran shigowar wani.
Can kuma ya kalleta


“Ina ganin idan an gama min allurar nan, ya kamata ace mu koma gida saboda asibitin nan in ban da kashin kuɗi babu abunda suke ja mana”


“Gidan ma sai an gyara za'a zauna, saboda gate ɗin ya ɓangale gefe ɗaya, kuma BQ nan tsoro take bani”


“A haka dai zamu daure mu zauna”


“Da ace da hali da an gyara gate ɗin, in yaso BQ ɗin sai a share a wanke”


“Sai ki gyara da kuɗin da Anty ta aiko ai zasu isa”


“Amman ba kaji nace bashi zan biya ba? Sai dai na siyar da sarƙa na gold a gyara”


Ya kalleta a kai-kaice


“Ina kika samu sarƙar gold? Ba kin ce komai ya ƙone ba?”


“A hannu Mardiya na gani ɗazu har da wayana ma, ita ce ta satar min”


“Mardiya? Ya akayi kika gani?”


“A ƙasan a kwatinta, saboda jiya na saka kuɗin daka bani a cikin kayanta, gurin nema ne sai na wayar har da sarƙar ma, da wasu ƴan kunne da Hajiya ta taɓa raba mana lokacin data dawo makka”


“Amman ya akayi Mardiya ta shiga har ciki ta ɗaukar miki sarƙa har da waya ma?”


“Ban san yadda ta ɗauka ba wallahi kawai dai na kamata da su ne a yau, kuma nayi mata masifa ita da Mamanta”


“Aikowa baki kyauta ba, yarinyar duk hidimar da ake ta zuwa asibiti da ita ake yinta, anya ma ita ta ɗauka? Dan gaskiya yarinyar nan tana da natsuwa da tarbiya”


“To idan ba ita ta ɗauka ba ya za'ayi na gani a akwatin ta? Kuma fa taji lokacin da ina nema”

“Yanzu idan kin siyar me zaki yi da kuɗin? Namra wai kin faɗawa Abbah mun yi wuta kuwa?”


Ƙasa tayi da kanta.


“Ban faɗa ba, babu wanda ya sani”


“Nima bana son kowa ya sani dan muna da maƙiya za su mana dariya, amman dai su ai kamata ace sun sani, rayuwa tayi haka? Namra ki duba halin da nake ciki, babu wani taimako sai na Allah, yanzu idan kuɗin nan da muka ranto suka ƙare kina tunanin akwai inda za mu sake dubawa? Ban san miyasa rayuwa ta zo mana a haka ba, kana neman ka ɗaga kayi gaba, amman sai baya kake abubuwa suna ƙaruwa”


Ya ƙarasa maganar idonsa cike da hawaye.


“Inshallah zan faɗa mata idan na je, tace na tambaye ka idan ka bar ni sai naje”


“Gurin me?”


“Tace tana son gani na ne”


Har zai ce wani abu, sai kuma yayi shiru yana nazari, idan har ya barta yaje be san abunda zata samo ba, musamman idan ta faɗa musu halin da suke ciki.


“Amman ba zaki daɗe ba ko? Kije amman kwana biyu za kiyi ki dawo”


Hannayenta tasa ta rumgume shi, tana murmushin jindaɗi.


“Na gode daman nima ba zan wuce kwana biyun ba, Allah kara maka lafiya”


Har cikin ƙasan zuciyarta take jin son Asim, sam bata iya gani illarsa, saboda zuciyarta tana muradinsa, a take zuciyarta ta fara raya mata ya ɓoye mata maganar kuɗin wata ƙila saboda karta sa ci suna da kuɗi, kuma ita kanta bata san yadda yayi ya samun kuɗin adashen ba, sai dai abunda ya faɗa a wacan lokacin ya tsaya mata a rai, a duk lokacin data tuna sai ta ji babu daɗi, har zuciyarta ta zarge shi akan haka.

HILAL POV.


A haukace ya isa asibiti, dan a tunaninsa Rashida ta mutu, shi da kansa ya kai ta emergency room, tare da taimakon wasu Nurses ya shiga neman numfashinta.


Da taimakon Allah komai ya daidaita, sannan ya ɗaura mata drip, yayi mata allurar. Tsaye yayi cikin ɗakin yana kallonta bayan Nurses ɗin sun fita.
Wayarsa ya shiga lalabe sam ya manta da tana ciki mota, sai yanzu. Fita yayi be daɗe ba ya dawo tare da rigar asibiti da wasu kayan aiki, sai ya canja mata tufafin jikinta, ya gyara mata jikinta sannan ya saka mata rigar, sai ya kira wata ma'aikaciyar gurin mai share-share ta kwashe kayan.


Zaunawa yayi a gurin ya ɗafa kansa, sai ga wasu daga cikin abokan aikinsa sun shigo duba ta, sama-sama ya amsa musu, suma sun ga damuwa ƙarara a fuskarsa, sun lura da yanayinsa, duk a tunaninsu saboda Madam bata da lafiya ne.
Fatan sauƙi suka mata sannan suka fita, shi kuma ya tashi yaje gurin motarsa ya ɗauki wayarsa ya kira Hajiyarsa ya faɗa mata, sannan ya kira Momy ita ma ya faɗa mata.


A cikin motar ya shiga ya zauna ya tasa abunda ke masa daɗi duniya, baya son yaransa su san komai a tsakanin su, kuma be san wane bayani zai yi ma Hajiyarsa ba da Momy, sam baya son duniya tasan abunda Rashida ta aikata, sai dai kuma be san yadda zai yi yayi ya ɓoye ba, cox he's no more to her.
Be ɗago kansa daga tunanin da yake ba, wayarsa tayi ringing, number Momy ce a rikice take tambayarsa wane ɗaki Rashida take.


Sai da ya buɗe Motar ya fito sannan ya amsa ta.


“Kin shigo Asibitin ne ?”


“Eh ina emergency”


“Okay tsaya a gurin zan ƙaraso yanzu”


Ya kashe wayar tare da rufe motar, sannan ya nufi gurin da yake zaton take. Tun daga nesa ya hango ƙannenta biyu. Cikin rashin kuzari ya ƙarasa inda suke ya gaishe ta, su kuma ƙannen suka gaishe shi. Sannan ya wuce dasu zuwa ɗakin da take.
Ganin halin da take cikin yasa Momy har ta fara hawaye, kallon ta kawai Hilal yayi yana ayyana irin abunda zata ji idana kace mata ƴarta na ɗauke da cuta mai ƙaryar garƙuwar jiki.


“Momy karku taɓa ta, ko da ta farka ne”


“Toh amman mi ya same ta haka ne?”


“Ta samu Miscarriage ne”


“Subhanallahi Allah ya bata lafiya”


“Amin”


Ya koma ya jingina da bangon ɗakin yana kallonta, ɗaya daga cikin ƙanwarta ta warware carpet ɗin da suka zo da shi ta shinfiɗa a gurin. Ta miƙawa Hilal Kujera, sai kawai ya girgiza mata kai.


“No Thanks”


A gurin yayi ta tsayi har Hajiya ta iso, ita sai da ta kira shi, yaje ya taho da ita sai suka gaisa da Momy, ta duba ta tayi mata fatan sauƙi sannan ta fito. Tare suka jero da ɗanta sai gaisuwar girmamawa ake mata, dan kowa ya ganta ya ga Hilal yasan itace mahaifiyarsa.


“Yanzu haka baƙin kishi ne ta sawa kanta, gashi yanzu kun yi losing wannan baby”


Shi dai be ce komai ba, ya buɗe mata Mota. sai da ta shiga, ta zauna sannan yayi mata sai da safe direba ya wuce da ita, shi kuma ya juyo ya dawo cikin asibitin.
Lokacin daya dawo, sai ya zauna saman gadon kusa da ita, babu abunda yake kallon sai fuskarta, rayuwarta da tasa yake ta tunani, irin yadda suka so junansu har suka haifi ƴaƴansu, yanzu kuma lokaci ɗaya komai yana shirin sauya musu, he just can't believe ace Rashida ta ci amanarsa da wani, haƙiƙa yana da tambayoyin da suke buƙatar amsa daga gareta.


“Ai da ka tashi kaje gida, tun da ga mu muma ai mun isa mu kula da ita”


Can ciki ya ji muryar Momy tana masa magana. Sai ya tashi cikin rashin ƙwarin jiki yayi musu sai da safe ya fice.



NAMRA POV.


Daga asibitin sai ta wuce bank, layi ta bi sai da ka kai gareta sannan tayi checking balance ɗinta, dubu ɗari huɗu ta hansin ta gani, a tunaninta ko Anty Amarya ta ƙaro mata wasu ne, sai kawai ta cire kuɗin gaba ɗaya, cikin farinciki da jindaɗi.


Kamin ta isa gida sai ta ta fara biyawa ta gidan dillaliya, ta ƙirga kuɗinta ta bata, sannan tasa a kira mutumen da yayi musu wacan rubutun yayi masu sheida saboda wata rana.
Sauran kuɗin daya rage mata sai taje kasuwa ta siye kuloli, da ƴan wasu kayan aiki da basu kai sun kawo ba, data dawo gida sai ta wanke kuloli ta siye abincin ta nufi asibitin da shi.


Ta jidaɗin ganin Asim a tsaye yana ɗan takawa, Mama na tiƙe da shi, suna zuwa ƙarshen ɗakin suna dawowa, wani farinciki ne ya mamayeta, bata san lokacin data aje kulolin ba ta tsaya tana kallonsu.
Hamdala take yi ma Allah cikin ranta, tana jindaɗin yadda taga mijin nata yau ya fara taka ƙasa, Mama ma farinciki take sosai daman ta fi kowa son haka dan zaman asibitin ya isheta.


Sun kusa minti latalin suna, suna zagaye ɗakin sannan Mama ta zaunar da shi saman gado.


“Allah ya bi da lafiya ya ƙara sauki”


Ita da Asim suka haɗa baki gurin amsawa da Ameen. Sannan ta zuwa ya fice.
Namra ta kalli Asim da far'ah a fuskarta.


“Da nice nace za kayi wannan yawo zaka ce min ba aka iya ba”


Ɗan murmushi yayi, shi kansa yana cikin jindaɗi a yau.


“Alhamdullillah, ban zaci zan iya ba”


“Ai babu abunda za a iya matuƙar aba'a gwada ba, Allah ya nuna min ka tashi ka koma kamar yadda kake”


“Ameen”


Ta kwantar da kanta saman jikinsa. Shi kuma yayi shiru yana nazarin rayuwarsa, irin mutanen da sukajuya masa baya yake lissafi a zuciyarsa, ace har abokansa da yake ganin sun kai amman kowa ya kasa takowa ya zo ganinsa


“Hmmm”


Ya furta a fili, yana sauke ajiyar zuciya. Sai Namra ta kalleshi


“lafiya?”


“Lafiya ƙalau, kawai ina tunanin tafiyarki ne, Mama tace karki je yanzu, idan ma wani abun ne ai aiko miki kawai, kuma ki faɗa wata komai ta waya kawai, tama kira ba ki nan”


Shuru Namra tayi bata ce komai ba, sai dai maganar tasa bata mata daɗi ba. Hannu ya kai ya shafa ta.


“Namra have you ever noticed that Anty bata taɓa kira kai tsaye da sunan jin jikina ba? Haba Namra ai ko wani na kashe musu sa ɗaga min ƙafaa balle auren ƴar su na ke, abun nan ya ɓata ran Mama sosai, nima shiyasa a duk lokacin dana ga ɓacin rai a fuskarta sai nawa rai ya ɓace, daman irin wannan ake gudu aje ayi aure a kasa samun kwanciyar hankali”


Shiru tayi tana taɓin hannunta, ita kanta tasan iyayenta basu kyauta ba, akan abunda aka yi mata kuma Asim yana da gaskiya kan abunda yake faɗa, tasan Abbah kam ba zai zo ganinsa ba, amman ya kamata ace ko Maryam ce ta zo ganinta, ganin yadda suke da ita jini ɗaya, amman ko waya bata taɓa bugo mata ba.
Anya ta cancanci su juya mata baya har haka?
Ba su da wani excuse akan haka, sai dai a yanzu bata son ta zurfafa amincinta ga Asim tun bayar maganar su da taji da Mama.


Kamar ya san abunda yake ransa, sai kawai ya rumgume ta.


“Ina son ki, kuma bana tunanin akwai abunda zai raba ni da ke, ina son na ɗanɗana miki rayuwar da baki taɓa mfarkin shigarta ba, irin rayuwar jindaɗin da tafi ta gidan ku, sai dai ina gudun ranar da zaki rabu da ni saboda wani baƙin talauci ko mugu abu ya same ni”


“Ba zan taɓa rabuwa da kai ba Asim na maka alƙawari, ko a wane hali na samu kai na, zan zama mai biyayyah a gare ka, zan maka sadaukarwar da ba kowa ce mace ce zata iya ba, son nuna maka son da ba kafai ake samun irinsa ba.
Sai dai ni zuciyarta ta kasa Aminta da kai, kana ɓoye min wani abu naka Asim”


Gabansa ya faɗi, yana Allah-Allah idan ba wani zancen nasu ta ji ba.


“Me zan ɓoye miki? Miyasa zuciyarki ta manta da waye Asim a duniyarta, taya Asim zai cuce ki, Asim be aure dan tsinkayar wani abu na gidan ku ba, shiyasa tun farko ban so na aure ki saboda na san zaki yi tunanin saboda haka na aure ki”


Jikinta ya mutu, hawayen da taga yana zuba a idon Asim ya tsayar da nata hawayen, a take ta manta da zargin da take masa, wani irin son sa da ƙaunarsa suka mamaye mata zuciya.








MORNING UPDATED
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

_Write by_
*Khadeeja Candy*


*PAGE - 39*


NOT EDITED ⚠


Ko da ya isa gida, Kalsoom na zaune a balcony tana zaman jiransa, hankalinta ya tashi sosai, ji take kamar itace a halin da Rashida take ciki.
Tana ganin yayi parking, ta tashi da sauri ta ƙarasa inda yake ta buɗe masa motar.


»“Ya jikinta? Da sauƙi?”


Ido ya sakar mata kamar yau ya fara ganinta, be ce mata komai ba kuma be kashe motar ba, balle ma ya fito. Ita kuma duk ta tsorata, gabanta sai faɗuwa yake kar ta ji mummunan labari.


“Dan Allah ka min magana mana”


Ta masa maganar irin tana daf da yin kuka. Sai a sannan ya kashe motar ya fito, ya ɗora kansa saman na ta, ya kai hannu ya riƙe hannunta yana sauke ajiyar zuciya.


“Da sauƙi ta samu bachi”


“Amman ka kira gida ka faɗa musu?”


“Na faɗa”


“Sun zo?”


“Sun zo”


“Allah ya bata lafiya, amman dai be zube duka ba ko?”


“Ya zube”


“Ayyah Sorry”


“Sorry too”


Duk maganar da take masa yana amsa mata, kansa na saman nata ne, sai a sannan ya riƙa hannunta, ya matsar da ita daga jikin motar ya rufe motar, ya jata zuwa ciki.


A falo ya zauna, sai ta zauna kusa da shi, tana ɗan shafa bayansa, a tunaninta zubarwa cikin ne be masa daɗi ba.


“Doc kayi haƙuri Allah zai sake baka wani”


Ya kalleta.


“Haka ne, Kalsoom do me a favor”


“Na me?”


“Ki min alƙawarin zaki kula da yarana zaki basu kyakkyawar tarbiya, and komai suka yi ba zaki gundura da su ba”


“Baka da buƙatar na maka alƙawari, amman miyasa kayi min wannan maganar na?”


“Zan raba muku gida ne, da Rashida zan wareta daban, ke zaki zauna a nan tare da yara”


“Miyasa?”


“Ita ta buƙaci haka”


“Kuma ta yardar ta bar min yaran?”


“Eh amman ba na son ki faɗa musu hakan, ni zan yi magana da su, ko da sun dawo karki faɗa musu Mamansu ta kwanta asibiti”


“Okay”


Ta faɗa a sanyaye, ita dai ta san ba lafiya ba, yanayinsa da kuma hukuncin daya yanke ya tabbatar mata haka.


“Bari na haɗa maka tea”


Ta tashi ta nufi kitchen, zuciyarta da tunani kala-kala, ko dai Rashida ce take da hiv! Shiyasa yake ta mata tambaboyi a baya? Kuma yanzu zai raba ta da ƴaƴanta, ai ba zai raba ta da su haka kawai ba, kuma yadda take ganin damuwar nan ta masa yawa ta san ba'a raba ɗayan biyu ba.
Har ta haɗa masa tea ta kawo masa tunanin take.


Fuskarsa ta tsurawa ido sosai, lokacin da zata miƙa masa tea, tana son gano gaskiyar zarginta, idonsa sun rine irin na ɓacin rai ɗin nan da damuwa idan sun yi ma mutum yawa.


Har zata ce masa wani abu, sai kuma wata zuciyar ta hana ta, sai kawai ta zuba masa ido har gama shan tea ɗin ya tashi ya nufi ɗakinsa.
Ita kam sai da ta gama abunda take sannan taje tayi wanka ta saka kayan bachi ta nufi ɗakin nasa, daman yau girkinta ne, ganin be shigo ɗakinta ba, ba zai hana ita ta kai kanta ba.


Washe gari har Kalsoom ta haɗa musu breakfast, idonsa biyu amman ya kasa tashi, jikinsa ya ɗibge kamar marar lafiya.

“Doc breakfast is ready”


Ta faɗa tana tsaye daga bakin ƙofa. Da ker ya ɗago kai ya kalleta.


“Je kiyi yau bana jin yunwa”


Ya unƙura ya tashi, ya nufi banɗaki. Ita kuma ta juya cikin rashin jindaɗi, ta fice. Wanka yayi ya fito, ya shiryar cikin ƙananan tufafi, ya feshe jikinsa da turare sannan ya fito falo cikin wani yanayi marar misaltuwa.


Ummu Faisak ya gani a falon zaune tana gaisawa da Kalsoom, tana ganinsa ta fara masa wani kallo ƙasa-ƙasa, sannan ta gaishe shi.


“Lafiya ƙalau ya ma su jiki?”


“Da sauƙi, ita ma tace na zo na ɗauko mata wayarta”


“Ta farka kenan?”


Kalsoom ta tambaya.


“Eh ta farka”


Kalsoom ta kalli Hilal


“Bari na tashi na shirya sai mu wuce tare na ganta”


“Ba yanzu ba”


Ya faɗa fuska ba yabo fallasa. Ba jira abunda zata sake cewa ba ya fice.
Kalsoom sai duk ya ji babu daɗi, Ummu Faisak ta buishi da kallon tana ayyana irin mallakar da Kalsoom tayi masa, har yake ƙoƙarin mantawa da Rashida a nan take, da ada ne aka ce bata da lafiya da duk ya bi ya haukaci amman yanzu dubu yadda rana ta fito be je ba, sannan ya hana Amaryarsa taje.
Wani dogon numfashi taja ta sauke irin an gulma ta tashi ta nufi ɗakin Kalsoom.




A hanyarsa ta zuwa Asibiti, Hajiya ta kira shi ta tambayi jikin Rashida, ya amsa mat d taji sauƙi, sai kuma g kiran Alhaji Bashir ya shigo, sai da Hilal yayi parƙing sannan ya ɗauki kiran suka gaisa sannan ya tambaye jikin Rashida.


“Ya Madam da jiki?”


“Jiki Alhamdillah, jiy ne ta samu miscarriage”


“Ayyah Allah ya bat lafiya”


“Amin Amin na gode”


“Dan Allah idan ka shiga, ka bani ita mu gaisa, Asma'u zata zo anjima Inshallah”


Ya kashe, sannan ya buɗe motar ya fita, duk inda y bi gaishe shi ake har ya isa ɗakin.
Wasu ƴan'uwanta ya tarar suna mata sannu ciki har da wasu Nurses da suke aiki gurin. Sai da ya fara gaida Momy sannan ya amsa gaisuwar da ƴan'uwan nata suke masa, ya nemi guri ya tsaya ya kafe Rashida d ido.


Momy ce ta fara fita sannan suma duk suka fita, ka barsa cikin ɗakin shi kaɗai sai ita, jin tayi kamar tace kar su fita, dan bata da idon kallon Hilal balle bakin yi masa magana.
Shi kuma ya tsare ta da ido kamar mai auna hawa da saukar numfashinta.


“Yanzu ba ki ji kunyar kan ki ba Rashida? Kina da aure ki bi wani namiji a waje? Wannan wane irin ƙazanta ne? Miyasa kika ɗauki zina ba komai ba? Idan kika mutu a yau mi zaki cew Ubangijinki? Me na rage ki da shi? Wanda kika bi miya fi ni da shi?
Ko kum kawai sheiɗan ne ya ƙawata miki yin haka? Kin manta ke uwar yara uku ce? Miyasa Zina ta burge ki Rashida? Ashe son da kika nuna min duk na ƙarya ne tun da har zaki iya ba wani halalina, kin lokacin da kike hana min kan ki a baya? A haka nake haƙuri ina bin ki har Allah yasa na haɗu da Kalsoom na aure, amman ko d mafarki ban taɓa tunanin aikata zina ba.


Tsakanin jiya zuwa shekaran jiya tausayinki nake, ina tunanin halin da zaki shiga idan babu a rayuwarki, amman yanzu nayi tunani baki buƙata na, sam ni da ke ba mu dace ba, nayi baƙinciki nayi nadamar da kika zama uwar ƴaƴana, faɗa min wanene wannan mutumen?”


Tun da yake maganar, bata balle shi balle tace wani abu, hawaye kawai take, irin hawayen nan da wani ke bin wani. Ya matsa kusa da ita ya ciro takardar take aljihunsa ya aje mata.


“Aure na da ni da ke yau ya ƙare, na sauwaƙe miki kije ki auri wanda kike ganin ya fi ni, ki dauwama ke da shi a duniyar da kuke son kasancewa”


Ɗagowa ta yi tmda sauri ta kalleshi, irin kallon nan da bata san tana masa ba, yau ta rasa gane duniyar da take, sama take ƙasa take, mafarki take ko gaskiya ne? Da gaske Hilal ne ko waninsa? Taya zata rayu ba da Hilal ba? Gidan ta da ƴaƴanta a yau sun zama mallakin kalsoom ba ita ba.


A saman gadon ta matsa can nesa ya rumgune kanta tana zubar ido kamar mai ganin aljanu. Ko kaɗan tausayinta a yanzu kam be ziyarci zuciyarsa ba, dan yasan ta cancanci fiye da haka, sai kawai ya juya ya fice daga ɗakin, cikin wani irin zafin rai da baƙinciki.






NAMRA POV.


Bata jin ko ta faɗama Anty Amarya sun yi wata, zat yarda dan ganin take kamar cewa zatayi shi ma haɗi ne, kuma bata iya tambayarta wani kuɗin, sai kawai ta kira ta da wayar Asim tace mata be bari ba yace ta bari har yaji sauƙi sai su zo tare, Anty Amarya bata jidaɗin hakan ba, sai dai babu yadda ta iya tun da mijinta ne.


Da dare Namra kasa, bachi tayi har sai da taje wani BQ dake maƙota ka d nasu ta nemi ƴar fulanin data zo ta taya ta kwana. Duk da haka har safe ba yi bachin kirki ba dan hankalinta be kwanta da gurin ba.
Da safe sai ta aika yarinyar ta siya musu ice su ɗora girki, a abun da bata taɓa ba a rayuwarta yau gashi zata yi. Kamin yarinyar ta dawo, sai taje waje ta ɗauko duwatsu ta haɗa murhu, kamin yarinyar ta dawo sai ta zauna saman bolcony tana kallon gidan.


Tunani take na ranakun baya, lokacin da Anty Amarya take saka ta girki da gas ko electric amman ta ƙi yi ta riƙa faɗin wahala, yau gashi zayi da abund bata ma taɓa gwada kunna wutar da shi ba, yau ga ta a ɗakin da babu katifa balle gado, duk wani abu mai muhimmanci a rayuwart i zuwa yanzu ta rasa shi.
Hawaye ne suka silalo mata sai tayi saurin gogewa, ganin ƴar fulanin ta doso inda take ɗauke d icen.


Sai kusan 12 ta gama girkin abun ka d wacce bata saba ba, sai ta zuba ma yarinyar ta zuba ma su Mama na su sannan ta zuba sauran a kula, sai ta janyo ruwa a rijiya, ta shiga banɗakin BQ ɗin tayi wanka, sannan ta fito ta shirya cikin atamfar jiya ta saka Hijabi ta ɗauki kular ta fito, yau kam a bakin gate ma ta samu Napep, tayi sa'ah an sauke wata ne, sai kawai ta shiga ya ɗauki hanyar asibiti da ita.
Suna kaiwa Babban titi, aka riƙa musu hannu akan su tsaya, amman ta hana mai Napep ɗin tsayawa, har sai da suka isa bakin asibitin. ta fito tana miƙawa mai Napep ɗin kuɗinsa, ta tsaya jiran ya bata canji, sai ta motar ta faka kusa da ita. Abdool ya fito ya nufo ta jiki na rawa. Kamin ya ƙaraso har Mai Napep ɗin ya bata canjinta ta kunna kai cikin asibiti, shi kuma sai sauri yake ya ci gabanta.


Mama na gurin zamanta ta sinƙayo yadda Abdool ya biyo Namra har cikin ward yana ƙoƙarin cin gabanta, sai ta tashi tsaye, ta matsa can baya tana leƙen su, ta tattara hankalinta gaba ɗaya ta mayar gurin.


*🌺🌺🌺 ZAGON ƘASA 🌺🌺🌺*

_Written by_
*Khadeeja Candy*


*PAGE - 40*


NOT EDITED ⚠


“Haba baiwar Allah, Wannan wane irin jan'aji ne? Dan Girman Allah ki tsaya ki saurare ni”


Abdool ya faɗa yana haɗe hannayensa, alamar yana roƙonta. Girman Allah daya haɗa ta dashi ne yasa ta tsaya har ta ɗaga kai ta kalle shi.


“Malam ni Matar aure ce”


“Matar aure mai igiya uku ko kuma matar aure kalar aure”


“Matar aure mai igiya uku, dan haka kar ka sake bina”


Wani irin faɗuwa gabansa yayi, a take gumi ya fara zubo masa, a take launin idanuwansa suka canja.


“Inshaallah ba zan sake ba, dan Allah ki yi haƙuri ban san kina da aure ba”


Sai a sannan ya janye ya bata hanya, ta raɓa gefensa ta wuce, shi kuma ya juya jiki a sanyaye ya nufi hanyar fita, kallonsa ake tayi a gurin saboda wasu sun san Namra tana da aure, wasu kuma suna masa kallon sani tun da akan nunasa a tv akan matsalar tsaro, kuma sun san ɗan sarki ne, tun da ga fuskar Mai-matarba nan a fuskarsa.
Sam be ji maganar da wani likita ke masa ba har sai da likitan ya cira ƙafa ya cin masa

Please Login or Register in order to submit comment