Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san waye Hilal ba shiyasa kike damuwar kan ki, yanzu haka za muje gida kina ciki damuwa da kuka? Kuka ba komai yake ƙara min sai karya min gwuiwa”


Be jira abunda zata ce ba, ya hau ttiti ya cigaba da tuƙa motar a hankali, har suka isa estate ɗin su. Gabanta ya faɗi sosai lokacin da ya danna horn a ƙofar gidansu.
An ɗan daɗe kamin a buɗe musu gate ɗin kasancewar a lokacin goma da ɗan gota, daman can a al'adar gidan da tara ta yi suke rufe gate.
Sai da mai gadin ya fara buɗe gate ɗin ya leƙo su ya ga su ne sannan ya koma ciki ya buɗe musu gate ɗin. Nesa da motocin gidan ya faka motarsa sannan ya jingina kansa jikin sitarin motar yana karanto irin bayanin da zai ma Daddy har ya fahimta.


“Ni ce zan faɗa musu komai?”


Dagowa ya yi ba tare da ya juyo ba ya ce


“Ta wace fuska?”


“Ta fuskar da za su fahimta, ka jira ni a nan”


Gefen hijabinta ta saka ta ƙara goge fuskarta sannan ta buɗe motar ta fita. Ita kanta tana fargaba yadda zata faɗa musu tun da ba magana ba ce mai daɗi, sai dai basa buƙatar a ɓoye musu komai. Ta daɗe tsaye jikin ƙofar falon tana tunani kamin ta tura ƙofar ta shiga.


Sallama tayi can ƙasan maƙoshinta, muryarta a dakishe alamar kuka ya kamata, babu kowa falon kuma kayan kallo a kashe, hakan ya tabbatar mata da sun shiga bachi ko kuma ƙannenta suna can suna karatu. Sai kawai ta juya ta fita daga falon ta nufi falon Dady.
Tun daga bakin ƙofar falon ta jiyo muryar tv, da alama yana kallon labarai ne.


“Assalamu alaikum”


Ta faɗa a daƙishe, haɗa baki suka yi gurin amsa mata. Duk da mamaki suka kalleta Momy ta aje plate ɗin abincin dake hannunta.


“Kalsoom shigo mana kika tsaya jikin ƙofa kamar baƙuwa”


Shigowa ta yi tana kuka, ta zauna kasa tana duƙunƙune fuskarka. Kallon natsuwa Dady yayi mata kana yayi gyaran murya ya ce


“Idan kin jin wani abu ne ya shiiga tsakanin ki da mijinki kuma ke ce mai laifi kar ma ki soma ba mu labari”


Cikin muryar kuka ta ɗago kai ta kalle shi


“Ba ni ce mai laifi ba, kuma Hilal ba shi da laifi, mahaifiyarsa ce ta saka ya sake ni”


Momi ta dafa ƙirjinta.


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Dady kuma ya rumtse ido yana sauraren yadda maganar ta daki dodon kunnensa.


“Me kika mata?”


Momi ta sake tambaya.


“Wallahi ban mata komai ba, saboda mutuwar Rafiq ne”


A nan ta kwashe labarin duk abunda ya faru ta faɗa musu, sai da ta kai aya, sannan Dady ya kalleta ya ce


“Je ki shigo da shi”


Ba musu ta tashi tana kuka kamar ta shure ta fita. Hilal na tsaye jikin mota ta fito, yadda ya hango ta zuciyarsa ta nasalta masa bata faɗa musu gaskiyar abunda ya faru ba.


“Dady ya ce ka shigo”


Ta faɗa tun kamin ta ƙaraso kusa da shi, sai kawai ta juya, shi kuma ya rufa mata baya, zuciyarsa cike da zullumi.
Jimmm yayi lokacin da ya isa bakin ƙofar falon, sannan ya shiga da sallama yana mai sadda kansa ƙasa. Can jikin ƙofa ya zauna dan baya jin sakewar da zai ƙarasa kusa da su ya zauna.


“Kalsoom ta faɗa mana komai, kuma ba mu ga laifin ka ba, ko nine kwatankwacin abunda zan aikata kenan”


Cewar Dady. Hilal ya ɗan ɗago kaɗan ya ce


“Fushin Hajiya na ɗan wani lokaci ne, nan gaba kaɗan zata sake, shiyasa na ce za tayi zaman idda acen kamin Hajiya ta yarda na mai da ta”


Dady ya gyara zamansa, yana yi ma Hilal kallon hankali da kamala.


“Hilal ina son ka kasance mai haƙuri a duk halin rayuwar da ka tsinci kan ka. Kalsoom zata koma gidan ka amman ba yanzu ba, zata zauna a nan har sai lokacin da Hajiya ta ce ka zo ka tafi da ita, kuma ina mai baka shawara ka nemi matar da mahaifiyarka dake jin hankalinta ya kwanta da ita ka aura”


Da sauri Hilal ya kalli Dady


“Amman Dady bata hana....”


Dady ya ɗaga masa hannu.


“Ni a ɗana na ɗauke ka, kuma ba zan baka shawarar da zata cutar da kai ta cutar ƴata ba. Ka ɗauki shawarata kawai”


Maida kansa ya yi ƙasa.


“Amman Dady ita Kalsoom ta yarda?”


Dady ya kalli Kalsoom da ke kusa da Momi tana aikin kuka ya ce


“Zata yarda, ai tasan mahaifinta ba zai mata abunda zai cutar da ita, ka tashi ka je kar dare ya yi maka, ke kuma ki wuce ɗakin ƴar'uwarki”


Ita ce ta riga tashi ta nufi hanyar da zata sadata da ɗakunan tana kuka. Hilal kuma ya miƙe tsaye jikinsa a sanyaye ya bar falon, zuciyarsa na raya masa Dady yayi fushi ne shiyasa har ya yanke wannan shawarar.
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *67*


Rasa ya yi inda zai sa kansa, gaba ɗaya ganin yake gabas da yamma sun haɗe masa, musamman ma daya dawo gida.
Sai tunani ya taru ya yi masa yawa, wanka daya saba yi kamin ya kwanta yau kam be yi ba, ko kayan jikinsa ma be damu ya canja ba haka ya hau gado ya kwanta, bachi ya ƙwauracewa idonsa gaba ɗaya, har safe be rumtsa ba, sai juyi yake kan gado.
Biyar da rabi na safe ya yi sallah asuba, bayan ya gama tasbihinsa ya ɗauko alƙu'ane ya buɗe ya fara karatu.


Ƴar ƙara wayarsa ta yi alamar saƙo ya shigo, sai dai be duba wayar ba, har sai ya gama karatun nasa yayi addu'ah sannan ya maida ƙur'ane mazauninsa ya aje. Kayan dake jikinsa ya cire ya ɗaura tawul ya shiga wanka, ya daɗe zaune a bathroom ɗin sai tunane yake kamin ya samu kuzarin watsa ruwa ya fito. Cikin rashin daɗin rai ya shirya, Farar shadda ya saka, be damu da duba kansa ba a madubi ba, ya saka agogon hannunsa tare da hulla, sannan ya ɗauki wayarsa yana duba ya nufi ƙofa,
Tunawa yayi da be saka turare ba hakan yasa shi ya dawo ya saka turaren sannan ya fice.


_Ka yi blocking ɗin number na, ka raba ni da ƴaƴana, Hilal ka ci amana ta, ina roƙon ka alfarma, dan Allah dan Manzon Allah ka bar ƴaƴa su dawo a gare ni su ne kawai gata na_


Yana karanta saƙon yasan daga inda ya fito duk da ba number ba ta bace. Wani godon tsaki yaja.


“Duk halin dana shiga ke ce sanadi Rashida”


Sai da ya yi deleted ɗin saƙon sannan ya buɗe motarsa ya shiga. Ya ɗauki hanyar da zata kai shi gidan Hajiyarsa.
Be iso mutane sosai a gidan ba, kasancesar Safiya ne, kuma mutum na ƙaramin yaro ɓe ba babba ba, ita kanta a lokacin da ya shiga cikin gidan tana can cikin ɗakinta tana shiryawa.
Guri ya samu a falonta ya zauna, yana kallon tv duk da hankalinsa baya gurin, ɗai da ɗai ƙannensa da mutanen gidan suka riƙa shigowa suna gaishe shi da yi masa ya haƙuri, shi kuma yana amsa musu kamar an cilasta masa.
Sai takwas saura Hajiyaraa ta fito daga ɗakinta. Ta yi mamakin ganinsa a falon kamar wani baƙo mutumen da ya saba shiga har ɗakinta idan ya shigo cikin gidan.
Ƙarara Hajiya ta ga damuwa da rashin bachi a idon ɗanta, ba ta yi mamaki ba, daman can ta tsammaci haka, sai dai ita aabunda yake duba mas ba shi yake hangowa ba.


“Hajiya ina kwana”


Ya gaishe ta ba tare da ya ɗaga ido ya kalleta ba.


“Lafiya ƙalau ya haƙurin mu?”


“Alhamdullah”


“Ka yi haƙuri Hilal haka rayuwa take zuwa wani lokacin, kai taka ƙaddarar ta rashin mata na gari ne, ta ɗayan ba daɗi wannan ma ba halin ƙwarai, amman inshallah zaka ji daɗi, zan nema maka mata mai hankali da ladabi, mun yi magana da mahaifin ka ma, da ba dan wannan gaisuwar ba da kaje ka ganta, dan bana son auren ku ya wuce wata biyu ko uku ba, yarinyar ƴar gidan mutunci ce”


“Duk yadda kika ce Hajiya haka za'ayi amman ina roƙon alfarmar zan je aiki idan da dama a yi addu'ah yau, tun da yaro ne kuma daman can sunna bata koyar da mu wannan zaman kwana ukun da ake ba....”


“Eh Mahaifinka ma yayi wannan maganar amman naga tun da kwana uku ne, kuma kaga yanzu kwana ɗaya ya rage ai ƙara ka yi haƙuri kawai,amman kai zaka iya juwa aikin ai”


Kamin yayi magana sai ga Ezzah da Ulfah sun fito cikin shirin makaranta, da gudu suka zo suka rumgume shi.


“Dady i miss you”


Ulfah ta faɗa. Ita Ezzah sai tasa kuka.


“Dady shikenan Rafiq ba zai dawo ba?”


Kansu ya shafa cike da ƙaunar ƴaƴan nasa, da kewarsu kamar ba jiya ya rabu da su ba.


“Kin taɓa ganin wanda ya rasu ya dawo? Sai dai ki yi masa addu'ah”


“Ni kam i hate Anty Kalsoom ita ta kashe mana Rafiq”


Ya buge mata baki kaɗan.


“Kar na sake ji, akwai mai kashe wani bayan Allah ne? Kar bakinki ya sake irin wannan furucin”


“Dady wallahi ita ce ta kashe shi”


Ulfah ma ta faɗa, ta fuskanta kamar za ta yi kuka.


“Kuje driver na jiran ku zaku je school”


Hannu yasa aljihu ya ciro dari biyu ya mika musu, suka karɓa da far'ah suna godiya.
Da kallo Hajiya ta bi su har suka fice sannan ta ce


“Ni wallahi tausayi suke ba ni, shiyasa nake son ka auri yarinyar nan dan ga alama tana da natsuwa zata kula da su”


miƙewa ya yi tsaye yana dai-daita hular kansa.


“Zan leƙa office, idan na gama abunda na ke zan dawo”


“Amman ka karya kuwa?”


“A a zan karya a can”


“Allah ya tsare amman da ka tsaya ka karya a nan dan na san a can ba komai za ka ci ba”


“Zan ci”


Daga haka yasa kai ya fice, ransa a jagule.








NAMRA POV.


A ɗakin ta wuni har yamma, tun tana kuka mai hawayen har hawayen suka daina zuba, sai dai tayi kukan kawai babu hawaye.
Gaba ɗaya yanzu hankalinta ya tattara ya koma gida, tana kewar ƴan'uwanta sosai, duk da tadan itace bata kyauta musu ba, sai dai tana jin son mahaifiyarta a ranta tana kewarta.


“Bana jin ina daga cikin masu daɗewa a duniya, ina ji kamar mutuwa ta tana kusa da ni, ina da bukatar ki Mama, Abbah ka yafe min na tuba”


Magana take da kanta kamar wata taɓɓabiya. Miƙewa ta yi tsaye ciki da ƙargin hali dan bata jin karfi sosai a jikinta, fitowa ta yi waje, tana sun sun da kai kamar mai jin kunyar kallon inda su Neina suke.



“Ba wuta ai ƙara ki fito nan kam ki sha iska”


Neina ta faɗa tana gyara mata gurin da zata zauna. Ita kuma har ga Allah kunyar haɗa ido takw da Lamido balle kuma ta zauna inuwa ɗaya da shi.


“Zo ki zauna mana, jiri zai iya ɗaukar ki idan kina tsaye”


Ya faɗa ganin yadda ta tsaya a bakin kofar kamar ba zata zo ɗin ba, sosai gabansa yake faɗuwa, har murƴarsa na ƙoƙarin gargadar a maganar da yake mata saboda faɗuwan gabansa da ya tsananta.
Tana fara takawa gabansa ya fara fisgarsa yana wani zillo, da zaka tsaida idonka a lokacin da kyau a ƙirjinsa zaka ga yadda zuciyarsa take bugawa. Saurin ɗauke kansa ya yi daga kallo tafiyarta da yake kamin ta ƙaraso kusa da su.
Tana ƙaraso gurin sai kawai ta ɗauki filon da Neina ta aje mata, ta kalli Uwani ta ce.


“Dan Allah dan duba cikin jaka na akwai waya sai ki ɗauko min”


Ba musu Uwani ta tashi nufi ɗakin. Bata ɗauki tsawon lokaci ba ta fito da wayar a hannu ta miƙa wa Namra.


“Na gode”


Ta faɗa sai ta juya da zimmar komawa.


“Ai da kin zauna a nan”


“A.a daman wayar kawai nake son ɗauko wa”


“Zauna a ɗakin kawai, make yourself comfortable”


Kai kawai ya iya ɗaga masa, ta juya ta koma cikin ɗakin. Zaunawa ta yi tana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta kafe wayar da ido kamar mai shakkun kunnawa.
Can dai ta kunna wayar zuciyarta cike da fargaba, da tunani kala-kala. Gabanta ya soma faɗuwa lokacin da saƙwanni suka riƙa shigo mata bayan ta kunna wayar. Sai dai mafi yawanci su duka na Mtn ne, sai saƙo ɗaya mai ɗauke da number Yasmeen. Saƙon ta fara buɗewa, tana tunanin wane irin saƙo ne Yasmin ta aiko nata.


_Salam Namra na haihu na samu baby girl, na kira wayarki ban samu ba_


Murmushi ta yi tare da hawaye a lokaci ɗaya.


“Allah ya raya miki babyn ki, ya baki lafiyar shayarwa”


Shine furucin da tayi a fili, ta rumgume wayar ta lumshe ido.


‘Ya kamata na koma gida, ko me me zai faru ya faru a can, na yi kuskure tun farko da ban sauka gidan mu’


Tunanin da take a ranta kenan, kamin ta buɗe ido, ta fara kallon ɗakin.


“Gobe... Gobe ya kamata na je gida, an cire duk wani fargaba da yake rai na, zan cire tsoro zan gwada ƙarɓar sunana ko Alƙah zai za na dace, ba zaka taɓa winning ko losing ba matuƙar baka taɓa gwadawa ba, i hate to try”


A fili ta yi furucin zuciyarta cike da yaƙinin lallai zata iya, kuma ta shirya fuskantar ko wane irin hukunci na Abbah.


“Taya zai yafe min idan ban je ba? Taya zan shirya da Anty idan ban je ba? I have to do this, Allah ka taimake ni”


Komawa ta yi ta kwanta, zuciyarta cike da saƙe-saƙe kala-kala.




ABDOOL POV.


“Lafiya ƙalau aka ɗaura aure”


“Mashallah Allah ya nuna mana na ka, ya maka albarka”


“Amin Mai Martaba”


“Ka yi kyau sosai, ka fito kamar wani babban sarki”


Kallon Mamaki Abdool yayi kamar ance masa Mai Martaba yana tsaye gabansa.


“Waya faɗa maka?”


“Babu ruwanka, ai har hoton ka an turo min alkyabar ta karɓe ka sosai”


Dariya yayi cike da mamaki, dan shi dai be san ya ɗora hoton daya saka alkyaba ba a media balle yace ko wani ne ya tura masa.


“Mai martaba kasan ance informer hukunsu ɗaya da da mai fashi da makami ko”


“To ayi haƙuri Major ayi haƙuri muma muna kan aikin mu ne”


Ƙyalƙyalewa yayi da dariya daga shi har Mai Martaba, daga bisani Mai martaba ya ɗora da.


“Ƙarfe nawa zaka ta so?”


Shiru yayi kamar mai tunani, haka kawai ya samu kansa da rashin jindaɗin tafiyar.


“Zan turo maka dogarawan ka sai a bar min Sadauki, zamu kwana biyu kamin mu dawo”


“Why?”


“Just kawai ina son ganin kaduna ne, kasan rabo na sa kaduna since... I can't even remember”


Ya ɗan sosa kansa yana kallon titi da mutake ta kai kawo suna sha'aninsu.


“Fine as you wish, amman aikin ka fa”


“Mun samu hutu ai ko ka manta?”


“Haka ne, to ba matsala amman dai karka ɗauki lokaci i have surprise for you”


“Thank you super Dad”


Daga haka ya kashe wayar ya kalli Sadauki dake front seat ya ce.


“Mai Martaba ya ce sauran za su iya kama hanya yanzu kai kawai zaka tsaya sai jibi za mu koma”


“An gama Yarima, Allah ya ƙara maka lafiya”


Be amsa ba sai kawai ya maida hankalinsa kan titi. Can kuma ya kalli agogo hannunsa.


“Yaushe zamu isa Kaduna?”




“Allah ya taimaki Yarima, nan da minti goma sha biyar zamu isa”


Daga nan be sake cewa komai ba har suka isa masaukinsa. Su suka buɗe masa mota ya fito suka rufa masa baya suna masa kirari, iya ƙofar falon suka tsaya. Sai ya juyo ya kalli Sadauki ya ce.


“A ba ko wannensu 30k kai kuma ka shirya anjima zamu je mu duba marar lafiyar nan”


“An gama Yarima, takawarka lafiya ɗan sarki jikan sarki, an gama ɗan adalin Sarki”


Sai da ya shige sannan suka janyo ƙofar suka rufe masa. Alkyabar jikinsa ya fara cirewa sannan ya buɗe maɓallan rigarsa, ya kishingida saman kujera, ya lumshe ido.
Tun da ya shiga ciki be fito ba sai da aka yi kiran sallah magariba daman basu baro zariya ba sai da aka yi la'asar.
Tare da Sadauki suka yi sallah a masallacin da ke kusa da gidan, sannan suka nufo gida. A hanyar su ta dawowa ne Abdool yake masa jan kunne.


“Bana son abunda kake min, karka sake ɗauko min takalmi ka aje min, kuma daga yau kar na sake jin wani kirari nawa a bakin ka, ka kira ni da Abdool kawai ko Yarima amman ba sai ka min kirare ba”


“Allah ya taimake ka za a daina”


Ya faɗa cikin girmamawa.


“Zaka iya tuna inda muka je gidan mai Napep ɗin nan da muka kaɗe?”


“Allah ya taimake ka, zan gane”


“To za mu koma mu duba shi, akwai canji a hannunka ko? Zamu siya musu fruits”


“An gama Yarima”


“Zan shiga na canja sai muje”


“A canja da kyau ɗan Sarki, Allah yaja zamanin ka”


Kallo ɗaya Abdool yayi masa ya kauda ido yana girgiza kai.




******************


Bayan salla magariba Uwani ta shigo ɗakin ta kunna mata kendir, ta aje mata maltina da Madara da kuma tea mai kauri, tare da biredi.


“Kuma ɗawainiya da ni na gode sosai”


Mirmushi Uwani ta yi


“Ba komai ai yi ma kai ne. Ki ci dai ki samu karfin jiki”


“Ni kaina ina son na samu ƙarfin jikin ko zan samu damar komawa gurin iyayena”


“Tafiya za ki yi?”


“Gobe na ke so idan Allah ya yarje min”


“Amman ina laifin ko nan da sati idan kin ƙara jin sauƙi?”


“Wata ƙila idan suka ga na samu sauƙi su ƙi karɓa na, amman ganina a hakan zai sa su tausaya min”


“Amman dai da kin yi haƙuri har ki ji sauƙi”


“Ina son tafiyar ne”


“To bari na faɗawa Neina”


Ta juya cikin rashin jidaɗi dan yanzu sun ɗan fara sabawa da Namra, zancen tafiyarta be mata daɗi ba.


“Neina wai kin ji Namra zata tafi”


Abunda ta fito tana faɗa kenan, ganin Yarima yasa ta yi saurin sadda kanta ƙasa jikinta ya shiga rawa.


“Barka da dare”


“Barka...”


Ya amsa kaɗan-kaɗan yana tsaye kan Lamido, dan ya kasa zama tun da ya shigo gidan yanzu ma ya samu kansa da ƙyamar gidan. Farar shadda dake jikinsa sai ƙara haska shi take. Uwani ta yi mamakin ganin sa ba dogorai, sai dai haka be hana ta gane shi ba.


Unƙurawa Lamido yayi ya tashi zaune daga kwance da yake, dan zuwan Abdool be sashi ya ɗago ba duk da cika masa ido da yayi, da kuma kwarjinin da ya yi masa, yana jin rashin sakewa da Abdool wata ƙila saboda ba matsayin ɗaya ba, ko kuma dan kaɗewar da yayi masa ne ya hana shi ganin farinsa sai haushinsa yake ji. A ƙoƙarinsa na avoiding ɗin Yarima ya kalli Uwani da Neina ya ce.


“Wani abu aka mata ne?”


“A'a wallahi sai dai ko ta gaji da zama ne, ko tana son ta koma Katsina ne”

Cewar Neina. Sai Uwani ta amsa da


“A'a wai ta ce tana son ta koma gida ne, ko zasu tausaya mata su karɓe ta, kuma wai gobe zata je, kamar wace ake kora”


“Amman Namra bata da tunani, taya zata koma gurin iyayenta cikin wannan hali?”


“Wlh kuwa, ni ma na ce ta yi haƙuri dai har gaba...”


Tsawa Sadauki ya katsawa Uwani, wanda shi kansa Lamido sai da ya zabura balle kuma Neina da daman jikinta rawa yake, ganin ɗan sarki tsaye a gidansu.


“Ke ƴar talakawa ba a wata magana a gaban Ɗan Sarki, kama kan ki ki iya bakin ki...”


Sosai Uwani ta shiga natsuwarta tsabar tsoro ma har ji tayi kamar ta amayar da hanjin cikinta. Abdool kuma wa watsa ma Sadauki Harara, dan sosai yake jin daɗin maganar da suke, sarau zuciyarsa ta raya masa da Namra ake, duk da bashi da tabbacin hakan.


Tsawar da Sadauki yayi ma Uwani ne yasa Namra ta san da akwai baƙo a gidan dan ta ji muryar da ba ta ɗan gidan ba. Hakan yasa ta aje maltinar dake hannunta, ta gyara tsawyuwar Hijabin dake jikinta ta leƙo ƙofar ɗakin.

Bata gane ko waye ba, bata kuma ta mu da ta sani ɗin ba, sai kawai ta juya ta koma ɗakin. Shi kam Abdool sarai ya gane ta, dan ya daɗe da haddace fuskarta, duk da duhun magariba ya fara saukowa hakan be hana shi gane ta ba.
Ya daidaita tsayuwar hannayensa da ke cikin aljihu, ya juya ba tare daya ce da su komai ba, sai sadauki ne yake musu Allah ya ƙara lafiya, duk suka amsa da Ameen ban da Lamido.


Be yarda yayi ma Abdool kallon banza ba, ko wata yassar magana sai da ya juya baya ya fice.


“Wani zai nunawa isa, girman kan tsiya”


“Aa Lamido karka jawa kanka, dan Allah ka iya bakin ka”


Neina ta faɗa zuciyarta cike da tsoro. Wani wawan tsaki Lamido yaja ya wuyar da fuskarsa zuwa ɗakin da Namra take ciki.




**************


Tafiya yake guda guda yana tsotsar bakinsa kamar mai shan minti. Jinginawa yayi da motar da suka zo, yana kallon Sadauki yana tsaya gefensa cike da ladabi.


“A bincika min baƙuwar fuskar da take gidan nan, wacce ta zo daga Katsina i can't recall her name amman ai ka ji yarinyar da suke magana akai ko?”


“Za a bincika, Allah yaja zamanin ka, ya ƙara maka lafiya”


Wannan karon Abdool da kansa yayi driver zuwa suka ɗauki hanyar masaukinsa, sai tariyar maganar su Uwani yake, yana analyzing.




ASIM POV.


Ledodin dake hannunsa ya dire mata yana sauke gajiya tare da miƙa mata ragowar canji.


“Yayi Kyau Asim kana ƙoƙari sosai. Ya kamata ka hutu kam nima zan je gida na da yake can cikin gari dan yata zata zo, kuma bata san ina wannan sana'ar ba, dole acan nake sauka idan zata zo, dan haka zaka yi hutun kwana biyu sai kaje gurin matar ka ku yi murnar mota ka ɗauke ta kuje gari ku shana”


Ya ɗan yi murmushi tare da sosa kansa, shi kansa ya jidaɗin wannan hutun da zata ba shi dan zai bashi dama ya je gurin baƙuwarsa, kuma daman can yana son ɗaukar Mardiya su fita gari.


“Ai bana da mata Hajiya bana da mata yanzu, ina dai kam nema”


Ta masa kallon rashin fahimta.


“ Kamar ya ba nasan kana da mata ba ada?”


“Eh mun ɗan samu matsala ne, har mun rabu ai”


“Subhanalillahi, kai kam Asim me ya kai ka?mata mai haƙuri da juriya haka? Me ta maka”


“Wlh Hajiya ta cika kwaɗayi ne, ga complain akan aiki nan, shiyasa kawai naga rabuwar ta fi, yanzu dai wata na ke so idan Allah ya yarda”


Idan ran Hajiya Sadiya yayi dubu ya ɓace a yanzu dam bata jidaɗin maganar nan ta Asim ba


“Amman Wallahi sam ba ka yi tunani ba, taya zaka sakin matar da ta rufa maka Asiri har haka, ka gaggauta mayarda matar ka matuƙar tana son mu shirya da kai, ni bana son ana ciwa mace mutuci”


“Wallahi Hajiya bana jin daɗin zama da ita ne, duk ita ce silar halin rayuwar dana shiga, sam arziki na da nata be haɗu ba, daman can ban yi istiƙara ba na aure ta, yanzu muna rabuwa komai nawa ya dawo daidai, arziki sai shigowa yake”


“Na dai faɗa maka, rufin asirin ka ka maida auren ka a yanzu duk inda matar ka take ka yi gaggawar mayar da ita shine kwanciyar hankalin ka, kaje ka yi tunani, ni sam bana son ana wulaƙanta mace akan aure, to kacewa iyayenta me? Sam dam baka da tunani Asim, idan ma akan aikin ka ai da ka yi sahawara da ni dole za mu samu mafita yadda za'ayi”


Miƙewa ta yi tsaye cike da ɓacin rai ta nƴfi ɗakinta. Shi kam Asim da kallo ya bi ta yana mamakin yadda ta haƙiƙan akan Namra kamar wata ƴar'uwata, tunani yake yi da ace ya fada nata gaskiyar rabuwarsu da Namra akan ciki ne wata ƙila ma ranta ya fi haka ɓaci.


[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *68 NOT EDITED*




Ta ina zai fara neman ta? Taya ma zai je neman yarinyar da yake ganin rabuwa da ita kamar ya huta da ƙaya ne?


“Zata dawo, na san bata je gidan su ai da yanxu an kira ni, amman na san zata dawo gare ni dole, amman neman ta yanzu a gare ni ai aiki ne sabo, kuma zata jidaɗi sosai idan har na neme ta”


Abunda yake faɗa kenan yana tuƙa motarsa a hankali. Wayarsa ce ta yi ringing, da sauri ya ɗauka ganin mai kiran har da murmushi a fuskarsa.


“Hello Babe”


“Hey how are you?”


“Fine i'm just thinking of you”


“Kar ka damu ai

Please Login or Register in order to submit comment