Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amal take. Ita ma lallaɓata yayi har tayi shiru sannan ya fito ya koma part ɗinsa ya canja kaya ya nufi gurin Mai Martaba.


Ba shi ya dawo ba sai da dare ya raba, daman duk yaje gurin Mai Martaba ko da rana ne sai ya daɗe balle ya je late. A falo ya sami Ummi Amal na saman ƙafafunta tana bachi, murmushi yayi ya zauna kusa da su yana kallon Amal ɗin.


“Har kun shirya”


“Ta ya za'ayi uwa da ƴa, ita ta kawo kanta tace min ta daina”


“Hmmm Amal kenan wannan ɗabi'ace kawai ta ɗan adam, amman idan kin lura har ƴan'uwanta bata bari ba”


“Jiya ma haka suka yai ita da Haleema akan Amirar nan”


“Ai tana gama wannan makararar ƙasar waje zan kai ta tayi karatu a can a huta”


“Ta dai ƙara lalacewa”


Dariya yayi ya miƙe tsaye.


“Ummi good night”


“Aha night, Abdallah yaushe zaka koma?”


“Jibi, akwai aiki a gaban mu abuja”


“Ai kai Allah be raba ka da aiki ba, ni dai kamin ka koma ina son kaje gidan nan na Haleema ka duba mana shi, yadda gyaran zai kasance sai ka kira yaron nan Isma'il ka faɗa masa, dan kasan gidan marayune ƙara a gyara idan ma wasu ƴan hayar za a zuba sai”


“Okay zaje gobe inshallah dan gobe babu inda zan je, a ina ne gidan ya ke? Tun da akayi gobarar nan ma ban je na duba shi ba”


“Yana nan Nasarawa na can wajen gidan action kuɗi ƙasa, kasan irin abubuwan nan sai maza, ni mace wano abu sai dai na ɗaga ƙafa”


“Inshallah gobe zanje”


“Allah ya kai mu”


“Sai da safe”


Yana hamma ya fice daga part ɗin dan duk ya gaji sosai.




*HILAL POV*


Lokacin daya isa asibitin be wuce ɗakin da Rafiq yake ba sai da ya biya ya karɓo hoton da akayi ma Rafiq ɗazun. Sai dai ba iya ya buɗe hoton ba har ya koma office saboda fargaba, sai yanzu ya gane irin abunda majinya suke ji idan wani nasu aka ce yana da wani ciwon ko kuma za ayi masa aiki.


Zamansa kenan a office, sai ga Alhaji Bashir ya shigo cikin mayan tufafin na shadda, tun kamin Hilal yayi masa uwarnin zama ya zauna yana nuna alhininsa akan abinda ya faru.


“Ɗazu nake jin labari babu daɗi ban samu na shigo ba sai yanzu”


Ya faɗa yana miƙawa Hilal hannu su gaisa. Hilal ya maiyarda Hoton gefe ya aje yana sosa kansa yace


“Ƙaddarori ne”


“Wallahi shiyasa kaga bana son ƙara auren nan dan rigima ce kawai ko wacce da kalar matsalar da take zuwa da ita, yanzu miye abin na sawa yaro guba”


“Babu tabbacin ita tasa Bashir, amman dai ita kaɗai ce a gidan”


“To ai shi ya nuna ita ɗin ce, kuma kasan fa ita ta fitar da Rashida a gidan yanzu kuma tana son ganin bayan ƴaƴanta, gaskiya abun be yi daɗi ba, ai ota Rashida tace ba zata ƙyale ba, dan Asma'u ta ce har ta aika mata sammaci ko? Amman dai ban jidaɗi ba gaskiya”


Hilal ya jingina da kujerarsa yana lilo.


“Ni ne na saki Rashida da kaina san ganin damana, maganar kotu kuma taje duk inda zata je ta kai Kalsoom i will surely depend her”


Alh. Bashir ya masa kallon mamaki.


“Doc kasan abinda kake faɗa kuwa? Ɗan ka ne fa ɗan ka ta nemi kashewa”


“Kana da hujjar ita ɗin ce ta kashe shi? Amanarta na karɓo a gurin iyayenta yanzu haka tana ƙarƙashin kulawa ta ne, dole na yi abunda zan kare ta”


“Kana nufin za ka ci gaba da zama da ita kenan?”


“What do you expect?”


Ya ɗaga kafaɗunsa.


“Nothing, ya mai jiki”


“Da sauƙi bachi ya ke”


“Okay Allah ya ƙara lafiya, ni zam koma da safe zan zo na duba shi”


Hilal ya miƙa masa hannu suka sake gaisawa.


“Na gode sosai”


Wani kallon Alh Bashir yayi masa, yana mamakin yadda Hilal ya sauya masa kamar ba shi, duk irin tare da suke a can baya yana aure Kalsoom duk ya watsar ta ɗauke masa hankali. Lallai yanzu ya yarda da maganar da ake cewa magani tayi masa, tun da har Hilal ya furta zai tsaya mata, bayan kuma ɗansa ne tayi ma wannan karen aiki.


Bayan Alh Bashir ya wuce Hilal ya koma saman kujear ya zauna, yana tunanin maganar sammacin da Alh Bashir yace Rashida ta aika Kalsoom. Duk waɗancan maganganun yayi ne kawai dan ya nuna kamar ya san abinda yake faruwa bayan kuma besan komai, yayi hakan ne dan bayan son ayi Alh Bashir yai insulting ɗin matarsa. Saboda ya tsani haka.


Ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin yadda zai ɓullowa lamarin. Sai kuma ya kai hannu ya ɗauki hoton ya buɗe yana dubawa. Abinda ya gani ya tayar masa da hankali, da sauri ya tashi yana ƙara dubawa dan tantance abinda yake ganin ɗin. Da sauri ya bar Office ɗin ya nufi inda zai laƙa hotunan su fito a majigi...




*RASHIDA POV.*


Tana sauke wayar ta ƙara ɓata fuska, zuciyarta ta sosu matuƙa, akan abinda Alh. Bashir ya gama faɗa mata, na cewar Hilal zai tsaya ma Kalsoom, a tunaninta shi da kansa zai saka ta kotu yadda tasan yana jin da ƴaƴansa.


Hawaye suka zubo mata sai tasa hannu ta share. Hankalin ƴan'uwa sai duk ya dawo kanta, daman tun ɗazu maganar da suke kenan har da wata ƙawarta wacce suka yi makaranta a tare.


“Ke mai ya faru?”


Khady ta tambaya tana dafa ta.


“Wani abokinsa ne ya kira ni yanzu yana faɗa min wai Hilal yace zai tsayawa Kalsoom”


Ummu Faisak ta daki ƙirji.


“Da gaske? Lallai wannan Kalsoom ɗin ta wanke ta bashi ya sanyen, kan uban nan ayi ma ɗanka abu amman kasa yin komai har kace zaka tsaya mata”


Dukansu jinjina lamarin suke. Zainab ta kada baki tace


“Wannan abun har ƴan Human Rights sai mun saka, ai idan ya san wata be san wata ba, ƙaramin yaro zaka bari a wulaƙanta yama baki ɗan kawai tun da bayan son zuri'arki”


Ummu ta jinjina kai.


“Hmmm Ai wallahi sai na masa rashin mutucin, dan har a tv sai na nuna su, ai daga ganin wannan abin kinsan Hilal ba cikin hankalinsa yake ba. Kuma wallahi tallahi matuƙar ina numfashi sai Kalsoom.ta bar gidan nan, ba ko mallaka ne aikinta wallahi ko a gabanta bokanci ya yake saƙa sai na nuna mata shayi ruwa ne, ai ko baba da babansa”


Rashida tayi saurin rufe mata baki 5ana kuka.


“Dan Allah ki ƙyaleta, ni dai bana iya, ita ta sani can ita da Allah”


“Ai ban ci ki iya ba bada kuɗin ki zan yi ba, amman wallahi tun da ta taɓa ki sai na taɓa ta”


Wani yatsine yake tana tsine ɗankwali irin ita ga ga tantsiriya ɗin nan. Maimunatu ta girgiza kai


“Daman kin yi sake tun farko Rashida Namiji kamar Hilal kinsan duk wace ta shiga gidansa kan ba fita, ni da nice ke Wallahi da wannan abokin nasa zan aura, in yaso ya mutu....”


Ta murguɗa baki. Fashewa Rashida tayi tda kuka tana narke musu kamar wata ta ƙwarai, su kuma sai tausayinsa suke suna bata haƙuri....






INA JINDAƊIN COMMENTS NA KU. THANKS........🙏
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *56*




Idonsa ya cika da hawaye, jikinsa ya mutu sosai har yana ƙoƙarin zamewa ya faɗi kamar ba Namiji ba.
Hannunya kai ya taɓa hancinsa ya lumshe, tana girgiza kai. Abinda yake bashi mamakin results a yanzu ya nuna ba guba bace gas ya nuna kuma har yayi effecting ɗin ƙwaƙwalwar Rafiq, that's mean zai zama wani iri kenan. Wanda abu ne mai wahala ya koma dai-dai, ko da kuwa an ɗora shi akan ganine.


Ya daɗe idonsa a lumshe, _Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un_ Shine abinda yake ta maimatawa a zuciyarsa. Daker ya buɗe idon ya ƙarasa ya ciro hoton ya bar ɗakin yana mai jin kansa kamar marar lafiya.
Be shiga office ɗinsa ba sai kawai ya nufi ɗakin da Rafiq yake kansa na mugun sarawa. Tsaye yai a bakin ƙofa yana kallon Rafiq cike da tausayin Rafiq, ya daɗe jikin ƙofar kamar mai tsoron ƙarasawa. Juyawa yayi ya koma office ɗinsa, ya zauna kaman kujera ya dafe kansa still takardun na riƙe a hannunsa. Babu abunda ya faɗo masa a rai sai ya sake ɗaukar wani hoton ya gani, wata ƙila wannan ƙarya ya nuna masa...
Ɗaga kai yayi ya sake kallon hotunan, yana sauke ajiyar zuciya. Ya ɗauki mintuna talatin yana kallon hotunan sannan ya buɗe wani gurin ya saka su ya ɗauki abubuwan daya shigo dasu office ɗin ya fito, da kansa ya kulle office ɗin sannan ya nufi ɗakin da Rafiq yake. Har lokacin bachi yake abunsa, be farka ba.
Wani ɗan ƙaramin tebur Hilal ya nufa ya ɗora kayan a kai sannan ya ƙarasa gurin da Rafiq yake yaja kujera ya zauna, ya riƙe hannunsa yana hafawa, wani irin tausayin Rafiq ne ya ke shiga zuciyarsa.


Haka ya zauna ya tsare Rafiq da ido yana jin kamar yayi masa kuka, ko da kuskure bachi be doshi idonsa ba.lokaci lokaci yake sauke ajiyar zuciya kana ya haɗe yawu. Rafiq be farka ba sai kusan uku da rabi na dare. Murje-murje ya fara yana kiran ruwa kamin ya buɗe ido. Da sauri Hilal ya tashi ya buɗe jakar da ya shigo da ita ya haɗa masa tea ya ta sheshi zaune ya soma bashi tea ɗin, yana masa sannu kamar wani babba.


Yana gama shan tea ɗin ya langwaɓarda kansa jikin Hilal bakinsa yai gefe kamar zai talalarda yawu.


“Rafiq”


Hilal ya faɗa yana girgiza sa dan zuciyarsa ta katse gaba ɗaya. Ɗagowa Rafiq yayi kaɗan ya kalli Daddynsa sai ya maida kai gurin ƙofa yana kallo kamar mai jiran shigowar wani.
Can kuma ya ɗaga kai yana kallon ɗakin, kamin ya sake kallon Daddynsa.


Rumgumesa Hilal yayi yana hawaye. Daga bisani ya ɗauko wasu magunguna ya bashi, sannan ya maida shi a ƙirjinsa ya kwantar. Haka suka kwana, Rafiq na kwance a ƙirjinsa, Hilal kuma be rumtsa ba, a kan idonsa aka kira salla asuba. A hankali ya kwantar da Rafiq yai alwala a toilet ɗin ɗakin ya nufi masallacin asibitin.


Ya daɗe yana addu'a bayan yai salla, a nan masallacin ma sai da ya gaisa da wasu da suka sanshi har suna masa ya jikinsa ɗansa.
Sai da ya koma ɗakin ya ganshi sannan ya fito harabar Asibitin yana amsa wayar Hajiya dake tambayarsa ya jikinsa. Be faɗa mata a results ɗin da hoton ya bada ba, dan ba labari bane mai daɗin ji.
Ko da ya isa gida 6:30am, dan garin be ƙarasa wayewa ba a lokacin. A mota ya zauna har 30 ɗin ta ƙarasa sannan ya buɗe ya shigo nufi ƙofar shiga gidan. A kulle ya jita hakan yasa ya kai hannu ya ƙwanƙwasa, sai ya kawar da fuskarsa. Bayan kamar minti biyu zuwa uku Kalsoom ta buɗe ƙofar.


“Sannu da zuwa”


Ta faɗa cikin sanyayayyiyar murya. Be amsa ba be kuma kalleta ba sai kawai ya raɓa gefenta ta shiga cikin falon.
Kai tsaye ɗakin su Ulfah ya nufa, shiri ya tarar suna yi na makarantar boko.Dukansu ya shafa kansu yana masa good morning ɗin da suke masa, sannan yaja su jikinsa ya rumgume.


“Gobe za ku koma gurin Hajiya da zama, a can za ku zauna har na gama gyara wannan gidan”


Ezzah ta daka tsalle, tana murna, Ulfah ma Murna ta yi, dan suna son zuwan gidan Hajiya ko dan su yi wasa da ruwaz ga gidan akwai yara da yawa sa'aninsu.


“Daddy har da Anty?”


Ulfah ta tambaya cikin zumuɗi. Shiru Hilal yayi kamin ya amsa mata.


“A'a Anty a nan zata zauna”


Bata wani damu ba dan tana son gidan Hajiya, sai dai ta san zatayi missing Anty kan sosai, a ranta take auna a weekend zata zo ta ganta.Bayan kamar minti biyar ya miƙe tsaye ya nufi ɗakinsa. Yana tura ƙofar ɗakin yana Kalsoom zaune saman gadonsa tana hawaye.


Be kulata ba ya nufi wardrobe ya buɗe yana cire wasu tufafin. Da kallo ta bishi har ya gama cire kayan sannan ta soma magana cikin muryar tausayi.


“Baka buƙatar canjawa yaran ka gida Hilal, ni kake buƙatar canjaw! Ni kaina ban cancanci zama da ƴaƴan da mahaifinsu be yarda da ni ba, ko kaɗan ɓan ga laifin ka ba akan abinda ka aikata, ko ni kwatankwacin haka zan aikata”


Sauka tayi daga saman gadon ta durƙusa ƙasa ta haɗe hannayenta alamar roƙo.


“Ma gafarta min akan abunda na yi maka Hilal, ba zan sake hararar yaran ka ba balle na cutar da su”


Juyowa yai ya kalleta.


“Kin Aikata kenan?”


Kai ta ɗaga alamar eh.


“Na aikata kuma ina neman ka yafe min, dan dajarar iyayenka ka sake ni a yau, irin sakin da aure ba zai sake shiga tsakanin mu ba, irin sakin da ko na so na yi tunanin zuciya zata hanani, irin sakin da zan manta da wanzuwarka a doron ƙasa, irin sakin da zai sa na cire ka a zuciya.


Ina roƙon ka Hilal karka horar da ni da irin horon da zan cutu, karka saka zuciyata cikin ramen da ba zata iya fita ba”


Tun da take maganar hawaye take, irin hawayen nan dake hana sautin kuka fita. Miƙewa tayi tsaye ta ɗauko takarda da biro dake gefen gadon ta zo gabansa ta aje masa gabansa, ta miƙe tsaye ta bar ɗakin.
Notebook ɗin ya tsurawa ido yana nazarin kalamanta.


Wanka yai ya shirya cikin wasu tufafin ya feshe jikinsa da turare, sannan ya ƙaraso gurin gadon ya ɗauki takardar yayi mata rubutu, ya naɗe ya ɗauki kayansa ya fito.


Ɗakin Kalsoom ya shiga, sai ya same ta zaune ƙasan gado tana rusar kuka. Tsayawa yai cak yana sauraren kuka nata dake shiga har cikin zuciyarsa, be san dalili ba duk da abinda Kalsoom ta aikata masa still yana son a zuciyarsa, har yanzu natsuwarta da yadda take gudanar da al'amuranta burgeshi ya ke. Sai da ya ɗan yi gyaran murya sannan ya ƙarasa cikin ɗakin ya miƙa mata takardar.Idonsa na shiga cikin nata gabansa yayi mugun faɗuwa, ta rame sosai kamar ba ita ba, ga wani ja da idonta yai, kamar ta saka garwashi a ciki, a take tausayinta ya rufe shi. Ita kuma ta sakarwar takardar ido sai kallo take tana tsoron karɓa, ta haɗe yawu ya fi a ƙirga kamin ta miƙa hannunta dake ɓari ta karɓi takardar.


“Na gode Allah ya haɗa ka da mata ta gari..”


Cikin sarƙewar murya ta faɗa bayan ta karɓi takardar. Har ya buɗe baki yai magana, sai kuma ya fasa ya juya ya fice.


A jikim mota ya tarar da yaransa suna jiransa. Yana shiga suma suka shiga, har suka isa scul ɗin Ulfah bata daina tambayarsa ina Rafiq ba, sai dai be amsa mata ba dan be san me zai ce mata ba, Hilal irin mutanen nan da idan matsala ta shiga tsakaninsa da iyalansa baya son kowa ya ji, har yaransa, dan aganinsa ba muhallinsu ba ne.


Ƴan canji ya zaro a aljihunsa ya miƙa musu, sannan ya kama hanyar asibiti yana neman number Rashida daya saka a blacklist ya kira ta. Ta daɗe tana ringing kamin ta ɗauka, dan sai da ta tabbatar ta tantance cewar number Hilal ɗin ce sannan tai picking.


“Ki janye maganar kotu nan”


Shine abinda ya fara faɗa mata, a tunaninta zai bata haƙuri ne ko kuma yai mata wata maganar ta daban.


“Ba zan janye ba, ba za a dake ni a hana ni kuka ba, ba zaka cutar da ɗana kuma ni ka hanani ɗaukar mataki ba”


“Ɗan ki ko ɗa na? Bakin ki yana kurkure gurin faɗar kalmar nan”


“Ai da ɗan ka ne da baka ce za ka goyi bayan ta ba, wai har ka kace zaka tsaya mata bayan ita ce take ƙoƙarin aika ɗan ka lahira, dan kawai ta mallake ka”


Ya taka burki.


“Kar ki soma faɗa min maganar banza, ni ba wawa ba ne irin ki, kuma na faɗa miki ki janye zancen kotunan ko kuma na faɗawa duniya dalilin sakin ki da na yi kuma try me ki gani”


Be tsaya jiran abinda zata ce ba, ya kashe wayar. Sai ya kira wayar Alh Bashir sai da yai masa two missing calls sannan ya ɗaga, Hilal be tsaya jiran komai ya ce


“Idan kana son shiga cikin maneman Rashida ka shiga kawai ba sai ka riƙa ɗaukar maganar da muka yi ba ka kai mata, wannan ba girman ka ba ne”


Ya katse wayar ya jefar a front seat yana wani huci da bugu sitarin motar.






*RASHIDA POV*


Mamaki ya isheta, yadda Hilal ya juye ya zama maƙiyinta, mutumen da ko a mafarki aka ce zai mata zata musa, balle kuma a fili.


“Lallai na yi sake da har na bar ka ka auri wata ban mallake ka a lokacin ba, Kalsoom ki biya bokan ki haƙiƙa ya iya aiki. Zan janye maganar kotu, amman kuma dukan ku sai kun ƙwamace kiɗa da karatu...! Wallahi wasan yanzu aka fara, Hilal sai ka zo da kan ka ka nemi yafiya ta, Wallahi zan aikata ko minene matuƙar buƙatana zata biya... Sai na banbance muku aya da tsakkuwa”


Tashi tai tsaye ta cigaba da shirin zuwa office da take zuciyarta a dake irin na masara imani ɗin nan, dan a yanzu babu imani a kusa da inda take ma balle ace kusa da ita.


Sai da ta shirya tsaf sannan ta ɗauki jakarta da keys ɗin mota ta fito falo, already tai breakfast tun 6:30. Ɓangaren Mahaifinta ta nufa dan har Momy tana can. Cikin ladabi ta shiga ta samu guri ta xauna ta gashe su sannan ta ɗora da..


“Daddy zan janye maganar kotu nan, mu barta kawai da Allah”


“Wallahi kin yi tunani Rashida, nima abunda naga yafi kenan, indai cin amana ne baya taɓa ɗaurewa, Allah zai nuna mata sakamakonta tun duniya”


Momy ta faɗa cike da jindaɗin hukumcin da Rashida ta yanke. Dady yaja dogon tsaki.


“Ku kan Allah ya waddaran zuciyarku komai sai a ace a bari ga Allah? Ai musulucin ya ce idan an yi maka cuta ka rama gwargwadon abunda aka yi maka idan ba zaka iya yafewa ba, sannan irin wannan abun bw kamata ace a ba ga Allah ba, sai fa anje lahira kenan fa? Haba ai ƙara ayi mata tun duniya ta kunyata dan Wallahi idan yai wasa har shi sai nasa an kulle”


“A'a Alhaji ya kake magana kamar ba mai tunani ba? Haka sam be dace ba, hukuncin data yanke shine dai-dai”


Ya kawarda fuskarsa daga ta Momy ya kalli Rashida dan a tunaninsa ko Momy ce tayi mata wannan shawarar.


“Ke kina son abi miki kadin yaron ki?”


Ta girgiza kai.


“A'a Abbah na janye, na barta da Allah”


“Akan me?”


“Kawai haka naga ya fi”


“To ni zan bi kadin jika na (grandson) idan ku baku san abunda ake kira da humanity ba, ni na sani... Tashi kije office Allah ya kiyaye hanya”


Ba zata iya musawa Dady ba kar ya zargi wani abu, sai dai zuciyarta bata so haka ba, dan babu banbanci mahaifinta ne yasa ba ita ba. Tasan Hilal zai iya cewa wani sabon salo ne ta mayardar shari'ar gurin Mahaifinta.


A hanyar ta zuwa office ta kira Mom Shuraim, bayan sun gaisa take faɗa mata idan ta tashi daga aiki zata biyo ta gidanta, akwai magana mai muhimmanci da zata yi da ita.har da narke murya tana faɗin wai tana cikin matsala, amman dai sai tazo zata ji komai.






*ABDOOL POV*


Sai ten ya tashi bachi, dan yana yin sallah azuba ya koma bachin gajiya, farkawar da yayi ma a yanzu ba dan ya gaji da bachi bane, sai dan son zuwa gurin da Ummi tayi masa magana ne jiya. Be fito part ɗinsa ba sai da yayi wanka bugaggar shadda mai tsana blue color, ta fito da shi sosai kasancewar fari sol, ga ɓaƙar hulal da ya ɗora akansa kamar wani sabon balarabe,baƙaƙen takalmi ya saka sannan ya feshe jikinsa da turare, ya fito daga part ɗinsa ya nufo part ɗin Ummi shaddar har amsawa take a jikinsa, ga wani maiƙo da take kamar an zuba mata mai.


Ita kanta Ummi sai da tayi murmushi ganin yadda ɗan nata ya fito mashallah kamar ta cinye abunta.

“Ina fatar ka yi addu'ah”


“Addu'ah me?”


“Idan mutum yayi kwaliya ya dubu kansa a madubi yana kyau yace Mashallahu laƙuwwati illa billah, to ko wani yayi maka baki (kanbun baka) Ba zai kama ka ba, idan ma zaka ita ka riƙa karantawa da safe kullum sau uku”


Dariya yayi yana kallon cucumber da Ummi take yankewa ya ɗauki ɗaya ya ci.


“To ni da ba mace ba miye na wani kanbu zai kama ni, amman dai zan riƙa yi”


“It better”


Ya faɗa tana cigaba da yanka cucumber take. Shi kuma ya zauna kusa da ita yana tambayarta yaje yanzu ko sai anjima.


Ƙamshim turarensa ne ya isarwa da Amira saƙon isowarsa a falon. Ras! ras!! ras!!! Ga banta ya faɗi kamar yadda ya basa mata a duk lokacin da ta ji ƙamshin turarensa. Da sauri ta walƙato ta sauko daga saman gadon da take ta nufo falon idonta cike da maitar ganin Abdool kamar bata taɓa ganinsa ba.
Cikin wata irin siga take tafiya, takalmin dake ƙafarta plate ne amman hakan be hana su amsa amon gurin ba saboda yadda take buga da tiles ɗin gurin. Ummi ce kawai ta ɗago ta kalleta wanda kuma ita bata so haka ba. Abdool kam ƙin ɗagowa yayi dan sarai zuciyarsa ta raya masa Amira ce, dan yasan by this time duka ƙanensa suna makaranta.


“Ina kwana”


Ta gaishe shi cikin ladabi har tana son risina masa.


“Lafiya”


A kaikaice ya amsa, yana mai miƙewa tsaye. Wanda hakan be ma Ummi dadi ba,sai kawai ta kada baki ta ce.


“Amira shiga ciki ki ɗauko mayafin ki ki rana yayanki unguwa”


Ta fasa zaman da zata yi ta miƙe ta nufi ɗakin data fito. Sai da ta shige sannan Abdool.ya kalli Ummi yana ware hannayensa ya ce


“Haba Sweet Mom ya za ki min haka? Kin san fa ni Allah be haɗa jinina da mata ba, kuma it so annoying naje da ita unguwa”


Wani Kallo Ummi ta masa.


“Abdool... Karka soma halin Amal, tun da yarinyar nan ta zo kullum tana ciki gida bata fita ita ma ai ƙara ta ga gari ko?”


Be ƙara cewa komai ba ganin Amira ta fito, sai kawai ya jiya ya nufi kowa yana wani shan ƙamshi.
Ko da ta isa har ya tashi motar ita kawao yake jira su wuce. Tana shiga ya fisgi motar kamar baya son ransa har sai da Amira ta tsorata.
Bata ce masa ba, shi ma be ce mata ba haka suka yi ta tafiya har suka isa nasarawa. A bakin gate ɗin gidan yayi parking ya fito yana ƙarewa gidan kallom ganin yadda ya kone.
Yana rufe gambun motar Amira ta buɗe ta fito, sai ya kalleta ya ce


“Ba daɗewa zan yi ba, kina iya zama a cikin kamin na dawo”


Ba musu ta koma cikin motar ta zauna, zuciyarta cike da tunani kala-kala.


Baya tunanin akwai mutane a gidan dan Ummi bata faɗa masa ba, hakan yasa be yi sallama ba ya tura kofar gate ɗin kawai ya shiga ciki. Gaban gidan ya fara dubawa kamin ya zagaya baya, tana nan ya hango mace tana girki a BQ. Hannayensa yasa aljihu ya nufi bq ɗin yana sallamar da kusan shi kaɗai ne zai iya jinta, sai kuma wanda yaga bakinsa ya motsa.


Namra na ganin mutum tayi saurin komawa ciki ta ɗauko hijabinta ta saka sannan ta fito. Ko da ta fito har ya ƙaraso bq ɗin yana ƙare ma bq ɗin kallo dan ita bata yi komai ba.


“Haba Malam waye kai zaka shigo babu sallama”


Dago da dubansa yayi gurin mai maganar. Ganin Namra yasa numfashinsa hijira daga jikinsa ma ɗan wasu daƙiƙu, sannan ya dawo. Be ɗauke idonsa daga gareta ba be kuma kyafta ba, haka ya ƙafe da ido kamar wani hoto. Nan da nan zuciyarsa ta soma rabawa jijiyoyin jikinsa jini da ƙarfi.
Rassss rassss rassss gabansa yake faɗuwa, sai dai kuma ba irin wacan faɗuwar ba, ta tsoro ko fargaba, faɗuwar gaba ne da shi kansa ba zai iya fassara na minene ba.


Ita sai yanzu ta gane ko wanene shi, daman tun ɗazu ta ga ganin kamar fuskar sani, mutume daya bita asibiti. Ƙamshin turaresan ya haddasa mata ciwon kan da bata yi zato ba, daman tun jiya bata cikin daɗin rai.


“Subhanallah malam wannan kallo ya haramta a musulumci”


Daɗin sautinsa yasa shi lumshe ido yana murmushi.


‘A'uzubillahi minal sheidanin rajin’


Ya furta a zuciyarsa yana ƙoƙarin da abunda

Please Login or Register in order to submit comment