Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

katse min uzuri na”


Zaunawa tayi saman kujera tana murmushi.
Sai shi ma ya zauna yana tambayar Amal abunda ya hana ta zuwa makaranta. Lemu Amira ta ɗauko ta kawo masa a gabansa ta dire masa, tana masa sannu da zuwa.

“Yauwa Thank you so much”


Ta jidaɗin kalma nan da yayi mata, bama kamar murmushin da ta gani shimfiɗe a fuskarsa. Cikin natsuwa ta tashi ta nufi dinning dan zuba masa abinci.


Kallon Ummi yayi fuskarsa ɗauke da abunda ke zuciyarsa.


“Ummi kin yi suruka, matar da na taɓa baki labari ina so na samo ta, finally mafarki na zai zama gaskiya...”


Tartsatsa... Suka ji ƙarar fashewar plate mai ɗauke da abinci, wanda Amira ta sake saboda maganarsa da ta soki gadon bayanta, da sauri ta ɗuka tana kwashewa, kamar wacce ta ruɗe, a take hawaye ya fara bin fuskarta, sai dai su basu gani ba kasancewar ta basu bayana ne.


“Ba ki ji ciwo ba?”


Ummi ta faɗa tana ɗan leƙen ta. Sai Haleema ta yi saurin amsawa.


“A'a plate ɗin ne kawai ya fashe”


Ummi ta maida hankalinta gurin ɗan ta.


“Im happy for you Son, na daɗe ina jiran wannan ranar, you have no idea how happy you make me, sai dai ban gane wacce kake magana ba akai kam ba”


“Ye... ”


Ringing ɗin da wayarsa ta yi ne ya hana shi ƙarasa maganar sai yayi saurin tashi ya nufi wani ɓangare na falon yana amsa wayar.


“Salim”


“Sir mun bincika, Manjo Usman Zamau yana sokoto da zama a unguwar clapperto, yana da mata biyu da ƴaƴa goma sha uku Namra ita ce ta goma, kuma ainahin sunan ta shi ne Khadija, ta yi makaranta a dan fodio tana level 300 aka yi mata aure, kuma har yanzu tana gidan aurenta zaune, facebook username ɗin ta Khadija Usman Zamau instagram kuma Namra's, haka yake a twitter da snapchat”


“Amman ba ku bincika zaman auren ta ba? Har yanzu tana da aure?”


“Binciken mu ya nuna har yanzu tana da aure kuma tana a garin katsina da zama, sunan mijin da take aure Ibrahim amman anfi kiransa da Asim”


“Thank you”


“Your Welcome Sir”


Wayar ya ƙurawa ido yana mamakin yadda Namra zata masa ƙarya, bayan ya tambaye tsakaninta da Allah, taya aurenta zai mutu kowa bai sani ba, hakan yana mufin ƙarya ta masa kenan ko kuma akwai abunda take ɓoyewa.
Juyowa yayi yana ƙoƙarin ɓatar da mamakin dake fuskarsa ya kalli Ummi yana tahowa ya ce.




“Wani aiki ya tashi Ummi Ana nema na a Kaduna yanzu yanzu nan”


“What?”


Ummi ta faɗa da mugun mamaki. Shi kuma ya ɗan ɗaga gira yana kallon Amal.dake zumuɗin labarin daya fara badawa.










Hello habibaties nasan kuna haƙuri da ni dan Allah ku ƙara haƙurin. Wallahi abubuwa ne suke min yawa, ga kuma rashin wutar nepa a gusau, yau four days babu wuta, sai an tashi engine ne muke samu mu saka. Idan kuma ka matsa za'a ce sai ka biya na Mai 😂 you know how our grandma's are, sai haƙuri 😂


Love you all fisabilliah ♥️🌹🌺❤
[7/18, 8:12 PM] Khadeeja Candy♥: *71*


Ɗauke kansa yayi daga kallon da yake ma Amal ya kalli Ummi, irin babu zacen wasa a kalamansa.


“Nima sai da na ce miyasa ba su bar ni nayi aikin ba acan ba sai yanzu da na dawo”


“Abdallah ka ce min kun samu hutu fa? Aikin me zaka je yi yanzu?”


“Wai General ne zai zo daga Abuja zuwa Kaduna gobe, kuma dole ne muje. Bari naje ya canja kaya gobe da safe ai zan dawo”


Be jira abunda Ummi zata ce ba, ya nufi ƙofar fita yana lalabar number Salim dan ya sama masa jirgin da zai koma Kaduna yanzu ko da Yammar nan.
Ummi dai da kallo Mamaki ta bishi, ta fi kowa sanin ɗanta dan haka ta san ba aiki ne zai maida shi Kaduna ba, sai dai wani abun na daban, kai ta girgiza tana kallon Amal data wani turo baki.


“Be ma ƙarasa mana labarin ba”


Ummi ta miƙe tsaye ta nufi kitchen tana faɗin


“Uhnm kya ji da shi”




AMIRA POV.


Tana gama kwashe plate ɗin da ya fashe ta zuba a shara, sai ta nufi ɗakinta cikin wani irin kuka marar misaltuwa.
Saman gadon Amal ta faɗa ta kife tana rera kukanta a hankali yadda wani ba zai ji.


“Shikenan na rasa komai, wata yake so ba ni ba, shi ma na rasa shi”


Tausayin kanta take da kanta tana tunanin irin rayuwar da zata yi nan gaba. Bayan ta rasa duk wani abun da zai iya saka ta farinciki. A hankali Haleema ta turo ƙofar ta shigo fuskarta ɗauke da tausayin Amira,wanda har zuciyarta haka ne. Kusa da ita ta zauna ta kai hannu ta taɓa ta.


“Ki yi haƙuri Amira, ni kai na ban san haka zai faru ba...”


Da sauri Amira ta ɗago ta kalleta da idonta da suka gana canja kala saboda kuka.


“Ke ma kin yarda na rasa ɗan uwanki ko? Babu wani abun da za kiyi? Dan Allah ki taimaka min Haleema kema mecece zaki iya shiga a halin dana shiga, kin san irin abunda nake ji, Wallahi ina son Yaya kuma tsakani da Allah zan zauna da shi, idan har na ci amanarsa na yarda amanar Allah ta ci ni, na rantse da Allah ba zan cutar da shi ba”


Kuka take sosai zuciyarta a narke, ta kama hannayen Haleema ta riƙa tana mai jin kamar Haleema ta yi mata maganin damuwarta.
Cikin kuka Haleem ta ce.


“Babu wani taimako da zan iya yi miki Amira, Big Bro babu mai saka shi dole idan ba Ummi ba, kuma idan har ya nuna baya so ita ma bata so, babu abunda ya cutar da ke kamar zama ba a gurin iyayen ki ba”


“Ba zan iya komawa ba, ban san yadda zan yi na koma ba”


Ya zube ƙasa zaune tana rushewa da sabon kuka. Haleema ta riƙa ta tana bata haƙuri. Kamin ta tashi cikin ɓacin rai ta nufi hanyar fita, Amal ta samu tsaye jikin ƙofar ta yi wani wuƙi-wuƙi da ido.


“Ummi tan kiran ki”


Ta faɗa a sagarce, sannan ta falfala da gudu ta nufi ɗakin Ummi ɗin. Haleema ta rufa mata baya tana share hawayenta. Ƙusƙus ta tarar Amal na yi gurin Ummi, hakan ya tabbatar ma da Haleema Amal ta ji abunda suke cewa.


Meesha na gaban maduba Ummi tana ɗanɗasa kwaliya ita da Fauza, dan su basu ma san Abdool ya dawo ba.


“Ummi ga ni”


Ta faɗa yayinda take ƙoƙarin zama kusa da ita.


“Gulma ta kuke yi?”


Da sauri Haleema ta sake kallon Ummi baki sake, kamin ta maida dubanta gurin Amal.


“Amman yarinyar nan munafuka ce Wallahi, gulamar ta kika ce na yi, aiko sai na miki ɗan banzan duka a gidan nan”




Ummi ta katsa mata tsawa.


“A'a akan me? Maganar me kuke ke da ita har kuke kuka?”


“Walahi akan big bro ne, dan ta ji ya samu mata shine take kuka ina bata haƙuri”


“Dan ya samu mata sai aka yi me?”


“Kin san son shi take sosai wallahi”


“Amman dai Haleema baki da hankali, ke ko a mafarki aka ce yayanki zai aureta idan kika farka ai kya nemi tsarin Allah, macen data zauna da yan fashi? Kika san ciki nawa ta zubar? Baki san zaman ta a nan ma it very risk ba”


“Haba Ummi ciwo ƴa mace na ƴa mace ne, yanzu idan nice a wannan hali zaki jidaɗi? Ba ita ta ƙaddaro ma kanta ba, kuma ta yi sadaukarwa ma Big Bro ita ta cancanci ya so ta wallahi”


Ummi kasa magana ta yi saboda mamakin furucin Haleema. Meesha ta taso daga gaban madubi da take zaune tana faɗin.


“Kin san me Ummi zata iya saka mana guba duka mu mutu idan har ta ji Big Bro ba zai aureta ba, ƙila ma turo ta aka yi, ta ina ma.taji Yaya ya samu mata? Kodai ta ga alamun ba zai so ta ba ne”


Fauza ta amsa.


“Kuma Wallahi irin waɗan nan ba tsoron kisan kai suke ba, tun da sun saba”


Ran Haleema ya ɓace sosai.


“Ku daina judge mutane ne, hakan be da kyau, Allah ma yana karɓar tubar bayinsa balle kuma mu....”


Shigowar Abdool ne yasa duk suka warsar da maganar, Fauza da Meesha suka fara ɗaukin shigowarsa tare da masa sannu da zuwa.


“Ai kune ba ku san ya dawo ba, mu tuni muka sani har ya ba mu labarin matarsa da zai aura”


Ya ɗaga gira ɗaya yana kallon Amal, ita kuna ta shigar da kai jikin Ummi dake dariya, ita ala dole ga auta.


“My girls ku fita za mu yi magana”


Ya faɗa yana ƙoƙarin zama a kujerar dake fuskantar gadon Ummi. Ba musu duk suka fita har Amal uwar son zancen dan bata ga alamun wasa a fuskarsa ba balle ta tsaya.


“Maganar gaskiya Ummi ba aiki zani ba, gurin yarinyar nan zan koma, kawai ki min addu'ah, gobe da safe zan dawo”


“Na gama karantar ka sarau Lamiɗo kallon ka kawai na ke yi. Allah ya kai ka lafiya, kuma a gaishe min ita sosai da sosai”


‘Ai ba gaisuwa ba, ni kaina ban san makomata ba’


Zance daa ya faɗo masa kenan a rai kamin ya ɗago ya saurari zancen da Ummi ta ɗora da shi.


“Dan Allah ka nemo iyayen yarinyar nan, idan ba zata iya zuwa ba, su suzo su tafi da ita”


“Ummi laifin wa? Idan na yi magana ai cewa kike na ɗaga mata ƙafa”


“Ai ba ƙafa ba komai ma.an ɗaga mata, yanzu kam ya kamata ace tana gaban iyayenta”


Miƙewa yayi tsaye yana faɗin


“Don't worry Ummi, if she planning something evil, za a sanar da ni, ai akwai mai kula da cctv camera. A min addu'ah jirgin mu zai tashi nan da ten minutes”




“Allah ya kiyaye ya kai ku lafiya”


Tasowa ta yi ta suka fito tare da shi yana labarta mata maganar da suka yi da Mai Martaba.




Ko da ya isa airport sauran minti uku jirgin ya tashi, abun ka da manya a take aka masa checking ya wuce.
Be da sukuni har sai da jirginsu ya sauka garin Kaduna, yana sauka airport yayi waya daga Abuja, suka kuma suka yi waya a kaduna, cikin minti ashiri sai ga direba in military uniform sun zo ɗaukarsa.


A cikin motar ya sha ruwa, kamin ya buɗe biscuit ya ɗan ci kaɗan yana faɗa musu inda zasu kai shi. A masallaci unguwar ya ce a aje shi, suna yin parking da sauri wani ya fito daga cikin motar yazo ya buɗe masa yana sare masa, umarni ya basu na suje sai ya nemesu. Ba musu suka sake tsara masa suka koma cikin motar suka juya. Yi yayi kamar be kula da mutanen da suke kallonsa ba, yayi alwalarsa ya bi jam'i, har aka gama sallar kowa da abunda yake faɗa, wasu wai ya zo bincike ne, wasu kuma wai akwai wanda zai kama, shi dai yana gama sallah la'asar ya kanyar kwanar da zata sadashi da gidansu Lamido,daman daga masalacin zuwa cikin gidan babu wani nisa sosai. Hango mustafa da yayi yasa shi sauri juyawo ya ciro wayarsa a aljihu ya neman number direban Mai Martaba da yake gidansa da suka sauka da ke Kaduna.


Cikin mintuna da basu bi goma sha ɗaya ba sai ga direba ya iso, be faka ko'ina ba sai gaban Abdool da sauri Abdool ya buɗe ya shiga, yana nuna masa inda zaije.
Mustafa na zaune gindin wani icce yana kallon motar har suka faka ta dai-dai ƙofar gidan su Lamido. Ya maida hankali sosai da son ganin wanda zai fito daga motar, sai kawai yaga baƙuwar fuska ta fito daga gidan gaba mazaunin direba yana buga ƙofar giɗansu Lamido.


“Waye...”


Suka amsa daga can ciki kamin ɗan uwani ya fito waje ganin mai buga ƙofar.


“Shiga ciki ka ce Abdallahi daga Katsina yana sallama da Namra”


“Toh ya juya da gudu ya koma”


Shi kuma direba ya juyo dan mayarma da Lamido saƙo.


“Wai Ance bata nan”


Yaron ya faɗa yana tsaye jikin ƙofar gidan. Abdool ya buɗe motar da kansa ya fito.


“Kije ka ce idan bata fito ba, ni zan shigo”


Yace da yaron babu alamar wasa a maganarsa, haka ma a yanayinsa. Da gudu yaron ya koma, ko minti biyu ba'ayi ba sai ga Namra ta fito cikin farin Hijabi ta doso inda yake. Yana kallonta dukan natsuwarsa taje gareta, kalaman daya tara zai watsa mata marar daɗi sai duk ya neme su ya rasa har ta ƙaraso kusa da shi ta tsaya.


“Ban ce kar ka sake zuwa nan ba? Jiya jiya ban maimaita maka wannan maganar ba? Ka ɓace ka bar ƙofar gidan nan”


Ta faɗa a tsawace, fuskarta babu annuri. lumshe ido Abdool yayi ya buɗe ya kalleta.


“Kina burge ni idan kina ba ni Umarni, da ma ace bakin ki be iya faɗar ƙarya ba, kin ce ba ki da aure bayan kina da shi”


“Idan na maka ƙarya nawa zaka ba ni? Miye ribata idan na maka ƙarya bayan ka tambaye tsakani da Allah?”


“Amman ƴan gidanku sun tabbatar mana da kina da aure, Asim be sake ki”


Wani irin kallon ta jefa mata mai cike da tashin hankali da mamaki.


“Ina ka san ƴan gidan mu? Waya faɗa naka sunan mijina? Waye kai? Me kake nema a gare ni”


“Naje har gidanku ne neman auren ki, kuma sun tabbatar min da kina da aure, auren ki be mutu ba”


Ta ɗora hannu saman kai.


“Na shiga uku na lalace, ka ɓata komai yanzu shikenan ba za su karɓe ni ba, miyasa baka bari na faɗa musu mutuwar aurena da kai na ba? Kaico na ni Namra, duk inda na dafa taɓen mi yake yi, ka cuce ni shiyasa ka tambaye ɗan ka ƙara jefani a halin baƙinciki da damuwa? Wayyo ni Allah na”


Ta juya da sauri ta koma ciki tana kuka. Shi dai kallonta kawai yake har ta gama faɗa masa abunda zata faɗa masa ta juya ta shige. Jikinsa yayi sanyi sosai, ko bata faɗa masa ba yasan there's something behind those words and tears da ya ga suna zuba a idonta. Juyawa yayi zai buɗe motar ya shiga sai ga Mustafa ya iso.


“Ranka ya daɗe naje kai maka kayan aka hanani shiga, kuma aka ƙi karɓa wai baka nan”


Ko kallonsa Abdool be yi ba ya ɗaga masa hannu.


“Na bar maka”


Ya shige motar, cikin rashin jindaɗin rai. Tun kamin su bar unguwar kalaman Namra suka riƙa dawo masa, idan ya tuna hawayen da ya ga suna zuba a idonta sai yaji wani abu ya tsaya masa a zuciya marar daɗi.


“Ranka ya daɗe ina za muje?”


Ya tambaya ganin har sun hau titi amman Abdool be ce da shi komai ba.


“Masaukin Mai Martaba”


Ya faɗa cikin sanyayiyar murya mai nuna mutun yana cikin damuwa.








-----------------------------------------------------------------
Ku yi haƙuri da wannan.




*72*


Da kuka Namra ta shiga gidan, bata kula su Neina da ke tsakar gidan suna gyaran giɗa ba ta wuce ɗakin Uwani, saman katifa ta faɗa tana cigaba da rera kuka.


Duk mamakine ya kama su, daman tun jiya ba su gane ma kanta ba.


“Uwani je ki gani mana”


Lamido ya faɗa yana kallon Uwani, duk ya ji babu daɗi ganin tana hawaye.
Da sauri Uwani ta tashi ta shiga ɗakin, hannu ta kai ta ɗago Namra tana tambayar


“Lafiya miya same ki?”


Sai kawai Namra ta faɗa jikinta ta cigaba da kukan. Jin kukan nata ya ƙaru yasa Neina shigowa ɗakin.


“Ke lafiya miya same ta?”


“Wallahi nima ta kasa min magana, sai kuka take”


“Toh Allah dai ya sa lafiya, ko wani ne ya mutu?”


Sai a lokacin Namra ta samu ta girgiza musu kai, tasa hannunta ta share hawayenta.


“Mutumen da ya zo yanzu, shi ne mutumen da ya zo jiya, kuma shine mutumen da ya kaɗe Lamido”


Ba shiri Neina ta zauna sake da baki dan shan labari, Uwani kuma ta yi ma Namra kallon Mamaki.


“To miyasa kawo shi? Miya ce miki”


A nan Namra ta kwashe labarin abunda ya faru, ta faɗa musu, sai dai bata yarda ta faɗa musu sanin da ta yi masa a Katsina ba.
Dukansun cika da tsananin mamaki, bama kamar Neina da take ganin kamar lokacin da ya zo gidan ba su yi ido biyu da Namra ba.


“Amman Namra in ban da abin ki miye abun kuka a ciki? Ke da Allah ya kawo miki ɗauki? Yanzu ko abunda tsohon mijin nan na ki ya yi miki ai wannan idan kika duba sakamako ne Allah zai miki”


Uwani na kai aya. Namra ta yi mata kallon baki fahimce ni ba.


“Ya ƙara ɓata min komai Uwani, yanzu iyaye na sun ji aure na ya mutu, kuma za su yi tunanin ko nice na tura sa neman aure na, idan yanzu na koma gida ban san mi zan ce musu ba”


Neina ta ɗaga kai ta kalleta


“A yadda na fahimta, idan har yana son ki da gaske ne, hakan ba zai sa ya ƙi ki ba”


“Ya so ni, ko ya ƙi i, ni duka ɗaya ne a guri na, ban shirya mutuwa sau biyu ba, ban shiryawa yaudara Namiji ba, wani na Namiji ba zai sake ɗiga min baƙinciki a rayuwata ba, na rufe shafin Namiji a rayuwata, dan haka ni ba shi nake ji ba, iyayena na ke ji da makomata”


Duk shiru suka yi, suna sauraren kukan da take rerawa. Kamin hankalinsu ya koma kan sallamar da Mustafa yake yi. Neina ce ta tashi ta fita Uwani kuma ta tsaya yana bawa Namra haƙuri.


“Maraba da Mustafa, yau an dawo shago da wuri?”


Ya zauna saman kujerar tsakar gida ta mata, yana faɗin


“Wallahi yau ban ma je ba, ya mai jiki?”


“Jiki yayi sauƙi Alhamdulillahi”


Lamido ya amsa da kansa yana miƙa masa hannu su gaisa.


“Allah ya ƙara sauƙi, naga kun yi wani babban baƙo ne a waje, amman kamar be shigo cikin gidan ba”


“Eh gurin Namra ya zo ɗan'uwanta ne”


Cewar Lamido, kamin Neina ta amsa da


“Wai Ɗan Sarki nan ne da ya kaɗe ka, shine ya zo wai yana son ta, kuma har yaje can gida ita bata ma sani ba”


Da sauri Lamido ya kalli Neina, wani irin abu ya daki ƙirjinsa, be ji daɗin maganar ba, kuma be ji rashin daɗinta ba, sai ya samu kansa cikin wani kalar yanayi na dabam.


“Me ta ce masa? Ai na ga ta dawo da kuka”


Ya tambaya kamar ba komai, sai a baɗini yana jin zuciyarsa kamar ta rabe biyu. A nan Neina ta kwashe labarin da Namra ta faɗa musu ta faɗa ma Lamido.


“Ba duka maza ne ƴan iska ba, ba duka maza ne mayaudara ba, ba a taru aka zama ɗaya ba, yadda wani yake da kwaɗayi ba haka wani yake da shi ba, ba a taru a zama ɗaya”


Ya faɗa a hankali yana kallon wani gurin kamar mai nazari. Har Neina ta buɗe baki zata yi magana, sai Mustafa ya jinjina kai ya ce.


“Amman abun da ya ba ni mamaki, wannan mutumen yayi min kama da wanda na sani, kuma shine mutumen da ya aiko yaronsa ya kira nia ka bani wanki, ya ɗauki dubu goma sha ɗaya ya ba ni wai na wanki ne, har yake labarta min wai shi ɗan'uwan ku ne, kuma yana zuwa gidan, da neje kai masa wankin sai aka ce baya nan, ina nan kuma zaune sai na gansa, ina masa magana wai ya ba ni tufafin”


Lamido ya riƙe baki.


“Wallahi ba mu da wani alaƙa da shi, ai baka nan lokacin daya kaɗe ne da ka gani, anya ba yana da wata muguwar manufa ba ce akan yarinyar nan da mu ma?”


Neina ta yi saurin rufe masa baki.


“Dan Allah ka rufa mana asiri, ɗan Sarki ne”


“Dan yana Ɗan Sarki fa? So what? Ba a da ikon faɗar gaskiya, ku kuke tsoron sa”


Mustafa ma ya saka baki.


“Kai da ka rufa ma kan ka asiri. Ko ma minene iya karka ka yi addu'ah ka zura na mujiya”


“Wallahi ba zan yi ba, ba zan zuba ido wani ya cutar da yarinyar nan ba, iya wahalar da tasha ta ishe ta haka”


Ya faɗa cike da ɓacin rai. Mustafa ya miƙe tsaye bakinsa cike da maganganun da be samu furtawa ba, yana musu Allah ya sauwaƙe.


“Amin an gode Mustafa”


Neina ce ta amsa da haka, Lamido kan hankalinsa na can wani gurin.






ABDOOL POV.


Samun kansa yayi da damuwar abunda be kamata ace ya dame shi ba, ya sara sukuninsa tun hawayen da ya gani suna zuba a idon Namra.


“Na ɓata komai? Na ƙara ruguza mata rayuwa? Mi take nufin da hakan?”


Magana yake yi da kansa yana kallon tv, babu abunda kunnuwansa suke da buƙata a yanzu kamar jin labarin Namra.


“Allah kai ka san ina son yarinyar nan, kuma Allah kai ka saka min son ta, ya Rabb help me, wallahi daga gani sai ta yi taurin kai”


Ya shafa fuskarsa yana busar da iskar bakinsa. Can kuma ya kai dubansa ga wayar dake gefensa ya ɗauka ya danna number Ummi. Bugu ɗaya Amal ta ɗauka.


“Dude zaka cigaba da ba ni labarin matar ka ko?”


Murmushi yayi marar sauti kamar tana gabansa.


“Ina Ummi?”


“Tana falo, ni ina game da wayarta”


“Tau ki ce mata na isa lafiya ƙalau kin ji”


Be jira abunda zata ce ba ya kashe wayar, yana sauke ajiyar zuciya. Sam be jin yau zan iya haƙura be ji labarin Namra ba, dare kawai yake jira yayi masa ya koma unguwar, sai dai me idan tace ba zata faɗa ba fa?


“Tau ya zan yi? Ni Wallahi tsoro ma yarinyar nan take ba ni”


Ya sake magana a fili kamar mai magana da wani. miƙewa yayi tsaye ya nufi bedroom ɗinsa yana ware hannayensa.


“Ina ta ƙoƙarin zama mahaukaci akan wannan yarinyar, Allah ka da ka jarrabe ni ta wannan hanyar”




RASHIDA POV.


Da taimakon Teema suka kwashe duk wani abu na amfaninta suka mayar a gidan da Mahaifinta ya bata. Ɗan madaidaicin gida ne mai ɗauke da ɗakuna biyar, da kuma madaidacin tsakar gida.
Gidan yayi datti sosai duk da kasancewar ba a taɓa zama a cikinsa, sai dai daɗewa da aka yi ba a buɗe shi ba yasa ya koma kamar anyi yaƙi a cikinsa. Tare da teema suka jera komai, sam bata yarda ta nunawa Teema damuwarta akan komawarta gidan ba, hasali ma tana yawan maimaita ita hakan ya fi mata daɗi kuma ita ce ta nemi Dady ta bata gidan alhalin ba haka ba ne, duk yadda hawaye suka yi ƙoƙarin zubar mata sai ta yi kamar abu ya faɗa mata a ido.


Sai dai abunda Teema ta saka samun natsuwa da shi, ganin babu ɗan'uwanta ko ɗaya daya zo rakata a gidan, ko kuma su tausasata akan karta bar wacan gidan ta dawo nan ita kaɗai. Bata nuna mata komai ba har suka gama tsara komai suka share iya inda za su iya, sauran ta ce almajiri zai gyara mata, daf da za su fita Momi ta iso gidan da kukanta kamar wance aka cirewa rai. Duk dauriyar da Rashida ta ke sai da ta fasa na ta kukan, sai ita da Momi aka rasa mai bawa wani haƙuri.


“Ni Wallahi sam ban ga amfanin wannan kukan ba, miye na barin gida Rashida in ban da abun ki? Ai ƙara ki zauna cikin danginki, ko danuwa ai kya rage”


Rashida ta share hawayenta, tana jan majina.


“Ni na zaɓi zama a nan, na fi son na zauna ni kaɗai”


Momi kan bata iya cewa komai ba, sai kawai ta miƙe tsaye tana faɗin.


“Dadyn ki ya ce zai aiko da furniture da abinci, da kuɗi kuma duk abunda kike so ki riƙa faɗa mana”


Daga haka ta fice hawaye na cigaba da mata zuba. Bayan fitarta da minti goma shabiyar Rashida ta tashi ta shiga bathroom ta yi wanke fuskarta ta fito suka ɗauki hanyar dutsen Malam.
Rashida ce take driving, Teema kuma na zaune front seat, sai kallon Rashida ta ke yi ƙasa-ƙasa. Ɗan ƙauye ne da yake can waje gari sai dai kuma ba sosai ba. Shi wannan malamin da alama aikinsa ba yayi ko kuma sabon farawa, dan babu ƙowa a ƙofar gidansa. Matan biyu masu far'ah da son mutane, suna shiga suka ɗauko musu tabarma suka shimfiɗa musu da zimmar za su aika a kira Malam wai yana gona.
Sai ga shi ya iso cikin ƙanƙanen lokaci, jikinsa har ɓari yake, bakin nan cike da goro. Bayan ya gaisa da su yayi musu iso zuwa ɗakin da yake aikin nasa.


“Bismillah”


Ya nuna musu gurin zama yana ɗauko farra ƙasarsa dake cikin ɗan ƙaramin windi. Sai da

Please Login or Register in order to submit comment