Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dawo tare da Maryam ɗin. A nan Meesha ta miƙe tsaye ta kama hannun Amal suka fice saboda ta san komai yana buƙatar sirri.


“Anty Namra ga ni”


“Maryam kin ga wanda ya tada rigima ɗazu?”


“Eh amman ban ga ko waye ba”


“Asim ne fa”


“Asim?”


Ya amsa da ƙarfi.


“Miya kawo shi a nan? Ko ganin ƙwan ya zo zuciyarsa ta kasa ɗauka shi ne ya tada rigima, yaso ya ɓata bikin ne Allah be bashi dama ba”


“Tsoro nake ji Maryam idan ba wani abun ya zo yi ba, idan ba haka ba to me zai kawo shi nan?”


“Ya zo yaga abunda za a yi ne, babu wani abunda zai yi rigima ce kuma ya samu dai-dai shi”


Maryam bata gama rufe baki ba wata mai kama da Abdool ta shigo ɗakin cike da ladabi ta ce


“Adda Namra Mai martaba na son ganinki yanzu”


Gabanta ne ya yankeya faɗi, cikin rawar muryar tace


“Maryam ɗauko min mayafina”


Maryan taƙe tsaye ta ɗauko mata farin mayafin da dake saman gado ba tare da ta kawo ma kanta komai ba.
Sai da ta yafa mayafin sannan ta miƙe tsaye yarinyar ta kama hannunta suka fice.


Ɓangaren Mai Martaba Yarinyar ta nufa wato turakarsa, wani ɗan ƙaramin falon Mai Martaba yarinya ta kaita, cike da ladabi Namra ta shiga kanta a ƙasa, sai dai hakan be hanata ango Abdool dake gaban Mai Martaba kamar mai neman gafara ba.
Ita ƙasa ta zauna, sai Yarinyar ta juya ta fice tare da rufo ƙofar.


Sun daɗe a haka, baka jin sautin komai a ɗakin sai sanyin ac dake tsara jikinsu. Zuwa can Mai Martaba ya ɗora ƙafarsa ɗaya saman ɗaya ya soma magana a tsanake.


“Namra kin san Asim?”


“Allah ya taimaki mai martaba, tsohon mijina ne”


“Taya zamu iya tabbatar da ya sake ki?”


“Ya sake ni a shakarar da ta gabata, kuma iyayena sun san da hakan”


“Akwai takardar saki a hannunki?”


“Be bani ba, da baki yayi furucin Mai Martaba, Allah shine shaidata”


“Mutumen da ya ɗauki hankalin mitane a ɗazun tsohon mijinki ne, kuma yana da'awar be sake ki ba har ma akwai akwai ɗa a tsakanin ku...”


Da sauri Namra ta ɗago kai ta kalli Mai martaba for the first time, idonta har ya kawo ƙwalla, kai ta girgiza.


“Ƙarya yake yi Mai Martaba, Wallahi ya sake ni”


Sai hawaye suka fara mata zuba. Kan Abdool na ƙasa saboda Mai Martaba be bashi damar magana ba.


“Babana!”


Mai Martaba ya kira sunanshi. Sai.ya ɗago da idonshi da suka rine suka canja kala saboda ɓacin rai ya ce


“Wallahi ya sake ta Mai Martaba”


“Kana da takardar sakin ne?”


“A'a amman nasan ba zata min ƙarya ba, kuma na san babban mutum kamar Manjo ba zai yarda ƴarsa ta yi aure kan aure ba”


Mai Martaba ya ɗauki wayarsa ya kira wata number.


“A shigo da shi”


Yana faɗar hakan ya sauke wayar. Ko minti uku ba a ƙara ba, sai ga Asim an shigo da shi yana tsingilta, gaba ɗaya kammaninsa sauya jini sai zuba yake a kansa.
Dogarawa suka durƙusar da shi gaban Mai Martaba.


“Me aka masa haka?”


“Allah ya taimake ka dukan da sojoji suka masa ɗazun ne”


Kai kawai ya ɗaga musu suka juya suka fice. Mai Martaba ya kalli Asim da kyau ya ce.


“Wannan ita ce matarka?”


Sai kawai ya fashe da kuka ya girgiza kai.


“A'a ba ita bace ƙarya na ke”


“Karka ji tsoro kar dukan da aka maka ya tsoratar da kai, na maka alƙawari babu wanda zai sake sa maka hannu, faɗa min gaskiya wannan itace matarka?”


Mai Martaba ya faɗa a natse. Da idonsa ɗaya ya kalli Namra saboda ɗayan ya kumbure, sai kuma ya maida dubansa gurin Abdool, sai a yanzu ya iya tantance Abdool.saboda ɗazun be san ko waye ba.


“Itace ranka ya daɗe. Namra ina ɗa na? Da cikina ta gudu, kuma sanadin wannan mutumen ta gudu, saboda yana tare da ita har yayi mata kyautar gida sanadin hakan na daketa sai ta gudu ta bar gidan, gidan yana nan a unguwar nasarawa”


Kai kawai Namra take girgizawa hawaye na mata zuba. Abdool kuma zuciyarsa ta yi mugun kawowa sai dai babu yadda zai yi tun da a gaban Mai Martaba suke, kuma duk wani unƙuri da zai yi zai ƙara ɗaure kansa ne kawai. Can ciki ya jiyo muryar Mai Martaba na jefo masa tambaya.


“Ka taɓa mata kyautar gida kuma tana da aure?”


Sai da ya taushe fushin da ke zuciyarsa sannan ya iya furta.


“Na taɓa Mai Martaba, amman ba da wata niyar na yi ba, a lokacin basa da kuɗin biyan hayar ne kuma Ummi ta basu lokacin tashi, saboda gidan Amal ne wanda gobara ta ƙone, a lokacin za ayi gyaransa ne”




Mai Martaba yayi shiru yana nazari a zuciyarsa, yasan ɗansa ba zai masa ƙarya ba, kuma baya daga cikin ƴaƴanan mazinata balle har ya zarge shi, kuma yasan lokacin da ya kawo masa labarin Namra, sai dai ɗan yau ba a shaidunsa, kuma zai iyayuwa ita Namra ɗin ta yaudari ɗansa.


“A wani guri kake zaune?”


Mai Martaba ya tambayi Asim a take ya amsa masa ya faɗa masa.


“Tashi ka yi tafiyarka”


Har ya miƙe tsaye sai kuma ya ce


“Mai Martaba kar naje gida wani abun ya same ni”


“Babu abunda zai same ka, indai ni na haifi Abdallah ko hararka ba zai sake yi ba”


Da tsinginta ya fice. Sannan Mai Martaba ya kalli Namra ya ce.


“Za a maidaki gurin Ummi ba zaki tare a yau ba, zan yi magana da mahaifinki”


Cikin wani irin nauyin jiki da zuciya Namra ta miƙe tsaye jiri na ɗibarta, aiko tana kaiwa bakin ƙofa ta sai tayi baya-baya ta faɗi ƙasa sumamamiya.
A take Abdool ya manta da agaban Mai Martaba yake, a guje ya ƙarasa inda take yasa hannunshi ya ɗauke yana kiran sunanta amman ina ta riga tayi nisa.
A firgice ya fita da ita a falon kamar wanda ya tallaɓo jaririya. Mamaki da aljab ya hana kowa magana sai kallon ikon Allah suke, Abdool ya talloɓo Namra sai gudu yake ya nufi parking space da ita. Sojojinshi na hango halin da yake da sauri suka buɗe mota ɗayan ya shiga a driver seat yayi ma motar key, Abdool na isa ya saka Namra gidan baya, sannan shi ma ya shiga.
Wasu sojojin suka shiga wata motar suka rufa masa baya.


@360 suka isa asibiti kai tsaye aka wuce da ita emergency, likitoci suka shiga bata taimakon gaggauwa.
Yana gurin zaune ya dafe kai wasu ƴan gidansu suka iso, cikin har da Hajiya Shafa.
Bayan kamar mintuna talatin likitocin suka fito, ɗaya daga cikinsu ne ya tsaya yana yi ma Hajiya bayani wai a barta ta samu bachi sun mata allura saboda akwai gajiya sosai a tare da ita.


Abdool na zaune a gurin har su Hajiya Shafa suka shiga suka fito, tare da sisters na shi.


“Babangida (Sunan da take kiransa da shi kenan kasancewar sunan mahaifin Mai Martaba ne aka sakaasa) Mu zamu tafi tun da abun da sauƙi, kuma likita yace ana buƙatar ta huta, Hajiya kilishi zata tsaya nan ta kwana, kuma ka faɗawa sojojinka kar su bar kowa ya shigo, ga kuma dogarawa nan Mai Martaba ya iko maka in case of...”


Kai kawai ya iya ɗaga mata, sai sisters ɗinsa da waɗanda suka zo tare suka masa Allah ya sauwaƙe.


Sai da suka fice sannan ya miƙe tsaye yana faɗawa sojan da ke kusa da shi cewar kar ya bar kowa ya shigo gurin, yana rufe baki sai ga Asiya Sister shi ta dawo da gudu ta miƙawa sojanshi carpet da hijab.


“Wai ance a bawa Gwaggo”


Da kanshi ya karɓi sallayar da Hijab ɗin ya nufi ɗakin. Wani abun burgewa sai da sojan ya sare masa sannan ya miƙa nasa.


Yana tura ƙofar ɗakin ya hango Namra kwance gefen gadon an ɗaura mata drip. Hajiya Kilishi kuma na zaune saman kujera sai amsa waya take. Tana ganinshi ta miƙe tsaye ta fice, ƙarasawa yayi ya aje carpet ɗin ya zauna saman gadon ya kai hannunshi ya shafa fuskarta. A hankali ya sauke ajiyar zuciya sai ya sauka ya zagaya ta bayanta ya hau saman hagon ya rumgumeta ya luma yatsunsa cikin nata, sai hawaye suka gangaro daga idonshi suka sauka saman ƙananan kitson da ke kanta.
Jin wayarsa na ringing yasa ya fiddota daga aljihun wandonshi ya kashe ta gaba ɗaya, ya lumshe ido yana ƙara janta jikinsa.


A wani ɗakin Hajiya Kilishi ta kwana, domin be sauka daga kan gadon ba sai da aka kira sallah asuba. Sannan ya sauka saman gadon ya shiga banɗakin dake room ɗin yayi alwala ya fito shi da sojojinsa suka nufi masallaci yayinda aka bar dogarawa suna cigaba da gadinta.


Bayan ya fita ne Hajiya Kilishi ya dawo ɗakin ta yi sallah asuba, bayan ta gama ya hau amsa wayar da ake mata dan tambayar jikin Namra. Sai ga Abdool ya dawo ɗakin a dole ta miƙe tana amsa gaisuwarsa ta fice daga ɗakin.
Wannan karon saman kujera ya zauna ya matsa can kusa da fuskarta ya ɗora tashi saman gado ya kwantar, sai hancinshi ya riƙa gogar nata, numfashinsu na taraiyya da juna.


A hankali ta buɗe ido karaf cikin nashi, bakinta da ke saitin nashi yayi ma kiss sannan ya tashi zaune daidai yana riƙa hannunta, sai itama ta tashi tana cigaba da kallonshi idonta sun yi wani fari.
Har cikin jininshi yake jin tsanyin dake cikin hannunta, zuciyarsa cike da tausayinta.


“Sannu”


Ya faɗa yana kai hannu ya shafa gefen fuskarta.


“Sallah”


Ta ce a kasale. Miƙewa yayi tsaye ya shiga bathroom ɗin ɗakin ya ɗauko ƙaramin bokin da ke ciki ya fito sai ya buɗe ƙofar ɗakin yayi magana da boys ɗinsa da suke gurin, sannan ya dawo ya zauna a kusa da ita.


“Za a kawo ruwa yanzu, muje ki yi fitsari”


Ƙoƙarin saukowa ta riƙa yi sai kawai ya ɗauke ta ya nufi bathroom ɗin da ita.
Ƙoƙarin ɗaga mata saket ɗin ya riƙa yi sai ta riƙe, ya kalleta.


“Baki da ƙarfi Abnam”


“Zan iya”


Baya son musa mata, sai kawai ya fito yaja mata ƙofar. Da dafe dafen bango ta yi fitsarin ta fito, sai ya sake ɗaukarta ya maida saman gadon.


“Allah ya baki lafiya”


Ya faɗa yana kwantarda kanta saman kafaɗarshi. Cikin ƙanƙanen lokaci aka buga ƙofar ɗakin sai ya ɗagarda kanta shi kuma ya tashi ya buɗe ya karɓo robar da carton ɗin ruwan faro, sai da ya buɗe ruwan sannan ya zauna kusa da ita ya kama hannayenta ya wanke mata su sau uku, sai ya zuba ruwa a hannunshi ya kai mata a baki ta kurkure bakinta ta zuba cikin robar sai yasa yatsansa ya wanke mata haƙora, sai ya sake zuba ruwan a hannunshi ya kai mata a baki ta kkurkura har sau biyu sannan ya shaƙa mata hanci sai kuma ya riƙa mata hancin ta face, ya wanke mata fuskarta sannan ya wanke hannayenta zuwa murafiƙai, ya shafa mata kai ya ƙwaƙwala mata kunnuwa sai ya saukar da robar ƙasa ƙasa ya kama ƙafafunta ya tsattsafe ya wanke su tas, sannan ya ɗauke robar ya kai bathroom ya fita ya karɓo mata carpet da hijab.
Sai da ya shinfiɗa mata carpet ɗin sannan ya saka mata hijabin, ya sauƙo da ita saman gadon ya tsayar, ganin jikinta rawa yasa ya zaunar da ita, ya tattara hankalinsa ya miƙa mata yana kallon yadda take sallah a zaune cike da tausayawa. Tana ƙarewa ya dawo kusa da ita ya zauna, sai ta kwantar da kanta saman kafaɗarshi tana hawaye. Hannayensa biyu yasa ya ɗago fuskarta ya kai bakinshi daidai hawayenta yayi mata kiss.


“Babu wanda ya isa ya shiga tsakanin mu Inshallah”


Ya faɗa kamar mai raɗa, sai kawai ta fashe da kuka shi kuma ya rumgumeta a ƙirjinsa, ya lumshe ido yana sauraren sautin kukanta dake tashi a hankali.






RASHIDA FINAL POINT OF VIEW (POV).


Ita ce ta biyu wacce ta miƙe tsaye ta yi jawabin bayan shugabar ƙungiyarsu ta gama, kasancewar yanzu ita ce mataimakiyar shugaba, a duk inda za a je da ita ake zuwa cikin da wajen garin kaduna, har South west, south south suke zuwa gurin wayarda kan al'umma akan a daina ƙyamar masu ɗauke da cutar hiv, suna kuma wayarda kai akan masu cutar su daina takura kansu da ganin kamar mutuwarsu tana kusa da su.
Har ƙauyuka suna shiga su wayarda kai, abun yanxu yayi gaba har nijar da sudan ghana sukan leƙa wani lokacin domin halartar taron ƙarawa juna sani ko kuma na ƙungiyoyin duniya qani lokacin ma.har.


Ta tattara rayuwar aure ta aje gefe, duk kuwa da irin tayin da Alhaji bashir da kuma wasu mazan suke mata, bata son abunda zai sake ɗaga mata hankali a yanzu, shiyasa bata kawowa kanta zancen aure a kusa.
A duk lokacin da ta tuna da Kalsoom ce take riƙe da ƴaƴanta sai ta yi ma Allah godiya, domin bata san Kalsoon ƴar'uwa ba ce sai a yanzu, tana ƙoƙari gurin ganin ta bawa yaranta tarbiya, basa mata complain ɗin sun rasa wani abu ko an musu wani abun sai ɗan abunda rai ba zai rasa ba, sai yanzu ta tabbatar good people are still exist, ba ko wace abokiyar zama ce kishiyaba wata kan ƴar'uwa ce.


Bata da matsala ta ko ina a yanzu, sai dai tana nadamar abunda duk ta tuna sai baƙinciki ya rufeta, wato sanadin wannan ciwon nata, a duk lokacin da aka tambaye ta dalilin wannan ciwon nata ta kan ce ta same shi ne ta hanyar ƙarin jini da aka mata, domin kawai ta kare kanta.

Shekara biyar da shiga ƙungiyar zuwa yau rayuwarta ta zama abar kwatance, rayuwarta darasi ce ga duk mace mai irin rayuwarta, ko kuma halinta, ita kanta yanzu ta koyi abubuwa da yawa na rayuwar duniya da kuma zama da mutane.


Ko da aka yi birthday ɗin Izzah tana Abuja gurin wani taro, washe garin ranar da ta dawo taje gidan ta kai musu tsarabarsu da kuma birthday gift ta bawa Izzah.
Ta jidaɗin yadda ta same su, baka iya banbance tsakanin Ƴaƴan Kalsoom da nata a gurin Kalsoom wato Amal da Rafiq da Husna, sam mutum ba zai iya cewa su ne ƴaƴan Kalsoom ba, sau da dama zata bawa su Izza abu ta hana ƴaƴanta.


Bata daɗe a gidan ba duk da ƴaran sun so haka, amman ta ƙi a duk lokacin da taje gidan haka take bata daɗewa take fitowa.
Ko da iso gidanta uku da rabi yayi, dan haka tana shiga bathroom ɗinta ta yi alwalar la'asar ta fito ta shimfiɗa sallaya ta saka hijab taja carbi tana la'zimi kamin lokacin tada sallah yayi.
Wayarta ce tayi ƙara daman ta ji tsayawar mota a harabar gidanta, sai kawai ta miƙe tsaye ta nufi falo ta buɗe masa ƙofa.


“Hajiya...”


“Alhaji Bashir”


Shigowa yayi yana faɗin


“Aiko na taki sa'ah dan ban tsamaci kina garin ba”


“Jiya na dawo”


“Mashallah ya Abujar?”


Ya tambaya yayinda yake ƙoƙarin zaunawa.


“Abuja sai hamdallah, ya aikin naku”


“Aiki da godiya, iv na zo na kawo miki”


“Ba dai na aurenka ba ko?”


“Shi mana ba kin ƙi ni ba”


“Dana ƙi ka ya hana dubu su soka ne?”


“Cikin dubun ai na ƙawo ƙoƙon barata a gareki amman kika ƙi yarda, kuma ni wallahi ko a yanzu kika yarda zan aure ki”


Ruwan tsanyi ta dire masa tana dariya tare da kai hannu ta karɓi iv ɗin.


“Lallai mutumen da gaske kake, budurwa ce ko bazawara”


“Budurwa ce yarinya ce ba zaki sha wahala gurin kishi da ita ba”


“Ai ni na yafe kishi da kowa, sai dai ina fatar tasan halin da kake ciki”


“Ta sani kan, sai dai bayan ke da ita da kuma Asmee babu wanda ya san da wannan maganar”


“To ita mai cutar ce kenan”


“Ai kema kin sani baƙya buƙatar na faɗa miki”


“Amman Asmee ta ji?”


“Ta ji mana, to me zata yi?”


“Ba komai kawai ina tuna lokacin da take cewa ba zaka taɓa aure ba ne”


“Ni kaina ina tuna wancan lokacin da ina son aure amman sai na kasa yi sanadin hakan muka faɗa hallaka ni da ke, sai dai kin san komai lokaci ne da shi, ko magani kika yi kika ga ya kama to daman can Allah ya rubuta zai kama ɗin”


“Na yarda da hakan ai ni sai dai na faɗawa wani, kuma ina fatar idan ka yi wannan auren zaka ɗaga min ƙafa, saboda mutane suna ta zargin muna tare ne, kuma zaka iya tonawa kanka asiri indan kana cigaba da ziyarta na, saboda kai ma za a iya gano kana ɗauke da cutar, abu na uku kuma kasan ance idan mace da namiji suka kasance su biyu sheiɗan ne na ukunsu, dan haka bana son wata alaƙa ta saɓon Allah ta sake shiga tsakanina da kowa”


“Nima bana nufin wani abun makamancin wannan saboda i realized that duk abunda ka yi wa ɗan wani sai an yi ma naka, tun bamu je ko ina ba a scul wani malami yayi raped ƴata, ban taɓa faɗa miki ba ne saboda ba labari ne mai daɗi ba, amman a lokacin na samu kai na a wani irin kalar mutum, abun da ciwo sosai Rashida, sai na dinga jin kamar na kama duka familynshi nayi musu yankan rago, but a dole na rufe magana domin idan na buɗe yanzu ne zata shiga duniya kowa yasan abunda ya samu ƴata bayan kuma nine sila saboda ban tsare kaina ba, kuma zan jawa ƴata abun faɗi ne kawai”


Ya share guntun ƙwalla da suka zubo masa.


“Ki dubi Family Hilal ki gani da yake ya tsare kansa, sai Allah ya tsallakar da shi, duk da kina a cikin gidanshi Allah ya tsare ƴaƴansa da matarsa da shi kansa mu kaɗai muka kwashi abun, dubi rayuwar gidansa ki gani gwanin sha'awa, ni ko rayuwa baƙinciki ne da kuka, saboda halin da muke ciki, ko wannan ciwon da ke jikinmu tawace gashi kullum muna cikin kafakafa kar ƴaranmu su ɗauka, muka tsoron mu kai su wani gurin riƙo asirinmu ya tonu”


Rashida ta girgiza kai cike da tausayawa.


“Ba ku kyautawa rayuwar ƴaƴanku ba, ku ɗauke su ku kaisu gurin ƙaƙaninsu mana, ko karka yi sake yaranka suma su kwasa su girma suna nadamar da kasancewar ƴaƴanka, karka ɓata rayuwar ƴaran ka tun suna da ƙurciya, ka taimaki future ɗin su, kai taka ta ƙare su kuma ka yi tattalinsu...”


Ajiyar zuciya ya sauke yafi sau goma sannan ya miƙe tsaye jiki a mace ya fice ba tare da ya ce da ita komai ba.
Rayuwa kenan sau da yawa Allah yake maka talala kayi ta iskancin da zarar ya tashi kama ka ba zaka ga da kyau ba, kuma matuƙar be yafe maka ba, zaka je lahira ka tararda abunda ka aikata. Duk magane-magane da Asmee ke yi tana ganin kamar ta ci riba wajen hana mijinta aure ashe ba riba bace lokacin auren ne be yi ba sai yanzu, tun da gashi yanzu zai yi auren,garin neman gira an rasa ido ta kwaso musu cuta tana nadamar da babu ranar daina kukanta. Ita kanta Rashida dake yi wa Kalsoom magani a dole ai yanzu ta saka mata ido ta ɗauke ta ƴar'uwa tun da taga addu'ah da tsarin Allah yana tare da wanda duk ya nemi taimakon Allah, tayi iya yinta amman bata raba Kalsoom da gidan mijinta ba saboda Allah ya riga ya rubuta ita ɗin ce dai.
Mata da yawa suna shiga haƙƙin mazajensu wajen ganin sun hanasu aure ko kuma sun mallake miji da kishiya, bayan kuma sun san Allah zai tsayar da su a gabanshi yayi masu shari'ah ranar da baki baya iya magana.


Jiki a mace ta miƙe ta yi nafila wato ƙabli asri sannan ta ɗora da la'asar ɗin, tasbihi da hailala da hamdala ne suka biyo baya tana gode Allah da ya nuna mata kuskurenta tun a nan duniya da ake karɓar tuba, kuma ya bata ikon tuban, kana ya tsare mata yaranta kuma ya basu uwar da zata riƙesu ta tarbiyantar da su, tabbas yanzu ta tabbatar Ubangijinta yafi kowa sonta, shi ta tsaɓawa kuma ya yafe mata har ya musanya mata ta wani ɓangare.
[7/31, 9:26 PM] Khadeeja Candy♥: *93*


Lafewa ta yi a ƙirjinsa tana sauraren yadda zuciyarsa ke bugawa, sai ƙara shigar da kanta take tana shaƙar ƙamshin turarenshi.


Hannu yasa yana shafa bayanta, idanuwansa a lumshe. Wani abu yaji yana sauko masa marar misaltuwa, be taɓa hugging wata mace kamar yadda yayi a yanzu ba, wata mace kuma bata taɓa kwantawa a ƙirjinsa kamar haka ba, ɗayan hannunta dake cikin hannunshi ya soma matsawa a hankali yana lume baki.


Jin shafar da yake mata ne ya sauya salo ne yasa ta ɗago kanta ta kalleshi, idonsa har yanzu kulle yake, hakan yasa ta ɗaga daga jikinsa gaba ɗaya ta zare hannunta daga nashi.
Sai ya buɗe idonsa yana kallonta, fararen idonsa sun fara rinewa zuwa ja ga wani ruwan hawaye da ya kwanta masa. Hannyensa yasa ya riƙa fuskarta.


“I Love you so much Abnam”


Kallonshi take kamar yadda shi ma yake kallonta, sai hawaye suka zubo mata.


“Ban san mi Asim yake nufi da ni ba, ban san miyasa ya ɓullo ta wannan hanyar ba, na masa iya hallacin da zan iya, saboda shi na rabu da iyayena, na bishi na zauna da shi a inda ban taɓa mafarkin zan zauna ba, lokacin da arziki ya zo masa sai ya guje ni, yace min baya son haihuwa, da cikin ya kure na je garin kaduna ba tare da na san kowa ba, Lamido yayi min masauki a gidansu, a gidan cikina ya zube.


Wallahi tallahi ya sake ni Abdallah, ban san miyasa ya canja min ba, har yana tambayar ɗan sa”


Hawaye na bin fuskarta take maganar zuciyarta cike da rauni. Fuskarta ya saki ya kama hannayenta ya riƙe gam.


“Na yarda da ke Abnam, Asim yana son shiga tsakaninmu ne, saboda yana tunanin zamu fara sabuwar rayuwa mai kyau, karki saka ranki cikin matsala nasara bata zuwa ba tare da wahala ba”


Ƙofar da Hajiya Kilishi ta buga ne yasa shi kallon ƙofar sannan ya kai hannu ya share mata hawayenta. Sannan ya miƙe tsaye ya buɗe ƙofar.


“Hajiya...”


“Na'am, Abdallah ya mai jikin”


“Ta ji sauƙi”


“Ga breakfast nan Hajiya ta aiko su Amal su kawo ance wayarka na kashe”


“Oh Okay bari na kunna”


“Okay ka gaishe da ita”


Ta juya shi kuma ya rufe ƙofar ya dawo yana ciro wayarsa da ke aljihu ya kunna, sai ya kira Ummi.


“Abdallah na kira wayarka kashe”


“Na kasheta ne saboda Doc yace min ana bukatar ta samu bachi, barka da safiya”


“An tashi lafiya ya jikinta? Miya same ta? Meesha tace min kawai sun ga ka fito da ita a sume”


“Ummi labari ne mai tsawo da rikitarwa zan zo anjima”


“Okay ga abinci nan na aiko muku nasan zata buƙaci abincin a yanzu, amman dai ka faɗa min ko minene”


A nan ya soma labarta mata abunda ya faru. Ta kiɗima sosai abun ya zo mata kamar almara, sai dai ta kwantarda hankalinta saboda kar hankalin ɗanta ya tashi.


“Allah zai muku mafita Abdallah”


“Na gode Ummi I love you”


“Allah ya maka albarka”


Yana sauke kiran wayar Mai Martaba ta shigo, cike da ladabi yayi picking.


“Assalamu Alaikum Mai Martaba”


“Wa'alaikassalam, Babana ya mai jiki”


“Alhamdullillah ta ji sauƙi fatar ka tashi lafiya”


“Alhamdullah, Babana bana son ka tashi hankalinka na san kana sonta sosai, sai dai bana son da kake mata ya iya rufe maka ido ka tsallake gaskiya, kai ɗana ne nafi son komai za'ayi ka tsaya kan gaskiyarka”


“Mai Martaba kafi kowa sani na, ba zan taɓa aikata abun assha ba, kuma zan saurareshi matuƙar yana da hujja”


“Allah ya maka albarka”


“Amin Mai Martaba Allah yaja kwananka”


Daga haka ya sauke wayar sai ga kiran sisters ɗinsa ya shigo sai kuma na Maryam, sai dai be ɗaga ba sai kawai ya kashe wayar. Ya miƙe tsaye ya fita. Sojojin da ke gurin da dogarai ya sallama sai dogara ɗaya ya bari, sannan ya dawo ɗakin.


Wannan karon jikin windo ya same ta tsaye fuskarta na kallon ƙasa kasancewar inda suke gidan sama ne. Ƙarasawa yayi ya riƙe kunkurunta ya ɗora kansa saman wuyanta.


“Jiya ya kamata ace na tare, amman hargitsin da ya faru jiya ya hana hakan, dare biyu kenan na amarci ina kwana ba cikin daɗi ba, a wacan daren fargaba da tunanin halin da na bar mahaifina da kuma tunanin makomar aurena, yanzu kuma wannan hargitsin ya taso, Ina

Please Login or Register in order to submit comment