Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: https://chat.whatsapp.com/K8mrKzSJTP1CYMAj1ci1of








*⚡ NEEHAL⚡*






_By_
_Zeey Kumurya_












_*Da sunan Allah mai kowa mai komai, Allah ka sa yanda na fara rubuta Littafinnan lafiya na gama shi Lafiya, Allah ka ba ni ikon rubuta abun da zai amfanar da Al'umma Ameen.*_







```Kamar yadda na yi alƙawari yau zan fara sakin sabon book ɗina NEEHAL, gashi na cika alƙawarin, sai dai ba na jin daɗi hakan ya sa za ku ga page d'in kaɗan, nima ba haka na so ba, ina buƙatar addu'ar ku🙏🙏😥 Masoya.```








0️⃣1️⃣








............A ƙaton parking space d'in gidansu driver'nsa wanda ya kasance soja kamarsa ya yi parking rantsatstsiyar motar da suke ciki, driver'n ya fito da sauri ya zagaya ɓangaren da yake ya buɗe masa motar, ya ɗan ja baya tare da sara masa irin nasu na sojoji, a hankali ya ziro da santaleliyar ƙafarsa ta dama, bayan 3 seconds ya ziro ta hagun itama tare da fitowa gabad'ayansa fuskarsa babu walwala ko kaɗan kamar kodayaushe, kai kawai ya gyad'awa driver'n ya fara tafiya cikin takunsa na ƙasaita da isa, part ɗin mahaifiyarsa ya nufa direct, duk inda ya gilma sojojin dake kai kawo a farfajiyar gidan na sara masa, kasancewar mahaifinsa shima GENERAL ne na sojoji, hannu kawai yake d'aga musu.




Da sallama ƙasa_ƙasa ya shiga main parlour na part d'in Mama, Mama da mahaifiyarta Hajiya dake zaune a parlorn suka amsa masa suna binsa da kallo, Hajiya tana washe baki ta ce "Aminullahi! sannunka da zuwa, ashe da rabon zamu haɗu da tuni yau na tafi baffanku ya ce in bari sai Monday zai zo mu tafi" ya ɗan saki fuska ya ce mata "Yawwa, ina yini" idanunta na kansa ta ce "Lafiya k'alau, ya aikin?" ba tare da ya amsa mata ba, ya zauna a kujerar dake fuskantar ta su ya dubi mahaifiyarsa wadda suke tsananin kama da shi tamkar an tsaga kara ya ce "Ina yini Mama" ya ƙarasa zancen yana dafe kansa tare da taune lips d'insa na ƙasa dan maganama wahala take masa" Mama data k'ura masa ido ganin yanda ya rame ta ce "Lafiya k'alau, yau sai yanzu kazo har ina shirin kiranka in tambayeka ko this week ba za ka zo ba, Dad ma kafin ya fita yanata ta tambayarka" ya gyad'a mata kai kawai tare da kwantar da kansa a jikin kujera ya lumshe fitinannun idanunsa, Hajiya data saki baki da hanci tana kallonsa ta ce "Aminullah cuta kayi acan Lagos ɗinne naga duk ka zabge ka rame haka, kamar wanda ke zaune cikin guggun mayu?" Shiru yay mata kamar ba da shi take ba , A ɗan fusace Hajiya ta ce "Nifa matsalata dakai jarababben miskilancinka na tsiya, ana maka magana kana yiwa mutane banza" nanma shirun ya kuma mata, Mama ta tab'e baki ta maida kanta akan wayarta dake hannunta, Hajiya ta dubeta ta ce "Ke kuma Fatima wacce irin uwa ce ke? Kina kallon yaro ya dawo a haka, ai kya tambayesa ki ji me ya samesa ya yi irin wannan zabgewa haka" Mama ta d'ago da kanta tana duban Hajiya ta ce "Amma fa Hajiya kinsan halinsa, ko zan kwana ina tambayarsa abin da ke damunsa idan bai ga dama ba, ba faɗamun ze yi ba, kema kuma gashi kin tambayesa ya miki shiru" cikin faɗa Hajiya ta ce "To kuma sai abiye masa, ai ba dan shi zaki yi ba" Mama ta ce "Hmmm, Hajiya Ameen fa ba yaro ba ne yasan ciwon kansa" Hajiya ta ce "Sai kuma ki yi, amma dai wannan rashin kula ne gaskiya, ace kiga yaro haka ki nuna masa halin ko in kula, ni tunda ya rainani ai ba ze bani amsa ba dama, amma ke tunda ke kika haifeshi dole ya sanar miki" Mama ta mata shiru ta cigaba da sabgarta, Hajiya ta cigaba da mitarta da masifarta.




Wata kyakkyawar budurwa ce take sakkowa daga kan steps d'in dake parlour'n, sanye take cikin wani wandon jeans dark blue wanda ya kama jikinta sosai, sai riga t_shirt pink colour, babu ɗankwali akanta, kawai ta tufke gashintane cikin ribbom, hannunta riƙe da waya tana latsawa da earpiece sanye a kunnenta, Mama ta d'ago jin takunta tana kallonta fuska a daure ta ce "kar ki kuskura ki ƙarasomun nan a haka" NEEHAL ta d'ago da kanta daga kallon wayarta da take ta kalli Mama sannan ta juya ta koma inda ta fito ta na turo baki gaba, Hajiya ta keb'e baki ta ce "Oh ni Zainabu, Allah kanunamun ranar da wannan yarinya za tai hankali ta san ta girma" Neehal ta koma ɗakinta tana kwab'e fuska ta ɗakko after dress ta ɗora a kan riga da wandon jikinta tare da sanya hula a kanta ta ƙara fitowa ta dawo falon ƙasan, Hajiya ta ce "To ba ki fi kyan gani ba yanzu, amma da kinfito kamar wata y'ar arna" Neehal ta turo baki gaba, ta na ƙoƙarin zama kusa da Mama ta lura da Ameen dake zaune yanda yake tun d'azu, waro manyan idanunta tayi waje cikin murnar ganinsa ta ce "Yayana yaushe ka zo?" Ameen wanda tun sanda ta ƙaraso falon ya buɗe idonsa yake kallonta ta ƙasan ido baice komai ba, Neehal ta koma kusa dashi ta zauna, dama tunda ta shigo falon taji k'amshinsa amma bata lura da shi ba saboda mitar da Hajiya take mata, ta tattaro duka nutsuwarta saboda sanin halinsa ta ce "Yaya ina yini" bai tanka mata
ba, sai idanunshi daya mayar ya lumshe kawai. Neehal ta ɓata fuska ta tashi daga kusa dashi ta koma kusa da Mama, Hajiya ta ce "Wannan mugun hali naka Aminu Allah ya sauya maka shi da gaggawa, yarinyar ta taho da murnarta tana maka magana amma ka shareta, saboda baƙin hali irinnaka" Mama ta dubi Neehal data kwanta mata a jiki ta ce "To mage, sai yanzu kika tashi daga baccin?" Neehal ta ce "Um" Mama ta ce "K'arfe nawa zaki aiki?" Neehal ta ce "Around 4" Mama ta ce "Sai ki tashi ki shiga kitchen for lunch, kinga 2 ta kusa" Neehal ta kwab'e fuska sosai tana barin jikin Mama ta ce "Tom" Arayuwar Neehal bata k'aunar aiki ko kaɗan, musamman ma girki ta fi tsanarshi, gashi in dai tana gida ita take yi, Mama ba ta yi, masu aiki dama wanke_wanke da shara kawai suke yi sai kuma ɗan tayayyar aiki, dan ko Neehal tana School ko gurin aiki Mama ke girkinta da kanta. Neehal ta mik'e tana duban Mama ta ce "Me zan dafa?" Mama ta ce "ki yi abun da zai yi sauri dan kar ki yi late gurin aiki, akwai ma soyayyen kayan miya na soya ɗazu, ki haɗa miya kawai sai ki dafa wani abun simple a ci da miyar" Neehal ta ce "Toh" tare da nufar hanyar kitchen. Hajiya ta ce "ki yi sauri da'Allah kar yunwa ta kashemu" Neehal bata bi takanta ba ta shige kitchen. Mama ta mik'e tana duban Ameen ta ce "Mit me in my room" batajira amsarsa ba tayi hanyar step, a hankali ya mik'e ya bi bayan Maman, Hajiya ta bishi da kallo cikin tausayinsa kamar zatayi kuka ta ce "Aminu Allah ya baka lafiya, bari jenal ya dawo gaskiya a san abin yi, tunda ita uwarta ta ka shashashace"




Mama tana duban Ameen dake zaune a gefenta a bakin gado fuskarta babu wasa ta ce "Ameen me ke damunka?" Shiru ya yi tare da sunkuyar da kansa, Mama cikin takaicin shirun da yay mata ta kuma cewa "Ameen da kai nake fa, ko ba ka jina ne, kasan bana son wannan iskancinnaka ko, ana maka magana ka na jin mutane ka yi musu banza" Jin yanda Mama ta yi magana a fusace ya sa shi d'agowa ya na duban Maman cikin muryarsa mai daɗin amo da sanyi ya ce "Babu komai Mum" ya ƙarasa zancen ya na taune Pink lips d'insa na ƙasa tare da maida idanunshi ya lumshe ya na sauke numfashi a hankali. Mama ta bishi da wani irin kallo cike da takaici gami da mamakin halinsa na zurfin ciki, tun yana ɗan ƙaraminsa haka yake, miskilancinsa da zurfin cikinsa ya yi over. Mama ta sauke numfashi cikin ƙoƙarin ganin ta danne tata damuwar, cikin sanyin murya mai nuni da rarrashi ga wanda akewa ta fara magana, "Al'Ameen!" Ta kira sunanshi a ɗan kausashe, bata jira amsarsa ba ta cigaba da magana da faɗin, "Ameen, Ni mahaifiyarkace duk duniya ba ka da kamata kamar yadda nima ba ni da kamarku, ko kaɗan ba na son ganinka cikin damuwa, amma kuma 2 years kenan idan ban manta ba kullum cikin damuwa nake ganinka, ka faɗamun menene damuwarka ko na samu nima hankalina ya kwanta" buɗe idanunsa da suka yi nauyi ya yi ya saukesu akan fuskar Mama wadda take kallonsa itama, matsowa jikinta ya yi ya kama hannayenta zuciyarta cike da tausayinta ya ce, "Babu komai fa Mum, ni babu wani abu da ya ke damuna, idanma da akwai addu'arki kawai nake buƙata" kallonsa kawai Mama ta tsaya ta na yi, duk wannan uwar ramar da ya yi amma ya ce mata babu abun da yake damunsa. Ajiyar zuciya ta sauke, dan tasan tunda ya faɗa mata haka ba zai taɓa faɗa mata abun da yake damunnasa ba, kome zata masa kuwa, kamar yadda ya faɗa addu'ar kawai za ta cigaba da masa. Ganin yanda take kallonsa ya ce "ki yi haƙuri UMMUNAH, ba na son ki sa damuwa a ranki, dagaske nake miki babu abun da yake damuna ki yarda da ni mana" Mama ta nunfasa ta ce "Shikenan, Allah ya sa mu dace" a saman lab'b'ansa ya amsa da "Amin" tare da sakin hannun mahaifiyartashi. Mama ta ƙara fuskantarshi ta ce "Saura kuma maganar da muka yi kwanaki, na gaji da yawo da hankalin da kake mini Ameen, ka fitar da mata ka ƙi" ɓata fuska ya yi ya ce "Har yanzu ban sami wadda tamun ba ne" Mama ta masa wani kallo ta ce "Ita kuma Hamidan da take jiranka kusan shekaru goman fa, koma ba Hamidan bama ai ba rasa masu sonka ka yi ba, dan haka banason wani zancen banza, wannan itace last Maganar da zan yi maka akan ka fitar da matar Aure, zan d'aga maka ƙafa zuwa bayan bikin Neehal, idan ba ka zaɓi mata da kanka ba Ni zan zab'a maka, danni da son raina ne ma a yi bikinka tare da na Neehal" jinjina mata kai kawai ya yi ya mik'e ya fice daga ɗakin, dan kwata_kwata baya son maganar Auren da Mama take yi masa a kodayaushe. Mama ta bishi da kallo zuciyarta babu daɗi.




Neehal ta na shiga kitchen ta dakko tukunya ta d'aurayeta ta zuba ruwa ta kunna gas ta ɗora, wayarta dake kan locker kitchen ce ta fara ringing, dakkowa ta yi ta sauri ta duba sunan *HEART CRUSH* ta ga ya na yawo akan screen ɗin, ɗagawa ta yi da murmushi akan fuskarta ta ce "Aloo" daga ɗaya ɓangaren Haneefah ta ce "Na bi Aloo d'in da gudu, dan iskanci na kiraki tun ɗazu amma shine ba za ki iya biyo bayan kirannawa ba" Neehal ta na murmushi mai sauti ta ce, "Sorry Bestynah, time ɗin da kika kira ina bacci ne, ban jima da tashi ba mama ta tura ni kitchen girki, so nake na ɗan rage aikin dama na kira ki ke da MY HUSBAND" Haneefah ta tab'e baki ta ce "To me miji, mun dai kusa miƙa ki gidansa kowa ya huta da rashin kunyarki" Neehal ta yi 'yar ƙaramar dariya ta ce "Na ji ɗin, ya kike ya Mommy?" Haneefah ta ce "Mommy tana Lafiya nima haka, ya Mama da Hajiya da Husband d'in naki?" Neehal ta ce "Suna lafiya ƙalau" Haneefah ta ce "Masha Allah, dama kiran ki na yi in ji ko kin dawo daga school" Neehal ta ce "Tun 12 na dawo" Haneefah ta ce "Da wuri haka?" Neehal ta ce "Kin manta yau Saturday lecture ɗaya gareni 10_12" Haneefah ta ce "Hakane fa, na sha'afane" Neehal ta ce "Yaushe za ki fito ne?" Haneefah ta ce "Ni yanzuma na gama shiryawa shiyasa na ƙara kiranki" Neehal ta ce "Toh ki zo mana, sai ki tayani na ƙarasa girki sai mu wuce kawai" Haneefah ta ce "In zo in taya ki girki ko kuma ki ce in zo in ƙarasa Miki girki?" Neehal ta ce "Ni dai koma yaya ne ki yi sauri ki zo" Haneefah ta ce "Toh Mommy ganinan" Neehal ta yi dariya ta ce "Sai kin ƙaraso" ta kashe kiran ta lalubo number'n masoyinta kuma mijinta nan da watanni biyu masu zuwa insha Allah wato ANWAR, kiransa ta yi amma no Answer, ajiye wayar ta yi batare data ƙara kirannasa ba, dan tasan ya na wani uzurinne da ya hanashi d'aga wayar tata, komawa ta yi ta cigaba da aikinta.




After 15 minutes Haneefah ta ƙaraso gidan, Mama tana sama har time ɗin, Hajiya ce kawai kwance akan kujera bacci ya ɗauketa, Ameen kuwa part ɗinshi ya yi bayan ya dawo daga ɗakin Mama. Kitchen Haneefah ta nufa bayan ta ajiye handbag d'inta da mayafinta a kan kujera, Neehal tana cikin slicing d'in cabbage da za ta yi co'slow da shi Haneefah ta yi sallama a kitchen d'in, da sauri Neehal ta ajiye abun hannunta tare da juyawa cikin farin cikin ganin besty'ntata ta amsa mata sallamar, itama Haneefah cike da murnar ganinta ta ƙaraso inda take, rungume juna suka yi Neehal tana faɗin "Welcome dear" Haneefah ta saketa tana faɗin "Thank you" Neehal ta ce "Yau gabad'aya ban ji d'uriyarki da takurarki ba, na yi missed ɗin ki" Haneefah ta ce "Nima haka diarling, ina Mama fa?" Neehal ta ce "Ta na sama may be" Haneefah ta ce "Na ga mutuniyartamu ana ta shan bacci ai" Neehal ta ce "Hajiya rigima, ta kusa tafiya ai mu huta da magana, yawwa dear dan Allah ɗan ƙarasa mini girkinnan na je na shirya kar mu yi latti" Haneefah ta harari Neehal ta ce "Ba wani dan ki shirya, kawai dai ki ce kin ga ji da aikin" Neehal ta b'ata fuska ta ce "Kamar kin sani kuwa" Haneefah ta ce "Hmm, yarinya idan ma za ki daure ki na girki ta daɗin rai ki daure, dan idan aka kai ki gidan ki dole ki yi" Neehal ba ta ce komai ba ta fice daga kitchen d'in.




Ta na fitowa falo ta ji mayen k'amshin turaren Ameen da har time ɗin bai bar falon ba, tunawa ta yi ashe fa ya dawo, kallon saman steps ta yi ta juya kamar wata mara gaskiya tana tafe ta na waige ta buɗe ƙofar falon a hankali ta fice ta nufi part d'in Yayannata dake kusa da nasu part d'in.......✍️












*Neehal it's free book, your comments and share kawai nake buƙata*












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: *0️⃣3️⃣*












.............Lumshe idanunta ta yi tana shaƙar daddaɗan kamshinsa da ya mamaye falon, numfashi ta sauke ta buɗe idanunta a hankali cikin ƙoƙarin dai_daita nutsuwarta ta cigaba da tafiya kanta a ƙasa, sallama ta yi masa cikin siririyar muryarta tana kyab'e fuska ita a dole fushi take da shi, ba tare da ya d'ago ba ya amsa mata sallamar a can ƙasan mak'oshi, har ta ɗan wuce shi za ta haura saman steps ya kirata ta hanyar faɗin "Miemah!" Tsayawa ta yi tare da juyowa amma ba ta ƙaraso inda yake ba, kamar ba shi ya kira ta ba ya wani waske abunsa yana ta aikin latsa wayarsa, sanin halinsa ya sa ta ƙaraso inda yake ta zauna a ƙasan kujerar da yake ta ce "Ga ni Yayah" Be kulata ba, kusan 2 minutes kamar ya manta da ita a gurin, sai kuma ya d'ago ya mata wani kallo, cikin daddaɗar muryarsa mai daɗin sauraro ya ce "Sau nawa zan hanaki bulbula turare a jikinki idan zaki fita?" Turo baki ta yi gaba ta ce "Kaɗan fa na saka" ya ce "Ƙarya na miki kenan?" Girgiza kanta ta yi alamar a'a, maida hankalinsa ya yi kan wayarsa, Neehal na son wucewa sama amma ta na tsoro tun da bai bata umarni ba, shikuma ya cigaba da al'amuransa kamar ya manta da ita a gurin, kuma ya na sane umarninsa take jira, ɗayar wayarsa da ke ajiye a kusa da shi ce ta yi ƙara alamun shigowar kira, dubawa ya yi, ganin sunan Dad na yawo akan wayar ya sa shi d'agawa da sauri. Dad ya ce "Muhammad ka dawo daga masallacin ne?" Ameen ya ce "Eh" Dad ya ce "Daughter din ta dawo ne" ya ce "Eh" Dad ya ce "Ok, ina son ganinka yanzu a part ɗina" Ameen ya ce "Ganinan zuwa yanzu" ya katse wayar tare da miƙewa ya nufi part d'in Daddy wanda akwai ƙofar da za ta sadaka da part d'in Daddy'n ta cikin falon Mama. Neehal ta mik'e da sauri kamar wadda ke zaune a kan ƙaya ta haye sama. Ɗakin da Hajiya take ta lek'a, Hajiya dake zaune kan darduma ta na lazimi ta dubi Neehal ta ce "A'a kin dawo ne?" Neehal ta ce "Ba gashi kin ganni ba" Hajiya ta ce "To sannunki da dawowa, ina ja'irar ƙawar taki?" Neehal ta ce "Ta wuce gida, Mama ba ta dawo ba?" Hajiya ta ce "Sai bayan magriba fa ta tafi, na yi_na yi ta haƙura da zuwa asibitinnan ta huta itama amma ta ƙi, kamar wadda aka yi wa wahayi haka ta tafi a darennan, dan ma aikin Allah za ta yi, tun da duba marasa lafiya ne" Neehal ba ta ce Komai ba ta juya ta fice ta nufi ɗakinta. Tana ajiye jakarta ta fito ta nufi kitchen, cake ta ɗauko da meatpie saboda wata irin yunwa ta ke ji, ɗakinta ta koma bayan ta ɗau drink a falo, sai da ta ci ta yi k'at, sannan ta tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala dan yin sallar isha'i.






Tun da Ameen ya shigo Dad yake binsa da kallo cikin mamakin irin ramar da ya yi, duk da Mama ta masa bayani a waya amma bai yi zaton abun ya kai haka ba, Ameen ya zauna a ƙasan kujerar da Abba yake tare da sunkuyar da kansa ƙasa, Dad ya nisa ya ce "Muhammad cuta ka yi a can barrak ɗinne ba mu sani ba?" Ameen ya ce "A'a Daddy" Dad ya ce "To wannan ramar fa ta menene?" Shafa lallausar sumar kansa ya yi tare da lasar lips d'insa na ƙasa, cikin girmamawa ya ce "Dad yanayin aiki ne kawai" Dad yay shiru ya na kallonsa ba tare da yarda da abin da ya ce ɗin ba, sanin halinsa koda zai kwana yana tambayarsa ba faɗa masa abin da ke damunsa zai yi sai ya kyale shi kawai, amma tabbas ya san akwai abin da ke damun ɗan nasa. Sauke numfashi Dad ya yi ya ce "Shikenan Captain, Allah ya taimaka ya ba da sa'a" Ameen ya amsa da "Amin" Dad ya gyara zama ya ce "Ɗazu kafin na fita mun yi magana da Doctor akan shirye_shiryen bikin Daughter, tunda bikin ya matso, ya kamata mu san abin yi mu fara shiri" Ameen ya ce "Hakane, Allah ya kai mu Lokacin da rai da lafiya, ya kuma sanya Alkhairi ya ba su zaman lafiya" Dad ya ce "Amin ya Allah, ta mun Magana kuma a kanka kaima, ya kamata a ce zuwa yanzun kaima ka fitar da matar Aure, dan mu da son samu ne ma a haɗa bikinka da na Daughter" Ameen ya d'ago kansa da sauri ya na duban mahaifinnasa amma bai ce komai ba, Dad ya ce "Kayi shiru Captain" Ameen ya sauke Numfashi ya ce "Dad a dan ƙara mini time, zuwa bayan bikinnata insha Allahu zan fitar da mata nima" Dad ya ce "To shikenan, Allah ya kai mu da rai da lafiya, ya kuma haɗa ku da abokan zama na gari, Allah ya muku Albarka" Ameen ya ce "Amin ya Allah" Wata hirar suka shiga daban akan aikinsu na sojoji.




Neehal tun tana sallah take jin wayarta na ringing, sai da ta idar ta yi shafa'i da wutri sannan ta ɗakko wayoyinnata dake cikin jakarta.




Wayarta da personnal sim ɗinta yake ciki ake kira, missed call ɗin Mama ta gani da na masoyinta, Layin Mama ta fara kira, ringing daya Mama ta d'aga, Neehal ta ce "Hello Mama" Mama ta ce "Wato Neehal har yanzu ba ki koyi sallama a waya ba ko?" Neehal ta ce "Sorry Mamanah" Mama ta ce "Sorry for your self, kin dawo gida ne?" Neehal ta ce "Eh tun ɗazu" Mama ta ce "Dad fa?" Neehal ta ce "Shima na ga car ɗinsa a parking space, amma ban je part d'in shi ba, na tsaya Sallah ne" Mama ta ce "Ok, kin ci abinci dai ko? Dannasan halinki da zama da yunwa" Neehal ta ce "Na ci snaks" Mama ta ce "Haka dai ki ka iya, Ina Hajiya?" Neehal ta ce "Ta na ɗakinta, Yaushe za ki dawo Mama?" Mama ta ce "Sai 10, dama kira na yi in ji ko kin dawo, zan yi abu yanzu ki kula" Neehal ta ce "Toh Mama sai kin dawo" daga haka ta katse wayar. Number'n Anwar ta dannawa kira, sai da ta kusan katsewa ya ɗauka, Neehal ta ce "Amincin Allah ya tabbata ga farin cikin zuciyata, dafatan ka wuni lafiya, kaina bisa wuya na, yau nasan Queen ta yi lefi" Anwar ya lumshe idansa cikin jin daɗin kalamanta da tsananin farin cikin jin muryarta ya ce "Tare da ke tauraruwar da ke haskaka birnin zuciyata, amma tabbas yau kam Queen ta mini laifi babba ma" Neehal ta waro kyawawan idanunta waje tana murmushin jin daɗin kasancewarta da masoyinnata ta ce "Haba my Habibi, a yi haƙuri mana insha Allahu Queen ba za ta kuma ba" Yanda ta yi maganar cike da shagwab'a ya sa sai da tsigar jikin Anwar ta tashi, ya ɗan sauke numfashi ya ce "Shikenan ai Queen ɗita ta wuce gaban komai a gurina, amma dai yau ta mini k'wauron jin muryarta wanda hakan ya sa na rasa nutsuwata gabad'aya" Neehal ta ce "Am so sorry mijin, missed call ɗin farko da ka mun ina bacci ne, da na tashi kuma na kira ka ba kai picking ba, har na je gurin aiki na dawo ba ka kira ba, sai yanzu" Anwar ya ce "Sarkin bacci, to ya kike?" Neehal ta ce "Alhamdulillah sai kewarka da ta cikamun zuciya da gangar jikina" Anwar ya ce "Missd You too my love, ya Mamana da Yayanah da Dad ɗinmu?" Neehal ta ce "Duk sunanan lafiya k'alau, ya Amminah?" Anwar ya ce "Masha Allah, Ammi tananan klu" Neehal ta ce "Ka gaidata Please da sauran 'yan gidan" Anwar ya ce "Za su ji Insha Allah, yaushe zan zo in ganki ne na yi missing kyakkyawar fuskarnan taki" Neehal ta ce "Gobe mana" Anwar ya ce "Allah ya kai mu amaryata" Hira suka ci gaba da yi irin ta masoya mai cike da nishad'i da farin ciki, ba su wani jima ba su ka yi sallama Neehal ta ce za ta part d'in Dad ne.








Da sallama ta shiga falon Dad, Dad na zaune akan kujera ya na karatun jarida time ɗin Ameen ya fita, Dad ya d'ago tare da amsa sallamar Neehal ɗin fuskarsa ɗauke da murmushi, Neehal ma murmushin ta ke yi ta ƙaraso cikin falon tana faɗin, "My Dad yau na yi missing ɗinka over" Dad ya ce "Nima haka my daughter, ya aikin" Neehal ta ce "Alhamdulillah" tare da zama a gefen Dad d'in, Dad ya ce "Ɗazu bayan mun fito daga meeting na kunna TV na ce bari in ga daughter nah, time ɗin ki na labaran yamma" Neehal ta yi murmushi "Dad ya ce, yanzu nake shirin kiranki na ce ki had'o mini fruits" Neehal ta Mik'e tana faɗin "Bari na had'o maka

Please Login or Register in order to submit comment