Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuskar Neehal ya ce. "Thanks You so much Darling, ban san me zan ce miki ba saboda tsananin farin ciki, Allah ya yi miki albarka ya raya mana su, ya sa mu zamto ababen alfahari a gare mu." Idanunta a lumshe ta amsa da Amin cikin jin kunyar su Mama. Ya ɗago yana ɗan jijiiga yaron dake ta mulmul da baki saboda dabino da Zamzam da aka saka a bakin. Mama ta ce, "Tunda ba ki yi baccin ba tashi ki gwada feeding ɗinsu." Ta buɗe ido a hankali tare da tashi zaune tana yamutsa fuska. Ameen ya yi saurin saka mata pillow a bayanta ta jingina da shi sannan ya ɗora mata yaron akan cinyarta. Ƙurawa kyakkyawar fuskarsa ido ta yi tana jin duk duniya babu abun da take so kamar shi da ɗan'uwansa a yanzu, wani irin feeling take ji a kansu wanda baki bazai iya faɗa ba, wannan ita ce soyayyar ɗa da Uwa data ji ana faɗa kenan. Daddy ya miƙawa Ameen ɗayan ya fita dan zuwa Masallaci jin an fara kiran assalatu, Mama ta mara masa baya dan akwai abun da zata yi a office ɗinta yanzu. Ameen ya zauna a kusa da Neehal bayan fitar su yana murmushi ya ce. "Ki bashi mana." Ba tare data ɗauke idonta daga kan ɗanta ba ta ce. "Me?" Ya ce, "Abincinsu mana." Ta yi murmushi tare da zuge zip ɗin rigarta ta ciro Brest ɗin ta ɗan raba bakin yaron ta saka masa a hankali. Kamar bazai sha ba sai kuma ya fara zuk'a, ta ɓata fuska tare da runtse ido. Ameen da ya kura mata ido ya ce. "What?" Ta ce. "Zafi na ji." Ya matsa jikinta sosai ya ce. "Sorry." Ta shafa kuncin yaron hannunsa ta ce. "Kamarku ɗaya da su." Ya ce. "Eh mana, ai saboda na fi ki son su ne." Ta ɓata fuska bata ce komai ba. Gyara Babyn hannunsa ya yi ya rungume ta, kwantar da kanta ta yi akan kafaɗarsa idanunta akan yaranta, jin abun take kamar a mafarki, yau ita ce da ƴaƴa har biyu, gaskiya ikon Allah ya wuce gaban komai a rayuwa. A haka Mama ta turo ƙofa ta same su, saurin barin jikin Ameen ta yi tana ƙara yin ƙasa da kanta. Mama ta dube shi ta ce. "Baza ka yi Sallar ba ne kai?" Ya shafa kansa bai ce komai ba, ya miƙa mata yaron ya fita, ta bi shi da kallo sannan ta mayar da kallon ga Neehal ta ce. "Ruwan Nonon ya zo kenan?" Neehal ta ce. "Ban sani ba, yana dai ta tsotsa." Mama ta ɗauke shi ta saka mata ɗayan ta ce. "Shi ma bashi ya sha, idan ma bai zo ba sosai nan gaba zai zo."










Kafin ƙarfe goma na safe Mama ta rubuta musu sallama tunda lafiya ƙalau take ita da Babies ɗin. Da daddare Neehal tana zaune akan gado a ɗakin Mama ita da Ameen ya ce mata. "Baby Wanne suna za'a saka musu ne?" Ta ce. "Duk wanda kake so Yaya." Ya shafi kan na hannunsa ya ce. "Wannan tunda shine Babba a saka masa Muhammad, Sunan Ma'aiki S.A.W, mun kuma yiwa Daddy da Abba takwara." Sannan ya shafi kan na hannunta ya ce. "Wannan kuwa Abubakar Sadik." Ta yi murmushi ta ce. "Masha Allah, sunaye masu daɗi da asali, Allah ya raya su ya saka su biyo hali da dabi'un masu sunan." Ya ce. "Amin, me za'a na ce musu?" Ta yi shiru na wasu sakanni sannan ta ce. "Sudais da Shureim." Ya ce. "Masha Allah, Allah yasa su kasance masu karatun Alqur'ani kamar masu sunan." Ta ce. "Amin." Suka cigaba da hirar su wadda gaba-d'aya akan yaran ne, idan ka ga yanda suke yiwa yaran sai ka rasa waye ya fi son yaran a cikinsu..... Tunda aka yi haihuwar kullum gidan cikin baƙi ƴan zuwa barka yake, Twins da Mamansu gwanin sha'awa kodayaushe tsaf_tsaf da su an shirya su cikin kaya masu kyau da tsada suna ta tashin ƙamshi. Da safe kafin Ameen ya tafi aiki yake zuwa sai kuma bayan Magriba idan ya dawo, idan ya ɗauki yaran nan daƙyar ake karɓar su daga hannunsa, Neehal kawai yake bawa su ta daɗin rai, ita ma wai dan saboda feeding ɗinsu ne. Saura kwana uku suna Hajiya ta zo, tunda ta zo ta sakawa Ameen ido, bai isa ya shiga sun zauna da Neehal a ɗaki ba sai ta fara mita tana cewa "Jego dai take yi Manne mata." Shi kuma yana sane sai yay ta yin wasu abubuwan yana ƙara kunna ta. Neehal tay ta yi musu dariya. Ana i gobe suna Ahmad ya zo ya ga Babies shi da twins, waɗanda farin ciki ya kusa kashe su saboda Aunty ta haifo musu k'anne guda biyu, kowa da nasa a cewarsu. Kayan Barka sosai Daddy ya siyawa yaran bayan wanda Ameen ya siya already tun kafin a haife su, ga waɗanda mutane suke ta kawowa, sai kayan suka yi yawa sosai Masha Allah. Ranar Suna aka sha shagali a gidan Mama, an yi komai cikin bajinta da wadata. Mai Jego ta sha kyau ita da Babies ɗinta har ma da Angon ƙarnin. Neehal ta cigaba da zama a gidan Mama, shi Ameen ya ɗauka da an yi suna zata koma, Mama ta ce sai bayan ta yi arba'in.












Yau Asabar wanda ya kama wata guda cif da haihuwar Neehal. Tana zaune a parlour ita kaɗai tana chatting a wayarta ta ci kwalliya ta yi kyau sosai sai tashin daddaɗan ƙamshi take. Ameen ne ya shigo parlour'n da sallama. Ta ɗaga kai ta kalle shi cikin mamakin ganin sa a dai-dai wannan lokacin, kasancewar time ɗin tsakiyar rana ne bai fi ya zuwa a irin time ɗin ba. Ta gyara zama tare da yi masa sannu da zuwa tana murmushi. Ya zauna a gefen ta yana kallon ta bai ce komai ba. Hannunsa ɗaya ta kama ta ce. "Ya dai?" Ya langwab'ar da kai ya ce. "Baby kullum ƙara kyau kike hankalinki kwance, but me ko bacci bana iyawa saboda rashin ki." Ta ce. "Who told you? Ina missing ɗinka sosai fa Yaya." Ya ce. "Ba wani nan, ni ban gani ba." Ta ce. "Me zan yi ka yarda to?" Ya ce. "Ki cewa Mum kin gaji ke gidanki zaki koma." Ta yi murmushi sosai bata ce komai ba. Ya ɓata fuska ya ce. "Oh dariya ma kike ko?" Ta kwanta a jikinsa tare da rungume shi ta ce. "No, kai ma ka san bazan iya faɗawa Mama haka ba, kuma idan ka yi haquri kwanaki kaɗan suka rage in koma." Ya ce. "Kafin lokacin na gama jiga ta kenan?" Tana yi masa tafiyar tsutsa a bayan kunne ta ce. "Tunda ka daure na baya zaka daure na gaba ma." Ya saka hannayensa ya zagaye bayanta cikin marairaicewa ya ce. "Ni dai ki sakawa Mama kuka ta bar ki mu tafi gidanmu, wankan ya isa haka." Ta ce. "Ka yi haquri Yayana Please mu ƙarasa sauran kwanakin." Banza ya yi mata ya ɓata fuska sosai. Ta kai finger ɗinta ta fara zagaye lips ɗinsa da shi tana faɗa masa wata magana a cikin kunnensa, ya lumshe idonsa tare da yin murmushi ya ce. "Ina Twins love?" Ta ce. "Suna gurin su Aunty Dije sun goya su." Ya ce. "Ke kullum sai dai a goya miki su, ke bakya goya su?" Ta ce. "Ban iya ba ni." Ya ce. "In mun koma gidanmu fa?" Ta ce. "Ai zaka na goya mun su ko?" Ya ja karan hancinta ya ce. "Sai dai ke in na goya ki." Ta ce. "Tom Yayana, su sai su yi ta kwanciyar su kawai." Wani kallo yay mata da ya saka ta yi dariya. Tashi ta yi ta karb'o Sudais Zulai ta biyo ta da Shureim, Ameen ya karb'i Shureim ɗin, wasa ya fara yi masa yana ɗan ɗaga shi. Ya ce. "Baby kin ga yana mun dariya." Ta ce, "Shureim ɗin ko? Yaushe ya iya dariyar?" Ya ce. "Gashi nan kuma." Ta ce. "Na gani ai." Ya ɗago ya dube ta ya ce, Wai ina Mum ne?" Ta ce. "Bacci take yi, jiya Sudais bai bar ta ta yi baccin kirki ba." Ya ce. "Kamarya?" Ta ce. "Kukan dare ya yi ta yi, ni kuma na kai mata shi ta rarrashe shi, tunda ni na yi na yi ya ƙi yin shiru." Ameen ya shafi fuskar yaron ya ce. "Ka daina kukan dare kana hana Mum da Baby bacci, dan wannan Mum ɗin taka raguwa ce, wataran in ka ƙi yin shiru taya ka kukan zata yi." Ta tura masa baki ba ta ce komai ba. Ya kalli lips ɗin da suke zuba k'yalli ya ce. "I want it." Ƙara tura masa su ta yi, ya matso da fuskarsa a hankali ya ɗora nasa akai..... Daƙyar ta samu ya cika ta, shi ma dan Shureim ya fara kuka ne. Ya dungure masa kai sannan ya miƙa mata shi, ta yi murmushi tare da bashi Sudais sannan ta fara feeding ɗinsa. Ƙura nata mata ido ya yi, kallon shi tare da saka hannunta ta kwantar da kansa akan kafaɗarta. Ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido yana shaƙar daddaɗan ƙamshinta........Kwanan su Neehal Arba'in da biyu ta koma gidanta ita da Dije domin tana taya ta rainon su Sudais, lokacin sati ɗaya da yin bikin Salma da Sadik. Sabon shafin soyayya Neehal suka buɗe ita da Ameen bayan ta koma wadda tafi ma ta farkon Auransu. Ranar Anniversary ɗinsu Ameen ya yi celebrate ɗinta sosai, kyaututtuka masu tarin yawa ya yi mata na k'auna tare da nuna mata tsantsar soyayya. Washegari kuma suka tafi yawon shak'atawa zuwa other countries su da twins ɗinsu wanda suka yi wayo sosai kamar ba ƴan wata biyu da kwanaki ba..........














*AFTER FIVE YEARS.*










Katafaren parlour ne babba mai ɗauke da duk wani abun ƙawata parlour a cikinsa, ƙamshi mai daɗi ne ke tashi a cikin parlour'n. Wasu yara ne ƙanana guda biyu kaɗai a cikin parlour'n Mace da Namiji waɗanda baza su wuce shekara uku ba. Macen tana zaune a kan kujera ta keɓe fuska kamar zata yi kuka. Namijin kuma yana zaune a kan Carpet yana playing game. Hanif da Haneefah kenan second born ɗin su Neehal. Turo ƙofar parlour'n aka yi aka shigo, gaba-d'aya yaran suka kalli bakin ƙofar. Ameen ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Da gudu Haneef ya tashi ya je ya rungume ƙafafunsa, Ameen ya ɗaga shi sama ya shilla sannan ya sauke shi ya kamo hannunsa suka ƙaraso cikin parlour'n. A gaban Haneefah ya tsaya ya ce. "Wa ya taɓa mun Hany Baby ɗita?" Yarinyar mai kama da uwarta exactly ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba ta ce. "Ba Mommy ce ta koro mu downstairs ba, kuma ta ce baza ta ƙara kai mu gidansu Yaya Afrah da gidansu Yaya Neehal da gidan Mama gurinsu Ya Sudais ba." Ameen ya yi murmushi ya ce. "Rashin ji kuka yi mata ko?" Ta ce. "Hanif ne ya barbaza mata kayan kwalliyarta." Hanif ya yi saurin cewa. "Allah Abbu ita ta ce in zo in taya ta kwalliya irin wadda Mommy take yi." Ameen ya ce. "How many times I told you ku daina yiwa Mummy rashin ji kuna saka ta magana saboda bata lafiya?" Haneefah ta ce. "Sorry Abbu mun daina." Ameen ya ɗauke ta ya ce. "Yawwa yaran albarka, ku zo mu je mu bawa Mummy haquri." Ya kama hannun Hanif suka nufi upstairs. A k'aton bedroom ɗin Neehal suka tarar da ita tsaye a gaban mudubi tana gyara kayan dake kan shi. Ta juyo a hankali ta kalle su sau ɗaya ta ɗauke kanta. Suka ƙarasa kusa da ita, Ameen ya ce "Mummy mun zo bayar da haquri." Ta kalle shi ta ce. "Bazan haqura ba yau kar ma ku ɓata bakinku." Haneefah data fi Hanif surutu ta marairaice fuska ta ce. "Please Mummy we are sorry." Harararta ta yi ta ce. "Kin fi kowa iya rashin ji da bakin bayar da haquri." Ameen ya ce. "Yanzu dai Please Mummy forgive us." Neehal ta ce. "Shikenan, amma kar ku kuma." Yaran suka rungume ta suna murna. Haneefah ta ce. "Mummy yanzu zaki kai mu gidansu Yaya Afrah da Yaya Neehal da gidan Mama ko?" Haneef ya ce. "Da gidansu Abul (Ɗan Sadik da Salma) ko Mummy?" Neehal ta ce. "Insha Allah." Ameen ya zaro choculates daga cikin aljihunsa ya ba su sannan ya ce. "A je a parlour asha ban da ɓata jiki da rashin ji." Da gudu suka fice, Neehal ta bi su da kallo a ranta tana jinjina rashin jin su, shi yasa Mama su Sudais ne ƴan wajenta, yanzu ma suna gidanta za su yi mata weekend, su Haneef kuwa ana kai mata su take tattaro su da kayansu ta bayar a dawo da su, dan baza ta iya ciwon bakin bari_bari ba.








Ameen ya janyo ta jikinsa ya ce. "Me ya faru ne Babyn Baby?" Ta shagwab'e fuska ta ce. "Kai ne mana, daga fita Masallaci tun ɗazu sai yanzu zaka dawo." Ya kama hannunta suka ƙarasa ya zauna a bakin gado ya zaunar da ita akan cinyarsa ya kwantar da kansa akan kafaɗarta ya ce. "I'm sorry Baby love, mun tsaya da Barrister ne, amma ke ma kin san duk inda nake my heart is with you." Ta yi murmusa tare da shafar sumar kansa bata ce komai ba. Cikinta dake ɗauke da Unborn ɗan wata huɗu ya shafa ya ce. "My Unborn Twins, Abbu missed you." Neehal ta ɓata fuska ta ce. "Na ce maka bazan ƙara haifar twins ba insha Allah, da su Haneef zan ji ko da su in na haife su?" Ya ce. "To ba tare muke rainon ba?" Ta ja kunnen shi ta ce. "Kaima ai rainon naka nake yi." Ya yi murmushi ya ce. "Exactly ƴar Aljannah, yanzu ma a zo a ji da ni." Ta kwantar da kanta a jikinsa ta ce. "Dole ne ma ai, I love You so much Nurul qalbi." Ya ƙara rungume ta tsam kamar zai mayar da ita ciki, cikin wani irin yanayi da ƙamshin jikinta ya jefa shi a ciki ya ce. "Love You too My Baby." Tare da ɗago fuskarta ya haɗe bakinsu guri guda cikin tsananin shauk'i..........✍️














_*Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah. Komai nisan dare gari zai waye, komai nisan jifa ƙasa zai dawo, sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'a je ba. Yau 02/06/2022 Ubangiji Mai girma da ɗaukaka ya nufa na kammala wannan book ɗin nawa mai suna NEEHAL, Kuskuren da na yi a cikinsa Allah ya yafe mun, abun da na faɗa dai-dai Allah ya haɗa mu a ladan. Da fatan za'a ɗauki darussan dake cikin labarin, a yi kuma watsi da abubuwan cikinsa marasa kyau. Masoya masu bibiyar littafin Neehal tun daga farko har kawo yau ina godiya tare da yi muku fatan Alkhairi, alkhairin Allah ya kai muku har gadon baccinku. Ina roqon wanda na ɓatawa a cikin wannan tafiyar ya yafe mun, domin ɗan Adam ajizi ne. Waɗanda suke ganin kamar ban yi musu dai-dai ba a cikin labarin su yi haquri haka na tsara labarin tun farko, Na gode Na gode Na gode sosai MASOYA, Allah ya bar k'auna. Sai mun haɗu a sabon Nobel ɗina nan ba da jimawa ba da yardar Allah. NEEHAL, AMEEN AND MAMA they will miss you😍🥰.*_








*DOMIN GYARA KO SHARHI AKAN LITTAFIN NEEHAL, Contact Me.*
👇
*09047871750*












*By*
*Zeey Kumurya* Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment