Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zauna jiransa, mintuna kaɗan ya dawo, ya zauna a ƙasan gado ya janyo ledar kazar ya ce. "Me kike jira baki fara ci ba?" Ta nuna masa kansa da hannunta, tana ƙoƙarin sarving ɗinsu ya katse ta da faɗin. "I forgot something." Ta kalle shi da alamun tambaya, ya ce. "Je ki yi alwala." Ta ce. "Na yi Sallah fa." Ya ce. "Wata zamu sake." Ba tare da tunanin komai ba ta je ta yo alwalar, kafin ta fito har ya shimfid'a musu darduma. Ya miƙe bayan ta saka hijabinta ya ja su suka yi Sallah raka'a biyu, ya dad'e yana yi musu addu'ar zaman lafiya da wanzuwar farin ciki a rayuwar auransu a cikin sujjadarsu ta ƙarshe. Bayan sun idar ya kama kanta ya yi mata addu'a kamar yadda ma'aiki (S. A. W) ya koyar da mu ga sabbun ma'aurata, sannan ya umarce ta data yi masa shi ma kamar yadda ya yi mata. Bata yi musu ba ta yi masan, ya ce su je su ci kazar. Tare suka ci amma wannan karon bai bata a baki ba, ko taɓa ta bai yi ba bai nuna alamar ma zai yi hakan ba, hakan yasa ta ji daɗi amma duk da haka a takure take jin ta, masifar tsoron da take ji a ɗazu ne dai ya ɗan ragu tun da ta ga bai yi mata komai ba tunda ya shigo ɗakin. Bayan sun gama tana tattare kayan ta ce. "Jiya ya ka yi da ragowar kazar nan?" Ya ce. "Tun a daren na kaiwa mai gadi." Ta gyaɗa masa kai sannan ta fice da kayan. Sai da ta dauraye su sannan ta komo ɗaki, ta tarar ya fita baya ɗakin. Ajiyar zuciya ta saki ta jin daɗi sannan ta rufe ƙofar ɗakin, toilet ta shiga ta yi ƴan uzurarrikanta, ta fito ta cire kayan jikinta ta saka wani riga da wando masu taushi na bacci, ta mitsitsika humra a jikinta kamar yadda mai gyaran jikin da ta yi mata ta ce tana yi duk dare sannan ta kashe light ɗin ɗakin ta kwanta ba tare da ta kunna bedside lamp ba. Bacci take ji sosai, ta bararraje akan gado tana murna a ranta zata yi baccinta cikin kwanciyar hankali babu fargaba da tsoron komai a ranta. Sai dai ko 5 minutes ba ta yi da kwanciyar ba ya turo ƙofa ya shigo, a lokacin bacci ya ɗan fara ɗaukar ta. Ta buɗe idonta a hankali gabanta na fad'uwa. Kunna torchlight ɗin wayarsa ya yi ganin ɗakin da duhu, ta yi saurin runtse idonta tana addu'ar Allah yasa idan ya ga bacci take ya k'yale ya koma ɗakinsa. Shi kam dama abun da yake so kenan, so yake ta saki jikinta sai ta sakankance sai ya dawo ɗakin. Ya ɗan tsaya yana haska ta sannan ya hau kan gadon ya yaye bargon data rufe jikinta da shi. Tana jin shi ta ƙi motsawa duk dan ya yi tunanin bacci take. Ya haske fuskarta yana murmushi cikin sanyin murya ya ce. "I know you are not sleeping." Ta buɗe idonta kaɗan tana kare fuskarta da hannunta bata ce komai ba. Ya matsar da wayar daga saitin fuskarta sannan ya matsa jikinta ya saka hannunsa akan lallausan gashinta ya fara shafawa a hankali. Ta sauke ajiyar zuciya a hankali tare da lumshe ido saboda yanda ƙamshinsa yake ratsa k'ofofin hancinta, a shagwab'e ta ce. "Yaya I want to sleep." Ya ajiye wayar hannunsa sannan ya ɗauki kanta ya ɗora akan cinyarsa, cikin wata irin murya da idan da za'a ce mata Yayan nata yana da ita baza ta yarda ba ya ce. "Ni kuma tunanin ki da san kasancewa dake ya hana ni bacci *Baby love*." Saboda tsananin mamaki bata san lokacin data buɗe idonta cikin sauri ta kalle shi ba, dan tabbatar da abun da ta ji ba kunnenta ne ya jiye mata ba dai-dai ba. Ya ja kumatunta tare da kashe mata ido ya ce. "It's so amazing ba?" Ta yi shiru kawai tana kallon shi. Ya yi murmushi, sannan ya rank'wafar da fuskarsa daf da ta_ta, cikin murya mai kama da rada ya ce. "Na san zaki yi mamaki idan na ce miki am in love with you tun lokacin da ban san menene so ba, ban ma san me kalmar son take nufi ba, lokacin kina only 5 years a duniya da muka zo gidanku da Mama kika zo kina mun ihu a cikin kunnena. Tun ranar tunanin ki yake manne a cikin raina, da shi nake kwana nake tashi. Sometimes sai in zauna ni kaɗai idanuna a lumshe ina hango ki a cikin raina kina yiwa Aunty shagwab'a ko kuma kina surutunki ko kuka da tsalle_tsallenki, sai in ji ina son na kuma ganinki, a lokacin ban gane ma'anar hakan ba sai daga baya na fahimta. Duk yanda zan miki bayanin yanda soyayyiyar ki ta azabtar dani baza ki gane ba Miemerh, amma dai na sha wahala. Bayan Allah ya yiwa su Abba rasuwa kin dawo hannunsu Mum da zama bazan iya kwatanta miki farin cikin da na ji ba a wannan lokacin, na tabbata ko Mum bata kai ni farin ciki da hakan ba, tunda ko ba komai idan na zo gida duk weekend zan gan ki in ji daɗi a raina. Dalilin da yasa ban bayyana miki soyayyata a gare ki ba a lokacin da ya dace, da na yiwa Daddy maganar ina sonki sai ya nuna mun in bar maganar dan bazai bani ke ba, ban kuma san dalilinsa na faɗar hakan ba har yau. Na haqura da maganar ko Mum ban faɗawa ba, ba kuma wai dan na daina son ki ba ne, ko kaɗan soyayyar ki bata ragu ba a cikin zuciyata sai ma ƙaruwa da take yi, saboda in yiwa Dad biyayya ne kawai na haqura." Ya yi shiru na wasu sakanni yana goga mata sajen fuskarsa a kuncinta sannan ya cigaba da magana. "FATEEMAH....! I LOVE YOU WITH ALL MY HEART, I LOVE YOU MORE THAN WORD CAN EXPLAIN, I LOVE YOU MORE AND MORE NEEHAL." Ta lumshe idonta tana jin ta kamar a cikin gajimare saboda wani irin shauk'i from no where da yake mamaye dukkan zuciyarta, an sha faɗa mata kalaman soyayya babu adadi a rayuwarta, an furta kalmar *i love You* babu adadi, amma bata taɓa jin waɗanda suka yi tasirin da wanda Yayanta yake faɗa mata a yanzu ba a cikin zuciyarta. Kalamansa sun ratsa dukkan zuciya da gangar jikinta. Ta ji kamar ta ce ya cigaba da yi mata kalaman kar ya daina. Hannunsa ta ji yana dawo a sassan jikinta cikin wani irin salo da yasa ta ji kamar jinin jikinta zai tsinke ya tsiyaye. Ya ƙara yin ƙasa muryarsa bakinsa akan kunnenta ya ce. "Baki ba zai iya faɗar irin tarin k'aunar ki dake cikin raina ba saboda yawanta, but i want to show you ta yadda zaki gamsu ki tabbatar da abun da nake faɗa miki." Ya ja numfashi tare da lumshe idonsa ya ɗora bakinsa akan nata, a tare suka saki wasu tagwayen sanyayan ajiyar zuciya. Cikin lokaci ƙanƙani Ameen ya juye mata daga wanda ta sani zuwa wani daban, sarrafa ta yake cikin wani irin salo mai tsayawa a rai da wuyar mantawa cikin k'warewa da nutsuwa. Da farko sak'onnin nasa sun fara tasiri a kanta, daga baya da ta ga yana ƙoƙarin kaiwa ga abun da take matuƙar tsoron faruwarsa sai ta fara ƙoƙarin k'watar kanta tare da saka masa kuka, amma ina bai gane wannan yaren ba, inda yake son zuwa kawai yake hanqoro. Bata ƙara firgicewa da al'amarinsa ba sai da ta ji yana karanta addu'ar data san mana'arta da dalilin da yasa ake yin ta, ta fara ture shi tana dukan duk inda hannunta ya kai a jikinsa a ƙoƙarinta na son ya k'yale ta amma bai ma san tana yi ba, burinsa kawai yakai inda ransa yake da murad'in zuwa. Duk yadda Haneefah ta dinga kwatanta mata wahalar abun ta ji fiye da hakan, sai da ta yi tunanin baza ta farka ta gan ta a duniya ba saboda azabar da ta sha, Mama da Daddy da duk sunan wanda ya zo bakinta sun sha kira da neman agajinsu, kuka kam har sai da muryarta ta dashe saboda yin sa.........
















Bayan komai ya lafa tana kwance a ƙirjinsa ya yi mata kyakkyawar runguma kamar zai mayar da ita ciki, idanunsa a lumshe ya cusa kansa a cikin gashin kanta yana shaƙar ƙamshin gashin, hannunsa ɗaya yana kan gadon bayanta yana shafawa a hankali cikin sigar rarrashi. Ita kuma ban da hawaye da sakin ajiyar zuciya babu abun take. Jikinta gaba-d'aya ciwo yake mata, ko ɗan yatsanta bata tunanin zata iya d'agawa. Sassauta riqon da ya yi mata ya yi ya ɗago fuskarta cikin tsananin tausayinta da k'aunar ta ya ce. "Please Miemerh ki bar kukan nan haka, zaki ƙarawa kanki wani ciwon fa." Ta cinno masa baki kamar zata yarda shi a ƙasa ta bar jikinsa cikin dauriya tare da juya masa baya tana ƙara ƙanƙame bargo a jikinta ta cigaba da kukanta. Ya yi murmushi kawai sannan ya tashi zaune, yau jin zuciyarsa yake fess tamkar wani baƙin ciki bai taɓa wanzuwa a cikinta ba saboda farin cikin da ya cika ta, yanda yake jin kansa cikin nishad'i da annashuwa ba zai misaltu ba. Jallabiyarsa ya lalubo ya zira a jikinsa sannan ya miƙe ya kunna light ya shiga toilet, bayan wasu mintuna ya fito ya hau kan gadon ya kama bargon jikinta da nufin ya yaye shi. Ta ƙanƙame bargon idanunta a runtse tana ƙara volume ɗin kukanta, ita kaɗai ta san azabar da take ji a cikin jikinta, jin cikinta take kamar an yi mata yasa, ƙafafuwanta kuwa kamar ba'a jikinta suke ba, ƙasanta kamar an jajjaga mata attaruhu a gurin saboda radad'in da yake mata. Ya rank'wafa ya ce. "Baby wanka zan miki fa." Ta ture fuskarsa da hannunta ta ƙara juya masa baya, wata irin kunyarsa ce ta ninku a cikin zuciyarta akan wadda take ji a da. Bata ankara ba sai ji ta yi ya ɗauke ta cak ita da bargon. Ƴar ƙara ta saki saboda ji ta yi kamar ya fama mata ciwon jikinta, ya rungume tsam yana rarrashinta sannan ya miƙe da ita a jikinsa ya kai ta toilet ya ajiye ta a cikin tub bayan ya zare bargon jikinta. Zabura ta yi ta ruk'unk'ume shi kamar zata janyo shi cikin tub ɗin saboda azabar data ji tana ratsa ta a sakamakon jin ta da ta yi a cikin ruwan zafi. Ya riƙe ta ya mayar da ita cikin ruwan ganin tana ƙoƙarin miƙewa. Sannu kawai yake jera mata cikin kulawa da soyayya, ita kuma sai taɓara take zuba masa, sai dai ta ƙi bari ta buɗe idonta ta kalle shi. Sai da ruwan ya huce sannan ya fita ya bar ta dan ta yi wankan tsarki. Ya dawo ɗakin ya cire zanin gadon ya sake wani sannan ya fice daga ɗakin ya je ɗakinsa ya yi wanka ya dawo. Ta ji sauƙin radad'in da gurin yake mata sanadiyyar ratsa ta da ruwan zafin ya yi. Bayan ta yi wankan, ta fito daga cikin tub ɗin daƙyar, a lokacin ya dawo toilet ɗin. tsugunnawa ta yi da sauri tana dunk'ule jikinta guri guda tare da fashewa da kuka. Ya dafe kansa a ransa yana faɗin 'Yau fa sai Allah Neehal da kuka, dama yaya lafiyar kura bare kuma ya taɓo ta.' Towel ya ɗauko ya ɗaura mata duk da daƙyar ta bar shi ya ɗaura matan wai ita bazai ga jikinta ba, sannan ya lullub'e mata kanta da wani ya ɗauko ta suka fito ya kwantar da ita ya shiga tsane mata kanta da towel. Sai da ruwan gashin nata ya ɗan tsana sannan ya kwanta ya janyo ta jikinsa ya ce. "Please Baby ki bar kukan nan mana, ko so kike zuciyata ta fashe ne?" Cikin kuka ta ce. Ni ka kai ni gurin Mama mutuwa zan yi." Ya shafi pink lips ɗinta ya ce. "Wai gurin da zafi ne sosai?" Shiru ta yi masa a ranta tana cewa. 'Dan ba jikinka ba ne ai.' Ya kai hannu ƙasan mararta ya ce. "Mu ji ya gurin yake." Ture hannun ta yi da sauri ta matse ƙafafuwanta. Ya ƙara rungume ta a jikinsa ya ce. "Gani fa zan yi ko da ciwo a gurin." Ta fashe da kuka sosai ganin shi nishad'in shi ma yake ita ya bar ta da jin azaba a jikinta, Cikin kuka ta ce. "Kuma sai na haɗa ka da Mama." Yana dariya ƙasa_ƙasa ya ce. "Me zaki ce mata ƴar gidan Mama?" Shiru ta yi masa ta cigaba da kukanta, ya yi murmushi sannan ya shiga rarrashinta, cikin lokaci ƙanƙani bacci ya dauke ta. Ajiyar zuciya ya sauke tare da gyara mata kwanciya. Ya shiryawa dukkan wata rigimarta dan ya san dole ya sha ta a wannan stage ɗin tunda ya siya da kuɗinsa. Ya lumshe idonsa d'umin jikinta na ratsa shi yana saukar masa da nutsuwa, bai san sanda shi ma baccin ya yi awun gaba da shi ba.......✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_*By*_
_*Zeey Kumurya*_














*8️⃣2️⃣*
















_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._










.........Da kansa ya haɗa mata tea cikin cup, ya zuba mata Irish da soyayyiyar waina ƙwai a cikin plate, ya ɗora bread a kai bayan ya shafa mata jam a jikinsa. Kallonsa kawai take yanda yake yin komai cikin natsuwa, ta dunk'ule jikinta guri guda gaba-d'aya ta kasa sakewa. Ya ɗago ya kalle ta fuska a sake ya nuna mata cinyarsa tare yi mata alamar ta je ta zauna akai. Ta waro ido tare da ɗauke kanta kamar bata gane me yake nufi ba. Ya matso kusa da ita a hankali ya daga ta cak ya ɗora ta akan cinyar tasa. Ta fara mutsu_mutsu tare da ƙoƙarin sauka daga jikinsa, ya riƙe ta sosai tare da juyo da fuskarta ya zuba mata narkakkun idanunsa a cikin nata, ba shiri ta lumshe nata idon ƙirjinta ya fara bugun da ya saba. Ya shafi gashin girarta tare da ƙara gyara mata a jikinsa. Gaba-d'aya sai ta rikice ta fara ƙoƙarin yi masa kuka, ko da wasa ta ƙi buɗe idonta saboda tsoron kar su ido. A hankali ya cusa kansa a wuyanta yana shaƙar ni'imtaccen ƙamshin jikinta. 'Ya Allah, wannan bawan naka zai kashe ni da raina, wannan abun kunyar har ina?' Ta faɗi haka a ranta. Rawar da jikinta ya fara yi ne yasa ya ɗago da kansa daga jikinta, murya ƙasa ƙasa ya ce. "Ni fa bana son wannan tsoron da kunyar sun ishe ni haka." Ta tura masa baki tare da ɓata fuska. Ya ce. "Okay, I know how I treat you tsoro da kunyar su tafi." Ya karashe zancen tare da kai hannunsa bayanta ya fara jan zip ɗin rigarta ƙasa. Saboda dimauta bata san sanda ta ƙanƙame shi ba tare da sakin kuka, sosai ta rikice, al'amarin Ameen ya girmewa kwanyarta. Ya tsaya da abun da yake yi yana murmushi ya ja karan hancinta bai ce komai ba. Juyar da ita ya yi yana faɗin. "Let us eat first, sai mu fi samun full energy." Ta zame ta sauka daga jikinsa da sauri tare da ƙoƙarin tashi, a nufinta ta ruga da gudu ta koma ɗaki. Ya kama hannunta tare da mayar da ita ta zauna akan cinyarsa. Ya ɗora kansa akan kafaɗarta yana kallon gefen fuskarta ya ce. "Common, wai wannan abun da kike yi na mene ne? Wannan Ameen ɗin fa ba Yayanki ba ne Mijinki ne?" Ta marairaice fuska ta ce. "Ni dai dan Allah ka barni in zauna a ƙasa." Ya ce. "Yanzu a sama kike?" Ta yi shiru tana ƙara marairaice fuska, shi bai san me take ji a jikinta ba da zuciyarta idan ya taɓa amma yay ta nanik'ar ta. Ya kama hannayenta da suka sha jan ƙunshi yana kallo, a hankali ya kai hannun bakinsa ya yi kissing sannan ya ce. "I like this." Ita dai ji take kamar ta fasa ihu, kunyarsa take ji sosai kamar zata hallaka ta, amma shi ta ga kamar bai san da wata aba kunya ba. Ya ɗauko cup ɗin da ya haɗa tea ya kai bakinta, ba musu ta buɗe bakin ta fara sha saboda so take su yi su gama ya sake ta ta huta, ita kam baza ta iya da wannan abun kunyar ba. Tea ɗin har ya fara hucewa amma haka take sha saboda a ganinta sake ƙara haɗa wani ma sabon wastern time ne da ƙara yawan kasancewarsu tare. Shi ya ciyar da ita amma shi bai ci komai ba, kamar ta share sai kuma zuciyarta ta kasa haquri da hakan. Kanta a ƙasa ta ce. "Kai baka ci ba." Ya yi shiru kamar bai ji ta ba. Ta ɗan ɗago kanta ta ce. "Yaya baka ci abincin ba." Ya shafi lips ɗinta ya ce. "Kina son in ci ne?" Da sauri ta gyaɗa masa kai. Ya ce. "To bani in ci."Bata kuma magana ba ta janyo cup ta haɗa masa sabon tea sannan ta zuba masa komai na gurin a cikin plate. Ta zame daga jikinsa ta zauna a ƙasa, ta gyara zip ɗin rigarta da ya fara zuge mata. Ta janyo kayan zuwa gabansa. Ya tallafe fuskarsa da hannunsa yana kallon kayan break ɗin ya ce. "What is this?" Ta ce. "Ci zaka yi." Ya ce. "Sai dai ki bani." Ta rufe fuskarta da hannunta kamar wadda ta yi sab'o tana girgiza masa kai. Ya ce. "To ɗauke abinki daga gabana." Ta cire hannun kamar zata yi kuka ta ce. "Dan Allah Yaya ka ci , ni dai bazan iya baka ba." Bai ce komai ba ya janyo ta jikinsa sannan ya fara cin abincin. Sai ta ji daɗi a ranta har da sakin ajiyar zuciya. Tana jikinsa har ya gama sannan ta samu ya sake ta. Tattara kayan gurin ta yi ta kai kitchen ta tsaya wanke su. Kafin ta gama har ya shiga dakinsa ya d'auko laptop ya dawo falon yana lallatsawa. Data fito har ta fara murna zata sarara babu takurarsa tunda yana aiki, ta yi hanyar balcony zata shiga ɗakinta ta ji ya ce. "Come here." Ta ɓata fuska sosai kamar zata fashe da kuka, ta ƙarasa inda yake tana k'unk'uni a cikin ranta. Ya zaunar da ita a gefensa tare da kwantar da kanta akan kafaɗarsa ya cigaba da aikinsa. Ta ce. "Yaya Mama fa zan kira." Ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "Not now." Ta turo baki wanda ya zame mata jiki, yana jin ta sai mutsu_mutsu take, she is totally uncomfortable, bata da damar tashi ne kawai. Ya yi ɗan murmushi tare saka hannunsa ɗaya ya shiga shafa bayanta, a ransa yana faɗin dole ya yi maganin rashin sakin jikin nan nata da shi tare da cire mata kunya da tsoronsa soon.








Sai da aka kira Sallar Azhar ya ajiye system ɗin, lokacin har ta yi bacci a jikinsa. Kamar kar ya tashe ta amma dai ya tashe tan dan ta yi Sallah. Ta buɗe idonta kaɗan, ya shafi saman idon ya ce. "Lokacin Sallah ya yi, idan kin yi Sallar sai ki koma baccin." Ta gyaɗa masa kai kawai. Ya taɓa goshinta ya ce. "Ya jikin naki da kan?" Ta ce. "Sun yi sauƙi." Ya ce. "Allah ya ƙara sauƙi." Sannan ya kama hannunta suka miƙe dan yin alwala. Bata koma baccin ba bayan ta idar da sallar kamar yadda faɗa. Gyaran gidan ta shiga yi duk da babu wani datti a cikinsa, cikin 1 hour ta gyara ko ina, ta kunne burner ta saka turaren wuta ƙamshi ya bud'ad'e gidan. Ameen bai dawo ba har 2 ta wuce, hakan ya yi mata daɗi ba kaɗan ba, dan ita al'amarin sa ya daina bata mamaki sai tsoro, sai tambayar kanta take 'dama haka auren yake miji ya yi ta manne maka kamar wani cingum.' Wayarta ta ɗauko ta kunna data ta shiga WhatsApp.










Ko gama shigowa messages ba su yi ba ya buɗe ƙofa ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Ta amsa masa tare da ajiye wayar hannunta ta miƙe ta ce. "Sannu da zuwa." Ya ce. "Yawwa, ki shiga daki za'a shigo da kaya ne." Ta juyo ta nufi ɗakin. Slindern gas ne ya yi repiling sai kuma cartoons ɗin lemuka da ruwa wasu samari guda biyu suka shigo da su. Bayan sun tafi ya shiga ɗakinta ya tarar da ita a kwance. Ya tsaya a bakin gadon ya ce. "Baccin kenan?" Ta tashi zaune ta ce. "Yanzu zan yi, gyaran gida na tsaya yi." Ya miƙa mata hannunsa ya ce. "Taso mu je ki ga wani abu." Bata yi musu ba ta sakko ya kama hannun nata suka fita, suna fita falo ta ga babu wayarta a inda ta ajiye. Ta kalle shi ta ce. "Yaya wayata ban gani ba." Ya ce. "Ni na ɗauka, i want check something." Bata kuma magana ba suka shiga kitchen. Lemukan suka sassaka a cikin fridge sannan Ameen ya kunna shi ya fice. Ita kuma tsayawa ta yi tana ƙara ƙarewa kitchen ɗin kallo, ya yi mata kyau sosai bata gajiya da kallonsa, dama ita a rayuwarta tana k'aunar kitchen. Ta fita falon ta tarar da shi kwance akan doguwar kujera ya kunna TV. A hankali ta ce masa. "Su Aunty sun ce za su zo kuma har yanzu na ji shiru." Ya kalle ta ya ce. "So?" Ta ce. "Ka bani wayar in kira su in ji me ya tsayar da su, sannan in yi magana da Mama." Ya miƙa mata hannunsa, ba musu ta taho ta kama amma fa a tsorace take da shi. Ya zaunar da ita a gabansa bai ce komai ba. Ta ɓata fuska zata fara shagwab'arta suka ji ƙarar shigowar Mota gidan. Da murna ta ce. "Ga su nan ma insha Allah." Ya mintsine ta a hannu ya ce. "So kike su zo saboda in rabu da ke ko? Ai ba kwana zasu yi ba zasu tafi ne." Ta sosa inda ya mintsine tan tana cinno baki gaba, dalle mata bakin ya yi ta keɓe fuska zata fara sana'ar tata. Knocking ɗin ƙofa ne ya hana ta yin abun da ta yi niyya. Ta tashi da sauri cikin murna, yana kiran ta ma bata ji ba. Da Haneefah ta fara cin karo bayan ta buɗe ƙofar. Ta doka tsalle ta rungume ta. Aunty Sadiya dake bayanta ta ce. "To kayar da ita ki yi muku asarar babyn." Ta saki Haneefan tana murmushi ta ce. "Da kuwa Ya faruq ya yi ƙasa ƙasa da ni a garin nan." Haneefah dai bata ce komai ba sai bin ta da kallo take tana murmurshin munafurci. Ta basu hanya suka shige, sai a lokacin ta ga Hameedah da Aunty Hauwa da Matar Uncle Usman. Ta yi mamakin ganin Hameedah amma bata nuna ba. Ameen ya tashi zaune yana yi musu sannu da zuwa. Aunty Sadiya ta shiga tsokanarsa, ya yi murmushi kawai ya ƙi biye mata. Haneefah sai kunshe dariya take, ya harare ta sannan ya gaishe da su Aunty Hauwa, Hameedah ta gaishe shi ya amsa mata ba tare da ya kalle ta ba sannan

Please Login or Register in order to submit comment