Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bi ta da kallon tsana, tana juyowa suka haɗa ido da Ameen yana mata irin kallon d'azu. Sai ta hau borin kunya ta fara yamutsa fuska tana faɗin. "Baby cikina na damuna da ciwo." Ameen ya janyo ta jikinsa ya ce "Sorry, bari na kira Mama ko akwai maganin da za'a baki ya daina ciwon." Ta gyaɗa masa kai, tare ƙara shigewa jikinsa.








A falo Neehal ta zauna bayan ta fito, bata koma bedroom ba. Tana zaune a nan Ameen ya fito daga ɗakin. Ta kalli agogon dake falon ta ga goma na safe ta wuce, ta ce masa "Yaya me za'a girka for lunch?" Ya zauna a kujerar dake fuskantar ta, ya ce. "Tun yanzu?" Ta ce "12 za ni gurin aiki ne, shi yasa." Ya ce "Ki dafa ko me kike so." Ta ce "Ka faɗa dai, kar in dafa abin da baka ci, ko kuma wanda Aunty Hafsah bata ci." Ya ce "Ita ai bata iya cin abinci, for me kuma ko me kika dafa i will eat." Ta ce "Ko tuwo ne?" Ya harare ta. Ta tashi tana dariya ta sauka ƙasa, ya bi ta da kallo. A falon ƙasa ta samu ƴan'mata guda biyu masu aikin gidan, ta shiga kitchen ba tare data musu magana ba. Kamar yadda ta tsokani Ameen tuwon ta ɗaura, duk da itama bata wani ci sosai amma kawai sai ta ji shi take son yi. Tuwon semo ta yi, miyar zogale tare da taimakon ƴan'mata nan, wanda bayan shigowar ta kitchen ba jimawa suka biyo ta wai za su taya ta aikin, ta ce musu to bismillah. Suna aikin suna mata hira, dan surutu ne da su ba kaɗan ba, farkon hirar kyawunta suka fara yabawa, har suna cewa sun kasa gano waya fi kyau tsakanin ita da Ameen. Yanda suke acting a hirar sai suke bata nishad'i, ta dinga murmushi, wani abun kuwa idan sukay dole sai ta dara, because they are so commedians. Sai ta ji daɗi a ranta ta samu masu ɗebe mata kewa a gidan, kuma ga su yara ne ba za su wuce 18 years ba. Ta tambaye su sunayensu suka sanar mata, Harira da Saude. Ba ta gama girkin ba sai kusan 12, saboda da ɗan yawa ta yi saboda ta san za'a iya yin baƙi ƴan zuwa dubiya, ta kwasawa Ameen nasa daban a cikin ƙaramar warmer, ta ce wa su Saude idan ya zo neman abincinsa gashi nan. Ta ɗibi kaɗan ta ci saboda saurin da take yi ta tafi gurin aiki dan ta yi late, bayan ta gama ci ta hau sama ta shirya cikin sauri ta fito ta shiga ɗakin Hafsah ta sanar mata zata tafi, kamar an mata dole ta ce ta je driver ya kai ta. Direban gidan ne ya kai ta gurin aiki kamar yadda Hafsan ta faɗa, ba ta ga Ameen ba kuma bata ga Motarsa a parking space ba, hakan ya tabbatar mata da baya gidan kenan.










Ƙarfe Shida na yamma ta tashi daga aiki, tun kafin ta fito daga office aka aiko an zo ɗaukarta. Bayan ta fito ta ga direban gidan Ameen ne, dama da ya kawo ta ya tambaye ta ƙarfe nawa zata ta tashi ta sanar masa. Bayan ta koma gidan ta shige ɗaki bata fito ba har akay Magriba, saboda baƙin da ta ga an yi. Tana zaune akan sallaya suna chat da Sadik aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, ta d'ago tana dubansa tare da amsa masa sallmar da ya yi. Ta ajiye wayar ta ce "Sannu da zuwa Yaya." Bai amsa mata ba ya zauna a kusa da ita. Ta ɗan lumshe ido ta buɗe saboda k'amshinsa da ya cika mata hanci. Ta yi ƙasa da kanta saboda yanda ta ga yana kallon ta, lokuta da dama tana mamakin yanda yake yawan kallon ta, ta kan tambayi kanta ko kallon na mene ne? Ganin ba shi da niyyar magana ta ce "Mun yi waya da Mama ta ce, idan tana free za su zo anjima ita da Daddy." Ya ce "Allah ya kai mu." Sai kuma ya ɓata fuska ya ce "Dama zuwa kika yi dan kina bari na da yunwa?" Ta masa kallon mamaki ta ce "Yunwa kuma Yaya?" Ya ce "Eh." Ta yi murmushi dan gano bakin zaren, ta ce. "Amma dai ka ci wani abun?" Ya girgiza mata kai, ta ɓata fuska cikin rashin jin daɗi ta ce, "Da ka ci tuwon Yaya ko kaɗan ne, ya yi daɗi fa, nima na ci, amma shine ka zauna da yunwa." Ya ce "Ai baki so in ci ba dama." Ta ce "To yanzu bari in tashi in dafa maka wani abun ka ci, me kake so in dafa maka Yayana?" Ya ce "No ki huta I knew you are tied." Ta ce "Zan iya fa Yaya, ai na huta." Ya ce "No ki bar shi, mu je dai ki raka ni unguwa." Ta ce "Toh Yaya."












Ya miƙe ya fita, ta tashi ta cire hijabin jikinta ta ninke, sannan ta ɗauko mayafin abayar dake jikinta ta yane kanta da shi, ta fesawa jikinta turare kaɗan sannan ta ɗauki wayoyinta ta bi bayan shi. A falo ta zauna jiran shi, ba jimawa ya fito daga ɗakinsa inda Hafsat take a yanzu. Da ido yay mata alamar ta tashi su tafi, ba tare ta ce komai ba ta miƙe ta bi shi a baya. A falo ta tarar da su Harira suna kallo, su kai musu a dawo lafiya. Restaurant suka je ya siyo musu abinci, daga nan kuma ya biya ya siyo mata ice-cream da choculate da ya san tana matuƙar son su. A hanyar dawowa ta shagwab'e fuska ta ce "Yaya ka kai ni in ga Mama, sai mu dawo." Ba tare da ya dube ta ba ya ce "Ba ta ce zasu zo ba?" Ta ce "Ai na san da ƙyar za su zo, dama haka ta ce sai ta samu time." Bai kuma magana ba bai kuma kaita gidan ba, gidansa suka koma. Bayan an yi Sallar isha'i ta ci abinci sai ta sauko ƙasa gurin su Harira dan su yi hira. Saude ta ce "Mai kyau, d'azu na gan ki a talabijin." Neehal ta yi murmushi ta ce "Ni kuma? ba ni ba ce gaskiya, sai dai mai kama da ni." Saude ta ce "Alkur'an ke ce, da na je kaiwa Hajiya kifin data ce in sake d'umama mata ne na ga mai_gidan yana kallo, kuma har ɗan tsayawa na yi na ga kayan da kika fita da su ne a jikin wadda na gani." Neehal ta yi ƴar dariya saboda yanda Sauden ta yi maganar ta ce "Ƴan biyu ce ni ai, to ɗayar kika gani ba ni ba." Saude ta ce "Tab' amma kuna kama sosai, har fa yanda kike yi da idonki haka take yi." Neehal ta ce "Ya nake da idon?" Harira ta gyara zama ta ce "Ni zan gwada miki." Sai ta wani lumshe ido ta buɗe tare da keɓe baki ita a dole iyayi take tana gwada yanda Neehal take magana. Neehal ta yi dariya sosai wadda ta ƙara fito da kyawun fuskarta, kumatunta suka lotsa kamar an cire naman gurin. Saude ta taɓa dai_dai gurin cikin santi ta ce "Ke kam ki godewa Allah, ya baki kyau, wannan abun yana ban sha'awa, tun ɗazu in kina magana shi kawai nake kallo." Neehal ta ce "Allah ya baki miji mai irinsa, sai ki yi ta kallon sa." Saude ta washe baki ta ce "Allah ya amsa bakin ki mai kyau." Suna cikin hirar su mai daɗi dake sanya Neehal nishad'i Ameen ya shigo falon, sai ta ga su Harira cikin sauri sun tashi sun shige ɗakin da suke bayan sun masa sannu da zuwa. Neehal ta bi su da kallo, sannan ta mayar da idonta kan Ameen dake kallon ta hannunsa riƙe da leda, ta ɗan ɓata fuska ta ce "Sannu da zuwa." Ya ce "Yawwa." Tare da shiga kitchen ya ajiye ledar hannunsa, ya dawo falon ya ce wa Neehal. "Miemerh Please ki shiga kitchen ki soyawa Hafsah kajin can." Neehal ta ɓata fuska amma bata ce komai ba ta tashi ta shiga kitchen ɗin dan babu musu a tsakanin ta da shi. Ya bi bayan ta zuwa kitchen ɗin, ta juyo ta kalle shi, ya nuna mata inda kajin suke. Ta ɗauko tana turo baki gaba ta juye su a abu, a yayyanke suke a wanke tass. Ta ƙara ɗauraye su, ta ɗauko tukunyar da zata cinye su ta ɗauraye ta juye su a ciki, sannan ta saka musu magi da spices da ɗan yaji ta kunna gas ta ɗora. Duk abun da take yana tsaye yana kallon ta, ya jingina da ƙofar kitchen ɗin. Bayan sun mata yanda take so ta sauke ta tsame su ta zuba a cikin colander, sannan ta tsiyayo mai a jarka ta zuba a kasko ta ɗora akan gas ɗin. Ta ƙara juyowa ta ga har lokacin yana kitchen ɗin, ta turo baki ta cigaba da abun da take. Har ta fara soyawa bai fita ba, ita kuma duk ta takura kamar ta ce masa ya fita. Sai da ya gaji dan kansa ya fita. Tana soya na ƙarshe ya dawo kitchen ɗin, naman ya yi irin ƙarar nan da yake yi a cikin mai, har man ya ɗan fallatso mata a hannu. Ta ɗan ja baya tare da yarfe hannun, ya matso kusa da ita da sauri ya kama hannun yana dubawa. Ta shagwab'e fuska kamar zata yi kuka. Murya ƙasa_ƙasa ya ce "Sorry dear, don't cry." Ta kalli fuskarsa tana turo baki gaba tare da gyaɗa masa kai, Idanunsa suna kan hannunta hakan yasa ta ƙurawa fuskarsa ido kamar mai neman wani muhimmin abu a fuskar, sai da ya d'ago sannan ta yi saurin lumshe idonta tare da sakin ajiyar zuciya a hankali. Ta matsa daga kusa da shi tare da zare hannunta daga nasa. Ya ce "Zaki iya ƙarasa suyar kuwa?" Ta d'aga masa kai alamar eh. Ya juya zai fita cikin siririyar murya ta ce "Yayah.!" Ya juyo ya kalle ta ba tare da ya amsa ba. Ta yi shiru dan ta kasa faɗar abun da yake ranta, ba yabo ba fallasa ya ce "What happened?" Ta ce "Nothing." Yay mata wani kallo sannan ya juya ya fice. Ta sauke numfashi tana jin zuciyarta na mata wari irin lugude, wani b'arin na zuciyar kuma mamakin Ameen take, yanda yake mata magana babu faɗa bare haɗe rai, ko dan ta zo gidansa ne? Jiki a sanyaye ta kwashe sauran naman da ya fara k'onewa. Sai da ta kimtsa kitchen ɗin sannan ta fice. Tana komawa ɗaki ta tarar da missed call ɗin Mama da Ahmad. Mama ta fara kira, tana ɗauka ta ce mata. "Shine ba ku zo ba Mama?" Mama ta ce "A gajiye Dad ya dawo ne shi yasa, sai gobe Insha Allah, ina kika shiga nay ta kiran ki?" Ta ce "Ina ƙasa, wayar kuma tana sama a ɗaki." Mama ta ce "Ya jikin Hafsan?" Ta ce "Da sauƙi." Mama ta ce "Babu matsalar komai dai?" Ta ce "Nothing Mama, ina Dad?" Mama ta ce "Ya kwanta bacci, saboda gajiyar dake damun sa, shi yasa ni kiran ki ɗazu ai, kuma baki d'aga ba, yanzu kuma ya yi bacci." Neehal ta ce "Ki gaishe shi idan ya tashi, har na fara kewarku Mama." Ta ƙarashe maganar cikin shagwab'a. Mama ta ce "Rigimarki da yawa take Daughter, yau ma fa kin gan mu." Ta ɓata fuska ta ce "Ni dai dan Allah ku zo gobe in gan ku." Mama ta ce "Allah ya kai mu goben lafiya, daga haka suka yi sallama ta katse wayar. Ahmad ta kira, kamar mai jiran kiran ringing ɗaya ya katse ya kira ta. "Princesss.!" Ya kira ta cikin shauƙi after she picked, ta ce "Uhm, Uncle ina yini?" Ya ce "Ga shi nan, babu daɗi tunda yau throughout ban ji muryarki ba." Ta ce "To yanzu ai ka ji ai, sai ka ji daɗin." Ya yi murmushi mai sauti ya ce "Ni da jin daɗi Baby ai sai ranar da aka kawo mun ke gidana a matsayin mata, na san zan yi farincikin da ban taɓa yin irinsa ba a rayuwata Princess, na san a ranar i war haka masu kawo mun ke sun tafi, sai mu kaɗai a gidanmu, muna making love." Ta rufe fuska kamar yana gabanta cikin jin kunya, ya ce "Princess ban san irin son da nake miki ba, kuma na san duk bayanin shi da zan miki baza ki gane ba, amma da zarar kin zama tawa, I know you will understand more." Ta sauke numfashi ba ta ce komai ba, Ahmad da Sadik suna ɗaure ta da jijiyoyin jikinta, ga abun da yake ƙara bata haushi idan tana tare da kowannen su Heart ɗinta shi kaɗai take tuna mata, ta rasa gane wa take so da k'auna a cikin su, zuciyarta ta kasa tantance mata wanda ya kamata ta zab'a a matsayin abokin rayuwarta. 'Na barwa Allah zaɓi, Allah ka zaɓan mafi Alkhairi.' Ta faɗi haka a cikin ranta. Ahmad ya cigaba da yi mata hira mai daɗi cikin iya tsara kalamai masu kwantar da zuciya. Har bacci ya fara cin ƙarfin ta, saboda gajiyar dake tattare da ita. Jin hakan yasa yay mata sai da safe ya katse wayar, tashi ta yi dak'yar tana lumlumshe idanuwa ta rage kayan jikinta sannan ta kashe hasken ɗakin, ta kunna fitilar gado. Har ta kwanta ta ƙara tashi ta kunna light ɗin ɗakin sannan ta shiga toilet ta yi fitsarin da ya matse ta, bayan ta fito ta kulle ƙofar ɗakin tare da kashe light, sannan ta hau kan gadon ta ware bargon dake ninke a gefen gadon daga gurin bango ta lullub'e jikinta. Da ƙyar ta iya yin addu'ar kwanciya bacci, saboda baccin dake cin ta.










Cikin dare ta yi juyi, haka Allah ya halicce ta indai zata yi juyi a bacci sai ta ɗan farka, kamar an ce ta buɗe ido sai ta ga kamar an turo ƙofar ɗakin an shigo, ta ware idanunta dan tabbatarwa gabanta na dokawa a million. kamar a mafarki ta ga ana nufo gadon ta ɗan hasken bedside lamp. Ta ƙara waro idonta ganin dagaske fa ita ake tunkarowa har anzo bakin gadon, ta yunƙura ta tashi zaune cikin rawar jiki tare da ware baki da nufin ta ƙwala ƙara, amma sai ta ji ana fesa mata wani abu a fuska kamar shantos, ta fara jujjuya kai a ƙoƙarin ta na nemo iskar Ubangiji ta shak'a ba wannan abun mai wari da ake fesa mata ba. Cikin sakanni ƙalilan hankalinta ya gushe daga jikinta, daga nan bata ƙara sanin inda kanta yake ba.........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*5️⃣6️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*














...........Alarm ɗin da ta saita wayarta da shi wanda yake tashin ta idan ta koma bacci bayan sallar asuba shi ya tashe ta ƙarfe 6:30 am. Ta ja gwauron numfashi sannan a hankali ta buɗe idonta da sukai mata nauyi, ɗakin data ke ta fara bi da kallo, a hankali ƙwaƙwalwarta ta fara tariyo mata inda take da kuma abun da ya faru a farkawar da tay daren jiya. Ta yunƙura ta tashi zaune da sauri cikin matuƙar tsoro zuciyarta na mata wani irin bugu kamar zata faso ƙirjinta ta fito. Ta kalli ƙofar ɗakin ta ga babu alamar an buɗe ta a rufe take ruf, ta dawo da idanta kan gadon da take ta kalli gefen ta, shima babu alamar an yi wani abu a gurin. Ta yaye bargon dake lullub'e a jikinta da sauri ta shiga duba jikinta, amma babu alamar ko hannu an ɗora a jikin nata. Ta miƙe cikin rawar jiki ta sauko daga kan gadon ta yi taku uku ta ji ta rass, babu alamar wani ciwo a jikinta. Dafe kanta ta yi da hannunta a fili ta ce "Ko mafarki na yi ne?" Ta ja numfashi mai ƙarfi hakan yasa ta ji warin abun da aka fesa mata jiya ta cikin mak'oshinta. Ta kai hannu ta shafa fuskarta sai ta ji wani abu mai maik'o a fuskar kamar ta shafa mai. Ta goga hannunta sosai a fuskar sannan ta kai hannun hancinta ta shinshina. Tsoron ta ne ya ƙaru jin warin abun da aka shak'a mata, hakan ya tabbatar mata da ba mafarki ta yi ba, da gaske wani ko wata ya shigo ɗakin nan jiya, kuma ga dukkan alamu cutar da ita ake son yi tunda gashi an fesa mata abun da ya gusar mata da hankali. 'To waye? Kuma me yake nema a gurin ta?' Tsoron ta ne ya ƙaru sosai kamar a yanzu ne aka shigo ɗakin, ta nufi ƙofa da sauri cikin kyarmar jiki ta buɗe ta fita falo da gudu a gigice. Ameen yana zaune akan carpet yana karatun Alqur'ani a hankali, ya ji an buɗe ƙofa da ƙarfi, ya juya da sauri idanunsa suka sauka a kanta. Ta ƙaraso inda yake da gudu ta faɗa jikinsa ta baya tare da fashewa da kuka. A ruɗe yake tambayar ta me ya faru ganin gaba-ɗayanta a firgice take. Ta kasa magana sai ƙofar ɗakin kawai take nuna masa. Ya matsar da Alkur'anin gaban sa gefe, ya dawo da ita gaban sa, tana ƙoƙarin ƙara ruk'unk'ume shi ya riƙe ta, cikin damuwa ya ce "Miemerh! Mai ya faru? Talk to me please." Cikin sheshshek'a ta ce "Wani ne ya shigo ina bacci, ya fesa mun wani abu a fuskata, dan Allah Yaya ka mayar da ni gurin Mama kar ya ƙara dawowa." Ta ƙarashe zancen tare da faɗawa ƙirjinsa ta k'ank'ame shi, ilahirin jikinta rawa yake. Fuskantar da ya yi a tsorace take sosai, sai ya saka hannunsa ya zagaye bayan ta da su, a hankali ya shiga karanto addu'a yana tofa mata, dan ya fi zaton mafarki ta yi wanda ya firgita ta. A hankali ta shiga sauke ajiyar zuciya, rawar da jikinta yake ta ragu. Jin haka yasa ya d'ago ta daga jikinsa, ta buɗe idonta dake shatatar da hawaye ta ce "Ni dai ka kaini gurin Mama dan Allah Yaya." Yana gyara mata gashin kanta da ya barbazo saman fuskarta ya ce "Relax Miemerh, babu komai fa, may be mafarki kika yi, dan babu wanda zai iya shigowa cikin gidan nan, saboda gaba-d'aya doors ɗin a rufe suke, ni da kaina na rurrufe su. Kuma babu ta yanda za'a iya haurowa a shigo, bare na ce ko haurowa akay." Cikin kuka ta ce "Wallahi Yaya ba mafarki na yi ba gaske ne." Ta bashi labarin duk abun da ya faru, cikin tashin hankali yake kallon fuskarta. Ta kai hannunsa kan fuskarta_ta, ta ce "Ka taɓa ka ji Yaya zaka ji wani abu kamar mai yana wani irin wari, kuma ni ban shafa komai ba kafin na kwanta." Bai ce komai ba ya sake ta ya miƙe ya nufi ɗakin, ta miƙe itama da sauri ta bi bayan shi. Dudduba ɗakin ya yi gami da toilet amma bai ga kowa ba, bai kuma ga wata alamar an shigo ba, ya tsaya yana sauke numfashi, shi kansa hankalin shi ya tashi ba kaɗan ba, saboda tabbatarwar da ya yi an shigo ɗin ba ƙarya ta yi ba, ya gane hakan ne ta ƙofar bantlation ɗin ɗakin da ya tura ya ji ta a buɗe, kuma shi ya san a rufe suke barin ta, tunda suka zo gidan ma zai iya k'irga time ɗin da aka buɗe ta. Neehal kam duk inda ya ɗora ƙafarsa nan take ɗora ta_ta, hannunta riƙe da nasa tana faman tsiyayar hawaye. Ya kamo fuskarta yana kallon idonta cikin tashin hankali ya ce "Kuma baa ki gane kowa ne ya shigo ba?" Ta girgiza kai ta ce "Ban gane ba Yaya, ai time ɗin ɗakin babu haske sosai, kuma cikin bacci ne idona bai gama washewa ba, da ƙyar ma na iya tashi zaune." Ya saki fuskarta ya ɗan lumshe idonsa a hankali tare ciza lip ɗinsa, tsawon wasu sakanni sannan ya buɗe idon ya ce "Kin yi Sallah?" Ta girgiza masa kai alamar a'a. Ya ce "Je ki yi." Ta ce "Toh Yaya karka fita dan Allah, ka jira ni in fito tsoro nake ji." Ya gyaɗa mata kai kawai sannan ya koma bakin gado ya zauna tare da tallafe kansa da hannayensa guda biyu ya faɗa duniyar tunani. Harta fito ta zira abayar data cire jiya ta zira hijabi ta tayar da Sallah bai yi ƙwaƙkwaran motsi ba. Sai bayan ta idar ya tashi ya fita ba tare ya ce komai ba, ta bi bayan shi da sauri dan gani take kamar tana kadaicewa za'a kuma zuwar mata. Dawnstairs ya sauka ya fice daga part ɗin gaba-ɗaya. Ganin su Harirah suna kaikawo a falon ƙasa sai ta zauna a nan dan jiran shi. Wata irin kalasa take ji a jikinta, ga wani bacci_bacci dake fizgar ta, da alama abun da aka shak'a mata har yanzu bai bar ta ba, amma tsoro da fargaba sun hana baccin ɗaukar ta. Ameen ya jima a wajen kafin ya dawo, dan sai wajen 8 ya dawo. Neehal ta takura masa da kukan ita dai ya mayar da ita gida gurin Mamanta, dole ba dan yaso ba ya mayar da itan, ko kayanta bata tsaya ɗauka ba balle su yi sallama da Hafsah, dan ko saman ƙin komawa ta yi. Cikin mamaki ganin su a wannan lokacin Mama ta tarb'e su, bayan sun zauna Neehal ta mata bayanin abun da ya faru cikin kuka. Hankalin Mama fa ya tashi ba kaɗan ba, ta je ta taso Daddy ta faɗa masa abun da yake faru. Cikin damuwa ya ƙaraso part ɗin Mama ya ƙara tambayar Neehal ƙarin bayani, ta faɗa masa. Daddy ya ce, ta kwantar da hankalinta Insha Allahu koma waye Allah zai toni asirinsa. Ameen kuwa ya tabbatarwa Mama da Daddy cewar, akwai binciken da zai yi koma mene ne zai gano da yardar Allah. Mama kuwa sai da ta caje ƴarta ciki da waje ta ga babu abun da akai mata sannan hankalinta ya ɗan kwanta. A daren ranar Neehal ƙin kwanciya ta yi a ɗakinta ita kaɗai, saboda a tsorace take, sai a ɗakin Mama suka kwana tare da Maman. Washegari da safe Ameen ya kawo mata kayanta, tare da saƙon Hafsah na ta tafi babu ko sallama, dan Ameen bai sanar mata abun da ya faru ba.








*AFTER FOUR MONTHS*








Neehal sun koma school inda suka ɗora karatunsu na final year first semester, 8 weeks da suka wuce, and now suna shirye_shiryen fara first semester level Four exam. A ɓangaren soyayyarta da Ahmad da Sadik kuwa kowa yana nan yana zuba mata gwanintar sa, ita kuma ta dage da addu'ar neman zaɓin Allah. Every weekend sai Ahmad ya zo Kano ya gan ta, sai da randa aka samu wani akasi ne ba ya zuwa, jiki da jini sai Allah. wani Ikon Allah ba su taɓa haɗuwa da Sadik ba, sai dai sun haɗu da Ameen ba iyaka, dan shi kullum sai ya zo gidan da daddare. Har wata rana ya kasa haquri ya tambayi Mama, wai me Ahmad yake zuwa yi gidan ne, A tak'aice Mama ta ce masa zumuncin Allah yake zuwa. Kafin Neehal su koma school ta je Gombe ta kwanar musu biyu, haka ma ta je Abuja gidan Yayan Dad da gidansu su Hameedah, har gidan su Ahmad ta je. Ta ga karamci da k'auna a gurin ahalin Ahmad, twins suka dinga murna Aunty ta zo gidan su. A ɓangaren Sadik kuwa, bayan mahaifinsa ya gudanar da binciken da ya ce zai yi ya zo ya sanar musu cewar gaskiya ne abun da Umma take faɗa akan Neehal. Hajiyarsu da Kawu suka ce dole sai dai Sadik ya rabu da Neehal ya nemi wata yarinyar ya aura. Shi kuma ya ce ba zai

Please Login or Register in order to submit comment