Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata burki ta ci mata mutunci, ta kuma hana Abba ɗaukar hukunci akan Sadik ko Maamah. Ita kuwa Maamah kullum cikin tausar Sadik take tana ba shi baki akan Abinda Umma take masa, duk da abun na damunsa amma haka yake haquri ba ya nuna ɓacin ransa saboda nasihar mahaifiyarsa. Bashir ne ma sarkin zuciya wataran yake ƙoƙarin tankawa Umma idan ta ƙure shi akan abun da takewa Mahaifiyarsa da ɗan'uwansa, duk da shi ɗinma tana masa ba tsira ya yi ba, amma shi tana ɗan shayin shi ganin yaron a tsaye yake, Sadik kuwa haqurin mahaifiyarsa ya ɗauko shi yasa tafi raina shi kuma tafi tsanar shi.








Misalin ƙarfe 11 na dare Maamah ta kwankwasa masa ƙofa, yana zaune gaban laptop, ya d'ago ya dubi ƙofa tare da faɗin "Come in." Maamah ta shiga bakinta ɗauke da Sallama, ya amsa mata ya ƙara da faɗin "Au Maamah ke ce, na ɗauka ma Basheer ne." Maamah tana murmushi ta ce "Ni ce Son ya aiki?" Ya ce "Alhamdulillah gashi muna ta fama." Maamah ta ce "Allah ya taimaka ya bada sa'a." Ya amsa da "Ameen." Cikin ladabi. Maamah ta dube shi ta ce "Daga ina kake ne Sadik?" Sunkuyar da kanshi ya yi yana murmushi ya ɗan sosa kai ya ce "Gidan su Neehal." (Da yake Maamah ta san Sadik yana zuwa gurin Neehal.) Maamah ta yi murmushi ta ce "Ka baro su lafiya?" Ya ce "Eh, tana gaishe ki ita da Mama." Ta ce "Ina amsawa." Ta miƙe tay masa sai da safe sannan ta fice zuciyarta fal da farin ciki, kullum addu'arta Allah ya bawa Sadik mace ta gari yay auransa ko ya huta da addabar Umma da kuma faɗan mahaifinsa, tunda ba su isa dai sun bi shi gidansa sun masa ba.












Washegari Mama ta koma bakin aiki, Neehal kuma gidansu Haneefah ta je dan yi musu ban gajiya ita da Twins ɗinta. Bayan sati ɗaya, Neehal ta koma gurin aiki, kuma har yanzu babu wanda ya kira akan su Afrah. Kullum Mama cikin saka ran kira take amma sai ta ji shiru, abun yana ɗaure mata kai sosai, dan yanda aka baza hotunan su Afrah a gidajen Televisions ya ci ace wani nasu ya gani, kuma kullum sai an yi cikiyar iyayensu a gidajen rediyo da Talabijin. Yau Juma'a Neehal aikin safe ta yi, 12pm da mintuna ta dawo gida, kasancewar Ran Monday za su yi resuming School Mama ta ce ta shirya ta je gidan Ameen, kar ta koma School ta zo bata samu damar zuwa ba, tunda every weekend tana gurin aiki, Monday to Friday kuma tana school. Ameen ɗin kuma yana ta yiwa Mama mitar ta hana Neehal zuwa gidansa. Neehal murna kamar ta kashe ta dan ba ƙaramin kewar Yayan nata ta yi ba, dan tunda yay aure ko waya ba su taɓa yi ba, kuma kusan kullum sai ya zo amma ba sa haɗuwa, duk time ɗin da zai zo tana gurin aiki. Cikin Sauri ta shirya Twins ɗinta itama ta shirya, ana sakkowa daga masallaci Driver ya tafi kai su, dan ita ba ta san gidan ba, duk da tana jin mararta na mata ciwo kaɗan_kaɗan amma ta daure, dan tana faɗa Mama cewa za ta yi ta fasa zuwan wani lokacin ta je, ita kuwa zuciyarta cike take da kewar Yayan nata............✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:44] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_












*2️⃣4️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*












...........Direct gida Ameen ya nufa da ita, domin ya san duk taimakon da za a bata a asibiti Mama za ta bata. Mama tana zaune a falo tana azkar ɗin yamma ta ga Ameen ya shigo mata da ƴa a hannu, a ruɗe a tashi tana dubansa ta ce "Al'ameen me ya same ta?" Sai da ya kwantar da Neehal a kan kujera sannan ya ce "Mama ciwon cikinta ne ya tashi." Mama ta ƙarasa inda take tana mata sannu, Neehal dai hawaye kawai take. Mama ta ce Ameen ya kai mata ita sama bari ta haɗa allura ta mata, insha Allah ciwon zai lafa mata yanzu.






Bayan 10 minutes Neehal har ta samu bacci saboda allurar da Mama ta mata, Mama dake zaune a gefen ta ta sauke ajiyar zuciya cikin tausawa Neehal ɗin, gyara mata kwanciya ta yi daga ruf da cikin da ta yi sannan ta fice. Ameen yana falo tare da Twins har time bai tafi ba. Ameen ya dubi Mama ya ce "Ya jikin nata?" Mama ta ce "Alhamdulillah ta samu ya lafa mata har bacci ya ɗauke ta, dama haka ciwon nata yake kamar aljanu, lokaci ɗaya zai zo amma tana shan magani ko aka mata allura zata ji sauƙin shi 70%." Jinjina kansa ya yi kawai, a ransa yana mamakin wannan ciwon nata da baya jin magani, dan idan bai manta ba kusan 10 years kenan Neehal take fama da shi. Sun ɗan taɓa hira da Mama akan rashin bayyanar wanda ya san su twins har yau, sannan yay wa Mama Sallama ya tafi. Ko da ya koma gida Hafsah bata nuna masa komai na ɓacin rai ba, sai ma tambayarsa jikin Neehal da ta yi. Washegari da Neehal ta tashi lafiya k'alau ta tashi, sai dai ɗaurewar ciki kawai wanda duk lokacin period ɗinta haka yake mata, sai ta gama take jin ta normal.












*ABUJA*










Tun ranar da aka ba da cikiyar su Afrah misalin ƙarfe goma 12 na rana, budurwar nan ce zaune a falon gidansu tana kallon ASTV, 12 na yi aka fara labaran rana. Hankalinta ba ya kan TV'n dan bata damu da kallon labarai ba, kamar an ce ta d'ago idanunta suka sauka a kan hotunan twins ana cikiyar iyayensu. Wata muguwar zabura ta yi gabanta na tsananta bugu, ba ta san sanda ta cillar da wayar hannunta ba a matuƙar razane cikin ƙaraji ta ce "What?" Mahaifiyarta ce ta fito daga bedroom tana dubanta da kyau ta ce " *Safeenah*! Ke da waye na ji kamar kina ƙara?" Tattaro nutsuwarta ta yi ta lalubi remote ta kashe TV dan kar mahaifiyartata ta ga cikiyar su Afrah da ake, ta sunkuya ƙasa ta ɗauki wayarta sannan ta dubi Mahaifiyartata ta ce "Ba komai Momma." Daga haka ta miƙe ta shige ɗakinta gumi na karyo mata ta ko ina a jikinta. Tab'e baki Momma ta yi ta wuce kitchen. Wani narkeken ashar Safeenah ta danna ta fara zarya a ɗakin a fili take faɗin "Lallai Gaye ya ha'ince ni, amma wallahi sai ya yi dana sanin cin amanata da ya yi." Ganin surutu ba mafita ba ne a gareta yasa ta ɗauki wayarta data cillar akan gado ta lalubo Numbern Aminiyarta kuma abokiyar shawararta. Bugu ɗaya ta ɗauka cikin tsananin tashin hankali Safeenah ta fara mata magana. "Na shiga uku Saudart, Gaye ya cuce ni ya ha'ince ni ashe Yaran nan be kashe su ba yar da su ya yi." "Ke wa ya faɗa miki haka?" Saudat ta tambaye cikin tarar numfashi. Safeenah na kuka ta ce, "Gashi nan na gani ana cikiyarsu a gidan TV an tsince su a Kano, yanzu ya zan yi ƙawata dan Allah ki ba ni shawara, ina tsoron kar asirina ya tonu." Ta ƙarashe zancen tamkar Numfashinta zai bar jikinta saboda tashin hankali. Saudat ta ce "Kin ga ƙawata ki kwantar da hankalinki, in dai ina raye ba zan bari hawayenki ya zuba ba, ki bani nan da zuwa yamma zaki sha mamaki, Gaye kuma zamu haɗu da shi zai san mu ya ha'inta." Safeenah zata yi magana ta ji wayar ta katse, zama ta yi a ƙasa dab'as tare da dafe kanta cikin rashin sanin abun yi. Ta san Saudat shu'umar kanta ce, yarinya ce mai buɗaɗɗan ido, ga shegen bin bokayen tsiya, a makarantar ABU Zaria suka haɗu da Safeenah har suka zama abokan juna. Ita Saudat ƴar cikin garin Zaria ce, ita ta bawa Safeenah shawarar tasa a sace su Afrah a kashe su, ita kuma ta haɗa ta da su Gaye sukai mata aikin. Yinin ranar cikin fargaba da tsoro Safeenah ta wuni, har wata yar ƙaramar rama ta yi, kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin firgici. Kamar yadda Saudat ta mata alƙawari da yamma ta kirata ta shaida mata ta je gurin wani boka ya mata aiki akan ko da mutum ya ga cikiyar su Afrah a rufe bakinsa ya kasa magana akai, kuma ta tabbatar mata aikin bokan tamkar yankan wuk'a yake. Wannan magana ta Saudat ita ta sanyaya wa Safeenah rai, domin kuwa ta tabbatar aikinsu ya ci tunda gashi har an fi sati amma babu wanda ya yi magana akan ya ga cikiyarsu Afrah da ake ta yi, kuma inda an gani za ta ji labari tunda gidansu ɗaya da Kakarsu Afrah ta wajen uwa, Safeenah ƙanwar mahaifiyar Su Afrah ce ubansu ɗaya. (Tsafi gaskiyar mai shi, Allah ka tsare mana imaninmu, Ameen ya Allah.) Su kam gidansu Mahaifin su Afrah ba su da nutsuwar wani kallon TV, kodayaushe suna zaryar asibiti hakan ya sa ba su ga cikiyar da ake ta yi ba. A ɓangaren su Kakarsu Afrah ta wajen uwa ma haka ne, tashin hankali bai barsu damar wani kallon TV ko sauraren Radio ita ƴaƴanta ba, hakan ya sa suma ba su ga cikiyar ko sun ji ta ba.










Ranar Laraba Neehal ta dawo daga school da yamma ta tarar da Aunty Sadiya wadda zuwanta kenan gidan daga wurin aiki ta biyo ta gidan. Neehal ta rungume ta tana faɗin "Auntyna oyoyo." Aunty Sadiya na murmushi ta ce "Oyoyo my Daughter, Ya school?" Neehal ta ce "Alhamdulillah, sai yau ma ni na koma." Aunty Sadiya ta ce "Allah ya taimaka, saura semester uku ku gama ko?" Neehal ta ce "Insha Allah." Mama ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da ruwa da glass cup, ta ajiye a gaban Aunty Sadiya, Aunty Sadiya ta ɗauki ruwan tana faɗin "Sannu Yaya, kamar wata baquwa sai kin kawo mun drinks." Mama ta ce "Ai na ga daga gurin aiki kike, kuma yanayinki ya nuna kin gaji." Aunty Sadiya ta ce "Hmmm bari kawai Yaya, yau tun 7 na fita office sai yanzu na samu kaina, case ɗin wannan Yarinyar da na ce miki an mata fyaɗe ne har yanzu ya ƙi ƙarewa, so kike ku murd'e gaskiya ƙarshe ma idan ba ai wasa ba su kori shari'ar." Mama ta ce "Ai Allah ya fi su, kuma insha Allahu zai baku nasara." Aunty Sadiya ta ce "Allah ya amsa." Neehal ta dubi Mama tana turo baki gaba ta ce "Mama na dawo fa." Mama ta ce "Ai na ganki." Neehal ta ce "Ai ba ki yi welcoming ɗina ba." Mama ta ce "To bari in ɗauke ki in goya ki uwata." Neehal ba ta ce komai ba ta tashi ta wuce sama tana ɓata rai. Aunty Sadiya ta yi murmushi zuciyarta cike da tausayin Neehal. Neehal tana shiga ɗakinta ta tarar da twins sun ba je kayan kwalliyarta akan gado suna ta yaɓa wa fuskarsu. Suna ganin ta shigo suka fara kifkifta idanuwa, dan tasha yi musu faɗa akan in ta fita su daina yi mata b'arna a ɗaki. Cike da takaici take kallonsu, ganin yanda suka bata jikinsu da bedsheet da janbaki, ta ƙaraso cikin ɗakin tana faɗin "Sannun ku da aiki." Afrah ta nuna Amrah ta ce "Aunty ita ta ɗakko miki." Amrah tai sauri ta ce "Ba ni ba ce ita ce." Neehal ta ce "Ku sauka ni ku bari guri." Sauka suka yi daga kan gadon da sauri suna mutsitstsika janbaki a ƴan'yatsunsu. Tattare kayan da suka barbazar mata akan gadon ta yi, sannan ta cire zanin gadon ta kai toilet. sai da ta sake wani sannan ta kamo su Afrah ta cire musu kayan jikinsu ta musu wanka, sukwa sai murna suke an ƙara yi musu wanka, dan suna k'aunar wanka a rayuwarsu suga suna ta facal_facal da ruwa.








Bayan Mama ta kawo wa Aunty Sadiya abinci ta ci, sannan ta tattara duka hankalinta akan Mama ta ce, "Yaya maganar Neehal ce fa ta biyo da ni." Mama ta ce "Ina jinki Sadiya me ya faru." Aunty Sadiya ta sauke numfashi cikin jimanta al'amarin ta ce "A binkicen da na yi ya nuna mun Mutum ɗaya ne yake kisan Jamil da Anwar!" Dammmm! Gaban Mama ya yanke ya faɗi, a razane ta ce "Ke ko Sadiya wacce shaida kika gani data tabbatar miki da haka? Kuma waye yake kisan?" Aunty Sadiya ta ce "Alamomi da yawa ne suka nuna hakan Yaya, sai dai kuma har yanzu ba mu gano wanda yake kisan ba, amma muna nan muna binkice a kan hakan kuma insha Allahu sai mun gano ko waye." Mama ta ce "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, wannan wanne irin abu ne? wanene yake bin yarinyar nan da irin wannan sharrin? Me tai masa yake ɗaukar wa rayuwarta wannan mummunan matakin?" Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce "Shine abun da muke son sani muma." Ƙarshen tashin hankali Mama ta shiga da jin wannan batun, da har hankalinta ya kwanta ta fara tunanin ko ba dan Neehal ake kisan ba, amma kuma jin wanda ya kashe Jamil shi ya kashe Anwar ya tabbatar mata da sanadin Neehal ake kisan. Duk yanda Aunty Sadiya ta so kwantar wa da Mama hankali amma hakan ya gagara, dan sosai hankalinta ya tashi da jin wannan K'ADDARAR da ta shigo cikin rayuwar Neehal, abun da yake ƙara tadawa Mama hankali shine idan ta tuna ta yanda MAHAIFAN Neehal suka bar gidan duniya, ta matsu Daddy ya dawo ta labarta masa wannan mummunan labarin dan su san ta inda za su ɓullo wa al'amarin.








Misalin ƙarfe goma sha ɗaya da mintuna na dare, Neehal ce kwance akan makeken gadonta Amrah kwance a kirjinta tana bacci, Afrah kuma ta rungume ta ta baya itama tana baccin. Hotuna take kallo a wayarta idanunta na zubar da hawaye tamkar an kunna famfo, a fili ta fara magana kamar haka, "UMMANAH, ABBANA, JAMIL ƊINA, ANWAR ƊINA, Allah ya ji k'anku ya gafarta muku, ya sa kuna cikin aljannatur firdausi, Allah ya toni asirin duk wanda yake da hannu a kisanku." Kuka ta shiga rerawa ƙasa_ƙasa cikin tausayin kanta, rayuwarta ta baya na dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, kewar mahaifanta na ƙara mamaye dukkan zuciyarta, ta rasa me yasa yau suke ta faɗo mata a rai tun da ta tashi, ta daɗe tana kukan kafin bacci barawo ya yi gaba da ita.






*ASALIN LABARI..........✍️*












_*Ku yi haquri da wannan, yau na yi busy ne.*_












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:44] Zeey Kumurya: *⚡NEEHAL⚡*












_By_
_Zeey Kumurya_














*2️⃣5️⃣*
















Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*


















............Alhaji *Muhammad Gabasawa*, Haifaffen garin Kano ne a wani ƙauye dake ƙaramar hukumar Gabasawa, mahaifiyarsa da mahaifinsa duk na can ne. Neman kuɗi ne ya kawo shi cikin birnin Kano tun yana saurayi gurin wani cousin ɗin mahaifinsa wanda suke kira da Baffa. Su biyu rak iyayensu suka haifa a duniya, daga shi sai Yayarsa mace, itama tana zaune a Gabasawan anan take aure. Gidansu babban gida ne a garinsu kuma sananne, kasancewar gidan yawa ne kuma kakansu na da arzik'i. Kayan masarufi suke siyarwa a ƙofar Nasarawa shi da k'anin Babansa wanda yake zaune a gurinsa, kuma Alhamdulillahi suna samu sosai. K'anin baban nasa (Baffa) wanda yake gurinsa yana riƙon yarinya sunanta *FATIMA* ƴar wansa ce uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, Fatima marainiya ce mahaifinta ya rasu tun tana ƙarama, da a gurin kakarta wadda ta haifi su Baffa take a Gabasawa, daga baya kuma Baffa ya ɗauko ta ya ci-gaba da riƙon ta. Soyyayyace ta shiga tsakanin Fatima da Muhammad har ta kai su ga yin aure suka tare a nan qofar Nasarawa, Muhammad ya kama musu hayar gida ɗaki ɗaya. Fatima ita kaɗai ce Ƴa a gurin mahaifinta, amma a gurin mahaifiyarta su uku ne, kasancewr mahaifinta ya rasu da dadewa har mahaifiyarta ta ƙara aure a wani gidan ta haifi maza guda biyu. Shekar Fateemah biyu da aure ta haifi ɗanta Namiji, sai dai bayan suna ba jimawa ya dinga wani irin ciwo har ya ce ga garinku nan. A lokacin ne kuma Muhammad ya samu aiki a Company'n wani hamshaqin Alhaji, kasancewar ya yi karatun boko amma iya secondary ya tsaya saboda halin rayuwa. Bayan shekara Fatima ta ƙara haihuwar ƴarta mace, sai dai itama watanni ta yi ta ce ga garinku nan. Hankalin Fateemah ya fara tashi garin tana haihuwa yaran na mutuwa, Muhammad ne ma ke tausar ta yana bata baki. A ƙauye kuwa mahaifiyarta da Kakarta suna ta aiko mata magungunan Hausa, a cewarsu jeji ne ke kashe yaran nata. A wannan lokacin suka tashi daga ƙofar Nasarawa suka koma Gadon k'aya inda Muhammad ya gina gidansa madaidaici mai kyau. Lokacin ne kuma arzik'i ya fara bunƙaso masa, saboda mutumin da yake aiki a wajensa mutumin kirki ne ga kyauta ga jama'a, kuma yana jin dad'i aiki da Muhammad kasancewar sa mai gaskiya da riƙon amana, hakan yasa ya ƙara masa matsayi a Company'nsa da suke sayar da takin zamani. A wannan shekarar ne kuma Muhammad ya ziyarci ƙasa mai tsarki ya sauke farali. Sai da aka kusa shekara biyu sannan Fateemah ta ƙara samun wanin cikin, addu'a suka duk'ufa ita da Alhaji Muhammad akan Allah ya yara mata abun da zata haifa, wannan karan ma mace ta haifa, cikin ikon Allah yarinya ta fara girma ba kamar sauran ƴan'uwanta ba, farin ciki a gurin Fateemah da Muhammad da ba zai faɗuba, sai dai watannin yarinyar bakwai ta ce ga garinku nan. Ko kaɗan Fateemah bata nuna damuwarta sosai ba, zuwa lokacin ta sare ta karbi ƙaddarar da Ubangiji ya dora mata, k'annenta Umar da Usman su ta karb'o daga gurin mahaifiyarta ta ci-gaba riƙe su a gurinta, dan gidan da mahaifiyartata take aure ba wani jin daɗin shi take ba, ana dai zaman haquri ne kawai. Umar da Usman suka ci-gaba da zama a gurin yayarsu cikin jin daɗi, lokacin ma sun fara zama samari. Alhaji Muhammad shi yake musu komai babu abun da ya rage su da shi. Fateemah ba ta yi boko ba amma ta yi ilimin Addini dai_dai gwargwado, dan da auranta ma ta yi saukar Alqur'ani mai girma a makarantar matan auren da take zuwa. Fateemah macece mai haquri ga kawaici babu ruwanta, shiyasa mijinta yake jin daɗi zama da ita. Watarana cikin dare Fateemah ta tashi da wani irin murd'awar ciki, tayta nurququsu ba tare da Alhaji Muhammad ya sani ba, har ta samu cikin ya lafa mata, sai dai kuma tana koma wa ta kwanta ta ji wani irin amai ya taso mata, da gudu ta tashi ta yi toilet ta shiga kelaya aman, kakarin amanne ya tashi Alhaji Muhammad daga bacci, sosai ya tausaya mata yay mata sannu. A wannan daren ta yi aman ya kai sau uku, ga zazzaɓi mai zafi daya rufe ta. Da safe kuma cikin ikon Allah sai ta tashi jikin da sauk'i sosai. Haka tai ta yi har kwana uku tana zazzaɓin dare, ranar na huɗu Alhaji ya ɗauke ta suka je asibiti aka dubata, gwajin farko likita ya tabbatar musu tana ɗauke da juna biyu. Murna a gurin Alhaji Muhammad ba a magana, Fateemah kam yak'e kawai take duk da ba ta san abun da Allah ze yi ba. Sosai Fateemah take shan wahala a wannan cikin kamar ba za ta kai ba, laulayi take mai wahala, ba ta iya bacci cikin dare sai kusan asuba yake ɗauke ta, kakarta ita ta zo daga Gabasawa take zaune da ita, dan ko aiki ba ta iya wa. Haka suka cigaba da rainon cikinsu har ya shiga watan haihuwa, tun cikin yana wata bakwai idan ka ga Fateemah sai ka zata ta kusa haihuwa saboda girman cikin. Ranar wata Juma'a ta tashi da nak'uda, cikin ikon Allah kuma ba ta wani sha wahala ba ta santalu ƴaƴanta guda biyu duk mata. Zo ku ga murna gurin Alhaji Muhammad da Fateemah dama sauran ahalinsu baki ɗaya, yaran kyawawa kamar Fateemah sak suka yo, sai dai ɗaya fara ce ɗayar kuma chocolate color kamar Fateemah. Wadda ta fi farin ita aka haifa sannan mai duhun. A ranar aka sallame su suka dawo gida. Kusan ɗaki guda Alhaji Muhammad ya cika da kayan babies saboda tsananin farin ciki, kodayaushe cikin addu'ar Allah ya bar masa rayan yake. Bayan kwana uku da haihuwarsu da daddare ɗaya daga cikin yaran Allah ya amshi abarsa, Hussainar ce ta rasu mai duhun kenan. Kuka sosai Fateemah ta yi akan rasuwar yarinyar, domin ba ta taɓa jin k'aunar ƴaƴan da take haifa ba kamar waɗannan Twins ɗin, ga fargabar itama ɗayar kar ta mutu. Alhaji Muhammad ya ji mutuwar yarinyar sosai shima, haka dai aka yi sunan ɗayar, Ranar suna ta ci Sunan mahaifiyarta *Fateemah Zahra* amma *NEEHAL* za'ana kiranta da shi. An sha Suna sosai wanda duk haihuwar Fateemah ba'a taɓa yin kamarsa ba. A wannan lokacin ne kuma Umar k'anin Fateemah ya gama karatun Secondary ɗinsa, bayan Result ya fito kuma an samu Alhaji Muhammad ya sama masa gurbin karatu a Bayero University Kano. Fateemah kullum cikin godewa Alhaji Muhammad take ita da mahaifiyarta na yanda baya gajiya da dawainiyar k'annenta, kama daga cinsu,shansu,surarsu,iliminsu na boko dana addini duk baya gajiya da yi musu. Dama Alhaji Muhammad mutum ne shi mai kyautatawa ƴan'uwansa na birni dana ƙauye, hakan yasa kullum yake ganin cigaba a al'amuransa. Kowa ya tashi da buƙatarsa sai ya zo gurinsa, shi kuma indai ba ta fi ƙarfinsa ba zai maka. Neehal irin yaran nanne masu shegen Kuka, musamman cikin dare ba ta barin iyayenta su rintsa, Fateemah idan ta gaji da rarrashi takance "Allah ya nuna mun ranar da zaki bar ni na huta nikam, tun daga cikin ki har yau bana samun isasshen bacci." A duk lokacin da ta faɗi haka Alhaji Muhammad sai dai ya yi murmushi kawai. Watan Neehal bakwai kacal a duniya amma sai wayon tsiya, a lokacin rarrafe take ɗan yi amma akwai son yawo, Abbanta kullum da wayo yake fita daga gidan dan idan zai fita ta dinga ihu Kenan. Uncle Usman shine mai d'aukar ta idan ya dawo daga makaranta ya fita da ita, shi yasa tafi sabawa da shi akan Uncle Umar. Shekarta ɗaya da wata biyu Umma ta yaye ta, dan zuwa lokacin ta yi ƙafa ta fara tattakawa ga surutu duk da gwaranci take yi maganar ba ta fita sosai, ga kuma masifa, dan Yaro ɗan shekara uku ma dan tsaurin ido sai ta dinga dukansa, musamman idan aka zo gidansu, ga ta'adi komai aka ajiye sai taɓa. Neehal yarinya ce mai farin jini dan kowa sonta yake, kullum zaka ganta fess Ummanta bata barinta da k'azanta, Abbanta kuwa ba ya gajiya da yi mata siyayyar kayan sawa masu kyau da tsada. Tun tana ƙarama ba ta son hula, ana sa mata zata cire ta yar, gata da gashi mai yawa da tsayi kuma baƙi sidik. Shekararta biyu bakinta ya buɗe cui_cui sai ɗan banzan surutu kamar ta ci aku, ga tsokana kamar me. Umma kullum sai dai ta kalle ta mata addu'ar shiriyar Ubangiji. Sosai mahaifinta yake nuna mata gata kasancewar ta yarsa guda ɗaya tilo a duniya, sai dai ba irin gatan da zai ɓata ba, kuma suna mata tarbiyya dai_dai gwargwado. Shekarar Neehal uku a duniya lokacin ta fara zuwa islamiyya da boko, mahaifinta ya sai filin kusa da gidansu ya haɗe da nasa ya gina wani part ɗin, nan ma da suke ciki ya ƙara gyarashi. Dan zai ƙara aure ne ba dan ya dena don Matarsa ba, sai dan yana da halin yi kamar yadda Allah ya ce. Umma ko kaɗan ba ta damu ba akan za a mata kishiya, addu'a take kawai Allah ya kawo mata ta gari,kuma ta toshe kunnuwanta daga duk wata zuga

Please Login or Register in order to submit comment