Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baya dan ta ba shi hanya. Ya ce "Yawwa Aunty." Tare da shigowa cikin falon bakinsa ɗauke da Sallama. Ta koma kitchen zuciyarta cike fal da mamakin zuwansa. Plate ta ɗauko ta ɗora masa drinks akai ta dawo falon, ya bita da kallo still fuskarta d'auke da murmushi. Ta ajiye plate ɗin a gabansa ba tare da ta ce komai ba. Ya ce "Mama bata nan ne?" Ta ce "Eh, ta je unguwa, amma na san yanzu tana hanyar dawowa, ina su Afrah?" Ya ce "Suna gida, ba su ma san zan zo ba dan kar su mun rigima." Neehal ta ce "Ai da ka zo mun da su, ya su Ummi?" Ya ce "Suna nan k'alau." Ta mik'e tare da faɗin "Ga ruwa ka sha, bari na ƙarasa girki." Ya ce "Okay thank you." Tare bin ta da kallo har ta shige kitchen ɗin, ya lumshe idonsa yana jin k'aunarta na ƙara mamaye dukkan wani gurbi dake cikin zuciyarsa. Ba jimawa da shigar ta kitchen ɗin ya ji shigowar su Mama falon ita da su Dije tare da wasu ma'aikatan gidan maza guda biyu hannunsu ɗauke da manya_manyan ledodi. Mama ta ƙaraso cikin falon da mamaki take duban Ahmad, cikin fara'a ta ce. "Doctor! Kai ne a gidan namu?" Cikin girmamawa ya ce "Nine Mama, sannu da zuwa." Mama tana ƙoƙarin zama ta ce "Yawwa, sannunka kai ma." Ya sauko daga kan kujerar da yake ya ce "Ina yini." Mama ta ce "Lafiya k'alau, ina ƴan tagwayena da su Ummi?" Ahmad ya ce "Suna nan k'alau." Mama ta ce "Masha Allah, ina Neehal ɗin ne ta bar ka kai kaɗai a zaune." Yana sosa kai ya ce "Ai babu komai Mama.,'" Mama ta miƙe ta nufi kitchen jin k'amshin girki ta gane Neehal ɗin tana can. "Oyoyo, Sannunku da zuwa." Neehal ta faɗa lokacin da Mama ta shiga kitchen ɗin. Mama ta ce "Yawwa, Sannunki da aiki." Ta shagwab'e fuska ta ce "Yawwa Mama, yau na sha aiki na gaji, jikina har ya fara mun ciwo." Mama ta ce "Allah ya baki lada kin ji ƴar albarka." Neehal ta ce "Ameen." Mama ta ce "Ki je gurin Doctor, bari na ƙarasa girkin. Babu daɗi a bar mutum shi kaɗai a zaune." Neehal ta ce "Na ma gama girkin, saukewa kawai zan yi, da kitchen ɗin zan gyara." Mama ta ce "Barshi, idan su Zulai sun huta sai su zo su gyara, ki zuba abincin ki kai masa." Neehal ta ce "Toh." Mama ta juya ta fita, ita kuma ta shiga zuba masa abincin kamar yadda Mama ta umarce ta. Sai da ta hau sama ta sako hijabi tare da ɗauko wayarta sannan ta dawo downstairs ɗin.








Yana zaune yana latsa waya ta yi Sallama ta ajiye masa abincin a gabansa, ganin bai sha drinks ɗin data ajiye masa ba. Ta ce "Ya baka sha ruwan ba." Ya d'ago yana kallon fuskarta da murmushinsa na gado ya ce "Zan sha yanzu." Ba ta ce komai ba ta buɗe ruwan ta tsiyaya masa a cikin glass cup ta miƙa masa. Ya karɓa tare da faɗin "Thank you." Neehal ta koma kujerar gefensa ta zauna ta shiga wasa da yatsun hannunta. Bayan ya gama shan ruwa ya fuskance ta a hankali ya ce "Gurinki na zo Neehal." Ta dube shi da sauri amma bata yi magana ba. Ya gyaɗa mata kai alamar tabbatarwa. Ya miƙe tsam daga kujerar da yake ya koma wadda take zaune ya zauna a gefenta. Ta lumshe ido da sauri saboda shaƙar sassayan k'amshinsa da ta yi. Muryar Ahmad da ta ji yana magana yasa ta buɗe idanunta. Wayar hannunsa yake miƙo mata, ta karɓa da alamar tambaya akan fuskarta. Hoton da ta gani akan screen ɗin wayar yasa ta waro Idanunta waje cikin tsananin mamaki. Hotonta ne tana ƙarama wanda bata san a inda ya same shi ba. Kafin ta yi magana ya riga ta da faɗin "Ki wuce kiga na gaba." Ba tare da ta yi magana ba ta wuce kamar yadda ya ce zuciyarta cike da al'ajabi, Wannan karon ɗan zabura ta yi tana ƙara kallon hoton, hoton tane ita da shi, tana murmushi shi kuma yana kallon fuskarta da murmushi ɗauke akan fuskarsa...........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*4️⃣4️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*












*🌈NIMCY'S LIBRARY🌈*


_Readers gareku, masu tambayar old books na NIMCYLUV SARAUTA, tayi shiru ne domin tana bada bunus kafin azumi, to Finally the day is here, tana sai da littafan ta gaba ɗaya akan 3k gaba ɗaya littafan guda 14 ne, to bisa Bunus ɗin da tayi na tsayin sati guda dukkan mai so zai biya 1500 mai makon 3k😍, nasan baku karanta littafan ta na baya ba, da am sure za kuce sunma fi na yanzu daɗi❤️🤨_


So what are waiting for.....??? Go and subscribe your own...


Abu Maleek
Sirrin mu
Uncle ne
The new emir
Izzar so
Sai na aureta😍
Tsintacciya
E.t.c guda 13 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616 a biya asha karatu Tabbas za kuyi farin ciki littafan babu baya #Love #Romance #Destiny


Bunus ya fara 6/2/2022
Share fisabilillahi😍
















.........Ahmad ne ya fara juyawa ya kalli ƙofa jin ana sallama tare da amsa Sallamar. Neehal kuwa bata san time ɗin data miƙe tsaye ba jin sallmar Ameen cikin kamilalliyar muryarsa. "Yaya! ga mahaifin su Afrah." Ta faɗa a diririce ba tare data san ta yi hakan ba. Ameen dake tahowa inda suke ya mata wani kallo bai ce komai ba. Ahmad kuwa bai lura da yanayin da Neehal ta shiga ba wanda ita kanta in za'a kashe ta baza ta ce ga dalilin da yasa ta haka ba, idanunsa suna kan Ameen. Ameen ya miƙa masa hannu bayan ya ƙaraso inda suke ba tare da ya ce komai ba. Da fara'a Ahmad ya miƙa masa nasa hannun suka yi musabaha. Ahmad ya ce "Barka da yamma." Ameen ya ce "Yawwa, ina maka murnar bayyanar kids ɗinka." Still fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Thank you." Ameen ya juya ya nufi sama ba tare da ya ƙara cewa komai ba. Neehal ta sauke numfashi tare da komawa ta zauna tana bin bayan Amee da kallo, wanda ya tafi ya bar musu k'amshinsa a falon. Muryar Ahmad da ta ji yana faɗin "Princess." Shi yasa ta juyowa ta kalle sa. Ya ce "Zan wuce, na ga time ɗin sallah ya yi." Ya ƙarasa maganar tare da duba agogon hannunsa. Neehal ta ce "Gidan Mamy zaka koma?" Ya ce "Eh." Ta ce "Ka gaishe ta Please." Ya ce "Zata ji Insha Allah." Ya miƙe tsaye yana jifanta da wani kallo mai cike da tsantsar k'auna. Ta miƙe itama kanta a ƙasa ta ce "Thanks for the visited." Ya ce "Thank you more and more Princess, nine da godiya ba ke ba, kasantuwar mu yau a tare ya sanya ni a cikin farincikin dana manta rabon da na yi kamar sa." Ta d'ago ta kalle shi amma ba yanda za su iya haɗa ido ba ta ce "Nima na yi farin cikin kasancewa da kai Uncle." Ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai alamar tabbatarwa. Ya tsaya kawai yana kallonta yana jin kamar ya tafi. Kiran Sallar da aka gwad'a a masallacin dake cikin layin nasu ne ya sa ya sauke ajiyar zuciya. A hankali ya matso daf da ita, hannunta ya kama cikin murya kamar mai rad'a ya ce "I love You....!" Ta lumshe idonta tare da ƙoƙarin zame hannunta daga nasa jin taku ana sakkowa daga sama, amma ya ƙi bata damar hakan, sai ma hannunta da ya kai saitin bakinsa ya mata pick tare da faɗin "Bye." Sannan ya sakar mata hannun ya juya ya nufi ƙofa ya barta anan sandare cikin wanin yanayi da bata san ya zata fassara shi ba. A hankali kuma ta buɗe idonta ta ga har ya fice daga ɗakin. Ta juya dan ɗaukar wayarta tana sauke numfashi suka yi 4 eyes da Ameen tsaye a cikin falon. Ta yi kamar bata gan shi ba, ta sunkuya ta ɗauki wayarta ta nufi upstairs. Ameen ya bita da kallo sannan ya tab'e ɗan bakinsa ya fice daga falon. Sai da ta zauna akan kujera bayan ta ƙarasa falon sama sannan ta latsa wayarta, message ɗin Sadik ta gani 11 minutes ago. Ta buɗe da sauri ta karanta. Ajiyar zuciya ta sauke ganin ya ce, tunda abu take yi yanzu zai je ya yi Sallah ya dawo tunda lokacinta ya gabato. Ta miƙe ta shiga ɗakin Mama. "Mama! Mama!" Ta shiga kiran sunanta bayan ta shiga, Mama ta fito daga toilet fuskarta da ruwa alamun alwala ta yo ta ce "Na'am Daughter wannan kiran fa?." Neehal ta yi murmushi ta ce "Wani labari zan baki mai daɗin gaske." Mama ta ce "To bari mu yi Sallah sai ki bani, Ahmad ɗin ya tafi ne?" Neehal ta ce "Eh, ya tafi yanzu nan." Mama ta ce "Amma ba a yau zai koma Abujan ba?" Neehal ta ce "Eh, akwai ƙanwar Ummi a nan Kano gidanta zai koma, amma gobe zai wuce Abujan." Mama tana shimfid'a Darduma ta ce "Alright." Neehal ta juya ta fice daga ɗakin zuwa nata dan yin Sallah. Bayan ta idar ba jimawa wayarta ta fara vibrate, ta ɗauko kamar yadda ta zata Sadik ne yake kiran ta. Ta d'aga tare yin sallama, ya amsa mata. A hankali ta ce "I'm sorry Yaya Sa..." Ya katse ta da faɗin "No Darling kar ki damu, na san abu kike yi time ɗin. Daga unguwa ma nake na biyo in ganki in kuma yi miki sallama." Neehal ta ce "Sallama kuma?" Ya ce "Eh, gobe in Allah ya kai mu zan tafi ibadan sai ranar Friday zan dawo." Neehal ta ce "Allah ya kai mu, ya tsare hanya ya kiyaye mun kai." Ya ce "Ameen ya Allah, na ce miki zan dawo kuma bayan mun yi Sallah Abba ya kira ni ya sanar mun in zo gida zamu fita tare da shi yanzu." Neehal ta ce "Idan kun dawo ba sai ka zo to." Ya ce "Idan mun dawo da wuri zan zo insha Allah." Cikin shagwab'a ta ce "Idan baku dawo da wuri ba sai nan da 5 to 6 days zan gan ka kenan?." Ya ce "Um'um Dear, ai za mu yi video call ko?" Ta ce "Shikenan Husby nah." Ya ce "Yawwa wifey." Daga haka suka yi sallama ya kaste wayar. Ta tashi ta tafi ɗakin Mama ta fara fara labarin Ahmad tun farkon haɗuwar su, duk da wasu abubuwan ta manta wanda ta riƙe kawai ta faɗa mata. Mama ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, Allah ya biya shi taimakon da yay miki." Neehal ta ce "Ameen, shi yasa nake son twins over, ashe....." Sai kuma ta yi shiru. Mama ta ce "Uhm? Ashe soyayyar Mahaifinsu ce ta shafe su." Neehal ta rufe fuska tana murmushi. Mama ta ce "Gobe idan ya zo ya kamata ki bishi ki je ki gaishe da ƙanwar Ummin nasu." Neehal ta ce "Gaskiya kam, dan tana da kirki kuma tana sona, har wanka ta taɓa mun." Cikin takaici Mama ta ce "ita matar Umar ɗin duk zuwa gidansu Ahmad ɗin da kike bata taɓa bibiya ta ji me kike zuwa yi ba, yanzu da ba shi da hali fa cutar dake yake babu ruwanta ko? Saboda ba ita ta haife ki ba, halin wasu mutanen sai dai mu ce Allah ya shirye su kawai yasa su gane." Neehal ta ce "Ameen Mama." Mama ta ce "A cikin week ɗin nan ya kamata ki je gidan A'isha da Sadiya, kin jima ba ki je ba." Ta ce "Toh Mama Insha Allah zani, ni Gombe ma nake son zuwa, duk sanda Hajiya ta zo sai ta mun complain akan rashin zuwa na." Mama ta ce "Na ji Ameen yana cewa yana son zuwa Gomben nan kusa shi ma, sai ku tafi tare. Ga Abuja ma kin daɗe baki je ba, Jiya da muka yi waya da Umma ma sai da ta ce ƙin daina zuwar musu yanzu." Neehal ta ce "Insha Allah, duk a cikin month ɗin nan zan je musu." Mama ta ce "Allah ya yarda, shi ma Uncle ɗin naki ya kamata ki lek'a musu." Neehal ta ɓata fuska dan ta gane Uncle Umar Mama take nufi. Ta ce "Ni fa Mama bana son zuwa yana kora ta da cin mutunci." Mama ta ce "Ki je dai, ai ba zama zaki yi ba, ganin su kawai zaki yi ki dawo, kin fi shekara biyu fa baki je ba." Ba don ta so ba ta ce "Toh." Mama ta ce "Yawwa my Daughter, ki yi haquri watarana sai labari, nina faɗa miki watarana sai sun zo suna neman ki har inda kike, komai lokaci ne. Kuma har abada su jininki ne ba'a taɓa sauya wa tuwo suna." Neehal ta gyaɗa mata kai cikin gamsuwa. Mama ta ci gaba da yi mata nasiha cikin taushin murya, daga ƙarshe kuma ta saka mata albarka tare da tarin addu'oi. Kiran Sallar isha'i ne ya tayar da su suka yi Sallah. Bayan sun idar ba jimawa Ameen ya dawo gidan kamar yadda Mama ta ce masa in an yi isha'i ya dawo Daddy yana neman sa. Ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo da sallama. Suka amsa masa a tare. Kan Neehal a ƙasa ta ce "Ina yini Yaya." Ko kallon inda take bai yi ba balle ya amsa mata, ya samu gefen gado ya zauna fuskar nan a haɗe. Neehal ta tashi ta fice daga ɗakin. Bayan ta fita Mama ta dube shi ta ce "Kana ji tana gaishe ka amma ka ƙi amsa mata." Ya ɗan yi murmushi bai ce komai ba. Cikin takaicin wannan halin nasa Mama ta ce "Bari na kira Dad ɗin, na ji bai shigo ba har yanzu." Ya ce "Tom." Tare da miƙewa ya fice daga ɗakin. Ɗakin Neehal ya buɗe ya shiga, tana kwance a kan gadonta tana latsa waya. Bata san ya shigo ba sai k'amshinsa ta ji ya cika mata hanci. Ta juyo da sauri sukai ido huɗu fuskar nan a haɗe, ta tashi zaune da sauri cikin tsoron yanayin data gan shi ta ce "Yaya!" Bai amsa mata ba sai harara da ya zabga mata. Tayi ƙasa da kanta da sauri. Ya fi mintuna biyar a tsaye bai ce komai ba, daga baya kuma ya juya ya fice daga ɗakin. Ta sauke ajiyar tare da tashi ta je ta kulle ƙofar ɗakin dan yanayin data gan shi a ciki na ɓacin rai ta ɗauka dukan ta ma zai yi, duk da bata san abun da ta yi masa ba. A ranta tana mitar ya yi auren ma amma ba zai barta ta huta da masifarsa ba, gashi shi mutum ne wani iri da baka sanin lokacin daka masa laifi, abun da kai a tunaninka ba laifi ba ne shi a gurinsa laifi ne. Duk da ta san yana da haquri, musamman ma ita ya yi haquri da ita a baya, ta saka masa ciwon kai lokacin da ya dawo daga karatu kafin ta saba da shi, dan a lokacin duk abun da ta san baya so shi take yi, shi kuma idan ya gaji da ɗauke kai daga abubuwan da take yi, ya kamata yay punishied ɗinta. Daga baya kuma da ta ƙara girma ta yi hankali sai ta ci maganin zama da shi, ta gane mutum ne shi mai sauƙin kai da kawaici, shi abun da kawai ba ya so a rayuwarsa raini, idan har zaka raina shi to baza ku taɓa shiri ba. Gashi da kyauta kamar mahaifiyarsa, bata neman komai ta rasa saboda kafin ma ta buƙata ya siyo mata, duk weekend ɗin duniya idan ya dawo daga Lagos da guzurin tsarabarta yake tahowa. Sometimes idan yana gari shi yake koya mata Assignment idan bata iya ba, haka ma hadda yana jiye mata ko kuma ya ƙara mata inda bata iya ba. Daga shekara biyar zuwa yanzu ne ya sauya mata gaba-d'aya, ya fara shashshare ta over dama gashi muskili, sai ran da ƴan mutuncin suke kansa shine zai ɗan sakar mata fuska.........






Wayarta dake gefenta ce ta katse mata tunanin da take ta hanyar yin vibrate, ta sauke numfashi sannan ta saka hannu ta ɗauka tare da duba mai kiran. Number ce babu suna, amma da yake da sim ɗin da ba kowa ne yake kiran ta da shi ba sai makusantanta yasa ta d'aga. Cikin sassanyar muryarsa ya mata sallama hakan yasa ta gane shi ne. Ta amsa tare yin shiru ya ce, "Are you Ok?" Ta ce "Eh, me ka ji?" Ya ce "Na ji muryarki so cool." Ta ce "Ba komai, ya ka je gida?" Ya ce "Lafiya k'alau, duk da baki kira ni kin ji ba sai da na kira ki." Ta ce "I'm sorry, bani da Numbern ka ne." Ya ce "Alright." Suka yi shiru gaba-d'ayan su, ita ta rasa me yasa ta ji gaba-d'aya zuciyarta babu daɗi, kuma daga shigowar Ameen ɗakinta ne mood ɗinta ya canza, amma da tana cikin farin ciki sosai. Fahimtar hakan da Ahmad ya yi yasa ya shiga bata labarin rayuwarsu ta da cikin sigar tsokana, nan da nan ta ware ta shiga ƙyalƙyala dariya. Ahmad He is so funny at all, amma idan ya shagwab'e sai ka ɗauka yaro ɗan shekara uku ne. Sosai ta ji daɗin wayar da sukai kamar kar su daina, sai da ta ga Sadik yana ta kiran ta sannan ta masa sallama ta kira Sadik bayan ta gama haɗa kalaman da za ta yi amfani da su gurin ba shi haquri akan kiran ta da ya yi ya ji waiting call......✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*4️⃣3️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*














.........Da sauri ta d'ago ta kalle shi gabanta na fad'uwa ta ce "Doctor! wa...." Ya katse ta da faɗin "Kin yi mamaki ba, na san yanzu kina tambayar kanki ina na samo waɗannan hotunan, kuma yaushe aka yi su?" Ya ɗan ja numfashi ya ce "Neehal! Na yi mamaki sosai da kika kasa gane ni a lokacin da kika ganni, duk da nasan shekarun da yawa kuma lokacin da muka haɗu kina yarinya ƙarama, amma na san yanzu waɗannan pictures ɗin sun tuna miki da ni a rayuwarki." Kallon fuskarsa ta shiga yi ko kiftawa ba ta yi, lokacin ɗaya idanunta suka ciko da k'walla, ta yi minti uku a tana kallonsa kallo irin na k'urilla sannan ta ce. "Uncle Ahmad! Are you the one please?" Ta faɗa cikin raunin murya da tsantsar mamaki. Ya yi murmushi cikin jin daɗin yanda ta iya tuno shi da wuri haka ya ce "Yes, kin manta ni a rayuwarki ko? kin karya alƙawarin da kika mun." Ta girgiza masa kai cikin ƙoƙarin mai da k'wallar data tarar mata ta ce "Ban manta ka ba a cikin raina, domin a duk lokacin da zan tuno da rayuwata ta gidan Uncle Umar sai na tuna da kai da irin taimakon da ka ba ni." Ya ce "Amma me yasa da kika ganni kika kasa gane ni." Ta ce "I don't know, amma kasan shekarun da yawa, kuma ranar dana ganka na ga kamar na san fuskarsa, amma na rasa a ina na santa." Ahmad ya juyo ya fuskance sosai ya ce "Neehal, duk tsawon shekarun nan da suke wuce dai_dai da rana ɗaya ban taɓa mantaki ba a cikin raina, kodayaushe ina tunanin ki tare da fatan na sake haɗuwa dake a rayuwata, ashe ta sanadin twins Ubangiji zai ƙara haɗu mu, haɗuwar da bana fatan mu rabu har abada." Neehal ta sauke numfashi ta ce "Ina Mamy?" Cikin mamaki ya ce "Baki manta Mamy ba?" Ta ce "Eh mana, kamar yadda ban manta ka ba itama ban manta ta ba, amma na san idan na ganta a yanzu ba zan gane ta ba, har yanzu tana unguwar su Uncle Umar?" Ya ce "A'a sun tashi daga unguwar, amma suna Kanon dai. Sai dai ita tafi shekara bata ƙasar nan, ta je Turkey, shekaran jiya ta dawo, yanzu ma daga gidanta nake." Ya ɗan ɓata fuska sannan ya cigaba da magana "Ni fa ban ga kina murnar gani ba, ko ba ki yi farinciki da sake haɗa mu da Allah ya yi ba?" Neehal ta yi murmushi ta ce "Hmm, wlh Uncle farincikin da yake cikin Zuciyata a yanzu na haɗuwa da kai a karo biyu a rayuwata ba zai misaltu ba, kawai tsananin mamaki ne ya hana murnar tawa bayyana, gani nake ma kamar mafarki nake, Uncle Ahmad, mutumin kirki, mai taimakon bayin Allah ba tare da ya san su ba, shine mahaifin Twins ɗina? Abun kamar almala Uncle." Ahmad ya yi murmushi yana jin zuciyarsa ta masa wasai ya ce "Ikon Allah ya fi ƙarfin komai Princess." Ta yi shiru kawai tana kallon sa, ta kasa ɗauke idanunta daga kansa. Ya d'age mata gira ɗaya ya ce "Wannan kallon fa?" Da sauri ta rufe fuskarta da hannunta tana murmushi, wani irin farinciki take ji a cikin ranta, kamar ta tashi tai ta tik'ar rawa haka take ji. Ya yi ƙasa da murya ya ce "Ya zaki rufe mun maganin ciwon idona? Please ki buɗen wannan kyakkyawar fuskar da idanuna ba sa gajiya da kallon ta" Ta buɗe fuskar amma sai ta yi ƙasa da kanta, wata irin kunyarsa take ji ba kaɗan ba. Ahmad da yake jin kamar ya rungume ta saboda wutar k'aunarta da take ƙara ruruwa a ransa ya ce "Now tell me, me ya faru bayan rabuwar mu." Ba tare data d'ago ba ta ce "Ka fara faɗa mun naka, da yanda har ka yi aure ka....." Sai kuma ta yi shiru. Ya ce "Uhm, ƙarasa faɗar abun da zaki ce mana." Ta ɗan turo baki ta ce "Babu." Ya gyara zama tare da faɗin. "Ranar da muka haɗu dake last, bayan na koma gida na kasa aiwatar da komai saboda tunanin ki, na farko ina tunanin kar a miki wani abu a gida saboda Uncle ɗinki ya ganmu tare. Na biyu kuma wanda shi ya fi sani cikin damuwa komawa Abuja da zan yi in yi nesa dake. Tun kafin ranar nake wannan tunanin, da farko na ɗauka tausayin ki ne yasa nake wannan tunanin, amma daga baya na gane na shak'u dake shak'uwa mai tsanani. A ranar ko baccin kirki ban iya yi ba saboda tunani. Da safe bayan na gama shiryawa kafin na fita sai da na je wajen gidanku ko Allah zai sa in ganki, amma ko me kama dake ban gani ba. Gashi ni ban san gidanku ba tunda bana ƙarasawa a hanya muke rabuwa. Haka na dawo gida jiki a sanyaye, gashi washegarin ranar ne tafiyata Abuja. Tun da na je Masallaci na yi sallar Azhar har aka kira la'asar ban koma gida ba, ina ƙofar gida ina jiran ki, ki zo wucewa, ranar ko abincin kirki ban iya ci ba. Bayan na yi Sallar la'asar na je gurin mai kayan miyan da kike siya a gurinsa na masa kwatancenki na tambaye shi ko kin zo siyan kayan miyan ranar ya ce mun A'a baki zo ba. Hankalina fa ya tashi matuƙa na ƙara komawa layinku ko zan gan ki, na tambayi wasu yara ko sun san gidanku suka ce mun bama su san ki ba. Ranar dai haka na kwana cikin tsananin damuwa. Washegari tun safe na wuce Abuja zuciyata babu daɗi ko kaɗan. Wata na uku da komawa Abuja na tafi India na yi wani course na shekara ɗaya, bayan na dawo da some weeks na fara aiki. A'isha ƴar gidan wani abokin Daddy ce, na santa sosai suna zuwa gidanmu tun kafin mu fara soyayya da Ita. Yarinyar

Please Login or Register in order to submit comment