Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Alqur'ani da sauran littatafai. Ita kuma Aunty Jamila sai ta ƙara mata da bayanin wasu abubuwan akan addinin. Sannan kuma idan zata yi girki tare suke yi, dan Hafsan tana gani tana koya. A hankali Hafsah ta fara sakin jikinta zaman gidan Aunty Jamila ya fara yi mata daɗi, ta kuma mayar da hankali akan karatun da ake yi mata. Sai dai fa kullum da tunanin Ameen take kwana take tashi a ranta. Lokuta da dama tana zama tay ta tunanin zaman Auransu, babu shakka ita akaran kanta ta san Ameen ya yi haquri da ita, a kodayaushe idan ta yi masa laifi uzuri yake mata ya dinga nusar da ita aibun abun da ta yi masa, sannan yana iyakar ƙoƙarinsa wajen ganin ta gyara addinta ta ko yi ilimin addinin, ta kan tuna lokacin data zubar masa da ciki, da farko fushi ya yi mai tsananin gaske da ita, daga baya kuma ya koma yi mata nasiha da nuna mata girman lefin da ta aikata ga Ubangiji. A lokacin gani take kamar rashin wayewa ne yasa ya kasa fuskantar abun da take nufi na ta yi ƙanƙanta da fara tara ƴaƴa a yanzu, sai yanzu da ilimi ya fara ratsa ta sannan ta gane ashe ita ce mara wayewar da kuma tarin duhun jahilci a kanta. Ranar suna zaune lokacin an yi wata biyu da sakinta take bawa Aunty Jamila labarin magungunan da Aunty Safiyya ta dinga kawo mata a matsayin su ne za su janyo da hankalin Ameen gare ta. Aunty Jamila ta yi salati ta ce. "Yanzu ita Safiyya an girma ma amma bata bar halin yarinta ba na bin Malam tsibbu? To Allah ya shirya ta yasa ta gane gaskiya. Ita kuma Yaya tana kallo bata yi magana ba?" Hafsah ta ce. "Bata ce komai ba." Aunty Jamila ta ce. "Dama ita Yaya haka take, duk abun da zaka yi bata k'wabar ka, na dai-dai ko na rashin daidai. Ke kuma wannan ya ishe ki izna, ki gane komai na Allah ne, ɓata wayonki da kika yi kika bi ɓata shi yasa Ubangiji ya barku da halinku, da a ce Sallah kika dage da ita da addu'a kamar yadda kika dage da yin amfani da magungunan nan da watak'ila al'amarin bai kai har haka ba, amma da kika kasa tsayar da Allah a al'amarinki kin ga illar hakan ai, tunda maganin bai yi aikin komai ba. Mutane su yi ta asarar kuɗaɗen su saboda jahilci suna zuwa gurin wani mutum ɗan'uwansu wai da sunan shi zai biya musu buƙata, ya baku maganin k'arya da wofi ya ci kuɗinku a banza, ga kuma tarin zunubi a gurin Ubangiji, dan shirka ba ƙaramar masifa ba ce, Allah ya raba mu da ita." Hafsah ta gyaɗa kai ta ce. "Amin Aunty na gode da tunatarwarki a gare ni. Amma Aunty kullum sai na saka ran ganin Ameen, ko ya turo wani nasa, ko ya kira ni amma shiru har na kusa gama iddata." Cikin tausayinta Aunty Jamila ta ce. "Ki ƙara haquri Hafsah kin ji, komai rubutacce ne a gurin Ubangiji, ki fawwala masa komai, idan ya nufa akwai sauran zamanku da Ameen a gaba sai ki ga kin koma, idan kuwa iya zaman kenan sai ki yi haquri, Allah ya kawo miki wani na gari." Gyaɗa mata kai Hafsah ta yi a hankali jikinta duk ya yi sanyi akan Ameen, ta san tunda ya samu mace kamar Neehal zai yi wahala ya ƙara waiwayar ta a cikin rayuwarsa..........✍️










*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_












*9️⃣0️⃣*










*ELEGANT ONLINE WRITER'S*








```I DEDICATED ALL THIS NOBEL TO MY LOVELY MOTHER, ONE IN THE BILLIONS, ONE LIKE NO OTHER, SUPER WOMAN, *HAJIYA FATIMA KUMURYA* ALLAH YA ƘARA MIKI LAFIYA DA NISAN KWANA MAI AMFANI, AMEEN.```












*SPECIAL THANKS TO*


*Abubakar Ak saraki,*
*Muhammad Kareem,*
*Mu'az,*
*S deen and*
*Yareema.*
*Mutanen kirki kenan wanda basa gajiyawa da yin share, Allah ya saka muku da Alkhairinsa.*














.........Rayuwa na tafiyarwa su Neehal yadda ya kamata cikin kwanciyar hankali da farinciki. Sosai Ameen yake k'aunar cikin jikinta tun kafin ya fito duniya, da daddare idan sun kwanta haka zai ta shafa cikin yana magana shi kaɗai, wai magana yake yi da ɗansa, wataran har ta yi bacci ta bar shi yana ta faman latsa mata ciki, da safe ma haka yana tashi zai ɗora daga inda ya tsaya wai gaisawa suke yi. Ita dai sai dai tay ta yi masa dariya, in ta gaji kuma ta ture hannunsa daga jikinta. Cikin Neehal ya shiga wata na uku lokacin farkon azumin watan Ramadan Haneefah ta haifi ƴarta mace mai kama da ita sak. Murna gurin Neehal ko ita ta haihu sai haka, ranar da ta je Barka daƙyar take bari a ɗauki yarinyar, tana hannunta ta rungume ta sai kallon ta take. Mommyn Haneefah ta yi ta mata dariya tana cewa in da rai ita ma kamar yau ne zata haifa, da yake gida aka mayar da Haneefan. Duk da azumi ne kuma ga laulayin da take fama da shi amma zuwanta uku kafin ranar suna. Ranar suna yarinya ta ci sunan Mommyn Haneefah Maryam, Haneefah ta ce Neehal za'ana ce mata. Neehal ta ji daɗin wannan karar da Haneefah ta yi mata sosai, kayan barka sosai Ameen ya siyawa takwararsu da ita kanta Haneefan, ita ma Neehal ta ƙara da nata kayan. Ba'a yi taron suna ba kasancewar azumi ne.








Wataranar Laraba Neehal tana kitchen tana girki da yamma ta ji ana knocking ɗin ƙofar parlour. Ta goge hannunta ta fito ta nufi ƙofar, lokacin cikinta ya fito ɗan wata shida, ya yi mata das a jikinta abun sha'awa, yanzu an bar laulayi. Sai da ta tambayi waye? Sannan ta buɗe ƙofar. Ɗaya cikin yaran gidan ne masu bawa flowers ruwa da yi mata aike. Bayan ya gaishe ta ya ce. "Hajiya wasu baƙi ne suka zo wai suna san ganin ki." Neehal ta ce. "Baƙi kuma? Maza ko Mata?" Ya ce. "Maza ne dattijai haka kamar almajirai." Neehal ta ce. "Kuma suka ce Ni suke son gani?" Ya ce. "Eh, dan sun ce daga can gidan Hajiya babba (Mama) aka turo su." Neehal ta ce. "Okay ka ce su shigo." Ta juya ta koma ba tare da rufe ƙofar ba a ranta tana Mamakin baƙin da aka ce ta yi, ɗakinta ta shiga ta ɗauko hijabi ta zira akan doguwar rigar abayar dake jikinta. Ta duba time ta ga biyar ta wuce lokacin dawowar Ameen gida ya kusa. Jin ƙarar turo ƙofa yasa ta fita parlour'n. Maza ta gani su biyu kamar yadda yaron gidan ya ce mata dattijai ne kuma kamar almajiran, tabbas ta san fuskokinsu amma ta kasa tuno inda ta san sun. A kan Carpet ta zauna tana bin su da kallo, su kuma sai aikin kalle_kalle suke a parlour'n suna baza ido a lungu da sak'o na cikinsa. Cikin girmamawa ta ce musu. "Sannunku da zuwa." Suka amsa da "Yawwa." Tare da dawo da kallon su gare ta. Ta ce. "Ina yininku?" Suka amsa mata sannan ɗaya daga cikinsu ya gyara zama ya ce. "Ikon Allah, Neehal ke ce kika zama haka? Girman ɗan Mutum babu wahala." Ta yi murmushi kawai. Ya cigaba da magana cikin sanyin murya. "Ga dukkan alamu baki shaida mu ba, amma hakan ba'abun mamaki ba ne bisa ga yadda muka wofintar da rayuwarki duk da kasancewar muna gari guda dake, Neehal Salisu ne da kuma Sani ƴaƴan Baffa mariki'n mahaifanki." Da mugun mamaki Neehal ta ɗago tana kallon su tare da tambayar kanta abun da ya hana ta gane su. Zuciyarta ta bata amsa da cewa 'Tsufan da suka yi mana' wanda ya wuce yawan shekarunsu a duniya, kuma ta manta rabon da ta gan su a, duk da Kawu Musa ya ce sun zo bikinta, amma da yake cikin hada_hada ake bata gan su ba. Cikin tsananin mamaki ta ce. "Kawu Sani da Kawu Salisu?" Kawu Sani ya gyaɗa mata kai. Ruwan hawaye fal cikin idonsa ya ce. "Mu ne Neehal, abun ya baki mamaki ko? Na ganinmu da kika yi a gidanki, mun zo ne mu roqe ki gafara akan abun da muka yi miki ko ma samu sassaucin k'uncin rayuwar da muka shiga, mahaifinki ya riqe mu tamkar ƴan'uwansa da suke ciki ɗaya a lokacin da yana raye haka ma mahaifiyarki, mahaifinki shine komai namu, ya yi mana komai a rayuwar nan, amma saboda butulci da wani tunanin banza da wofi muka wofantar dake ƴarsa ƙwaya ɗaya tal a duniya, muka yarda zumunci muka kasa riqe ki saboda muna gudun wahalar d'awainiya dake. Amma da yake Allah ba azzalumin bawansa ba ne sai gashi Allah ya ɗaukaka ki, mu kuma ya bar mu da iyawar mu, dan Allah Neehal ki yafe mana, wallahi muna cikin tsananin k'uncin rayuwa. Abun da zamu kai bakinmu ma gagarar mu yake, karayar arzik'i Ubangiji ya ɗoro mana lokaci ɗaya, hatta da muhallin da muke rayuwa a cikinsa ba mu tsira da shi ba, yanzu a wani rubab'b'en gidan haya muke tare da iyalanmu, shi ma wani bawan Allah ne ya ji k'an mu ya biya mana kuɗin shekara ɗaya....." Sai ya fashe da kuka.








Neehal Sarkin kuka har ta fara hawaye, ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Kawu ni ba ku yi mun komai ba dama, ko kun mun na yafe muku." Kawu Salisu yana matsar ƙwalla ya ce. "Kayya Neehal, ba iya wannan ne cutar da muka yi miki ba, Mahaifinki kafin ya rasu ya ranta mana wasu kuɗaɗe masu kauri da muka buƙata daga gare shi dan mu ƙara jarinmu, amma bayan rasuwarsa saboda son zuciya irin tamu muka ƙi kawo kuɗin a haɗa a raba muku haqqinku ku iyalansa, muka riqe saboda mun san ba mu da gadonsa, muna baƙin cikin a ce ba mu ci komai ba daga cikin dukiyarsa. Dan Allah ki yafe mana Neehal ko za mu samu sassauci a gurin Ubangiji bayan mutuwar mu." Neehal ta ce. "Na yafe muku Kawu, dan Allah ku bar waɗan nan maganganun komai ya wuce." Bata jira cewar su ba ta miƙe ta kawo musu drinks masu sanyi, ai ko bi takan cups ɗin data kawo ta ajiye musu ba su yi ba suka buɗe robar suka shiga kuk'k'uta. Kitchen ta koma ta ƙarasa girkin da take, ta zubo musu a cikin tire ta kawo musu. Shi ma ba su bi takan spoons ba suka saka hannu duk da tururin da abincin yake suka shiga zabga lauma, kana ganinsu ka ga wanda suke tattare da yunwa. Cikin mintunan da ba su fi biyar ba suka share abincin, suka fara sakin gyatsa. Neehal dai kallon su kawai take cike da tausayawa. Suna wanke hannu suka miƙe za su tafi suna zabga mata godiya, ɗakinta ta shiga ta tattaro duka kuɗin dake hannunta ta fito ta miƙa musu ta ce. "Kawu ga wannan a yi cefene, ku yi haquri bani da enough cash ɗin kuɗi a hannuna, amma insha Allahu cikin week ɗin nan zan zo har gida, sai ku bani address ɗin gidan." Ai kamar za su yi mata sujjada saboda murna da godiya, ita abun ma kunya ya bata. Sai da suka bata address ɗin sannan suka tafi. Tattare kayan gurin ta yi ta kai kitchen jikinta a sanyaye, ta dawo ta gyara gurin ta ƙara fesa room freshener a ɗakin. Hijabin jikinta ta cire ta zauna akan kujera ta fara tunanin rayuwa da yanda al'amuran cikinta suke wakana. Ta tuna su Kawu Salisu a da sanin data yi musu ƴan gayu ne masu ji da kansu, amma ƙarshe ga yanda Ubangiji ya yi da su, ba su da maraba da almajirai gashi duk sun tsofe. Ta tuna Uncle Umar da yanda shi ma rayuwa ta juya masa baya, ga ƴarsa Iman ta haifa masa ɗan gaba da Fatiha, Aunty Fauziyya kuwa ta koma kamar zautacciya saboda tension ɗin rayuwar da take ciki. Ta nuna a baya yanda duk suke jin daɗin rayuwarsu suke yin abun da suka ga dama, a lokacin ba sa tunanin akwai lokacin da zai zo da zasu girbi ABIN DA SUKA SHUKA, shi yasa aka ce a rayuwa ka yi mai kyau sai ka ga mai kyau a gaba. Allah yasa mu dace, Amin.












A haka Ameen ya dawo ya same ta. Ta ɗaga kai a hankali ta kalle shi tare da amsa masa sallamarsa. Ajiye kayan hannunsa ya yi ya tsaya yana murmushi, ta gane mai yake nufi amma sai ta kasa motsawa balle ta tashi ta yi masa abun da yake jira. Ya ƙaraso inda take ya tsugunna a gabanta yana kallon fuskarta ya ce. "What happened Baby?" Ta lumshe idonta kawai bata ce komai ba. With so worry ya ce. "Oh My God, Baby me ya faru? Ko baki da lafiya ne?" Ya shiga tattab'a wuyanta da fuskarta. Girgiza masa kai kawai ta yi. Ya kama hannunta ya ce. "Please Baby tell me abun da ya faru, hankalina ya fara tashi da ganin yanayinki, ko wani abu ya faru da bana nan?" Ta buɗe idonta tana kallon fuskarsa, damuwa ta hango ƙarara a cikinta, sai ta ji tausayinsa ya cika mata zuciya, daga dawowarsa ta saka shi cikin damuwa, haka yake ko yaya ya ga ta ɗan canza yanzu zai rud'e ya yi ta tambayar ta abun da yake damun ta, in ya gan ta a cikin damuwa kuwa rasa inda zai saka kansa ya ji daɗi yake. Hannu ta kai ta fara shafa fuskarsa ta ce. "Babu komai fa Mijina, kewar ka ce kawai take damu na." Ya saki ajiyar zuciya a hankali yana kallon cikin idonta ya ce. "Kin tabbata? Dan Allah idan wani abu yana damun ki Baby ki faɗa mun." Ta ce. "Da gaske fa Dear babu komai." Ya shafi cikinta ya ce. "Sorry My Boy, da na ƙi kula welcoming ɗinka, rigarmar Mamanka ta saka, yau ka hana ta bacci ka rama mana, Daddy missed you too." Murmushi ta yi tana jin yanda yake shafa cikin nata a dukkan jikinta, ta shafi lallausar sumar kansa ta ce. "Dama can ai ba baccin ake bari na in yi ba." Ya ce. "Ban da sharri dai Baby." Sannan ya yi kissing cikin nata, lumshe idonta ta yi tana sauke numfashi. Ya miƙe ya koma kusa da ita ya zauna ya janyo ta jikinsa ya ce. "Baby! Akwai abun da yake damunki wallahi, dan Allah ki faɗa mun, ganin ki a haka yasa gaba-d'aya na rasa nutsuwata." Ta saka hannunta ta rungume shi sosai tana shaƙar ƙamshinsa tare da sakin ajiyar zuciya, tabbas akwai abun da yake damun ta, kuma ba komai ba ne face yanda ta ga su Kawu Sani da halin matsin rayuwar da suka ce mata suna ciki, amma bata san ta ina zata fara faɗa masa ba. Ta fara shafa kafaɗarsa da hannunta ɗaya ta ce. "Da gaske yaya babu komai, Just I'm not in the mood." Ya ce. "Sorry, bari na yi wanka sai mu fita, na san zaki jin daɗin hakan, ina kike son mu je? Gidan Mama ko gidan Aunty ko gidan Aunty Sadiya ko gidansu little Neehal ko gidan Kawu ko wani gurin daban?" Ta ce. "Gidan Mama, daga nan sai mu biya inga namesake ɗina sannan mu je mu sha ice-cream, Gobe sai mu je gidansu Auntyn." Ya shafi kuncinta ya ce. "An gama Gimbiya Sarautar Mata." Ta ce. "Sarautar Ameen dai." Ya ɗago ta ya ce. "Me kika ce?" Ta yi dariya kawai. Ya ce. "Ni ban taɓa jin kin faɗi sunana ba sai yau, ƙara faɗa mu ji ko kin iya." Kafaɗa ta mak'e masa. Ya ce. "Shikenan mu je in yi waka." Ya miƙar da ita sannan shi ma ya miƙe suka shiga ɗakinsa. Ta taimakonta ya cire kayan jikinsa, ya ɗaura towel a k'ugu Sannan ya fara ƙoƙarin cire mata abayar jikinta. Ta riƙe hannunsa tana ɓata fuska dan ta san me yake nufi ta ce. "Ni fa ban jima da yin wankana ba." Ya langwab'e kai ya ce. "Yanzu kuma taya ni zaki yi." Cikin shagwab'a ta ce. "Ai na san ba iya wankan zaka tsaya ba, sai ka saka ni jik'a gashina da yamman nan." Bai ce komai ba ya cire mata abayar, ya janyo ta jikinsa ya kai bakinsa saitin kunnenta ya ce. "To ai ke ce Baby kullum ƙara kyau kike da......." Saurin rufe masa baki ta yi dan ta san me zai ce. Murmusawa ya yi ya ɗauke ta cak ya nufi toilet da ita.......Suna hanyar zuwa gidan Mama ne take sanar masa da zuwan su Kawu Salisu, anan ya gane dalilin damuwartata. Washegari ya tambaye ta address ɗin su Kawu Salisu, ta faɗa masa ba tare da tunanin komai ba. Yana fita ya aika yaransa suka siyo kayan abinci masu yawa ya haɗa musu da kuɗi ya ba su address ɗin su Kawu Sani ya ce sukai musu, bai faɗa mata ba sai daga baya take jin labari wataran ta kai musu ziyara suke faɗa mata, su ma suka ce bai ce a ce in ji shi ba, yaran da suka kawo kayan ne suka kwatanta musu shi anan suka gane shi ne.










Haka rayuwa ta yi ta tafiya, kwanaki na shud'ewa. Mama ta yi nacin Ameen ya mayar da Hafsah amma ya ƙi, ya ce idan ya dawo da ita ya san ba zai yi adalci a tsakanin su da Neehal ba, dan haka gara bai kwasarwa kansa zunubi ba, dan shi a yanzu babu gurbin wata ƴa mace a cikin zuciyarsa, Neehal ta kanainaye ko ina, dama can tun fil azal ita ce a ciki, ya Auri Hafsat ne kawai saboda matsawar da Mama ta yi masa a time ɗin akan ya yi Aure. Ita ma Neehal ɗin tana yawan yi masa maganar ya mayar da Hafsat ɗin ɗakinta, amma duk sanda ta yi masa maganar basa kwashewa ta daɗi, dan fushi yake yi sosai ya ce dama ya san ba son sa take yi ba. Daƙyar take samu ta lallab'a shi ya sauko. Lokacin da cikin Neehal ya shiga wata tara idan mutum ya gan ta sai ya tausaya mata saboda girman cikin, ƙafafuwanta duk sun kumbubbura. Hana ta aikin komai Ameen ya yi, shi yake komai na gidan kafin ya fita, daga baya kuma Aunty A'isha ta turo musu Maryam ɗinta take taya ta zama da aikace_aikace. E.d.d ɗinta saura one week Mama ta je ta ɗauko ta, ta dawo da ita gida. Ameen bai so haka ba amma babu yadda zai yi, sai dai kusan raba dare yake a gidan kafin ya tafi, a hakan ma sai Mama ta kora shi. Neehal tay ta yi masa dariya. Zuwa wannan lokacin Hafsah ta tabbatar Ameen ba zai taɓa dawowa gare ta ba, ta yi kuka ta yi dana sani mara iyaka, daga baya ta haqura ba dan ta daina son shi ba, sai dai fa har a yanzu tsanar Neehal na nan a cikin ranta, musamman da take ganin kamar ita ce silar rabuwar su da Ameen. An yi bikin Hameedah da wani abokin aikinta mai Mata da yake nacin son ta, a da ta ƙi shi sai da taga bata da kowa sai shi sannan ta amince masa, Tunda Ameen ɗin da take nacin so baya ta ita. Neehal bata je bikin ba saboda time ɗin ta yi nauyi sosai. Matar Ahmad ma ta haifi ɗanta Namiji watanni uku da suka wuce, su Afrah an yi k'ani sai murna, yanzu ma kullum cikin murna suke Auntinsu ta kusa ƙara haifo musu new Baby........












Ranar wata Alhamis cikin dare Neehal ta fara jin ciwo a jikinta, kusan kwana uku kenan tana jin jikin nata babu daɗi, amma ciwon na yau ya fi na kullum. Tun tana yi tana daurewa har ta fara nurk'ususu tare da salati, Mama take Sallah ta sallame ta yi kanta. Ganin Haihuwa ce ta kira Daddy a waya ta sanar masa, cikin hanzari ya baro part ɗinsa suka ɗauke ta da su kai asibiti da ita bayan Mama ta ɗauki duk abun da ake buƙata, Asibitin Nasarawa suka je inda Maman take aiki, dama a can take yin awu. Haka kawai Ameen ya ji ya kasa bacci a daren ranar, sai tashi ya yi ya yo alwala ya shiga yin Sallah. Mama da kanta ta karb'i haihuwar Neehal, sai kusan asuba Allah ya sauke ta lafiya ta santalo Ƴaƴanta Maza guda biyu masu tsananin kama da mahaifinsu. Ba tare an goge musu jiki ba Mama ta rungume su idonta cike da ƙwallar farinciki, sannan ta ɗorawa Neehal su duka akan cinyarta. Neehal tana kallon su ta ji gaba-d'aya zafin wahalar labour da ta sha ta gushe daga cikin zuciyarta, wata zazzafar k'aunar yaran ta maye gurbin su. Mama ta lek'a ta faɗawa Daddy ta ce ya kira Ameen ya sanar masa. Kiran sa Daddy ya yi ya ce masa ya zo suna asibiti Neehal ta haihu, ba tare da ya faɗa masa abun da ta haifa ba. Ga mamakin Ameen sai ya ji hankalinsa ya tashi, mukullin Motor kawai ya ɗauka ya fice cikin sauri. Sam zuciyarsa bata ta Babyn da ka haifa tana ga Neehal, so yake kawai ya gan ta ya ga halin data ciki, ya ga lafiyar jikinta.










Neehal tana kwance a ɗakin hutun da aka kaita ita kaɗai, Mama da Daddy suna can tare da Babies ɗin. Ameen ya shigo ɗakin kamar an jefo shi, ya ƙarasa gaban gadon ya kama hannunta yana kiran sunanta cikin damuwa. Bacci ya fara ɗaukar ta hakan yasa daƙyar ta iya buɗe idonta ta kalle shi. Ya ce. "Baby kina lafiya? Ya jikin naki? Mene yake miki ciwo yanzu? Kin sha wahala ko? Sannu Allah ya yi miki albarka." Ta ɗaga hannunta a hankali tana murmushi ta shafi sajen fuskarsa ta ce. "Yaya me yasa baka zo ba, ina ta kiran ka ina son na gan ka." Ya ƙanƙame hannunta a cikin nasa ya ce. "Ban sani ba ne Baby, ban san kina labour ba wallahi, da sai na zo mun yi tare, Mum bata faɗa mun ba." Ta ɗora hannunsa akan cikinta cikin shagwab'a ta ce. "Na sha wahala fa sosai Yaya, haihuwa akwai wahala, ni bazan kuma ba, karka kuma mun ciki ka ji." Ya kwantar da kansa akan ƙirjinta ya ce. "Sorry Baby, Allah ya saka miki da gidan Aljannah, sannu kin ji, yanzu ina ne yake miki ciwo?" Ta ce. "Duka jikina da kaina, more especially cikina." Kamar wanda aka tsikara ya ɗago kansa ya ce. "Sannu Allah ya baki lafiya, insha Allahu zaki samu lafiya soon." Ta gyaɗa masa kai. Ya shiga shafa cikinta ya ce. "Ina Babyn da kika haifa? Mece ce ko Namiji?" Kamar amsar tambayarsa sai ga Mama ta shigo ɗakin rungume da Baby, ya miƙe da sauri ya karb'e shi, Mama ta ce. "Ka jira ai in baka ko?" Ya yi murmushi tare da sakin wata kakkafar ajiyar zuciya, rungume yaron ya yi kam a ƙirjinsa cikin tsananin farin ciki. Ya koma ya zauna a gaban Neehal ya zubawa yaron ido kamar zai cinye shi yana murmushi, cikin ransa kuma yana godiya ga Allah. Mama ta miƙa masa dabino da Zamzam ta ce. "Ka tauna ka ba shi tare da ruwan, ka kuma yi masa addu'a ba kallo kawai ba." Neehal ta yi murmushi, Ameen ya yi kamar yadda Mama ta ce. Ya ɗago ya kalle ta ya ce. "Mum me yasa baki kira ni ba da tana labour?" Mama ta ce. "In ka zo me zaka yi?" Ya ce. "Addu'a mana." Mama ta ce. "Yanzu dai tunda ta sauka lafiya shikenan." Shigowar Daddy dake ɗauke da ɗayan Babyn ne ya hana shi magana. Ya saki baki yana kallon sa, Daddy ya ƙaraso ya miƙa masa Babyn yana murmushi ya ce. "Ga Al_hussain nan." Waro ido Ameen ya yi ya ce. "Dad! Twins ta haifa?" Sai kuma ya juya ya kalli Mama. Ta gyaɗa masa kai tana murmushi. Matsar da na hannunsa ya yi Daddy ya ɗora masa ɗayan akan cinyarsa, ya haɗa su duka ya rungume cikin tsananin farin cikin da bazai misaltu ba, yana ƙara godiya ga Allah da wannan baiwar da ya yi masa." Ya yi mintuna uku a haka sannan ya miƙa wa Daddy Al_hassan ya yiwa Al_hussain addu'a kamar yadda ya yiwa Al_hassan. Ya sunkuya dai-dai

Please Login or Register in order to submit comment