Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da yin gaban kamar yadda ta ce.






Sadik ne ya buɗe musu ƙofar part ɗin suka shiga bakunan su ɗauke da Sallama, kan Neehal a ƙasa, da ƙyar take iya d'aga ƙafarta, sosai take jin wata irin kunya tun ba ta yi tozali da surukan nata ba. A ƙasan carpet suka zauna dukan su. Afrah tana kallon falon ta ce "Uncle Sadik gidanka ne nan?" Ya kamo hannunta yana murmushi ya ce "Gidanmu ni da my Family ne." Neehal ta janyo ta tana hararar ta, ta zaunar da ita a gabanta. Sadik ya zauna a kusa da ita ya ce "Me tay miki kuma?" Kamar zata yi kuka ta ce "Ni dai ka tashi daga kusa da ni dan Allah kar Maamah ta fito." Ya tashi yana mata dariyar tsokana, sannan ya nufi ɗakin Maamah. Tare suka fito shi da Batul da Maaman, cikin fara'a Batul ta tarb'e su, suka gaisa. Maamah ma da fara'a ta zauna a Falon, suka gaishe ta cikin girmamawa. Daga yanda kan Neehal yake ƙasa Maamah ta gane ita ce sirikar ta_ta, and 100 💯 ta yaba da Neehal a matsayin surukarta. Batul ta cika musu gaban su da kayan ciye_ciye da na sha, wanda aka tanada domin su. Maamah ta ja su Afrah ɗakinta dan yaran sun burge ta ba kaɗan ba, gashi ba su da wahalar sabo. Maryam da Salma ne kawai suka ci abubuwan da aka kawo musu, amma Neehal ƙin ci ta yi, duk da Maamah ta bar falon, Batul ma korar ta Sadik ya yi duk dan Neehal ta sake amma ta ƙi sakin jikinta. Sadik ya dawo kusa da ita ya zauna ya ce. "Ki ci abincin mana Wifey, Maamah fa da kanta ta yi girkin nan musamman dan ke, ko in baki a baki?" Ya ƙarashe zancen da kashe mata ido. Ta harare shi dama ciki take da shi, ya nuna wa Maamah ita sai ka ce haka aka ce masa ana yi. Da ƙyar ta kurb'i juice ɗin da ya zuba mata a cup, ganin yanda ya wani marairaice mata. Kafin su tafi Abban Sadik da yake yana gari ya zo sun gaisa cikin fara'a da nuna jin daɗin ganin su. Umma ma ta zo sun gaisa ita ƴaƴanta ƴan'mata guda biyu, su kay ta satar kallon Neehal kuwa, amma duk kallon nasu ba su ga makusa a jikinta ba. Sai kusan Magriba suka tafi, Maamah ta sa Batul ta juye musu Gaba-ɗaya sauran kayan ciye_ciyen da suka bari, Abba kuma ya bawa su Afrah kuɗi wanda da farko ƙin karɓa su kay, sai Sadik ne ya karɓar musu. Sosai Abba ya yaba hankali da tarbiyya gami da kunyar Neehal. Suna fita Batul ta ce, "Gaskiya Yaya ya iya zaɓen mata, mai kyau da kunya." Maamah ta yi murmushi cikin jin daɗi, Umma kuwa tab'e baki ta yi. Gidan Aunty A'isha Sadik ya mayar da su, bayan ya shigar musu da kayan ciki, Neehal ta rako shi bakin Mota tana ɓaɓɓata fuska. Ya shiga cikin motar, amma ya bar murfin a buɗe ya ce mata, "To ba mun baro gidan Maaman ai, ki saki jikinki mana." Ta turo baki ta ce "Ina ruwanka da ni, ai mun ɓata." Ya marairaice ya ce "Ni ɗin Wifey, Please ki yi haquri na tuba." Ya ƙarashe zancen yana haɗa hannunsa biyu guri ɗaya. Ta kalli fuskarsa wadda take bayyana farincikin da zuciyarsa take ciki a yau. Ta ce "Sanda ka bani kunya a gaban su Maamah ai baka san da haqurin ba." Da ƙyar dai ya lallaɓa ta, ta haqura suka yi sallama. Bayan ya mata godiyar zuwa gaishe da su Maamah. Ana yin Sallar Magriba suka bar gidan Aunty A'isha, saboda Salma da zata wuce gida. Suna zuwa gida Salma ta fara bawa Mama labarin irin kyakkyawar tarb'ar da suka samu a gidan su Sadik, Mama ta ji daɗin hakan sosai. Salma bata jima ba ta tafi bayan Mama ta cika ta da Alkhairi, Neehal ma ta bata turaruka da sabbin undies.








Ranar Sunday kamar yadda Ahmad ya faɗa da hantsi ya sauka a Kano a gidan Mama. Neehal tana bacci su Afrah suka tashe ta cikin murna. Ta tashi da ƙyar dan bata jima da kwanciya ba, suka sanar mata Daddy ya zo. Sai ta ji gabanta ya faɗi, dan har yau ba su kuma magana da shi ba, tun ɗan chat ɗin nan da sukay ta message. Ta tashi ta shiga toilet ta wanke baki da fuska, sannan ta fito ta ɗauki Hijabi ta fice. A falon sama ta gan shi yaransa a jikinsa suna masa surutu. Ta zauna akan carpet kanta a ƙasa ta ce "Sannu da zuwa Uncle." Ya d'ago ya dube ta cike da d'okin ganin ta, ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani sanyi na ratsa zuciyarsa. Sauke su Afrah ya yi daga jikinsa ya ce su tafi gurin Mama, sannan ya sauko daga kan kujerar da yake ya zauna a kusa da ita. "Princesss!" Ya kira sunanta a hankali. Ba tare da d'ago kanta ba ta ce "Na'am." Ya lumshe ido ya buɗe ya sauke su akan fuskarta ya ce "I missed you so much." Ta d'ago ta kalli fuskarsa itama saboda azalzalar da zuciyarta take mata akan hakan, ta yi murmushi ba ta ce komai ba. Ya tallafi fuskarsa da hannunsa ɗaya ya ce, "Wow, Princess kin ƙara kyau, Please karki daina mun wannan murmushin." Kamar zuga ta ya yi sai ta ɓata rai tare da ɗauke kanta daga gare sa. Cikin damuwa ya ce "Why Princess?" Ta turo baki ta ce "Babu komai." Ya ce "No, akwai Princess, tell me what happened? Bana son na gan ki cikin damuwar nan." Ta yi shiru, ya kamo hannunta ya ce "Please." Ta k'wace hannunta ta ce "Ba kai ne ka daina kula ni ba, yanzu ma na san dan su Afrah ka zo ba dan ni ba." Ya yi shiru yana kallonta, yana tunanin abun da yasa yay mata hakan ko kuma ya ce sukai wa juna." A hankali ya ce "Ke kika fara daina kula ni Princess, idan baki manta ba ranar dana tafi na kira ki da daddare Twins suka ɗauka, nay ta jiran kiran ki idan kin dawo tunda sun ce mun ba kya nan, amma baki kira ni ba, dana kira da safe kuma sai na ji Twins ne suka ɗauka again. That is why na ƙyale ki, may be haka kike buƙata, i thought ina takura miki ne. But I'm sorry." Sai ta ji bata kyauta masa ba, amma ita kunyarsa ce tasa ta yi haka, yanzu ma kawai daurewa ta yi har ta iya kallon sa bisa tilastawar zuciyarta. Ta marairaice ta ce "Ka yi haquri Uncle." Ya yi murmushi ya ce "Babu komai Princess, Princess bata taɓa laifi a wajen Uncle ɗinta." Cikin shagwab'a ta ce "Kuma ni baka takura mun ba." Ya ce "To me yasa kika daina kula ni?" Ta juyar da kai gefe ta ce "Kunyar ka nake ji, ban san ta yaya zan maka magana a time ɗin ba." Ya matso ya juyo da fuskarta ya ce "Let me hug you, sai ki daina jin kunya ta." Ta ja baya da sauri kamar zata yi kuka ta ce "Ai na daina since." Ya yi murmushi yadda duk ta tsorata ya ce "Shikenan, amma idan kika ƙara mun haka, i know what I did." Ta kawar da zancen da faɗin, "Ya su Ummi?" Ya ce "Suna nan k'alau, Mamy ta ce "Kun je gidanta jiya." Ta ce "Uhm." Sai kuma ta shagwab'e fuska ta ce "Wai dagaske tafiya zaka yi da Twins yau?" Ya ce "Eh mana, Gobe za su yi resuming School, hutun nasu babu yawa 2 weeks ne kawai." Ta ce "Shikenan, but i will miss them." Ya ce "Ki bi mu, mu tafi tare." Ta ce "Soon, Insha Allah zaku ganni, Relatives ɗin Dad ma suna ta complain bana zuwa." Ya ce "I was so surprised fa, ace kin zauna a Abuja for some years amma Allah bai taɓa haɗa mu ba." Ta ce "To ai bana fita, daga gida sai School, in kuma zan fita tare da Mama ne." Ya ce "Haka ne, Mummy's girl." Sai ta yi murmushi, ta tuno Ameen saboda shi yake yawan faɗa mata haka. Sai bayan Azhar suka tafi suka bar Neehal cikin kewar su, su ma yaran kuka suka saka da za su tafi, wai sai da ita za su tafi. Da ƙyar Ahmad ya lallashe su ya ce zata biyo su itama soon.












*A WEEK AFTER*










Ranar Friday da safe Mama tana gyaran part ɗin Daddy Ameen ya kira ta a waya, ta ɗauka suka gaisa, daga yanda ta ji muryarsa ta san ba k'alau ba. Ta ce "Ya jikin Hafsan?" Cikin damuwa ya ce "Muna asibiti Mum, ta yi Miscarriage." Mama ta ce "Subahanallahi, yaushe?" Ya ce "Cikin daren jiya." Cikin jimantawa da damuwa Mama ta ce "Allah ya bata lafiya, yanzu tana ina?" Ya ce "Hospital." Mama ta ce "Wanne?" Ya faɗa mata wani private Hospital ne dake kusa da su." Mama ta ce "Bari ta shirya ta zo." Daga haka su kay sallama. Ta kira Daddy ta faɗa masa, sannan ta ƙarasa aikin da take cikin sauri ta shirya ta tafi ita kaɗai, tunda Neehal tana wurin aiki.








Jikin Hafsan da sauƙi ta tarar da ita, tunda tun daren jiyan akay mata ƙarin jini da wankin ciki. Tana kwance akan gadon marasa lafiya, sai mahaifiyarta da mahaifinta a ɗakin. Mama tay mata ya jiki, suka gaisa da parent ɗin nata cikin fara'a da mutunta juna. Kusan wuni Mama ta yi a Hospital ɗin tare da mahaifiyar Hafsah, Daddy ma ya zo ya duba ta da rana, da yamma kuma su Aunty A'isha da Aunty Sadiya suka sun zo. Mama ta kira Driver ya kawo su Dije tare da abincin data saka su, su girka. Ƴan'uwan su Hafsat ma suna ta zuwa duba ta. Tun zuwan Mama ta fuskanci Ameen yana cikin damuwa da b'arewar cikin Hafsat, ko tantama bata yi ya k'walla fa ransa akan cikin ne Allah kuma ya yi ba mai fitowa doron ƙasa ba ne. Tay masa addu'ar Allah ba su wani. Sai can yamma Mama ta dawo gida, lokacin Neehal itama bata jima da dawowa ba. Mama ta sanar mata abun da ya faru, ta ji ba daɗi sosai akan barewar cikin itama, dan duk sun san Hafsan na da ciki, har tana ta murna a ranta sun kusa samun new Baby. A daren ranar aka sallame su Hafsah, mahaifiyarta ta so tafiya da ita gida amma Ameen ya nuna bai so hakan ba, Mahaifin Hafsah kuma ya goya masa baya, ya ce tunda jikin nata da sauk'i ta wuce gidanta kawai. Dole mahaifiyar ta_ta, ta haqura, ta ce zata samo mata dattijuwar da zata na kula da ita har ta samu sauƙi, kamar wata wadda ta haihu, bayan kuma already tana da masu aiki ƴan'mata har guda biyu.








A daren Mama tana part ɗin Daddy suna hira ya ce mata. "Son fa ya kira ni d'azu in nemar masa alfarma a gurin ki." Mama ta ce "Alfarmar me?" Ya ce "Wai Daughter yake son ki ba su ta je ta musu ɗan kwana biyu, kafin Hafsah ta gama warwarewa." Mama ta ce "Ba tana da masu aiki ba, me kuma Neehal zata je tay musu?" Daddy ya ce "Kin san ɗan naki, ba ya cin abinci masu aiki." Mama ta ce "Ohh girki zata je tana yi masa kenan? To ban yarda ba, idan dan abinci ne zan na badawa akai musu." Daddy ya ce "Dama sai da ya ce mun baza ki bari ba, shi yasa ma ya kira ni, in lallame ki, ki barta ta je Doctor, kin ga akwai abubuwan da dole masu aiki baza su iya yi masa ba tunda matarsa bata da lafiya, amma ita Neehal ɗin zata iya masa." Mama tay shiru, Daddy ya ce "A taimaka mana ƴar Amaryata." Ya ƙarashe zancen da dariya. Mama ta ce "Ka ce mun amarya mana tunda zaku yaudare ni kai da ɗanka." Ya yi dariya sosai ya ce, "Yanzu dai kin bari ya zo ya ɗauke ta da safe? Just 1 week za ta yi ta dawo." Mama ta ce "Ka san ba zan iya har 1 week babu ƴata a gabana ba." Ya ce "Idan kuma da Allah yasa an yi auranta fa?" Ta ce "Aure daban, wannan na san gidan miji na kai ta ba gidan Ameen da basa shiri ba, Neehal rigima da shiririta shi kuma masifaffe, ta yi abu kaɗan ya rufe mun ƴa da masifa, na yarda dai tay musu kwana biyu ta dawo." Daddy ya ce "To hakan ma, mun gode, bari na kira shi na sanar masa.










Washegari wajen ƙarfe tara na safe Neehal tana breakfast a ɗakin Mama. Maman kuma tana karatun Alkur'ani mai girma, bayan ta kammala ta ce "Ki yi ki gama uwar janjani, Ameen zai zo ya ɗauke ki, ki je gidansa ki musu kwana biyu." Neehal ta d'ago da sauri har tana k'warewa ta ce "Mama kwana biyu kuma?" Mama ta ce "Eh, kin ga Hafsan bata da lafiya, zaki ɗan taimaka mata da wasu ayyukan, ita kuma ba k'annena ba bare su je su taya ta." Kamar zata yi kuka ta ce "Amma Mama tana da masu aiki fa." Mama ta ce "Ki je dai Neehal, mene in kin je kin taimaka mata, Dad ne da kansa ya ce ki je." Neehal ta fara hawaye tare da ture abincin gabanta, ita ba zuwan ne damuwarta ba, yanda zata zauna gida ɗaya da Ameen har na wasu kwanaki ne damuwarta, dan tun ranar da ta dawo daga gurin Sadik suka haɗu a bakin part bata ƙara bari sun haɗu ba, wasan b'uya take da shi, saboda tsoron punishment ɗin da ya ce zai mata. In ya zo gidan tana nan har ya tafi bata fitowa daga ɗakinta. Tana matsar hawaye ta ce "Mama aikina fa, kin ga ban jima da komawa ba, kuma ina siwes." Mama ta ce "In kin je can ɗin ma zaki na zuwa ba wai daina zuwa zaki ba, kina gama ayyukan ki sai ki tafi, idan Ameen ɗin yana gida da kansa ma zai dinga kai ki." Ta saka kuka ta ce "Ni dai Mama....." Mama ta haɗe rai ta ce "Bana son iskancin banza, mene a gidan Ameen ɗin da baki son zuwa? Ko yayyanka naman jikinki za'ai in kin je? Ki tashi ki je ki yi abun da na ce, tunda kin gama cin abincin. In kuma ban isa ba ne to." Ta tashi tana kuka ta fice daga ɗakin. Mama ta bi ta da kallo, tana sane da su kwana biyu ita da Ameen ɗin, da wasan b'uyan da take da shi, shi kuma idan ya zo gidan ya dinga baza ido kenan yana neman ta inda zata ɓullo. Ta girgiza kai tare da yi musu addu'ar shiriya a cikin ranta.........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*5️⃣5️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
















...........Tana Kuka ta janyo small trolley ta zuba kayanta da bata ma tsaya zab'a ba kawai buɗe wardrobe ta yi ta kwaso. Ta saka hijabai guda biyu a ciki ta zuge. Ta ɗauki wani ta zira a jikinta, ta koma bakin gado ta zauna tana cigaba da kukan ta. A haka Mama ta shigo ta same ta. Cikin takaici Mama ta ce "Neehal kukan ne har yanzu kamar wadda akaiwa wani mugun abun, haka zaki je gidan mutane kina musu kuka?" Ta yi shiru tare da daina kukan. Mama ta tab'e baki ta ce "Ki fito yana falo yana jiran ki, kuma ki cigaba da kukan kin san halinsa dai." Ta goge hawayen fuskarta ta ce "Ki yi haquri Mama na daina." Mama ta ce "Allah ya shirya mun ke, ya nuna mun ranar da zaki girma ki daina wannan kukan, ko jariri haka ya gan ki ya bari a kuka Neehal." Ta turo baki ba ta ce komai ba, ta miƙe ta kwashi wayoyinta ta zuba a small handbag. Mama ta kama hannunta ta ce "Ki saki ranki mana Daughter, ko kuma kin fi so idan kewarki ta dame ni in dinga tuno fuskarki a cukule." Ta yi murmushi saboda yanda Maman ta yi magana. Itama murmushin ta yi ta shafa kuncinta ta ce, "Je ki wanke fuskarki maza ƴar albarka ta." Ta gyaɗa mata kai tare da tashi ta shige toilet. Mama ta miƙe ta fita, a falo ta tarar da Ameen zaune inda ta bar shi. Ta zauna a kusa da shi ta ce "Gata nan zuwa, saura kuma a dinga ci mun zalin yarinya idan an je." Ya yi murmushi ya ce "Ƴar taki ce bata ji ai ba daga ni ba ne." Mama ta ce "Ni dai na faɗa maka, inna ji ba dai-dai ba da kaina zan zo in ɗauke ƴata." Ya ce "Baza ma ki ji ba Insha Allah." Dai-dai nan Neehal ta fito daga ɗaki tana jan trolley, Ameen ya bi ta da kallo. Ba tare data kalle shi ba ta ce "Ina kwana." Ya ce "Lafiya." Tare da miƙewa ya karb'i trolley'n hannunta ya fice daga falon. Ta dubi Mama ta ce "Daddy ya fita ba mu yi sallama ba." Mama ta ce "Sauri yake ne, amma ya ce idan ya dawo da daddare zai zo har gidan Ameen ɗin ya gan ki." Ta shagwab'e fuska ta ce "Please Mama ku zo tare." Mama ta ce "To Allah ya kai mu, make sure dai kin ɗauki komai na zuwa gurin aikin ki?" Ta girgiza kai tare da faɗin. "Mama wai kwana nawa zan yi ne?" Mama ta ce "Just 2 days." Ta gyaɗa mata kai sannan ta juya ta koma ɗakinta, ta ɗauko laptop ɗinta da duk wani abu da zata buƙata a gurin aiki, sannan ta fito. Mama ta bata kuɗi ko zata buƙata, ta ce mata a'a ta ɗauki ATM ɗinta, idan tana buƙata zata ciro. Har waje Mama ta raka ta, amma iyakacin ta bakin part ɗinta ta koma. Gabanta na fad'uwa ta nufi parking space inda ta san yana jiran ta, a hankali take tafiya har ta ƙarasa. Kafin ta ƙarasa gurin Motarsa ya buɗe ya fito ya buɗe mata baya, ba tare da ya ce komai ba ya karb'i laptop ɗin hannunta ya saka a bayan Motar, ya mayar ya rufe sannan ya buɗe mata gaban Motar. Cikin mamaki take kallon sa zuciyarta cike da tsoro, gani take kamar wani abun yake shirya mata na punishment ɗin da ya ce zai mata, sai ta kasa shiga Motar. Ya haɗe rai amma cikin sanyin murya ya ce "Ko sai na ɗauke ki na saka ki ne?" Ta kalle shi ta turo baki sannan ta shiga Idanunta cike da k'walla. Ya zagaya ya shiga mazaunin driver, ya yi looked Motar sannan ya kunna ta ya yi reverse suka fice daga gidan. Ta lumshe idonta tare da kwantar da kanta a jikin kujera. Ji take kamar garin zata bari saboda damuwa, dan ita bata taɓa yin tafiyar kwanaki ba tare da Mama ba, and kuma tana tunanin yadda zata yi kwanaki a gidan matar da bata k'aunarta ko kaɗan, Matar dake mata fuska biyu a gurin Yayanta da Mamanta. Har suka je gidan babu wadda ya yi magana a cikinsu, sai karatun Alkur'ani ne yake tashi a cikin Motar. Ta buɗe idonta jin Motar ta tsaya, idanunta suka sauka a cikin nasa saboda juyowa ya yi sosai yana kallonta, harara ta yi tsammanin samu daga gare shi amma sai ta ga saɓanin haka, wani tattausan murmushi ya sakar mata, murmushin da tun tana yarinya yake matuƙar burge ta, kuma bata tunanin akwai na biyun shi a kyau a idonta. Ta mayar da idonta ta lumshe cikin jin bugun zuciyarta na sauyawa, gaba-ɗaya ya juye mata ya koma Mamanta data baro a gida, kamar Ameen da Mama ta ɓaci, babu abun da ya baro nata, hatta yanayin kallon su iri ɗaya ne, the only difference is shi Namiji ne ita kuma mace ce. A hankali ya ce "Cry cry girl, kukan ne dai?" Ta buɗe ido tare da turo baki gaba ta ce "I start missing my Mum." Ya ce "Sorry, ai taimakon mu zaki yi Mummy's girl." Ta ɓata fuska ba ta ce komai ba, shi ma bai kuma magana ba ya buɗe Motar ya fita, itama bin bayan shi ta yi ta fito hannunta riƙe da handbag ɗinta. Ya buɗe bayan Motar ya ɗauki laptop ɗin sannan ya fara tafiya ta bi bayan sa. Babu kowa a falon ƙasan da suka shiga, amma fess yake a gyare sai tashin k'amshi yake, sama ta ga ya hau hakan yasa itama ta bi bayan sa. Bedroom ɗin Hafsah ya shiga ita kuma ta zauna a falo, ba jimawa ya fito ya ce ta shiga ɗakin. Ta tashi ta shiga a tunaninta Hafsan tana ciki, amma sai ta ga babu kowa, ga laptop ɗinta ya ajiye mata akan bedside locker. Ta zauna a bakin gado tana bin ɗakin da kallo, dan bata taɓa shigar sa ba sai yau. Knocking ƙofar da akai yasa ta tashi ta je ta buɗe, ɗaya daga cikin masu aikin gidan ce, cikin girmamawa ta gaishe da Neehal sannan ta bata trolley ɗinta tana faɗin. "Gashi mai gidan ya ce akawo miki." Ta karɓa tare yin murmushi ta ce "Na gode." A ɗakin Hafsat zata zauna kenan? A fili ta ce "Lallai ma Yaya." Sai kuma ta tab'e baki da ta yi tunanin wani abu. Tana ajiye trolley'n ya turo ƙofa ya shigo da sallama, ta amsa masa, ya dube ta ya ce "Ki zo ku gaisa." Ba ta ce komai ba, dan ta gane wadda yake nufi, ta fito ta biyo bayan sa suka shiga ɗakinsa, Hajiya Hafsat na kwance akan gado idanunta akan ƙofa. Already ta san da zuwan Neehal gidan dan Ameen ɗin ya sanar mata tun jiya, kuma ko kaɗan bata ji daɗin hakan ba, babu yanda zata yi ne kawai. Neehal ta ƙarasa bakin gadon ta ce "Ina kwana Aunty Hafsah, ya jikin?" Cikin fake smiling Hafsah ta ce "Lafiya k'alau sisina, ai na yi fushi tunda sai yau zaki zo duba ni, da haihuwa na yi ma sai Babyn ya kwana sannan zaki zo ki gan shi ko?" Neehal ta saci kallon Ameen da ya zauna a kusa da matarsa ta ce "A yi mun afuwa Aunty, na je gurin aiki ne, sai bayan da Mama ta dawo take faɗa mun abun da ya faru, I hope dai jikin naki da sauƙi." Hafsah ta ce "Jiki da sauƙi, Welcome, Yaya ya ɗauko ki zai wahalar wa da Mama ke da aiki ko?" Ta ƙarashe zancen da kallon Ameen, yay mata wani kallo bai ce komai ba. Neehal ta yi murmushi ta ce "Babu komai Aunty, mene abun wahala a aikin gida?" Hafsah ta ja tsaki a ranta cikin tsanar Neehal ɗin, maganar nan da suke yi ma daure zuciyarta kawai take yi, tsanar yarinyar kullum ƙaruwa take a ranta, ko dan yanda Ameen yake nuna caring a kanta ne? Gashi duk ganin da zatay mata sai ta ga kamar ƙara kyau take, ga iyayi a idan tana magana, ita a dole mai class. Ta ja ɗan ƙaramin tsaki ba tare da ta san a fili ta yi ba tare da yamutsa fuska, kallon da Ameen yay mata ne ya fargar da ita, ta taune lip ɗinta tare da dafe cikinta dan ya yi tunanin ciwon cikin ne ya sata tsakin. Ya ɗauke idonsa daga kanta a kallon da yake mata data rasa yaren da zata fassara shi, shi ba kallon tuhuma ba shi ba na gargadi' ba. Neehal ta ce "Sannu Aunty, ko kina buƙatar wani abun ne?" Hafsah ta girgiza mata kai alamar a'a. Ta ce "Allah ya sauwaqe." Sannan ta da juyawa ta fice daga ɗakin. Hafsah ta

Please Login or Register in order to submit comment