Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cire cikin sauƙi ta samar masa. A hankali ya kama hannunta dake kan cinyarta ya riƙe tare da sakin wata sassanyar ajiyar zuciya, ƙamshin jikinta ya fara tasiri a gare sa, riƙe hannunta da ya yi ya zo mata a bazata har ƴar zabura ta yi tare da ƙara yin ƙasa da kanta. Ya damƙe hannun nata sosai a cikin nasa jin tana ƙoƙarin zare shi, cikin wata sassanyar murya mai daɗin amo mai kama da raɗa ya ce. "Welcome home my bride." Ta turo baki a hankali maganarsa na yi mata yawo a cikin zuciyarta da kwanyarta, kalmar *my Bride* ɗin da ya furta ta fi komai bata mamaki, da kuma yanda ya yi mata magana cikin sanyi da wani irin salo. Ya yi murmushi mai sauti tare da kai ɗayan hannun nasa ya ɗago haɓarta, ta yi saurin lumshe idonta tana jin zuciyarta kamar zata faso ƙirjinta ta fito saboda bugu, yanayin da take jin kanta da zuciyarta ba zai misaltu ba, ita kanta ta kasa tantance yanayin da take ciki, kafin ya shigo ta san tsoro da fargabar ganinsa da kasancewar da za su yi a gida ɗaya take, amma yanzu da ya shigo inda take yake tsugunne a gabanta sai ta ji wani baƙon al'amari a game da shi a cikin zuciyarta. Tana jin yanda ya ƙurawa fuskarta ido yana kallon ta ko kiftawa babu a jikinta, sai ta ji ita ma zuciyarta tana azalzalarta da ta buɗe idonta ta kalle shi, duk yanda ta so bijirewa daga umarnin zuciyarta amma zuciyar ta ƙi bata goyon baya, bata ma san lokacin data buɗe kumburarrun idonta da suka ci kuka suka ƙoshi ba ta zuba su akan kyakkyawar fuskarsa da gangar jikinsa a lokaci ɗaya, amma bata bari sun haɗa ido ba. Sanye yake cikin wani tsadadden yadi milk colour, kansa sanye da hula, duk da bai fiya sakawa ba amma ta yi masa kyau sosai. Yanda ya kafe ta da ido yasa ta kallon nasa idon ita ma, hakan ya ƙara mata jin abun da take ji a cikin ranta, ta yi saurin janye nata idon saboda wasu abubuwa da take gani suna shiga nata idon daga nasa masu kaifi suna ƙoƙarin fasa mata zuciya. Ta lumshe idonta a hankali hawaye ya zubo daga cikinsu tare da ƙoƙarin cire hannunsa daga kan fuskarta saboda yanda ta ga yana yi mata wani irin kallo da ya kashe mata jiki. Ya shafi kuncinta cikin sanyin murya ya ce. "Cry cry baby, kukan barin gidan Mama ne ko na zuwa gidan Ameen?" Ta turo baki tare da cire hannunsa daga fuskarta, amma ko 2 second ba'a yi ba ta ji hannun nasa a gefen wuyanta yana shafawa cikin wani irin salo, hakan yasa ta ji tsigar jikinta ta fara tashi, wani abu da bata san ko mene ma yana yawo a cikin jikinta, kawai sai ta saka kuka tare da ja baya, yanayin da zuciyarta da gangar jikinta suke ciki bazai misaltu ba, ta rasa ya zata yi, ta rasa ina zata saka kanta. A hankali ya ce. "God! Kukan dai miemerh, Please ki daina kukan nan, na ji jikinki da zafi kar zazzaɓi ya rufe ki, kuma na san wannan kukan da kika sha kanki sai ya miki ciwo." Cikin shagwabarta ta ce. "Ni bacci nake ji." Ya ɗan yi murmushi sannan ya miƙe ya ce. "Ni kuma na hana ki ko? To ki bar kukan haka, indai ni ne na tashi, amma kafin ki kwanta ya kamata ki ci wani abu ki sha magani." Ta turo baki ta ce. "Ni na ƙoshi bacci kawai zan yi." Bai ce komai ya matsa daf da ita sannan ya ɗora goshinsa akan nata ya ɗora hannunsa a ƙirjinta saitin zuciyarta ya ce. "Wannan bugun zuciyar duk na tsoron mene ne?" Ta ja wani gwauron numfashi ta sauke tana jin abun da bata taɓa ji ba a tsahon rayuwarta a dalilin kusancin da suka samu, ga ƙamshinsa dake ƙarawa zuciyarta hauhawar yanayin da take ciki. Ta runtse idonta numfashinta na fita da sauri da sauri. Ya janye fuskarsa daga ta_ta, yana kallon tsoro ɓaro_ɓaro akan fuskarta_ta, ajiyar zuciya ya saki a hankali tare da jan gwauron numfashi. Ta ƙara jan mayafinta ta lullub'e jikinta. Ya yi murmushi kawai wanda ya kasa b'acewa daga fuskarsa tunda ya shigo ɗakin sannan ya juya ya fice. Ta sauke ajiyar zuciya tare buɗe fuskarta ta bi ƙofa da kallo, a ranta tana mamakinsa yanda yake mata magana da wasu abubuwan. Bayan kamar 15 minutes ya dawo ɗakin, saurin rufe idonta ta yi tana keɓe fuska, ya ajiye ledodin hannunsa sannan ya juya ya ƙara fita, bai jima ba ya dawo hannunsa ɗauke da tire da glass cup da fork. Ya d'auko kaza ɗaya dake cikin ɗaya daga cikin ledodi biyun da ya ajiye ya saka a cikin tiren sannan ya kalle ta ya ce. "Oya come and eat." Ta mak'e kafaɗa alamar a'a. Ya miƙe ya ce. "Okay, idan baki sauko ba kin san dai baza ki gagare ni ɗauka ba ko?" Jin haka yasa ta buɗe idonta da sauri tare da ja baya, kamar zata yi kuka ta ce. "Ni fa Yaya na ƙoshi Allah." Ya kalle ta na wasu sakanni ba tare da ya yi magana ba ya tunkari gadon, da sauri ta sauko tana cize lip saboda ciwon kai idonta cike fal da hawaye. Ta zauna a gaban tiren tana turo baki gaba. Ya dawo ya zauna shi ma a kusa da ita, ba tare da ya yi magana ba ya saka fork ya gutsiro naman ya kai bakinta, ta kawar da kanta gefe, ya saka hannu ya juyo da fuskarta tare da haɗe da rai yana yi mata kallon warning. Ganin babu wasa a fuskarsa ta buɗe bakinta ya saka mata tare da fara hawaye. A kausashe ya ce mata. "Ki haɗiye mun wannan kukan naki, karki bari hawaye ya ƙara zubowa daga idonki." Ba shiri ta haɗiye kukan amma cikin ranta ji take kamar ta fasa ihu. Duk yanda take ɓata fuska da turo baki bai saka ya daina ya bata ba sai da ya tabbatar ta ƙoshi, ita kanta ta san tana jin yunwa, amma yanda take jin kanta na sara mata babu abun da take buƙata a yanzu sama da bacci. Fresh milk ɗin da ya zo da ita a ɗayar leda ya d'auko ya tsiyaya ya bata, ta kurb'i kaɗan ta ajiye, yay mata wani kallo alamar ta d'auka ta ƙara sha. Ta saka kuka ta ce. "Yaya cikina fa zai fashe." Ya yi murmushi tare da kai hannu saitin cikin ya ce. "Mu ji ta inda zai fashe ɗin." Ta ture hannun nasa tana cigaba da kukan nata. Ya janyo ta jikinsa a hankali tare da kwantar kanta akan kafaɗarsa ya ce. "Kuka, kuka dai Miemerh? I know baki ci wani abincin kirki ba yau saboda hada_hada, ta yaya zan barki ki kwana da yunwa? ko so kike Mamanki ta sab'ar mun? Baki san warning ɗin data ja mun a kanki ba ne shi yasa." Ta yi shiru bata ce komai ba sai ƙoƙarin tashi da ta yi daga jikinsa, bai hana ta ba har ta miƙe ta haye kan gado. Tana ƙoƙarin kwanciya ya miƙe ya ce. "Ta so mu je ki ga gidan naki kafin ki yi bacci." Ba musu ta miƙe ta ja mayafinta ta yafa ta sauko daga kan gadon saboda ita ma bata so daga cin abincinta ta kwanta ba, shima kuma nasa nufin kenan." Ya kama hannunta ta k'wace, ya ƙara riƙewa, ta kalli fuskarsa ya harare ta, ta ɗauke idonta da sauri tare turo baki. Ko ina a gidan sai da ya kai ta ya nuna mata, tsarin gidan ya yi mata kyau sosai kuma ya burge ta. Sannan ya raka ta, ta koma nata ɗakin. Suna shiga ta nufi kan gado. Ya ce. "Kin yi Sallah ne?" Ta gyaɗa masa kai. Ya ce. "Wanka fa?" Ta ce. "Na yi shi ma." Ya ce. "Ki sake wani, sai ki fi jin daɗin baccin." Bai jira amsarta ba ya d'auki tiren da ta ci kaza da sauran kayan gurin ya juya ya fice. Ta turo baki ta yi kwanciyarta. Mintuna kaɗan sai gashi ya dawo ɗakin, bai ce mata komai ba ya shige toilet hannunsa ɗauke da soap da soso, ya ajiye su sannan ya kunna mata heater. Ya fito yana duban ta ya ce. "Ki tashi ki yi wankan kar bacci ya ɗauke ki." Ta tashi tana babbata fuska ta shiga toilet ɗin. Ya sauke ajiyar zuciya sannan ya juya ya fita..........✍️
















_*I'm sorry, na san kuna ta jirana, tun rana na yi typing amma network ya ban matsala, sai yanzu na samu ya yi. Thank you so much masoyan Neehal, ina jin daɗin yanda kuke k'aunar book ɗin nan, masu mun magana a PC da masu kirana da masu magana a group suna cikiya ta ina godiya sosai da kulawa, alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke masoyana na.😘🥰😍*_














*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_*By*_
_*Zeey Kumurya*_














*8️⃣1️⃣*
















_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._












..........Tana mita a ranta an saka ta wanka alhalin bata dad'e da yi ba sai ka ce wata kwad'uwa ta yi wankan ta gama. Sai kuma ta ji jikinta ya yi mata daɗi, ta ɗauki zanin data cire ta d'aura ta yafa d'ankwalin kayan akanta ta fito. Ganin baya nan ta saki sassanyar ajiyar zuciya tare yin sauri ta ƙarasa ta yi locked ƙofa. Ta dawo ta zauna a bakin gado ta janyo jakar da Haneefa ta ajiye mata ta buɗe dan duba abun da zata sakawa jikinta mara nauyi dan baza ta iya bacci da atamfa ba. Wasu kayan bacci ta fara cin karo da su riga da wando, rigar idan ta saka ta ko cibiya baza ta rufe mata ba, wandon kuwa ba shi da maraba da pant, ga kayan sharara, ta ɗaga su a hannunta tana kallon su cikin takaici, bata ma san time ɗin da Haneefah ta sako mata su ba, watsar da su ta yi a gefe tana jan tsaki. A fili ta ce. "Wa ake tunanin zai saka wannan kayan? Ba dai Neehal ba." Ta cigaba da duba jakar, Allah ya taimake ta ta samo wata doguwar rigar bacci mai ɗan santsi. Ta ajiye ta a gefe sannan ta mayar da kayan data fito da su ta yi zipping jakar ta rufe. Cikin sauri ta zira rigar ta ɗaura zanin jikinta akai, sannan ta tashi ta kashe light ɗin ɗakin ta kwanta tare da lumshe idonta. A ranta tana mamakin yau ita ce zata yi bacci akan gadon gidan Aurenta, ta ƙara yarda komai yana da lokaci a rayuwa. Bacci ya ɗan fara fizgarta kamar a mafarki ta ji ya buɗe ƙofa ya shigo, ta buɗe idonta da sauri gabanta na faduwa amma bata motsa ba. Ya kunna light hakan yasa ta yi saurin mayar da idonta ta rufe. Da alama shi ma wanka ya yi, dan ya sauya kayan jikinsa zuwa jallabiya ash colour. Ya ƙaraso bakin gadon ya zauna tare da ɗora hannunsa a goshinta ya ce. "Jikinki da zafi har yanzu, ki tashi ki sha magani." Ta ƙudundune jikinta guri ɗaya tare da buɗe idonta kaɗan ta ce. "Bacci nake ji, idan na yi bacci zan ji ni normal." Bai ce komai ba ya tashi ya fita ba tare da ya kashe mata light ɗin ba, ta bishi da kallo sannan ta lumshe ido ta koma baccin dake cin ta. Ya ɗan jima sannan ya dawo ɗauke da sabon duvet, ya lullub'a mata a jikinta sannan ya je ya rufe ƙofa ya dawo ya kashe light ya kunna bedside lamp. A hankali ya hau kan gadon ya kwanta ya shiga cikin bargon tare da janyo ta jikinsa, ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da lumshe idonsa yana ƙara cusa fuskarsa a jikinta dan sosai ƙamshin jikinta ya yi masa daɗi tare yin tasiri a gare sa. Ta motsa tare da buɗe idonta a tsorace saboda yadda ya ƙwaƙume ta a jikinsa, dama baccin ba wani nisa ya yi ba. Ta zare jikinta da sauri ƙirjinta na dokawa a million ta tashi zaune tana keɓe fuska kamar zata yi kuka. Ya ɗan ɗago yana kallon fuskarta ta cikin ɗan hasken bedside lamp, shi dariya ma ta bashi yanda ta yi da fuska kamar wadda ta ga dodo ko fatalwa saboda tsoro. Ya kama hannunta a hankali ya ce. "What happening?" A shagwabe ta ce. "Bacci fa nake ji sosai, dan Allah Yaya ka koma ɗakinka ni bazan iya bacci kana nan ba." Ya janyo ta gaba-d'aya ta faɗa jikinsa ya saka hannunsa ya matse ta, yana jin yanda jikinta yake rawa saboda tsoro. Ɗayan hannun nasa ya kai kanta ya shiga shafa gyararren gashin kanta slowly. Dai-dai kunnanta ya kai bakinsa ya ce. "Relax, babu abun da zan miki." Ta buɗe baki zata yi magana ya hana ta ta hanyar ɗora finger ɗinsa akan lips ɗinta ya ce. "Shiiiii.....Just sleep." Ta turo baki tare da lumshe idonta tana sakin ajiyar zuciya a hankali. Mamakin Ameen take ba kaɗan ba, ko kaɗan bata yi tunanin zai kalli ɗakin da take ba ma a yau a yanda yake nuna mata a baya balle har ya shigo su kwana tare, shi yasa babu fargaban hakan ko kaɗan a ranta, amma yanzu ya dasa mata fargabar, sai faman mammatse jikinta take guri ɗaya kamar wacce take kwance kan a ƙaya, a matuƙar tsorace take sai faman jan numfashi take tana saukewa. Saboda tarin gajiya da ciwon kai da baccin dake kanta cikin mintuna ƙalilan bacci ya kuma ɗauke ta ba tare data sani ba. Ajiyar zuciya ya sauke jin saukar numfashinta, ya ɗan rabata da jikinsa tare da gyara mata kwanciyarta, ta wani dunk'ule jiki kamar dafaffiyar kaza. Ya tsurawa fuskarta ido yana sakin murmushi shi kaɗai, yanda yake jin kansa a yau ba zai misaltu ba, sosai yake cikin farin ciki da nishad'i gami da annashuwa. Ya saka finger ɗinsa guda ɗaya yana zagaye lips ɗinta da shi, zabura ta yi amma bata farka ba, ya ƙara yin murmushi ganin gaba-d'ayanta a tsorace take. Imagine yanda bata jin daɗin jikinta a yanzu ya yi mata wani abu, ya san idan bata fasa masa kunne da ihunta ba to sai an jiyo kukanta a mak'wabta. Yanda take uwar raki, ko yaya ciwo yake ta yi ta kuka kenan, ina kuma ga ya yi mata abun da ya san dole sai ta ji jiki. Bai san tsawon lokacin da ya ɗauka yana kallon ta tare shafa kanta zuwa fuskarta ba cikin shauƙi, a haka dai bacci ya ɗauke shi.














Da asuba kusan makara suka yi saboda dukkan su da tarin gajiya a jikinsu. Ameen ne ya fara tashi lokacin har an shiga Sallah, ya tashe ta sannan ya shiga toilet ya yi alwala a gaggauce ya tafi masallaci. Daƙyar ta iya tashi dan ji ta yi kamar ta koma ta cigaba da baccin, dan bai ishe ta ba. Ta dai cize ta tashi ta shiga toilet ta yo alwalar ta fito ta ɗauko hijabi a cikin jakar kayanta ta zira ta tayar da Sallah. Bayan ta idar ta ɗauko wayarta a cikin hand bang ɗinta ta yi karatun Alkur'ani tare da azkar ɗin safe, Alhamdulillah ta ji sauƙin jikin nata da ciwon kan sosai. Har gari ya fara haske bai dawo daga Masallacin ba, ta miƙe ta yi locked ƙofa sannan ta kwanta ta koma baccinta. Bata jima da kwanciya ba ya dawo gidan, duk abun da ya san zata buƙata na toilet ya kwaso ya kawo mata, sannan ya cire jallabiyar jikinsa ya hau kan gadon ya jawo ta jikinsa suka cigaba da baccin tare. Wannan karon ta riga shi tashi. Ta buɗe idonta a hankali ta sauke su akan kyakkyawar fuskarsa, baccinsa yake yi hankali kwance. Ta zame jikinta daga nasa a hankali ta tashi zaune, a lokacin ta gane babu riga a jikinsa, ta ƙurawa faffaɗan ƙirjinsa dake ɗauke da farar fata da kwantaccen ƙananun gashi ido. Sai ta ji kamar ta kai hannu ta shafa su amma sai ta kasa. Jin ta take kamar a mafarki, wai yau ita ce kwance gado ɗaya da yayanta akan ƙirjinsa? Abun har yanzu bai daina bata mamaki ba. Ta yunkura da nufin ta sauka ta ji ya riƙo ta, ta kalli fuskarsa da sauri ta ga still idanunsa a rufe suke. Ta yi ƙoƙarin k'wace jikinta ya buɗe idanunsa dake lumshe saboda bacci ya ce. "Where are you going?" Ta yi ƙasa da kanta cikin kunya a ranta tana addu'ar Allah yasa bai san ta tsaya kallon shi ba. A hankali ta ce. "Toilet." Ya jawo ta jikinsa ya ce. "Me zaki yi?" Ta yi shiru tana rarraba ido cikin tsoro kamar ace kyat ta ruga da gudu. Ya shafi saman idonta ya ce. "Matsoraciya." Sannan ya sake ta. Ta ɓata fuska tare da sakin ajiyar zuciya ta sauka daga gadon. Tana mitar abubuwan da yake mata a ranta, fargaba fal a cikin ranta na kar abun ya wuce haka. Sai ta fara tambayar kanta 'anya kuwa Yayanta data sani a da shine na yanzu? Wannan kamar ba Yayanta ba an canza mata wani' ga abubuwan da yake mata ko kunya ba ya ji, ko dama haka mazan suke ba su da kunya ne? Ta yi mamakin ganin sabon toothpaste da brush da robar jower jel da takarcen sabulan wanke toilet na ruwa, sai kuma sabbun towels guda biyu an yi hanging ɗin su a cikin toilet ɗin. Brush kawai ta yi ta fito, tana son yin wanka amma bata san a yaya zata iya fitowa idan ta yi wankan yana ɗakin ba, sai kawai ta yi fitsari ta wanke toilet ɗin duk da babu dattin komai a cikinsa ta fito. Ta tarar baya ɗakin ya fita sai mayen ƙamshinsa mai kama guri, gaba-d'aya ya gama ɗakin. Cikin murna ta koma cikin toilet ɗin ta yi wanka tana addu'ar Allah kar ya dawo da shi ɗakin har sai ta gama shiryawa. Adduarta ta karɓu kuwa, har ta gama ta fito ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa bai dawo ba, tana cikin d'aura ɗankwali ya shigo ɗakin da sallama, ta amsa masa ba tare da ta juya ta kalle shi ba. Ya tsaya a kanta yana kallon ta har ta ƙarasa ɗaurin nata. Cikin sanyin murya ta ce "Ina kwana?" Bai amsa ba sai tsugunnawa da ya yi a gabanta tare da lek'a fuskarta ya ce. "Kwalliyar ce ba'a son in gani ake boye mun?" Ta rufe fuskarta da hannunta zuciyarta ta fara bugun da take yi mata a duk lokacin da suka yi over close. Ya cire hannun nata ya matsar da fuskarsa daf da tata ya ce. "Wai wannan wacce irin kunya ce da ta ƙi ƙarewa? Ko sai na yi maganinta ne?" Ta shagwab'e fuska tare da turo baki gaba. Ya ƙurawa lips ɗin nata ido, a hankali kuma ya ɗora nasa soft lips ɗin akan nata, bata yi aune ba ta ji ya haɗe bakunansu guri guda ya shiga bata hot kiss. Abun ya zo mata a bazata hakan yasa lokaci ɗaya jikinta ya d'auki rawa, gaba-d'aya ta ƙara firgicewa da al'amarin sa, amma duk da haka sai da sak'onsa ya ratsa dukkan jikinta, ta dinga jin wani irin abu tun daga kanta har tafin ƙafarta yana yawo a cikin jininta. Yanda yake kissing ɗin nata kamar zai cinye mata baki shi yake ƙara tsorata ta, ta yi ƙoƙarin k'wace kanta amma ta kasa, ƙara jawo ta jikinsa ma ya yi alamun ba shi da niyyar bari. Ƙarar knocking ƙofar parlour ce tasa ya sake ta a hankali yana sauke numfashi gami da ajiyar zuciya. Runtse idonta ta yi tana jin kamar ƙasa ta tsage ta shige dan kunya, ita kam ta ga ta kanta Ameen zai kashe ta da wannan abubuwan da yake mata. A kasalance ya tashi ya fita daga ɗakin idanunsa har sun fara sauya kala. Ta buɗe idonta a hankali tana jin lips ɗinta kamar har yanzu suna cikin bakinsa, ta kai hannu ta shafa lips ɗin nata tare da lumshe idonta, tana jin jikinta kamar ba nata ba.






A hankali ta tashi ta ɗauko wayarta ta duba time, ƙarfe goma sha ɗaya saura na safe ta gani. Gyaran ɗakin ta shiga yi bayan ta gama ta fita da niyyar gyara falo suka ci karo da Ameen. Ya kama hannunta ya ce. "Mu je mu yi breakfast Mamanki ta kawo mana abinci." Ta yi ƙasa da kanta kewar Mama na ƙara cika mata zuciya, cikin sanyin murya ta ce. "Waya kawo breakfast ɗin?" Ya shafi kuncinta ya ce. "One of our soldiers staff." Bata kuma magana ba ya ja hannunta suka ƙarasa tsakiyar falon inda abincin yake akan Centre Carpet. Har ya d'auko plates da cups da spoons da kayan tea duk ya ajiye a gurin, tana mamakin yanda yake ɗauko mata duk abun da ya san zata buƙata in time tun kafin ta yi yunk'urin ɗaukowar, Shi da a gida komai sai dai a ɗauko masa yana daga zaune. A ranta ta ce. 'Ko Matarsa yakewa hakan shi yasa itama yake mata.' Haka kawai ta ji gabanta ya fadi tunowa da ta yi da Hafsat..........✍️










*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_*By*_
_*Zeey Kumurya*_














*8️⃣3️⃣*
















_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._












.........Saurin yin ƙasa da kanta ta yi daga kallon sa tare da amsa masa sallamarsa. Ya ajiye ledodin hannunsa a gaban gadon sannan ya zauna a kusa da ita. Ba tare data kalle shi ba ta ce. "Sannu da zuwa." Ya amsa mata a can ƙasan mak'oshi, sannan cikin kulawa ya ce. "Kin ci abinci?" Ta ce. "Eh." Ya ce. "Na dare fa nake nufi bana rana ba." Ta girgiza masa kai alamar a'a. Ya ce. "Okay sakko mu ci wannan." Ya yi maganar yana nuna ledodin gabansu. Ta ce. "Akwai sauran abincin da Mama ta kawo fa." Ya ce. "Mu je ki bani na kaiwa mai gadi sai mu ci wannan ɗin." Ta miƙe ba tare da ta yi magana ba ya bi bayanta. Abincin duka ta juye masa sannan ta ɗauko plates da cup da spoon kamar yadda ta ga ya yi jiya. Sai a lokacin ta tuna data tashi yau da safe ba ta ga ragowar kazar jiya ba. Ta kai kayan ɗakinta ta

Please Login or Register in order to submit comment