Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi muku albarka ya kau da fitina a tsakaninku, Allah ya haɗa maka kansu, kai kuma ka zamto mai adalci a tsakaninsu, Allah ya baka ikon hakan kai ma." Ya ce. "Amin, insha Allah." Mama ta ce. "Tun ɗazu na yi girki gashi har rana ta yi ba'a kai muku ba, zaka tafi da shi ko su A'isha su tafi da shi?" Ya ce. "Daga nan ba gidan zan koma ba direct, zan biya can gidan Hafsah na ɗauko abu." Mama ta ce. "Yanzu gidan babu kowa kenan a cikinsa?" Ya ce. "Daa da masu aikinta, last week na je su je gida kawai idan ta dawo sa dawo, mai gadi ne kawai a gidan." Aunty Sadiya ta ce. "Allah ya kyauta." Mama ta ce. "Ya Neehal ɗin? I'm trying her number bata shiga." Ameen ya ce. "May be network ne, idan na koma zan kira ki sai na haɗa ku." Mama ta ce. "Toh, ta ce ma tabar ɗayar wayarta a nan gidan, in zaka tafi sai ka tafin mata da ita." Ya ce. "Okay, Ina tsohuwar gidan nan ne?" Mama ta nuna Aunty Sadiya ta ce. "Sai dai in wannan uwar taka ce tsohuwa amma ba tawa ba." Aunty Sadiya ta yi murmushi ta ce. "Hajiya tana ɗakin Neehal na da tana bacci." Ameen ya ce. "Aikin kenan." Harararsa Mama ta yi, ya yi murmushi.




Ƙarfe Uku da ƴan mintuna Neehal tana ɗaki tana drying gashinta data manta tun safe bata yi ba su Aunty A'isha suka zo. Ta yi packing gashin ta d'aura ɗankwali ta fita parlour. Murna kamar ta kashe ta da ta ga su ne. Suka zauna suka ci abincin da suka zo da shi tare suna ta hira. Ana yin Sallar la'asar Aunty ta ce za su tafi. Neehal ta dinga roƙon ta kar su tafi su ƙara zama, harda hawayenta su Amira na yi mata dariya. Daƙyar Aunty ta yarda suka kai ƙarfe biyar a gidan.












Kwana biyun nan Hafsat ta yi su ne cikin k'unci tamkar tana cikin k'abari, idan ka gan ta sai ka ɗauka cuta ta yi duk ta lalace ta yi duhu. Yau tun safe ta je ta tasa mahaifiyarta a gaba da kuka, wai ta bar ta ta koma gidanta ita ta gaji da zaman nan, ta san halin Ameen bazai taɓa zuwa ba. Mom ta yi shiru bata ce komai ba, ita kanta al'amarin ya fara isarta, abun kunya ne a gurinta k'awayenta su san ƴarta ta yi yaji, kuma indai aka cigaba da tafiya a haka dole wataran su sani, gashi Ameen ya wuce duk inda take tunani, bata taɓa zaton za'a kawo har i yanzu bai zo ba, ta tabbatar da maganar Hafsah na cewa Ameen ya wuce duk inda suke tunani kuma ba ya ɗaukar raini da wulaqanci. Ta dubi Hafsat cikin tausayawa ta ce. "Ki yi haquri Daughter mu jira babanki ya dawo, ya ce wani aiki ne ya tsayar da shi amma insha Allahu next week zai dawo, idan ya dawo sai ya je ya samu mahaifin shi Ameen ɗin su yi maganar." Hafsat ta gyaɗa mata kai ta ce. "To Mom ina son na je gidan Aunty Safiyya na yi kwana biyu, na gaji da zaman nan haka." Mom ta ce. "Indai hakan zai saka ki ji daɗi to ki shirya anjima driver ya kai ki, kuma ki saki jikinki dan Allah kina cin abinci ko kya yi kyan gani ki ɗan ciko, idan shi Ameen ɗin ma ya gan ki a haka ai sai ya raina ki, ya ce saboda shi kika damu kanki haka." Ita dai Hafsah bata ce komai ba, koma a yaya Ameen zai gan ta bata damu ba, ita dai fatanta Allah ya dai-daita su ta koma gidanta, babban abun da yake bak'anta mata rai idan ta tuna yana can tare da wannan shegiyar yarinyar data tsana, sai ta ji wani baƙin ciki ya cika mata zuciya, kamar zata haɗi zuciyar ta mutu. Bayan ta je gidan Aunty Safiyya ta ɗauki wayarta a b'oye ta kira Ameen tunda ita Mom ta ƙara k'wace wayartata, sai dai har wayar ta yi ringing ta gama bai ɗauka ba, dama ta yi tunanin hakan. Ta ji daɗin zuwanta gidan Aunty Safiyya, saboda yanda ta daɗa kwantar mata da hankali, ta ce tana nan tana shiri na musamman wanda zai saka dole Ameen ya zo da kukansa yana roqonta ta koma gidansa, lokaci kawai take jira a gama aikin.






Kafin Magriba Ameen ya dawo gida, lokacin Neehal tana zaune a falo tana karatun Alkur'ani kaɗaici ya ishe ta. Ya tsaya yana kallon ta bayan ya yi sallama yana shaƙar daddaɗan ƙamshin dake tashi a cikin parlour'n. Sai da ta kai aya sannan ta rufe Alkur'anin ta ajiye ta ɗago tare da amsa masa sallamar. Ya sakar mata murmushi sannan ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta yana kallon ta kamar zai lashe ta. Ƙasa ta yi da kanta cikin sanyin murya ta ce. "Sannu da zuwa." Ya ɓata fuska ya ce. "Haka aka welcoming ɗin miji dama?" Ta ɗan kalle shi ta ce. "To ya ake yi?" Ya ce. "Special hug and kiss to him." Ta waro ido sai kuma ta yi saurin rufe fuskarta da hannunta. Ya yi murmushi a ransa yana ƙara hasko wani bambancin na Hafsat da Neehal wato kunya, Hafsat ko a ranar da aka kawo ta gidansa bata nuna kunya ba sam, hasalima da ya je ko irin kukan nan na amare bata yi, babu alamun ma ta yi dan idonta ragal da shi. Ya rungume ta a hankali cikin kulawa da k'auna ya ce. "I missed you so much baby love." Ta yi shiru tana shaƙar ƙamshinsa tare da sakin ajiyar zuciya a hankali, tana jin wani abu yana yawo a cikin zuciyarta game da shi, kenan ita ma she missed him? Ya kama hannunta yana ɗan murzawa ya ce. "Have you eaten food?" Ta gyaɗa masa kai ta ce. "Kai fa?" Ya ce. "Na ci a gidan Mum." Ɗago kanta ta yi daga ƙirjinsa tare da ɓata fuska ta ce. "Shine ka je gidan Mama baka tafi da ni ba?" Ya shafa kanta ya ce. "Kin taɓa ganin amarya ta fita kwana biyu da kaita inba wata lalurar ba?" Ta girgiza masa kai. Ya ce. "To kin gani, idan an kwana biyu sai na kaiki ko?" Ta gyaɗa masa kai sannan ta ce. "Ina wayata? Ko baka gama checking ɗin ba ne?" Ya gyaɗa mata kai yana shafa kuncinta. Ta ce. "To ka bani, ina son na kira Family and Friends na yi musu ban gajiya." Ya ce. "Alright, Mum ma ta bani ɗayar wayarki da kika manta a gida." Ya zaro ta a aljihunsa ya miƙa mata. Ta karɓa ta ce. "Contacts ɗina duk suna cikin ɗayar ai." Ya ce, "To bari na ɗauko miki." Ya sake ta ya miƙe ya shiga ɗakinsa ya d'auko mata wayar ya kawo mata. Ya zauna ya ce. "Ki bari a yi Sallah sai ki kikkira su." Ta ce. "Toh." Ya janyo ta jikinsa ya shiga aika mata da saqonninsa masu rikitarwa, sai da aka kira Sallar Magriba sannan ta samu ya k'yale ta. Bayan an yi Sallah ta shiga kiran wayar, Daddy ta fara kira sannan Mama sannan Haneefah. Da suka gama waya da Haneefah sai ta kira Ummin su Ahmad, suka gaisa ta yi mata ya suka je gida da bangajiyar biki gami da godiya sannan ta ce ta bawa Zahra wayar. Bayan ta bata sun gaisa ta ce. "Shine kuka tafi ba ku zo ba, aida ko twins kun kawo mun, amma sai tafiyar ku na ji kawai ko sallama babu." Zahra ta ce. "Ki yi haquri, wallahi sai da na ce zamu zo washegarin da aka kaiki Ummi ta hana, na ce a kawo miki twins to shi ma Yaya ya hana ya ce sa zo miki wani lokacin." Neehal ta ce. "Shikenan ina twins ɗin nawa?" Zahra ta ce. "Suna gidan Yaya." Neehal ta ce. "Ki gaishe mun da su sosai, ko kuma ki turo mun ma numbern Aunty Khadijan sai na kira ta mu gaisa da su." Zahra ta ce. "Toh shikenan zan tura miki." Daga haka suka yi sallama ta katse kiran. Ta cigaba da kiran friends ɗinta da abokanan aikinta tana yi musu ban gajiya, har Batul k'anwar Sadik ma sai da ta kira. Ta yi mamakin yanda katin wayarta ya ishe ta wannan kiraye_kirayen, sai bayan ta gama ta duba ta ga ashe Ameen ne ya tura mata credit daga account ɗinsa.








Har bayan isha'i Ameen bai dawo ba. Ta yi wankanta ta shirya cikin wasu riga da wando masu kyau, wandon irin mai buɗewan nan ne ta ƙasa, ta saka hula pink colour a kanta da yake kwalliyar jikin kayan pink colour ce, ta yi kyau sosai. Ta zauna a falo tana kallo sai baza ƙamshi take. Tara saura Ameen ya shigo gidan bakinsa ɗauke da sallama. Ta kalle shi cikin wani irin salo ta juya masa ido tare da amsa masa sallamarsa cikin karyar da murya. Sandarewa ya yi yana kallon ta dan salon nata ya shige shi ba kaɗan ba. Bata motsa ba sai ido data zuba masa tana murmushi. Ya ƙaraso a hankali ya ajiye ledodin hannunsa ya rungume ta tare da sakin ajiyar zuciya. Ita ma ajiyar zuciyar ta sauke ta ɗan shafa kansa ta ce. "Welcome Yayana." Ya lumshe idonsa yana ƙara shigar da ita jikinsa tare da shaƙar ƙamshinta da ya fara saukar masa da kasala. Ta ɗan ture shi ta ce. "Daga zuwanka zakai mun syqueising ɗin kaya." Ya buɗe idonsa yana sauke numfashi ya ce. "Kin yi kyau sosai baby, ina son wannan ƙamshin naki." Ya ƙarashe zancen yana shafa kwantaccen gashin gaban goshinta. Ta ɗan murmusa ta ce. "Thank you." Sannan ta bar jikinsa ta tashi ta nufi fridge. Ya bi ta da kallo. Ruwa ta tsiyayo masa mai sanyi a cikin glass cup ta kawo masa, ya karɓa tare da yi mata godiya ya shanye. Ya janyo ta ya ɗora ta akan cinyarsa sannan ya buɗe ledodin da ya shigo da su, ice-cream ne da choculates da wafer da popcorn a ciki, abubuwan da ya san tana matuƙar son su sosai. A baki ya bata komai ta ci, shi kuma ya sha ice-cream kawai. Ta tattare sauran ta ajiye a fridge bayan sun gama. Ya Ɗauke ta cak ya kai ta ɗakinsa ya dire akan gado shi kuma ya shige toilet. Murmushi ta yi ta tashi ta fice ta koma ɗakinta ta kwanta. After 20 minutes ya biyo bayanta, ya shirya cikin wasu white ɗin kayan bacci. Ya hau kan gadon ya yaye bargon data lullub'a ya ce. "Da kika gudo nan ɗin bazan iya zuwa ba ne."Cikin marairaicewa ta ce. "Ni fa Yaya bacci nake ji, ka koma ɗakinka." Ya ɗora hannunsa a kan cikinta ya ce. "I can't." Ɓata fuska ta yi bata kuma magana ba, Ƙasa ya yi da hannun nasa a jikinta ya ce. "Ya jikin naki? I hope kin warke?" Kamar zata yi kuka tsoro ƙarara akan fuskarta ta ce. "Ni ban warke ba." Ya kwanta tare da janyo ta jikinsa ya ce. "Kar ki mun kuka, babu abun da zan miki, I just want to sleep with you." Ta sauke ajiyar zuciya tare da lumshe ido ta saka hannayenta ta zagaye bayansa da su kamar yadda ta ji ya yi mata..........✍️










```Ban yi edit ba.```












*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_*By*_
_*Zeey Kumurya*_














*8️⃣6️⃣*
















_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._












*⚜️BUƊAƊƊIYAR SOYAYYA⚜️*


Jameey yar'mutan kankia




*Promo* *Promo* *Promo*




Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara,har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah,ga yanda promo din yake.


#300-sau biyu a rana
#500 -sau ukku a rana
#700 -sau hudu a rana




Kiyi man wanann number magana danjin ynda zaki biya 08160508316
















.........Cikin one week Ameen ya koyawa Neehal son sa da k'aunarsa, wata shak'uwa ce ta ƙara shiga tsakaninsu mai ƙarfin gaske, a yanda suke jin junansu a zuk'atan su ko 1 second basa son su yi ba tare da junansu ba. Ameen ƙarshe ne a iya soyayya da kula da tattali da tarairayar mace. Through out yana gida manne da Baby love ɗinsa suna zuba k'auna, Sallah ce kawai take fitar da shi zuwa Masallaci, sai kuma idan ta yi baƙi, dan kusan kullum a cikin Family ko friends ɗinta wasu sai sun zo mata, Haneefah ma ta zo ta wunar mata. Neehal ta yarda ta kuma gasgata cewa Ameen ba ƙaramin so yake mata, kwata_kwata yanzu babu wannan miskilancin bare haɗe rai. Ita ce ma take ɗan taɓa masa idan class ɗin ya motso mata. Neehal an samu abun da ake so tay ta zuba masa shagwab'a yana lallab'a ta. Sai dai har yanzu bata daina jin kunyarsa ba, tana dai ɗan daurewa ta ƙoƙarta ta nuna masa soyayya dan ta lura yana jin daɗin hakan sosai. Za su wuni tare manne da juna sai dare ya yi ta gudu ɗaki ta kulle, shi kuma ya yi amfani da spare key ya buɗe ɗakin ya bita ya nuna mata bai san wannan zancen ba, tay ta bab'b'ata fuska tana rigima amma duk da haka sai ya yi abun da take gudun, idan ya gama sai ya shiga aikin rarrashi.










Yau asabar, wanda ya kama kwana takwas da tarewar Neehal. Misalin ƙarfe goma sha biyu na rana tana tsaye a kitchen tana aikin girkin rana. Sanye take cikin wani straight skirt Black colour mai tsaga a baya, sai riga mai ƙaramin hannu light Brown, irin roban nan ce mai bin jiki, ta kama jikinta sosai. Kanta babu ɗankwali sai bana data saka kalar rigar jikinta, ta yi parking ɗin gashinta sai sheƙi yake ya sha oil na man kitso mai ƙamshi. Sauri take yi ta kammala aikin nata kar Ameen ya tashi daga baccin data bar shi yana yi, tun bayan kwana uku da Mama ta daina kawo musu abinci ita take girkinta. Idan zata yi girkin kodayaushe Ameen yana manne a jikinta, duk inda ta ɗora ƙafarta nan zai saka tashi, in ta yi complain ya ce taya ta aikin yake yi, alhalin ba haka ba ne delay ma yake ja mata a aikin nata, abun da zata yi shi in one hour sai ta yi kusan 2 hours. Tana aikin tana tunanin a ka'ida fa jiya Ameen zai bar gidanta ya koma gidan Hafsah, amma sai ta ga ya ƙara kwana. Ta yi ta mamakin abun amma dai bata yi masa magana ba, yau ma kuma ta ga bashi da alamar zuwa gidan Hafsan. Amma ta ƙudurce a ranta zata yi masa magana anjima akan hakan.










Ƙamshin turaren Ameen ta ji ya cika mata hanci da kuma sign na ana kallon ta, ta juya da sauri ta gan shi tsaye yana kallon ta, jikinsa sanye da single da threequarter wando. Bata ce masa komai ba ta juya ta cigaba da aikinta. Ya ƙarasa inda take a hankali ya rungume ta, ta baya tare da sakin ajiyar zuciya. Ta lumshe ido ta buɗe ta juya tana kallon shi tare da ɓata fuska ta lakuce masa hanci ta ce. "Wa ya ce ka tashi yanzu?" Ya langwab'ar kai ya ce. "Saboda kin tashi mana." Ta ɗan ture shi ta ce. "Ka koma baccinka ka bar ni in yi aikina." Ya jingina da jikin cabinet bai ce komai ba, sai kalar tausayi da ya yi da fuskarsa kamar sabon maraya. Ta juya ta cigaba da aikinta tana murmushi ƙasa_ƙasa. After 5 minutes ta juyo ta ce masa. "Ya da shiru kuma?" Ya ɓata fuska kamar wani yaro tare da ɗauke kai. Ta ƙarasa jikinsa ta saka hannayenta duka ta zagaye wuyansa ta ce. "Wa ya taɓa mun Yayana a tsakar ranar nan?" Bai kalle ta ba shi a dole fushi yake ya ce. "Ke ce mana, na zo zan taya ki aiki kin gwale ni." Ta kwanta a jikinsa ta ce. "Ka taya ni aiki ko ka ƙara mun wani aikin?" Ya zagaye bayanta da hannunsa ya ce. "Duk a cikin tayin aikin ne ai." Ta ɗago daga jikinsa ta ce. "To mu je a taya nin." Ya yi murmushi yana bin ta da kallo. Ta juya masa ido. Ya ƙara janyo ta jikinsa ya ce. "Ko dai barin aikin nan zamu yi ne mu je mu yi wani." Cikin shagwab'a ta ce. "Um,um Yaya baƙi fa zamu yi, sai sun zo bamu tanadar musu komai ba." Ya kwantar da kansa akan kafaɗarta bai ce komai ba. A haka ta cigaba da aikin yana jikinta kamar kullum. Sai da aka kira Sallar Azhar sannan ta samu ya bar ta ya tafi masallaci.












Bayan sun ci abinci sun yi wanka sun shirya suna zaune a parlour akan kujera 2 seater suna game a wayar Neehal aka yi knocking ƙofar parlour. Neehal ta bar jikinsa tana dariya ta yi masa gwalo sannan ta tashi cikin sauri dan kar ya cafko ta, ta nufi ƙofa. Haka take yi masa kodayaushe idan ta yi baƙi, ya yi murmushi tare da yi mata alamar zan kama ki ne. Kamar yadda ta zata Salma ce wadda ta raka ta gidansu Sadik ita da sistern ta. Neehal ta ce. "Sannunku da zuwa, amma fa na yi fushi sai yanzu zaku zo?" Salma ta ce. "Ki yi haquri, sai da muka yi girki ne." Neehal ta ba su hanya suka wuce sannan ta mayar da ƙofar ta rufe. Suka gaisa da Ameen cikin mutuntawa da fara'a sannan ya tashi ya shige ɗakinsa. Neehal bata zauna ba sai da ta kawo musu drinks da abinci da kayan snacks ɗin gararta. Suka ƙara gaisawa sannan Salma ta ce. "Amarya kin sha ƙamshi, kin ga yanda kika yi kyau kuwa? Anya kuwa idan Mama ta gan ki zata gane ki?" Murmushi kawai Neehal ta yi dan ita akaran kanta ta san cikin one week ɗin nan ta sauya. Sai bayan Magriba su Salma suka tafi, saurayin Salman ne ya zo ɗaukar su, har bakin Motarsa ta raka su. Ga mamakinta sai ta ga Sadik ne. Ta riƙe haɓa tana kallon sa cikin tsananin mamaki, shi kuma ya shiga tsokanarta da amarsu ta Ango yana murmushi. Ta dubi Salma zata yi k'orafi Salman ta yi saurin ce mata. "Bari na yi ki gani da idonki dama." Suka yi dariya gaba-d'aya sannan ta yi musu fatan Alkhairi suka yi sallama ta koma cikin gida, a ranta tana jin daɗin haɗewar Salma da Sadik . Da daddare suna shan fruits a falo ta dubi Ameen cikin nutsuwa ta ce. "Wai Yaya ba tun jiya ya kamata ka koma gidan Aunty Hafsah da kwana ba ne? Ya ɗago ya kalle ta bai ce komai ba amma fuskarsa ta sauya. Sai ta ji babu daɗi gabanta har fad'uwa ya yi saboda ta dad'e bata gan shi a cikin irin wannan yanayin ba. Sai ya daina shan fruits ɗin ma, ita ma ganin haka sai ta daina sha. Tana shirin tattare sauran yay mata wani kallo data san mana'ar shi, dole ta koma ta cigaba da sha. Sai da suka kwanta ta ga har lokacin ransa a b'ace yake sannan ta bashi haquri har da hawayenta. Ya rungume ta ya nuna mata komai ya wuce amma kar ta sake yi masa maganar. Abun ya bata mamaki ba kaɗan ba. Ta dinga tambayar kanta me zai saka Ameen ɗin ya yi haka?










Washegari da murna ta tashi dan Ameen ya gaji da rigimar da take masa na son ganin Mama ya ce zai kaita bayan Magriba ta gan ta. Da yamma tana aiki a kitchen ya shigo kitchen ɗin ya tsaya a kusa da ita. Ta dube shi tare da turo baki ta ce. "Kallon kenan?" Ya ce. "Na gaji da watching TV na zo kallon ki." Ta ɓata fuska ta ce. "Dan Allah Yaya ka barni in yi aikin nan, yanda ka koyi cin nan idan ban yi maka abinci ba me zaka ci?" Ya ce. "Au acici ma na zama?" Ta ce. "Eh mana, da ai baka cin abinci sosai." Ya ce. "A da ɗin ma Soyayyar ki da damuwar rashin mallakar ki ya saka hakan, yanzu kuma na same ki bani da wata sauran damuwa." Ta yi murmushi kawai. Ya kwanta a jikinta yana sakin ajiyar zuciya. Cikin shagwab'a ta ce. "Allah Yaya kana takura mun fa a gidan nan, zan haɗa ka da Mama fa." Ya ce. "Ke ce kike yin kyau ai ki yi ta ƙamshi mai daɗi, duk ki saka in zauce." Ta yi murmushi kawai ta cigaba da aikinta.












Bayan Magriba kamar yadda ya alƙawarta suka je gidan Mama. Murna da zumuɗin Neehal suka kasa b'oyuwa. Dije ce ta buɗe musu ƙofa, cikin murna ta rungume ta suka gaisa sannan ta shige ciki tana ƙwalawa Mama kira. Girgiza kai kawai Ameen ya yi ya zauna a falon ƙasa. A ɗakin Mama ta tatar da ita akan darduma tana jan carbi, faɗawa jikinta ta yi ta rungume ta. Mama ta shafa kanta cikin farin cikin ganin ta, ta ce. "Yau Amarya ce a gidan namu?" Ta rufe fuskarta da hannunta tana dariya. Mama ta ce. "Ina Ameen ɗin?" Ta ce. "Yana falon ƙasa, ina yini Mamana." Mama ta ce. "Lafiya ƙalau." Tare da bin ta da kallo ganin yadda ta ƙara kyau ta murje alamun tana cikin kwanciyar hankali. Ta ɓata fuska ta ce. "I missed you so much my Mum." Mama ta ce. "Nima haka Daughter, kwana biyu gidan ya mun faɗi Ni kaɗai, babu mai zuwa ya ɗane mun jiki, sometimes da shagwab'a sometimes da murna." Ta yi murmushi ta ce. "Ina Daddy?" Mama ta ce. "Yana masallaci, kin san sai an yi isha'i yake shigowa." Neehal ta gyaɗa mata kai sannan ta ce. "Mama yanzu wa ya ke yi miki girki?" Mama ta yi murmushi ta ce. "Ni nake abuna mana." Ta marairaice fuska ta ce. "Kullum kuma, ni bana son kina wahala." Mama ta ce. "Mene abun wahala? Kin fi so in jibge inta zama babu ɗan motsa jiki." Ta girgiza kai. Mama ta ce. "Ki bari In kin haifi Baby girl sai ki bani ita in ta girma sai ta dinga yi mun girkin." B'oye fuskarta ta yi a jikin Mama tana murmushi. A haka Ameen ya shigo ya same su. Bayan Daddy ya dawo ta je part ɗinsa, ya yi farinciki sosai da ganin ta da yanayin data gan ta a ciki. Ta zauna suna ta shan hirarsu. Shi kuma Ameen yana can Mama ta saka shi a gaba tana yi masa faɗan ƙin zuwa gidan su Hafsah. Tana mitar suka je part ɗin Daddy, shi dai Ameen bai ce mata komai ba. Suna zama ta dubi Daddy ta ce. "Ka yi masa magana ya je gidansu yarinyar nan tunda ni ya ƙi jin tawa maganar." Daddy ya ce. "Ba ƙi ya yi ba nina sani, baki san dalilinsa na ƙin zuwan ba, shi yasa kika ga ni ban shiga cikin maganar ba." Mama ta ce. "Babu wani dalili, kullum sai dai ya dinga ce mun zai je zai je amma ya ƙi zuwa, ita rayuwa ai komai ɗan haquri ne, dama haka zaman tare yake zo mu zauna zo mu saɓa. Amma yarinya ta kusa wata biyu a gida ka ƙi zuwa, sai yaushe kenan zaka je?" Ya ɗago cikin sanyin murya ya ce. "Ki yi haquri Mum, insha

Please Login or Register in order to submit comment