Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tana cikin rakinta da shagwab'arta bacci ya yi awon gaba da ita.........✍️












*By*
*Zeey kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*5️⃣2️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*


















..........A hankali take tafiya kamar bata son taka ƙasa, as always shi kuma tunda ya hango ta ya ƙura mata ido. Kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon ta zauna a kan carpet ɗan nesa da shi tare da kawar da kanta gefe, su Afrah kuwa gurinsa suka nufa, wayoyinsa guda biyu ya basu bayan ya kunna musu game, cikin murna suka karb'a suka fara yi. Ba tare da ta kalli inda yake ba kamar an mata dole ta ce, "Ina yini." Bai amsa ba sai tashi da ya yi ya dawo kusa da ita ya zauna ganin yanayinta ya kira ainihin sunanta. "Fateemah." Ta d'ago ta dube shi cikin mamaki dan ko da can bai taɓa kiran ta da Fateemah ba. A hankali ta ce "Na'am." Ya ce "Jikin naki ne har yanzu?" Ta girgiza masa kai, ya ce "To me ya faru na ga ranki a ɓace, ko nine ba kya son gani ko kuma kawo miki su Afrah da na yi ne ba ki ji daɗi ba?" Ta ɗan saki fuskarta ta ce "A'a ba komai Uncle." Ya ƙara matsowa kusa da ita ya sassauta murya ya ce "To me yasa ba kya farin ciki, Please be happy, bana so na ganki a haka Pleaseee.." ya ƙarashe maganar da jan kalmar ƙarshe cikin wani irin wani salo da yasa ta ji wani iri a jikinta. Ta ɗan yi murmushi tana kallon shi ta ce "To na yi Uncle, ya kuka baro Mamy?" Shima yana murmushin ya ce "Lafiya k'alau, tana ta tambayar ki, ta yi zaton ma tare zamu zo." Bata kuma cewa komai ba ta miƙa masa wayarsa dake hannunta, ya karɓa tare da faɗin. "Oh, na ma manta, thank you." Yana ƙoƙarin zira wayar a aljihu ba tare daya latsa ta ba ta ce "An kira ka fa." Ta yi maganar cikin ɓata fuska. Cikin mamaki ya zaro wayar ya duba dan ba permanent sim ɗinsa ba ne a ciki bai yi tunanin wani zai kira shi a wayar ba. Tab'e baki ya yi bayan ya ga mai kiran ya saka wayar a aljihu ba tare da ya bi bayan kiran ba. Neehal ta ɗauke kanta daga kallon sa ta ɗan turo baki gaba. Ya saka tafin hannunsa ya taɓa goshinta ya ce "Har yanzu da sauran zazzaɓi a jikinki Princess, kina shan magani kuwa?" Ta ce "Uhm." Kawai. Ya ƙura mata cikin nazartar ta, ya lura kamar akwai abun da ke damunta tunda ta fito, ko kuma wacce ke cikin ɓacin rai. Ya ɗauke hannunsa daga goshinta ya d'ago hab'arta be serious ya ce "Neehal me yake damunki?" Ta lumshe idonta tare da girgiza masa kai tana ƙoƙarin saka hannunta ta cire nasa daga fuskarta. Ya riƙe hannun nata ya ce "Please talk to me Princess, ko kina so ki ganni a cikin damuwa nima?" Ta yi shiru. Ya ƙara tambayar ta, nan ma bata tanka masa ba. Ya sauke numfashi ya cire hannunsa daga hab'arta tare da sakar mata hannunta ya ce "Okay, Good bye Dear, tunda na fuskanci kamar nine ba kya son gani." Ta buɗe idonta da sauri sai hawaye sharr wanda bata san sanda suka zubo ba. Ya dafe kansa tare da faɗin "Oh my God, Dan Allah Princess me yake damunki ne, ko na miki wani abun ne da baki ji daɗi ba?" Ya yi maganar a ɗan ruɗe yana kallon ta. Ita kanta bata san me ya saka ta a cikin wannan yanayin ba, kuma ta yi ƙoƙarin ta danne kar ya fuskanta amma ta kasa. Ta turo baki gaba sosai ta ce "Ka ce mun tunda Maman twins ta rasu baka ƙara kula wata mace ba, and now kuma naga wata ta kira ka harda text, who is she?" Ta yi maganar iya gaskiyar ta. Sai yanzu ya gane bakin zaren, shi dariya ma ta ba shi ba kaɗan ba, amma yanda take a sama ɗin nan in ya dara ya san da matsala, musamman yanda ta tsare shi da kyakkyawan idanunwan nan nata tana jiran amsa. Ya danne dariyarsa ya ce "Oh wai Jamila, she is my cousin, ƴar ƙanwar Dad ce." Ta juya masa idonta ba tare da ta ce komai ba, amma bata gamsu da abun da ya faɗa ba. Ya yi ɗan murmushi tare da matsowa daf da ita, ya kai bakinsa dai_dai saitin kunnenta ya ce "Princess ce kaɗai a zuciyar Uncle ɗinta, since, now and for ever, daga ita kuma babu ƙari." Ta rufe fuskarta da hannunta cikin jin kunyar gano ta da ya yi. Ya yi ƴar dariya ya ce "Ashe Babin Uncle ta fara sonsa har da su kishi?" Ta juya masa baya a shagwab'e ta ce "Ni ba kishi nake ba?" Ya ce "To me kike? Jealous? Kamar zata yi kuka ta ce "Ni fa Allah ba kishi nake ba." Ya juyo da ita da hannunsa ya sa tafin hannunsa ya share mata hawayen data zubar d'azu, zuciyarsa fess da yanda ta nuna tana kishin nasa. Ya zubawa fuskarta ido yana jin kamar ya mayar da ita cikin jikinsa saboda k'auna. Jin maganar Afrah a kusa da shi yasa ya ɗauke idonsa daga kallon ta ya mayar kan yarinyar da take miƙo masa wayarsa tana faɗin "Daddy kiran Sallah ake a cikin wayar." Ya karɓa ya ce "To aje a yi alwala a yi Sallah." Ta ce "Tom Daddy." Ya yi mata kiss a goshi itama ta mayar masa tana dariya sannan ta nufi upstairs da ɗan gudunta tana cewa Amrah sai ta riga ta hawa saman. Jin haka itama Amrah ta kawo masa ɗaya wayar ta bi bayan ta. Neehal ta bi su da kallo cikin k'auna. Ya ce "Princess zan wuce?" Ta juyo ta ce "Sai yaushe?" Ya ce "Gobe da safe Insha Kafin na wuce." Ta ce "Allah ya kai mu." Ya miƙe tsaye yana faɗin "Amin." Itama miƙewar ta yi, ya ja karan hancinta ya ce "Bye, I love You." Ta ce "Allah ya kiyaye." Ya ɓata fuska tare da langwab'ar da kansa ya ce "Ba feedback?" ta yi murmushi bata ce komai ba, ya ce "Shikenan." Ta ce "Thank you for coming, and..." "Kawo miki twins ko?" Ya ƙarasa mata dan ya san haka zata faɗa. Ta yi murmushi tare da gyaɗa masa kai. Ya yi mata murmushin nan nasa mai kyau tare daga mata hannu sannan ya juya ya tafi. Ta sauke ajiyar zuciya bayan ya fice, a ranta tana faɗin 'Ko sallama bai yi da ƴaƴansa ba.' Ta juya ta haye upstairs, ɗakin Mama ta shiga ta tarar da ita tana ƙoƙarin shimfid'a darduma, su Afrah suna taya ta. Amrah ta ce mata "Aunty ina Daddy? Ya tafi?" Ta ce "Eh ya tafi gidan Mamy, amma gobe da safe zai dawo." Mama ta ce "Ki je ki yi alwala ki zo ki yi Sallah, tunda kin warke sai ki shiga kitchen ki yi masa something special gobe in ya zo sai ki ba shi ya tafi da shi" Ta ɓata fuska ta zauna a bakin gado ta ce "Mama ban fa warke ba, cikina ma tun safe ya fara mun ciwo." Mama ta ce "Allah ya sauwaqe." Daga haka ta tayar da Sallar ta. Miƙewa ta yi itama ta shiga toilet ta fito ta tayar da Sallar.












Daf da Magriba Sadik ya shigo gidansu a gajiye, a falon Maamah ya tarar da Hajiyarsu da Batul, Maamah kuma tana bedroom ɗin Abba tana gyara saboda ta karɓi girki da yammar nan. Ya zauna a kusa da Hajiya cikin mamakin ganin ta ya ce "Ƴar tsohuwar nan ke ce a gidan namu? Zuwa babu sanarwa, ai da kin faɗa dana taho miki da tsarabar goruba." Ta rank'washi kansa ta ce "Giginya zaka siyo mun ba goruba ba, ɗan nema kawai." Ya yi murmushi tare da miƙewa yana faɗin "Kin yiwa kanki tunda ba kya so, bari na shiga ciki na fito." Ta ce "To a fito lafiya." Batul ta ce "Sannu da zuwa Yaya." Ya ce "Yawwa, ina Maamah?" Ta ce "Tana ɗakin Abba." Bayan ya dawo daga masallaci Maamah ta kawo masa abinci yana ci suna hira da Hajiya har ta sako masa zancen Neehal inda ta ce "Abubakar ashe ka fara yunƙurin yi mini kishiya ban sani ba?" Ya yi murmushi ya ce "Har kin samu labari kenan?" Ta ce "Shine ma abun da ya kawo ni gidan nan yau?" Ya ce "Kamar ya Hajiya, ko duk kishin ne?" Ta sanar masa yanda suka yi da su Abba da Kawu a tak'aice." Sadik ya ajiye cokalin hannunsa fuskarsa na nuni da damuwa ya ce "Hajiya wannan zancen fa ba gaskiya ba ne, shati faɗin mutane ne kawai." Hajiya ta ce "Koma mene ne dai mahaifinka ya ce zai bincika, in ma gaskiya ne in ma ƙarya ne duk zai gano, amma kafin nan ka fara tuntubar ita yarinyar da zancen, idan har tana sonka da gaskiya saboda Allah kuma ba su da wata manufa akan kisan ake yi zata faɗa maka gaskiya da bakinta." Sadik ya marairaice ya ce "Insha Allahu Hajiya zan tambaye ta, Amma dan Allah Hajiya ko me zai faru karki bari su Abba su hana ni Aurenta, ina sonta sosai wallahi." Maamah dake sauraren hirar tasu cike da tausayin ɗan nata ta ce "Sadik, ka yi addu'a kawai, idan Alkhairi ce a gare ka Allah ya baka ita, idan kuma ba Alkhairi ba ce Allah ya baka wadda ta fita, sautari wani abun da muke so ba shine Alkhairi a gare mu ba, rashin sa a tare mu ya fi zama Alkhairi." Ya kalli mahaifiyar tasa ya ce "Shikenan Maamah, Insha Allahu zan cigaba da addu'a akan wacce nake yi." Hajiya ta ce "Shi ya fi dai, muma zamu taya ka da addu'ar, abun da mahaifiyarka ta faɗa gaskiya ne." Ya yi shiru cikin damuwa, amma a cikin ransa yana jin ba zai iya rabuwa da Neehal ba, kuma Insha Allahu itace matarsa."










Bayan su Neehal sun idar da Sallah ba jimawa Ameen ya zo gidan. Su Afrah suka tafi da gudu gurinsa suna faɗin "Oyoyo Uncle." Ya d'aga su ɗaya bayan ɗaya ya shilla yana murmushi. Sannan ya kamo hannunsu zuwa bakin gado ya zauna ya gaishe da Mama. A hankali Neehal ta dube shi ta ce "Ina yini Yaya." Ya kalle ta ya ce "Lafiya k'alau." Ta ce "Ya jikin Aunty Hafsah?" Ya ce "Da sauqi, ya naki jikin?" Ta ce "Alhamdulillah." Ya mayar da duban sa ga su Afrah ya ce "Yaushe kuka zo?" Afrah ta ce "D'azu Daddy ya kawo mu." Ya shafi kuncinsu bai ce komai ba. Mama ta ce masa "Ya aikin naku? Ya ce "Alhamdulillah, Hajiya ta wuce kenan?" Mama ta ce "Eh, tun safe ba ku yi waya ba ne?" Ya ce "Na ga missed call ɗinta tun safe, na kira ta kuma d'azu bata ɗauka ba." Mama ta ce "May be time ɗin suna hanya, amma mun yi waya kafin Magriba ta ce sun ƙarasa." Ya ce "Okay." Mama ta dubi Neehal ta ce "Zubo masa abinci, na san da ƙyar in ka ci tunda Hafsah bata da lafiya, suma su Afrah ki zubo musu." Ta ce "Toh." Tare da miƙewa ta fice. Ya ce "Allah yasa ina cin abin da kuka dafa." Mama ta ce "Koma mene haka zaka ci, har yanzu baka daina zaɓe zaɓen abinci ba ko Ameen? To tuwo na yi, itama Neehal yanzu ta gama cewa baza ta ci ba, na ce mata ta kwana da yunwa kuwa dan babu mai sake mun wani sabon girki yanzu, tunda ku tsurfar ku ta muku yawa." Ya yi ɗan murmushi tare da miƙewa ya fice daga ɗakin. Kitchen ɗin ya shiga inda ya tarar Neehal tana ƙoƙarin zuba miya. Ya ce "Kar ki zuba." Ta juyo ta dube shi ta ce "Ka fasa ci?" Ya gyaɗa mata kai. Ta ce "Na manta ashe fa baka cin tuwo, in dafa maka wani abun to?" Ya ce "Like what?" Ta ce "Akwai miya, sai ka faɗi abun da kake so in dafa maka." Ya ce "Okay, dafa mun ko mene ma." Ta ce "Toh." Ya juya ya fice. Ta dauko tukunya ta ɗauraye sannan ta zuba ruwa ta kunna gas ta ɗora. Ta buɗe frizer ta ɗauko kayan salad ta zauna ta fara yankawa kafin ruwan ya tafasa. Mama ce ta shigo kitchen ɗin ta dubi tukunyar data ɗora ta sannan ta dube ta, ta ce. "Me kike yi haka?" Ta ce "Yaya zan dafawa abinci, kin san ba ya cin tuwo." Mama ta ce "Oh, yanzu kin warke kenan zaki iya girki?" Ta ce "To Mama naga bai ci abinci ba, kar ya zauna da yunwa, kuma ba wani girki mai wahala zan yi ba." Mama ba ta ce komai ba ta juya ta fice. Mintuna kaɗan ruwan ya tafasa, ta ɗauko macaroni ta zuba fiye da rabin leda. Bayan ta gama ta juya a plate ta kai masa falo ta ajiye a gaban sa. Ya dube ta ya ce "Thank you." Sannan ya sauko daga kan kujerar da yake ya zauna a kan carpet, ya dubi abincin ya ce "Take another spoon." Ta koma ta ɗauko ta kawo masa, bai karɓa ya ce "Zauna mu ci." Ta ce "Yaya na k'oshi." Yay mata wani kallo, ba shiri ta zauna suka fara ci tare. A takure take sosai saboda ba su taɓa cin abinci tare ba, kanta a ƙasa take cin abincin ta kasa d'agowa ta kalle shi. Shi kuwa kallon ta ya ma fi cin abincin nasa yawa. Ba su fi rabin abincin ba ta ce ta ƙoshi, ya ce bata isa ba sai sun cinye duka. Dama Mama ta gama masa mitar tunda yasa a yi masa girki, to kar ya bar mata sauran abinci ko d'igo ya cinye duka. Haka ta haqura suka ƙarasa ci. Bayan sun gama ta ɗauke plate ɗin ta kai kitchen, su Afrah ta zubawa ragowar abincin a plate ɗin, kafin ta fito har ya fice daga falon. Ta wuce sama ta kai musu abincin, ta tarar su Cake ma suke ci da yoghurt. Ta ajiye abincin ta ce in sun gama sa ci, sannan ta fita zuwa ɗakinta. Tana ɗaukar wayarta ta tarar da missed call ɗin Sadik har huɗu, da chaji ma zata saka wayar, amma dai ta kira shi duk da ta ji an fara kiran isha'i, ya d'aga ya ce mata idan ya dawo daga masallaci zai kira ta.










Bayan an yi Sallar ya kira ta, ta daga suka gaisa ya tambaye ta jikinta ta sanar masa ta ji sauƙi. Cikin damuwa ya ce "Wifey wai me yake faruwa ne?, kwana biyu naga gaba-ɗaya kin canza mun, kafin ki yi rashin lafiyar nan idan na kira ki sometimes da daddare sai in ji call waiting, ina tsoron kar wani ya mun ƙafa fa." Ta yi shiru dan ita kanta ta san tunda Ahmad ya shigo cikin rayuwarta ta canzawa Sadik, dan ma yana da haquri da wani ne da tuni sun yi faɗa, ko kuma inda ita ce yake mata haka bata san ya za tay ba. Cikin sanyin murya ta ce "Ka yi haquri Husby, ni kaina na san ban kyauta maka ba, amma babu abun da ya faru, kuma babu wanda yay maka wata ƙafa balle hannu, har yanzu kai kaɗai ne a zuciyar Neehal." Cikin jin daɗi ya ce "Dagaske Wifey?" Ta ce "Gasken gaske ma, Ya Sadik ina da kai me zan yi da wani ɗa_namiji kuma?" Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Har na ji daɗi a raina, dan bana son abun da zai raba ni da ke." Ta ce "Insha Allahu Husby zamu rayu tare har ƙarshen rayuwarmu." Ya ce "Amin Amin Wifey." Suka Cigaba da hirar su ta masoya Sadik ya sanar mata Insha Allahu gobe zai zo, akwai maganar da yake son su yi. Ta ce Allah ya kai mu lafiya sai ya zo ɗin. Bayan sun gama wayar ta yi tagumi ta fara tunani, tabbas ta san zuciyarta Sadik take so, so mai tsanani ma kuwa, amma abun da ta rasa ganewa matsayin Ahmad a gurin ta, da farko tana masa kallon like ɗan'uwanta na jini, amma a kwanakin nan lissafin yana ƙoƙarin sauyawa a cikin zuciyarta game da shi. Ga kuma tausayinsa mai tsanani da take ji, saboda koda bai faɗa ba tana hango sonta mai tsanani a cikin kwayar idonsa, ga kuma yaransa da Allah ya ɗora mata kaunarsu, bata jin zata iya jurar Ahmad ya auri wata matar ta riƙe masa su Afrah, ta san kuma koda bata aure shi ba in ta ce masa ya bar mata su zai bata, amma ta san Mama baza taɓa yarda da hakan ba. Last abu kuma da yake damunta shine, ko zata yi auren at this time ko baza ta yi ba sai Allah, za'a barta da wanda zata aura ɗin ne ko za'a kashe mata shi kamar su Anwar?.... Shigowar su Afrah ya katse mata tunanin da take. Suka haye jikinta suka ce ta kira musu su Ummi, ta kira Zahra bayan ta ɗauka sun gaisa ta ba su wayar, suka yi mata surutun su sannan ta kaiwa Ummi wayar itama suka yi magana, har Dad ɗin su Ahmad yau sun gaisa da Neehal. Ta gaishe su cikin girmamawa su kuma su kay ta saka mata albarka. Bayan sun gama wayar ta ja su toilet tay musu wanka, tana shirya su suka dame ta akan ta kira musu Daddy'nsu. Ta kira shi kuma bai d'aga ba. Bayan ta shirya su, ta kama hannunsu suka nufi part ɗin Daddy dan su gaishe shi. Sai da goma ta wuce ta dawo part ɗin Mama ɗauke da Amrah a hannunta, Mama kuma ta biyo ta da Afrah dan har sun yi bacci. Bayan ta yi wanka ta sha magungunanta ta kwanta, lokacin sha ɗaya saura ƴan mintuna, ta ɗauko wayarta ta tarar da missed calls ɗin Ahmad, ta bi bayan kiran nasa, sai da ta kusan katsewa ya ɗaga cikin muryar bacci suka ɗan yi magana kaɗan, ya sanar mata fita suka yi da Mamy bayan ya koma gida, shi yasa bai kira ta ba, sai bayan sun dawo ya ga missed call ɗinta. Suna gama wayar itama bacci ya ɗauke ta.








Washegari Neehal ta tashi da ciwon cikinta, amma bai yi tsanani sosai ba. Sai wajen ƙarfe goma na safe ya tasar mata sosai, gashi Mama bata nan ta tafi gurin aiki tun 8. Ganin yanda take nuk'urk'usu da juyi akan gado su Afrah suka sauka ƙasa da gudu suka kira su Dije. A tare suka dawo da yaran. Dije ta riƙe mata hannu cikin tausayawa ta ce "Sannu Neehal, ina maganinki yake a ɗauko ki sha?". Tana hawaye ta buɗe baki da ƙyar cikin rawar murya ta ce "Yana ɗakin Mama." Zulai ta tafi da sauri ta duba amma bata gani ba. Ta dawo ta cewa Neehal "A ina take ajiyewa ban gani ba." Neehal ta taune lip ɗinta ta tashi zaune da ƙyar ta nuna musu wayarta, Dije ta ɗauko da sauri ta miƙa mata, ta karɓa ta cire key ta yi dialing ɗin Numbern Mama ta miƙa musu, ba tare da ta yi magana ba ta koma ta kwanta, hannunta dafe da mararta dake barazanar fashewa dan ciwo da murd'awar da take mata. Har wayar ta katse Mama bata ɗauka ba, suka ƙara kira bata ɗauka ba. Cikin damuwa Zulai ta ce "Bata ɗauka ba Neehal." Ta fashe da kuka saboda azabar ciwo, dama Maman ta ce mata yau surgery zata yiwa har mutum uku, ta san may be ta shiga theatre room ɗin shi yasa bata ɗauki wayar ba. Cikin Kukan ta ce "Ku kira Yaya ko Daddy su zo mutuwa zan yi." Su Afrah suka saka kuka ganin yanda take kukan itama. Zulai ta yi searching sunan Yaya ta kira. Sai da ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauka. A gaggauce Zulai ta sanar masa abun da yake faruwa, yana gurin aiki amma ya ce gashi nan zuwa gidan. (This week Ameen ya dawo Kano da aiki kamar yadda ya sanar da Mama, and an ƙara masa matsayi from captain to lieutenant Colonel.) Dije ta riƙe hannun Neehal tana zuba mata sannu, Zulai ta sauka ƙasa dan ɗauko ruwa ta tofa mata addu'a ta sha ko Allah zai sa a dace kafin Ameen ɗin ya ƙaraso. Bata kai ga ɗauko ruwan ba ta ji ƙarar door beil, ta nufi ƙofar da sauri ta buɗe cikin addu'ar Allah yasa wanda zai iya taimakon Neehal ɗin ne Allah ya kawo musu. Ahmad ta gani, ta bashi hanya ya shigo falon, cikin girmamawa ta gaishe shi. Ya amsa mata da fara'arta sannan ya tambaye ta Neehal, ta sanar masa bata da lafiya tana sama kuma Mama bata nan. A rikice ya ce su je ya ga jikin nata.












Suna shiga ɗakin, su Afrah suka tashi da gudu suka nufe shi. Amrah ta ce "Daddy Aunty bata da lafiya, sai kuka take." Bai bi takan yaran ba ya ƙarasa bakin gadon ya kamo hannun Neehal a ruɗe, lokacin ta galabaita matuƙa sai numfarfashi take kamar zata shid'e. Ya sunkuyo a hankali ya ce "Princess! Me yake damun ki?" Zulai ce ta faɗi amsa da faɗin "Ciwon ciki take." Ya ce "Okay." Ta buɗe idanunta da ƙyar ta kalle shi, sai kuma ta saka kuka cikin azabar ciwo ta buɗe baki da ƙyar ta ce "Uncle ka kai ni gurin Mama Please mutuwa zan yi." Ya shafa fuskarta cike da tausayawa ya ce "Sorry dear, zaki samu sauqi soon Insha Allah." Ya dubi su Dije ya ce "Dama tana yin irin haka?" Suka ce "Eh." Ya miƙe da sauri dan ya gano mai yake damunta, ya ce musu yana zuwa zai je ya dawo yanzu. Afrah ta ce "Daddy ta kai ta hospital please." Ya ce "No yanzu zan dawo na bata magani." Cikin sauri ya fice daga gidan ya je wani pharmacy ya siyo allura ya dawo gidan. Kafin ya dawo har ta yi amai a ƙasan gadon, su Dije suna cikin gyara wurin ya dawo. Ya haɗa allurar sannan ya hau kan gadon ya d'ago ta a hankali. Ta faɗa jikinsa ta k'ank'ameshi sosai cikin gigitar ciwo. A hankali ya d'aga rigar jikinta tare da ɗan zame dogon wando jikinta yay mata allurar. Ta saki gwauron numfashi tare da ƙoƙarin barin jikinsa, ya ƙara riƙe ta da kyau da ɗaya hannunsa, ɗayan hannun kuma yana mulmula mata wurin allurar. Fita su Dije su ka yi da kayan da suka gyara inda tay aman. After 5 minutes har lokacin tana jikinsa, ta yi lamu a jikinsa tare da lumshe ido, ga dukkan alamu ta fara samun relief, sai ajiyar zuciya take saukewa akai_akai. Amrah ta ce "Daddy ta ji sauqi ko? tunda ka yi mata injection?" Ya gyaɗa mata kai. Afrah ta saki ajiyar zuciya ta ce "Thank God." Neehal ta fara ƙoƙarin tashi daga jikinsa dan tun sanda ta yi amai ta ji jinin ya fara zuba a jikinta, kuma gashi bata saka pad ba tana tsoron kar ta yi stain a jikinsa. Ya ƙi bata damar hakan sai ma ƙara gyara mata kwanciya da ya yi a jikinsa, ji yake kamar ya mayar da ciwon jikinsa, a hankali ya ce "Princess ya jikin?" Ta gyaɗa masa kai kawai, ya fara gyara mata gashin kanta wanda ya ɗan barbaje har saman fuskarta ya ce "Allah ya baki lafiya Baby." Ta jinjina masa kai kawai, ita so take ta bar jikinsa amma ya hanata, gashi sai ƙara jin zubar jinin take a jikinta, tana tunanin ma ta ɓata shi. Turo ƙofar ɗakin akai da ƙarfi hakan yasa ta buɗe idonta da sauri ta kalli ƙofar, Ahmad ma ƙofar ya kalla.

Please Login or Register in order to submit comment