Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

damuwarta take a halin yanzu, shima shirun ya yi, amma ba ka isa ka gane ko wani abu ya na damunsa ko akasin haka ba a halin yanzu.






Washegari Neehal ta tashi jikin nata da ɗan dama, dan Mama a gurinta ta kwana, tun dare jinin ya ɗauke mata, hakan ya sa da asuba ta yi wanka ta yi sallar ta, ta daɗe ta na wa Anwar addu'ar samun dacewa, da waɗanda kullum da koyaushe cikin yi musu take, da Jameel da ma dukkan Musulman da suka rigamu gidan gaskiya baki ɗaya. Zuwa yanzu zuciyarta ta gama tsinkewa ta haƙura ta fawwalawa Allah komai, Amma kallo ɗaya Mutum zai mata ya hango ramar da ta yi lokaci ɗaya, bayan ta gama addu'o'inta ta janyo wayarta wadda rabonta da ita tun jiya, missed calls d'in da akai mata take dubawa, Numbobin da ta sani da wanda ba ta sani ba gasunan rututu har ta rasa kiranwa ma za ta bi. Aranta ta ce "Da waninta ne ya mutu ba Anwar ba, da har da missed calls d'inshi za ta gani, kuma shi kaɗai za ta iya bin kiranshi, wani abu ta ji ya tokare mata a k'irji, a hankali ta shiga App din free kur'an ta buɗe ta fara karanta Suratul Baƙara, domin ta san shi kaɗai zai mata maganin abun da yake damunta. Ta yi nisa a karatun Ameen ya shigo ɗakin, ba ta ma san ya shigo ba har ya yi sallama, saboda hankalinta gabad'aya ya na kan karatun da take, a ƙoƙarin ta na ganin ba ta ba wa damuwa damar zama a cikin zuciyarta ba, sai dai k'amshin turarensa da baya b'uya ya sanar mata da zuwan nashi, ta d'ago da kanta da sauri cikin mamaki dan ba ta san ya kwana a gidan ba, gabanta ya faɗi haɗa idon da suka yi da shi, ta ɗauke idonta da sauri daga kallon shi bugun zuciyarta na ƙaruwa ba tare da tasan dalili ba, nufar inda take ya yi cikin takunsa na ƙasaita da burgewa..........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:31] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_










0️⃣8️⃣












..........Tsugunnawa ya yi a gabanta ya na kallon ta, ƙasa ta yi da kanta zuciyarta na cigaba da bugawa, lumshe idonta ta yi saboda daddad'an k'amshinsa da ya mamaye mata hanci, numfashi ta ja tare da lumshe idanunta, a hankali ya kama tattausan hannunta da nasa, cikin sanyin murya ya ce "Miemerh! Ya hakurin rashin Anwar?" Cikin muryarta da ta ɗan dashe saboda damuwa ta ce "Alhamdullah" fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce "Allah ya ji k'an shi, ya sa ya huta." Neehal ta d'ago kanta a hankali tare da buɗe idanunta da suka cika taf da hawaye, ta ce "Amin, amma Yayah me ya sa ba ka zo tun jiya ba?" Ta k'arashe zancen hawaye na zubo mata, ba tare da ya saki hannunta ba ya shiga share mata hawayen fuskarta da ɗayan hannun nasa, cikin murya mai nuni da rarrashi ya ce "Am sorry, ban samu labarin mutuwar da wuri ba ne." Neehal ba ta ce komai ba, sai hawaye kawai take kamar jira take a taɓa ta dama. Ameen ya ce "Kukan na mene kuma? Kin san dai mamaci ba ya buƙatar kuka ko?" Neehal ta na kuka ta ce "Dole in yi kuka Yaya, me Anwar ya yi aka kashe shi, haka ma fa a ka kashe mun Jameel, shima Anwar d'in ba za su bar mun sh......." Rungumeta Ameen ya yi tsam a jikinsa cikin tsananin tausayinta, sosai shima al'amarin ya rud'a shi, Ajiyar zuciya Neehal ta shiga saukewa ta yi luf a kirjinshi tare da dena kukan. Shigowar Mama d'akin ya sa ta janye jikinta daga na shi da sauri, Mama ta kalle su ta ce "Me ya faru?" Ameen ya mik'e tsaye ya ce "Babu komai" Sannan ya sa kai ya fice. Mama ta zauna a bakin gado ta na duban Neehal ta ce "Kukan me ki kay?" Neehal ta girgiza mata kai alamun babu, Mama ta ce "Shikenan tashi mu je ki yi breakfast, Haneefah na hanya idan ta zo sai ku wuce gidan su Anwar" Neehal ba ta yi musu ba ta mik'e suka sauka k'asa tare da Mama. Tea kawai tasha kaɗan, shima dan kar Mama ta mata fad'a ne, Mama ta ce "Shikenan abin da zaki sha kuma ki ce kin k'oshi?" Neehal ta ce "Eh Mama ba zan iya ƙara cin komai ba" Mama ta ce "Daurewa za ki, ki ci ko Irish ne kaɗan" Neehal ta ɓata fuska, sannan ta d'ibi Irish d'in kadan ta ci, ta na kokarin barin falon Haneefah ta shigo da sallamarta, suka amsa mata ta gaida Mama, sannan ta dubi Neehal ta ce "Besty ya hak'urinmu?" Neehal ta ce "Alhamdulillah, ya kuka je gida jiya?" Haneefah ta ce "Lafiya k'alau" Sama suka hau tare, suka je d'akin Hajiya suka gaisheta. Neehal ta ɗauki wayoyinta suka fito suka yi wa Mama sallama, sannan suka je part d'in Dad suka gaisheshi. Yau ma Neehal an zo mata ta'aziyya sosai, Uncle Mahmud da ya koma gida jiya yau ma ya dawo har da matarsa da 'yarsa budurwa kamar su Neehal, sai dai Neehal ta ɗan girme ta. Ameen da Dad yau da su a ka wuni gurin zaman makoki. Da yamma Police masu fararen kaya suka zo gidan mutuwar domin yin tambayoyi ga ahalin Anwar, bayan sun gama da mutanen waje suka shigo cikin gidan, inda suka ce a kai su gurin Mahaifiyar Anwar. Ammi ta na ɗakinta ta ce su shigo, su su uku ne kuma duk maza ne, ɗaya daga cikin su wanda da alama shine babban su ya dubi Ammi ya ce "Hajiya ina yini, ya ƙarin hak'uri kuma?" Ammi ta ce "Lafiya k'alau Alhamdulillah" Ya ce "Allah ya ji k'an shi ya gafarta masa" mutanen d'akin suka amsa da "Amin" gabatar wa da Ammi kansa ya yi da na abokan aikinsa sannan ya ɗora da faɗin "A daren ranar da ana washegarin Anwar zai mutu, kun zauna da shi? Ma'ana kun yi doguwar hira?" Ammi ta ɗan yi jim na wasu sakonni kafin ta ce "Eh mun yi hira amma ba wata me tsayi ba" Mutumin ya ce "Ko a cikin hirar taku ya faɗa miki sun yi faɗa da wani ko kuma sun samu ɗan sabani haka?" Ammi ta ce "Gaskiya A'a, dan gaba-da'ya ma hirar a kan kai lefen sa da za'a kai ne washegari" Mutumin ya jinjina kai ya ce "Kuma ba ki ga wata alamar ɓacin rai ko damuwa a tattare da shi ba?" Ammi ta ce ko kaɗan, sai ma tarin farin cikin da ya kasa b'oye shi, abun ma da na san ya faɗa mun wanda ya ɗan dame shi, sai rashin lafiyar da ita yarinyar da zai aura take yi, harma ya ce mun zai je ya gano jikin nata a wannan lokacin" Mutumin ya ce "Daga nan ba ku sake haɗuwa ba a wannan daren?" Ammi ta ce "Eh, sai dai sallama da ya zo ya mun, lokacin wajen 11 na dare" Mutumin ya ce "Kuma a nan ma ba ki ga ya na cikin wani yanayi ba ko kuma damuwa haka?" Ammi ta ce "Gaskiya ko kaɗan ban ga haka ba" Mutumin ya gyara zama ya ce "Ki yi hak'uri da tambayoyi na fa, sha'anin aiki ne" Ammi ta ce "Babu komai, ka ci gaba insha Allah zan faɗa maka duk abin da na sani" Mutumin ya gyad'a kai sannan ya ci gaba da magana "To a baya fa, ya taɓa faɗa miki ya na da wani wanda ba sa shiri da shi, ko a makaranta ko gurin aiki ko unguwa ko wani guri daban?" Ammi ta yi shiru na wani gajeren lokaci ta na tunani, sai kuma can ta girgiza kai ta ce "Gaskiya babu, domin Anwar tunda ya girma ba zan ce ga abokin faɗan sa ba, ko cikin abokansa da 'yan'uwa da unguwa harma gurin aikin na su, idan ma da akwai bai taɓa faɗa mun ba, kuma gaskiya ba ya b'oye mini duk wani abu nashi, komai zai faɗa mun ya ce Ammi ki ta ya ni da addu'a." Mutumin ya jinjina kai ya ce "A ranar da zai rasu ya yakasance ya tashi kamar kullum da ya saba ko da wani canji?" Ammi ta sauke Numfashi muryarta na ɗan rawa ta ce "Lafiya k'alau muka tashi kamar kodayaushe, Misalin ƙarfe 7 da k'wata kamar yadda ya saba ya zo nan gurina, muka gaisa k'annensa suka kawo masa abincin kari ya ci, sannan ya mun sallama ya tafi gurin aiki, kuma kamar yadda ya saba da ya ƙarasa wajen aikin ya kira ni ya ce mun ya je lafiya, daga nan sai mummunan labarin da muka j......." Ta fashe da kuka mai ban tausayi. Mutumin ya jinjina kansa a karo da yawa ya ce "Sai hak'uri Hajiya, Allah ya ji k'an shi, Mun gode da haɗin kai da ki ka ba mu, Insha Allah za mu yi iya ƙoƙarin mu wajen ganin an gano waɗanda su kai kisan kuma an bi muku hakkin ran ɗanku, idan da buƙatar sake zuwa mu miki wasu tambayoyin za mu dawo" Ammi ta gyad'a masa kai ta na share hawayen fuskarta. Mutumin ya dubi ɗaya daga cikin wanda suka zo tare mai rubuce_rubuce ya ce "Ya kamata mu ga yarinyar da zai Aura ita ma" Ɗayan ya ce "Haka ne Sir" Ammi ya tambaya ina Neehal ta ce ta na falo bari a kira masa ita, bayan ta zo sun gaisa ya mata ta'aziyya sannan ya dubeta da kyau ya ce. "Malama Neehal, a zamanku da Anwar ko ya taɓa faɗa miki cewa ya na da wani abokin faɗa ko kuma wanda ba sa jituwa?" Neehal da kanta ke ƙasa cikin sanyin murya ta ce "Gaskiya bai taɓa faɗa mun ba, Ni tunda nake da shi ma bai taɓa ce mun yau sun yi faɗa da wani ba, ko kuma wani ya ɓata masa rai ba" Mutumin ya ce "Ke ce wadda ya yi waya da ke ta ukun ƙarshe kafin rasuwar sa, shin da kuka yi waya kin ji wata alama da take nuni da ba ya cikin wani firgici ko damuwa? duba da a gurin aikinsa har cikin office d'insa a ka je a ka kashe shi, kuma wayar ki da shi ko 2 hour ba'ayi ba hakan ta faru" Neehal ta ce "Ko kaɗan ban ji alamar hakan ba gaskiya" Mutumin ya jinjina kai ya ce "Shikenan Malama Neehal bari na barki haka, next time idan buƙatar mu ƙara tattaunawa da ke ta taso, za mu nemi ki" Neehal ta gyad'a masa kai kawai, zuciyarta na bugawa.




Haka a ka ci gaba da zaman makokin mutuwar Anwar, Neehal kullum su na zuwa gidansu Anwar da safe sai dare suke tafiya har a ka yi sadakar uku, daganan kuma bata ƙara komawa ba saboda ita ma ana zuwa gida yi mata gaisuwa, sai ranar sadakar bakwai suka kuma komawa. Yau Juma'a wanda ya kama kwana goma sha biyu da rasuwar Anwar, zuwa yanzu Neehal ta sakawa zuciyarta dangana game da mutuwar Anwar, Anwar ya riga ya tafi ya zama tarihi addu'ar su kawai yake buƙata, duk da wani lokacin ta na damuwa sosai har ta zauna ta yi ta kuka, Mama,Dad, Haneefah sune 'yan rarrashin ta da bata baki gami da nasihohi, Ameen ma yanzu wata kulawa yake bata ta musamman saboda tausayi take basa sosai, ta zama wata so silent wannan rigimar da neman magana gurin Mama duk ta daina, Magana ma ba sosai take yinta ba, ga rama da ta yi. Misalin ƙarfe Biyar na yamma Neehal ta na zaune a falon ƙasa ita kaɗai ta na kallon Sunna TV, gani ta yi Dije mai aiki ta fito daga dakinsu da sauri, ashe ƙarar bell ta ji, ita ba ma ta ji ba ta na can duniyar tunani. Dije ta na buɗe door d'in ta ga kanwar Dad ce ta zo tare da 'yarta, hanya ta ba su ta na musu sannu da zuwa cikin girmamawa, Matar ce kawai ta amsa mata a wulak'ance amma 'yarta ta ko kallon ta ba ta yi ba, ta wuce ciki ta na taunar cingum ƙas_ƙas ga takalmin ƙafarta mai shegen tsini sai ƙara yake a kan tiles ɗin falon, k'amshin turarenta mai hawa kai ya cika falon, fara ce tass kamar ka tsaga jikinta jini ya fito amma gajeriya ce ta na da madaidaicin jiki, ta na sanye da wata doguwar riga 'yar kanti, ta yafa mayafi kalar rigar kanta babu ɗankwali sai fuskarta da ta sha uban make up. Neehal ta bita da kallo fuskarta ba yabo babu fallasa, ita kuwa wani matsiyacin kallo take bin Neehal da shi. Neehal ta yi ɗan murmushi ta ce "Sannunku da zuwa Aunty Hamida" kamar ba ta ji ba, ta yi banza da ita, Neehal dama ta san za'a rina, duk da kasancewar Hamida 'yar gidan k'anwar Dad ce amma ba sa shiri ko kaɗan, ko dan hakan ya samo asali ne daga rashin shirin Mahaifiyar Hamidan da Mama ne?. Neehal ranta ya ɓaci a kan abin da Hamida ta mata, dama shi ya sa bata son shiga sabgarta, Mama ce ke tursa sata dole, ta rasa me ta yi wa Hamidan ta tsane ta over. Hamida ta zauna ta na kar kaɗa ƙafa, Mahaifiyarta wadda suke k'ira da Mumy ta ƙaraso cikin falon ta zauna ita ma ta na huhhura hanci, Neehal ta dube ta ta ce "Sannu da zuwa Mumy ina yini?" Ta mata wani kallo ta ce "Lafiya k'alau, ya hak'uri kuma?" Neehal ta ce "Alhamdulillah." Daga haka suka yi shiru, Neehal ta maida hankalinta a kan kallon da take, bayan wasu mintuna Mama suka sakko ita da Hajiya da Dije da ta je kiranta. Mama ba yabo ba fallasa ta ce "Sannunku da zuwa" Mumy ta ce "Yawwa" Mama ta ce "Ya gida Suwaiba?" Mumy ta ce "Lafiya k'alau" Mama ta ce "Masha Allah" tare da zama a kan kujera, Hajiya ma ta zauna. Hamida kamar ba ta so ta ce "Ina yini Mama?" Mama tace "lafiya k'alau, Hamida ya aiki" tace "Fine Mama" Hajiya yadda ba su mata magana ba, itama ba ta musu ba, TV kawai take kallo hankalinta kwance. Su Dije suka dawo falon da ruwa da lemo gami da drinks, Zulai ta gaishe su kamar yadda Mumy ta amsa wa Dije haka ta amsa wa Zulai a wulak'ance. Can dai Mumy ko me tuna sai ta dubi Hajiya ta ce "Ina yini Hajiya?" Hajiya ta ce "Lafiya" tana keb'e fuska, Hamida da ke ta latsa wayarta ita ma ta gaishe ta a yangance. Mumy ta gyara zama ta dubi Mama ta ce "Sai muka ji kuma an kashe saurayin Neehal" Mama ta ce "Eh ƙaddara ta riga fata." Mumy ta ce "To Allah ya ji k'an shi, amma ni fa ina ganin wannan abun kamar da sa hannu, a ce yarinya duk wanda maganar aure ta shiga tsakaninsu sai an kashe shi, sai ka ce firlm ko labaran tatsuniya?" Mama ta yi shiru ba ta ce komai ba, domin da rainin hankali Mumy ta yi maganar. Hamida ta tab'e baki ta ce "Hmmmm gaskiya dai Mumy, dan Ni na ma fi tunanin ko wani baƙin Aljanin ne ya aure ta.........✍️








*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:31] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*












_By_
_Zeey Kumurya_








0️⃣9️⃣










...........Hajiya ta dubi Hamidah ta na mitsi_mitsi da ido ta ce "Ke! Ki iya bakinki, mugun nufinki Insha Allahu ba dai a kan Neehal ba, ato, bakinki ya sari ɗanyen kashi" Hamida za ta kuma magana Mommy ta girgiza mata kai, tab'e baki ta yi ta ci gaba da latsa wayarta a gadarance, Mama kuwa kamar ba ta ji su ba, ta musu banza. Neehal ma ko d'aga kanta ba ta yi ba, balle ta nuna ta san me su ke cewa. Hakan kuwa ba ƙaramin k'ona ran Mommy ya yi ba, domin kuwa ta so Mama ta kula ta su yi ta yi, ko kuma Neehal ta tankawa Hameedah Dad ya dawo ta haɗa mata sharri, sai kuma ba ta samun haɗin kai ba. Mama tashi ma ta yi ta wuce sama abin ta, Neehal ma bin bayanta ta yi dan zaman falon ya ishe ta. Hakan kuwa ya ƙara kona ran Mommy. Ɗakin da suke sauka idan sun zo Mama ta sa su Dije suka gyara musu, da yake daga Abuja suke a can suke da zama, su Dije suka kwasar musu kayansu zuwa d'akin. A gadarance su Mommy da Hameedah suke yin komai a gidan, Mama kuwa ba ta tanka musu haka ma Neehal, Hajiya ce ma sarkin magana, amma Mama ta roƙe ta a kan ko me za su yi kar ta kula su. Ko da Dad ya dawo part d'insa suka je su na hira, har sai da dare ya yi sosai sannan ya ce ya kamata su je su kwanta, Mama kuwa dama ta san hali shi ya sa ba ta je ba, sai da ya kira ta da kansa a waya. Washegari Neehal tun safe ta wuce gurin aiki, dama tun ranar mutuwar Anwar ba ta koma ba sai yau.




Misalin ƙarfe 11 na safe Ameen ya shigo gidan, kamar yadda ya saba part d'in Mama ya nufa direct, da key d'in hannunsa ya yi amfani ya buɗe kofar, da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga. Hameedah ce kwance a kan kujera ta na latsa waya, Mahaifiyarta kuwa ta fice gidan k'awayenta. Da sauri ta tashi zaune jin sallamarsa tare da faɗaɗa fara'arta wadda tun da ta zo gidan ba ta yi kamarta ba. Ameen ya kalle ta sau ɗaya ya kau da kansa, har ya ƙaraso cikin falon kallon sa take kamar za ta lashe shi bakin ta ya ƙi rufuwa dan farin ciki. Cikin kaud'i da iyayi ta ce "Sannu da zuwa Ya Ameen." Ta ƙarashe zancen tare da mik'ewa ta koma kusa da shi. Ya kalle ta ba yabo ba fallasa ya d'aga mata kai. Hameedah ba ta damu ba ta ce "Yayanah I missed you so much, na manta when last da na ganka, last zuwan da na yi ba mu haɗu ba, gashi kai kuma ba ka zuwa gidanmu." Ameen ya banzatar da zancen nata ya ce "Yaushe ki ka zo?" Cike da jin daɗin ya biye mata suna hira ta ce "Yesterday, ni da Mommy mun zo gaisuwa ne?" Ameen ya ce "Tun yaushe aka yi rasuwar amma sai yanzu za ku zo?" Hameedah ta ɗan shagwab'e ta ce "To ai Yaya ka ga ina zuwa aiki, sai weekend nake da time." Ameen ya yi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma can ya ce "Neehal as she is your cousin sis, amma a mata rasuwa ki ce sai kin samu time za ki zo mata gaisuwa?" Hameedah ta tab'e baki tare da ɓata fuska ba ta ce komai ba, sai kuma can ta ce "Kasan Mommy ma ba ta ji dad'i ba time ɗin shi ya sa ba mu zo ba, kuma na ga ita gaisuwa ai ba ta tsufa, tun da mun masa addu'a ai is ok." Ameen bai kuma ce mata komai ba ya mik'e ya nufi sama gurin Mahaifiyarsa. Mama ta na operating system ya yi knocking k'ofar ɗakin, Mama ta ba da umarnin a shigo. A hankali ya buɗe k'ofar bakin sa ɗauke da sallama. Mama ta d'ago ta na duban sa ta amsa masa, ya ƙaraso ya zauna a gefen ta ya ce "Gud Morning Mum, how are you?." Mama ta ce "Lafiya, ka zo lafiya? Ya aiki?" Ya ce "Alhamdulillah, ina Neehal fa?" Mama ta ce "Ta je aiki." Ya gyad'a kai kawai tare da ƙoƙarin mik'ewa. "Koma ka zauna ina son magana da kai." Muryar Mama ta katse masa hanzarinsa. Ya gyara zama tare da bata duka hankalinsa. Mama ta ture laptop d'in gabanta ta na dubansa da kyau ta ce "Ameen me kake tunani a kan al'amarin Neehal? Ba ka ganin kamar wasu ne suke bibiyar rayuwarta? Duba da a baya an kashe Jameel ma" Shiru ya yi alamun nazari kafin ya sauke Numfashi ya ce "Mum, babu irin tunanin da ban yi ba a kan wannan al'amarin, tun lokacin na ci karo da labarin mutuwar Anwar dake ta yawo a media, amma kuma da na yi wani nazari da lissafi sai na ga kamar kisan Anwar da Jameel ba shi da alaƙa da Neehal." "Saboda me ka ce haka?" Cewar Mama ta na kallon sa. Ameen ya ce "Idan ba ki manta ba Mum, shi Jameel dama can ya na da 'yan adawa a rayuwarsa duba da yanayin aikinsa." Mama ta ce "Hakane, domin kuwa tun a wancan lokacin da aka kashe Jameel ko kaɗan ban yi tunanin kisan ya na da alaƙa da Neehal ba, dan some times Idan ya zo gaishe ni ya na yawan cewa a taya su da addu'a saboda magauta da mahassada, amma kuma kashe Anwar da aka yi ya birgita mun duk wani lissafi na Ameen." Ameen ya ce "Duk da an kashe Anwar amma ba na tunanin kisan Anwar ya na da alaƙa da na Jameel" Mama ta yi shiru ta na jin dama furucin Ameen zai tabbata da sai tafi kowa farinciki, za ta so a ce ba dan Neehal ake kisan ba, amma kuma abun da kamar wuya musamman idan ta yi duba da....... "Kar ki sa wa ranki damuwa Please Mom, kuma ki cire tunanin wai ko dan Neehal aka kashe Anwar" Ameen ya katsewa Mama tunaninta da faɗin haka. Mama cikin damuwa ta ce "Ameen! Ka na so ka kwantar mini da hankali ne kawai kamar yadda ka saba a kodayaushe idan ka ga ina cikin damuwa, amma ba ni kaɗai ba ma, ko A'isha da Sadiya mun yi maganar da su kuma suma duk tunanin su haka ne." "To ai dama tunanin ku duk ɗaya ne ku mata." Cewar Ameen ya na murmushi. Mama ta ɗan harara shi ta ce "Su kuma sauran mazan da muka yi maganar da su fa?" Kamar a ɗan rud'e ya ce "Su wa kenan?" Mama ta masa wani kallo ta ce "To mene na yin hakan kuma, kamar wanda aka zabura?" Ameen ya ɗan lumshe idonsa ya ce "Nothing, kawai ban so ki ka yi maganar da wasu ba" Mama ta ce "Ahmad ɗin Sadiya ne fa sai Mahmud, su kuma ka ga ai duk na gida ne." Ameen ya ce "Hakane, Insha Allahu ko ma yaya ne Allah zai warware mana, kuma Insha Allahu problem ɗin ba daga wurin Neehal ta ke ba." Mama ta ce "Ameen ya Allah." Ameen ya mik'e ya na faɗin "Ina Hajiya fa?" Mama ta ce "Tun safe driver ya kaita gidan Sadiya yau can za ta wuni." Ya ce "Ok" har ya juya Mama ta ce "Ka ga Hameedah kuwa" ya gyad'a mata kai alamar Eh ba tare daya juyo ba, Mama ta yi murmushi kawai dan tasan tun da ya yi haka ba ya son zancen Hameedan ne.




Neehal ta na zaune a office d'inta ta na duba wasu takardu Haneefah ta shigo office d'in bakinta ɗauke da sallama. Neehal ta amsa mata tare da dire da takardun a kan table ɗin gabanta. "Har kun gama editing ɗin?" Neehal ta tambayi Haneefah dake ƙoƙarin zama. Haneefah ta ce "Eh, ai time ɗin labaran ya kusa" Neehal ta ce "Hakane" sannan ta gyara zama ta na duban Haneefah ta ce "Haneefah!" Haneefah ta dube ta da mamaki domin tasan tunda Neehal ta kira ta da sunanta abu mai mahimmanci za ta faɗa mata. Neehal ba ta jira amsar Haneefah ba ta cigaba da magana. "Haneefah zuciyata ta na cikin fargaba gami da zullumi da tsoro a kan kisan Anwar, Ina tsoron a ce ta dalilina aka kashe Anwar" Haneefah ta ce "Me ya sa ki ke cewa haka ne wai Neehal, ta yaya kisan Anwal zai zama saboda ke?" "Saboda an kashe Jameel ma a baya." Haneefah ta ce "Ki dena tunanin saboda ke aka kashe su, na faɗa miki wannan maganar tun kafin yau amma kin k'i ki daina ta, akan me za'a na kashe miki samari?" Neehal ta ce "Shine ban

Please Login or Register in order to submit comment