Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata gani ba? Ko kuma ka zo ne ka aiwatar da mummunan nufinka a kanta a gaban mu?" Daddy ya ƙaraso kusa da ita ya kama hannunta kamar zai yi kuka ya ce. "Dan Allah Fateemah ki tsaya ki saurare ni in miki bayani, na san a yanzu ji kike kamar ki kashe ni saboda tsana, amma dan Allah ki tsaya ki ji mai zan faɗa miki, wallahi ba laifina ba ne nima babu yadda zan yi ne." Mama ta fizge hannunta ta ce. "Muhammad ko ganin ka bana k'aunar yi balle na ji wannan muryar taka mai ƙara mun k'una da baƙin ciki a cikin raina, dan Allah ka fice daga ɗakin nan ko kuma ni in fita in bar maka gidanka. Ka ba ni mamaki kuma ka bani kunya, ashe dama ba dan Allah kake riƙon Neehal ba? Yanzu duk abubuwan da suke faruwa da ita kai ne sanadi?" Daddy ya ƙara riƙe hannunta ya ce. "Please Doctor, ki mun wannan alfamar ki tsaya ki saurare ni in miki bayani, ko da wannan zata kasance alfarma ta ƙarshe da zaki mun a rayuwata. Please and please, ni kaina a yau na ji tsani kaina da rayuwata." Mama ta kuma k'wace hannunta ta ce. "Bayanin me zaka mun Tafiya? Bayanin kai ka kashe Jameel da Anwar ko kuma bayanin kana riƙon Neehal ne saboda ka lalata rayuwarta? Ko kuma bayanin da zai ƙara tabbatar mana kana cikin ƙungiyar matsafa kai ɗan shan jini ne?" Abba dake bakin ƙofa yana kallon su cikin tsananin mamaki ya ce. "Subhallahi, Fateemah me kike faɗa haka? Kin san kuwa mai kike cewa? Mijinki ne fa General Muhammad Tafida a gabanki ba wani ba." Mama tana hawaye ta ce. "Na sani Yaya, Na sani." Sai ta mayar da duban ta ga Daddy ta ce. "Ka cuce ni, ka cuce ni Muhammad, ka ɓata wayonka, ka ɓata rawarka da tsalle, yanzu duk damuwa da k'aunar da kake nunawa Neehal duk na Ƙarya ne? pretended kawai kake yi saboda kar mu gano mummunan nufinka a kanta? Muhammad why? Me yasa? Mai Ubangiji ya rage ka da shi a rayuwar nan da ka zaɓi saɓa masa da laifin da ba ya yafewa? *Shirka* fa muham......" Kasa ƙarasa abun da take son faɗa ta yi saboda numfashinta da ba ya fita sosai, sai haki take jikinta na wani irin ƙyarma. Daddy ya yi ƙoƙarin riƙe ta ta yi baya da sauri kamar zata faɗi, da sauri Aunty Sadiya ta tashi ta riƙe ta, ta zaunar da ita a bakin gado. Cikin kuka Hajiya ta ce. "Na shiga uku ni Zainabu, wannan wacce irin masifa ce, Allah ka farkar da ni idan mafarki nake." Aunty A'isha ta dubi Mama cikin sanyin murya ta ce. "Ki yi haquri mu saurari Yaya Tafida mu ji me yake tafe da shi, ki bi komai a sannu dan Allah, kar wani mummunan ciwon ya kama ki." Mama zata yi magana amma ta kasa, sai jujjuya kanta kawai take. Abba ya ce. "Ni fa ƙara saka ni a cikin duhu kuke, dan Allah ku fahimtar da ni abun da yake faruwa." Aunty A'isha ta ce masa. "Ka zauna yanzu zamu ji komai daga bakin Yaya Tafida." Abba ya ƙaraso ya zauna akan carpet cikin tsananin al'ajabin wannan murdadden al'amarin. Aunty A'isha ta mayar da duban ta ga Daddy dake ta yiwa Mama sannu cikin tsananin tashin hankali, ta ce masa. "Ka zauna ka yi mana bayanin muna sauraren ka." Daddy ya sauke nannuyar ajiyar zuciya ya goge gumin da ke ta tsalala a fuskarsa sannan ya zauna shi ma ya fara magana kamar haka.












Shekaru goma sha uku da suka wuce baya Abokaina Alhaji Karbir Ginyau da Alhaji Idris suka dame ni akan na shiga harkar siyasa, tunda ina da kuɗi kuma na san manyan mutanen ƙasar nan gani General na sojoji mulki ba zai mun wahala ba. Na nuna musu ni bana son harkar siyasa ko kaɗan kuma ba zan yi ba. Alhaji Kabir abokina ne tun samartaka, zan iya kiran shi ma da aminina. Sai dai halayyar mu k'wata_k'wata ba iri ɗaya ba ce, shi mutum ne mai matuƙar son abun duniya dan zai iya yin komai akan kuɗi, sannan yana harkar bin matan banza. Ina faɗa masa gaskiya a kodayaushe a matsayinsa na abokina amma ko kaɗan ba ya ɗauka. Yakan ce mun idan mutum bai shana ba a gidan duniya mai zai yi? Da na ga ba zai taɓa dena halinsa ba sai na koma bin shi da addu'ar fatan shiriya idan mai shiryuwar ne. Kabir ya dinga mun naci da magiya akan in shiga siyasa harkar akwai samu sosai a cikinta. Na nuna masa ni fa ba zan yi ba, amma ya ishe ni da naci da magiya, har na amince masa zan yi amma na ce sai na yi shawara da iyalina. Na tuntubi Fateemah da maganar, da farko ƙin amincewa ta yi sai daga baya na lallaɓa ta ta yarda da ƙyar ta amince in yi siyasar, bayan ta kafa mun sharad'an yin komai cikin gaskiya da tsoron Allah. Zuwa lokacin nima ina son yin siyasar sosai, Kabir ya ƙwadaita mun yanda ake samun Alkhairi a cikin ta. Ban fara siyasa daga matakin ƙasa ba sai na fito takarar shugaban ƙasa. Na saka kuɗi na mai yawa na siyi Form ɗin takara. A hankali na fara tara mabiya da magoya baya, na samu waɗanda suka daɗe a cikin siyasar ake damawa da su suka d'aga hannuna. Tunda na fara harkar sai na fara shiga busy, yau mu ne nan garin gobe mu ne can. Wannan dalilin yasa Fateemah ta ƙara tsanar harkar, har ta fara mun zancen ko zan haqura in daina. A lokacin ni kuma abun ya shiga raina sosai gaskiya, sai na lallaɓa ta na ce mata da zarar komai ya dai-dai ta zan koma normal kamar da. Ana haka Kabir ya ce mun harkar siyasa fa dole sai an haɗa da taimakon malamai. Ban kawo komai a raina ba nake ba shi kuɗi a matsayin wanda za'a kaiwa malamai suke yin addu'a. A lokacin ni akaran kaina na san idan aka yi Elections ba zan taɓa winning ba, amma sai na saka a raina komai dan dagiya ne wani lokacin zan iya cin zaɓen. Sai na dage da taimakawa jama'a da takalawa, ta hanyar samar da maguda nan ruwa a wuraren da ba su da ruwa, da kuma gina masallatai a ƙauyuka. A hankali sunana ya fara baza ƙasar nan, mutane suka san ni sosai. Watarana ranar da ba zan taɓa iya mantawa da ita ba a rayuwata, ranar baƙin ciki ranar da tsautsayi yasa na faɗa cikin k'azamar ƙungiyar da babu komai a cikinta sai shirka da tsantsar rashin imani. Alhaji Kabir ya zo ya same ni har office ɗina ya ce mun, yanzu na fara yin masoya sosai a ƙasar nan, zata iya yiyuwa in ci zaɓe, dan haka in zo mu je zai kai ni wani guri da za'ai mun aikin da zai saka in ci zaɓen, dan siyasar yanzu dole sai da haka. Na ce masa in dai gurin kaucewa hanya ne baza ni ba, ni babu wanda zan kaiwa kukana sai Allah shi zan roƙa da shi na dogara. Kabir ya dinga nuna mun ba wani abu ba ne ai wannan is common thing, in ma ban yi yanzu ba sai na yi watarana, dan indai na ce kwanciya zan yi a siyasa zan ga kwanciya, za ai komai babu ni. Nan dai ya dinga saka mun san abun a raina yana mun huɗubar banza har kalamansa suka yi tasiri a kaina, sheɗan ya dinga zuga ni tare da ƙawata mun daɗin mulki da cigaban rayuwa da zan samu in har na haye kujerar mulkin shugabancin ƙasar nan. Ni har ga Allah na bi Kabir da niyyar zai kai ni wurin wani malamin, irin malaman soron nan ko masu duba, amma ko kaɗan boka da masu tsibbu ba su zo raina a matsayin wanda Kabir zai kai ni gurin su ba. Amma me? Mun yi tafiya ta kai ta awa uku kafin mu tsaya a wani tangamemen gida dake can wajen gari, babu gida gabansa babu gida bayansa, shi kaɗai a gurin. Muna zuwa ƙofar gidan na ji gabana ya faɗi, na dubi Kabir da ya gaji da mitata da nake ta yi masa tunda na ga muna ta tafiya ta ƙi ƙarewa na ce masa. "Ina ka kawo ni Kabir?" Ba tare da ya kalle ni ba ya ce. "Inda na ce zan kawo ka mana." Daga haka ya buɗe Motar ya fita, nima ban da zaɓi sai bin bayan nasa.














Ya k'wank'wasa ƙofar gate ɗin gidan, mintuna kaɗan wani ɗan tsoho ya zo ya buɗe mana, suka yi maganar da ni ban ji me suke cewa ba sannan Kabir ya shige gidan. Na tsaya na ƙi shiga saboda yanda gabana yake ta faɗuwa sosai, sai hasbunallahu'wani'imal'wakil nake maimaita a cikin raina. Kabir ya juyo ganin ban bi shi ba ya ce in shigo mana. Na ƙara tambayar sa Kabir wai inane nan ka kawo Ni? Ni fa hankalina ya ƙi kwanciya da gurin nan, gaskiya gida zan koma. Ya ce, ka zo mu je ka gani mana, haba ka cika garaje matsalata da kai, mu ci wannan uwar tafiyar sannan ta tashi a banza, wannan abun da taimakon ka zan yi ba kaina zan yiwa ba. Na yi tsaki sannan na bi bayan shi. Wani dogon lungu ne a cikin gidan, nan muka bi mu kaita tafiya sannan na ga mun shiga wani ƙaton Parlour, wanda babu komai a cikin sa sai wasu irin abubuwa marasa kyan gani a rarrataye, na shiga bin Parlour'n da kallo tsigar jikina na tashi. Kabir ya buɗe wata ƙofa dake falon ya shiga tare da yi mun alamar in biyo bayan shi. Ban musa ba na bi shi na shiga nima, abun da na tarar a ɗakin ba ƙaramin daga mun hankali ya yi ba ya kuma girgiza tunanina, har na yi tunanin ko mafarki nake. Wata mace hakimce akan kujera ta mulki tsirara haihuwar uwarta, kanta babu gashi a aske yake tal kamar Namiji. Ta ɗaura wani jan k'yalle a hannunta da ƙafarta. Sai zazzare idanu take yi. Gabanta kuma wani tulu ne na zinare wasu k'artan maza guda biyu suma ba kayan kirki a jikinsu suna tsiyayo mata wani jan abu mai kauri a cup tana ƙarba ta sha. A fili na ce A'uzubill...... Amma kafin na ƙarasa na ji an buge mun bakina, na juya dan ganin waye amma ban ga kowa ba. Kabir ya tsugunna yay sujjada ga matar nan wanda hakan ya ƙara tayar mun da hankali. Na sunkuya na d'ago shi cikin fusata na sharara masa mari na ce. Kabir gurin matsafa masu shan jini ka kawo ni gurin mushirikai? To rashin imanina bai kai haka ba, neman duniya ta ba zai saka in ɓata har haka ba. Na juya na fice daga ɗakin cikin tsananin fusata da baƙin ciki ina Allah wadaran halin Kabir. Tafiya nake kamar zan tashi sama ina haɗa hanya har na kai bakin gate ɗin gidan, na dubi mai gadin gidan a fusace na ce masa ya buɗen ƙofa. Amma kafin ya yi wani yunƙiri sai gani na na yi a ɗakin dana bar Kabir da wannan matar yanda na bar su. Na shiga rarraba ido cikin tsananin al'ajabi ina bin ɗakin da kallo tare da tunanin da yanda aka yi na iya dawowa ɗakin cikin kiftawar ido ni da nake a bakin gate. Na bi su da kallo kamar yadda suka tsaya cak suna kallo na su ma, na buɗe baki da niyyar magana ko addu'a amma na ji na kasa. Sai na juya da sauri na ƙara ficewa daga ɗakin, wannan karon da gudu na ƙarasa gate ɗin gidan. Amma nan ma kafin kiftawar ido na ƙara ganin an mayar da ni wannan ɗakin. Sai da muka yi haka har sau uku, ni na ƙi haqura in tsaya a ɗakin kamar yadda suke so, su kuma sun ƙi bari na in fita daga gidan, sai na kai bakin gate sannan su ƙara dawo da ni cikin ɗakin. A na ukun ne matar nan ta shek'e da wata mahaukaciyar dariya tana duba na, ni kuma inata aikin zazzare idanu da numfarfashi. Sai da ta yi dariyarta mai isarta ta gama sannan ta murtuke fuska kamar an aiko mata da saqon mutuwa ta fara magana cikin amon murya da faɗin.........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*7️⃣0️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
















......."Barka da zuwa Muhammad Tafida, ƙungiya na farin ciki da kasancewar ka a cikinta. A kodayaushe muna san irinku masu tsantsar riƙo da addini a cikin mu, domin mu mun fi son mu ɓata shiryayyu su koma ɓatattu, wannan shine burinmu akodayaushe." Sannan ta dubi Kabir ta ce masa. "Aikinka yana kyau mai jan kai bawan mai jan kai, a yau za'a ƙara maka matsayi a cikin wannan ƙungiya, sakamakon kawo mana wannan babban mutum cikinta da ka yi. Markus da Jamus suna alfahari da kai." Na dubi Kabir na dube ta ba tare da na gane inda maganganunta suka dosa ba. Ina son na yi magana amma na kasa koda motsa labbana ne balle na iya sarrafa harshena. Na yi ƙoƙarin juyawa na fice daga ɗakin kamar yadda na yiyyi d'azu amma na kasa, daga nan ma ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai farkawa na yi na ganni kwance akan wani irin gado ɗan ƙarami, babu komai a jikina sai jan k'yalle ɗaure a hannuna da kaina da ƙafata. Na yunƙura na tashi sai na ga mutane mata da maza kusan hamsin zagaye da gadon da nake, dukkanin su tsirara haihuwar uwarsu sai ɗan jan k'yallen nan kamar na jikina. Suna watsa mun wani jan abu ajikina wanda na fahimci jini ne, suna kuma yin wani abu da bakinsu kamar wak'a amma da wani irin yare irin nasu na matsafa. Na gaza yin komai sai bin su da ido, Kabir kawai na gane a cikinsu sai wannan ƙatuwar matar dake facing ɗina tana mun wani irin kallo. Sun daɗe suna yin abubuwan su akaina, su shaƙa mun hayak'in wannan, su fesa mun wancan su watsa mun wannan, haka dai sukay ta yi. Sai na ji gaba-ɗaya jikina kamar ba nawa ba, kamar an canza ni, na ji zuciyata da ƙwaƙwalwata kamar ba su taɓa sanin abu a cikin duniyar nan ba sai waɗannan mutanen. A tak'aice dai a ranar na zamto member na wannan ƙungiyar ba dan son raina ba sai sanadiyyar la'anannen abokina, kuma duk abun da suka saka ni in yi bana musu nake yi. Ni ban sani ba ashe har mun kwana a gidan, wannan farkawar da na yi ma tsakar dare ne. Sai washegari da hantsi sannan aka bani kayana na saka muka baro gidan ni da kabir, bayan Sarauniya kamar yadda na ji suna kiran wannan ƙatuwar matar ta kafa mun sharad'an zuwa kullum wannan gidan ana aikin ƙungiya tare da ni. Ta tabbatar mun babu abun da zan nema a duniyar nan in rasa komai girman buƙata_ta da burina zan samu, sannan kuma dole duk aikin da ƙungiya ta saka ni in yi shi komai wahalarsa, kuɗi kuwa idan suna bautawa mutum sai sun bauta mun a duniyar nan saboda yawan kuɗin da zan yi. Ta kuma raɗa mun suna jaririntah, sauran ƴan ƙungiya kuma suna kira na autan ƙungiya. Jikina kamar ba nawa ba muka taho gida ni da Kabir dake ta murmushin farinciki da jin daɗi. Ni dai kawai kallon sa nake ina jin kaina ya mun wani irin nauyi kamar duka mutanen duniyar a kaina suke. Sai da muka shigo cikin gari sannan na fara dawowa nutsuwata, hankalina ya fara dawowa jikina. A fili na ce. "Shikenan na zama matsafi ɗan shan jini kenan?" Na yi tambayar cikin tsananin mamaki da al'ajabi. Kabir ya tuntsure da dariya ya ce. "Harkar akwai samu na gidana, zaka yi bala'in kuɗi nake faɗa maka mutumina, na san inna faɗa maka gaskiya tun kafin mu zo baza ka taɓa amincewa ka biyo ba, shi yasa kawai na kawo ka. Na daɗe ina son saka a cikin wannan harkar dan na san ƙungiya tana buƙatar irinku masu tsoron Allah." Ban san lokacin da nay masa wata muguwar shak'a ba, ya yi saurin taka burki. Ina huci na ce masa, "ka cuce ni Kabir ka cuci rayuwata, yanzu mai zan ce da Ubangiji na da kuma iyalina akan wannan mummunar harkar daka saka ni a cikin ta? Mene ribarka na mun hakan Kabir? Wanne laifi nay maka a rayuwar nan ka zaɓi sanya ni cikin wannan mummunar harkar? Wacce irin tsana kai mun har haka? Dan wannan ba k'auna ba ce." Ya k'wace jikinsa dak'yar daga shaƙar da nay masa yana mayar da numfashi ya ce. "Aikin gama ya riga ya gama, duk wani hargagi da zakai baza ka taɓa fita daga cikin ƙungiyar nan ba har abada, ƙungiya ce da in aka shiga ba'a fita, sai dai in mutuwa ka yi." A hasale na ce masa ƙarya yake, kuma zai sha mamakina, ni da ƙara zuwa wannan gidan har abada. Anan muka rabu da Kabir baram_baram ya fice ya bar mun Motata ina girmama rashin imani da son duniya irin na Kabir, ko kaɗan ban taɓa sanin yana wannan harkar ba, dan ban yi zaton son duniyar tasa har ya kai haka ba. Bayan na koma gida na tarar da Fateemah duk ta tayar da hankalinta akan rashin dawowata gida jiya. Tana gani na ta saka kuka ta ce. Indai har ina son zama da ita daga ranar in bar siyasa, ta gaji da wannan bala'in yawa_yawan, ga wani mummunan mafarki da ta yi a daren jiya a kaina. Na tabbatar mata daga ranar na bar siyasa har abada, dama ko bata faɗa ba na yi niyyar dainawa saboda a sanadinta na faɗa wannan mummunar harka. Saboda tana cikin murnar gani na bata lura da canjin yanayin da nake ciki ba. Amma tay ta tambaya ta inda na je na kwana, na sanar mata wani ƙauye muka je campaign motarmu ta lalace mana a hanya. Tay ta mun wani irin kallo kamar bata yarda da abun da na ce mata. First maganar data fara fitowa daga bakinta a lokacin in rabu da Kabir Ginyau domin ba mutumin arzik'i ba ne, bata son alaƙa ta da shi, dan ta san duk inda na je tare muka je da shi. Na ce mata Insha Allahu na rabu da shi kenan. Daren ranar ban iya runtsawa ba saboda tsananin damuwa, na yi dana sanin, sanin Kabir a rayuwata babu adadi. Na yi kuka, na yi kaico da rayuwata, na tsani kaina, na dinga addu'ar Ubangiji ya ɗauki raina a daren in huta, da dai in cigaba da rayuwa a matsayin ɗan shan jini. Washegari safiya tana yi na ji hankalina gaba-d'aya ya yi gurin matsafan nan, na ji kamar zan mutu idan ban je gurinsu ba. Lokacin ina aiki ban yi retired ba, na shirya da zummar zuwa gurin aiki na fita, ina fita na kira Kabir na ce ya zo ya kai ni gidan jiya dan ba zan iya gane hanya ba. Kabir ya zo ya dinga mun dariya yana faɗin dama ya ce ba zan taɓa iya fita ba daga ƙungiya ba da kaina zan koma, to sun riga sun gama tsaface ni na zama na su. Tun daga wannan rana idan ban je gidan nan ba yau to gobe zan je. Amma ko sau ɗaya ban taɓa kwana a can ba, duk da kowanne member akwai ranar kwanansa a gidan, dan an fi yin aiki cikin tsakiyar dare. Ni kaɗai ne bana kwana saboda ban san me zan faɗawa Fateemah ba idan na je na kwanan, ina zan ce mata ina zuwa? Sarauniyar ƙungiya tana matuƙar sona a cewarta, hakan yasa ko da an ce a yi abu na ƙi yi bata iya hukunta ni, saɓanin sauran members da babu wanda yake iya yi mata musu. Ni kuma ina sane nake ƙin yi wani abun idan ta umarce ni, saboda ta yi zuciya ta kashe ni. Dan wallahi ina cikin ƙungiyar ne kawai amma bana so, ni kaɗai na san baƙin cikin da nake ciki a sanadiyyar kasancewa ta a cikin wannan ƙungiya, kodayaushe cikin yiwa Kabir Allah ya isa nake, tunda shi ya jefani a cikin wannan iftila'in, kuma har abada ba zan yafe masa ba. Babu abun da ake aikatawa a cikin wannan ƙungiyar face zallar rashin imani da shirka da tsantsar tsafi. Zaku sha mamaki idan kuka ji manya da wasu daga cikin masu mulki a ƙasar nan wanda ake musu kallon mutanen kirki amma suna cikin wannan ƙungiya. Lokaci ɗaya na sauya daga aihin Muhammad Tafida na, na koma wani daban, na watsar da duk abokaina saboda tsoron kar su gano mummunar hanyar dana faɗa, ƴan ƙungiyar nan su suka zama aminaina da su kaɗai nake hulɗa. Dole ne ko kuma in ce sharad'i ne na wannan ƙungiya, duk wanda yake cikinta sai ya yi tarayya da ƴarsa ta cikinsa budurwa, idan kuma macece ta yi da ɗanta saurayi wannan tilas ne ga kowa. Amma naga su members ɗin ƙungiyar kamar hakan ba ya damun su, daɗi ma suke ji da murnar hakan, wasu ma ba ƴaƴa ɗaya suke ɓatawa ba, in sun kai goma ƴan'matan da samarin duk sai sun ɓata su, wasu ƴaƴan ma sanadiyyar hakan suke rasa ransu. Iyayen kuma su fi kowa nuna damuwa da zak'ewa akan al'amarin a idon duniya. Wanda ba shi da yar ko ɗan ne kawai ake masa uzuri, amma za'a ba shi wani aikin a madadin wannan ya yi, ko lalata ƙananan yara mata da maza, ko kuma wani babban saɓon ga Ubangiji. Nima hakan ce ta kasance da ni, bani da ƴa mace dan haka aka bani aikin ɓata ƙananan yara mata ta hanyar yi musu fyaɗe. Kai tsaye na ce ba zan iya ba, duk da ina cikin wannan ƙungiya amma imanina bai tafi duka daga cikin zuciyata ba. Manyan ƙungiya suka mun caaa aka da masifar dole sai na yi, ai ba fin su na yi ba da za'a saka ni abu ina ƙin yi, amma Sarauniya ta tsawatar musu ta ce su rabu da ni, ta san ya zata yi da ni. Haka na cigaba da rayuwa cikin takatsantsan da ɓoye abun da nake aikatawa, dan babu wata alama da zata nuna maka ina wannan mummunar harkar idan ka gan ni, ba ma ni kaɗai ba, duka yan ƙungiyar idan suka fito cikin gari haka ne, ko iyalanmu ba su isa sun gane ba.










Na karb'i riƙon Neehal a lokacin da Fateemah ta zo mun da shi gidana saboda Allah ba dan wani abu ba, kuma Allah ne shaidata akan hakan. Tun kafin nan dama ta saba zuwa mana hutu tun iyayenta suna da rai, haka kawai na ji ina son yarinyar tamkar ƴar cikina dana haifa haka nake kallon ta. Da zuciya ɗaya nake riqonta kuma nake yi mata komai. Watarana lokacin Neehal ta kusa shekara da dawowa hannunmu gaba-d'aya da zama Kabir ya zo gidana. Ban shigar da shi ciki ba saboda bana son Fateemah ta san muna tare sai muka zaune a farfajiyar gidan. Muna zaune sai ga Neehal an dauko ta daga makaranta ta dawo, tana hango ni ta taho da gudu ta rungume ni kamar yadda ta saba, nay mata Welcome sannan ta gaishe da Kabir ta wuce cikin gida. Kabir ya bita da kallo sannan ya dube ni ya ce wannan yarinyar fa? Na haɗe rai dan na san halinsa da maitar mace komai ƙanƙantarta nay masa bayanin yanda take a gurina. Ya jinjina kai bai ce komai ba, ashe shi ya k'udurce abun a ransa, washegari muna zuwa ƙungiya ya ce ai ina da 'ya mace budurwa ƙarya nake

Please Login or Register in order to submit comment