Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saka da Alkhairi." Ba ta jira amsar sa ba ta buɗe Motar ta fice ta fara tafiya. Sadik ya bita da kallo wani abu na yawo a cikin zuciyarsa game da ita, Haneefah ma fita ta yi tare da yi masa sallama. Mai da dubansa ya yi gareta ya ce "Sai yaushe kuma?" Haneefah ta ce "Sai ransa Allah ya kuma haɗa mu." Complimentary card ɗinsa ya mik'a mata, Haneefah ta karb'a ta ce "Bye bye, Insha Allahu zan kiraka."






A falo Neehal ta tarar da Mama zaune ta na kallo, Neehal ta ƙarasa kusa da ita ta zauna a gefen ta, Mama ta juyo ta kalle ta ta ce "Sai yanzu?" Neehal ta ce "Ki yi hak'uri Mama akasi a ka samu." Mama ta ce "Da Ameen ya na nan sai ki faɗa masa akasi a ka samu, kin san ba ya nan shi ya sa ki ka yi daren ai." Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba, "Ina Haneefan Kuma?" Mama ta tambayeta ta na maida duban ta ga TV. Kafin Neehal ta ba ta amsa Haneefah ta shigo falon bakin ta ɗauke da sallama, suka amsa mata a tare. "Ina ki ka tsaya kuma?" Cewar Mama ta na kallonta. Haneefah ta yi wani munafukin murmushi ta na kallon Neehal. Neehal ta ɗauke kanta daga kallonta ta na ɓata rai. Mama ta tab'e baki ta maida hankalinta ga kallon da take. Haneefah ta ƙaraso ta zauna a saman carpet ta ce "Mama mun dawo, duk su na gaishe ku." Mama ta ce "Muna amsawa, ya kuka baro su?" Haneefah ta ce "Lafiya k'alau." Neehal ta tashi ta haye sama, Haneefah ta bi bayanta. Ta na ajiye card d'in da Sadik ya bata a kan mudubi ta ce "Ga card nan ya bani, ashe ma Barrister ne." Neehal ta tab'e baki ta ce "Sai ki nemi ma'ajiya ki killace shi ai, daga ganin mutum ba ki san shi ba, sai uban surutu ki ke zuba masa." Haneefah ta ce "Kin manta ne, I'm Jornalist fa." Neehal ta ce "Ke dai ki ka sani."












************************








Rayuwa na ta tafiya kwanaki na ta wucewa, cikin ikon Allah har an yi sadakar arba'in Anwar, su Neehal har wannan lokacin cikin hutu suke ba su koma school ba. Sosai Haneefah suke zumunci ita da Sadik, tamkar 'Yan'uwan juna tun da, dan Mama da Mommy'n Haneefah duk san Sadik a bakin Haneefah. Neehal ce dai sama_sama suke gaisawa, shima sai dai idan suna tare ya kira Haneefah sai ta bata su gaisa. Dad sun je sun samu Mahaifin Hafsat sun yi magana, sai dai har yanzu Hameedah da mahaifiyarta da sauran Family ba su da labarin Ameen ba Hameedah zai aura, kuma ƙarshen watan nan Insha Allahu za'a kai kuɗi gidansu Hafsat ɗin. Haneefah ta na kitchen ta na dafa Indomie da daddare ta ji Mommy dake zaune a falo ta na k'wala mata kira. Haneefah ta amsa tare da faɗin "Ina zuwa Mommy." Sai da ta kammala ta juyo Indomie'n a plate sannan ta fito. Ta na ajiye Indomie'n a kan Centre table ta ce "Ga ni Mommy." Mommy ta ce "Wayar ki a ke ta kira." Haneefah ta ƙarasa inda ta ajiye wayar ta ɗauka ta duba missed call d'in, Saurayinta ne wanda za ta aura ya mata 1 missed call sai kuma Sadik da ya mata 2 missed call, kiran Saurayinta ta fara bi amma bai d'aga ba, bayan ta katse ta kira Sadik. Ringing biyu ya yi rejected ya kira ta. Haneefah ta d'aga tare da yin sallama, ya amsa mata ya ƙara da faɗin. "K'anwata Ya kike? Ya Mommy?" Haneefah ta ce "Ina lafiya Yayanah, Mommy ma haka, kai fa?" Sadik ya ce "Lafiya k'alau nake, am Haneefah dama ina so mu yi wata magana dake yanzu idan babu damuwa." Haneefah ta ce "Alright, to bari na ci abinci minti goma i will call you back." Sadik ya ce "Ok sai kin gama." Bayan ta gama ci ta koma d'akinta sannan ta kira sa, rejecting ya ƙara yi sannan ya kira ta. Bayan ta d'aga ya ce"Haneefah, Magana za mu yi a kan k'awarki Neehal." Haneefah ta yi ɗan murmushi domin tun kafin yau ta gano nufin Sadik a game da Neehal. Ta ce "Ina jin ka Ya Sadik." Sadik ya ɗan numfasa ya ce "Haneefah, tun kafin nu haɗu da ku na san ku a Television, kasancewar ni ma'abocin kallon labaranku ne, Sosai ku ke burgeni saboda yanda ku ke yin komai na ku cikin nutsuwa, ga shiga ta mutunci da kamala wanda yake nuna kun fito daga gidan tarbiyya. Ranar da na ganku a unguwarmu ji na yi tamkar mafarki nake dan farin ciki, hakan ya sa na kasa hak'uri har sai da na tsaya na muku magana, kuma wannan ita ce rana ta farko da na taɓa tsaida mace na mata magana." Ya ɗan numfasa sannan ya cigaba da magana. "Haneefah maganar gaskiya, zuciyata ta kamu da matsanancin son k'awarki, amma ban san me ya sa nake tsoron tunkarar ta da maganar ba............✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:33] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_










*1️⃣2️⃣*












...........Ya ƙara yin shiru a karo biyu sannan ya cigaba da magana kamar haka. "Abun da ya sa nake tsoron tunkarar Neehal da maganar saboda ina tunanin kamar ba za ta amince ta karb'i tayin soyayyata ba." Haneefah ta ce "Ya Sadik na ji batun da ka zo mun dashi, kuma na ji dad'i sosai, amma maganar gaskiya tunkarar Neehal da maganar soyayya a yanzu abu ne mai matuƙar wahala, domin har yanzu ba ta warware daga rasuwar tsohon saurayinta Anwar ba." Sadik ya ce "Allah sarki, ai dole dama sai a hankali za ta warware daga rad'ad'in mutuwar ta sa, Allah ya ji k'an sa ya gafarta masa." Haneefah ta ce "Amin, amma kar ka damu Ya Sadik ka bar komai a hannuna zan san ta yadda ta ɓullo mata." Ta yaya kenan?" Anwar ya tambaye ta. Haneefah ta ce "Ka bani nan da wani lokaci, na san me zan yi." Sadik ya ce "Shikenan Na gode, sai na jiki." Daga haka suka yi sallama. Haneefah ta yi shiru kawai ta na tunanin ta yanda za'a yi Neehal ta amince da soyayyar Sadiƙ. Ta dad'e ta na tunanin abun kafin ta mik'e ta koma falo. Mommy har yanzu ta na zaune a falon, Haneefah ta zauna a kusa da ita ta ce "Mommy kin san me?" "Sai kin faɗa." Cewar Mommy da ta juyo ta na kallonta. Haneefah ta ce "Ya Sadik ne ya ce min wai ya na son Neehal." Mommy ta faɗaɗa fara'a a fuskarta ta ce "Kai Masha Allah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi." Neehal ta ce "Amin, amma fa Mommy akwai matsala."


"Matsala kuma tame Haneefah?"


"Mommy Neehal mana, na san ba za ta taɓa amincewa da soyayyar Ya Sadik, saboda kwanaki mun yi magana da ita, ta ce mun ita ba za ta ƙara kula wani ɗa Namiji da sunan soyayya ba, Tun da Anwar ya rasu." Mommy ta ce "Zancen banza, to haka za ta yi ta zama ba ta yi aure ba ko kuma me take nufi? Mace ma take yin Aure mijinta ya rasu kuma ta sake wani auran su zauna lafiya, balle ita da yake Saurayinta, yarinta ce kawai ke damunta." Haneefah ta ce "To ai ita Mommy dan ta ga ankashe Jameel da Anwar wai karta ƙara yin soyayya da wani shima a kashe shi." Mommy ta ce "Wannan duk ba hujja ba ce, mutuwa da rayuwa duk na Allah ne, su ma da suka mutun kwanan su ne ya ƙare, Allah dai ya ji k'an su, ita kuma Allah ya fito mata da miji na gari ta yi auranta." Haneefah ta ce "Amin."








Washegari da yamma Neehal ta zo gidansu Haneefah suna zaune a d'akin Haneefah Neehal ta dubi Haneefah ta ce "Besty ban baki labari ba." Haneefah ta ce "Labarin me?" Neehal ta ce "Yayanah ya kusa aure." Haneefah ta waro ido waje ta ce "Wow, nice story, ki ce su Aunty Hamida an kusa shiga daga ciki.?" Neehal ta ce "Hmmm, na yi farin ciki sosai da Yaya zai yi aure, sai dai kuma harna fara kewar shi." Haneefah ta ce "Iskancin banza, abun da ba kullum ki ke ganin sa ba." Neehal ta ce "Duk da haka, amma i will miss him over." Haneefah ta ce "Sai ki bishi gidan nashi, dama ba kwa shiri da Aunty Hamida sai ku yi ta fafatawa." Neehal ta ce "Ke ba fa ita zai aura ba." "Kamarya. Haneefah ta tambaya cikin mamaki. "Kamar yadda Allah ya yi, wata tsohuwar budurwarsa zai aura, Hafsat." Neehal ta bata amsa da faɗin haka. Haneefah ta jinjina kai ta ce "Allah sarki Aunty Hamida ta bani tausayi wlh, yanda take son Yaya ban taɓa tunanin ba ita zai aura ba." Neehal ta ce "Nima haka Besty, na yi mamaki, Mama ma duk ta damu." Haneefah ta ce "Allah ya sanya Alkhairi ya kai mu da rai da lafiya mu sha shagali." Neehal ta ce "Amin dai." Haneefah ta numfasa ta ce "Dama a haɗa a muku auren tare da Yaya." Neehal ta mata wani kallo ta ce "Sai dai a haɗa dake, dama na ji Mama ta na cewa Month d'in bikin da za a sa kamar ɗaya da naki." Haneefah ta ce "Sai a haɗa mu duka a mana tare." Neehal ta tab'e baki ta ce "Ke nifa na cire wani zancen aure a tsarina, karatuna kawai zan yi ta yi." Haneefah ta ce "Zance ma ki ke, idan ke kin yarda kin zauna ai Mama ba za ta yarda ki zaunar mata ba aure ba." Neehal ta ce "To za ta mun aure ba miji ne? Ina dai sai na kawo mata mijin?" Haneefah ta ce "Ai miji ba zai miki wahalar samu ba, duk tarin masoyan da ki ke da su." Neehal ta ce "Kan ki ake ji, ni dai na riga na hak'ura da wata maganar soyayya a rayuwata balle kuma har na kai ga aure." Haneefah ganin yanda Neehal take magana bil hak'k'i, ya sa ta saki baki kawai ta na kallon ikon Allah, amma ta mata uzuri, domin ta san har yanzu Anwar ya na nan a cikin ranta, shi ya sa take ganin kamar ba za ta iya ƙara tarayya da wani ɗa Namijin ba.....










*********** *ABUJA* ***********




Mommy'n Hameedah ce tsaye a falonta ta na zarya cikin tsananin ɓacin rai da damuwa. K'awarta mai suna Haj. Saratu dake zaune a falon ta dube ta da mamaki ta ce "Wai Suwaiba lafiya kuwa, na ga kin fito daga d'aki kin hau zarga kamar wata me fareti?" Mommy ta ja wani dogon numfashi ta sauke cikin tsantsar ɓacin rai ta ce "Ina fa Lafiya Saratu, waccan munafukar matar 'yar abu ta kazar uba ta shirya makircin da ta saba." Haj. Saratu ta ce "Wake nan.? Mommy ta ƙaraso kujerar da Haj. Saratu take ta zauna a gefenta, cikin ɗacin rai ta fara magana. "Yanzu nan Yaya Gen. ya kira ni, ya ce mun za mu yi wata magana, na tattara hankalina duka na bashi dan na ɗauka wata maganar arzik'in ce, buɗar bakinsa sai ce mun yayi. Suwaiba! Magana za mu yi a kan yaran nan Ameen da Hameedah. Na gyara zama cikin jin daɗi na ɗauka zai ce mun za a yi maganar bikin su ne, amma sai na tsinkayi muryarsa da faɗin akasin haka, wai ya kira Ameen ya masa maganar Aure ya ce ya fitar da mata, shine Ameen ɗin ya ce ba ya son Hameedan wata yake so, yanzu maganar da yake mun har sun je gidan su yarinyar an yi magana, next week za su kai kuɗi a yi Engagement ɗinsu haɗe da sa rana." Wani uban ashar Hajiya saratu ta narka ta ƙara da faɗin "Eh, lallai kam dole ki ce makira ta yi markici, dan wannan ko tantama ba na yi shirin wannan Matar tasa ne, me ji da kanta kamar tafi kowa." Mommy ta ce "Ai dama ni na san za a rina, domin matar nan ba ta k'auna ta da ni da ƴaƴana, amma wlh wannan karon ba ta isa ba, zan nuna mata asalina za ta san ko wacece Suwaiba, shima Yayan dan takaici kashe wayata na yi, ya tsaya ya na mun wata nasiha wai matar mutum kabarinsa, komai na Allah ne, Ni ko gama saurararsa ma ban yi ba." Haj. Saratu ta ce "To yanzu mene abin yi?" Mommy ta ce "Ni na san me zan yi, dan idan kinga ba a yi auran Ameen da Hameedah ba to wlh sai dai in ba na numfashi. Amma kafin na yi abin da zan yi bari na fara kiran ita makirar na ci mata mutunci." Mommy ta ƙarashe Zance tare da mik'ewa ta shiga d'akinta ta ɗauko wayarta, jikinta har tsuma yake ta nemo number'n Mama ta danna mata kira. Mama ta na asibiti ta na ƙoƙarin tafiya gida ma tunda yamma ta yi kiran Mommy ya shigo wayarta. Ba tare da tunanin komai ba ta ɗauka, dan ita ba ta masan Dad ya kira Mommy'n ya mata maganar ba.






"To makira, munafuka Algunguma, wato kin yi halin naki da ki ka saba kin hana ɗanki Auren 'yata, dan nasan Ameen haka kawai ba zai ce ba ya son Hameedan ba, wa ya sani ma ko hadda siddabarunku na Fulani ki ka haɗa masa saboda ya ƙi amincewa." Kalaman da Mama ta ji kenan lokacin da ta kai wayar kunnenta, wani ɗan guntun murmushi ta yi, cikin maganarta mai cike da aji da nutsuwa ta ce "Na isa ne ai Suwaiba na hana Ameen abu kuma ya hanu, dan haka ki yi duk abin da za ki yi a kan hakan." Kamar mahaukaciya Mommy ta ce "Wlh kuwa za ki ga abun da zan yi, za ki san da ni Suwaiba ki ke maganar." Ta ƙarashe zancen ta na bubbuga k'irjinta. Mama ta yi tsaki ta na ƙoƙarin cire wayar daga kunnenta ta ji Mommy na faɗin. "Kuma nasan duk saboda me ki kai haka, dan tun ba yau ba na fuskanci wannan figaggiyar yarinyar da danginta suka kasa riƙe ta ki ke son bawa Ameen." Mama harda za ta bata amsa sai kuma ta kashe wayarta, domin ba ta da time ɗin Mommy'n. Mommy kuwa jin Mama ta katse wayar hakan ya ƙara k'ular da ita, ta yi ta masifa da d'uran_d'uran ashariya kamar sabuwar kamu. Haj. Saratu na ƙara zugata.






Daf da Magriba Hameedah ta dawo gidan daga gurin aiki a matuƙar gajiye kamar wadda ta yi aikin ƙarfi. Jakarta da mayafinta ta cillar a kan kujera sannan ta zauna tare da faɗin "Wash, Mommy na gaji." A dak'ile Mommy ta ce "Sannu" Hameedah ta kalli mahaifiyarta ta, yanayin da ta mata magana ta gane ba k'alau ba, da mamaki ta ce "Mommy what happened na ga kamar ranki a ɓace?" Mommy ta ce "Akwai matsala ne Daughter babba ma kuwa." A ɗan firgice Hameedah ta ce "Me ya faru Mommy? Har kin sa hankali na ya fara tashi." Mommy ta ce "Hmmm, bari kawai Hameedah, ni da waccan matar ne Fateema matar Yaya......." Labarin duk abun da ya faru Mommy ta faɗawa Hameedah. Wani irin ihu Hameedah ta yi tare da mik'ewa tsaye cikin tashin hankali ta ce. "Wallahi Momy ba zai yiyu ba, shekara nawa ina zaman jiran shi sai yanzu a ce ba ni ze Aura ba." Ta ƙarashe zancen tare da fashewa da kuka. Mommy ta taso ta zo kusa Hameedah, dafa kafadunta ta yi cikin lallami ta ce "Share hawayenki Daughter, indai Ina raye babu abun da zai hana auranki da Ameen, ki kwantar da hankalinki." Cikin kuka Hameedah ta ce "Mommy Dan Allah ki san abun yi, wlh ba zan iya rayuwa babu Ya Ameen" Mommy ta zaunar da ita a kan kujera ta ce "Ki kwantar da hankali kamar tsumma a cikin ruwa, ki sa a ranki ma auranku da Ameen tamkar an yi angama."








*******************








Neehal ta na kitchen ta na girkin dare Mama ta dawo gidan, ta fito daga kitchen d'in ta yi hugging d'inta ta na faɗin "Welcome sweet Mom." Mama ta yi murmushi ta ce "Thanks You Daughter, ya gida?" Neehal ta ce "Alhamdulillah, sai gajiyar aiki." Ta ƙarashe maganar a ɗan shagwab'e. Mama ta ce "Sannu, me ake girka mana ne, na ji k'amshi duk ya baɗaɗe ko'ina?" Neehal ta murmusa ta ce "Sai kin zo ci za ki gani." Mama ta yi murmushi ta wuce sama jin a na kiran sallar Magriba.........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:33] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*












_By_
_Zeey Kumurya_














*1️⃣3️⃣*












..........Neehal ta koma kitchen ta cigaba da aikinta. Bayan Sallar Magriba Mama ta na zaune a ɗakinta a kan darduma ta na lazimi wayarta ta yi ƙara, ɗauka ta yi ta duba ta ga Mommy'n Hameedah ce ke kuma kiranta. Tsaki ta yi cikin takaici ta maida wayar ta ajiye, dama ta san Mommy'n Hameedah za ta yi abun da yafi haka ma indai ta ji maganar Ameen ba zai auri Hameedah ba. Kiran Mama Mommy ta yi_ta yi, amma Maman ta ƙi d'agawa. Hakan ba ƙaramin ƙara tunzura Mommy ya yi ba, ta yi ta masifa ta na kiraye_kirayen 'yan'uwa ta na faɗa musu abun da ke faruwa. Hameedah kuwa kiran layin Ameen tayi_tayi amma shima be d'agawa ba, hakan ya ƙara ta da mata da hankali ta zauna tayi ta rufzar kuka.






Mama ce zaune a falon Dad dake shan fruits, Dad ya na duban ta da murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce "Kamar da magana a bakin nan naki Doctor." Mama ta ce "Babu maganar komai Hubby, Idan ma da akwai ba ta wuce ta zancen bikin Ameen ba, yaushe za ku kai kuɗin ne.?" Dad ya ce "Ranar Sunday Insha Allah." Mama ta ce "Allah ya kaimu." Dad ya ce "Amin, ina Daughter ne?" Mama ta ce "Tana can ta na hutawa wai yau a gajiye take." Dad ya ce "Bari na kirata a waya na yi missed ɗinta yau.'' Neehal ta na kwance a kan luntsumemen gadonta ta yi nisa a cikin tunanin rayuwarta, wayarta dake gefenta ta fara vibrate, ajiyar zuciya ta sauke me ƙarfi tare da share hawayen da yake zirarowa daga idanunta, tashi zaune ta yi ta na cize lips d'inta zuciyarta na mata zafi. Duba wayar ta yi ta ga Dad ke kiranta, cikin sanyin jiki ta d'aga wayar tare da karawa a kunnanta. Dad ya ce "Daughter bacci ki ke ne?" Neehal ta ce "A'a, ina kwance dai." Dad ya ce "Yau tun safe ban gan ki ba, na dawo kuma na jiki shiru, ko yau ba za ki zo mu yi hirar ba ne." Neehal ta yi murmushi cikin daɗi da kuma k'aunar Dad d'in nata ta ce "Zan zo My Dad, gani nan." Dad ya ce "Yawwa d'iyar albarka sai kin ƙaraso." Neehal ta ajiye wayar bayan ya kashe kiran ta na sauke ajiyar zuciya, sosai take kewar Anwar a cikin zuciyarta, musamman idan ta kaɗaice ita kaɗai babu abun da take sai tay ta tunanin sa, addu'a ta masa ta samun dacewa sannan ta mik'e jiki a sanyaye ta fice ta nufi part d'in Dad. Da sallama ta shiga falon, Mama ta kalle ta tare da amsa mata, kusa da Dad ta je ta zauna ta na faɗin. "Abbunah barka da dare." Dad ya shafi kuncinta ya ce "Yawwa Daughter, Mamanki ta ce kin gaji yau ni kuma na taso ki ko?" Neehal ta ce "A'a Dad ba komai ai na huta." Dad ya ce "To ya aikin na ku? Dafatan dai babu wata matsala.? Neehal ta ce "Babu Dad." Dad ya ce "Masha Allah." Neehal ta Kalli Mama ta ce "Mama ina son na je gidansu Ammin Anwar gobe in gaishe ta." Mama ta ce "Allah ya kai mu." Dad ya ce "Ai ko ni yakamata na kai ki da kaina, daga nan sai ki rakani zance, gurin...." Ya ƙarashe zancen da kannewa Neehal ido. Neehal ta yi murmushi ta ce "Gurin wannan kyakkyawar matar mai kirkin nan ta unguwar da muke zuwa?" Dad ya ce "Ehh ita fa, kin san ta iya girki sosai na yi kewar abincinta." Neehal ta yi dariya ta na kallon Mama. Mama ta tab'e baki domin ta saba da zolayar Dad da Neehal, sun maida ita kamar wata kakarsu, idan 'yan nishad'in na kansu haka za su yi ta tsokanarta, idan ta ga dama wani lokacin ta biye musu idan kuma ta so sai ta yi musu shiru. Yau ma biye musu ta yi sukai ta yi, hakan ya rage wa Neehal damuwar da take ciki ba kaɗan ba, dan Dad akwai shi da barkwanci. Sai wajen 10:30 Mama ta raka Neehal ta koma part ɗinsu.




Dad ya na zira kayan bacci bayan fitowarsa daga wanka ya ce "Doctor ban faɗa miki yanda muka yi da Suwaiba ba a kan batun su Ameen." Mama ta ce "Ya ku ka yi." Dad ya ce "Ai ko maganata ba ta gama saurara ba ta kashe wayarta, ina idar da Sallar Magriba kuwa sai ga kiran Yaya na Abuja, na d'aga muka gaisa ya ce mun wai ya ji wata magana a bakin Suwaiba, na ce masa dama ina shirin kiran shi a kan maganar, jibi Insha Allahu zan je har Abujan." Mama ta ce "Allah ya kyauta ya kaɗe fitina." Dad ya ce "Amin." Mama ba ta faɗawa Dad Mommy'n Hameedah ta kira ta ba saboda gudun Fitina, dan tasan halin Dad bai iya ɓacin rai ba, yanzu sai ya kira ta ya ɓata rai. Neehal ta na fitowa daga wanka ta ga a na kiranta a waya, d'agawa ta yi da sauri ganin Yayanta ne. "Hello Yaya!" Neehal ta faɗa bayan ta d'aga. "Sallamar kenan ko?" Shima ya faɗa cikin daddadar muryarshi mai cike da nutsuwa. Neehal ta ce "Sorry duk murnar ka kira ni ce fa Yaya." Ameen ya ce "Ba ki yi bacci ba?" Neehal ta ce "Uhm"


"Me ki ka tsaya yi?"


"Ina part d'in Dad muna hira, yanzu na dawo zan kwanta."


Ameen ya ce,


"Ya yi kyau." Cikin shagwab'a Neehal ta ce "Yaya ina Aunty Hafsat?" Ya ce "Wacece haka?" Neehal ta ce "Aunty Hafsat d'inka fa." Cikin basarwarshi ya ce "Oh tananan k'lu." Neehal ta ce "My regard please." Ya ce "Insha Allah, Bye." Neehal ta ce "Gud night." Daga haka suka yi sallama ya kashe wayar. Neehal ta shirya cikin kayan baccinta masu taushi white color sannan ta rage light d'in ɗakin ta kwanta, hotunan Anwar ta lalubo a wayarta ta shiga kalla, saboda gajiyar dake addabar jikinta ba ta san sanda bacci ya yi awon gaba da ita ba.






Washegari ya kama Talata Neehal ba ta da aiki ranar, bayan sallar la'asar ta fito cikin shirinta na fita. Ɗakin Mama ta je domin yi mata sallama. Mama ta ce "Har kin shirya kuma Haneefan ba ta zo ba." Neehal ta ce "Yaya Faruq ya na gari fa, shi yasa yanzu ganin ta sai an cike Form." Mama ta ce "Shi yasa 2 days na ji ta shiru, yanzu ke kaɗai za ki tafi.?" Neehal ta ce "A'a zan biya na ɗauke ta mu wuce." Mama ta ce "Shikenan amma kar ku yi dare fa, kin ga ke za ki yi driving, ban san ki na hawa manyan titi da daddare." Neehal ta ce "Insha Allah Mama ba za mu jima ba." Mama ta ce "Allah ya kiyaye, kar ki manta da addu'a dai idan za ki fita da kuma hawa Mota." Neehal ta ce "Ba zan manta ba Mama." Mama ta ce "Yawwa, sai kun dawo, ki ɗauki saƙon fa, a gaishe su." Neehal ta amsa da "Toh" tare da ficewa daga d'akin. Sun je gidansu Anwar lafiya, tarb'a sosai Ammi ta musu kamar yadda ta saba. Su na zaune a falo bayan sun gama gaisawa da Ammi Najwa k'anwar Anwar ta shigo falon hannunta ɗauke da tire, ta dire a gaban su Neehal ta na faɗin "Aunty Neehal ku sha ruwa." Neehal ta ce "Toh mun gode." Hira suka shiga yi da su Najma da Ammi, can Haneefah ta dubi Ammi ta ce "Ni ko Ammi ya batun mutanen da suka

Please Login or Register in order to submit comment