Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a 'yan shekarun da ta yi ba ta ganta ba sai ta ga ta ƙara kyau da gayu, ba za ka taɓa cewa ta haifi Ameen ba. Mama ta mik'e ta na faɗin "Bismillah ku ƙarasa dinning ku ci abinci, bari na kira Neehal ta yi sarving ɗinku."




Neehal ta na shiga ɗakinta ta zauna a bakin gado hannunta dafe da kanta, mamaki take sosai a kan abun da Hafsat ta mata, dan ta ji haushi ba kaɗan ba kawai ta danne zuciyarta ne, domin ita mutum ce wadda bata son wulak'anci ko kaɗan kuma ba ta son a yi mata, hakan ya sa itama ba ta yi. Kawar da tunanin Hafsah ta yi daga ranta ta na ƙoƙarin tashi kira ya shigo wayarta, ta daga tare da karawa a kunnenta. Cikin daddad'ar muryarshi ya mata sallama, Neehal ta amsa tare da faɗin "Ina yini Yaya." Ameen ya ce "Lafiya k'alau, su Hafsat sun zo kuwa.?" Neehal ta ce "Ehh." Ya ce "Ok" tare da kashe wayar, ya bar Neehal da mitar faɗin ya kira Hafsan mana ya tambaye ta.




Su Hafsat sun ɗan jima a gidan Mama kafin su tafi, sosai Neehal suka sha hirarsu ita da Fadeelah, dan da ta fito ma ko ƙara kallon inda Hafsat take ba ta yi ba, hakan kuwa ya burge Fadeelah dan ko ba komai Neehal ta nunawa Hafsah tafi ƙarfin raini. Da za su tafi Mama ta basu turaruka da kayan kwalliya. Suna Mota Hafsat ta dinga yi wa Fadeelah masifa a kan wai me yasa ta sakarwa Neehal fuska su ka yi ta hira kamar wata sa'arta salon ta jawo ta rainasu. Fadeelah kallon Hafsat kawai ta tsaya ta na yi cike da mamakinta, kawai daga ganin mutum sai ka ɗauki k'iyayya ka ɗora masa ba tare da wani dalili ba.?"






Bayan Magriba Mama ta na kitchen Dije ta zo ta sanar mata ta yi bak'o, Mama ta ce ta je ta shigo da shi gata nan zuwa. Ta na fitowa falon ta ga ashe Sadik ne. Ta na dubansa ta ce "Sadik ashe kai ne?" Ya ɗan sosa kai kansa na ƙasa ya ce "Ni ne Mama." Mama ta ce "Shine kuma ka tsaya a waje ba za ka shigo ba, sai ka ce wani bak'o.? Sadik ya yi murmushi kawai tare da gaishe da Mama, Mama ta amsa cikin fara'a sannan ta mik'e ta hau sama dan ta kira masa Neehal. Neehal ta na duba abu a system Mama ta shigo d'akin ta ce "Ba ki gama abun da ki ke ba har yanzu?" Neehal ta ce "Ehh, amma na kusa." Mama ta ce "To ki sauko ƙasa kin yi bak'o." Neehal ta d'ago da sauri ta na duban Mama da mamaki ta ce "Mama bak'o kuma?" Mama ta ce "Eh, ya na ƙasa ya na jiran ki." Ba ta jira amsar Neehal ɗin ba ta juya ta fice. Neehal ta mik'e ta na turo baki ta ɗauki Hijabinta ta zira ta sauka ƙasan. Babu kowa sai shi kaɗai ya na latsa wayarsa, Neehal ta ƙaraso cikin falon ta na kallonsa, a hankali ya d'ago kansa suka haɗa ido, gaban Neehal ya yanke ya fadi. Ƙasa ta yi da kanta da sauri bugun zuciyarta na sauyawa, dama tun da ta shigo falon ta ji kamar tasan baƙon k'amshin da ta ji a falon, ashe shine. Zama ta yi a kujerar dake fuskantar sa kanta na ƙasa ta ce "Ina yini." Ba tare da ya ɗauke idonsa daga kanta ba ya ce "Lafiyar k'alau, ya aiki." Neehal ta ce "Alhamdulillah." Shiru suka yi na tsawon mintuna biyu, Sadiƙ ya katse shirun nasu da faɗin "Kun kusa komawa school ko?" Neehal ta ce "Ehh." Ya ce "Yaushe." Cikin k'osawa ta ce "This coming Monday." Sadiƙ ya jinjina kai ya ce "Allah ya taimaka." Suka ƙara yin shiru na wasu mintuna, Sadik ya na lura da Neehal gabad'aya a takure take sai turo baki gaba take. Neehal ganin bashi da niyyar tafiya ta ɗan d'ago kanta ta ce "Gashi kuma ka zo k'anwar taka ba ta nan." Sadik ya yi murmushi ya ce "Ok, you mean Ke ba k'anwata ba ce.?" Neehal ta yi shiru tare da ƙara mai da kanta ƙasa, Sadik ya ƙara yin murmushi ya ce "Shikenan bari in tashi in tafi." Neehal cikin shagwab'arta da ta zame jiki ta ce "Am sorry ba haka nake nufi ba." Ya ce "To ya.?" Ta yi shiru ta na wasa da yatsun hannunta dan ba ta da abun cewa. Mama ce ta sakko ƙasa za ta ɗauki abu, da mamaki a kan fuskarta ta ce "Neehal ya ba a kawo masa ruwa da abinci ba.?" Kafin Neehal ta yi magana ya riga ta da faɗin "Ba komai Mama a k'oshe nake ma." Mama ta ce "No, ba za a yi haka ba, Neehal tashi ki kawo masa abinci." Neehal ta mik'e a hankali ta nufi kitchen, Mama kuma ta ɗauki abun da za ta ɗauka a falon ta koma sama. Neehal ta fito da k'aton tire a hannunta ta ajiye a gaban Sadik, sannan ta koma ta ɗakko drinks ta kawo masa. Shi dai kawai bin ta yake da ido. Neehal ta koma ta zauna, ganin bashi da niyyar taɓa abincin ta ce "Ka ci mana." Ya ce "Na k'oshi." Neehal ta marairaice ta ce "Dan Allah Ya Sadik ka ci, idan ba ka ci ba Mama faɗa za ta mun." Ya yi murmushi a karo da yawa ya ce "Shikenan zan ci." Neehal ta yi murmushin itama. Ruwa kawai ya tsayaya ya sha, Neehal tayi_tayi ya ci abincin amma ya ƙi, dole ta hak'ura ta k'yale shi. Jin an fara kiran Sallah ya mik'e ya na faɗin "Ni zan wuce." Neehal ta ce "Bari na kira Mama ku yi sallama." Ya ce "A'a ki ce mata na wuce kawai." Neehal ta ce "Sai da safe ka gaida gida." Daga haka ta wuce sama. Ɗakin Mama ta leƙa ta sanar mata ya tafi. Mama ta ce "Ok, zan kira shi, kema ya kamata later ki kira shi ki ji ya ya koma gida." Neehal ta ce "To" kawai, amma ita Mama ba ta ma san ko Number'nsa ba ta da shi ba. Ɗakinta ta koma domin yin Sallah.




Bayan ta idar da Sallar, ta ɗakko wayarta da niyyar kiran Haneefah ta faɗa mata Sadik ya zo sai ta tarar da missed call d'in Ameen har 3, waro manyan idanunta ta yi cikin mamaki dan ta san ze yi wuya ka ga ya kira ka ba ka d'aga ba kuma ya ƙara kiran ka, amma gashi ita ya mata har 3 missed call. Bin bayan kiran ta yi, ringing biyu ya d'aga tare yin da sallama. Neehal ta amsa masa ta ƙara da faɗin "Ina yini Yaya." Ameen bai amsa mata ba, sai cewa ya yi "Ina ki ka shiga.?" Neehal ta ce "Ina ƙasa wayar kuma ta na sama a ɗakina."


Me ki ke yi a ƙasan?"


"Bak'o na yi fa Yaya, ina...."




"Alright Gud."


Ya katseta da faɗin haka tare da kashe wayar. Neehal ta bi wayar da kallo bayan ta cire ta daga kunnenta, dama tunda suka fara wayar ta ji kamar ransa a ɓace yake, bakinta ta tab'e ta ajiye wayar ta koma ta cigaba da abun da take yi a laptop d'inta. Ta na cikin aikin a ka ƙara kiran wayarta, ba dan taso ba ta tashi ta ɗauko wayar, baƙuwar number ta gani, kamar ba za ta d'aga ba sai kuma dai ta d'aga. Sallama a ka mata cikin murya mai tattare da nutsuwa, Neehal ta amsa ba tare da ta gane mai magana ba, sai dai kuma ta ji kamar ta san muryar.




"Tunda ba ki kira ni kin ji ya na je gida ba, ni na kira ki na ji dafatan na barki lafiya."




Neehal ta sauke ajiyar zuciya dan ta gane Sadik ne, a hankali ta ce "Am sorry, tunda muka rabu aiki nake yi ne shi yasa." Sadik ya ce "Ok, amma ko ba haka ba nasan ko Number ta ba ki da shi." Neehal ta yi shiru ba ta ce komai ba. Sadik jin ta yi shiru ya ce "Ki je ki cigaba da abun da ki ke yi, sai da safe." Neehal ta ce "Allah ya kai mu, thank you." Sadiƙ ya ce "Gud night daga haka ya kashe wayar."






.Washegari Friday Neehal ta dawo daga gurin aiki da yamma, ta na shiga Falon Mama ta ga Ameen zaune a kan kujera ya na latsa wayarsa, Neehal ta waro manyan idanunta cikin mamakin ganin sa, domin ba ya dawowa Ranar Friday sai dai Saturday or Sunday. Cikin murnar ganinsa ta nufi gurin shi ta na faɗin "Yaya yaushe ka zo.?" Kamar ba da shi take ba, ko d'ago kai ya kalleta ma bai yi ba, balle ya ba ta amsa. Neehal ta turo baki gaba ta wuce sama. Wannan weekend d'in gabad'aya Ameen ya ɗauke wa Neehal wuta, ko gaishe sa ta yi ba ya amsawa. Ita kam Neehal ko a jikinta domin ta saba da wannan halin nasa, idan muskilancin nasa ya motsa.








*****************






Neehal sun koma school inda suka ɗora karatunsu a first semester Level 3, Neehal da Haneefah tare suke tafiya a matakin karatu, sai dai ba department d'aya suke ba, Neehal ta na Department of Mass communication, ita kuma Haneefan ta na karantar Law ne. Neehal zuwa yanzu ta fara sabawa da Sadik, domin Sadik cikin 1 Month sai da yasan yanda ya yi ya shiga jikin Neehal sosai, sam bai nuna mata sonta yake ba, suna mu'amalane a matsayin Yaya da K'anwa. Sosai Neehal take jin daɗin tarayya da Sadik, kusan kullum sai ya zo sun sha hira, ya yi ta bata labaran ban dariya da nishad'i, wani lokacin kuma idan an bata assignment a school tare suke yi, wani lokacin kuma ya yi ta tsokanarta ita kuma tai ta ɓata rai ta na turo baki gaba, haka za su rabu ta na fushi da shi, sai bayan ya tafi ya kira ta ya lallab'ata su shirya. A hankali kaso mafi yawa na damuwar rashin Anwar ya fara barin zuciyarta a sanadiyyar shigowar Sadik cikin rayuwarta.........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:34] Zeey Kumurya: *⚡NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_












1️⃣6️⃣














INAYI MUKU ALBISHIR 💃💃💃💃DA SABON LITTAFINA NA KUD'I MAI SUNA(sarauniya SADDIK'A) PAID BOOK NE GA MASU SO SUYI MIN MAGANA NAN DA NEX WEEK 16 October, 2021 Ranar Asabar IDAN ALLAH YAKAIMU 😍😍😍😍😍😍


GAMAI BUKATAR KARANTA LITTAFIN SARAUNIYA SADDIKA
YAMIN MAGANA TA PC GA NUMBER (07089540330 Asmeety) Sai najiku kadda kubari abaku labari 😍😍😍💕💕💕💕💕


(Hot Sexy 🍌, Love❤️,and💞 Romantic 👄 than Funny 🤣)💞


All in this Book (SARAUNIYA💞 SADDIKA)💞


KADDA KUBARI ABAKU LABARI💞 😍 LOVE YOU FAN'S GOOD LUCK💞




BY ASMEETY💞


















............"Ke!" Neehal ta juyo da sauri jin yanayin da ya yi maganar a zafafe. Ganin yanda ya haɗe fuska tamau ya sa ta shiga nutsuwarta, cikin raunin murya ta ce "Na'am." Ɗauke kansa ya yi kamar ba shi ya kira ta ba, dawowa cikin falon tay ta tsaya a gabansa tare da faɗin "Gani Yaya." Abincin da ta kawo ya nuna mata da hannunsa, cikin rashin fahimtar abun da yake nufi ta ce "Ɗaukewa zan yi na kai dinning?." Wani kallo ya watsa mata, ƙasa tay da kanta da sauri idanunta suka cicciko da k'walla, ta na ƙoƙarin mai da k'wallar ta ji ya ce "Da kike ƙoƙarin fita ki na rawar jiki saboda za ki gurin wani, Ni zan zuba wa kaina abincin.?" Neehal ta ce "Ka yi hak'uri ban san yanzu za ka ci ba." Ta ƙarashe zancen hawaye na zubawa a kan kuncinta, a rayuwar Neehal kwata_kwata ba ta san a mata faɗa ko tsawa, shi kuma Yayan nata ta fuskanci ya na k'aunar hakan. Ta na share hawayen fuskarta ta tsugunna ta haɗa masa tea a ƙaramin cup d'in da ta haɗo da shi, miƙa masa tay ya karb'a tare da faɗin "Thanks." Sauran kayan soye_soyen ta zuba mata a cikin plate ta ajiye masa a gefensa ganin ya sakko ƙasa ya fara shan tea d'in. Harta mik'e ya dawo da ita, ya na kallonta fuskarsa a ɗan sake ya ce "Kukan me ki ke.?" Neehal ta turo baki gaba ba ta ce komai ba. Hannunsa ya zira a aljihun wandonsa ya ɗakko handkerchief ɗinsa dake tashin daddad'an k'amshinsa ya mik'a mata, ba ta yi musu ba ta karb'a ta share hawayennata. Cikin sanyin murya kamar ba shi ya gama mata magana cikin faɗa yanzu ba, ya ce "Rigimammiya kawai, tashi ki tafi." Neehal ta mik'e zumbur ta na ƙara turo baki gaba, Ameen ya bi ta da kallo har ta fice.




Parking space ta nufa kamar yadda Sadik ya ce mata ya na can. Sadik ya hangota ya buɗe Motarsa ya fito ya jingina da ita ya na kallonta, gabad'aya fushin da take a kan abun da Ameen ya mata nemar sa tay ta rasa a dalilin ganin Sadik, murmushi ne kawai yake bayyana a kan fuskarta. "Assalamu alaikum." Neehal ta faɗa lokacin da ta ƙaraso inda Sadik yake, cikin sauke numfashi Sadik ya ce "Wa'alaikissalam." Neehal ta na murmushi ta ce "Ashe da gaske ka zo, Ni fa na ɗauka wasan da ka saba mun ne, ba zuwa kai ba." Sadik dake kallonta ta ce "Shi yasa ki ka shanya ni kenan.?" Neehal ta ce "A'a, Yaya ne ya saka ni abu fa, am sorry." Sadik ya ce "Babu komai, kin san ai yanda amarya ba ta lefi ango ma haka, dan haka tunda aikin Yaya ki ka yi na hak'ura." Neehal ta ɗan murmusa ta ce "Mu shiga ciki mana." Sadik ya ce "Ai tunda ki ka ga na tsaya a nan wucewa zan yi, dan sauri nake, sak'o na biyo in kawo miki." Neehal ta ce "Ba za ka shiga ba kenan.?" Ya ce "Eh, bari na baki na wuce ina sauri ne ana jira na." Bai jira amsar ta ba ya buɗe murfin Motar ya ɗakko abu a cikin wata leda ya mik'o mata. Neehal ta karb'a ba tare da ta gane mene a ciki ba. "Me ne wannan Ya Sadik."? Ta tambaye shi bayan ta karb'a. Ba tare da ya amsa mata tambayar ba ya ce"Ki gaida Mama sai mun yi waya." Ya faɗa ya na shigewa cikin Motar sa, Neehal ta bi shi da kallo kawai cikin mamaki. Reverse ya yi ya d'ago mata hannu, itama hannun ta d'aga masa ta juya ta fara tafiya. Buɗe ledar ta yi kafin ta ƙarasa part d'in Mama, kuɗi ta gani bandir ɗin 1k, zaro ido waje tay cikin mamaki, da sauri kuma ta maida ledar yanda take sannan ta ɗauko wayarta tay dialing number'n Sadik amma bai d'aga ba. Part d'in Mama ta ƙarasa, Mama ba ta falon ƙasa hakan ya sa ta wuce sama, dakin Maman ta nufa direct, bayan ta yi sallama Maman ta amsa mata ta shiga. Mama ta ce "Sai yanzu Neehal daga kai abinci?" Neehal ta ce "Mama Ya Sadik ne ya zo, gurinshi na je." Mama ta ce "To ya shigo mana, sai kuma ku tsaya a waje kamar wani bak'o." Neehal ta ce "Har ya tafi ai, yace sauri yake yi, kinga ma ya bani wannan." Mama ta karb'i ledar ta buɗe, ganin kuɗi ya sa ta d'ago ta na duban Neehal ta ce. "Kuɗin me ne wannan?" Neehal ta ce "Bani kawai ya yi ya wuce bai mun bayani ba." Mama ta ce "Ke kuma ba sai ki tambaye shi ba." Neehal ta ce "Ya na mik'o mun ya shige Motar ya tafi." Mama ta ce "To ki ajiye may be wani abun za ki masa da su, idan kun yi waya sai ki tambaye shi." Neehal ta ce "Toh." Dan ita ko kaɗan ba ta yi tunanin kyauta Sadik ɗin ya bata ba." Mama ta ce "Ki je ki ci abinci Driver ya kaiku ku karb'o ragowar ɗinkunanku ke da Ameerah." Neehal ta amsa mata tare da ficewa daga d'akin.




Bayan sun dawo daga karb'o ɗinkin Sadik ya kira ta, maganar farko da ta fara masa a kan kuɗin nanne, ya ce mata nata ne ai ita ya bawa ta yi hidimar biki. Neehal ta ce ya dawo ya karb'i kuɗin, Mama ta sai mata komai, kuma itama ta na da kuɗi a hannunta tunda duk wata ta na ɗaukar albashi. Sadik ya ce ya riga da ya bata ba zai karb'a ba, Neehal tai ta masa magiya a kan ya zo ya karb'a kamar wani abun, da ya gaji da magiyar ma sai ya kashe wayarsa. Da Neehal ta faɗa wa Mama abun da ya ce, sai Maman ta ce ta masa godiya tunda ya riga ya bata ba za a matar masa ba, itama za ta kira shi ta masa. Kamar yadda Sadik ya bawa Neehal kuɗi 100k haka ya je ya bawa Haneefah ita ma.










************ABUJA************








Yau tun sassafe Hameedah da ta tashi take ta rufzar kuka kamar wadda aka ce uwarta ta mutu, sosai hankalinta ya tashi ganin dagaske bikin Ameen za'a yi. A haka Mommy ta shigo ta same ta Misalin ƙarfe shida na safe, ganin irin kukan da take Mommy ta fara mata magana cikin faɗa. "Haba Hameedah, wai kukan nan ba zai ƙare ba ne, sai kin je wani ciwon ya kama ki a aikin banza, ki barmu da wahala." Cikin kuka Hameedah ta ce "Mommy ta yaya ba zan damu ba, bikin Ya Ameen fa za'a yi da wata ba da ni ba, Mommy ba ki san Yadda nake ji a cikin zuciyata ba ne, wlh Mommy kamar zan mutu haka nake ji." Mommy ta ce "To ba nace ki kwantar da hankalinki ba, indai Auren ku da Ameen ne kamar an yi an gama." "Tun yaushe ki ke faɗin haka Mommy, amma babu abun da ki ka yi akai gashi har auren ya matso, kuma kin ce mun za ki san yadda za ki yi auren nan bai yiyu ba, amma ban ga wata alamar hakan ba." Mommy ta sauke numfashi ta ce "Hameedah ki dena damuwa da matsowar auren kusa, ai ba ki ga an ɗaura Auren ba, kuma wallahi ko da an ɗaura Ni Suwaiba ba zan bari su samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaman auran nasu ba, sai na zame musu masifa da bala'i wadda za su yi da na sanin yin auren." Hameedah ta ce "To Mommy ai idan sun yi auran Ya Ameen ba zai aure ni ba, domin ya sha faɗa ba shi da ra'ayin auren mace biyu." Mommy cikin tarar numfashi ta ce "Kar ki damu da wannan, duk zancen banza ne, shi ya ma isa, ki rubuta ki ajiye Ameen dole sai ya aure ki indai ina numfashi." Hameedah ta yi shiru ta na sauke ajiyar zuciya, maganganun mahaifiyarta ta sun ɗan sanyaya mata zuciya, domin ta san ta idan ta ce za ta yi abu tofa sai ta yi shi. Mommy ganin Hameedah ta yi shiru ta dena kukan sai ta ce mata, "Yanzu zan shirya zan tafi nemo mafita daga nan zan biya Kano ganin kayan lefen." Da sauri Hameedah ta kalle ta ta ce "Yanzu Mommy sai kin je kin ga kayan, ki na farin ciki da auran kenan.?" Mommy ta ce "Ba ki ji ina na ce miki zani ba ne, yanzu daga nan Katsina zan wuce gidan Haj. Rakiya daga nan za ta rakani gurin wani malami, ta sanar mun aikinsa tamkar yankan wuk'a yake, sai na gama da nan sannan in wuce Kanon, kin san idan ban je ba yanzu sai ya zama abun magana, tun kwana uku da suka wuce Yaya ya kira ni akan in je inga kayan, ina sane na ƙi zuwa a washegarin ranar dan Family duk yawanci ranar suka je, ɗazu ma Yayan ya kuma kirana ya ce mun ya ban zo ba? gashi har gobe za'akai kayan. Shi ya sa zan je kar a ce Yayanka Uwa ɗaya Uba ɗaya ɗansa zai yi aure ba ka je ganin lefe ba, yanzu sai ya zama abun magana." Hameedah tay shiru ba ta kuma cewa komai ba jin abun da mahaifiyar tata ta faɗa. Kafin ƙarfe 7 Mommy ta gama shirinta na tafiya Katsina, bayan ta cewa Abban Hameedah Kano za ta ganin lefe. Sai washegari da safe Mommy ta je Kano, Mama ta tarb'e ta ba yabo ba fallasa harma ta tambaye ta ina Hameedah ita ba ta zo ba.? Mommy ta kada baki ta ce "Ba ta da lafiya ne, itama rashin lafiyar Hameedan ne ya hana ta zuwa tuntuni ganin kayan." Mama ta mata addu'ar samun sauƙi. Baƙin cikin da Mommy ta ji a ranta lokacin da ta na kallon kayan ba zai misaltu ba, saboda ganin yanda aka kashewa lefen kuɗi, zuciyarta na faɗa mata da tuni wannan uban kayan ƴar ta za'a kaiwa fa, Takaici da hassada bai barta ta gama ganin kayan duka ba. Washegari a ka kai kayan inda aka tsaida Ranar biki sati uku masu zuwa.






Shirye-shiryen biki ya kankama ta ko ina, kasancewar mahaifin Hafsat Babban Mutum ne a ƙasar nan kuma sananne ya sa tun saura sati bikin a ka fara sanarwa a gidajen Radio, amarya an shirya events kala_kala, shi dai ango ya sanar mata ba kowanne zai halarta ba. Ɓangaren Mama kuwa Events biyu kawai za ta yi, daga Dinner sai Yini/Mother's day. Su Neehal kam k'annen Ango suma suna ta shirye-shiryensu. Kasancewar wannan shine karon farko da Mama da Dad za su fara aurar da ɗa ya sa tun ranar Larabar satin bikin gidan ya fara cika da baƙi ta ko ina zuwa ake, Dangin Mama da dangin Dad. Hameedah wadda har rama tay saboda damuwa da ta sawa ranta itama ta zo bisa tilastawar mahaifiyarta wadda take ta kwantar mata da hankali akan ta daina damuwa ko anyi Auren Ameen ɗinma babu inda auren zai je zai lalace, ganin yanda Mommy'n take ta sintiri gidan Malamai sai hakan ya ƙara kwantarwa da Hameedah hankali. Yau Alhamis, yau ne kuma Ranar Dinner d'in da Aunty Sadiya ta shirya musu su Dangin Ango, Dangin Amarya kuwa tuni suka fara shagulgulan bikinsu.............✍️












*A yi hak'uri da typing error, ban yi edit ba ne.*














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:39] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*








_By_
_Zeey Kumurya_












*1️⃣7️⃣*








_*Alhamdulillah am back*_














*🔥🔥 FITATTU HUƊU🔥🔥*
_Zangon farko 2022_




_Allahamdulillah kuna ina💃🏽! Nace kuna ina?? Masoya wa ƴan nan shahararrun Marubutan wanda ake masu take da *(TAURARI MASU HANNUN LU'U LU'U)*_




_Uhm kada na cika ku da magana, nasan kun matsu kuji wannan taurarin kuma Jaruman wannan shekarar ta 2022 wanda suka wasa alƙalaman su domin farantawa masoyan su rai_


_Munyi duba da halin rayuwa na rashi da ake fama dashi, wannan dalilin ya sanya muka haɗe kanmu tare da Alƙalamanmu, waje guda, wajan ganin mun sauƙaƙa kuɗin da zaku sayi wannan FITATTU HUƊUN da zasu zama Abun ƙwatance a gareku, muje zuwa💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽._


*AUTAR MANYA* _fitacciya ƴar zamani wacce ta nishaɗan tar daku a littafin ta mai suna *AURAN BARE* a yanzu ta shirya tsaf domin bawa masoyanta farin ciki a cikin littafin ta mai taken 💃🏽💃🏽🔥 *BAƘAR FATA* kuna jin sunan kun san na musamman ne kada ku bari ayi babu ku_


*RAHMA REAL LADINGO* _Marubuciyar *RUWAIDA* ba sai na tsaya baku labarin Wacece ita ba, sunanta kaɗai zai sanya ku san cewa tayi fice a duniyar marubuta yanar gizo yanzu ta shirya tsaf domin kawo maku Nagartaccen littafin ta mai suna *DATTIJON ARZIƘI* 💃🏽🔥 Uhm Kuna jin sunan kun san daban yake_




*NIMCYLUV SARAUTA*
_matashiyar marubuciyar wacce alƙaminta yake kan ci, wacce ta faɗa kar daku a littafin ta mai taken *MOON* *AURAN FANSA* yanzu ma ta shirya tsaf a cikin littafinta mai taken *TSINTACCIYA* 💃🏽🔥 Kuna jin sunan ba sai an tsaya magana ba_




*MSS FLOWER BATOOL*
_Ƙasaitacciyar marubuciyar nan wacce littattafan ta suka karaɗe nahiyar makaranta littattafan Hausa, wacce ta wa'azantar daku a *ƳAR SO* yanzu ma ta shirya ta gyara Alkalamin ta, ta ciro maku littafinta mai suna 💃🏽💃🏽 *SULTAN* Uhm sunan kaɗai zai sanya kusan akwai????????_




_Zaku iya fara payment a yanzu haka domin samun damar zama mace ta farko wacce ta siyi wannan littafan, nasan

Please Login or Register in order to submit comment