Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana da hankali da nutsuwa, shine abun ma da ya ja hankalina a game da Ita. Mun kai 3 years muna soyayya kafin mu yi aure, dan sai da na jira ta ƙarasa karatunta na degree. Na ji daɗin zaman aure da A'isha sosai, saboda macece mai haquri da biyayya ga ilimin addini, ta bani kulawa da kowanne ɗa Namiji yake fatan samu a gurin Matarsa ta sunna. A'isha ta san labarinki tass a gurina, saboda yawan zancen ki da nake mata, a duk lokacin da na mata zancenki sai ta ce mun ita dai tana son ta ga Neehal ɗin nan, Allah ya nuna mata ke kafin ta mutu. Ashe baza ku taɓa haɗuwa domin a haihuwar twins Allah ya mata rasuwa. Mutuwar A'isha ta dake ni ba kaɗan ba, sanadiyyar mutuwar ta hawan jini ya kama ni saboda damuwar da na saka a raina da yawan tunani. Idan na kalli twins ne kawai nake jin sanyi a raina. Afrah suna biyu ta ci a gurina, da sunan Ummi da sunanki, Amrah kuma A'isha na yiwa takwara. A hankali radadin mutuwar A'isha ya fara raguwa a zuciyata, sai dai up to now ban ƙara kallon wata mace da sunan soyayya ba balle na yi tunanin ƙara aure, shekara biyar kenan da rasuwar A'isha. Yarana sune farincikina, su suke ɗebe mun kewar Mahaifiyarsu, kuma tun suna jarirai ni na riƙe su, Ummi ta so ɗaukar su ita da Ammi na ce bazan iya yin nesa da ƴaƴana ba su yi haquri zan riƙe su a gurina. Aka samo mun wata dattijuwa (Baaba Talatu) ita take taya ni kula da su, tun suna jarirai har time ɗin da aka sace su." Ya sauke numfashi tare da kallon Neehal cikin ido ya ce "Duk waɗannan abubuwan da suka faru, kamanninki da tunaninki suna manne a zuciyar *Ahmad Aliyu Bulama*. Lokaci zuwa lokaci ina kallon pics ɗinki wanda na adana su a Email ɗina. Ni ba ma'abocin kallon TV ba ne, dan tun ina ƙarami na kallo ba ya gabana, shi yasa ban san ki ba. Na yi mamaki sosai da Aunty Mardiyya da Zahra suka ce mun shahararriyar ƴar jarida ce ke domin ban taɓa sani ba. Dan da nasani kafin yanzu da tuni na binciko inda kike na zo mun haɗu. Tun Ranar da na bar Kano ban ƙara zuwan ta ba sai last zuwan da mukai dalilin su Afrah. Ina sauka a cikin garin Kano ke kika fara faɗo mun a cikin raina, amma ko kaɗan ban yi tunanin ganinki a nan kusa ba, duk tunani ma zuwa yanzu kin yi aure. Lokacin da na yi 2 eyes dake yanayin dana tsinci kaina a ciki na shock ɗin ganin ki ba zai misaltu ba, na kasa banbance tsakanin bayyanar su Afrah da ganin ki da nayi a bazata wanne ya fi sakani farinciki, sai dai rashin gane ni da baki yi ba shi ya kashe mun gwiwa, kuma a ranar ba mu da ishashshen time ɗin zan miki bayanin da zaki iya tunawa da ni. Tunda muka koma gida tunanin ki ya hanani sakat, so nake kawai na ƙara saka ki a cikin idona, amma saboda yanda mutane suke zuwa mun murnar ganin su Afrah that is why ban samu dama na zo ganin ki ba sai yau." Ya yi shiru yana sauke numfashi. Neehal ta d'ago da kanta wanda yake ƙasa tunda ya fara bata labarin, cikin sanyin jiki ta ce "Allah ya ji k'an Aunty A'isha ya gafarta mata." Ahmad ya ce "Amin ya Allah." Suka yi shiru na wasu mintuna kowa da tunanin da yake a cikin ransa. Ahmad ne ya katse shirun da faɗin "A zak'e nake in ji labarin abun da ya faru da ke bayan rabuwar mu, gashi kuma na ga magriba ta gabato." Neehal ta ce "Next time idan muka haɗu sai na baka labarin, dan yana da tsayi." Ya ce "Gobe zan wuce Abuja, amma kafin na tafi zan biyo ta nan Insha Allah." Neehal ta ce "Allah ya kai mu." Ya ce "Amin." Ta ce "Bari na zuba maka abinci, tun d'azu muna ta hira baka ci ba." Ya ce "No, kar ki zuba am full." Ta shagwab'e fuska tare da turo baki gaba. Ya yi murmushi ya ce "Kin san me?" Ta girgiza masa kai ita a dole fushi take da shi, tun da ba zai ci abinci ba. Ya ce "Kin ƙara kyau sosai da zaƙin murya, sai dai shagwab'arki mai kyau tun ta yarinta tana nan har yanzu, tun last zuwan da muka yi na lura da hakan, sai nake tuno da, idan na zaunar dake a gidan Mamy, sai ki shagwab'e mun ki ce, Uncle please zan tafi gida, idan na daɗe Aunty zata dake ni." Ta rufe fuska tana murmushin da ya kufce mata ba tare da ta shirya masa ba saboda yanda ya yi maganar yana kwaikwayon muryarta. Shima ƴar dariya ya yi wadda ta ƙara fito da zallar kyawunsa. Wani irin nishad'i yake ji yau a cikin zuciyarsa, wanda rabon da ya ji irinsa tun kafin rasuwar A'isha. Neehal ita ce first love ɗinsa a duniya, a kanta ya fara sanin menene so. Wayarta dake gefenta ce ta shiga vibrate, ta duba ta ga Sadik ne yake kirancta. Ta ɗan saci kallon Ahmad ta ga ita yake kallo, sai ta ji baza ta iya d'aga wayar a gaban sa, ta ƙi pick. Tana katsewa wani kiran ya ƙara shigowa, shima har ya katse bata d'aga ba. Ahmad ya ce "Ba kiran ki ake ba, ki d'aga mana." Zata yi magana ta ji shigowar sak'o cikin wayar, ɗauka ta yi ta cire key ta duba, ganin Sadik ne ta shiga karantawa a zuciyarta. _Where Are you sweetheart inata kiran ki baki ɗauka ba, gani kuma a cikin gida na zo na ganki._ 'Ya Sadik kuma da sakaliyar yammar nan?' ta faɗi haka a cikin ranta. Reply ta masa da faɗin _Ina abu ne, na zo zan yi pick kafin na ɗauka ta katse, Okay ka ƙaraso ciki mana._ Ta ajiye wayar tare da d'agowa ta kalli Ahmad wanda ya ƙura mata ido. Ta shagwab'e fuska ta ce "Ni fa kallon nan naka yana sa in ji wani abu a jikina, Please ka daina." Ya ce "Idan kina kusa da ni ba zan taɓa iya daina kallon wannan kyakkyawar fuskar taki ba Princess." Ta yi ƙasa da kanta ba ta ce komai ba. Ya ɗauki wayarsa dake kan cinyarta ya shiga Camera ya fara ɗaukarta a hoto ba tare data sani ba. Ta d'ago zata yi magana ya katse ta sauri da faɗin, "Please Princess ko ɗaya ne." Ta yi murmushi saboda yanda ya wani marairaice fuska. Ya ce "Yawwa, Wow da murmushin ya fi kyau." Ya ƙarashe maganar tare da ɗaukarta hoton tana murmushin. Dai_dai nan Ameen ya buɗo ƙofar falon ya shigo...........✍️














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*4️⃣5️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*












...........Washegari tun kafin 7 na safe Neehal ta bar gida zuwa gurin aiki. Kafin ƙarfe ɗaya kuma ta dawo gida. A gajiye ta dawo ga yunwa dake nuk'urk'usar hanjin cikinta dan babu abun da ta ci ta tafi gurin aikin, da ta je can ma ba ta ci komai ba, gashi jiya kafin ta kwanta ta so cin abinci amma wayar da suka yi da Ahmad da Sadik yasa bata ci ba, saboda dare da ya yi. A falo ta ajiye jakarta ta zarce kitchen dan samarwa kanta abun da zata ci. Tea ta fara haɗawa ta sha, bayan ta samu nutsuwa ta fara tunanin abun da zata girka mai sauƙi for lunch, dan Mama bata nan ta je aiki, sai 2 zata dawo. Indomie ta fara dafawa ta ci a cikinta sannan ta ɗora girkin ta fito daga kitchen ɗin dan zuwa ta yi Sallah ta watsa ruwa a jikinta. A falo ta tarar da Zulai tana kallo, ta zauna tana duban Zulan ta ce "Aunty Zulai sannu da gida." Zulai ta juyo cikin fara'a ta ce "Yawwa Neehal, kin dawo ashe? Muna daki muna ta barci ban ma ji shigowar ki ba, yanzu ma tashi na yi nay Sallah, na ce bari dai na fito in yi kallo." Neehal ta ce "Ban ma jima da dawowa ba, bari na ƙarasa upstairs na yi Sallah, na ɗora girki dan Allah ki duba mun kafin na sakko." Zulai ta ce "Shikenan a sauko lafiya." Neehal ta ɗauki jakarta ta wuce sama. Wanka ta fara yi sannan ta fito ta yi sallah, bayan ta idar tana cikin shiryawa ta ji ana knocking ɗin ƙofar ɗakin. "A shigo." Ta faɗa ba tare data tambayi waye ba. Zulai ce ta shigo bakinta ɗauke da Sallama. Ta amsa mata. Zulai ta ce "Kin yi baƙo." Neehal ta ce "Waye?" Zulai ta ce "Babansu Afrah ne, yana falon ƙasa." Ta ce "Okay ki ce masa gani nan zuwa." Zulai ta amsa da "Toh." Sannan ta juya ta fita. Ta ƙarasa simple d'aurin d'ankwalin da take yi, sannan ta ɗauki mayafinta ta yafa a ƙafaɗa ta fice.






Tunda ya jiyo taku ana sakkowa ya ƙurawa step ɗin ido cikin zak'uwa da son ganin ta. Cikin nutsuwarta ta ƙaraso cikin falon kanta a ƙasa saboda kallon da yake jifan ta da shi. Ta zauna a kujerar dake gefen sa a hankali ta ce "Ina yini Uncle." Ya ce "Lafiya k'alau Princess." Ta ce "Ya Mamy?" Ya ce "Tana nan k'alau, Mama bata nan ne?" Ta ce "Eh tana gurin aiki." Ya jinjina kai tare da miƙewa ya dawo gabanta ya zauna a saman carpet." Ta d'ago kanta da sauri ta ce "Uncle ka koma kan kujera ka zauna mana." Ya ce "No, barni a nan, sai nafi ganin wannan kyakkyawar fuskar taki yanda ya kamata." Ta ce "A kan kujerar ma fa zaka gani Uncle." Ya ce "Ba kamar nan ba princess." Saukowa ƙasan ta yi itama ta zauna a ɗan nesa da shi ba ta ce komai ba. Ya yi murmushi ya ce "Kin yi kyau sosai Princess!" A hankali ta ce "Thank you." Ya kwaikwayi muryarta ya ce "Nima thank you." Ta yi ɗan murmushi ta ƙara yin ƙasa da kanta, kunyarsa take ji sosai har yanzu moment ɗinsu na jiya ya kasa ɓacewa daga zuciyarta. Zulai ce ta ƙaraso inda suke hannunta ɗauke da tire mai ɗauke da drinks ta ajiye a gaban su. Ahmad ya dube ta ya ce "Na gode." Ta ce "Babu komai yallaɓai." Sannan ta juya ta koma kitchen dan ƙarasa girkin da Neehal ta ɗora. Neehal ta ɗan matsa kusa da tire ɗin ta ɗauki juice ta tsiyaya masa a cikin glass cup, sannan ta matso kusa da shi ta miƙa masa ba tare da ta kalli fuskarsa ba. Ƙin karɓa ya yi ya tsaya yana kallon fuskarta, ta d'ago ta kalle shi cikin sa'a suka haɗa ido, kashe mata ido ya yi wanda yasa tay saurin yin ƙasa da idonta tana turo baki gaba. Ya karɓa cup ɗin data miƙo masa tare da yin murmushi mai sauti, dama so yake ta kalle shi su haɗa ido kuma ya yi nasara. Ta koma inda take d'azu tana satar kallon sa ƙasa_ƙasa, shi kuma yana kurb'ar juice ɗinsa hankali kwance. Ya yi mata kyau ba kaɗan ba, yana sanye cikin ƙananan kaya wanda suka amshi jikinsa, sassayan k'amshinsa mai daɗin shak'a ya cika mata hanci. 'Yana nan a ɗan gayun sa up to now' ta faɗi haka a ranta. Ya sha juice ɗin fiye da rabin wanda ta zuba masa sannan ya ajiye cup ɗin, ya dube ta ya ce "Idan kin gama kallon nawa sai ki cika mun alƙawari na." Ta ɓata fuska ta ce "Ni ba kallon ka nake ba." Ya yi murmushi ya ce "Tom Shikenan, now start from where we stopped yesterday." Ta ce "Da me fa?" Ya mata kallan ƙasan ido ya ce "Your story mana." Ta ja numfashi a hankali tare da runtse idonta, sannan ta fara ba shi labarin abun da ya faru bayan rabuwar su a tak'aice, daga time ɗin data farka ta gan ta a asibiti Uncle Usman ya kai ta up to now, sai dai ta ɓoye masa abu ɗaya a labarin nata, shine kashe su Anwar da akai, ta ce masa dai kawai rasuwa suke. Bai katse ta ba, har sai da ta kai aya ta yi shiru da kanta. Ajiyar zuciya ya sauke cikin jin daɗin bata kuma shan wata wahalar ba bayan rabuwar su, sai ma cigaba na rayuwa data samu. Abu ɗaya ne ya ɗan taɓa masa zuciya a labarin nata har ya ji tausayinta over da ta ce masa samarinta biyu duk sun rasu, dan ya san ɗacin mutuwar masoyi tunda ya ɗanɗana da A'isha ta rasu. Cikin sanyin murya mai cike da alhini ya yiwa su Anwar da Jameel addu'ar dacewa da samun Rahamar Ubangiji. Neehal ta amsa da "Ameen Na gode, ƙarfe nawa zaka wuce Abujan?" Ya ce "Ƙarfe Shida na yamma." Ta ce "Alright, ina son ka kai ni da gaishe da Mamy idan babu damuwa." Ya ce "Kamar kuwa kin san tana son ta gan ki, dan na bata labarin ki." Neehal ta ce "Har ka bata labarina?" Ya ce "Eh mana, tun a waya ma kafin na zo na ce mata aike kika tsinci su Afrah." Ta ce "Kuma ta tuna ni?" Ya ce "Ina mata bayanin ki ta gane ki." Ta jinjina kai sannan ta miƙe tare da faɗin "Ina zuwa." Upstairs ta hau ta ɗauko wayarta ta kira Mama, dan ta sanar mata za su je gidan Mamy, amma Maman bata ɗauka ba. Ta duba agogo ta ga 2 ta wuce, hakan yasa ta yi tunanin may be Maman tana hanya ne, dan in tana driving bata ɗaukar waya. Sauran wayoyinta ta ɗauko ta zira a aljihun doguwar rigar jikinta, kasancewar rigar mai aljihu ce. Ta fito ta dawo downstairs, kitchen ta shiga ta duba ko Zulai ta ƙarasa abincin ta zubawa Ahmad. Ganin ta kammala har ta bar kitchen ɗin ma, sai ta ɗauko plate ta zuba masa, ta rufe da wani plate ɗin ta ɗora akan tire. Sannan ta ɗauko bowl ta zuba masa kayan salad a ciki, shima ta ɗora akan tire ɗin ta saka spoon ta ɗauko ta fito. Yana ƙasa a zaune har time ɗin bai koma kan kujera ba, ta ajiye tire ɗin a gabansa ta ce "Ga abinci Uncle." Ya d'ago yana duban ta ya ce "Thank you so much." Neehal ta juya ta bar falon dan bashi guri ya ci abincin ta shige ɗakinsu Dije. After some minutes ta hango Mama ta window ta shigo falon suna gaisawa da Ahmad. Ta miƙe ta fito falon. "Welcome Mama." Ta faɗa cikin murnar dawowar Maman. Mama ta ce "Yawwa Neehal, ina hanya na ga kiran ki." Neehal ta ce "Eh, dama za mu je gidan Mamy ne da Uncle Ahmad shine na kira na faɗa miki." Mama ta ce "Okay to sai kun dawo ku gaishe ta." Ta juya ga Ahmad wanda kansa ke ƙasa tun shigowar Mama ta ce. "Idan kun dawo ka shigo zan baka sak'o ka kaiwa Ummi." Cikin girmamawa ya ce "Toh Mama Insha Allah." Mama ta wuce sama, ita kuma ta ƙarasa inda yake. Ta kalli tiren abincin data ajiye ta ga ko taɓa shi ba ai ba, yanda ta bar shi haka yake. Ta ɓata fuska sosai ta ce "Uncle baka ci abincin ba ai." Ya miƙe cikin son kawar da zancen abincin ya ce "Tashi mu tafi." Ta miƙe bata ce komai ba ta je ta yiwa sallama sannan ta sakko suka tafi. Har ya fice daga falon, a waje ta tarar da shi suka jera suka ƙarasa parking space. Ya buɗe mata motar da ya zo a cikin ta ta shiga, bayan ya rufe mata murfin ya zagaya ya shiga driver seat ya kunna Motar suka fice daga gidan. Har suka ƙarasa gidan Mamy babu wanda ya ce kala a cikin su, sai cool music ne yake tashi a cikin motar. Ita fushi take a kan ya ƙi cin abinci, shi ma kuma yasan laifinsa shi yasa shi ma ya yi shiru, ya barta ta ɗan huce sai ya rarrashe ta.










Bayan ya yi parking ta buɗe murfin Motar ta fito, shi ma ya biyo bayan ta ya fito. Ya zagayo inda take tsaye a jikin Motar ya kama hannunta yana kallon ta ya ce "Princess what happened?" Ta girgiza masa kai tana ƙoƙarin k'wace hannunta. Ya sakar mata hannun tare da matsowa daf da ya marairaice ya ce "I'm sorry Dear." Ta sauke numfashi ganin kamar zai rungume ta, ta ce "Babu komai fa Uncle." Ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa tana murmushi. Ya sauke ajiyar zuciya tare da kama hannunta suka nufi cikin gidan, ta yi ƙoƙarin k'wace hannun nata amma ya ƙi sakar mata. Mai aikin Mamy ce ta zo ta buɗe musu ƙofa bayan ya danna beil. Neehal ta samu ta k'wace hannunta ta bi bayan sa suka shiga cikin falon da sallama. Ahmad ya nuna mata kujera ya ce ta zauna, ta zauna, amma a ƙasa kan carpet. Ba jimawa Mamy ta fito daga ɗakinta mai aikinta da ta kira ta na biye da ita a baya. Da fara'a haɗe da murna Mamy ta ce "Sannu da zuwa yarinyar kirki, d'iyata ashe zan ƙara ganin ki?" Neehal ta yi murmushi cike da kunya ta gaishe da Mamy. Mamy ta amsa mata tare da rungume ta a jikinta cikin kulawa, tana tambayar ta su Mama. Neehal ta ce "Tanan nan lafiya, ta ce a gaishe ki." Mamy ta ce "Ina amsawa." Ahmad ya miƙe yana duban Mamy ya ce "Bari in je in dawo tunda yau bata ni kike ba." Mamy ta ce "Sai ka dawo, ina ta murnar ganin Ƴata ina zan tuna da kai." Ahmad ya ce "Shikenan ai." Sannan ya kalli Neehal ya kashe mata ido ya ce "Sai na dawo Princess." Bata iya ce masa komai ba saboda kunya har ya fice. Mai aikin Mamy ta kawowa Neehal abinci da drinks da su snacks. Mamy kam sai nan_nan take da Neehal. Da ƙyar ta tilasta mata ta tsakuri abinci cikin jin kunya. Mamy kam sai janta take da hira. Da lokacin Sallar la'asar ya yi ta kai ta bedroom ɗinta ta yi Sallah. Bayan ta idar ba jimawa Ahmad ya dawo gidan, ta fito suka tafi. Mamy ta bata leda mai ɗauke da turaruka da kayan shafe_shafe, shi ma dak'yar ta karɓa dan Ahmad ne ma ya karɓar mata. Kafin biyar sun ƙarasa gida, ta fito ta bar shi a Mota dan karɓo masa sak'on da Mama ta ce zata ba shi. Sai da ɗauko tsarabar data yiwa su Afrah sannan ta biya ɗakin Mama dan karɓar sak'on Ummi. Mama ta bata wata leda wadda bata san mene a ciki ba ta kay masa, ta buɗe bayan Motar ta ajiye sannan ta shiga cikin motar kamar yadda ya ce mata, tana shiga ya kulle motar sannan ya tasa ta a gaba da kallo, ganin lokaci yana tafiya ta ce "Uncle kar fa time ya ƙure baka tafi ba, kuma ka ce sai ka koma gidan Mamy kafin ka wuce airport." Ya sauke numfashi cikin sanyin murya ya ce "Ban gaji da kallon ki ba ko kaɗan Princess, kamar na d'aga tafiyar haka nake ji." Ta juya masa ido ta ce "Ni dai nafi son ka tafi yau, saboda na san yanzu twins ɗina suna can suna damuwar rashin ganin ka two days." Ya ɓata fuska ya ce "Kin fi son yaranki akaina kenan?" Tana dariyar tsokana ta ce "Eh mana." Ya marairaice fuska kamar wani maraya ya tallafi fuskarsa da hannayensa biyu ya tsura mata ido. Ta ce "Me nene?" Ya nuna mata kanta da hannunsa, a shagwab'e ta ce "I'm sorry My Uncle." Ya lumshe ido ya buɗe bai ce komai ba, seriously kamar ya fasa tafiyar saboda ita haka yake ji. Amma ya san hakan ba zai yiyu ba, saboda aikinsa da kuma yaransa da su Ummi. Ya duba agogon hannunsa sannan ya dube ta ya ce "Zan wuce Princess." A sanyaye ta ce "Sai yaushe?" Dan itama ta fara jin ba daɗi saboda tafiyar da zai yi. Ya ce "Next week idan na samu chance, idan kuma ban zo ba sai upper week." Ta ce "Amma zaka taho mun da Yarana in gan su ko?" Ya ɗan matso kusa da ita ya ce "Idan ma cewa kikai in dawo miki da su gurin ki gaba-ɗaya da zama zan iya Princess." Ta kalle shi da sauri cikin mamakinsa, ya gyaɗa mata kai alamar tabbatarwa, ya ƙara da faɗin "In dai a kan farincikin ki ne Princess babu abun da ba zan iya ba." Cikin murna ta ce "To ka dawo mun da su Please ka ji Uncle?" Ta yi maganar da iya gaskiyar ta har cikin ranta. Ya yi murmushi ya ce "An gama Princess, next zuwan da zan yi Insha Allahu zan taho miki da su da kayan su gami da komai na su." Cikin jin daɗi ta ce "Thank you so much Uncle." Ya ja dogon hancinta ya ce "You deserve everything from me my Baby." Ta yi murmushi ba ta ce komai ba, ya kama hannunta tare yi mata pick a kuncinta, so romantic voice ya ce "Bye Princess I will miss you." Ta lumshe idonta murya ƙasa_ƙasa ta ce "Allah ya kiyaye hanya ya kai ku lafiya." Ya amsa da Ameen tare da sakar mata hannunta. Ta buɗe murfin Motar a hankali ta fito cikin sanyi jiki, bayan ta rufe ta d'aga masa hannu. Yana murmushi ya ce "I love You!" Ta juya da sauri ta nufi part ɗin Mama cikin matsananciyar kunyar sa, zuciyarta cike fal da murnar ya ce zai dawo mata da twins ɗinta su cigaba da zama a gurin ta........✍️










_*A yi haquri da wannan hilis*_










*By*
*Zeey Kumurya*






[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*4️⃣6️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*












.........Mama tana kitchen tana girkin dare, Neehal ta shiga kitchen ɗin ta rungume Mama tana murmushin farinciki. Mama ta ce "Lafiyarki kuwa zaki zo ki ɗane mun jiki, ina cikin aiki?" Neehal ta bar jikinta cikin murna ta ce "Mama Uncle Ahmad ya ce zai dawo mun da su Afrah." Mama tabar abun da take ta juyo ta fuskance ta, ta ce "Kamar ya fa?" Ta ce "Mama zai dawo mun da su, su cigaba da zama a gidan nan." Mama ta ce "Uhm, na san Ahmad zai yi haka ne saboda da ke, ni kuma ba zan taɓa yarda da hakan ba, saboda Ahmad da Family ɗinsu sun fi mu buƙatar twins a kusa da su, especially ahalin mahaifiyarsu data rasu, tunda su suke kallo su ji daɗi a madadin mahaifiyarsu." Neehal ta shagwab'e fuska ta ce "Mama wlh na yi kewar twins over, kawai ina daurewa ne saboda karki mun faɗa ki ce ina damuwa." Mama ta ce "Nima ai na yi kewar su, sometimes ina zaune sai inga kamar za su zo su haye mun jikina kamar yadda suka saba, amma ya za mu yi dole mu haqura mu barwa danginsu su." Neehal kamar zata yi kuka ta ce "To ai za suna zuwa gurin Family ɗin nasu akai_akai." Mama ta ce "Sai kuma ki yi, amma ba dani za ai wannan son zuciyar ba." Ta juya ta cigaba da aikin ta. Neehal ta matso jikin Mama kamar zata yi kuka ta ce "Ki yi haquri Mama idan ranki ya ɓaci, zan je masa ya fasa dawo su ɗin kawai." Mama ta sassauta murya ta ce "Shikenan kar ki mun kuka, je ki ki

Please Login or Register in order to submit comment