Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gurin bikin ta ce "Wai Hameedah meke damunki ne? so kike har sai mutane sun fuskanci halin da kike ciki, masu dariya su yi miki suna Allah ya ƙara, na ce miki daure zuciyarki za ki yi ki nuna kamar baki damu ba, a yi bikin nan a gama." Hameedah ta d'ago kanta cikin sheshshek'a ta ce "Mumy na yi iya yina nayi ƙoƙarin hakan amma na kasa, wallahi Mumy ba ki ji yanda nake ji a cikin zuciyata ba kamar ana rura mun garwashin wuta." Mumy ta ce "Na san abun da ciwo, kuma nima ina jin yanda kike ji, amma ki daure dai, na faɗa miki ko mai daren daɗe wa sai kin auri Ameen in dai da bokaye a cikin duniyar nan, yanzu dai ki share hawayenki in faɗa miki wani abu kin ji My daughter." Hameedah ta gayd'a mata kai ta fara share hawayen nata.






Misalin ƙarfe 12:30 na dare Ameen ne zaune a falon Daddy shi da Mama da ta kira shi, ya tattara duka hankalinsa yana sauraren abun da zata faɗa masa. Mama ta ce "Dama d'azu kai ka tsayar da Neehal?" Ya ce "Eh." Mama ta ce "Akan wanne dalili?" Ya yi shiru, Mama ta ce "Ka yi shiru ina maka mgn." Ya ce "Babu komai Mama." Mama ta girgiza kai ta ce "To me ne dalilin da yasa ka bata kayan data saka? bayan ga wanda suka ɗinka za su saka ita ƴan'uwanta." Ameen ya ce "Mama wai dama wannan shine kiran da kika mun? wallahi na ɗauka wani babban abunne ya faru." Mama ta harare shi ta ce "Ban sani ba." Shigowar Neehal falon ya hana Ameen faɗar abun da zai faɗa. "Ke kuma daga ina?" Mama ta tambayi Neehal tana kallonta, Neehal ta turo baki gaba ta ce "Bacci zan yi a nan saboda ina son na kwana tare da yaran." Mama ta nuna mata dakin da suke da hannu tana faɗin "Suna nan, zaki wani kwaso jiki a daren nan ki taho kamar da tare da su kike kwana." Neehal ba ta ce komai ba ta shige, Ameen da ya bita da kallo har ta shige dakin sannan ya dubi Mama ya ce "Wanne Yara ne kuke magana akansu." Mama kamar ta share ta ƙi faɗa masa sai kuma dai ta sanar masa, don abokin kuka shi ake fadawa mutuwa. Shima ya girgiza da lamarin, amma dai ya ce wa Mama da safe sai akai yaran gidan Radios da Televisions a bada cikiyarsu ko za a dace a samu iyayensu. Mama ta yi na'am da shawarar shi. Neehal ta daɗe kafin bacci ya ɗauke ta, tana ta aikin kallon yaran, tana jin ƙaunar su na mamaye mata zuciya.




Washegari da safe Neehal tana tattare ɗaki Yarinya ɗaya ta tashi tana kiran sunan Daddy, Neehal ta ajiye tsintsiyar hannunta ta ƙarasa gadon ta d'ago ta tana faɗin "Kin tashi, mu je ki yi fitsari to." Yarinyar dake binta da kallo ta gyaɗa mata kai. Bayan ta yi fitsarin Neehal ta wanke mata baki da fuska suka fito, suna fitowa ta ga itama ɗayar ta tashi zaune tana ta mutsitsika ido, Neehal ta kama ta itama ta kaita toilet, Bayan sun fito ta kalle su ta ce "What is your names?" Wadda tafi surutu ta ce "Afrah, amma Daddy yana ce mun Princess, a lesson da islamiyya kuma *FATIMA AHMAD*." Neehal ta jinjina kai ta ce "Nice name Darling." Sannan ta juya ta kalli Ɗayar ta ce "Ke fa." Yarinyar ta ce "Amrah, amma Daddy yana ce mun Jewel a lesson da islamiyya kuma *AISHA AHMAD*." Neehal ta Jinjina kai tana murmushi ta ce "Nice name sweetheart." Afrah ta ce "Aunty safiyar ta yi zaki kai mu gurin Daddy ko?" Neehal ta gyaɗa mata kai zuciyarta cike da k'aunar yaran. Mama ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da tea flaks da ƙananun cups, yaran suka bita da kallo kafin su haɗa baki a tare su ce "Ina kwana." Mama ta ajiye kayan hannunta tare da amsa musu, ta ƙaraso ta shafa kansu da cike da kaunarsu, dan yaran sun matuƙar burge ta ba kaɗan ba, musamman da suka gaishe ta, ga dukkan alamu daga gidan tarbiyya suke. Mama ta dubi Neehal ta ce "Ɗauko musu kayansu a saka musu, bari na haɗa musu breakfast su yi." Neehal ta amsa mata tare da ficewa daga ɗakin, yaran suka bita da kallo kamar za su bita. Bayan sun yi breakfast Neehal ta musu wanka ta shirya su cikin rigunansu na jiya. Kasancewar yau ne d'aurin Aure yasa gidan ya ƙara cika da baƙi mata da maza, duk inda Neehal ta ɗora k'afarta su Afrah na biye da ita a baya, duk wanda ya tambaye ta yaran waye sai ta ce na wata Friend ɗinta ne. Ɗaya daga cikin sojojin gidan ta bawa kuɗi ya siyo wa musu kayan sakawa da takalma da panties, kafin Azhar ya kawo mata ta shirya su tsaf suka yi kyau sosai. kowa so yake ya ɗauke su ko ya musu hoto, amma yaran sun ƙi yarda da kowa sai Neehal, saboda ganin taron jama'a, ita kuwa ta cika su da kayan zaƙi dangin su chocolate da sweet suna ta sha. Mama kanta ya ɗau caji tana da hidima da mutane, hakan ya sa ba ta bi takan zancen yaran ba, dama kuma da taywa Daddy maganar su ya ce a bari bayan biki sai a san abun yi. Ƙarfe biyu na rana aka ɗaura Auren AL'AMIN MUHAMMAD TAFIDA da amaryarsa HAFSAT AHMAD ƊAN GASKE. Anan babban masallacin Juma'a dake cikin Narasawa G.R.A. Yau ma Neehal ta yi kyau sosai, shadda ta saka da safe Wadda aka mata akai mai kyawun gaske, ta kafa ɗaurinta. Su Afrah sai faɗin "Kin yi kyau Aunty." suke, Murmushi Neehal take idan suka faɗi haka. Ta ce musu "Thank you Dearies." Wajen ƙarfe uku Sadik ya ƙaraso gidan. Neehal ta fito tare da twins ɗinta, tunda ta fito ya ƙura mata ganin irin kyawun da ta yi. Neehal ta gaishe shi ya amsa yana kallon yaran, Neehal ta ce "Ya su Maamah da Abba?" Sadik ya ce "Suna Lafiya, Ya taro?" Neehal ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Allah ya sanya Alkhairi ya ba su zaman lafiya, saura naki kuma." Neehal ta yi murmushi ta ce "Yau har na gaji da jin wannan furucin, kowa muka haɗu sai ya ce sai mun zo naki kuma." Sadik ya ce "To ai gaskiya ne, gwara Mama ta aurar dake ta huta da rigimarki." Neehal ta ce "hmmm." Kawai, Sadik yace "Wannan cutes babies ɗin fa?" Neehal ta ce "Yaran wata Friend ɗina ne." Sadik ya ce "Masha Allah, Allah ya raya su." Neehal ta ce "Ameen." Tare da dubansu ta ce "Ba ku gaida Uncle ba." Amrah ce ta fara gaishe shi da faɗin "Ina kwana." Sannan itama Afrah ta gaishe shi, ya kama hannunsu tare da amsa musu. Bai wani jima ba ya tafi saboda Ameerah data zo kiran Neehal. Suna tafiya Ameerah ta ce "Amma Yaa Neehal wannan saurayinki ne?" Neehal ta girgiza kai tare da faɗin "Ko ɗaya, he is just Friend." Ameerah ta yi shiru amma ba dan ta yarda ba. Ƙarfe huɗu aka tafi gurin da za ai Mother's Day, sai bayan magriba aka tashi. Yau kam amarya ba ta zo ba, tana gida suna nasu suma, shima Ameen ɗin bai je ba, hakan yasa yau kwata_kwata ba su haɗu da Neehal ba. Twins kam ganin hada_hadar mutane yasa ba su ƙara takurawa Neehal akan ta kai su gurin Daddy'nsu ba, sai da suka zo bacci nema suka so yi mata rigima ta lallaɓawa su da faɗin sai an gama biki zata kai su. Washegari ma anyi taro a gida inda akai kidan ƙwarya manyan mata suka cashe, tun kafin Azhar aka fara har bayan la'asar ana yi. Yau za a miƙa Amarya gidan angonta, misalin ƙarfe biyar na yamma Neehal dake jin duk jikinta a sanyaye ba tare da tasan dalili ba ta barwa Haneefah twins ta nufi part ɗin Ameen............✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:40] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_












*2️⃣1️⃣*














..........A hankali ta buɗe ƙofar falonsa ta shiga bakinta ɗauke da Sallama, kanta na ƙasa ba ta yarda ta d'ago ba saboda falon cike yake da abokanansa. Suka amsa mata suna binta da kallo, Salman ganin yanda ta takure a tsaye ya dube ta ya ce "Shiga mana Neehal, yana ciki ai." Neehal ta ce "Toh." Tare da gaishe su a lokaci ɗaya, ba ta jira amsarsu ba ta wuce. Wani a cikinsu da ya bita da kallo ya ce "Salman, wannan kamar ƴar jaridar nan ta ASTV?" Salman ya ce ba kama ba ce ita ce." Ya ce "Wow yarinyar me kyau tana burge ni wlh." Kafin ya ce wani abu ya ji wani a cikinsu yana faɗin "Ita ce wadda suka zo tare da Al'ameen ranar dinner ai, dama ƙanwarsa ce?" Salman ya ce "Yeah." Wanda ya fara magana da farko ya ce "To ai ni ranar na ɗauka ita ce ma Amaryar saboda ta yi kyau sosai har ma tafi Amarya....." Haka dai sukaita magana akan Neehal.










A hankali take knocking ƙofar bedroom ɗinsa kamar me tsaron wani abu, Ameen dake shiryawa a gaban mudubi don bai jima da fitowa daga wanka ba ya ɗan yamutsa fuska ya ce "Waye?" Neehal tay shiru yanayin da take jin jikinta da zuciyarta na ƙara tsananta, Ameen ya taho ya buɗe ƙofar zuciyarsa cike da masifa, a tunaninsa a cikin abokansa ne wani ya zo zai ƙara masa ciwon kai akan wanda suka sa masa d'azu. Cike da mamaki yake kallonta, kanta na ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, Ameen ya koma ciki yana faɗin "Come in." Neehal ta shiga kamar munafuka ta zauna a gefen gado, yana fesa turare ya ce "What happened." Ganin ta ƙi cewa komai tunda ta shigo. A hankali ta d'ago ta kalle shi amma yanda ba za su haɗa ido ba ta ce "Yaya..." Sai kuma ta yi shiru hawaye ya fara zuba daga idonta, Ameen ya sauke numfashi sannan ya dawo kusa da ita ya zauna ya kama hannunta murya ƙasa_ƙasa ya ce "Tell me what happened?" Neehal ta share hawayenta ba ta ce komai ba, Ameen ya ƙura mata ido domin yasan dalilin kukanta a hankali ya ce "Kin fara missing Yayanki ko?" Neehal ta d'aga masa kai da sauri sannan ta ce "Shikenan Yaya na dena ganinka every weekend?" Ameen ya girgiza mata kai tare da faɗin "Wa ya faɗa miki? Zan dinga zuwa kodayaushe." Neehal ta ce "Na san baza ka zo ba tunda ka yi aure." Ameen ya ce "Dolena ma inzo inga my Mum da little sis ɗina." Neehal ta ce "Dagaske?" Ya d'ago kanta ya saka idanunsa a cikin nata yana mata wani kallo ya gyaɗa mata kai, Neehal ta kumshe idanta da sauri gabanta na fad'uwa. Ameen ya sakar mata fuska yana sauke numfashi, tashi ya yi ya ɗauko wayarsa ya shiga gallery ya miƙa mata, ta karb'a tana dubawa. Waro idanta ta yi tana murmushi ta ce "Wow Yaya pics ɗin sun yi kyau sosai." Ya yi murmushi kawai yana kallonta, ita kuma ta cigaba da kallon hotunan. Pictures ɗinsu ne wanda aka musu ranar dinner ita da shi, wani suna zaune wani kuma a tsaye lokacin da ta je yi musu lik'i, sosai hotunan sukai kyau, kuma babu ta yanda za'ai ka gani ka ce ba Neehal ce amaryar ba. Ta ajiye masa wayar bayan ta gama ta gani tare da mik'ewa ta ce "Yaya Bari in koma." Ameen ya mata wani kallo ya ce "Ba za ki raka ni gidan Amaryata ba?" Neehal ta waro Ido ta ce "Ni kuma Yaya? ga Freinds ɗinka nan." Ya kau da zancen da faɗin "Ina new kids ɗinki?" Neehal ta ce "Suwa?" Ya ce "Twins." Neehal ta ce "Oh, suna gurin Haneefah." Ya ce "Me yasa ba ki zo mun da su ba?" Ta ce "Na ga baka son hayaniya ne kar su dame ka." Ameen ya ce "Ok, me kike so in baki a ɗakin nan?" Neehal ta hau juya ido a ɗakin ganin babu abun da zata buƙata a ɗakin, ta ce "Nothing." Ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai, sai kuma ta kalli kan mudubi ta ɗan shagwab'e fuska ta ce "Na tuno, your perfumes." Ya ce "Ai is only for male." Ta turo baki gaba ta ce "Ai ba ajikina zan dinga sawa ba, kawai zan dinga jin k'amshin ina tunawa da kai." Ameen yay murmushi ya buɗe wata jaka ya ɗauko mata turaruka kala uku ya bata, Neehal ta karb'a da murnarta ta ce "Thank you so much."






Tare suka fito daga ɗakin, Neehal ta fice shi kuma ya zauna yana haɗe rai dan kar su cigaba da tsokanarsa, aikwa kamar ma ya ce su yi suka fara, daga baya kuma suka koma zancen Neehal kowa yana faɗin yana kamu. Shi dai ko kanzil bai ce musu ba. Neehal tana koma Haneefah ta miƙa mata su Afrah da suke ƙoƙarin saka kuka ganin shiru_shiru ba su ga Neehal ɗin ba, Neehal ta kama hannunsu suka shiga ɗakinta, ta adana turarukan. Bayan Magriba aka tafi ɗaukar Amarya, su Neehal kam ba a je da su ba, Mama ta ce sa je daga baya. Bayan isha'i mutane suka fara watsewa, gidan ya rage daga su Aunty Sadiya sai na nesa waɗanda za su tafi gobe da safe, Hameedah ma da Mamanta suna nan. Sai yau Mamansu Anwar ta zo ita da k'annenshi, ba ta jin dad'i ne shi yasa tunda aka fara bikin ba ta zo ba. Neehal dai tana kwance a ɗakin Mama tana ta matsar kwalla, Twins na manne a jikinta suna cin Cheese, tunda ta idar da Sallah ta haye gadon tay kwanciyarta. Hajiya ce ta shigo ɗakin tana ƴan mitocinta da ba ta rabo da su, kallon Neehal ta yi ta ce "Ke kuma lafiya kike kwance?" Neehal tay mata shiru, ta tab'e baki ta ce "Wai waɗannan Yaran ina uwarsu ne?" Daidai nan Mama ta shigo ɗakin, Hajiya ta ce "Yawwa, Ta Abuja (Da yake haka take ce mata idan fulatancin ya motso mata) yanzu nake tambayar wannan uwar langwan ta mun shiru, waɗannan Yaran waye ne haka, take ta wahala da su?" Kafin Mama ta ce wani abu Neehal ta juyo da sauri idanunta da guntun hawaye ta ce "Ƴaƴan ƙawata ne, ba ta da lafiya ba ta samu zuwa ba shine ta aiko aka kawo mun su." Mama ta kalle ta kawai, Hajiya ta ce "Ayyo, ga su kuwa kyawawa kamar Ƴaƴan Turai." Mama dake kallon Neehal ta ce "Kukan me kike?" Kafin ta yi magana Afrah ta yi karaf ta ce "Ba ta da lafiya." Da yake haka Neehal ɗin ta ce musu da suka dame ta da tambaya ganin tana kuka. Mama ta ce "Allah ya sauwaqe." Ta juya ta fice. Hajiya ta ce "Sannu gajiyar biki ce." Ciki_ciki Neehal ta ce "Yawwa." Hajiya ta fara yiwa su Afrah surutu da tambayoyi kamar wasu manya, su dai shiru kawai suka yi suna kallonta tare da ƙara lafewa a jikin Neehal, ta gaji ta tashi ta fita.










Da daddare wajen 12 Mama suna zaune ita matar Yayan Daddy da Hajiya dake ta gyangyad'i, ance ta koma ɗaki ta ƙi. Neehal ce ta fito daga ɗakin Mama wadda bacci ya ɗauke ta bayan ta gama shan kukanta, yanzu ma Amrah ce ta tashe ta, idanunta kuwa har sun kumbura. Mama ta bita da kallo kafin ta ce "Wai lafiyarki kuwa Neehal, me aka miki kike kuka?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba, Mama ta ce "Ba na son halin kin nan fa, ana miki magana kina ji ki yi shiru." Neehal ta ce "Ba komai kawai dai.." sai kuma ta yi shiru, Mama ta ce "Kawai dai me?" Neehal ta ce "I start missing Yaya." Mama ta tab'e baki ta ce "Shine kuma zaki zauna kina kuka, kamar wanda ya mutu, ko ce miki aka yi ya tafi kenan?" Neehal ta ce "To ai ba zai dinga zuwa kodayaushe ba." Mama ta ce "So you can follow him ai, tunda tare aka haife ku." Matar Yayan Dad wadda ake kira da Umma ta ce "Ai da gaskiyarta dole ta yi kewar ɗan'uwanta." Hajiya data wartsake tun fitowar Neehal ta ja tsaki ta ce "Wai dama akan Ameen kike asarar hawayenki saboda baki san ciwon kanki ba, Ameen ɗin da ba wani k'aunarki yake ba, ai daɗi ma ya kamata ki ji yanzu zaki wataya babu mai ƙara takura miki a gidan nan, kafin kema Allah ya kawo miki miji ki tafi." Neehal ta turo baki gaba ta nufi kitchen dan haɗawa Amrah tea.










Washegari tun safe sauran baƙi suka tafi, su Aunty Sadiya ma suna gama gyaran gidan kafin Azhar suka wuce nasu gidajen, Hajiya ma ta bi Ammin Amirah sun wuce Gombe. Gida ya rage daga Mama da Neehal sai su Dije masu aiki da Twins, sai Hameedah da Mom ɗinta da Umma wanda suma da Yamma za su wuce Abuja. Driver Mama ta aika ya kaiwa su Ameen breakfast, da rana ma haka. Neehal kam wuni ta yi a ɗaki ita da Twins ɗinta. Sai can yamma Haneefah ta zo gidan. Da daddare bayan kowa ya tafi Mama ta je part ɗin Dad su yi magana akan su Afrah, Mama tana duban shi ta ce. "Daddy yanzu sai mu san abun yi akan yaran nan, dan yanzu na san duk inda hankalin iyayensu yake a tashe yake ba kaɗan ba." Daddy ya ce "Hakane, tunda gobe Monday idan Neehal zata aiki sai mu tafi tare mu bada a yi cikiyar iyayensu, na san Insha Allahu za'a samu iyayen nasu ko a'ina suke a ƙasar nan, tunda babu inda ba'a kallon ASTV, daga nan sai mu biya wasu gidan Radios ɗin duk mu bada cikiya. Mama ta ce "Allah ya kai mu goben lafiya. Dad ya ce "Ameen, kira mun Neehal ɗin ma tunda aka fara biki haɗuwar mu ta yi wuya." Mama ta ce "Kuma a part ɗin nan take kwana, dan dai ana sha'anin biki ne." Mama ta kira Neehal a waya ta ce ta zo part ɗin Daddy. Ba jimawa ta ƙaraso tare da Twins. Mama ta ce mata "Kai Neehal kina cika wa yaran nan kayan zaƙi, duk sanda zan gansu da sweet ko chocolate a hannunsa." Neehal ta yi Murmushi tare da zama a kusa da Daddy. Ta gaida Daddy suma su Afrah suka gaishe shi, ya amsa musu cike da fara'a. Sun ɗan taɓa hira da Daddy har su Afrah suka fara bacci. Mama ta dubi Neehal ta ce "Gobe za mu je mu yi report akan yaran nan, daga nan mu biya mu ba da cikiyar iyayensu." Gaban Neehal ya faɗi, dan bata k'aunar abun da zai rabata da yaran ko na second ɗaya, ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mama data kula da yanayinta na canzawar da fuskarta ta yi ta ce "Sai ki shirya da wuri, dan ke zaki yi bayanin yanda kika tsince su." Neehal da idanunta suka ciko da k'walla ta ce "Mama gobe ya yi wuri a bari a ƙara wasu kwanaki sai a...." Kallon da Mama ta watsa mata yasa ta had'iye maganarta. Mama ta ce "Kina cikin hankalinki kuwa? Yanzu kin san irin tashin hankalin da iyayensu suke ciki na rashinsu har na kwana biyu ba su san inda suke ba." Neehal ta ce "To ni Mama ban san rabuwa da su." Mama ta ce "Uhm, ke da kika same su sama ta ka kenan, kuma dudu kwana biyu kawai kuka yi tare, amma ba kyasan rabuwa da su, balle kuma mahaifiyarsu da ta haife su ta raine su na shekaru." Neehal ta ce "Ai ba su da Uwa, ta rasu." Mama ta ce "Who told you?" Neehal ta ce "Su ne, suka ce mun Daddy'nsu yace their Mom ta tafi ba za ta dawo ba for ever." Mama ta ce "Allah ya ji k'anta, amma ai suna da Uba da dangi ko?" Neehal ta yi shiru ba ce komai ba sai hawaye take. Daddy dake kallon su Ya ce "Daughter me yasa bakya son su tafi?" Neehal ta ce "Dad I love them and kuma bana son na rabu da su, na ji ina son su sosai, kuma ga su marayu ina tausayin Maraya sosai because....." Mama ta katse ta da faɗin "Shut up, Stupid, komai za ki ce yara dai sai an maida su gurin iyayensu, duk yanda kike son su ba ki kai iyayensu ba." Tana gama faɗar haka ta mik'e ta shige bedroom ɗin Daddy. Dad ya rarrashi Neehal ta bar kukan da take sannan ya rakata part ɗin Mama da Afrah a hannunsa, ita kuma ta ɗau Amrah. Ko wanka ba ta yi ba ta kwanta rungume da yaran gam a jikinta kamar wanda za'a k'wace mata su..........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:43] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_










*2️⃣3️⃣*














Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
*Whatsapp OR* *Call 08066268951*
















..........Cikin ƴan mintuna suka ƙarasa gidan Ameen dake Lamido Cresent. Driver ya danna horn mai gadi Ya zo ya buɗe masa madaidaicin gate ɗin gidan, tun daga farfajiyar gidan zaka tabbatar da gidan ya haɗu gami da tsaruwa. Bayan ya yi parking Neehal ta fito Twins suka biyo bayanta, sallama suka yi da driver sannan ta nufi inda take hango ƙofar shiga ainihin cikin gidan, Mota ɗaya ta gani a harabar gidan, hakan yasa take tunanin da ƙyar in Ameen yana gidan. Hafsah tana ɗakinta a kwance ta ji ƙarar door beil, a tunaninta Ameen ne ya dawo daga masallaci hakan ya sata tashi da sauri ta fito ta sakko ƙasa ta buɗe ƙofar falon. Kamar a mafarki ta ga Neehal tsaye a bakin ƙofa, haɗe rai ta yi sosai kamar ba ta taɓa dariya ba ta shiga ƙarewa Neehal kallo, wadda ke sanye cikin doguwar riga pink colour, an mata ado da blue color, rigar ta ci guga har wani ɗaukar ido take, ta yi sosai kamar ka sace ta. Neehal ta danne zuciyarta tana murmushi ta ce "Sannu da gida Aunty Amarya." Ƙara haɗe rai Hafsat ta yi ta ce "Yawwa." Sannan ta juya ta koma ciki, Neehal ta shiga Falon bakinta ɗauke da Sallama Twins na biye da ita, suna ta murna sun zo unguwa. Kan kujera suka yi da gudu suka haye, Hafsah ta dube su kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa. Amrah ta dubi Hafsah ta ce "Ina kwana." Kafin ta gama rufe baki Afrah ma ta gaishe ta, ta amsa musu tana bin su da kallo. Neehal ta ƙaraso cikin falon ta zauna jikinta a sanyaye, a hankali ta ce "Ina yini Aunty." Hafsah kamar an mata dole ta ce "Lafiya." Daga haka ta wuce warta sama. Neehal ta bi ta da kallo duk murna da dokin zuwan da take ya koma ciki, gaba-d'aya ta ji dama ba ta zo ba, kamar ta tashi ta koma gida haka take ji, amma ta daure saboda idan ta koma gida ba ta san me zata cewa Mama ya dawo da ita ba. Falon ta shiga ƙarewa kallo, babu ƙarya falon ya haɗu, domin kuwa an narkawa Hafsah kaya. Komai dake cikin falon Dark and light purple colour ne. Neehal ta ɗauko wayarta daga cikin handbag ɗinta ta kira layin Haneefah ta sanar mata ta je gidan Ameen yau amma Haneefan ba ta ɗauka ba. Su Afrah kuwa tsalle_tsalle suka hau yi a falon, Neehal ta musu mgn su bari, ta nuna musu kusa da ita ta ce su dawo su zauna. Suka dawo suka zauna suna turo baki gaba. Har mintuna goma suka wuce Hafsah ba ta dawo gurinsu Neehal ba, kamar ma ba baƙi ta yi ba ta koma ta yi kwanciyarta. Afrah da ta gaji zama ta dubi Neehal ta ce "Aunty bari na kira Aunty'n data hau sama." Neehal ta ce "Ban aike ki

Please Login or Register in order to submit comment