Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta k'awaye da ƴan'uwa. Neehal kam sai murna take Abbanta ya ce ya kusa kawo mata Aunty.










A'isha Sunan Matar da Abba zai aura, Ƴar asalin garin Gombe ce, mahaifanta duka na can ne kuma Fulani ne. Ƴan'boko ne na bugawa a jarida, amma bokon bata hana su yin ilimin Addini ba, ga su ƴan'gayu kyawawa. Bautar ƙasa ce ta kawo ta Kano har Allah ya haɗa ta da Abba suka fara soyayya. Su A'isha su Huɗu ne a gurin iyayensu, Fateemah (Mama) ita ce babba sai Mahmud (Uncle Mahmud) sai A'isha (Aunty A'isha) sannan auta Halimatus Sadiya ( Aunty Sadiya.) An yi bikin Abba da Aunty A'isha lafiya an gama Lafiya, a garin Gombe a ka yi komai, sai kuma ranar D'aurin Aure da Ƴan Gabasawa suka zo aka yi wuni a gidan Umma, Neehal daɗi kamar ya kashe ta ana taro a gidansu, tana ta b'arna Umma ba ta hana ta ba, balle ta faɗa ko ta dake ta. Ƴan kawo Amarya sun zo sosai daga Gombe, kwanan su ɗaya suka koma, suma ƴan Gabasawan ranar suka tattafi. Tun a washegari Aunty A'isha ta fara hidima da Neehal, duk da Umma ta hanata amma ta ƙi. Bayan kwana biyu shak'uwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin Neehal da Aunty A'isha, dan Aunty A'isha ba ruwanta ita take mata komai, Neehal kam abun da yasa take son Aunty A'isha idan ta yi ta'adi bata faɗa kamar na Umma, Umma kuwa idan ta gaji da magana har make ta take. Da tafiya ta yi tafiya ma Neehal gurin Aunty'n ta koma da zama gaba-d'aya, Umma ta ce "Ala raka taki gona, ta huta da ciwon bakin bari_bari." Zaman lafiya ake tsakanin Umma da Aunty A'isha, Abba kuma yana yin adalci a zamansu, hakan yasa ba'ajin kansu kwata_kwata. Duk inda Aunty A'isha zata da Neehal take zuwa ko da kuwa tafiyar kwanaki za ta yi, hakan yasa danginta duk sun saba da Neehal tamkar jininsu haka suke kallonta.












*Bayan shekara biyu*










An yi bikin Uncle Umar k'anin Umma, inda ya tare da amaryarsa a unguwar Sabuwar gandu, bayan ya gama degree ɗinsa ya yi service Abba ya samar masa teaching a wata secondary school. Gidan da zai zauna ma Abban ne ya siya masa, Umma ta ce gaskiya ba zai karb'a ba abun ya yi yawa, dawainiyar ta yi yawa. Abba ya ce mata "Idan ba zai musu ba wa zai yi wa? Ko tana so ta nuna masa k'annenta ba nasa ba ne." Umma da ta ji ya faɗi haka sai ta haqura, amma fa ranar ya sha godiya da addu'oi a gurinta. Har yanzu da Neehal ta yi shekara biyar Umma ba ta kuma samun ciki ba, Aunty A'isha ma haka. Neehal kullum cikin mitar ita a haifa mata k'ani take, wataran har da kukanta, saboda Freinds ɗinta na makaranta duk yawanci suna da k'anne. A duk lokacin data faɗi haka Abba kan rarrashe ta ya ce ta yi addu'a Allah ya kawo. Neehal ta ƙara girma iyayi da surutu sun ƙaru.






Ranar wata Saturday da yamma ta dawo daga islamiyya, part ɗin Aunty'nta ta nufa direct tana k'wala mata kira, tana shiga falo ta yarda jakarta wadda Exercise book ne kawai a ciki sai pencil, ta cire ɗan mutsin hijabin jikinta shima ta yar, kanta babu d'ankwali saboda bata k'aunarshi ko kaɗan, fakakken gashin kanta da Aunty A'isha ta tsefa mata da safe ya bayyana, wanda ya sauka har ƙasan wuyanta. Har ta nufi bedroom ɗin Aunty ta tsaya turus saboda ganin wani matashi wanda ba zai wuce 17_18 years ba a zaune akan kujera yana latsa system ɗin Aunty A'isha. Neehal ta waro Ido dan bata taɓa ganinshi ba ta ce "Kaii! Waye kai, wa ya kawo ka gidanmu?" *AMEEN* Da bai masan da shigowar ta ba sai muryarta kawai ya ji ya mata banza, kasancewar sa muskili na bugawa a jarida. Neehal ta matso kusa da shi da ɗan ƙarfi ta ce "Kai baka ji ina maka magana." Ko d'agowa bai yi ba balle ya kulata, Neehal ta hau kan kujerar da yake ta kai bakinta dai_dai kunnansa da iya ƙarfinta ta ce "Kai ba ka ji ne, ko kai kurma ne!" Ameen ya d'ago a mugun fusace jin zata kashe masa dodon kunne ya wurga mata wani mugun kallo tare da hankad'e ta daga kusa da shi, Allah ya so kujerar da yake kai doguwa ce ta faɗa a kanta. Da sauri ta tashi zaune tana keɓe fuska tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba. Sauka ta yi daga kan kujerar ta yi bedroom ɗin Aunty da gudu tana kukan shagwab'ar da babu hawaye, Aunty A'isha ta tare ta da sauri tana faɗin "Me kuma ya faru Daughter?" Neehal ta keɓe baki ta ce "Wani ne a falo ya dake n......" Hango Mama da ta yi zaune a gefen gado yasa bata ƙarasa maganar ba ta nufe ta tare da d'ane mata cinya tana faɗin "Maman Abuja, yaushe kika zo?" Mama ta shafa kanta tana murmushi ta ce "D'azu na zo Daughter, wane ya kika ce ya dake ki?" Neehal ta turo baki ta ce "Ni ban san shi ba, wani yaro ne a falo." Aunty A'isha ta ce "Ba yaro ba ne Neehal Yayanki ne." Neehal ta ce "Aini ban da Yaya, kuma su Annur da Aslam duk suna da Yaya." Ta ƙarashe maganar kamar za ta yi kuka, Mama ta shafa kanta tana murmushi ta ce "Ke ma Daughter ga Yayanki nan na kawo miki kin ji? Daga yau kema kina da Yaya." Neehal ta gyaɗa mata kai tana murmushin jin daɗi an ce ga Yayanta. Mama ta dubi Aunty A'isha ta ce "Nikam A'isha da zaku bar mun Neehal ai da naji daɗi sosai wlh, ina son yarinya mace amma Allah bai bani ba." Aunty A'isha ta yi murmushi ta ce "Tab' Wannan kam Ubanta ba zai iya bayar da ita ba, dan tsoka ɗaya ce a miya." Mama ta ce "Ni shaidace kam akan k'aunar da Alhaji Muhammad yake mata." Aunty A'isha ta kama Neehal ta cire mata uniform ɗin jikinta ta saka mata best da dogon wando. Neehal ta ce "Aunty kin dafa mun macaroni na?" Aunty A'isha ta ce "Yana kitchen na dafa miki, bari na zubo miki." Bayan Aunty ta zubo mata macaronin da miya ta fice falo da shi a hannu, gurin Ameen ta nufa tana faɗin "Yayanah! Yayanah, Maman Abuja da Aunty sun je kai Yaya ne ko?" Cike da murna take maganar, Amma Ameen ya ƙi kulata kamar tana magana da dutse. Neehal ta matso kusa da shi sosai ta d'ebo macaronin da ya ji miya sosai a ƙaramin spoon ɗin da take cin abinci da shi ta kai bakinsa tana cewa "Yayanah ungo ka ci." Ai macaronin be kai ga shiga bakinsa ba ya zube a jikinsa, miyar jiki ta b'ata masa white T_shirt ɗin dake jikinsa............✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:45] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*2️⃣6️⃣*


















Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*














.........Cikin tsananin takaici ya d'ago yana jifan ta da wani irin kallo, ita ma kallon nashi take da kyawawan idanunta cikin shock ta turo small pink lips ɗinta gaba. Tsaki ya ja tare da ɗauke idonsa daga kanta, ajiye abincin hannunta ta yi a ƙasa ta kai hannunta jikinsa inda abincin ya zuba tana faɗin "Sorry Yayanah bari na goge maka." Shi dai be ce mata komai ba sai harara da yake ta banka mata, maimakon ta goge masa kamar yadda ta ce sai ma ƙara damula masa miyar take a inda babu, cikin k'ufula ya buge hannun nata tare da jan wani wawan tsaki ya tashi fuuu ya nufi ɗakin da Aunty A'isha ta sauke shi, shi fa shiyasa tun farko bai so Mama ta yo wannan tafiyar da shi ba, sai da ya ce mata ba zai biyo ta ba amma ta takura masa sai ya zo, gashi nan daga zuwan shi wata tsaregar yarinya ta fara ɓata masa rai. K'wafa ya yi lokacin da yake cire rigar jikinsa, ba dan ya kai zuciyarsa nesa ba da sai ya gaggaura wa yarinyar maruka, dan ta gane shi ba sa'an wasanta ba ne. Neehal kuwa ɗakin Aunty ta yi da gudu tana kuka, Mama kuwa tana ganin Neehal ta shigo da kuka ko da ba a faɗa mata ba tasan ita da Ameen ne, dan tasan halin kayanta sarai. Tashi ta yi ta fito falo, Aunty A'isha kuwa rarrashin Neehal ta shiga yi. Ba ta ganshi a falon ba hakan yasa ta bi shi har ɗakin da yake, ta tura ƙofar ta shiga da Sallama, trolley ɗinsa da ya ɗauko riga a ciki ya saka yake zipping, ya amsa mata sallamar cikin muskilar muryarsa. Mama fuska ɗaure ta ce "Ameen! Me yarinyar mutane ta maka kake dukanta? dan na saka ka zo sai ka huce a kanta?" Kamar ba zai yi magana ba sai kuma dai ya ce "Mum ni ban dake ta ba, kawai ta zo tana samun ciwon kai ne shine na ɗan maketa." Mama ta ce "Uhm lallai, ai gwara daka ɗan maketan, to tunda ka make ta kuwa kai zaka zo rarrashe ta." Tana gama faɗin haka ta juya ta fice, cize lips d'insa na ƙasa ya yi, ya tashi ya fito falo. Da Mama ta koma ɗaki ta tarar Neehal ta yi shiru tana bawa Aunty A'isha labarin dalilin kukanta. Aunty A'isha ta ce "To ki yi haquri kin ji, kuma ai ke kika ɓata masa kaya dole ya dake ki, ki je ki bashi haquri ki ce masa ba za ki kuma ba kin yi yarinyar kirki tah." Neehal ta gyaɗa mata kai ta fice daga ɗakin da saurinta. Aunty A'isha ta yi murmushi ta ce "Neehal rashin ji Ameen kuma babu haquri." Mama ta ce "Dama da abunsa, har yanzu fushi yake na taho da shi, na rasa irin wannan muskilanci na Ameen da baya son shiga cikin mutane, ya fi son in barshi a gida yay ta fama da system da takarda, kamar a kansa aka fara study." Aunty A'isha ta ce "Ameen halinsa sai shi kam." Neehal tana fita ta ɗan nutsu saboda tsoron Ameen da ya dirar mata a zuciya. A hankali ta ƙaraso kusa da shi cikin sanyi ta ce "Yayanah ka yi haquri ba zan kuma ba." Ameen ya sauke numfashi ya kamo hannunta ya ce "Shikenan na haqura, amma ki daina rashin ji da yiwa mutane ihu kin ji." Neehal ta gyaɗa masa kai, cikin murnar ya ce ya haqura ta ce "Yayanah za ka kai ni islamiyya gobe? Nima ince wa su Noor ga Yayanah." Ameen ya ɗan murmusa tare da gyaɗa mata kai. Ganin fa ya sake mata sai ta shiga yi masa hira tana bashi labarai kala_kala, shi dai kallon ɗan ƙaramin lips ɗinta da kyawawan idanunta kawai yake, a zuciyarsa yana mamakin surutu irin na Neehal sai ka ce Radio, ko ya ta motsa bakinta sai dimples ɗinta sun lotsa abun sha'awa. Kiran Sallar Magriba ne ya tada shi, tare suka fita da ita bayan ya yi alwala ita kuma ta yi part ɗin Ummanta. Washegari da safe Mama ta je part ɗin Umma suna hira, kamar ko wacce Sunday Aunty A'isha ta kamo Neehal ta fara yi mata kitso duk da zillewar da tai ta yi, saboda a rayuwarta ba ta k'aunar a taɓa mata kai ko kaɗan, kitso kuka, tsifa kuka, wankin kai kuka, haka Allah ya yi ta. Yauma gaba-d'aya ta cika part ɗin Aunty A'isha da ihun kukan kitson, Ameen yana daga ɗaki a kwance amma yana jiyo ihun nata, dan ware murya ta yi iya ƙarfinta, kamar wadda ake yankar naman jikinta. Da abun da ya ishe sa ne ya fito a fusace ya daka mata tsawa, ba shiri ta yi tsit sai tsiyayar hawaye kawai take, daga baya kuma sai bacci ma ya ɗauke ta. Haka rayuwa tay ta tafiya, Neehal tana girma kyawunta na ƙara fitowa, gata ƴar gatan Abbanta babu abunda ya rage da shi, Haka ma mahaifiyarta da Aunty'nta. Tana zuwa Gabasawa sosai musamman lokacin hutu, haka ma tana zuwa Abuja gidan Mama, amma tun daga time ɗin da Ameen suka zo gidansu ba ta ƙara ganin shi ba, saboda ya tafi Turkey karatu. Tun tana tambayar Mama shi harta manta da shi ma. Neehal yarinya ce mai ƙoƙari ga iyayi da son gayu, hakan yasa take da farin jini a ko'ina, duk inda ta shiga sai an k'aunace ta.








Tana da shekara takwas kakarta Inna mahaifiyar Umma ta rasu, mutuwar Inna ta girgiza mutane da yawa, Umma ta yi kuka ita da su Uncle Umar, Neehal ma duk yarinya ce a time ɗin Amma ta ci kuka ta gode Allah. Shekarta goma sha biyu ta zana commen entrance, a lokacin ne ta samu hutun makaranta mai tsayi kusan na 3 months, Gabasawa ta fara zuwa ta yi 1 week daga nan ta dawo gida ta je gidan Baffa ƙofar Nasarawa ta musu kwana uku, daga nan ta je gidan Uncle Umar ta yi kwana biyu, dan duk da Uncle Umar yana da ƴaƴa guda biyu amma Neehal ba ta jin daɗin zaman gidan saboda matarsa ba ta da kirki, shi ma Uncle Umar ɗin kuma dama ba ya wani sakar mata fuska, hakan yasa babu wata shak'uwa mai ƙarfi a tsakaninsu, sai masifar tsoransa ma da take ji. Daga nan Gombe ta wuce gidan Hajiya (Mahaifiyar su Aunty A'isha), time ɗin ba'ayi auren Aunty Sadiya ba, kuma ga Ameerah ƴar gidan Uncle Mahmud suna wasa tare, shi ya sa take jin daɗin zaman Gombe. Satinta ɗaya a can ta wuce inda tafi jin daɗin zamansa akan ko'ina wato Abuja gidan Mama. Daga cewa za ta yi 2 weeks sai gashi tar tafi wata ba ta dawo ba, su Abba da Umma da Aunty sun yi kewarta, kullum suna waya a wayar Mama, idan suka tambaye ta yaushe zata dawo sai ta ce musu ta kusa amma kuma ta ƙi dawowar. Ameen ya dawo Naija time ɗin, amma ba ya Abuja yana Lagos acan ya fara aiki, zuwa time ɗin ya zama cikakken saurayi mai cikar zati da kwarjini, miskilanci kuwa da tsare gida sai abun da ya yi gaba. Neehal tana jin daɗin zama a Abuja sosai, saboda yanda Mama da Daddy suke tarairayarta tare da nuna mata tsantsar k'auna tamkar su suka haife ta. Ita kam babu abun da za ta ce da dangin Aunty A'isha sai godiya da sam barka, ƴan'uwan kishiyar babarta ne amma har sun fi wasu ƴan'uwan Abbanta kula da ita, dan idan ta je Gabasawa a yanzu da babu ran Kakarta Yayar mahaifinta wadda take kira da Ummi ita kaɗai take kula da ita, sauran cousins ɗin Abbanta kuwa tsakaninta da su gaisuwa ce kawai, amma idan zata shekara a garin babu mai aiko mata da abun biyar, amma su komai na su sa kwashi jiki su tafi gurin Abbanta ya biya musu buƙatar su. Gwara ƴan'uwan Umma su ko ba su bata komai ba, amma akwai sakin fuska kuma suna janta a jiki. Ƴaƴan Baffa kuma wanda ya rik'i Ummanta da Abbanta suma dai ba wani jin daɗin su take ba, Ƴaƴansa duka maza ne guda huɗu, duk sun yi aure sun hayayyafa, wasu ma sun haifi wanda suka girme ta, Baffan ne dai ya nuna mata k'auna da ya raye, ba ya banbanta ta da sauran jikokinsa. (Da yake tun Neehal tana shekara goma Allah ya masa rasuwa.) Akwai wani cousin ɗin Abba da yake nan Kano Yaya ne a gurin Abban, mutumin yana da kirki ga ilimin Addini, kaf cousin ɗin Abba ya fi zumunci da Abba sosai, dan tamkar uwa ɗaya uba ɗaya haka suka ɗauki junansu. Mutumin yana son Neehal sosai, dan Abba yana yawan kai masa ita, to shi kuma matsalar matarsa ce makira kuma muguwa, zata nuna babu ya kai a zahiri, amma a cikin zuciyarta ba haka ba ne, da wani abu na sharri zai same ka sai ta fi kowa murna. Duk da haka dai suna Zumunci sosai da Umma da Aunty A'isha. Dangin Abba haushin yanda Neehal take da ƴan'uwan Aunty A'isha suke ji, a cewar su wai itama Umman kwad'ayi ne yasa ta bar Neehal take shige musu, dan ta ga suna da kuɗi. Ita kuwa Umma daɗin yanda Aunty A'isha da danginta suke son Neehal take ji, ga kuma tausayin Aunty A'ishan na rashin haihuwa da Allah bai bata ba, shi yasa ta bar mata Neehal ɗin, dan komai na Neehal yana hannun Aunty A'isha, dan in ba faɗa maka aka yi ba za ka ce ba Aunty A'isha ce ta haife ta ba, dan Umma tana mata kawaici sosai akan Neehal, dan ko abu ne za ta cewa Neehal je ki gurin Mamanki ta miki kaza, Mamanki kaza, Aunty'n Neehal ma take cewa Aunty A'isha. Abba kam sosai yake jin daɗin yanda Umman take wa Aunty A'isha, hankalinsa a kwance yake tun da kan matansa a haɗe yake. Ita kuwa Aunty A'isha sosai take girmama Umma, haka ma ƴan'uwanta, babu ruwansu da wai su masu kuɗi ne ƴan'boko, ita kuma Umma ƴar talakawa ce talakawan ma na ƙauye balle su wulak'anta ko suna mata gani_gani.








Ranar wata Laraba lokacin Neehal satin ta shida da kwanaki a gidan Mama, da yamma tana bitar haddadarta da zata bayar ranar Asabar, da yake tun bata fi sati da zuwa ba Mama ta nemi islamiyya ta saka ta, da ta je sai ta ɗora daga inda ta tsaya a haddarta ta gida. Gabanta ne ta ji ya yi wata mummunar fad'uwa, runtse idanta ta yi da sauri tana karanto Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, mike wa ta yi tsam ta nufi bedroom ɗin Mama. Bayan ta yi sallama ta shiga Mama ta amsa mata ta ƙara da faɗin. "Har kin gama haddar?" Jiki a sanyaye ta zauna a gefen Mama sannan ta ce "Eh." Mama ta ce "To ki je ki wanke panties ɗinki kar Magriba ta yi, dan nasan halinki da k'ailula sai ki yi awanni a wankin panties kawai." Ta ce "Toh." har ta miƙe sai kuma ta koma ta zauna ta ce "Mama yaushe zan koma gida?" Mama ta dube ta cikin mamaki ta ce "Gida kuma? Ke da kullum aka miki zancen komawar sai ki ce ba yanzu ba, amma yau kuma da kanki kike tambayar yaushe zaki koma." Shiru ta yi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, Mama ta cigaba da kallonta cikin nazartar ta, ta lura kamar wani abu na damunta dan wata nutsuwa ta ga ta yi, alhalin ta san Neehal da rawar kai da surutu, babu yanda za'ayi ta shigo bata ishe ta da hira ba, sai dai idan da wani dalili. Mama ta kira sunanta a hankali tare da kama hannunta ta ce "Neehal! Meke damunki? Ko baki da lafiya ne?" Girgiza mata kai ta yi alamun babu komai, Mama ta ƙara tambayarta da faɗin "Wani abun aka miki?" Nan ma girgiza kan ta ƙara yi, Mama ta ce "To me yasa kike son tafiya gida?" Neehal ta ce " Kawai ina son ganin Ummata da Abbana da Aunty." Mama ta sauke numfashi ta ce "To Shikenan, gobe Yayanki Ameen zai dawo, Ranar Saturday insha Allah sai na saka shi ya kai ki gida." Neehal ta gyaɗa mata kai cikin gamsuwa duk da bata san wanda Maman ta ambata mata a matsayin Yayanta ba. Tashi ta yi ta koma ɗakinta dan yin abun da Mama ta sata. Washegari ma haka ta tashi tana jin kanta wani iri, gabanta kuma bai dena fad'uwa, Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un kawai take maimaita wa kamar yadda Mama ta koyar da ita a duk lokacin da ji ko ta ga wani abun tashin hankali. Ranar Ameen ya dawo gidan da yamma, shima ba wani jima wa ze yi ba, Ranar Sunday da zai koma. Neehal ba su haɗu ba ranar saboda wuni ta yi a ɗaki a kwance, Mama ta mata tambayar duniya ta faɗa mata me yake damunta amma amsar ɗaya ce babu komai, ƙarshe ma sai ta saka kuka, sai da suka yi waya da Abbanta da Ummanta da daddare, ta ji suna lafiya k'alau sannan ta ɗan ji daɗi a ranta. Duk da Neehal a lokacin yarinya ce amma tana da hankali, shi yasa Mama take jin daɗin zama da ita.






A Kano kuwa bayan su Umma sun gama waya da Neehal, Umma ta dubi Aunty ta ce "Aunty'n Neehal kin ga ikon Allah, yau kuma Neehal ce take cewa tana so ta dawo gida." Aunty A'isha ta yi murmushi ta ce "Kin san halin Neehal sai ita, may be ta gaji da Abujan ne take so ta dawo." Umma ta ce "Hakane, amma da fa da kuka take baro Abujan." Abba ya ce "Ai kin san ba ta taɓa dadewa kamar wannan lokacin ba, shi ya sa." Umma ta gyaɗa kai tana faɗin "Sai dai haka, amma yanzu tana dawo wa ana mata abu zaku ji tana ita gidan Mamanta zata koma dan tafi sonta." Abba ya yi murmushi ya ce "Ai soyayyar Yaaya da Neehal sai Allah, Allah ya haɗa jininsu." Aunty A'isha ta ce "Ai ita Yaaya tana son yara ne, musamman mata, Allah kuma bai bata ba, gashi duk yarinyar data ɗauka a Family'nmu tana ɗan yin kwanaki sai su ce su gida za su koma, kin san yara ba sa son zaman gida shiru kuma gashi ba'a fita, daga makaranta sai gida, haka take komar da su gurin iyayensu." Umma ta ce "Allah sarki, Allah ya bata nata itama, ai ba'a fitar da rai da rabo a rayuwa." Abba ya ce "Allah ya kawo masu albarka." Suka amsa da Ameen gaba-d'aya. Ranar sun jima suna hira a falon Umma gwanin sha'awa, da yake ranar girkin Umma ne, sai Kusan 12pm Aunty A'isha ta koma part ɗinta. Misalin ƙarfe biyu da mintuna na dare, Abba yana zaune akan sallaya yana lazimi bayan ya idar da sallar Nafila, Umma kuma tana kan gado a kwance amma ba barci take ba, tun da suka baro falo ta kwanta amma bacci ya ƙi zuwar mata, sai wata irin faduwar gaba ce take riskarta akai_akai, addu'ar neman tsari daga sharri ta shiga karantawa a cikin zuciyarta, ana haka kawai suka ji an banko musu ƙofar ɗakin baram............✍️
















*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:46] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*












_By_
_Zeey Kumurya_












*2️⃣7️⃣*














Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*






















...........A firgice Umma ta yaye bargon data lullub'a tare da tashi zaune tana kallon bakin ƙofar k'irjinta na dukan tara_tara. Abba kuwa ko kaɗan bai nuna razana ba, kallon mutanen da suke shigo musu ɗakin kawai yake a ransa yana faɗin, "La'ilaha'illa'anta subhanaka'inni'kuntu'minazzlimuun." Su su biyar ne, suna sanye cikin bak'ak'en kaya, fuskokinsu a ɗaure da wani baƙin k'yalle, hannunsa ɗauke da bindigu. Sosai hantar cikin Umma ta kad'a, addu'ar da take yi a zuci bata san sanda ta fito fili ba. Abba kuwa kallonsu kawai yake amma bece musu komai ba kamar yadda suma ba su ce ba, sai ƙare wa ɗakin kallo kawai suke. Cikin wata irin tafiya ta ƙasaita ɗaya daga cikinsu ya ɗora ƙafarsa ɗaya akan bedside locker ya ɗan sunkuyo da fuskarsa dai-dai inda Abba yake. Cikin wata irin shakakkiyar murya ya ce "Na gaida Jarumi uban Jarumai." Sannan ya saki wata uwar dariya ya maida dubansa ga Umma ya ce "Ke! ki adana addu'arki zatai miki amfani a gaba dan yanzu baza ta hana mu yin abun da mukai niyya ba." Umma ta tab'e baki duk da yanayin tsoron da zuciyarta take ciki amma ta dake ta cigaba da karanto addu'arta, domin ta san ita ce kaɗai makaminta a wannan lokacin. Mutumin ya juyo ya yi wa ɗaya daga cikin yaransa inkiya da ido, cikin sauri yaron

Please Login or Register in order to submit comment