Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi. Ta miƙe tsaye tana jin kamar ana wujijjigata a cikin iska saboda juyawar da kanta yake mata. Lokaci ɗaya ta ji numfashinta ya tsaya cak, idanunta sun daina ganin komai sai duhu, a hankali ta yi baya luuu ta faɗi ƙasa babu alamar numfashi a jikinta..........✍️












*To masoya makaranta littafin Neehal, anan zamu dakata sai bayan Sallah idan mai kowa mai komai ya kai mu zamu cigaba da yardar Allah. Allah yasa muga wannan wata na Ramadan lafiya, Allah ya karb'i ibadun da zamu yi yasa muna cikin 'yantattun bayinsa da zai ƴanta a cikin wannan wata mai albarka. Allah ya bawa dukkan Musulmi lafiyar yin ibada, Amin ya Allah.🙏*












*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*7️⃣2️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*












..........Cikin dare Mama ta farka, Aunty Sadiya da idanunta biyu har lokacin ta tasa ta a gaba ta tashi da sauri ta kira likita, ya zo ya ƙara duba jikin Maman, Alhamdulillah an samu numfashinta ya daidaita yana fita da kyau, hakan yasa suka cire mata Oxygen ɗin suka yi mata allurar bacci dan ta ƙara samun relief. Sai a lokacin Aunty Sadiya ta ji ta samu nutsuwar zuciya ganin Maman tana numfashi normal. Da Asuba Mama ta kuma farkawa, alhamdulillah ta farka cikin nutsuwarta, kanta ne kawai ta ji yay mata nauyi da ƙirjinta da har yanzu take jin ciwo a cikin zuciyarta. Ta shiga bin inda take da kallo abubuwan da suka faru na dawo mata cikin kwanyarta. Ta runtse ido saboda wani ɗaci da ta ji ya ƙaru a cikin zuciyarta akan na da. Ƙoƙarin tashi zaune ta yi cikin ƙarfin hali da na zuciya duk da yanda take jin jikinta kamar ba nata ba. Jin motsinta Aunty Sadiya dake kan darduma ta juyo ta kalli gadon da take da sauri, miƙewa ta yi ta ƙarasa gaban gadon tana faɗin. "Sannu Yaya." Mama ta gyaɗa mata kai cikin dauriya tana ƙoƙarin tashi zaune, da sauri Aunty Sadiya ta taimaka mata ta tashi sannan ta saka mata pillow a bayanta. Kanta ta dafe da hannunta tana sassauke numfashi cikin muryar dake fita da ƙyar ta ce. "Sadiya ina Neehal da Ameen?" Aunty Sadiya ta sauke numfashi ta ce. "Suna gida, anjima kaɗan idan gari ya waye zasu zo." Ta gyaɗa mata kai sannan ta ce. "Suna lafiya dai ko?" Aunty Sadiya ta ce. "Lafiya k'alau, jiya har wajen ɗaya na dare Ameen yana nan, na san nan da anjima zaki gan shi ya dawo." Mama ta lumshe idonta ta ce. "Hajiya fa?" Aunty Sadiya ta ce. "Suna tare da Ya A'isha da Neehal." Mama bata kuma magana ba sai hannunta data ɗora a kan ƙirjinta. Aunty Sadiya ta ce. "Sannu, Ya jikin naki? Bari na Doctor ya ce mun in kin tashi na kira shi." Mama ta girgiza mata kai, sannan ta d'ago a hankali ta cire drip ɗin hannunta. A hankali ta ce. "Taimaka mun mu je toilet na yi alwala." Aunty Sadiya ta ce. "Haba Yaya baki da lafiya fa, ki bari idan likita ya duba ki sai ki je, na san yanzu ko tafiya baza ki iya yi ba." Mama ta girgiza kai ta ce. "Zan iya Sadiya, ki bari na fara yin Sallar tukunna." Aunty Sadiya bata kuma magana ba ta kama ta, ta sauko daga kan gadon ta raka ta toilet. Ita kanta Maman ta san ƙarfin hali ne kawai irin nata, amma ba ƙaramin jiri take ji ba, tafiyar ma duk da Aunty Sadiya ta riƙe ta amma jinta take kamar zata faɗi. A zaune ta yi sallolin dake kanta da ƙyar, bayan ta idar Aunty Sadiya ta taimaka mata ta koma kan gadon ta kwanta. Sai a lokacin ta fita ta kira likita ya zo ya ƙara dudduba jikin Maman tare da yi mata faɗan ta rage tunane_tunane. Ya cewa Aunty Sadiya ta bata magungunan da ya rubuta mata jiya idan an siyo, amma ta fara shan koda tea ne first. Bayan fitarsa Aunty Sadiya ta dubi Mama ta ce. "Bari na yiwa Ya A'isha waya ta kawo ruwan zafi da kayan tea, jiya ba ma cikin nutsuwarmu babu abun da muka taho da shi, magungunan ma Yaya Rufa'i (Mijin Aunty A'isha) ne ya siyo su da ya zo, ya ce ba zai yiyu ki farka kuma ba'a siyo ba." Mama ta jinjina mata kai kawai, amma bata jin zata iya saka wani abu a bakinta da sunan ci ko sha. Aunty Sadiya ta ce. "Dan Allah Yaya ki bar wannan tunanin, kin ji dai abun da Doctor ya ce, jininki ya hau sosai a cikin yini ɗaya kacal, inaga kuma kin ɗore da tunanin na kwanaki da yawa? Kuma kin san hakan already a matsayin ki na babbar Likita." Mama ta buɗe idonta da suka yi kamar na masu shaye_shaye saboda cuta ta ce. "Ta yaya Zuciyata zata bar tunani alhalin an riga an dasa mata baƙin ciki, Sadiya Muhammad fa, Yaya Tafida mijina ne a cikin ƙungiyar matsafa, me...." Sai numfashinta ya sark'e ta fara tari, hakan yasa ta kasa ƙarasa abun da take son faɗa. A ruɗe Aunty Sadiya ta ce. "Dan Allah Yaya ki bar wannan maganar, mu yanzu ta lafiyarki muke, kin ga karki ƙarawa kanki wani ciwon akan wanda yake damun ki already." Mama ta samu tarin ya lafa mata, cikin dashashshiyar murya ta ce. "Tunani ya zama dole Sadiya, dole in yi tunanin rayuwata ni da ɗana yanda zata kasance mana a gaba babu Muhammad, da kuma yanda baƙin fenti ya barwa rayuwarmu zai mana illa." Aunty Sadiya ta ce. "Insha Allahu zaku cigaba da rayuwarku tare da Yaya Tafida cikin kwanciyar hankali." Mama ta juyo idanunta a kanta ta ce. "Ta yaya? Ko kin manta abun da ya faɗa kafin su tafi na sharad'in ƙungiyar su?" Aunty Sadiya ta ce. "Ban manta ba, dan nima jiya da zullumun abun na kwana, amma kuma a yanzu na san babu abun da ya faru da shi, saboda da wani abu ya faru da tuni mun samu labari." Mama ta ce. "Idan ma ƴan ƙungiyar basu kashe shi ba ai hukuma baza ta taɓa barin shi ba, dole ne a yanke masa hukunci dai-dai da abun da suke aikatawa." Aunty Sadiya ta ce. "Ni kuma bana tunanin hakan, domin idan kika duba labarin da Yaya Tafida ya bamu gaba-d'aya ba'a cikin son ransa yake zaune a cikin wannan ƙungiyar ba, tun asali saka shi aka yi ba bisa yardar shi ba, hasalima tsaface shi akai yanda ba zai iya barin cikin ta ba." Mama ta ce. "Hmmmm, ke kika san wannan Sadiya, amma su hukuma basu san haka ba, kuma na shiga ban ɗauka ba bata fitar da b'arawo." Aunty Sadiya ta ce. "Haka ne, amma Insha Allahu Ubangiji zai fitar da shi, tunda ya ga zuciyarsa." Mama ta girgiza kanta kawai cikin takaici, tana jin dama Ubangiji ya karb'i ranta kafin zuwan wannan mummunar ranar. Aunty Sadiya ta cigaba da magana. "Yaya Fateemah a da na fiki takaici da baƙin cikin halin Yaya Tafida, har ji na yi na tsatse shi bana son ganin sa, amma a jiya tsanar ta juye zuwa tsantsar tausayi. Na tabbata duk halin damuwa da baƙin cikin da muke ciki ya fi mu, domin shi abun a kansa yake faruwa. Yaya Fateemah akwai ciwo ba ƙarami ba kana aikata abu a rayuwarka amma kuma zuciyarka bata son abun da kake aikatawar, irin wannan abun ba ƙaramin ciwo ne da shi a zuciyar ɗan Adam ba." Mama zata yi magana suka ga an turo ƙofar ɗakin an shigo. Aunty A'isha ce hannunta ɗauke da tea flaks da leda. Mama ta bita da kallon mamaki ganin har ta zo cikin mintuna ƙalilan bayan yi mata waya. Ta ƙaraso cikin ɗakin suka gaisa da Aunty Sadiya bayan ta ajiye kayan hannunta, sannan ta ƙarasa bakin gado ta zauna a wajen kan Mama, ta yi mata ya ya jiki bayan sun gaisa. Mama ta ce. "A'isha har kin fito kin zo a safiyar nan?" Aunty A'isha ta kalli Aunty Sadiya ta ce. "Dama ina cikin asibitin nan gurin Neehal." A razane Mama ta ce "Gurin Neehal kuma? Mai ya same ta?" Tana ƙoƙarin tashi ta yi maganar. Aunty A'isha ta taimaka mata ta tashi zaune sannan ta ce. "Ba wani abu ba ne, suma ta yi, lokacin muna ƙoƙarin kawo ki asibiti, shine muka haɗo ku duka muka kawo, amma yanzu jikin nata alhamdulillah da sauƙi, nama tashe ta ta yi Sallah, ina jin allurar da akai mata ce bata sake ta ba sai ta koma baccin, amma zuwa anjima ma muna saka ran su bata sallama." Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Allah sarki Daughter, Allah ya nuna mun ƙarshen wannan jarrabawar taki." Aunty A'isha ta ce. "Insha Allahu komai ya zo ƙarshe." Mama ta ce. "Allah yasa, ina Hajiya fa?" Aunty A'isha ta ce. "Tana can gurin Neehal, ina komawa zaki gan ta, ta zo, dan dake ta kwana a cikin ranta, ta tafi gida ma jiya ta dawo yau ƙi ta yi ta ce anan zata kwana." Jinjina kai kawai ta yi tare da lumshe idonta. Aunty A'isha bata jima ba ta tafi, ta ɗauki wata Nurse a waje suka tafi tare zata dawo tare da Hajiya. Hajiya data zo taga yanda Mama ta rame ta zabge sai ta saka kuka, da ƙyar Aunty Sadiya ta lallame ta ta bar kukan.








Ƙarfe bakwai saura na safe Ameen ya shigo ɗakin. Lokacin bacci ya fara fizgar Mama sakamakon Magungunanta da ta sha. Hajiya ta bar ɗakin ta koma wajen Neehal saboda Aunty A'isha data je gida dan ɗebo musu abubuwan buƙata na amfani. Aunty Sadiya ta amsa sallamar da ya yi tana kallon sa ganin yanda shima ya fita hayyacinsa a kwana ɗaya, kana ganin sa kaga wanda yake cikin damuwa. Ya gaishe ta, tare da tambayar ta jikin Mama. Kamar Maman ta ji sai ta buɗe idonta dake cike da bacci tana kallon sa. Ya ƙarasa bakin gadon ya zauna tare da kama hannunta yana tambayar ta jikin ta cikin tsananin kulawa. Ta amsa masa da sauƙi. Ya sauke ajiyar zuciya tare da damk'e hannunta a cikin nasa. Duk da baccin da Mama take ji amma haka ta daure ta tashi zaune tana ciccize leb'e, domin tana buƙatar tattaunawa da ɗanta a halin yanzu. Ta yi gyaran murya haɗe da ɗan tari ta ce. "Ameen, ka ji abun da Dad yake yi ko?" Taune lip ɗinsa ya yi da ƙarfi tare da sakin numfashi alamun maganar ta taɓa masa zuciya ba kaɗan ba. A hankali ya ce. "Na daɗe ina zargin shi Mum, a jiya kuma na tabbatar." Mama ta ce. "Amma mai yasa baka taɓa faɗa mun ba Ameen? Kuma ta yaya ka gane?" Ya ƙara taune lip ɗinsa sannan ya ce. "Na ɓoye miki ne saboda ban tabbatar ba, bana son na faɗi abun da ba shi ba ne. Ta yanda aka yi na gane kuwa tun lokacin da Miemerh ta zo gidana time ɗin da Hafsah ta samu miscarriage aka shigo gidan dan cutar da ita, a vantlation ɗin ɗakin da take na ga wani ƙaramin card, kuma na Daddy ne. A lokacin na shiga ruɗu ba kaɗan ba, amma duk da haka ko kusa ban yi tunanin shi ba ne, na yi tunanin dai wani wanda ya san shi ne ko a cikin abokansa. Sai dai daga baya dana zauna na yi dogon nazarin ta yanda aka shigo gidan an yi amfani da keys ɗin gidan ne, kuma Daddy ne kaɗai yake da su. Tun daga sannan na fara saka ido akan dukkan al'amuransa tare da zurfaffen bincike akan duk waɗanda yake mu'amala da su. A lokacin bana zargin sa, na fi zargin wanda yake mu'amala da su ne suke son cutar da shi ta hanyar Neehal. Sai dai duk yanda naso gano komai hakan ya gagara duk da bani kaɗai nake aikin ba, ni da wasu Freind's ɗina ne da suke aiki a hukumar SS ta ƙasa. Ba ƙaramin shiri ne da su Daddy ba na ɓoye dukkan sirrinsu, ta yanda ko kana bibiyar su baza ka iya gano su da wuri ba. Daga baya ne wata dabara ta zo mun, lokacin da za'a yi bikin Miemerh da Sadik sai na saka a dinga bibiyar mun al'amarin shi, cikin ikon Allah kuwa haƙana ya cimma ruwa, domin kuwa na yi nasarar gane ana bibiyar rayuwarsa musamman lokacin da aka shiga satin bikin. Da kaina na yi badda kama na dinga bibiyar masu bibiyar rayuwar tasa, ana i gobe za'a sace shi na yi nasarar sace na'urar ɗaya daga cikin masu bibiyar tasa. Lokacin da zai tafi gurin kamu ne, a gurin kamun suka b'uya a wani waje amma sun kakkasu kowa da kafar da ya samu ya buyan. Da wannan damar na shammaci ɗaya daga cikinsu na shak'a masa powder bacci, ko 2 minutes bai yi ba ya langwab'e. Na lalabo aljihunsa na ɗauki wannan na'ura dana lura kowa a cikinsu yana da ita. Da ita na gane dukkan shirinsu akan kashe Sadik ana i gobe d'aurin Auren sa, hankalina ya tashi ba kaɗan ba, daga nan muka ƙara duk'ufa akan bincikar al'amarin. Nina tura yarana suka ɗauke Sadik a lokacin da su kuma suke daf da zuwa kashe shi. A lokacin ne kuma na gane da hannun Daddy a cikin al'amarin, ta yanda ya gigice da ɓatan Sadik ɗin. Da kuma yanda a cikin week ɗin kullum sai ya fita da daddare, ba ya fita da Mota amma yana yin ƴar tafiya daga sai a zo an ɗauke shi a Mota, ina yin ƙoƙarin bin su a baya a daren a kullum idan aka ɗauke shi, amma tafiya kaɗan sai in ga sun ɓace mun bat in neme su in rasa. A jiya bayan na ɗauko Meimerh daga gurin nan na yi tracked Numbers ɗin Daddy, gaba-ɗaya location ɗin da suke nuna mun nesa kaɗan ne da gurin da na ɗauko Meimerh, hakan ya tabbatar mun da zargi na. Dad yana dawowa gida officer Gobir ya kira ni ya sanar mun kamar yadda na ce masa, ni kuma na kira hukumar SS nan da muke aikin tare na ce su je su tafi da shi su tuhume shi." Ya yi shiru na wasu sakanni yana sauke numfashi idonsa sun kada sun yi jajur. Cikin wata irin murya ya cigaba da magana. "Na yi takaici da baƙin cikin ganin ranar jiya a rayuwata, na ji dama Ubangiji ya ɗauki raina in huta da kunyar duniya a lokacin da halin Dad ya bayyana ga mutanen cikinta, na yi fata da roqon Ubangiji ya ɗauki rana babu a dadi, na yi fatan ace mafarki nake zan farka. Ban taɓa tunanin koda Dad zai yi wannan harkar za'a haɗa baki da shi a cutar da rayuwar Miemerh ba, tare da kisan Mutanen da basu ji ba, ba su gani ba. Na ji kamar in kashe kaina a lokacin da na yi realised Mahaifina matsafi ne, Mahaifina ɗan ƙungiyar asiri ne masu shan jinin......." Sai ya kasa ƙarasawa numfashinsa ya fara wata irin fizga, hawaye kawai Mama take yi tunda ya fara magana. Hannunta na rawa ta kwantar da kansa akan ƙafaɗarta saboda ganin abun da ta manta rabon da ta gani a tattare da shi, baza ma ita tuna ranar data ganin ba wato hawaye. Dama abun da take gudu kenan damuwar ɗanta, ta san duk duniya babu wanda zai kaishi baƙin ciki da takaicin halin Daddy, ko ita baza ta fi shi ba tunda ita mijinta ne, a duk lokacin data so zata iya sauya miji a rayuwarta, amma shi kuma fa? Mahaifinsa ne, abun da ba'a taɓa iya sauyawa a rayuwa, kuma paint ɗin abun da Daddy ya yi shi zai ta bibiya har ƴaƴa da jikokinsa. Ta ɗora hannunta akan lallausar sumar kansa tana shafawa cikin alamun rarrashi, ɗayan hannun kuma tana goge masa hawayen fuskarsa duk da itama hawayen take yi. Aunty Sadiya dake kallon su ta lumshe idonta cikin ƙoƙarin mayar da hawayen tausayinsu da ya cika mata ido.










Sun yi 5 minutes a haka sannan Mama ta d'aga kanshi daga jikinta, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya share mata hawayen fuskarta ita ma. Murmushin ƙarfin hali Mama ta yi tare da kissing hannun nasa. Cikin sanyin murya sosai ta ce. "Ka yi haquri Ameen, ƙaddara ce Ubangiji ya ɗora mana, shi ma Dad ba son ransa ba ne ƙaddararsa ce a haka. Ka rage wannan damuwar da nake gani a cikin idanunka, kar wani ciwon ya kama mun kai, bana son in rasa ku kai da Neehal, tunda na tabbatar na rasa Daddy har abada. Sannan ina maka godiya da jinjina akan yanda ka sadaukar da lokacin ka gami da lafiyarka akan kare rayuwar marainiyar Allah, Na gode sosai Allah ya biya ka da Aljannah." Ta ƙarashe zancen da shafar kuncinsa. Ya sauke numfashi tare da gyaɗa mata kai, ya motsa labbansa a hankali ya ce. "Amin." Aunty Sadiya ta dube shi ta ce. "Ameen ka rage jin zafin Daddy a cikin ranka, domin shi ma ba laifinsa ba ne hakan ta kasance da shi, hasalima jefa shi cikin wannan harkar ba bisa son ransa da yardarsa ba." Ameen ya kalle ta cikin alamun tambaya amma bai ce komai ba. Aunty Sadiya ta jinjina kai sannan ta bashi kaf labarin da Daddy ya ba su. Ya lumshe idonsa yana sakin ajiyar zuciya, ko ba komai ya ji daɗi da ya kasance mahaifinsa ba bisa son ransa ya faɗa wannan mummunar harkar ba, amma kuma hakan ba zai saka a ce ba shi da laifi ba shi ma. Ya buɗe idonsa ya ce. "Duk da haka Dad ba zai taɓa fita daga cikin wannan case ɗin ba, domin case ne babba ba ƙarami ba, kuma a idon mutane da hukuma duk ɗaya yake da sauran ƴan ƙungiyar, tunda duk abun da suke aikatawa shi ma yana yi kuma a cikinsu yake." Aunty Sadiya ta ce. "Jikina ya bani Insha Allahu zai fita, ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne." Mama ta ce. "Ameen ka kira Abokinka waɗanda suka tafi shi ka ji yana lafiya, saboda jiya kafin ya tafi ya ce ƴan ƙungiyar zasu iya kashe shi saboda labarin su da ya sanar mana." Aunty Sadiya ta yi ɗan murmushi a ranta ta ce. 'Ashe har yanzu tsohuwar zumar tana nan." Ameen bai yi musu ba ya ɗauki wayarsa ya kira abokin nasa kamar yadda Mama ta ce amma bai d'aga ba. Ya dube ta ya ce. "Daga nan can zan je, duk halin da ake ciki zan sanar muku." Mama ta ce. "Allah yasa mu ji Alkhairi." Suka amsa da Amin, sai dai shi Ameen ko kaɗan ba ya ji a ransa Daddy zai fita daga cikin wannan case ɗin. Har ya tashi zai tafi Mama ta tsayar da shi, ya koma ya zauna dan jin mai zata faɗa masa. Mama ta ce. "Ameen dama kana son Neehal tuntuni mai yasa baka taɓa sanar mun ba?" Ya yi shiru na wasu sakanni kansa a ƙasa sannan ya ce. "Na yi zaton baza ki amince mun ba, shi yasa na fara faɗawa Dad domin ya shawo mun kanki, shi kuma ya ce mun in bar maganar ba zai bani ita ba,ban kuma san dalilinsa na yi hakan ba, shi yasa kawai na haqura." Mama ta ce. "Me zai saka in ƙi amince maka Son? Komai kake so a duniyar nan idan ina da shi zan baka, da ka faɗa mun da abu ɗaya zai saka bazan baka ita ba, idan ita ta ce baka so." Ya yi shiru bai ce komai ba. Mama ta ce. "Tashi ka je, Allah ya yi maka albarka, ya jib'anci al'amuranka ya shirya ka." Ya yi murmushi cikin jin daɗin addu'arta ya ce. "Amin Mum, Allah ya ƙara sauƙi." Mama ta yi murmushi ta ce. "Ameen, ka biya ka duba Neehal ɗin kafin ka wuce." Ya amsa mata sannan suka yi sallama da Aunty Sadiya ta yi masa kwatancen inda aka kwantar da Neehal ya tafi, yana jin zuciyarsa na masa sanyi kasancewa da ya yi da Mama, sai ya ji wani kaso na cikin damuwarsa na yayewa. Har lokacin da ya je dakin Neehal bata tashi ba baccinta take. Suka gaisa da Hajiya ta shiga tambayar sa ko shi ma cutar yake ne duk ya yi wani iri. Bai bi takan ta ba ya ƙarasa bakin gadon da Neehal take ya tsaya yana kallon ta, zuciyarsa na k'issima masa abubuwa da yawa a kanta. Ya yi kusan 10 minutes sannan ya yiwa Hajiya sallama ya tafi.












Sai da sha ɗaya ta wuce sannan Neehal ta tashi daga baccin. Toilet kawai take je ta yi uzurinta ta kuskure baki ta fito ta cewa Aunty A'isha ta kai ta gurin Mama. Aunty A'isha ta ce ta bari a basu sallama mana, amma ta ƙi yarda harda kukanta, ganin haka yasa Aunty A'ishan ta raka ta. Suna shiga ɗakin ta tafi da gudu ta rungume Mama dake kwance idanunta a lumshe. Mama ta buɗe ido ta ce. "Daughter, Ya jikin naki?" Cikin sanyin murya tana duban yanda Maman ta zabge lokaci ɗaya ta ce. "Da sauqi Mama, ya naki?" Mama ta ce. "Alhamdulillah." Sai kuma ta fara kuka. Aunty Sadiya ta ce mata. "Kukan na mene ne kuma Neehal?" Bata yi magana ta cigaba da kukanta. Mama ta ce. "Me ya faru?" Cikin kuka ta ce. "Ki yi haquri Mama, na san ni ce sanadin wannan ciwon naki, saboda......." Cikin sauri Mama ta katse ta da faɗin. "Wanne irin shirme ne wannan Neehal, bana hana ki irin waɗannan maganganun ba, ciwo Ubangiji ne ke ɗora shi kuma shi ya ɗora mun. Ki bar kukan hakan kin ji ƴar albarka, ke ba lafiya karki ƙarawa kanki wani ciwon." Ta gyaɗa mata kai tana share hawayenta. A ranar aka sallami Neehal duk da dama already ta sallami kanta, sai magungunanta da zata cigaba da sha. Ranar haka aka dinga zuwa duba Mama, ƴan'uwa da abokan arzik'i ko ta ina, ana kuma yi musu murnar bayyanar Neehal. Da yawan mutane sun ɗauka damuwar ɓatan Neehal ce ta sakawa Mama ciwo har ta kwanta a asibiti. Kwanan Mama huɗu aka sallame ta daga asibitin, Alhamdulillahi jikin nata ya yi sauƙi, amma cikin zuciyarta cike take fal da damuwar abun da mijinta ya aikata da zullumin makomar rayuwarsa, duk da dai har yanzu abun da ya faɗa na sharad'in ƙungiyarsu akan kisan duk wanda ya fallasa sirrinsu har yanzu bai tabbata a kansa ba. Su Uncle Ahmad da Abba da Uncle Mahmud suna ta cuku_cuku akan case ɗin Daddy, amma abun ya ci tura ko damar ganin sa basu taɓa samun yi ba. Ameen kuwa ya yi busy suna ta aikin ganin sun kamo sauran ƴan ƙungiyarsu Daddy. Duk inda Daddy yake tunanin za'a ga wani daga cikin ƴan ƙungiyar an je duk ba'a same su ba, gaba-d'aya sun ɓace bat tamkar aljanu, da alama su ma suna can suna shirin ko ta kwana akan farautar su da suka fahimci ana yi. Babu wanda yasan halin da Daddy yake ciki sai ƴan'uwa na jiki_jiki da ya zama dole, ko ƴan dubiya sun tambaye shi idan an zo su Mama sukan san abun da zasu faɗa na rashin ganin shi da ba'a yi ba, wanda zai saka baza a yi tunanin ko da akwai wata matsalar ba.........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*7️⃣1️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*














*Barkanmu da Sallah, fatan an yi Sallah lafiya? Allah ya maimaita mana, Amin.*
















.........Aunty Sadiya ta yi kanta tana kiran sunanta tare da jijjigata. Neehal ta faɗa jikinta ta rungume ta tana faɗin. "Please Mama wake up, karki mutu ki bar

Please Login or Register in order to submit comment