Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko gurin kwalliyar ba mu tafi ba, ina tunanin fa ya zo da ya kira ni ban ɗauka ba shine ya tafi." Haneefah da hankalinta ke kan wayarta ta ce "To ke me yasa kika ƙi d'agawar?" Neehal ta ce "I think in ya ji ban d'aga ba zai kira ki shi yasa." Haneefah ba ta kuma cewa komai ba jin wayar Sadik ta shiga, har ta yi zaton ba zai d'aga ba sai kuma ta ji ya d'aga tare yin sallama. Ta kalli Neehal tare da amsa masa, ta ƙara da faɗin "Ya Sadik ina yini." Ya ce "Lafiya k'alau, Ya taro?" Haneefah ta ce "Alhamdulillah, ya na ga ban ganka a wurin bikin ba?" Sadik ya ce "Na zo ai na kira Neehal ba ta ɗauka ba, kawai na wuce." Haneefah ta ce "Ayya da ka kira ni ai, dan get pass ɗinka ma yana wurina." Sadik ya ce "Don't worry, Allah ya sanya Alkhairi." Haneefah ta ce "Ameen." Tana shirin ce masa ga Neehal ta ji ya katse wayar, Neehal dake kallon Haneefah ta ce "Me ya ce?" Haneefan ta ce "Ya zo ya tafi." Neehal cike da damuwa ta ce "Fushi ya yi da ni kenan? Shi yasa ma naita kiran shi ya ƙi pick." Ta ƙarashe zancen kamar zata yi kuka." Haneefan ta ce "Ki kuma kiran shi yanzu nasan zai d'aga, d'azun ma may be ba ya kusa da wayar ne." Neehal ta ce "Toh." Sai da ta fice daga hall ɗin saboda hayaniya sannan ta kira shi amma still bai ɗauka ba. Text ta tura masa kamar haka. _I'm sorry Ya Sadik, Please ka d'aga wayata_ Sadik ya yi murmushi lokacin da ya ga text ɗin Neehal, kafin ya kirata har wani kiran nata ya kuma shigowa, rejected ya yi sannan ya kira ta. Ta d'aga da sauri cikin shagwab'a Ta ce "Ya Sadik I'm sorry please, time ɗin da ka ki......" "Kar ki damu ba komai, ya taron?" Sadik ya katse ta da faɗin haka. Neehal ta turo baki gaba ta ce "Ai na yi fushi tunda baka dawo ba." Sadik ya ce "Haba 'yar ƙanwata a yi mun afuwa mana." Neehal ta ce "Um, um nidai sai ka zo zan haqura." Sadik ya ce "Shikenan ki ba ni 15 minutes gani nan zuwa." Neehal ta ce "Yawwa Yayanah sai ka zo." Sadik ya katse wayar yana murmushi, yana jin farin ciki a cikin zuciyarsa. Neehal tana yin taku kaɗan ta ga wasu maza biyu a gabanta a tsaye, ta canza hanya da sauri ta ga sun ƙara shan gabanta, ɓata fuska ta yi sosai tare da tsayawa ta ce "Lafiya?" Suka yi murmushi sannan wani a cikinsu ya ce "Lafiyar kenan ƴan'mata." Neehal ta ja ɗan ƙaramin tsaki ta wuce da sauri ta bar su a gurin. Tunda ta koma cikin hall ɗin ta ji kanta na mata ciwo, ta yi tunanin ko yunwa ce dan rabon ta da abinci tun safe hakan yasa ta nemo abinci ta ɗan ci, amma a banza kamar ma ƙara mata ciwon kan aka yi har wani jiri_jiri take ji, gaba-d'aya gurin bikin ya gundure ta, so take kawai ta ganta a gida. Gurin Aunty Sadiya ta je ta ce mata "Aunty dan Allah ara mun key ɗin Motarki idan da ita kika zo." Aunty Sadiya ta ce "Me za ki yi da shi?" Neehal ta ce "Wata Friend ɗina zan kai gida yanzu zan dawo." Aunty Sadiya ta ce "Ina?" Neehal ta ce "Anan cikin Narasawan suke." Aunty Sadiya ta ce "Ta bari a tashi mana, ai an kusa tashi sai a kaita." Neehal da take magana cikin dauriya saboda ciwon kai ta ce "Ana ta kiran a gida ana cewa ta dawo, a hakan ma sai an mata faɗa." Aunty Sadiya ta buɗe Pos ɗinta ta ɗauko key ɗin Motar ta bawa Neehal tana faɗin "Take it, amma ki yi sauri, ki kuma kula da hanya sosai kin ga dare ne." Neehal ta ce "Insha Allahu Aunty, thank you." Aunty Sadiya ta faɗa mata inda ta yi parking Motar ta fito ta nufi gurin.








A hankali take driving saboda ciwon kai gashi kuma dare ne, ta cikin layika take bi saboda ta yi saurin zuwa gida, abunka da G.R.A ko ina tsit babu mutane, amma akwai wadatuwar haske, tana shiga wani layi ta taka wani wawan burki da ƙarfin gaske cikin tsananin razana saboda abun da ta gani, ƙara dallare gabanta ta yi da hasken filitar Motar dan ta ƙara tabbatar da abun da idanunta suke gane mata..........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:40] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*








_By_
_Zeey Kumurya_










*1️⃣9️⃣*












...........Dafe kanta dake barazanar tarwatsewa ta yi saboda yanda yake sara mata, tattaro dukkan dauriyarta ta yi ta buɗe Motar ta fito ba tare data kashe ba, da fitilar wayarta ta haske Yaran mata guda biyu wanda suke ta kuka manne da juna, ga haushin da wasu karnuka suke yi wanda ga dukkan alamu shike ƙara firgita Yaran. Neehal addu'a take acikin ranta zuciyarta cike da tsoro, domin ba tasan yaran mutane ba ne ko aljanu, ƙura musu ido ta yi cike da tausayawa a ranta tana faɗin "Idan har Yaran nan mutane ne to duk wanda ya ajiye su anan bai da imani ko kaɗan, yanda duniyar nan ta lalace ace yara ƙanana a daren nan amma su kaɗai a bakin layi, layin ma irin wannan da babu mutane, ga su ƴaƴa mata, yanda duniyar nan ta lalace idan wani mugun ya ƙyalla ido ya gansu ai sai ya ɓata musu rayuwa.' Lokaci ɗaya Neehal ta nemi ciwon kan dake damunta ta rasa tunanika kala_kala ta shiga yi akan yaran, cike da faragaba ta kama ƙafar ɗaya daga cikin yaran ta duba, jin kamar ƙarar tahowar Mota cikin layin yasa ta yi addu'a ta kamo hannun yaran wanda ganin tana haska su yasa suka ƙara rukunkume junansu. Babu musu yaran suka biyo ta still suna cigaba da kuka, Neehal ta buɗe bayan Motar ta saka su sannan ta shiga gaba ta tada Motar ta nufi gida, har suka je gida yaran ba su dena kuka ba tare da kiran sunan *Daddy* a kofar part ɗin Mama ta yi parking Motar, ta fito da sauri ta fito da yaran suma da har yanzu ta gaza ce musu ko ƙala, ɗaukar ɗaya ta yi ta ja hannun ɗaya suka shige ciki, babu mutane sosai a gidan duk suna gurin dinner, sai tsoffi kawai da waɗanda ba a rasa ba. Neehal ta gaida mutanen data tarar a falo sannan ta wuce sama, babu wanda ya tambaye ta game da yaran tunda biki ake za su yi tunanin ko ƴaƴan wata ne.






Direct Neehal ɗakinta ta nufa ta sauke yarinyar dake hannunta wadda ta yi shiru tare da yin luf a jikinta, Neehal ta zauna a gefen gado tasa yaran duka a gabanta tana kallo, koda ba'a faɗa mata ba tasan yaran twins ne, saboda komai nasu da ya kasance iri ɗaya. Kyawawa ne kuma farare ga gashi an musu two babies, babu alamar talauci a jikin yaran, fatarsu luwai_luwai ga dukkan alamu daga gidan kuɗi suke, sai k'amshin turaren yara mai daɗi suke. Neehal ta fara tambayar kanta da faɗin "To wa ya ajiye su a waje a wannan daren? Ko dai fitowa suka yi suka kasa gane gida, ko kuma sato su aka yi? Gashi yaran da shigarsu tsaf cikin doguwar riga ƴan kanti masu kyau da tsada, ƙafafuwansu ne kawai babu takalmi ga....." "Aunty ki kai mu gurin Daddy." wadda da Neehal ta ɗauka da za su shigo ta katse ta da faɗin haka cikin maganarta ta yara. Neehal ta sauke numfashi tare da shafa kan yarinyar ta ce "Ina Daddy'n yake?" Ɗayar da hanyar yanzu bata daina kuka ba tace "Yana gida." Neehal ta janyo ta jikinta ta ce "Wa ya ajiye ku a waje?" Yarinyar ta ce "Wasu ne." Neehal ta ce "Ina mom ɗinku." Suka haɗa baki gurin faɗin "Daddy ya ce ta tafi ba zata dawo ba." Neehal ta yi shiru kawai tana kallon yaran, lokaci ɗaya suka cigaba da kuka suna kiran "Daddy Daddy, su dai akai su gurin Daddy'nsu." Neehal ta rungume su a jikinta tausayin yaran na ratsa dukkan jikinta, domin ta fahimci ba su da uwa saboda yanda suke kiran sunan Daddy kawai da kuma abun da suka ce mata. A hankali kuma ta d'ago su daga jikinta ta shiga goge musu hawayen fuskokinsu, tsabar kuka idanunsa sun yi jajir fuskarsu ma haka. Neehal cikin lallashi ta ce "Ku yi hakuri da safe zan kai ku gurin Daddy kun ji." Yaran suka d'aga mata kai suna sakin ajiyar zuciya. Neehal ta ce "Kun ci abinci?" Suka girgiza mata kai alamar a'a, Neehal ta shafi fuskokinsu ta ce "Bari na dafa muku indomie da tea, kuna ci ko?" Wadda tafi magana ta ce "Eh, Daddy Yana dafa mana every Morning." Neehal ta ce "Bari in dafa muku to." Ta mik'e ta cire ɗan kwallin dake kanta, tana cire ɗan kunne yarinyar ta ce "Aunty amarya ce ke.?" Neehal ta yi murmushi tare da d'aga mata kai, Ta lura yarinyar na da wayo da surutu saɓanin ɗayar data fahimci miskila ce. Neehal ta cire gown ɗin jikinta ta ɗauko wata riga mara nauyi ta nufi kitchen yaran na biye da ita a baya, ta lura duk a tsoro ce suke.






A can gurin biki kuwa Sadik ya ƙaraso ya kira wayar Neehal ba ta ɗauka ba, sai ya kira Haneefah ta zo ta shigar da shi, Haneefah ta kai shi suka gaisa da Mama da Ya Ameen ya musu Allah ya sanya Alkhairi. Haneefan tana ta neman Neehal amma bata ganta ba, ta kira wayarta kuma bata ɗauka ba, ta bawa Sadik hakuri ya ce babu komai. Sai wajen 11 aka tashi daga dinner, Aunty Sadiya tana ta neman Neehal itama dan ta bata car key ɗinta. Mama ta kira Haneefan ta ce mata "Ina Neehal ne? Ta zo mu wuce gida." Haneefan ta ce "Mama tun d'azu ban ganta ba, da Ya Sadik ma ya zo nay ta neman ta za su gaisa amma ban ganta ba." Mama ta ce "Kin kira wayarta kuma?" Haneefan ta ce "Eh, bata ɗauka ba." Mama ta yi shiru kawai tana sauke numfashi. Sai da za su shiga Mota Aunty Sadiya take faɗa mata yanda suka yi da Neehal, Mama tay ta faɗa tana cewa Aunty Sadiya "Me yasa zata bawa Neehal Motar a daren nan ta yi driving?" Aunty Sadiya ta ce "Mu yi fatan Allah yasa tana lafiya kawai." Ameen ma yana ta baza ido ko zai ga Neehal su tafi tare amma bai ganta ba.










Kallon yanda yaran suke cin abinci kawai Neehal cike da tausawa, a nutse suke ci amma kana gani ka san suna tattare da yunwa, sun ci sosai ɗaya ta fara kakarin amai, Neehal ta yunk'ura ta dauke ta da sauri ta yi toilet da ita, aikwa suna shiga ta fara kela amai, kafin ta gama itama ɗayar ta shigo tana yi, Neehal sai sannu take musu cike da tausayawa. Ta wanke musu baki bayan sun gama, ta cire musu rigunan jikinsu saboda sun ɓaci, ta dawo da su ɗaki suna ta sauke numfashi, Neehal ta lallaɓa su da ƙyar suka sha tea kaɗan, sannan ta kai su toilet ta musu wanka, dan duk sun yi kashi a cikin pampers ɗin jikinsu. Neehal tay ta mamakin yanda yara sun girma kamar waɗannan amma ake sa musu pampers, kuma da bakinsu za su iya cewa za su yi kashi. Komai na yaran iri ɗaya ne, babu wani abu daya bambanta a jikin su, harta da fingers ɗinsu iri ɗaya ne. Neehal ta naɗo su da ƙananun towels ɗinta, ta shafe su musu jiki da lotion sannan ta karkaɗe gado ta kwantar da su, har sun kwanta wadda tafi magana ta tashi kamar za ta yi kuka ta ce "Aunty ki kai mu gurin Daddy." Neehal ta matso ta janyo su jikinta sannan ta ce "Zan kai ku insha Allah, amma yanzu dare ya yi ku kwanta ku yi bacci da safe sai na kai ku." Yaran suka yi lamo a jikin Neehal ba su ƙara cewa komai ba, cikin 5 minutes ta ji saukar Numfashinsu alamun bacci ya ɗauke su, sai sakin ajiyar zuciya suke. Neehal ta raba su da jikinta a hankali tare da gyara musu kwanciya, ƙura musu ido ta yi zuciyarta cike da tunanika kala_kala. Jin hayaniyar mutane sun fara dawowa ta sauke ajiyar zuciya tare da tashi zaune, addu'a ta tofa musu sannan ta tashi ta ɗauko blanket ta lullub'e musu dukkan jiki da shi kansu ne kawai a waje. Toilet ta shiga, rigunan yaran ta fara wanke wa sannan ta goge make up ɗin fuskarta da tissue, tana cikin wanke fuskarta da sabulu Haneefan ta shigo ɗakin tana kiran sunanta. Turus Haneefan ta tsaya bayan ta ƙaraso tsakiyar ɗakin tana kallon yaran dake bacci akan gadon cikin mamaki, a hankali ta ƙarasa gadon ta zauna tana duban yara cike da sha'awa, a rayuwar Haneefan tana bala'in son twins, kan yaran ta shafa tana addu'ar Allah ya bata twins itama. Neehal ta fito daga toilet tana faɗin "Kiran me kike mun haka kamar sabuwar makauniya?" Haneefan ta harare ta tace "Makauniyar ce, ashe kina nan hankalinki kwance mu muna can namu a tashe." "Akan me?" Neehal ta tambaya tana shimfida Darduma domin yin Sallah. Shigowar Mama dakin ya hanata tada Sallar, Mama ta tsaya kawai tana bin ta da kallo. Neehal ta ce "Sannu da zuwa Mama." Rai a ɓace Mama ta ce mata "Kin kyauta Neehal Na gode." Neehal data san kwanan zancen ta ce "Ki yi haquri Mama, wallahi kaina ne ke ciwo kamar zan mutu shi yasa na dawo gida dan na huta." Mama ta ce "Shine ba za ki faɗa a dawo dake gidan ba sai kin yi ƙarya." Neehal ta yi ƙasa da kanta ta ce "I'm sorry ban san na wahalar da kowa ne." Mama ta tab'e baki ba ta ce komai ba, ta juya zata fita idanta ya sauka akan *twins* dake bacci akan gado. Ta dubi Haneefan wadda ta kasa ɗauke idanunta daga kansu ta ce "Haneefan Waɗannan Yaran fa ?" Haneefan ta ce "Nima anan na zo na same su Mama." Mama ta maida dubanta ga Neehal wadda gabanta ke fad'uwa dan bata san ya Mama zata karb'i zancen yara ba, ta ce "Ƴaƴan waye?" Neehal ta sauke numfashi ta ce "Mama long story ne." "Long story kuma?" Mama ta tambaya cikin rashin fahimta, Neehal ta gyaɗa mata kai tare da bata labarin yanda ta samu yaran. Ta ƙara da faɗin, "Na ji tsoro sosai a time ɗin da na gan su, har da zan wuce na barsu sai kuma na yi tunanin kar na barsu wani abun ya cutar da su, gashi sai kuka suke suna kiran Daddy." Mama ta yi shiru kawai tana kallon Neehal, tana son gano gaskiyar abun da Neehal ɗin ta faɗa, ta san Neehal bata mata ƙarya dan ko ta yi ma sai ta gano ta. Mama ta ce "Neehal kin san bana son ƙarya ki faɗa mun gaskiya yaran waye?" Neehal ta ce "Wallahi Mama abun da na faɗa miki shine gaskiya ki yarda mana." Mama ta ce "A ina kika gan su?" Neehal ta ce "Titin Ahmadu Bello ta cikin layika amma." Mama ta yi shiru tana tunani tare da kallon yaran cike da tausayawa, Haneefan ta ce "Allah sarki ko dai sato su aka yi Allah ya yi nufin kub'utar da su shine aka yarda da su a gurin." Mama ta sauke numfashi ta ce komai ma zai iya faruwa, ɗauko ɗaya Haneefan bari na ɗauki ɗaya mu kai su part ɗin Daddy, tunda nan akwai baƙin da za su kwana, kafin safiya mu san abun yi akan su." Haneefan ta ce "Toh." tare da lallaɓawa ta ɗauki ɗaya, yarinyar ta ɗan firgita cikin bacci ta ce "Daddy." Haneefan ta rungume ta ajikinta tana shafa bayanta. Mama ta ce "Babu kaya ajikinsu dama?" Neehal ta ce "Akwai, ya ɓaci da amai ne shine na wanke suna toilet." Mama ta ɗauki ɗayar itama suka fice daga ɗakin. Neehal ta bisu da kallo kafin ta tada Sallah, tana hamdala a ranta da Mama ta fuskanci lamarin Yaran cikin sauƙi.












*▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️*
*ABUJA*
*▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️*










Wata matashiyar budurwa ce ke kai kawo a cikin wani madaidaicin bedroom hannunta riƙe da waya ƙirar iPhone, yanayinta ya nuna tana cikin wani tashin hankali, wayar hannunta ce ta ɗau ruri wanda hakan yasa ta ɗan firgita tare duba wayar da sauri, jikinta har rawa yake ta d'aga wayar ta kara a kunne. A ɗan zafafe ta ce "Haba Gaye ya zan yi ta kiran ku amma ku ƙi d'aga mun waya, kun sa hankalina gaba-d'aya ya tashi ina tunanin ko an samu matsala ne a aikin." Gayen ya ƙyalƙyale da dariya cikin wata ƙatuwar muryarsa ta ƴan shaye_shaye ya ce "Haba haba, ki yi hanzarin tofar da yawunki domin ni bana taɓa yin aiki a samu matsala kuma bana son ana ambata mun ita a cikin aikina, yanzu nan yarana suka kira ni akan aiki ya kammala yanda ake so, yanzu ke kawai nake jira da cikon kuɗina." Wata doguwar ajiyar zuciya budurwa ta sauke ta sharce gumin dake goshinta ta ce "Baka da matsala Gaye indai kuɗi ne yanzu nan zaka ji alert har da ƙari ma akan wanda na ce zan baka." Gaye ya yi murmushi ya ce "Sai na jiki." Tare da kashe wayar. Wani tsalle budurwar ta yi ta faɗa kan gado tana ƙyalƙyala dariyar farin ciki da samun nasara. A fili ta fara faɗin "Ahmad dole yanzu hankalinka ya dawo gare ni tunda na rabaka da abun da yake hanaka kallon mata da sunan soyayya." Ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya tare latsa wayarta domin turawa Gaye kuɗinsa.










Had'ad'd'en asibiti ne wanda daga gani babu tambaya na masu hannu da shuni ne, wata mata ce tsaye a Emergency ward tana kaiwa da komo wa tare da karanto duk addu'ar da ta zo bakinta cikin kuka, kallo ɗaya za kai mata ka fuskanci tana cikin tashin hankali ba kaɗan ba. A gefe guda kuma wata yarinya ce zaune akan kujerun dake gurin wadda ba za ta wuce shekara 15 ba, tana rufzar kuka da dukkan ƙarfinta. Wani Babban Mutum ne ya ƙaraso gurin tare da wasu mutane biye a bayansa, matar na ganinsa ta ƙara fashewa da kuka tana faɗin, "Alhaji ba a gansu ba ko? Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, ya ALLAH ka bayyana mana yaran nan a raye ko a mace, Allah ka kare su da kariyarka a duk inda suke, Allah kasa suna hannu na gari, Allah ka dubi maraicinsu." Sai kuma ta fashe da kuka abun gwanin ban tausayi. Ta ƙarasa inda mutumin yake ta riƙe hannunsa tana faɗin "Alhaji dan Allah ka taimake ni kasa a nemo yaran nan, ko dan mummunan halin da mahaifinsu yake ciki sanadiyyar ɓatansu, dan Allah Alhaji karna rasa ɗanaa." Mutumin wanda ga dukkan alamu mijinta ne cikin lallami ya ce, "Police suna can suna iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin sun nemo yaran, kuma insha Allahu muna saran za a gansu, ki kwantar hankalinki kin ji." D'ago da jajayen idanunta da suka ci kuka suka koshi ta yi tana duban sa ta ce "Ta yaya hankalina zai kwanta Abbansu, alhalin ga yarona can kwance rai a hannun Allah, jikokina kuma an neme su an rasa ka faɗa mun ta yaya hankalina zai kwanta!" Ta ƙarashe maganar cikin tsananin kuka. Mutumin ya sauke numfashi cikin ƙoƙarin ɓoye tasa damuwar ya ce "Allah yana sane da mu Fatima, kuma insha Allahu shi zai kawo mana mafita, ke dai kawai ki dage da addu'a." Ta gyaɗa masa kai tare da sakin hannunsa ta zauna saboda jirin dake neman yar da ita, mutumin ya nufi gurin da yarinyar dake ta kuka take ya zauna tare da janyo ta jikinsa ya fara rarrashinta. Mutanen da suka zo tare da mutumin suka jinjina kai zuciyoyinsu cike da tausayin wannan ahali. Matar ta d'aga hannunta sama a fili take faɗin, "Ya Ubangiji na roƙe ka ka tashi kafaɗun *AHMAD* ɗina, ka bayyana masa yaransa da gaggawa a duk inda suke, Allah duk wanda yake da hannu a ɓatan yaran nan Allah ka tona asirinsa." Gaba-d'aya mutanen wurin suka amsa da "Amin ya Allah.".........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:40] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_












*2️⃣0️⃣*














..........Bayan wasu mintuna wani likita ya fito daga ɗakin da Ahmad yake yana goge fuskarsa da handkerchief, Matar ta riga kowa mik'ewa tana faɗin "Doctor, ya ya jikin nasa?" Likitan ya sauke numfashi yana dubanta ya ce "I'm sorry to say Hajiya, just pray." Bai jira amsarta ba ya juya ga Alhajin ya ce "Ka biyo ni office Alhaji." Matar tana sheshshek'a ta ce "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, likita me kake nufi? Har yanzu kenan Ahmad be farfaɗo ba?" Alhaji ya dube ta ya ce "Ki zauna ki yi addu'a kamar yadda Doctor ya ce, zan je inji bayaninsa." Matar ta gyaɗa kai tana salati ta koma ta zauna jagwab, yarinyarta ta matso kusa da ita tana sauke numfashi ta ce "Ummi, tunda har yanzu ba'a gansu ba ki kira gidan su Ammi ki sanar musu, ya kamata zuwa yanzu su ma su san halin da ake ciki." Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Tun d'azu naso kiran su Zahra, Abbanku ne ya hana ya ce kar a tayar musu da hankali a bari aga abun da hali zai yi, amma yanzu tunda ba a gansu bari na kira Yaseer na faɗa masa, kin san Ammin tana da hawan jini yanzu in ta ji sai ya tashi, amma shi Yaseer ɗin ya san ta yanda zai faɗa mata hankalinta ba zai tashi ba sosai." Zahra ta gyaɗa mata kai kawai cikin sanyin jiki.












▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️
*KANO*
▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️












Jiki a sanyaye su Mama suka kwantar da yaran a wani ɗaki dake part ɗin Daddy, sosai al'amarin yaran ya girgiza kwanyar Mama, tafi 5 minutes tana kallon yaran kafin ta sauke numfashi ta juya ta fita bayan ta lullub'a musu bargo, Haneefah dama suna kwantar da yaran ta fice. A falo suka ci karo da Aunty Sadiya da Aunty A'isha. Aunty Sadiya ta dubi Mama ta ce "Ya Fatima kin ga Neehal ɗin?" Mama ta ce "Eh, ashe gida ta dawo wai kanta na ciwo." Aunty A'isha ta ce "Ayya, hayaniya ce Allah ya sauwaaqe." Aunty Sadiya dake kallon Mama ta ce "Lafiya kuwa na ganki wani iri?" Mama ta sauke numfashi ta ce "Ina fa lafiya Sadiya." A rude Aunty Sadiya ta ce "Me ya faru?" Mama ta ce "Ku zauna maganar ba ta tsaye ba ce." Sosai Aunty A'isha da Aunty Sadiya suka jimanta al'amarin, zargika kala_kala suka yi akan yarda yaran da akay, Mama ta ce "Sanin gaibu sai Allah." Ɗakin da yaran suke suka shiga suka gan su, Amma Mama ta roƙe su a kan kar su sanar da kowa hatta da Hajiya kuwa. Bayan Neehal ta idar da Sallah ta ɗauko wayarta ta kira Sadik, rejected yay kamar ko da yaushe sannan ya kira ta. Tana d'agawa ta ce "I'm sorry Ya Sadik Please." Sadik ya kwaikwayi yanda take magana ya ce "Um um, ba zan yi sorry'n ba." Neehal ta yi murmushi me sauti jin yanda ya yi ta ce "Haba Yayanah na kaina, idan baka hakura ba kuka fa zan yi." Ta ƙarashe maganar cikin shagwab'a. Sadik ya sauke numfashi ya ce "Shikenan komai ya wuce dear, amma ina kika shiga?" Neehal ta ce "Kaina ke ciwo shi yasa." Cikin tausayawa Sadik ya ce "Subhallah, sannu Allah ya sauqaqe, amma dai kin sha magani ko?" Neehal ta ce "Yanzu dai zan sha." Sun taɓa hira kaɗan suka yi sallama, saboda ta samu ta sha magani ta kwanta ta huta.






Hameedah ce zaune ta ɗora kanta akan cinyar mahaifiyarta tana kuka ƙasa_ƙasa, ganin tabbas ta rasa Ameen tunda gobe zai angonce da wata. Mumy wadda ta gaji da rarrashi tun a

Please Login or Register in order to submit comment