Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

to" Dad ya ce "Yawwa ɗiyar albarka" Neehal ba ta wani jima ba, ta dawo ɗauke da vowl wanda ta yayyanka fruits d'in a ciki, ta ajiye akan Centre table ɗin dake gaban Dad, Dad yana dubanta da murmushi a kan fuskarsa ya ce "Thank you Amarya" Neehal ta rufe fuskarta cikin jin kunya. Tare su ka sha fruits d'in da Dad, ya na ta zolayarta da yake Dad mutum ne mai barkwanci, hirar su suke irin ta ɗa da mahaifin da ya ja ƴaƴansa a jiki, har sai da Mama ta dawo sannan Neehal ta koma part ɗinsu. Sau da ta biya ɗakin Hajiya ta mata sai da safe sannan ta wuce nata ɗakin, wanka ta fara yi sannan ta ɗauki wayoyinta ta kwanta akan lumtsumeman gadonta bayan ta kashe light d'in ɗakin, data ta kunna ta shiga yanar gizo, sai wajen 1pm ta kashe datar bayan ta gama shan hira da masoyinta Anwar da besty'nta Haneefah da sauran freinds ɗinta da 'yan'uwa da abokan aiki. Misalin ƙarfe uku da ƴan mintuna na daren Mama ta kirata, ɗagawa ta yi muryarta cike da bacci ta yi sallama, Mama ta amsa mata tare da faɗin "Ki tashi ki yi Sallah toh" Neehal kamar za ta yi kuka ta ce "Mama dan Allah ki bar ni na yi bacci na, gobe fa da safe za ni aiki, kuma ban daɗe da kwanciya ba" Mama ta ce "Ni na hanaki kwanciya da wuri, ai kin san da sallar ki ka tsaya chat" Neehal ta ce "Ba fa chat na yi ba, karatu na yi, kin san 2 weeks ya rage mu fara exam" Mama ta ce "Na ji, ki tashi ki yi Sallar dai, ko raka'a biyu ce, kin ga auren ki ya kusa, ki roƙi Allah ya kawar muku da fitintunu a zama auranku, yanda auren yanzu ya zama na zamani, dole sai mun dage da addu'a" Neehal ta ce "To Mama" Mama ta ce "Yawwa my daughter, ki yi addu'a sosai, sharrin mutum da Aljan Allah ya kare mu" Neehal ta ce "Ameen, bye" Mama ta katse wayar, Neehal ta yunk'ura ta tashi ta shiga toilet dan d'auro alwala.






Washegari, bayan ta idar da sallar asuba ta yi karatun Alkur'ani mai girma izifi biyu, sannan ta ɗauko materials ɗinta na school ta ɗan dudduba, gari na fara haske ta tashi ta gyara ɗakinta, sannan ta faɗa toilet ta yi wanka. 7:30 ta sakko ƙasa cikin shirinta na zuwa gurin aiki, ta na sanye da hijabinta wanda ya zo mata har ƙasa, Mama ta na kitchen ta na haɗa break fast, ƙarasawa kitchen d'in ta yi ta ce "Morning Mum" Mama ta ce "Morning dear, har kin fito" Neehal ta ce "Ehh, kin san yau Sunday za mu haɗa labaran week d'in gabad'aya dole sai na je da wuri" Mama ta ce "Amma dai ki tsaya ki yi break" Neehal ta ce "Idan na je can zan ci, bari na ɗiba cake" Mama ta ce "A'a ki dai tsaya ki ci abincin ko kaɗanne nasan halinki ba ci za ki yi ba" Neehal ba ta musa ba, ta haɗa tea a ƙaramin cup ta d'ebi soyayyayen phatatoe d'in da Mama ta soya kaɗan, ta koma falo ta ci. Kayan ta dawo kitchen ta ajiye bayan ta gama ci, ta yi wa Mama sallama, Maman ta mata addu'a ta fice. Sai da ta biya part d'in Dad sharp_sharp ta gaishesa sannan ta fito ta tafi........✍️










*Ku cigaba da haƙuri, ina yin garau za ku na samun Read more da yawa insha Allah.*














*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: *⚡NEEHAL ⚡*








_By_
_Zeey Kumurya_










*0️⃣2️⃣*










.............A hankali ta tura ƙofar falonsa, ta yi sa'a kuwa ƙofar a buɗe ya barta, shiga ta yi gabanta na ɗan fad'uwa saboda sanin halin Yayannata da kuma tsoronsa da take masifar ji. Ya na zaune a kan kujera 2 seater ya jingina bayansa a jikin kujera idanunshi a lumshe hannunshi dafe da kanshi, Neehal ta ƙaraso kusa da shi a hankali idanunta k'ur a kansa, gabantane ya fadi ganin irin ramar da ya yi, dan ɗazu kwata_kwata bata lura ba, a ɗan ruɗe ta ce "Yaya!" Bai motsa ba balle ya nuna ya ji ta. Ba ta damu ba ta zauna a kusa dashi kamar za ta yi kuka ta kuma faɗin "Yayah ba ka da lafiya ne?" Shiru yay mata kamar ba zai amsa ba, sai kuma can ya d'ago da kansa ya na ɗan sauke numfashi ya dubeta, kallon ta ya yi na 3 seconds kafin ya daukey idonshi daga kanta tare da girgiza mata kai alamar a'a. Idanunta na kawo ruwa ta ce "Gashinan ka rame, Please yaya mai ke damunka?" Haɗe rai ya yi sosai har sai da gabanta ya fadi amma bai ce komai ba, hawaye ne ya fara zuba daga idanunta wanda ta kasa tantance na banzan da ya yi da ita ne ko kuma na ganin shi cikin damuwa da ta yi?" Ta na hawayen ta ce "Yay......" cikin tsawa ya dubeta ya ce "Kin san bana son takura ko? tashi ki fita" turo ɗan karamin bakinta ta yi gaba ta na share hawayen fuskarta ta tashi ta fita, Bin ta ya yi da kallo ta ƙasan ido har ta fice, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya maida idanunshi ya lumshe zuciyarsa na masa ɗaci.




Haneefah ta dubi Neehal da ta tsaya jiki a sanyaye tun da ta dawo kitchen d'in ta ce "Besty me ya faru na ganki haka?" Neehal ta sauke ajiyar zuciya idanunta na cikowa da k'walla ta ce "Yaya ne" Haneefah ta ci gaba da juya miyar da take dan in da sabo ya ci ace ta saba da rashin shirin Neehal da Yayannata, kamar ba za ta kula da zancen ba sai kuma dai ta ce "Me yay miki kuma yau" Neehal cikin raunananniyar murya ta ce "Besty ba ki ga yanda Yaya ya rame ba, amma na tambayeshi meke damunshi shine ya ce mun bakomai, na roƙe shi ya faɗamun shine ya koro ni" Ta ƙarashe zancen hawaye na zubo mata akan kuncinta, Haneefah ta juyo ta fuskance ta, ta ce "Ni fa daɗina dake saurin kuka, yanzu mene abun kuka anan?" Neehal ta ce "Ba za ki gane ba ne Besty, amma ba ki ji yanda nake ji araina ba, ganin shi cikin damuwa da na yi" Haneefah ta ce "Tom shikenan ki yi masa addu'a, koma me ya ke damunsa Allah ya yaye masa ya kuma bashi lafiya" Neehal ta ce "Ameen" Haneefah ta ce "Yawwa ko ke fa, to share hawayennaki 'yar Mama, kin san fa ke amarya ce ba na son na ga kina damuwa, kar mu kaiwa ya Anwar ke a rame" Neehal ta yi Murmushin yaƙe, saboda fad'uwar da gabanta ya yi, ta rasa me ya sa a duk lokacin da a ka yi zancen bikinta sai ta ji fad'uwar gaba, daurewa kawai ta ke yi, fita ta yi daga kitchen d'in domin ta je ta shirya, ɗakin Mama ta shiga ta tarar da Mama zaune ta na karatun Alkur'ani mai girma, zama ta yi har Maman ta kai ƙarshen aya, Mama ta d'ago ta dube ta, ta ce "Kin gama girkinne?" Girgiza mata kai Neehal ta yi, Mama ta ce "Toh menene kuma na ganki haka?" Cikin damuwa Neehal ta ce "Mama Yaya ne na ga kamar bashi da Lafiya, kuma na tambayesa me ke damunsa ya ƙi faɗamun sai ma koroni ya yi" Mama ta ce "To ke halin Ameen ɗinne ba ki sani ba ko me? Kin san ba faɗa miki zai yi ba, wa ya aike ki?" Neehal ta b'ata fuska ta ce "To ba Yayana ba ne?" Mama ta ce "Kin ga Yayanki ai, Ni tashi ki je ki ƙarasa mun girki kar time ya k'ure ki bar Ni da shi" Neehal ta tashi tana turo baki gaba ta fita. Bedroom ɗinta ta shiga, rage kayan jikinta ta yi ta shiga toilet dan yin wanka.




K'arfe uku dan wasu mintuna Neehal ta gama shirinta cikin wata rantsatstsiyar doguwar rigar abaya maroon colour, wadda ta ji kwalliyar stones milk colour, rolling mayafin abayar ta yi, ta yi kyau sosai duk da ba wata kwalliya ta yi ba, daddad'an turarenta mai daɗin ƙamshi ta feshe jikinta da shi, zoben gold ta zira a ɗanyatsanta na tsakiyar hannun damanta, na kusa da shi kuma ta zira zoben azurfa mai kyan gaske, yatsun hannun hagunta suma fashion ɗin zobuna masu kyau ta sa musu guda biyu, tsadadden agogon hannu milk colour ta zira tare da abun hannu mai kyau, flate shoe mai kyau milk colour ta zira, wayoyinta dake kan mudubi ta kwasa ta zuba a cikin handbag ɗinta mai kyau itama milk colour. Light din ɗakin ta kashe ta janyo ƙofar ta fito ta sauko ƙasa. Haneefah ta kammala girkin cus_cus ɗin da Neehal ta ɗora, ta na zaune a falo Neehal ta sakko, Haneefah ta bita da ido tana murmushi ta ce "Kaga amaryar ya Anwar, kin yi kyau sosai" Neehal ta yi murmushi ta ce "Har na kai ki yin kyan?" Haneefah ta ce "Wane Ni, ke fa harkin fara irin shining ɗinnan na amare" Neehal ba ta kulata ba, ta nufi kitchen, Haneefah ta tashi ta koma kusa da Hajiya ta fara tashinta.




Hajiya ta buɗe ido a hankali tana salati, tashi zaune ta yi tana mutsitstsike ido, duban Haneefah da take dariya ƙasa_ƙasa ta yi ta ce "Ai dama nasan sai ke, dan Neehal dai ba za ta yi mun wannan muguntar ba, To ke da Allah, ina cikin baccina mai daɗi kin katsemun ko uban me zan miki idanna tashin Oho?" Haneefah ta tsuke fuska ta ce "Hajiya dan na tashe ki ki ci abinci ki yi Sallah, shine za ki ce mugunta, gani na yi ke bakya wasa da Sallah kuma lokacinta ya kusa" Hajiya ta ce "To yi haƙuri ai ban sa ni ba, yaushe ki ka zo gidan? ya kuma Maryam ɗin?" Haneefah ta ce ɗazu na zo ai, na tarar ki na ta sharar baccinki, Mommy kuma tananan Lafiya k'lu" sakkowar Mama ƙasa ya katse musu maganar da suke, Haneefah ta mik'e ta je ta yi hugging Mama. Mama na murmushi ta ce "Welcome, yaushe ki ka zo?" Haneefah ta ce "Na ɗan jima" Mama ta ce " sannunki Ya Barrister?" Haneefah ta ce "Tananan klu" Mama ta kalli kofar kitchen ta ce "Neehal ba ta gama girkin ba ne, ta yi ta fito ku shirya ku tafi kar ku yi late" kafin haneefah ta ce wani abu Neehal ta fito daga kitchen d'in, Mama ta bita da kallo fuskarta ɗauke da mamakin ganin ta a shirye, Neehal ta ƙaraso kusa da su ta ce "Mama na gama abincin" Mama ta mata wani kallo ta ce "To sannu" Sannan ta juya ta kalli Haneefah ta ce "Kin taya ta girki ko?" Haneefah ta sunkuyar da kanta ƙasa ba ta ce komai ba, Mama ta ce "Ba magana nake miki ba Haneefah?" Haneefah ta ce "Mama ƙarasa mata miya kawai na yi, na ce ta je ta shirya dan mu yi sauri mu tafi" Mama ta ce "Ba na ce ko sauke abu ki dena taya ta da shi ba, ki barta ta dinga yin komai da kanta" Haneefah ta gyad'awa Mama kai. Neehal ta ɗan turo baki gaba ta wuce za ta ɗauki jakarta, Mama ta ce "Kun ci abincinne?" Haneefah ta ce "Na k'oshi Mama, ina gama cin abinci na fito, sai dai idan mun dawo" Mama ta dubi Neehal ta ce "Ke fa?" Neehal ta ce "Ni ma haka" Mama ta ce tunda kin cika cikinki da kayan zak'i ba, ki wuce kitchen ki d'ebo abinci ki ci kar na ɓata miki rai" Neehal ta ɓata fuska, amma ba ta da zaɓi sai bin umarnin Maman, kitchen d'in ta koma ta d'ebo abinci kaɗan a plate ta dawo falon ta zauna a ƙasa ta fara ci kamar ba ta so, ta na ci ta na yamutsa fuska, kaɗan ta ci Mama ta ce ta tashi su tafi, tun da ɓata musu lokaci kawai take ba cin abincin za tay ba. Neehal na duban Mama da Hajiya ta ce "Sai mun dawo" "Mama ta ce ƙarfe nawa za ku dawo?" Neehal ta ce "8" Mama ta ce "8 ina Hospital" Neehal ta ce "Mama yau fa Saturday me za ki yi a Hospital kuma?" Mama ta ce "Akwai patients d'in da zan duba ne" Neehal ta ce "Toh, idan mun tashi zan biya Zoo road na siyo popcorn a'one" Mama ta ce "In ma a 10 ne ba damuwata ba ce, kin san Yayanki na gida ai, 8: 15 in ba ki dawo ba, ke da shi ne" Neehal ta ɓata fuska ta yi gaba, Haneefah ta yi wa su Mama sallama, Mama ta musu addu'a suka tafi, Hajiya na faɗin "Wai yaushe zaku kai ni gidan talabijin d'innan naku ne nima a hasko Ni a ciki?" Suna jin ta suka mata shiru. Parking space suka nufa suka shiga Mota Driver'n Neehal ya ja su zuwa *ASTV* fitaccen gidan TV'n da ya shahara a nan ƙasarmu Nigeria dama nahiyar Africa baki ɗaya.






Ƙarfe 8 kamar yadda Neehal ta ce suka tashi daga gurin aiki, bayan sun gama gudanar da shirin *'Yancin mata* wanda suke yinsa duk Ranar Asabar da misalin ƙarfe 7 na dare zuwa 8. Su na gamawa suka yi sallama da ma'aikatan gidan TV suka nufo gida, Neehal ta yi_ta yi Haneefah ta bita ta gidansu kamar yadda take yi wani lokacin amma ta ce ita gida za ta wuce, sai da suka biya suka fara sauke ta sannan suka wuce, da yake duk ba su da nisa, gabad'aya a cikin Nasarawa G.R.A suke har ASTV'n. Driver na parking Neehal ta fito, ganin Motar Dad a gurin alamun ya dawo ta ji daɗi a ranta, dama yau gabad'aya ta yi missing ɗinsa. Part d'in Mama ta nufa, ta shiga falon bakinta ɗauke da sallama, gabantane ya faɗi ganin Ameen zaune shi kaɗai a falon ya na latsa waya..........✍️










*Ku yi haƙuri da wannan, har yanzu jikinnawa ne sai addu'a, dan kar ku ji shiru ma yasa na yi wannan ɗin, insha Allah next page za mu shiga cikin gundarin labarin, Nagode da addu'oinku Masoya.🙏❤️*








*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_
[10/03, 08:30] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*








_By_
_Zeey Kumurya_








*0️⃣5️⃣*










.............Tab'e ɗan ƙaramin bakinsa ya yi tare da ɗauke kansa daga inda suke. Neehal ta janye hannunta ta na sauke Numfashi ba ta ce komai ba, saboda abun ya mata wani banbarakwai, duk da Anwar ko hannunta bai taɓa riƙe wa ba amma sai ta ji wata irin kunyarsa ta rufe ta. A hankali ta daure ta ce "Nagode sosai Ya Anwar" Anwar ya yi murmushi ya ce "Kin ga yanda hannunki ya yi wa zoben kyau kuwa?" Neehal ta yi ɗan murmushi idanunta na kan hannunta da zoben yake sanye dass kamar an gwada ta ce "Hannun nawa ne ma ya yi wa zoben kyau, ba ma zobenne ya yi wa hannuna kyau ba?" Anwar ya ce "Eh mana, ai ke ko kwalliya ki kai ke ki ke wa kwalliyar kyau ba ita take miki ba" kafin Neehal ta ce wani abu Ameen ya ƙaraso kusa da su, Anwar ya yi sauri ya ce masa "Yayanmu Barka da dare" Ameen ya ɗan saki fuskarsa ya na mik'owa Anwar hannu ya ce "Yawwa barkan mu" suka yi musabaha Anwar ya gaisheshi ya amsa sannan ya wuce ba tare da ya kalli ko inda Neehal take ba, saɓanin ita kuma da ta zira masa na mujiya. Anwar ya kalle ta ganin ta bi Ameen da ido ya ce "Ya dai Queen?" Neehal ta sauke ajiyar zuciya, zuciyarta babu daɗi ganin yanda Ameen ya shareta, ya ƙi kulata, Alhalin yau ba su haɗu ba kwata_kwata, ta rasa me yasa kwana biyunnan yake mata haka, duk da ma can shi mutum ne ba mai sakewa ba kuma ga miskilanci, amma ya na nuna mata kulawa sosai a matsayinta na k'anwarshi tilo guda ɗaya...... Anwar ya katse mata tunaninta ta hanyar faɗin "Wai me yake farune na ga kamar kina cikin damuwa Neehal?" Neehal ta sauke ajiyar zuciya a karo na biyu ta ce "Bakomai Ya Anwar" ya ce "Sure?" Ta gyaɗa masa kai kawai tare da ƙoƙarin boye damuwarta dan kar ya fuskanci wani abu. Anwar ya duba tsadadden agogon hannunsa ya ce "Shikenan Queen bari na je gida na ga time ɗin Sallah ya yi" Neehal ta ce "Ba ka ci cake din ba kuma?" Ya ce "Na k'oshi ne" Neehal ta bata fuska ta ce "Please ya Anwar ka ci mana" ba tare da ya ce komai ba ya buɗe Plate d'in da'aka rufe cake d'in ya d'au 1 ya gutsira ya ajiye, ya na kallonta ya ce "Thank you" Neehal ta ce "Ka ƙara Mana, wannan ai baka ci ba" ya ce "I'm sorry dear, ciki na ya cika ne" Neehal ba ta kuma komai ba, Anwar ya Mik'e ya ce "Bye sai mun yi waya?" Neehal ta mik'e ta na faɗin "Mu je in raka ka" Suka jera su na tafiya har inda ya yi parking Motarsa ta raka shi, tsayawa su ka yi ta dubeshi ta ce "Thank you so much ya Anwar for your time, da kuma kyautar da ka ba ni, Allah ya sa ka da Alkhairi ya ƙara buɗi" Anwar ya ce "Ni ma Nagode sosai dear, kuma na ji daɗi, Allah ya barmu tare" Neehal ta ce "Amin, Allah ya kiyaye hanya ya tsare, ka gaida Ammi" ya ce "Amin, za ta ji Insha Allah bye" Neehal ta ɗaga masa hannu ta na murmushi, shima d'aga mata hannun ya yi ya buɗe motar sa ya shige" Neehal ta juya ta koma cikin gida. Su Dije ta faɗa wa su je su ɗauko cake ɗin su cinye, Mama da Hajiya duk suna ɗaki tasan jiran Sallah su ke yi, itama ɗakinta ta shiga ta faɗa toilet ta dauro alwala ta fito ta bi jam'i itama.




Misalin ƙarfe tara na dare Hajiya ce zaune a falon sama ita da Ameen, Hajiya sai washe baki take tana zubawa Ameen hira, da alama dai ya cika mata aljihunta da kuɗi, Neehal ce ta fito daga ɗakinta, ganin Ameen ta ɓata fuska tare da turo baki gaba, Hajiya ta bi ta da kallo ta ce "Har Auwar ɗin ya tafi?" Neehal ta gyad'a mata kai kawai, Hajiya ta ƙara faɗin "To kuma mene ki ke ta ɓata rai, kamar za ki kai duka?" Neehal ba ta kula ta ba ta zauna a kasan kujerar da suke. Ameen ya d'ago ya na kallonta a hankali ya ce "I saw your missed call since?" Neehal ta ce "Uhm" kawai, ya ce "What Happen?" muryarta na rawa ta ce "Nothing" ƙoƙarin maida kwallar da ta cika mata ido ta yi, wadda batasan dalilin ta ba. Ameen ya maida hankalinshi kan wayarsa bai ƙara cewa komai ba, Neehal ta tashi ta koma ɗakinta.






Ta na shiga ta hango wayarta na haske alamun a na kira, ɗauka ta yi ta duba ta ga Anwar ne, ɗaga wa ta yi ta kara a kunnenta ya yi sallama ta amsa masa ta ƙara da faɗin "Ka je gida lafiya?" Ya ce "Lafiya ƙalau" Ta ce "Nagode fa ya Anwar sosai" Ya ce "Kin san fa ban san yawan godiyar nan, kin kai na miki komai Neehal a rayuwarnan, kuma kin san wani abu?" Neehal ta ce "A'a" Ya ce "Wannan ring d'in kyautar da na ajiye zan miki ce ranar aurenmu, kuma kawai sai na canza shawara na ce bari na kawo miki kawai" Neehal ta ce "Aiko na ji daɗi sosai Ya Anwar ɗina, Allah ya bar k'aunah." Ya ce "Ameen My Queen." Hirarsu suka cigaba da yi cikin nishaɗi, duk da Neehal ba ta wani jin daɗi a ranta kawai daurewa ta ke yi.






Washegari gari Uncle Mahmud k'anin Mama ya zo da sassafe ɗaukar Hajiya za su wuce Gombe, Neehal kafin ta wuce School suka yi Sallama dan lecture din safe gareta. Kwanaki na ta tafiya Rayuwa ta na wucewa, sai gashi har satika huɗu sun shud'e, a wannan week ɗinne kuma su Neehal za su gama exam ɗinsu ta second semester Level two (2), sosai Neehal ta zama silent saboda kusantowar bikinta, Tsakaninta da Ya Ameen kuwa ba ta sauya zani ba, tsakaninta da shi gaisuwa ce kawai sai kuma kyauta da tsarabar da yake yo mata a duk satin duniya idan ya dawo gida weekend bai fasa mata ba, amma kwata_kwata ba ya sakewa da ita, ita kuwa Neehal hakan ba ƙaramin damunta ya ke ba.




Yau Laraba ƙarfe 12 Neehal ta fito daga exam, ta na cikin tafiya ta ji a na kiranta da faɗin *"Fateema Tafeedah*" juyawa ta yi ta ga best freind ɗin ta ce a school ɗin Zee, tsayawa ta yi har Zee ta ƙaraso inda take, Zee ta ce "Fateemah tafiya za ki yi" Neehal ta ce "Ehh" Zee ta ce "Tun yanzu, yau ba shiga Library kenan?" Neehal ta ce "Na gaji ne, bacci ma nake ji, da daddare kawai na yi karatun" Zee ta ce "Ok sai mun yi waya tunda gobe bamu da exam" Neehal ta ce "Ba za ki zo ke da su Meesha ku karb'i Ankonku ba?, gobe fa Aunty Sadiya za ta kawo duka" Zee ta ce "Allah ya kai mu goben, za mu shigo da yamma mu karb'a insha Allah" Suka yi sallama Neehal ta tafi. Ta na zuwa gida ta wuce sama ta shiga ɗakinta ta kwanta ta na tunanin rayuwarsu tun daga k'uruciya, haka kawai ta ji kuka ya kufce mata ta shiga rera shi, sai da ta ga ji dan kanta ta yi shiru, dan babu mai rarrashin ta a kusa, Toilet ta shiga ta dauro alwala ta dawo ta zauna kanta na mata wani irin ciwo, ga yunwa dake nuk'urk'usar cikinta dan bata karya ba ta tafi school. Da k'yar ta daure ta yi Sallar sannan ta sakko ƙasa, tea ta haɗa mai kauri tasha, duk da tasha tea d'in amma ba ta dena jin ba daɗi a jikinta ba, haka dai ta daure ta shiga kiciniyar ɗora girki kar Mama ta dawo ta tarar ba ta yi ba. Washegari ta tashi ba ta jin daɗin jikinta ko kaɗan, amma ta ta'allak'a hakan da period ɗinta da ya kusa, dan ta na cin wahala ba kaɗan ba idan za ta yi. Ta na kwance a kan gadonta lullub'e da duvet Mama ta shigo ɗakin, Janye duvet d'in Mama ta yi ta na faɗin "Neehal wanne irin bacci ki ke haka har 10 ta wuce ba ki tashi ba?" Neehal ta buɗe idonta a hankali ta ce "Ba na jin daɗi ne Mama" Mama ta ce "Ayya sorry Daughter, Month ɗinki ya yi ko, ki tashi ki lallaɓa ki yi wanka ki sha ko tea ne, sai kisha magani" Neehal ta ce "Ai bai zo ba,ciwon kawai na ke ji" Mama ta ce "Ki dai tashi ki sha" Neehal ta yunk'ura ta tashi zaune tana taune lips d'inta.




Ƙarfe 12 Aunty Sadiya ta ƙaraso gidan da atamfofi da leshuka da yadin bridal shower na k'awayen amarya, aka zube su a falo. Neehal ta na kwance a kan doguwar kujera ba ta ko motsa ba duk da ta na jin duk budurin zuwan Aunty Sadiyan, sai ma runtse idanunta da ta ƙara yi zuciyarta na bugawa. Aunty Sadiya ta kalli sashen da take ta ce "Neehal lafiya kuwa take bacci da ranar nan?" Mama ta ce "Ba ta jin daɗi ne, ciwon mararta ne ya tashi, amma na bata magani tasha, shine bacci ya ɗauketa" Aunty Sadiya cike da tausayawa ta ce "Ayya Allah ya ba ta lafiya, Amarya ba lafiya ai babu kanta, dan ma insha Allahu ta na yin Aure za ta dena ciwon marar" Mama ta ce "Allah ya sa, kin san ta da shegen shan zak'i kamar me, na hanata na hanata amma ta ƙi denawa" Aunty Sadiya ta ce "Allah ya sauwak'e, bari na kira Haneefah ta zo ta ɗibi na freinds ɗinsu" Mama ta ce "Ya kamata kam, tunda bikin

Please Login or Register in order to submit comment