Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa yanzu sunana dana iyalina ya fara ɓaci a idon duniya." Uncle Mahmud ya ce. "Wannan shawarar ta yi, kuma ita ma Neehal ɗin ya kamata a tuntube ta akan maganar da Alhaji Musa ya yi ta farko, akan ko sun taɓa samun matsala da wani, like criminal person haka, ko kuma wani da suka samu saɓani ya taɓa yin wani mummunan ƙudiri a kanta a matsayin ɗaukar fansa." Abba ya jinjina kai ya ce. "Ya kamata kam, domin komai zai iya faruwa, tunda mu har yanzu lalube muke a cikin duhu, muna neman gaskiyar al'amari." Umma ta ce. "Har wannan ƙawarta_ta itama a tuntube ta ko san wani abu akai, tunda kodayaushe suna tare." Aunty A'isha ta ce. "Wai Haneefah kike nufi?" Umma ta ce. "Ehh." Aunty A'isha ta ce. "Insha Allahu duk zamu yi ƙoƙarin yin hakan, Allah Ubangiji dai ya toni asirin masu aikata wannan abun da gaggawa, ko zuciyoyinmu zasu samu salama." Suka amsa da Amin, kuma kowa ya yi na'am da wannan shawarwarin da aka bayar. Aunty Sadiya dai kawai kallon su take bata ce komai ba, cikin ranta tana tunanin wani abu daban. Uncle Usman ya ce, "Ni Neehal ɗin ma nake tausayawa, yarinya duk za'a sa ta tsani kanta da rayuwarta, dan babu wanda zai so a ce ana rasa rai ta dalilin sa, ko kuma an cutar da wani." Kawu Musa ya ce. "Wallahi fa, tunda k'uruciyarta za'a ɗora mata tension ɗin da ya fi ƙarfin kanta." Umma ta ce. "Ƙaddara ce, wadda ta riga fata, babu yanda zamu yi, sai dai mu yi addu'ar Allah ya tsayar haka, kuma da izinin Allah komai zai zo ƙarshe, zai kuma zama tarihi kamar ba'ai ba." "Haka muke fata." Cewar Uncle Umar. Hajiya ta ce. "Tana kwance har yanzu ko?" Aunty A'isha ta ce. "Eh, tunda akai mata allurar bacci bata farka ba har yanzu." Mama ta ce. "Bari mu gama sai in je in tashe ta, na ga yamma ta yi sosai Magriba ta gabato, gwara ta tashi ta yi sallolin dake kanta." Hajiya ta ce. "Ni fa da wannan abun ya faru na yi zargin ko dai aljanu ne da yarinyar nan." Kawu Musa ya ce. "Zata iya yiyuwa su ɗin ne ma, amma kuma shi sha'anin jinnu ba haka yake ba akan al'amarin Aure, yawanci tun kafin maganar aure ta yi nisa suke tarwatsa abun, ko kuma ki ga yarinya ta girma sosai babu mashinshini, amma indai ba turo su akai ba zai yi wahala su yi kisa, in ma zasu yi kisan ba ta hanyar harbi ba, sai dai kawai a wayi gari a ga mutum ya rasu." Umma ta ce. "Tabbas haka ne, dan na taɓa ganin yarinyar da irin wannan ya faru da ita, ita auranta aljanin ya yi, da farkon ƴan'matancinta tana samari, daga baya kuma sai suka daina zuwa dif, sai daga baya aka gane aljanin ne ya aure ta." Aunty A'isha ta ce. "Subhallahi, Allah ya kiyaye mu da zuri'armu baki ɗaya. Suka amsa da Amin. Uncle Mahmud ya ce. "Hakan ma zata e yiyuwa, kin san su ma aljanun babu abun da ba za su iya ba, sai a gwada yi mata magani a ga ko Allah zai sa a dace." Kawu Musa ya ce. "Allah yasa mu dace, yasa mu fi ƙarfin zuk'atanmu, ya kare mu daga abun da yafi ƙarfin mu, ya raba mu da mummunar ƙaddara." Suka ƙara Amsawa da Amin. Abba ya nisa ya ce. "Ni fa ina da wata shawara, a gani na tunda duk wannan abun da ake yi mun fahimci saboda kar yarinyar ta yi aure ne, auren ne ba'a son ta yi, me zai hana a ɗaura mata Auren kawai ta tare a gidan mijinta ba tare da duniya ta sani ba, kun ga kenan daga lokacin da tai auran koma waye yake bibiyarta da mugun nufinsa ta yi auranta, magana ta ƙare." Uncle Usman ya ce. ,"Tunanin dana yi d'azu kenan nima, na ce a ɗaura mata auran a yau, amma Daddy'n ta ya hana." Dad ya ce. "Ba wai na ƙi ba ne, abubuwa guda biyu na duba, na farko iyayen yaron Sadik nan baza su ji daɗi ba idan muka ɗaurawa Neehal Aure a yau, zasu yi tunanin ba ma mu damu da ɓatan ɗansu ba ta auran ƴarmu kawai muke, alhalin kuma duk mun fuskanci ko na ce muna tunanin saboda da ita aka sace shi, duk da ba ma fatan hakan. Na biyu kuma ita kanta yarinyar bazai yiyu tana cikin halin baƙin ciki da tashin hankalin ɓatan Sadik sannan mu ƙara mata da wata damuwar mu daura mata aure da wanin sa ba da sanin ta ba, may be wanda zamu aura matan bata son shi, kun ga mun jefa ta a cikin wata damuwar bata gama fita daga wata ba." Suka jinjina kai gaba-d'aya cikin gamsuwa da bayanan Daddy. Mama ta ce, "Maganar ka gaskiya ce Gen. Amma in dan wanda Neehal zata aura ne ba mu da matsala da wannan, dan ta son yaron nan Ahmad Baban twins, shima kuma yana son ta, gashi yaron kirki ne ba shi da matsalar komai haka ma iyayensa, amma kamar yadda ka faɗa koda za'ai mata auran ba yanzu ba, mu ɗan jira zuwa wani lokaci kafin nan Insha Allahu mun warware daga cikin wannan matsalar, dan yanzu babban burin mu Allah ya bayyana mana Sadik cikin k'oshin lafiya." Haka dai suka ci-gaba da tattaunawa, shi Daddy yana ganin gwara a jira bayyanar Sadik idan ma Auren za'ai wa Neehal a aura mata shi. Uncle Mahmud ya ce, kamar hakan da wuya, tunda a rabuwar da suka yi ɗazu da danginsa sun nuna ko Allah ya bayyana shi ba zai auri Neehal ba, kuma ba ya jin yanda suka ɗauki zafi akan al'amarin zasu amince ta cikin ruwan sanyi. Suna cikin tattaunawar ne Aunty Sadiya ta ce. "Wai ina Ameen ne? Yau gaba-d'aya duk wannan abun da ake ban gan shi ba." A ɗan firgice Daddy ya ce. "Bai zo gidan nan ko da safe ba? Ni sai ma yanzu da kikai magana na yi released ban gan shi ba yau kwata_kwata ko a gurin d'aurin Auren." Cikin damuwa Mama ta ce. "Nima rabo na da shi tun jiya da rana, to ina yaron nan ya shiga?" Hajiya ta ce. "Matar shi ma haka ta ce, kuma tun safe take kiran wayarsa a kashe." Kawu Musa ya ce. "Subhallahi, Allah dai yasa lafiya yake." Uncle Ahmad ya ce. "Insha Allahu yana lafiya k'alau, kun san halin Ameen, may be ya samu wannan labarin ne shi yasa bai zo ba saboda tashin hankali." Daddy ya ce. "To kuma sai ya kashe wayoyinsa, Ameen da koyaushe wayoyinsa a kunne suke." Mama da gabanta ke faɗuwa ta ce. "Bari na dauko wayata na kira shi mu ji ko zata shiga yanzu." Uncle Mahmud ya ce. "Bari na kira shi ba sai kin tashi ba." Ya ƙarashe zancen tare da zaro wayarsa daga aljihun gaban rigarsa. Yana kira ta shiga, sai dai har ta katse bai ɗauka ba. Mama ta ce, "To ina Yaron nan ya shiga ya bar wayar tasa kuma?" Daddy da yanayinsa ya nuna rud'ewa ya ce. "To shi kuma me ya faru da shi?" Umma ta ce. "Babu komai Insha Allahu, tunda wayar ta shiga zai biyo bayan kiran ko anjima ne, wataƙila ba ya kusa da wayar ne, ku kwantar da hankulanku, kar ƙarawa kanku wata damuwar, mu yi masa addu'a kawai." Sukay shiru kowa da tunanin da yake a cikin ransa. Kiran Sallar Magriba ne ya tashe su.










A ɓangaren su Abban Sadik su ma bayan dawowar su daga masallaci suka zauna zaman cigaba da tattaunawa akan al'amarin. Suma kamar su Daddy sun amince dalilin Neehal aka sace Sadik, har wasu k'annen Abba na cewa k'ila ma da haɗin bakinta, tunda ita ce last wanda ya yi waya da ita cikin dare. Abba ya ce, ya yarda ta sanadin Neehal aka sace Sadik, shi ma hakan zargi yake ba wai ya tabbatar ba ne, amma sam ba zai taɓa yarda da saka hannunta ko haɗin bakinta a sace shin ba, dan ya san baza ta taɓa cutar da Sadik ba. Kuma batun waya da suka yi, ai idan aka duba Sadik ɗin ne ya kira ta ba ita ta kira shi ba, bare ace akwai abin da ta shirya a wayar suka yi. Abby ya ce duk wannan maganganun ba su ne mafita ba, mafita kawai a dage da addu'ar Allah ya bayyana Sadik. Maamah ta farfaɗo, amma ko magana bata iya yi, ƴan'uwan ta na kanta suna yi mata firfita. Ƴan'biki kuwa duk an watse cikin alhakin abun, sai ƴan'uwa na jiki ne da baƙin nesa sukay saura, al'amarin dai babu daɗin ji ko kaɗan, abun tausayi da rud'ani.








A ɓangaren Ahmad al'amarin ya rud'a shi fiye da tunanin mai karatu, musamman da Zahra ta sanar masa abun da ta ji ana faɗa a gidansu Neehal lokacin da suka riski labarin ɓatan Sadik, cewar samarinta biyu na baya ma kashe su aka yi. Abun ya matuƙar ɗaure masa kai da jefa shi cikin tunani, Neehal ta sanar masa samarinta biyu sun rasu, amma bata ce masa kashe su akay ba. Idan kuwa har haka ne ya tabbatar da akwai wata b'oyayyiya kenan a rayuwar Neehal ko kuma ya ce wata babbar matsala. A gefe guda kuma tausayinta mai tsanani ne ya cika masa zuciya, a ransa ya dinga faɗin wannan wanne irin zalunci ne ake mata haka? Wunin yau gaba-d'aya cikin tunanin al'amarin ya yi shi, ya kulle kansa a ɗakin da yake sauka a gidan Mamy, Sallah ce kawai take fito da shi. Hankalinsa in ya yi dubu yau a tashe yake, ba ya son wani mummunan abun ya samu Princess ɗin sa, yanda yake jin zuciyarsa ba abun da yake buƙata sama da ya je ya ga halin da take ciki, dan ya san tana can tana kukan nan nata, ya san hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, abun da yake ƙara d'aga masa hankali da Zahra ta ce har suma ta yi. Twins ma waɗanda su Ummi suka taho da su gidan Mamy sai kuka suke suna kiran Aunty, da ƙyar Ummi ta lallame su suka ci abinci. Ummi saukar su kenan ita da Abban su Ahmad suka tarar da wannan mummunan labarin, hakan yasa ba su wani jima ba a gidan Mama suka yo gidan Mamy tare da Mamin da ta je bikin ita ma, tunda maganar biki kuma ta tashi tunda babu Ango. Zuciyoyinsu babu daɗi ko kaɗan, wuni suka yi suma suna jimanta wannan al'amarin mai rikitarwa. Neehal da ahalinta sun ba su tausayi sosai, more especially ma Neehal da ƙarshe komai a kanta zai ƙare.










Mama tana zaune a bakin gadon Daddy, ta saka Neehal dake kwance a gaba tana kallon ta cikin tsananin tausayawa bayan ta idar da Sallah. Tunanin rayuwar Neehal kawai take da irin jarrabawoyin da take gamuwa da su a rayuwarta, tun tana ƙarama aka kashe mata iyayenta, ta tashi a wahalce a hannun iyayen riƙon ta, bayan ta dawo hannunta da zama kuma danginta suka nuna suna ƙin ta ƙuru_ƙuru ba k'aunarta suke ba, ta san wannan abun ma yana damun ta, boyewa kawai take tana barin abun a cikin ranta. Bayan ta isa aure kuma ta fara fuskantar wannan challenges ɗin, abun ya yi mata yawa a ƙananun shekarunta. Daga nan Mama ta fara tunanin abun da suka tattauna d'azu, and she noticed one thing a zaman d'azu da akai game da Aunty Sadiya, tana magana ne kamar mai habaici a gurin, tana kuma yin wani irin kallo kamar na gargadi' ko kuma na tuhuma. Gashi ta ƙi faɗar wannan ta ce tana zargin, Mama ta kasa gane me Aunty Sadiyan take nufi da kuma inda ta dosa, amma ta k'udurce a ranta zata tambaye ta idan sun keɓe. Sai kuma ta juyar da akalar tunanin nata kan Ameen bugun zuciyarta na ƙaruwa, tana tambayar kanta ina ya shiga? Me yake yi har yanzu bai zo gidan ba? Kuma ana ta kiran shi ba ya pick. Bayan shigowar ta ɗakin ta masa kira ya kai sau biyar amma bai ɗauka ba.






A hankali Neehal ta buɗe idonta da yay mata nauyi ta sauke su akan fuskar Mama. Cikin muryar marasa lafiya dake fita da ƙyar ta ce. "Mama!" Mama ta sauke wahalallen numfashi muryar Neehal ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi. A hanzarce ta ce. "Na'am, Daughter kin tashi? sannu kin ji." Ta ƙarashe zancen da kama hannayen Neehal duka a cikin nata. Neehal ta gyaɗa mata kanta wanda take jin sa kamar dutsen dala saboda nauyin da yay mata, ta fara hawaye ta ce. "Mama da gaske ne ba mafarki na yi ba Sadik ya ɓata an sace shi?" Mama ta mayar da k'wallar data tarar mata a ido dan kar ta ƙara karyar wa Neehal zuciya ta ce. "Eh Daughter, amma za'a gan shi Insha Allah, ana nan anata neman sa da cikiyar sa tare da addu'a." Neehal ta fashe da kuka mai karyar da zuciya ta ce. "Me nay musu Mama? Su waye suka ɗauke mun Sadik? Me yasa basa san na yi aure kamar kowa? Ya Allah in wani laifin nay maka ka yafe mun w....." Mama tay saurin rufe mata baki tana faɗin. "Ya isa haka Neehal, ki bar wannan maganganun kar ki je ki yi sab'o, gashi baki da lafiya. Ki yi haquri komai kika gani ya samu bawa rubutacce ne a rayuwarsa tun fil azal daga Ubangijin sa, wannan abun ƙaddarar ki ce da mu baki ɗaya, amma baza mu gaji da kaiwa Allah kukan mu ba, da shi kaɗai muka dogara kuma shi zai yaye mana, jarrabawa ce Neehal, kowanne Mumini akwai irin tasa, ki kwantar da hankalin ki Insha Allahu za'a ga Sadik." Ta lumshe ido hawaye masu d'umi na zubo mata, bata taɓa jin ta tsani rayuwarta irin yau ba, ta gaji da cutar da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da ake yi saboda ita. "Ya Allah kar ka ba su ikon cutar mun da Sadik, My Sadik where you? Ka dawo gare ni karka tafi ka barni kamar yadda su Anwar suka tafi suka bar ni Please, i'm in needing you in my life, please my Sadik come back to your wife." Abun da take faɗa a ranta kenan cikin ɗacin zuciya, kamar ta cire zuciyarta ta yar haka take ji saboda zafin da take mata. Har yanzu bata bar fatan ace zata farka daga wannan mummunan mafarkin da take ba, zuciyarta ta kasa yarda cewar da gaske ne abun da yake faruwa. Mama ta d'ago ta tana faɗin. "Tashi mu je ki yi wanka ko zaki ji daɗin jikinki, ki kuma rama sallolin dake kanki, sai ki sha ko tea ne ki sha magani, na ji jikin naki da zafi zau alamun zazzaɓi." Bata musa wa Mama ta ɗaure ta sakko dak'yar tana cize lip ɗinta hannunta dafe da kanta, Mama ta taimaka mata ta kai ta toilet ta yi wanka tare da brush ta ɗauro alwala sannan suka fito, kayan data cire ta mayar ta zira hijabin Mama ta tayar da Sallah, a zaune ta yi sallolin da ake bin ta duka ta haɗa isha'i da ake yi yanzu, ta daɗe tana addu'a cikin kuka a sujjadarta ta ƙarshe akan Allah ya bayyana Sadik, ya kuma kawo mata ƙarshen wannan al'amarin. Bayan ta idar ta lallaɓa ta koma kan gado ta kwanta, Mama bata ɗakin ta fita hado mata tea, wanda tana da yaƙinin a halin k'uncin da take ciki a yanzu ba zai iya shiga bakinta ba balle har ya wuce ta mak'oshinta ya tafi cikinta. Bata san musawa Maman ne kawai, amma ita a yanda take jin zuciyarta da Allah zai ɗauki ranta a yanzu da ta yi murna da hakan fiye da wannan rayuwar da take ciki. Mama ta dawo ɗakin ta ajiye mug ɗin hannunta ba tare da yi magana ba, sannan ta juya ta kuma fita dan ɗauko mata magani, sauri take saboda tana son ta yi ta kawo mata maganin sannan ta je gurin baƙin da suke rage a gidan, dan fiye da rabin mutanen d'azu duk sun koma gidajensu tunda maganar biki ta tashi. Ta buɗe ƙofar falon kenan da nufin fita suka yi karo da Ameen dake ƙoƙarin shigowa...........✍️










*By*
*Zeey Kumurya*
*⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*6️⃣5️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*














..........Bayan Sadik ya gama cin abinci suka haɗu gaba-ɗaya a Parlour'n Abbansa, shi, Abba, Maamah, Umma, Hajiya, Kawu da mahaifiyar Maamah da ƙannen Abba guda biyu. Abba ne ya fara magana da faɗin. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Masha Allah, muna ƙara godewa Ubangiji buwayi gagara misali, mai mayar da farin ciki zuwa baƙin ciki, da mayar da baƙin ciki zuwa farin ciki. Kwana takwas i war haka zuk'atanmu cikin tsananin farin ciki suke, amma cikin ikon Allah washegari sai ya canza mana zuk'atanmu zuwa baƙin ciki da fargaba da tsoro gami da zullumi. A yau kuma sai ya sauya mana su da tsananin farin ciki, muna fata kuma ya yarje mana mu cigaba da kasancewa cikin farin ciki har ƙarshen rayuwarmu, Ubangiji Allah kar ka ƙara maimaita mana irin wannan tashin hankalin da muka shiga har ƙarshen rayuwarmu." Suka amsa da Amin gaba-ɗayan su. Kawu ya kalli Sadik ya ce. "Masha Allah Abubukar, mun ji daɗin dawowar ka cikin k'oshin lafiya wanda ba mu taɓa zaton haka ba, babu irin sak'e_sak'en da ba mu yi ba akan ɓatan ka, mu ce kidnappers ne, mu ce ko masu satar mutane ne, mu ce ko kai ka gudu da kanka, mu ce ko asiri akai maka ka bazama duniya, babu abun dai ba mu ayyana ba, sai daga baya muka gane bakin zaren, amma duk da haka muna son jin ƙarin bayanin abun da ya faru daga gare ka wanda shi zai sa mu ƙara tabbatar da abun da muke zargi." Sadik ya sauke numfashi cikin sanyin murya ya ce. "Misalin ƙarfe uku na daren ranar ina cikin yin Sallah na ji kamar motsi a bayan ɗakin da nake, wanda ga dukkan alamu ƙofar BQ ta baya ake bugawa da ƙarfi. Na cigaba da Sallah ta ba tare da tunanin komai ba a raina, amma kafin na sallame Sallar na ji an banko ƙofar falo da ƙarfi, gabana ya faɗi ba shiri na sallame Sallar na tashi na je na lek'a window, bana ganin Parlour'n sosai saboda babu wadataccen haske, amma ina iya hango alamun mutane a Parlour'n, kuma ɗakin da nake ciki suke tunkarowa. Na tsaya ina cigaba da kallon ikon Allah, cikin mintuna ƙalilan na ji ana dukan ƙofar ɗakin da nake, na koma bakin ƙofar da sauri na ƙara locked ɗinta, sannan na koma ƙarshen ɗakin ina ambaton sunan Allah tare da neman ɗaukin sa. Kawai sai gani na yi an banko ƙofar ɗakin ta faɗi ƙasa an ɓalle ta ɓal. Na firgita sosai tsorona ya ƙaru, ban gama zullumun ba na ga ana haske ɗakin da wata fitila mai hasken tsiya, sannan aka dallare mun fuskata da ita, hakan yasa ban tantance adadin mutanen da suka shigo ba, balle naga kammanin su, na fara kare idona saboda hasken fitilar dake ƙoƙarin yi masa illa, ba tare da sun ce mun k'ala ba na ji sun watsa mun wani abu a fuska kamar powder, lokaci ɗaya na ji numfashi na yana ƙoƙarin ɗaukewa, kaina ya fara wata irin juyawa, na ji ƙafafuna sun kasa ɗauka ta, na tafi luuu zan faɗi ƙasa, daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba. Sai farkawa na yi na gan ni a wani ƙaramin ɗaki a kwance akan wani ƙaramin gadon ƙarfe. Na shiga bin ɗakin da kallo kwanyata na tariyo mun last abun da ya faru, na yunƙura da sauri da nufin in tashi amma sai hakan ya gagara, na ji jikina kamar ba nawa ba, kamar an zare mun lakar jikina, kamar an zuk'e mun jinin jikina, na kasa d'aga ko da ɗanyatsana ne duk iya ƙoƙarin yin hakan da na yi kuwa. Idanuna ne kawai suke iya aiki a jikina suma ba kamar da ba, dan sun mun wani irin nauyi. Na shiga ƙarewa ɗakin kallo a tunanina ko zan iya tuno ɗakin da nake, ko na taɓa zuwan sa a rayuwata. Amma babu abun da na gane, na kasa tantance dare ne ko rana lokacin. Na lumshe ido ina tunanin me na yi aka kawo ni nan? Su waye suka zo har gida suka ɗauko ni saura awanni kaɗan d'aurin Aure na? Bayan ku san minti talatin ina ta yiwa kaina tambayoyin da ba ni da amsar su na ji an turo ƙofa a hankali an shigo ɗakin, na buɗe idona da sauri ina kallon mai shigowar, wani ƙaton mutum ne dogo fuskarsa a rufe da bak'ar face maks ta roba, ƙwayar idanunsa kawai ake gani wanda suka kasance jajaye ne. Na buɗe bakina da na ji ya mun nauyi da ƙyar na ce. "Who are you? What do you want to me?" Kamar da dutse na yi magana bai ce mun k'ala ba, ƙarasowa kawai ya yi ya tattab'a jikina, ni kuma ina cigaba da yi masa tambayoyin dalilin da yasa suka kawo ni gurin. Ya fita bayan ya gama tattab'a jikina, jimawa kaɗan ya dawo da abinci da ruwa a hannunsa, ya ajiye a gefen gadon sannan ya tayar da ni zaune, ya buɗe abincin ya turo mun gabana sannan ya tashi ya fita. Na bi shi da kallo har ya fice, ban ko kalli inda abincin yake ba balle na yi tunanin ci. Bayan wasu mintuna ya ƙara dawowa ɗakin, ganin ban ci abincin ba sai ya kalle ni kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Ya rufe abincin ya kamani na tashi ina jin jikina kamar ba nawa ba saboda rashin k'wari, wata ƙofa dake cikin dakin ya nufa da ni, yasa hannu ya tura ƙofar ta buɗe sannan muka shiga, ashe toilet ne. Ya zaunar da ni akan toilet sannan ya juya ya fita, na gane mai yake nufi in ina jin wani uzurin in yi kenan. Na tashi da ƙyar ina layi na kunna pampon sink na yi alwala, duk da ban san ƙarfe nawa ba, ban kuma san sallar da zan yi ba, amma na san a lokacin baza a rasa sallar da ake bina ba wadda ban yi ba. Bayan na idar da alwalar na fito dak'yar ina jin kamar iska zata ɗauke ni saboda rashin k'warin jiki. Na tarar da darduma a shimfid'e a tsakiyar ɗakin, bangon ɗakin kuma ta inda dardumar take fuskanta alamun nan ne gabas an saka wani ƙaton agogon bango mai 24 hours a jikinsa, na ga a lokacin ya nuna ƙarfe bakwai da mintuna na safe. Sai dai na kasa gane time ɗin na wacce rana ne, safiyar ranar juma'ar d'aurin Aure na ce ko kuma wata ranar ce daban? Na ƙarasa gaban agogon sai na ga ashe har da rubutun days mitsi_mitsi a cikin sa, a yanda ya nuna kuma safiyar ranar juma'a ce. Na sauke ajiyar zuciya sannan na tayar da Sallah, na yi Sallar asubahin dake kaina. Bayan na idar na zauna na rafka tagumi zuciyata cike da tsantsar tashin hankalin sabon al'amarin da ya same ni, wanda ban san dalilin sa ba amma na fawwalawa Allah komai, na shiga roƙon sa akan ya kare ni daga dukkan wani mai nufi na da sharri mutum ko na aljan. Sai kuma na fara tunanin gida da mahifina da sauran ƴan'uwa, dan na san zuwa yanzu an farga da rashin gani na a gidan, an fara nema na hankali a tashe. Ina zaune inata tunanen gida da dalilin sato ni da aka yi aka kawo wannan gidan har goma na safe ta yi. Na tashi da sauri kamar

Please Login or Register in order to submit comment