Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya zagaya ta bayan Abba ya ƙarasa kan gado inda Umma take ya damk'o ta, Umma tana cizewa Abba kuma yana faɗin su sakar masa mata cikin tsananin ɓacin rai ganin wani k'aton banza yana taɓa masa mata, ganin Abba ya zabura zai miƙe wani daga cikin yaran ya riƙe shi, tare da ɗora masa bindiga a goshi, Umma ganin haka ta ruɗe ta fara kuka, a kusa da Abba yaron ya cillar da ita, shi kuma wanda ya riƙe Abba ya sake shi tare da koma wa baya. Babban nasu ya ƙara sakin wata kafirar dariya, ya daɗe yana dariyar sannan ya tsagaita ya zira hannunsa a aljihun gaban rigarsa ya ɗauko waya ya latsa ya haska wa su Abba da Umma yana faɗin "Kun san wannan?" A tare Umma da Abba suka kalli juna cikin al'ajabi, Abba ne ya fara ɗauke kallonsa daga kan wayar ya mayar ga mutumin ya ce "Eh na san sa, farin sani ma kuwa." Mutumin ya yi wani guntun murmushi sannan ya matso da fuskarsa kusa da su Abba sosai ya fara magana ƙasa_ƙasa wanda ni dai zeey ban ji ba. Zuwa can dai na ji Abba cikin d'aga murya wadda ke nuni da tsantsar ɓacin rai ya ce "Ba zan iya wannan haukan da shirmen ba, ƴar tawa guda ɗaya zan yarda in ɓata mata rayuwa in jefa ta a halaka, to bazan yi abun da kuke so ba ku yi duk abunda zaku yi, Allah ya fiku kuma da shi na dogara." Mutumin ya jinjina kai ya mai da dubansa ga Umma ya ce "Kema kin zaɓi mutuwa akan amincewa da buƙatar mu?" Umma ta saka kuka, cikin kukan ta ce "Ko me zaku mun ba zan taɓa amincewa da buƙatarku ba, kuma ƴarmu ko da bama raye Allah zai kare mana ita daga mugun nufinku, kuma da ku da wanda ya turo kun mun kai ƙarar ku gurin mai duka, shi zai mana maganin ku ya kawo ƙarshen ku da duk wasu irin hali da mummunar d'abi'arku, kuma......." Ƙarar harbin da ta ji ya katse mata zancenta ta runtse idanta da sauri, kafin ta yi wani yunk'uri ta ƙara jin wani saukar harbin, buɗe idonta ta yi zuciyarta na wani irin bugu tamkar zata faso kirjinta ta fito, wata gigitacciyar ƙara ta saki ganin duk harbin da ta ji a ƙirjin Abba aka yi su, rungume shi ta yi k'am ajikinta tana kiran sunansa cikin fitar hayyaci, amma ko motsi ba ya yi, jini har ya fara ɓata farar jallabiyar dake jikinsa. Janye Abba suka yi da sauri daga jikinta itama suka sakar mata harbin a ƙirji, a take Umma ta bi bayan Abba ta zube a gurin babu alamun numfashi a tattare da ita. kafin kiftawar ido suka fice daga ɗakin a guje suka bi ta inda shigo suka fice daga gidan gaba-d'aya.








Aunty A'isha tana part ɗinta tana bacci ƙarar harbin ne ya tashe ta, amma ko kaɗan ba ta yi tunanin a cikin gidan ba ne, ta yi tunanin wani gidan custom ne da suke mak'ota b'arayi suka shigar masa. Amma duk da haka sai da ta ji gabanta ya faɗi a lokacin da akai harbin ƙarshe, wayarta ta ɗauka ta kira Numbern Abba amma bai ɗauka ba, jin shiru kusan minti talatin da yin harbin Ba'a kuma ba ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta, amma sai ta nemi bacci a idonta ta rasa, haka kawai ta ji jikinta wani iri, zuciyarta har wani rawa take dan fargaba. Ƙara kiran wayar Abba ta yi amma bai d'aga ba, hakan yasa ta kira Umma itama ba ta ɗauka ba, gashi Uncle Usman ba ya nan ya yi tafiya balle ta kira shi, dan ita ta rasa mai yasa hankalinta ya kasa kwanciya da harbukan da akai. Ranar Aunty A'isha bata iya bacci ba, ga wani irin tsoro da ya rufe ta, wadda ko kwakwkwaran motsi tsoron yi take. Sai da aka shiga Sallar Asuba sannan ta iya tashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito ta tada Sallah, tana idarwa kuwa ta yi part ɗin Umma. Da Sallama ta shiga falon Umma amma ta ji shiru, corridor ta nufa inda ɗakunan Umma guda biyu suke suna facing juna, tun daga bakin ƙofar ta fara hango jini ta ƙasan ƙofar, wani mummunar fad'uwa gabanta ya yi, da gudu ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, wata gigitacciyar ƙara ta k'walla ganin Umma da Abba kwance cikin jini, kamar kuma wacce aka tsikara ta fito da gudu ta yi waje tana k'wala wa mai_gadi kira, mai gadi da dawowarsa kenan daga masallaci ya fito da sauri yana tambayar "lafiya Hajiya?" Part ɗin Umma kawai Aunty A'isha take nuna masa amma ta kasa mgn, hakan yasa ya nufi part ɗin da sauri a zatonsa ko wuta ce ta kama a ciki. Gigitar da mai_gadi ya shiga baza ta faɗu ba, ga mamakin ta ya ya aka iya shigowa gidan har aka aiwatar da wannan mummunan aikin, dan shi ko da za shi masallaci ma ƙofar gidan a rufe take shi ya bude ta da hannunsa, kuma gidan baza a iya haurowa ba saboda tsayin katangar gidan. Kuka sosai Aunty A'isha ta shiga yi lokacin da mai_gadi ya sanar mata babu numfashi a tattare da su Umma, tana faɗin "Su waye suka kashe ku? Me kukai musu?" Mai_,gadi kuwa da sauri ya fita ya faɗa wa mak'ota, nan da nan kuwa mazan layin suka fara shiga gidan cikin tashin hankali, dan kuwa duk yawanci sun ji harbin da akai, babu ɓata lokaci custom ɗin dake layin ya kira Police aka sanar musu, kafin gari ya yi haske har sun zo gidan. Aunty A'isha kuwa tuni ta suma, wata makociyarsu ce da ta shigo ta ɗauki ƙaramar wayar Umma ta shiga kiran ƴan'uwanta tana sanar musu, haka ma wayar Abba mai_gadi ne ya ɗauka ya kira ƴan'uwa da abokan arziki yana sanar musu. Aunty A'isha bayan an shafa mata ruwa ta farfaɗo itama tana kuka ta shiga kiran mutane tana sanar musu wannan mummunan labarin wanda take ganin tamkar al'amara ko kuma mafarki take zata farka. Mutuwar su Abba ta girgiza zuk'atan mutane, kafin ka ce me, labari ya fara baza gari, musamman da matasan unguwar suka yaɗa a social media.








Lokacin da Aunty A'isha ta sanar da Mama rasuwar Umma da Abba kusan zaucewa ta yi ita kaɗai a ɗaki, saboda tsananin kaɗuwa dan mutuwar ta dake ta ba kaɗan ba, wayar da suka yi jiya da daddare kawai take tuna wa. Da ƙyar ta samu yar nutsuwa ta fara dawo mata sanadiyyar karanta Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, da ta shiga maimaitawa a fili. Miƙewa ta yi da ƙyar ta fito ta nufi part ɗin Daddy, tana shiga ta tarar da shi yana waya. Sai da ta jira ya gama wayar sannan ta rattabo masa abun da faru, iya rudewa shi ma Daddy ya ruɗe, ba shiri ya yi kira a waya dan asamar musu Visa zuwa Kano shi da Mama, da Ameen da Neehal. Neehal tana kwance a ɗaki Mama ta shigo ta same ta. "Neehal, tashi ki shirya zamu unguwa." Mama ta faɗi haka cikin sanyi da raunin murya. Neehal ta tashi zaune tana duban Mama ta ce "Ina zamu Mama? Ni fa Umma da Abba nake son gani." Ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka, Mama ta daure dan kar Neehal ɗin ta gane wani abu ta ce "Daga can zamu biya gida ki ga su Umman." Neehal ta sauke ajiyar zuciya sannan ta miƙe ta shiga toilet, Mama ta bita da kallo cikin tsananin tausayinta. Tashi ta yi ta fice daga ɗakin da sauri jin kuka na neman kufce mata. Neehal kam cikin sanyin jiki sosai ta fito ta shirya, ta rasa me yasa ta ji bata wata murna duk da Mama ta ce mata za su biya ta ga Su Ummanta. Kafin ƙarfe tara su Mama sun ƙarasa Airport, cikin mintuna aka gama komai suka shiga jirgi suka yo Kano, Neehal sai kallon Ameen take cikin zuciyarta tana mamakin tsakanin kamarsu da Mama, daga gaisuwa babu abun da ya kuma haɗa su, dan shi ko kallonta bai kuma yi ba. Sai dai cikin zuciyarsa cike take taf da tausayin ta, dan Mama ta sanar masa rasuwar Mahaifan nata. Driver'n Abba ne ya je ya ɗauko su lokacin da suka sauka a Kano, Neehal ta yi mamakin hakan amma ba ta ce komai ba. Yanda Neehal ta ruɗe, ta gigice tare da firgicewa ba zai misaltu ba, balle ya faɗu, lokacin da ta yi arba da gawar iyayenta kwance duk jini ya ɓata likkafanunsu, duk da Kasancewar ta yarinya a time ɗin amma tasan mutuwa, ta san shikenan ba zata ƙara ganin Ummanta da Abbanta ba sun tafi kenan, ta yi kuka ta yi kalamai wanda sai da suka karya zuciyar duk wanda yake gurin tare da zubar mata da hawaye, haka ta rungume Aunty A'isha sukai ta kuka abun tausayi. Mama ma duk dauriyarta ranar ta ci Kuka. Saboda tsabagen Kukan da Neehal ta sha kafin dare zazzaɓi mai zafi ya rufe ta, sai da aka mata allura sannan jikin nata ya ɗan yi dama, da safe kam jikin sai ya ƙara rikicewa, sai da ta yi kwana biyu ana saka mata drip tare da allurori sannan ta ji sauƙi. Umma da Abba sun yi jama'a sosai wanda suka raka su gidansu na gaskiya, dan Abba mutumin k'warai ne, kowa sai faɗar Alkhairinsa yake, haka ma Umma, gashi kuma sun yi sa'ar dace wa da Ranar Juma'a. Tun daga Ranar da akai kisan jami'an tsaro suka duk'ufa da binkice dan gano waɗanda suka yi nisan, dan har mai_gadi sun kama a tunaninsu ko da haɗin bakinsa, amma daga baya sun sake sa da suka gane babu haɗin bakinsa a kisan, ta ƙofar baya ma waɗanda suka yi kisan suka shigo gidan. Bayan sadakar bakwai kowa ya watse gida ya rage daga Neehal sai Aunty A'isha da hajiyarsu da Yayar Abba. Nan fa mutuwar ta dawowa da su Aunty A'isha da Neehal sabuwa, sai ya kasance Kullum sai sun yi kuka. Nasiha sosai Hajiya da Yayar Abba suke musu akan su yi haquri, dama duk mai rai mamaci ne, kowa jiran mutuwarsa yake fata dai kawai Allah yasa mu cika da kyau imani. Uncle Umar da Uncle Usman ma mutuwar ta dake su ba kaɗan ba, dan suma kuka wurjanjan suka dinga yi. Aunty A'isha kullum tunaninta su waye suka kashe su Umma, kuma akan wanne dalili? Dan a binkicen da akai ya nuna wanda suka yi kisan ba b'arayi ba ne turo su akai, dan babu abunda suka ɗauka a gidan. Kafin a yi arba'in Yayar Abba ta koma Gabasawa, sai Hajiya ce kaɗai take zaune da su Neehal. Kusan kullum suna waya da Mama da Daddy, Mama ta ƙara zuwa sau ɗaya ta duba su. Sosai Ubangidan Abba ya sa aka tsananta bincike dan gano wandanda suka yi kisan su Abba, amma shiru babu wani information, duk da jami'an tsaron na iya bakin ƙoƙarinsu a binkicen.








Washegari garin Arba'in Uncle ya zo da wata magana wadda ta gigita Su Aunty A'isha ta kuma ba su mamaki, ya zo ya same su suna zaune da Mama, da Yayar Abba da Aunty Sadiya, da Ammi matar Uncle Mahmud wanda duk sun zo ne saboda sadakar Arba'in su Umma. Maganar da ya musu kuwa itace akan rabon gado, wai nan da kwana uku insha Allah za su zo da Alk'ali a raba a bawa kowa nasa. Kuka Aunty A'isha ta saka tana faɗin "Ita bata son wani gado, dan ta riga ta yi rashin da har abada ba zata mai da kamarsa ba, rashin adalin mijinta da kuma Abokiyar zamanta salihar mace." Hajiya da Yayar Abba suka ce "Haba saurin me ake, ya bari Aunty A'isha ta fita daga takaba mana." Amma ya ƙi, wai hakan shine dai_dai. Uncle Usman kuwa k'ala bai ce ba akan maganar ba. Maganar fa ta girmama har gurin manya, dole ba son ran su Aunty A'isha ba aka raba gadon. Kasancewar Neehal ita kaɗai ce 'yarsu Abba ya sa a cikin kadarorin Umma da Abba ya mallaka mata kafin ya rasu sai da aka raba da su Uncle Umar, haka ma na Abba sai da aka raba da Yayarsa. Aunty A'isha ma aka bata tumunin takabarta. Gidan da suke ciki a gadon Neehal ya zo. Sai dai kuma wata sabuwa batun riƙon Neehal, da farko Yayar Abba ta so tafiya da ita Gabasawa amma akace hakan ba zai yiyu ba saboda ƙauye ne, ga kuma karatun Neehal ɗin, idan ta koma Gabasawa zata tawaya. Ƴan'uwan Abba kuwa da suke cikin Kano kowa ƙin ɗaukar ta ya yi, a ganinsu wahala zata zamar musu. Aunty A'isha kuwa tun farko ita ta ce a bata Neehal ɗin zata cigaba da riƙon ta, amma Uncle Umar yay ruwa yay tsaki ya ce ba za su ba da Neehal ga bare ba, tunda ba rasa dangin da za su rike ta ta yi ba, dan haka shi zai ɗauke ta. Ai Neehal na jin haka ta dinga kuka tana faɗin Ita "Gurin Aunty'nta zata zauna, babu inda zata je." Amma Uncle Umar ya sawa idonsa toka, ya ce "Ko kukan jini za ta yi wallahi a gidansa zata zauna, shi zai cigaba da riƙon ta." Aunty A'isha dama ba wani shiri take da shi ba, ta san ko zata mutu tana roƙon sa ya bata Neehal ba zai bata ba, kuma babu yanda zata yi da shi tunda ɗan'uwan mahaifiyarta ne, yafi ta kusanci da Neehal ɗin. Neehal tana ji tana gani Aunty A'isha suka haɗa kayansu ita da Hajiya suka wuce Gombe, tana kuka Aunty A'isha na yi, mutuwar Abba da Umma ta dawo musu sabuwa, duk mai imani idan ya gansu a wannan lokacin yanda suka rungume juna suna kuka mai ban tausayi sai ya zubar musu da k'walla, amma Uncle Umar ko ajikinsa, Neehal har shid'ewa take saboda kuka. A ranar da suka tafin da daddare yasa ta itama ta haɗa kayanta kaf ya tasa ƙeyarta suka tafi gidansa tana ta faman tsiyayar hawaye, dan ya mata tsawa akan kar ya ƙara jin kukanta............✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:46] Zeey Kumurya: *⚡NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_












*2️⃣8️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*














..........A falon gidan suka tarar da matarsa Aunty Fauziyya hakimce akan kujera suna kallo, yaranta guda biyu mace da Namiji suna ta wasansu akan doguwar kujera. A hankali Neehal ta shiga Falon tana goge hawayen fuskarta dan kar Uncle Umar ya gani, kan kujera ta nufa zata zauna Aunty Fauziyya ta buga mata wata uwar tsawa tana faɗin "Kar ki kuskura ki zauna mun akan kujera zauna nan ƙasa." Ba musu Neehal ta zauna a ƙasan cikin mamaki, dan ta saba ita a gidansu da gidan Mama akan kujera take zama. Uncle Umar ya zauna yana hararar Neehal ya ce "Hmmmm, yarinyar nan ai sai an dage mata, gaba-d'aya waccan matar da Ƴan'uwanta sun ɓata mata tarbiyya, Ni wlh Yaaya ta ban mamaki da ta yarda suke riƙe mata ƴa." Fauziyya ta tab'e baki ta ce "Kai kwa kuɗii, kuɗi fa aka ce maka, ta ga suna da kuɗi ne shi yasa, ka ga in an ɗan yi Zakka a dinga tunawa da ita ai." Shiru Uncle Umar ya yi jin abun ya fara komawa cin fuska. Yaran su Aiman da iman suna wasa suka fado tim akan Neehal, Uncle Umar ya ce "Subahanallah, Aiman ban hana ku wasan banza ba? gashi nan kun faɗo wa Aunty'nku akai." Aunty Fauziyya dake ta aika wa Neehal harara ta ce "Kamar ya sun faɗo mata? Ita bata gani ne, makauniya ce ita, ai tana kallonsu zasu faɗo ɗin dan baƙin hali ta ƙi matsawa, salon ace daga zuwanta an fara cutar da ita." Neehal dai ba ta ce komai ba, kanta na ƙasa tana ta hawaye. Su Aiman suka kwantar da trolley ɗinta suka buɗe suka fara zak'ulo mata kaya suna yar wa a dakin, Uncle Umar cikin tsawa ya ce musu "Wai wanne iskanci haka, ko kun mata ajiya a cikin kaya ne.?" Cikin tarar numfashi Aunty Fauziyya ta ce "Ka ga, ka dena dakawa ƴaƴana tsawa irin haka, nan gidan ubansu ne ba cin arziki suka zo ba, dan haka dole su sakata su wala san ransu." Tsaki Uncle Umar yay ya ce wa Neehal ta tashi ta tattara kayanta ta shiga ɗakin yaran. Aunty Fauziyya ta ce "Kar kuma ki hau mun kan katifar ƴaƴa, a ƙasa zaki zauna, anan kuma zaki dinga kwana." Neehal dai ba ta ce komai ba ta tashi ta shiga ɗakin tana janye da trolley ɗinta da ƙyar. A ƙasan ta zauna kamar yadda Fauziyya ta ce ta rafka tagumi, kanta ne ke mata wani irin ciwo hakan yasa ta kwanta a ƙasan, amma gaba-d'aya sai ta ji kwanciyar bata mata daɗi ba, ita data saba kwana akan luntsumemiyar katifa da lallausan bed sheet ta lullub'a da lallausan bargo, ta yaya zata iya kwanciya akan dandaryar
ƙasa kan tayis? A hankali ta miƙe dak'yar ta buɗe trolley ɗinta ta ɗauko kayanta ta shimfid'a a ƙasan ta kwanta akai, amma duk da haka bata wani ji daɗin kwanciyar ba, ya dai fi ta kwanta a ƙasan ne kawai. Allah ya so ma Aunty A'isha ta saka mata bargo acikin kayan nata, da yake ita ta haɗa mata kayan. Amma saboda garin da ɗan zafi shi yasa bata lullub'a ba, ɗakin kuma da fanka amma bata wani ba da iska, ko dan ta saba da Ac ne a gida. Tafi awa da kwanciya amma ta kasa bacci sai juyi take, idanunta dai a lumshe suke kamar mai bacci, tana jin Aunty Fauziyya ta shigo ta kwantar da ƴaƴanta akan katifa ta daura musu Net sannan ta kashe musu light ɗin ɗakin, nan fa sauro ganin duhu ya ce wa Neehal salamu alaikum, ita kuwa bata saba da sauro ba, nan da nan ya gigita ta, ta tashi zaune tana hawaye, ga ciwon kai tamkar ana ƙara mata ake, lallaɓawa ta yi ta shige Net ɗin su Aiman dan bata da wata mafita, katifar ma zata ishe su amma ɗan baƙin halin Aunty Fauziyya ta hanata kwanciya akai. Tana shiga ta sauke ajiyar zuciya, ba jimawa baccin wahala ya kwashe ta. Sanyin asuba ne ya tashe ta, cizon sauron da tasha jiya da kukan da tay ya haifar mata da zazzaɓi, cikin rawar ɗari ta sauko daga kan katifar ta dunk'ule a waje ɗaya tana numfarfashi, kayanta data shimfid'a a ƙasa ta rarumo ta rufe jikinta saboda sanyin da take ji. Sai wajen ƙarfe 7 su Iman suka tashi daga bacci, kamar wasu ƴaƴan karnuka da faɗa suka tashi, gashi sun tsutstsula fitsarinsu a kwance, Allah ya taimaki Neehal ba su ɓata ta ba. Da ƙyar Neehal ta iya tashi ta ƙarasa toilet ɗin dake ɗakin ta yi fitsarin da ya matseta, da ƙyar take tafiya saboda jiri, ga yunwa dake nuk'urk'usar hanjin cikinta, rabonta da abincin tun lunch ɗin jiya da ta yi a gida.






Aunty Fauziyya kamar kullum tana jiyo hayaniyar yaranta ta shigo ɗakin da sauri, dan kullum da hakan take gane tashinsu, Neehal na rakub'e jikin kayanta tana ta rawar sanyi, cikin muryar marasa lafiya ta ce "Ina kwana Aunty." Wani mugun kallo Aunty Fauziyya ta watsa mata, a harzuk'e tana zazzaro ido kamar sabuwar kamu ta ce "Yana gidan Ubanki shi kwanan." Neehal bata kuma cewa komai ba, ita kuma Fauziyya ta ja ƴaƴanta sukai toilet, wanka ta musu ta shirya su cikin uniform ɗinsu, sannan suka fita falo dan karyawa. Uncle Umar ya ce wa Fauziyya "Ina Neehal ɗin, itama ta fito ta karya mana." A fusace Aunty Fauziyya ta ce masa "Ka san yar gold ce bata tashi ba har yanzu." Sai wajen ƙarfe tara Aunty Fauziyya ta ƙwalawa Neehal kira lokacin Uncle Umar ya fita, cikin hanzari Neehal ta taso dan wani bala'in tsoron matar take ji, k'osan Talatin ta bata da wani ɗan bread da ruwan bunu rabin ƙaramin cup a matsayin breakfast. Neehal ta bi abun da aka bata da kallo sannan ta fara ci tana yamutsa fuska saboda bakinta babu daɗi, yunwa ce kawai ta sa take ci, ga shi ita k'osai ba mutuminta ba ne, gara ma bread ɗin. Ruwan bunun kuwa ko kurb'a ba ta yi ba, dan tasan baza ta iya sha ba. Bayan ta gama cikin faɗa Aunty Fauziyya ta ce "Tunda ciki ya ɗauka, sai ki tashi ki haɗa kayan nan, ki kai tsakar gida ki wanke, sannan ki dawo ki share mun falo ki yi mopping, ɗakin da kika kwana ma haka." Cikin sanyi Neehal ta ce "Aunty ban da lafiya, kuma ban iya b......." "Ai ko cutar mutuwa kike yau sai kin mun aikin nan, dan Ubanki Jakar uwarki ce ni zan dafa miki ki ci kina daga kwance, zaki tashi ko sai na miki dukan mutuwa a gidan nan." Jiki na b'ari Neehal ta tashi ta fara haɗa kayan, duk da zazzaɓin dake damunta, amma saboda tsoron Fauziyya da take ji dole ta yi. Ba ta taɓa wanke_wanke ba a rayuwarta, sai a gidan Mama ne ma idan ta ci abinci Mama take sata ta dauraye flate ɗin da taci abincin. Ai kuwa Fauziyya ta sha asarar omo, gashi kafin ta gama ta jik'a jikinta jagab da ruwa, a haka ta yi share_sharen da mopping, Fauziyya kuwa tuni ta fice yawon mak'ota. Tana gama aikin ta yi daki ta kwanta akan tiles, zazzaɓi mai zafi ne ya rufe ta. Da Fauziyya ta dawo ta ga b'arnar Omon da Neehal ta mata, ta dinga surfa mata ashariya da masifa, da dukanta ma zata yi wata makociyarta data shigo ta hanata, ganin yanda Neehal ɗin take rawar sanyi. Da rana ma kiranta Aunty Fauziyya ta yi ta bata wata shinkafa da wake ƴar kaɗan a roba, ko man kirki babu a ciki. Lauma ɗaya Neehal ta yi ta ture ta koma ɗaki ta kwanta, Fauziyya ranar wuni ta yi tana zagin Neehal. Da daddare Uncle Umar ya lek'a ɗakin da Neehal take ganin Shiru_shiru bai ji motsinta ba tunda ya dawo, ganin ba ta da lafiya ya bata panadol da Paracetamol ta sha, ya kuma kawo mata lemo da ayaban daya shigo gidan da su har ɗaki, ta kuwa ci ayabar ba laifi dan tana sonta sosai. Fauziyya tayta kumbure_kumbure tana huci kamar zata naushi iska ganin abun da Uncle Umar ya yi wa Neehal. Washegari ma Neehal ce ta yi wanke_wanke da shara, jikin nata ya yi sauƙi tunda ta sha magani, sai dai bata warke sumul ba, ranar kam sai da Fauziyya ta mare ta akan ta'adin omon data mata. A daren Ranar Uncle Usman ya zo gidan yi musu sallama dan zai koma garin da yake aiki ne. Tsaraba sosai yayo wa Neehal da su Aiman ta sweet da chocolate, da zai tafi Neehal tai ta Kuka, Aunty Fauziyya ta tab'e baki a ranta ta ce 'Munafurcin banza.'








Tun daga ranar Neehal ce take wanke_wanke da shara da mopping da aiken gidan, yanda ka san baiwa haka Fauziyya ta mayar da ita, ga masifa da tsawa da bala'i. Wani matsifaffen tsoronta Neehal take ji, gashi idan Uncle Umar ya dawo ta haɗa wa Neehal sharri a gurinsa wai ta zage ta, haka zai zo yay mata masifa shi ma kamar zai dake ta. Kullum Neehal sai ta ci kuka ta gode Allah, kuma duk wani abu na amfani da Aunty A'isha ta sako mata acikin kayanta Fauziyya ta k'wace, kama daga MacLean, sabulan Wanka hatta bargonta duk ta k'wace. Yau kwanan Neehal goma sha biyu a gidan Uncle Umar, amma gaba-d'aya ta rame ta yi duhu saboda wahala, baza ka taɓa cewa itace yar gatan Ummanta da Abbanta ba. Kitson dake kanta ya tsufa ya dugurguje, ga farcenta ya fara taruwa, ta saba duk ran Friday Aunty'nta tana yanke mata, haka ma Mama idan tana

Please Login or Register in order to submit comment