Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin na kammala school, a hakan ma idan ba'a tafi strike ɗin ƙasar nan na gado ba. Wannan wainar fulawar ta Ya Faruq ce ya saka ni in yi masa, kin san masoyiyarsa ce." Neehal ta ce "Faɗi gaskiya dai, wannan murjewar da kyawun da kika yi duk na mene ne?" Haneefah ta ce "Auran kenan Yarinya." Neehal ta waro Ido ta ce "Hmm, ya kk ya gida da school?" Haneefah ta ce "Lafiya k'alau, Alhamdulillah ya Mamana? Duk da fushi nake da Mama ta ƙi zuwa gidana." Neehal ta ce "Kin san Mama, ita fita wahala take mata." Haneefah ta ce "Daga gida kike ko school?" Ta ce "Daga gida mana, takanas na zo dan na gan ki." Haneefah ta yi murmushi ta ce "Kin kyauta kuwa, ki shiga falo ki huta kafin na ƙarasa." Neehal ta ce "Toh, Ya Faruq yana nan ne?" Haneefah ta ce. "Eh yana ɗaki, da na ji shigowar mota ma na ɗauka abokansa ne, ashe my Besty ce ta mun surprised." Neehal ta yi murmushi ta wuce ciki. Bayan Haneefah ta kammala wainar ta kaiwa Ya Faruq ɗaki tare da sanar masa zuwan Neehal, ya fito suka gaisa cikin fara'a. Haneefah ta kawowa Neehal abinci da drinks da wainar data toya, tana ci suna hira. Sai da suka yi Sallar la'asar lokacin Faruq ya fita sannan Neehal ta zayyanowa Haneefah problem ɗinta.












Haneefah data ƙura mata ido tana sauraren ta, ta numfasa ta ce "Yanzu Neehal ke a karan kanki kin kasa zaɓar wanda zuciyarki ta fi so, ta yaya wani zai iya zaɓar miki? Ke baki san wa kika fi so a cikin su ba?" Cikin damuwa Neehal ta ce "Wallahi ban sani ba Besty, na kasa tantancewa, idan ina tare da wannan sai in mata da waccan." Haneefah ta ce "To duk ba son su suke ba." Neehal ta dube ta cikin mamaki tare da faɗin "Kamar ya?" Haneefah ta ce "Kamar yadda kika ji na faɗa, ai shi wanda zuciya take so baya b'uya, Neehal da ace kina son Sadik ko Ahmad idan kina tare da ɗayan su ba zaki taɓa mantawa da wanda kikewa son gaskiya a ba a cikin su. Daga Sadik har Ahmad tausayin su kawai kike ji, ko kuma wani a cikin su yana miki wani abu da yake burge ki, and kuma kina duba halacci ko kyautatawar da sukay miki a rayuwarki, amma so dai da k'auna na soyayya ba kya yiwa Sadik da Ahmad. Ni nafi tunanin akwai wanda zuciyarki take so, wanda ke kanki baki sani ba." Neehal ta ɓata fuska ta ce "Ni babu wani wanda nake so daban kuma, to wani saurayin ne dani bayan su da zan so shi?" Haneefah ta ce "Wanda ba kya taɓa mantawa da shi a cikin ranki, ko da kuwa kina tare da Sadik da Ahmad. Indai akwai wanda kike jin haka a kan shi to shi kike so." Neehal ta tab'e baki ta ce "Babu shi gaskiya, kema kin sani." Haneefah ta ce "Lokaci ne zai faɗa mana haka, amma now back to our business, wa kike ganin hankalinki ya fi kwanciya da shi a tsakanin su?" Neehal ta ce "Wannan ita ce tambayar da Mama tay mun, kuma na kasa tantancewa, shi yasa na zo mu haɗu mu tantance." Haneefah ta ce "Indai a yanda kika bani labari ne gaskiya zan fi so ki auri Sadik, saboda yanda yake da rauni akan soyayyar ki, kece mace ta farko da Sadik ya fara so a rayuwarsa, idan kika rabu da shi saboda Ahmad kin zalunce shi, saboda sai da ya gama sakankancewa ya samu mata sannan kuma ki canza zance. Time ɗin da Ahmad ya dawo cikin rayuwarki already kuna tare da Sadik, dan haka yanzu idan kika bar shi kin yaudare shi, kuma hak'k'in shi ba zai barki ba. Sannan kuma ki duba yanda danginsa ba kowa ke son ku tare ba, idan kika rabu da shi kika watsa masa ƙasa a ido za ai masa dariya, ace shi yana ta wahala a kanki ashe ma ke ba k'aunar sa kike ba, kuma Sadik ya riga Ahmad fara sonki." Neehal ta yi sauri ta ce "Uncle Ahmad ya riga, na faɗa miki fa tun ina yarinya farkon haɗuwar mu yake so na." Haneefah ta ce "Ai wancan lokacin daban, kuma ya wuce. Zancen yanzu ake da girmanki, amma ni dai shawara nake baki, dan ni Baban twins ɗin nan ma bai wani mun ba, ya miki tsufa, gwara ki auri saurayi ɗan shawalwali wanda zaku fi jin daɗin rayuwar auranku. Kuma na lura kalaman Ahmad da iya tsara mace ne suke rud'ar ki a kansa, dan na san ki da son soyayya, da son a nuna miki k'auna." Neehal ta ce "Ni duk ba wannan nake dubawa ba, ina duba taimakon da yay mun a baya, ni kuma yanzu yana buƙatar nawa sai in ƙi taimaka masa? Kuma ga yaransa da muka shak'u da su, bana son rabuwa da su" Haneefah ta ce "Idan dan Allah yay miki ba zai yi wannan tunanin ba dan baki zaɓe shi ba, su Afrah kuma dan kin yi aure ai ba yana nufin kin rabu da su ba kenan, zaki cigaba da zumuncin ki da su, tunda Allah ne ya haɗa ku." Neehal ta yi shiru na tsawon mintuna biyu, sannan kamar zata yi kuka ta ce. "Haneefah! Uncle Ahmad yana so na Sosai, kuma duk abun da kika faɗa akan Sadik gaskiya ne, ya cancanci zama miji a gare ni, amma ban san da idon da zan kalli Uncle Ahmad na faɗa masa wannan maganar ba, Allah na yi dana sanin haɗa two dating at one time." Haneefah ta ce "Haka nan Sadik ɗin shima idan kika zaɓi Ahmad zaki ji nauyin sanar masa kin zaɓi wanin shi a matsayin miji. Neehal! matar mutum kabarinsa, tun kafin ki zo duniya Allah ya riga ya rubuta wanda zaki aura, ki yarda da wannan, ki kuma dage da addu'a da neman zaɓin Allah, tunda kin san dai baza ki auri maza biyu ba ko?" Neehal ta ce "Haka ne ƙawata, daren jiya ma kusan kwana na yi ina kaiwa Allah kukana tare da neman zaɓin sa." Haneefah ta ce "Yawwa, kisa a ranki kawai wanda kika zab'a shine mafi Alkhairi a gare ki, kuma shi Allah ya rubuta zai zamto mijinki." Neehal ta ji wani ɗan sanyi a ranta, lallai ta yarda shawara tana daɗi. A hankali kamar wadda aka tilasta mata ta ce "Na zaɓi Ya Sadik, Allah yasa haka shi yafi Alkhairi." Haneefah ta ce "Amin ya Allah, shi kuma Ahmad Allah ya bashi tasa matar mai Alkhairin." Kamar zata yi kuka ta ce "Amin, amma ban san yanda zai ɗauki wannan al'amarin ba, ina jin kamar ban kyauta masa ba." Haneefah ta ce "He is a Muslim, kuma ya san qaddara mai kyau da mara kyau, Insha Allahu zai fahimce ki. But I'm not forcing you Neehal akan Sadik, kawai ina baki shawara ne kamar yadda kika nema daga gurina, idan kin ji zuciyarki ta fi k'aunar Ahmad karki cuci kanki, ki zaɓi wanda kike so ki aura, dan aure ba abun wasa ba ne." Neehal ta ce "Hmm, Allah yasa ya fahimta ɗin. No, ni da Ya Sadik da Uncle Ahmad duk ɗaya ne a gurina, duk wanda na zab'a dai-dai ne, saboda duk sun cancanta." Ta yi shiru tare da ɓata fuska, sannan cikin damuwa ta ce. "Ni duk ba wannan ba ma, ina tsoron abun da ya faru a baya ya kuma faruwa." Sai ta fara hawaye sannan ta cigaba da magana. "Ina tsoron a kuma kashe mun wanda zan aura yanzu ma." Haneefah ta ɓata fuska ta ce "Oh my God, Neehal har yanzu baki daina wannan banzan tunanin ba, kin manta Allah ne me rayawa da kashewa." Neehal ta girgiza kai kawai ba ta ce komai ba, hawaye na cigaba da shatata a fuskarta. Haneefah ta matso ta rungume ta, cikin lallami ta ce. "Insha Allahu, Besty babu abun da zai faru sai Alkhairi, Allah yana sane da ke, ki miƙa masa k'ok'on bararki, shi kuma da yardarsa na san zai kawo miki ɗauki. Kuma duk wanda yake kisan nan matuƙar dan ke ake yi bisa zalunci da son zuciya Ubangiji zai saka miki cikin gaggawa, dan Allah yana karɓar addu'ar wanda aka zalunta. Kuma rayuwar mumuni bata tafiya sai da jarrabawa, ke kuma wannan ita ce taki jarabawar, amma in kika yi haquri sai ki ga komai ya wuce tamkar bai taɓa faruwa ba, be a good Muslim please Dear." Haka dai Haneefah tay ta nusar da Neehal da nasihohi da kalamai masu daɗi gami da ƙara mata k'warin gwiwa akan Sadik, daga baya kuma ta koma tsokanarta da matar Barrister, an kusa shiga daga ciki. Har ta ji zuciyarta ta mata sanyi, kaso mafi yawa na damuwar da take ciki ya tafi. Shi yasa take son Haneefah, because she is a good person, kuma ta san baza ta taɓa bata shawarar da zata cutar da ita. Amma wani b'arin na zuciyarta sai tambayar ta yake akan anya ta yiwa Ahmad adalci kuwa? Sai bayan Magriba sannan ta bar gidan, shi ma sai da Mama ta kira ta a waya, dan sosai ta ji daɗin kasancewa da Besty'nta_ta.........✍️












*By*
*Zeey Kumurya*
[10/03, 08:56] Zeey Kumurya: *⚡ NEEHAL⚡*










_By_
_Zeey Kumurya_














*5️⃣8️⃣*












Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I selling MTN data with this cheap price*


*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.
*Validity 1 month*


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp OR*
*Call 08066268951*131*4#*
















...........A falon sama ta tarar da Mama tana kallo. Ta tafi da murnarta ta faɗa jikinta tare da faɗin. "Oyoyo Mamana." Mama ta harare ta, ta ce. "Aina na ɗauka a can zaki kwana." Ta ƙara ruk'unk'ume ta tana murmushi ta ce "Sorry My Mum, hira ce ta yi daɗi." Mama ta ce "Ya yi kyau, idan da Daddy ya dawo sai ki faɗa masa hira ce ta yi daɗi shi yasa kikai dare." Ta yi dariya kawai, Mama ta ce "Ya kika baro Haneefan?" Neehal ta ce "Lafiya k'alau, tana gaishe ki." Mama ta ce "Ina amsawa." Neehal ta miƙe ta shige ɗaki. Kwanciya ta yi akan gado bayan ta ajiye handbag ɗinta da mayafinta. Ta kwanta rub da ciki tare da tallafe kanta da hannunta. Tunanin Ahmad take da irin tarin soyayyar da yake mata, har yanzu ta kasa amincewa da zaɓin da ta yiwa kanta, tana ganin kamar ba zata iya barin Ahmad ba a rayuwarta. To amma Sadik fa, kamar yadda Haneefah ta faɗa idan ta bar shi ta zalunce shi, ta cuce shi ta yaudare shi. Ta runtse ido cikin tsananin damuwa, ita bata taɓa dating two persons at one time ba sai wannan karon, ta yi dana sani mara iyaka, amma kuma babu yanda zata yi wannan ma is another addiction in her life. Ta tashi ta ɗauko jakarta jin wayarta na ringing a ciki, Sadik ne yake kiran ta. Ta d'aga cikin ƙoƙarin ganin bai fuskanci tana cikin wata damuwa ba, gaisawa kawai sukai ya tambayi lafiyarta saboda lokacin Sallah da ya gabato. A daren ranar ta sanar da Mama Sadik ta zaɓa, Mama ta ce Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi. Washegari da safe Mama ta ce mata gobe Sunday ta cewa Sadik ya zo Daddy yana son ganin sa. Kamar zata yi kuka ta ce, "Toh Mama zan faɗa masa, amma Mama har yau na kasa sanar da Uncle Ahmad, wallahi ban san ta yaya zan faɗa masa ba, kuma na san zai yi wahala ya ƙi zuwa yau ko gobe." Mama ta ce "Shikenan idan ya zo ni zan masa bayanin da zai fahimta da kaina." Ta gyaɗa mata kai tana ƙoƙarin ganin bata bar hawayen idonta ya zubo ba. Ta tashi ta koma ɗakinta dan zata iya fashewa da kuka saboda yanda take jin zuciyarta, ita kuma bata son ta yi kuka a gaban Mama. Tana hawaye ta yiwa Sadik text ta sanar masa abun da Mama ta ce ta faɗa masa. Ta kwanta tana kukan da bata san dalilin shi ba. Tana jin wayarta tana ringing amma bata bi ta kanta ba. Sai da ta gaji dan kanta sannan ta yi shiru, ta tashi ta ɗauki wayar ta duba ta ga Sadik ne ya kira ta, da ya ga bata ɗauka ba yay mata reply ɗin text ɗinta, tare da daɗaɗan kalaman soyayya a ƙarshe. Ta yi ɗan murmushi, sannan ta tashi ta je ta wanke fuskarta. Bayan Sallar Azhar tana zaune a ɗakinta da materials ɗin karatun ta tana dubawa. Mama ta shigo ɗakin ta ce mata. "Neehal Ahmad ya zo." Ta d'ago da sauri gabanta na wani irin fad'uwa saboda razana. Mama data kula da yanayin da ta shiga ta ce. "Ki je ku gaisa, yana ƙasa yana jiranki, kuma karki nuna masa wani abu, idan zai tafi i will explain to him." Neehal ta gyaɗa mata kai kawai. Kamar wadda k'wai ya fashewa a ciki ta tashi cikin sanyin jiki ta yane kanta da mayafin abayar dake jikinta. Ta ɗan gyara fuskarta sannan ta fesa turare kaɗan, sannan ta fice daga ɗakin cikin matuƙar sanyin jiki.










As always yana zaune akan carpet idanunsa akan steps. Ta sakko cikin nutsuwarta kanta a ƙasa, gabanta na cigaba da faɗuwa ta zauna a kusa da shi tare yin sallama. Yana murmushi ya amsa mata. Ta ce "Ina yini Uncle." Ya ce "Lafiya k'alau Princess, ya weekend?" Ta ce "Alhamdulillah." Ya ce "Ya School da aiki?" Ta ce "Alhamdulillah." Ya gyara zama tare da juyowa ya fuskance ta sosai ya ce. "Kin yi kyau, kullum kamar ƙara miki kyau ake Princess." Ta d'ago tare da ƙirƙirar murmushi akan fuskarta a ƙoƙarin ta na ganin bata nuna masa akwai wata damuwa ba, ta ce. "Ni ɗin kuwa?" Ya ce "To da wa?" Ta sake yin murmushi ta ce. "Ina Yarana?" Ya ce "Suna gida." Ta ce "Da fatan dai suna lafiya, kuma baka barin wani abu yana damar mun su?" Ya kafe ta da ido ya ce. "Suna lafiya, ni kam me zan bari ya damu ƴaƴan Aunty? Ai lallaɓa su nake kar Aunty ta ce ta fasa Aure na." Ta yi ƙasa da kanta da sauri saboda yanda ta ji bugun zuciyarta ya sauya, ta hasaso yanda yake cikin farincikin nan da nishad'i ya zai ji idan Mama ta yi masa bayanin ta kusa zama mallakin waninsa, daga yau ba zai ƙara zuwa su yi irin wannan zaman ba, duk soyayyar da ya nuna mata ta zama tahiri, a...... "Princess.!" Ya katse mata tunani ta hanyar kiran sunanta. Ta d'ago tay masa kallon cikin ido cikin dakiya. Ya lumshe ido ya buɗe su a cikin nata ya ce. "Tunanin me kike?" Ta ce "Babu komai Uncle." Ya karyar da kai ya ce, "Let me snap you, kin mun kyau sosai yau." Ya ɗauko wayarsa yay mata pictures, ita kuma tana ta murmushi, sannan ya ɗauke su tare. Ta karɓi wayar tana dubawa, hotunan sun yi kyau sosai. Ta yi murmushi ta cigaba da kallon pictures ɗin wayar, wanda fiye da rabi na twins ne. Ta tura wanda yay musu yanzu sannan ta tuttura wasu na twins da nasa ta whatsapp. Mama da kanta ta sakko ta shiga kitchen ta zubo masa abinci ta kawo masa, ya dinga yi mata godiya cikin jin kunya. Bayan Mama ta koma sama ya dubi Neehal ya ce. "Ina son Mama sosai, saboda kirkinta, da sanin darajar ɗan Adam gami da karamci." Ta yi murmushi kawai, sannan ta zuba masa abincin, yana ci suna hira, wanda Neehal ta ji kusan rabin damuwarta ta tafi. Sai da aka kira Sallar la'asar sannan ya tashi ya je masallaci ya dawo. Neehal bata sakko ba tana ɗakinta akan darduma bayan ta idar da Sallah, addu'a take yi akan Allah ya sanyayawa Ahmad zuciyarsa, Allah yasa kar abun da Mama zata faɗa masa ya yi hurting heart ɗinsa over.








Jin dawowarsa Mama ta sakko ta zauna akan kujera sannan cikin kulawa ta ce. "Neehal ta faɗa maka za mu yi magana ko Doctor?" Cikin fad'uwar gaban da bai san ko ta mecece ba ya ce "Eh Mama." Mama ta danne tausayinsa dake cikin ranta ta fara yi masa bayani, cikin tausasan kalamai ta yanda zai fuskanta. Da farko ji yay kansa ya masa wani irin juyawa, yawun bakinsa ya kafe kaf, dak'yar ya iya had'iye wani abu mai ɗaci da ciwo daya tsaya masa a mak'oshi ya ce. "Babu komai Mama, na fahimce ki, Allah kuma yasa hakan shi ya fi Alkhairi a gare mu gaba-ɗaya." Ya yi maganar cikin tsananin dauriyar zafin da zuciyarsa take masa. Bai kuma fuskantar abun da Mama take kuma faɗa masa ba, ya dai ji kamar haquri take ba shi da kuma ƴar nasiha. Ya gyaɗa mata kai kawai, ita kuma ta tashi ta nufi upstairs tana faɗin bari ta turo masa Neehal ɗin su yi Sallama. At the first bayan barin Mama falon ya d'ago kansa tare da lumshe idonsa yana fatan ya kasance mafarki yake ba gaske ba ne abun da Mama ta sanar masa. Ya yi imagine wai hakan na nufin ya rabu da Princess ɗinsa kenan har abada, nan da wani ɗan lokaci za'ai mata aure da wani ba shi ba. Innalillahi,wa'inna'ilaihirraji'un ya shiga maimaita a fili cikin sanyin murya mai cike da damuwa, har ya ji ya fara ɗan samun salama a cikin ransa. Neehal wadda da ƙyar Mama ta yaƙo ta, ta fito saboda ta ce bata san da idon da zata kalle shi ba, ta ƙaraso falon idanunta na shatatar hawaye, da ƙyar take iya ganin gabanta. Ya ƙura mata ido cikin sarewa da karayar zuci, karon farko a rayuwarta ta faɗa jikinsa tare da fashewa da kuka. Ya runtse ido ya buɗe saboda yanda kukan nata yake taɓa masa zuciya. Ya tsotsi lips ɗinsa da suka bushe lokaci ɗaya saboda damuwa cikin marainiyar murya ya ce. "Please Princess Stop crying, ko so kike nima in yi kukan?" Ta girgiza masa kai. Ya d'ago kanta da hannunsa ɗaya, ɗayan kuma ya shiga share mata hawaye da shi. Ta bar jikinsa tana sakin ajiyar zuciya. Cikin muryar kuka ta ce, "I'm so sorry Uncle, I..." Ya katse ta da faɗin. "Me kikai mun Princess da zaki bani haquri? Na fuskanci bayanin Mama kuma na gamsu. Princess! Ba mu muke da ikon tsarawa kanmu rayuwa ba, Allah ne yake tsara mana. I'm a Muslim, na yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau, tabbas rasa ki a cikin rayuwata ba ƙaramin rashi ba ne, amma kuma babu yanda zamu yi da ikon Allah. Karki damu akan wannan Please Princess, I knew you love me so much." Ta kalli fuskarsa yay mata murmushin da ya fi kuka ciwo tare da kamo hannunta ya ce. "Princess! Sau da yawa abun da zuk'atansu suke so ba shine Alkhairi a gare mu ba, sai mu ga wanda bama so ɗin ya fi zama Alkhairi a gare mu. Duk da na san kina son guy ɗin da zaki aura ba wai auren dole za'ai miki ba. Amma ko kaɗan ban ji a raina kin yaudare ni ba or something like this, abun da kikai shine dai-dai, kuma shine adalci. Tunda shi guy ɗin he came first before I came, abun da baza ka so ai maka ba kaima karka so kaiwa wani, dan haka ki daina damun kanki indai ni Ahmad ne na haqura, dama rayuwa cike take da farinciki da baƙinciki, idan ka yi haquri kuma zaka ga ribarsa a gaba, kuma komai zai wuce kamar bai faru ba." Ya yi shiru yana sauke numfashi, dan shi kansa ya san ba ƙaramin dauriya yake ba wajen ɓoye mata damuwarsa. Ta ƙura masa ido cikin mamakin kalamansa zuciyarta cike da tsantsar tausayinsa, ta san daurewa kawai yake dan ya ga ta damu kar ta tashi hankalinta. A hankali ta ce "Thank you so much Uncle, for your cares and everything to my life." Ya yi irin murmushin d'azu ya ce. "Nima na gode da k'aunar da kika nuna mun Princess, and I will never forget you in my life. Na gode Na gode sosai, da k'aunar kike wa ƴaƴana. Allah ya yiwa rayuwarki albarka, ya baku zaman lafiya ke da mijinki idan kun yi aure, ya kuma baku zuri'a d'ayyiba." Ta ce "Amin Uncle tare da kai." Ya ja karan hancinta ya ce, "Zan wuce sai mun zo biki." Dan ba ƙaramin dauriya yake ba, so yake kawai ya kadaice ya rarrashi zuciyarsa. Ta lumshe ido hawaye ya zirnano daga cikin idanunta. Kamar zai yi kuka ya ce. "Oh My God Princess, dan Allah ki bar kukan nan, baki san yadda nake jin zafi a cikin raina ba idan kina yi. Ta share hawayen bayan ta zare hannunta daga cikin nasa ta ce. "Na daina Insha Allah Uncle." Ya ce "Promise to me ko na tafi baza ki yi kuka ba." Ta ja hanci a hankali ta ce. "Ba zan yi ba Uncle Insha Allah." Ya shafi kuncinta ya ce, "Good lady, yanzu fa kin girma Princess, ko kina so twins ɗinki su gan ki kina kuka?" Ta girgiza masa kai. Ya ƙara kamo hannunta ɗaya ya ce. "Tashi mu je ki raka ni." Ta kalle shi sannan ta tashi ganin shima ya miƙe. Ya taune lip ɗinsa jin kamar zai faɗi tare da dafa hannun kujera yana ambaton sunan Allah. Ta ƙura masa ido kawai cikin damuwa. Ya d'ago yana murmushi ya ce, "Wannan kallon fa?" Ta ƙara waro masa manyan kyawawan idanunta haɗe da juya masa su sannan ta lumshe su a hankali. Salon nata ya shige sa ba kaɗan ba, bai san sanda ya dafa kafaɗunta ba ya yi kissed saman idanun, a hankali kuma ba tare da ta taɓa zato ba ta ji saukar lips ɗinsa akan nata. Ta sauke wani gwauron numfashi lokacin da ta ji yana kissing ɗinta, kafin a hankali ya janye fuskarsa daga ta_ta. Cikin raunin murya ya ce, "Good bye Princess, I love You.!" Sannan kamar wanda aka tsikara ya juya da sauri ya fice daga falon. Sai buɗe idanunta ta yi ta ga babu shi sai k'amshinsa da ya bar mata a jikinta da falon. Ta ja ƙafafuwanta da sukay mata nauyi ta ƙarasa kujerar dake kusa da ita, ta faɗa kanta ta fashe da kuka, a ranta tana faɗin. 'This means daga yanzu mun rabu da Uncle, rabuwa ta har abada.' Ta cigaba da kukan ta a gurin, ta ma manta da alƙawarin data ɗaukar masa na baza ta kuma yin kuka ba, akan rabuwar ta da shi.












Da ƙyar Ahmad ya iya jan ƙafarsa ya je parking space, yana zuwa ya buɗe Motar da ya zo da ita ya shiga ya zauna ya ɗora kansa akan sitiyarin Motar, yana jin zuciyarsa tamkar zata soye saboda zafin da take masa. Ganin abun yake tamkar almara, domin bai taɓa tunanin zai ƙara rasa Neehal a karo na biyu ba. Amma ya yadda da ƙaddara, ya kuma yarda wani ba ya taɓa auran matar wani. Zai dage da addu'a akan Allah ya cire masa sonta ko da ba duka ba daga cikin ransa, ya kuma bashi mace ta gari wadda zata kula da shi da marayun ƴaƴansa. Sai dai ya rasa me yasa wani b'arin na zuciyarsa yake tabbatar masa da bai rasa Neehal ba, yake nuna masa zai mallake ta. Ya sauke numfashi tare da addu'ar idan rabonsa ce ita, Allah ya bashi, zai je ya dage da addu'a. Sunan Allah yay ta maimaita a ransa, har ya ɗan samu nutsuwa. Cikin dauriya ya kunna Motar ya fice daga gidan bayan an buɗe masa gate ya nufi gidan Mamy. Yanda Mamy ta ganshi ya shigo a sanyaye kamar mai cuta ta san da matsala, a ɗan rikece ta tambaye shi me nene? Kamar zai ɓoye mata sai kuma ya sanar mata. Itama Mamy ta ji ba daɗi a ranta sosai, domin ta yiwa Ahmad sha'awar Neehal, dan ta yaba da hankalinta da nutsuwarta. Amma sai ta kwantar masa

Please Login or Register in order to submit comment